MUSABBABI CHAPTER 11 BY HAJ HABIBA

yi yawa gaskiya, kuma ni ban goyi bayan wannan shawara ta ki ba. Shin ba kya ma tunanin ko Musaddik ya rasu, ‘yan-uwan mahaifiyarsa za su iya bin kadin dukiyar Musaddiq daya mallaka miki, ba gara kin bar shi a raye, shi ya gaya ma duniya da kowa ma cewa shi ne ya mallaka maku dukiyar ba. Idan ko mai kaya ya ce ya bayar, to waye ya isa ya ce bai bayar ba? Idan kuma ki na tunanin shi • zai yi miki bore wata rana ne, ai akwai wata hanyar da ta fi wacce ki ke son bi saukin bi.” Hajiya Kilishi cike da gamsuwa da maganganun Hajiya Rakiya ta ce “Wace. hanyar ce?” Hajiya Rakiya ta ce “Ba sai a lalata rayuwarsa ba, a raba shi da kyakkyawan tunani, a hana shi shiga cikin mutanen kirki, balle har shawarwarinsu su yi tasiri wata ran a rayuwarsa. Me zai hana a kwace kwarjini da kamalar da jama’a suke ganinsa da ita, ina nufin a hada shi da shaye-shaye, domin shaye-shaye shine tushen lalacewar rayuwar duk wani matashi. Shine kuma zai zama abin kyama a wajen mutanen kirki.”Ta gyara zama tana kallon aminiyar…