MUSABBABI CHAPTER 12 BY HAJ HABIBA

ita, don haka babu komai, addu’a za mu ci-gaba kawai da yi akan Allah ya daidaita rayuwarsa. Ya dawo da shi kan hanyar daya bari, mu shi ne addu’a da bukatarmu.” Tun daga wannan lokacin. Musaddik yake rayuwa ba iyali, hakan ya sa komai ya Kara lalace masa, ragowar dan burbushin kimarsa da ake gani, aka daina gani. Daga bisani gidan da yake ciki daya mallaka ma Hannatu. Hajiya Kilishi ta daga ta sayar. Hakan ya sa’ ya dawo ainihin dakinsa na gidan mahaifinsa, ya ci-gaba da zama cikin tashin hankalin rayuwa. Hajiya Kilishi ta kira mahaifiyar Hannatu suka zauna, abinda ta ba su a cikin kudin gidan Musaddik da ta sayar Naira miliyan bakwai, su ne a matsayin kasuwancin da ta yi da Hannatu. Ta ji dadin yadda yayarta ta cika masu alkawari, wanda ba ta taba zaton za su tashi da wadannan makudan kudin ba, idan tayi la akari da son kai irin na yayarta. Suka kunshe kudadensu, sannan ta tafi da ‘yarta cikin matsanancin farin-ciki da jin dadi mara misaltuwa.Hajiya Kilishi kuwa ta zama harshakiya, don yanz…