MUSABBABI CHAPTER 12 BY HAJ HABIBA

ita, don haka babu komai, addu’a za mu ci-gaba kawai da yi akan Allah ya daidaita rayuwarsa.

Ya dawo da shi kan hanyar daya bari, mu shi ne addu’a da bukatarmu.” Tun daga wannan

lokacin. Musaddik yake rayuwa ba iyali, hakan ya sa komai ya Kara lalace masa, ragowar dan burbushin kimarsa da ake gani, aka daina gani.

Daga bisani gidan da yake ciki daya mallaka ma Hannatu. Hajiya Kilishi ta daga ta sayar. Hakan ya sa’ ya dawo ainihin dakinsa na gidan mahaifinsa, ya ci-gaba da zama cikin tashin hankalin rayuwa.

Hajiya Kilishi ta kira mahaifiyar Hannatu suka zauna, abinda ta ba su a cikin kudin gidan Musaddik da ta sayar Naira miliyan bakwai, su ne a matsayin kasuwancin da ta yi da Hannatu.

Ta ji dadin yadda yayarta ta cika masu alkawari, wanda ba ta taba zaton za su tashi da wadannan makudan kudin ba, idan tayi la akari da son kai irin na yayarta.

Suka kunshe kudadensu, sannan ta tafi da

‘yarta cikin matsanancin farin-ciki da jin dadi mara misaltuwa.Hajiya Kilishi kuwa ta zama

harshakiya, don yanzu tana daya daga cikin matan da suke cikin jin dadin rayuwa wadanda ba su nemi komai sum rasa ba. Dukkan burinta ya gama cika.

Tana cikin jin dadin rayuwa mara misaltuwa. Akalla a yau Afrah da Musaddik sun sami kimanin wata uku da aure, amma koda sau daya Afrah ba ta ta6a samun farin-ciki daga Musaddik ba, duk da yana kokarin faranta mata, amma hakan baya tasiri, domin Musaddik kwata-kwata baya zaman gida.

Wata rana ma a waje yake kwana, duk yadda Afrah ta dauki lamarin, ya wuce nan.

Saboda haka ta daukar ma kanta yin hakuri da juriya akan Musaddik, domin ta tabbatar da cewa lalle yana bukatar taimako, don haka ya sa ba ta taba nuna damuwarta akan dabi’un nasa ba, hakan ko shine abinda ya fi kona ma Hajiya Kilishi rai. Ta rasa wace irin mace ce Afrah?

Ta kuma kasa gane da manufar da ta auri Musaddik, domin dai a cikin wata ukun nan.

Musaddik ya yima Afrah abubuwan daya kamata ace ta gudu ta bar shi.

Amma sai ta ga ko a kwalar rigarta, tamkar ba ita yake wulakantawa ba tare da nuna mata mugayen halayensa karara! Hakan ya sa Hajiya Kilishi ta dau tsanar duniya ta dora akan Afrah, ko kadan Afrah ba ta jin dadinta, haka zalika ba ta taba ba ta koda abincin gidan ta ci ba, garar da Malam Mahmud ya yi mata, ita take ta ci.

Shi kansa Musaddik har yanzu babu abinda ya fara sayowa ya kawo gidan a matsayinsa na mijinta. Hutun da ta dauka na Islamiyya, ya kare. don haka ta nemi izinin mijinta akan za ta koma makaranta. Ya amince mata, domin dama ya sani, akan haka kuma ya amince.

Komawarta makaranta ta fara samun sassaucin damuwa, domin ko banza tana samun shawarwari da karfafa guiwa daga Ya Sayyadi Habib, domin dai ba ta boye masa komai ba akan halin da take ciki da Musaddik.

Sai dai shi kadai ne ya san gaskiyar halin da take ciki. Domin ko mahaifinta ta boye masa, duk da ya san dole akwai matsala. Amma bai yi tsammanin ta kai yadda ta kai ba.

Don haka ita ma ta sakaya. A kullum tana nuna masa akwai sauki a al’ amuran, hatta halin da take ciki da Hajiya Kilishi ba ta gaya masa ba, ba ta kuma sanar da Inna Halima ba, domin kwanciyar hankalinsu take bukata, ba tashin hankalinsu ba.

Afrah ta ci-gaba da boye dukkan wani sirri na auranta, ta kuma daukar ma kanta alkawarin hakuri da juriya da dukkan halayensa, duk da babu soyayyarsa a ranta, to za ta cika dukkan wani hakki nasa da Allah ya dora a kanta, don haka ta daukar ma kanta hakurin zama da shi tare da. yi masa addu’a, domin ita ce abinda ya fi bukata.

Yau Alhamis ne. Afrah ba ta da makaranta, don haka ta kwaso kayan. Musaddik da suka cika mata daki da wari ta fara wankewa, bakin-cikinta daya, duk rigar da ta sa hannunta a cikin aljihun, sai ta tsinci karan sigari ko Kullin wiwi, a gefe ta yi ta tarasu, da nufin idan ta gama wankin, ta kwashe ta zubar. Tana tsaka da wankin ne ta ji sallamar Mama Hauwa da Na’ima.

Cike da fara’ a ta taresu, domin dai tunda ta y aure ko da wasa Mama Hauwa ba ta ta6a zuwa ganin dakinta ba sai yau. “Sannu da zuwa Mama, ku shiga dakin mana.

Mama Hauwa ta yamutsa fuska ta dubi tulin kayan da take wamkewa da tsubin kayan maye a gabanta, ta ce “Tafdijan! Allah me yadda ya so.

Sannu da bautar aure Afrah”.

Ta fada tana wucewa dakin. Afrah ta wanke hannunta, ta bi bayansu, amma ga mamakinta, tana shiga dakin ta tarar da su a tsaye cirko-cirko

“Mama, Na’ima ku zauna mana.” Na’ ima ta dubi mahaifiyarta sannan ta dubi Afrah ta ce “Ba zama za mu yi ba sauri muke yi’

Mama Hauwa ta ce “Me zai hana ki gaya mata gaskiyar cewa dakin nata wari yake yi, ba za mu iya zama a ciki ba. Meye ke wari haka a dakin naki? Na san dai ke ba kazamiya bace, amma ban sani ba ko har Musaddik ya canja miki hali ne irin nasa na kazanta. Don na san ko wanka baya yi.

Fatarsa ma ta nuna hakan”

Afrah ba ta ji dadin yadda Mama Hauwa ke fadin irin wadannan maganganu ba, ta dan dubeta ta ce “Ni ma ban san meke wari ba, amma na fi yarda da tunanin ko bera ne ya mutu”

Mama Hauwa ta tabe baki tana kare ma dakin ta kallo ta ce “Biyayya ta yi rana Afrah, tunda mahaifinki ya kawata miki daki, ya maida ke cikin sahun ‘yan gata, ya yi miki kokari kwarai da gaske, tunda dakinki ya fi na sauran yan-uwanki kawatuwa”

Ta Kara kallonta ta ce “Sai dai ban damu ba, tunda sun fiki sa’ar miji na-gari, don haka na san duk wannan daular da aka zuba miki, babu abinda za su tsinana miki, tunda ba za su kawo miki farin-ciki ba.”

Ta kara kallonta ta ci-gaba da cewa “Dubi kayan mayen da suke gabanki, kalli yadda ki ke tikin yi masa wanki, wanda duk ba shi zai sa ya canja ba.”

Na’ima ta dan gyara tsayuwarta ta ce “Ai

Mama ni Allah ya taimakeni da wannan jifan ya wuce kaina. Allah ya dubeni da idon rahama, da ba ni bace matarsa”. Mama Hauwa ta ce “Ai ke aka so a bata ma rayuwa, amma Allah ya kubutar da ke, uwar biyayya ta fanshek”

Afrah ta goge hawayen da ya fara zubo mata, ta yi zaton sun zo ganin dakinta ne, ashe cin mutunci ne ya kawosu. Ta koma ta zauna ba tare da ta ce komai ba. Haka Mama Hauwa ta ci-gaba da maganganunta na tozartarwa, amma har ta yi ta gama. Afrah ba ta ce uffan ba. Mama Hauwa ta mika hannu saman firiji ta dauko wata bakar leda, ta fice ita da Na’ima. Afrah ta mike da nufin rakasu, amma ga mamakinta suna fitowa, sai ta ga Mama Hauwa ta dur kusa ta kwashe tarkacen kayan mayen da ta tara, ta dura a cikin ledar. A nan ne Afrah ta dubeta ta ce “Mama me za ki yi da su?”Ta balla mata harara ta ce «Zan kai ma mahaifinki tsarabar da na samo daga gidanki ne.” Gaban Afrah ya yi mummunian faduwa, da sauri ta karasa gabanta ta cencikin magiya “Don Allah, Mama kada ki yi min haka, kada ki tayar ma da Baba hankali, mèye amfanin yin hakan?”

Ta kara sakar mata harara ta ce “Tashin hankalin me zai yi, bayan duk wanda ya sai rariya, ya san za ta zubar da ruwa, ke mu tafi da Allah”. Ta ja hannun Na’ima suka fice ba tare da ta damu da magiyar da Afrah take yi mata ba.

Haka Afrah ta kasance a cikin bakin-ciki.

Bayan tafiyarsu Mama Hauwa da kyar ta gama wankin, amma ta kasa yin guga, haka ta ninke ta ajiye, hatta abincin da tayi, ta kasa ci, saboda damuwa, ga Musaddik tun safe daya fita, har yanzu bai dawo ba.

Ta bangaren Mama Hauwa kuwa, haka ta kasance cikin nishadi da farin-ciki, bayan komawarta gida. Har sai da Malam Mahmud ya dawo, bayan sallar Issha’i, ya zauna kan tabarma, ta kawo masa tuwo, zai fara ci kenan, saboda wulakanci da rashin mutunci, kawai sai ta koma ta zauna kan kujera ‘yar tsugunno tana murmushi ta ce.

“Ba ka tambayeni yana baro Afrah ba, bayan ka san na ce maka zan je gidanta yau?” Ya dan dubeta ya ce “Na san lafiya lau take ai, shi ya sa ban tambayeki ba, kuma ko kadan, kada ki bari jama’a su san cewa sai yau ki ka je gidan Afrah, domin abin kunya ki ka yi. Ace tsawon wannan lokacin ba ki je kin ga dakinta ba, sai yau. Ta tabe baki ta ce “Idan jama’ar suka ji, me za su yi min? Dole ne na je akan lokaci? Ba sai na sami lokaci ba, sannan zan je.’

Ya juya kan tuwonsa zai fara ci, ba tare daya Kara magana ba. Amma sai ta Kara katse shi, tamkar tana yi masa bakin-ciki da cin tuwon ta ce.

“Na je na tadda ita tana ta aikin yima mijinta wanki, gama tsarabar dana taho maka da ita daga cikin wadanda yake ragewa a aljihun wandonsa.

Malam Mahmud ya juya yana kallon kayan mayen da take zazzagewa masa a gaba, a fusace ya ce «Meye haka Hauwa?” Ta ce “Kayan mayen Musaddik ne, na taho maka da su domin ka gani”

• Ya yi mata wani mummunan kallo ya ce.

«Amma Hauwa ba ki da mutunci, to yanzu da ki ka kwaso min, idan na gani, me zan yi, meye kuma amfanin kawo min?” Ta tabe baki ta ce “Haka ne fa kuma, babu amfanin na kawo maka, tunda ka riga ka sani, ka san komai, amma ka dauki

‘yarka ka ba shi

Hakika ni ma na fara tunanin akwai abinda ka ke hange a gun Musaddik, da ya sa ka ba shi auran

“yarka, don idan ba hangen dukiya ba, ban ga dalilin da za ka kashe ma *yarka rayuwa da auran

Musaddik ba.

Malam Mahmud ya buga tsaki ya ce “Dukiya, dukiyar banza, me Musaddik din ya aje? Kin sani, na sani. Musaddik komai nasa ya Kare, tabbas ina da manufar hada su aure.

Amma ba irin manufar da ku, kü ke tunani ba, don haka Afrah ‘ya ta ce, ni na ga damar yin hakan da ita. Kuma ina gargadinki da ki fita harkata da ta

“yata, tunda ba ‘yarki bace balle ki ce ban isa na yi iko da ita ba’

Mama Hauwa ta mike “Eh ai dama ban ce

“yata bace, ba kuma na fata ta zama ‘yar tawa.” Ya ce “Na ji, ki tafi ki ba ni waje, kuma kada ki Kara takawa gidan Afrah balle har ki je ki sa idon daukar magana, babu ruwanki da ita, balle mijinta”

Ta yi shewa ta ce “To sai me? Sai ka ce wani mijin kirki, gidan Afrah kuma ba zan Kara zuwa ba, tunda ba aljanna ake rabawa a can ba, ga kayan mayen nan, idan ka gama gani, sai ka san inda za ka aje

• Ta saki tsaki ta shige daki ta rufe kofarta. Malam Mahmud ya Kura ma kayan mayen ido,

idanunsa cike da hawaye, hakika ba haka ya so

rayuwar ‘yarsa ta kasance. ba, amma babu yadda ya

iya, haka Allah ya kaddara.

Tausayin Afrah ya kara kama shi, a hankali ya

janyo kayan, ya kwashe ya maida su cikin ledar,

,cikin matsanancin tashin hankali, ya ture kwanon

tuwon gefe, ya tashi ya nufi bandaki, ya jefasu

cikin masai. Sannan ya shige dakinsa ya kulle

kofarsa ba tare daya ci tuwon ba.

Washegari kuwa cike da damuwa Malam

Mahmud ya je gidan Inna Halima, ya gaya mata

komai gami da yi mata umarnin ta je ta kara karfafa ma Afrah guiwa tare da ba ta hakuri. Inna Halima

ba ta yi kasa a guiwa ba, ta nemi izinin mijinta, ta

tafi gidan Afrah. Wanda Afrah ta ji dadin ganinta, amma tana fara mata maganar Musaddik. Ta san

Mama Hauwa ta je ta yi abinda take zaton za ta yi.

Ta dubi Inna Halima ta ce “Inna me zai sa ku

tashi hankalinku, don kawai Mama Hauwa ta je ta

gaya maku abinda ku ka riga ku ka sani? Kun san

Yaya Musaddik ba mutumin kwarai bane, akan wannan dalili ne ma na aure shi, to me zai sa ku

damu? Bayan addu’ a kawai ya kamata ku bi mu da shi” Inna Halima ta jinjina kai ta ce “Maganarki haka take Afrah, don haka Allah yayi maku

albarka, ya taimake ki akan duk abinda ki kasa a gaba”. Ta amsa da “Amin Inna”. Ta dan dubeta ta ce “Amma Afrah yaya zamanku, ki na jin dadin zama da shi, kuma ki na ganin akwai alamun yana rage mugayen dabi’unsa, ma’ana ana samun canj! kuwa?”

‘Afrah ta danyi murmushi me kama da yake ta ce “Inna ai Yaya Musaddik yana da dadin zama kwarai, kuma ana samun canji da abubuwa da dama ákan halayensa, sai dai mu ci-gaba da addua kawai.”

Fuskar Inna Halima ta cika da fara’a da jin dadi tace “Alhamdulillahi. Allah ya Kara taimakawa. Allah ya saka miki da alheri.”

Duk wasu tambayoyi da Inna Halima tayima

Afrah, tana kokarin ba ta amsar da za su sata farin-ciki, ta kuma yi sa’a har ta bar gidan, ba ta fahimci

Karya ko daya a cikin maganganun Afrah ba..

Hmmmm