MUSABBABI CHAPTER 11 BY HAJ HABIBA

yi yawa gaskiya, kuma ni ban goyi bayan wannan shawara ta ki ba.

Shin ba kya ma tunanin ko Musaddik ya rasu,

‘yan-uwan mahaifiyarsa za su iya bin kadin dukiyar

Musaddiq daya mallaka miki, ba gara kin bar shi a raye, shi ya gaya ma duniya da kowa ma cewa shi ne ya mallaka maku dukiyar ba.

Idan ko mai kaya ya ce ya bayar, to waye ya isa ya ce bai bayar ba? Idan kuma ki na tunanin shi

• zai yi miki bore wata rana ne, ai akwai wata hanyar da ta fi wacce ki ke son bi saukin bi.” Hajiya

Kilishi cike da gamsuwa da

maganganun Hajiya Rakiya ta ce “Wace. hanyar ce?” Hajiya Rakiya ta ce “Ba sai a lalata rayuwarsa ba, a raba shi da kyakkyawan tunani, a hana shi shiga cikin mutanen kirki, balle har shawarwarinsu su yi tasiri wata ran a rayuwarsa.

Me zai hana a kwace kwarjini da kamalar da jama’a suke ganinsa da ita, ina nufin a hada shi da shaye-shaye, domin shaye-shaye shine tushen lalacewar rayuwar duk wani matashi. Shine kuma zai zama abin kyama a wajen mutanen kirki.”Ta gyara zama tana kallon aminiyarta ta ce Ina jinki.

. Hajiya Rakiya ta ci-gaba da cewa, “Kin ga kuma mutane ba za su tada zarginki ba, za su dauka don dukiyar da aka bar masa ne ya canja halinsa da kuma bakin-cikin rashin mahaifinsa, ke wasu ma cewa za su yi ya sayar da kaddarorinsa ne, ya yi iskancinsa”

Hajiya Kilishi ta yi dariya sosai ta ce ” Amma ban ta6a tunanin ki na da kaifin basira haka ba, idan ka kashe makiyin ka ma, ai ka taimaka masa ne,

• gara ka’aje shi ka yi ta kallon sa yana wahala a rayuwarsa, don haka shawararki ta yi, na kuma dauketa, ki na kuma da tukuici na musamman

Hajiya Rakiya ta ce “To godiya na ke babbar giwa.

” Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce “Amma ina fatan za kici-gaba da rike min sirrina kamar yadda kika saba?”

Ta yi dan murmushi ta ce “Haba, haba, ai ba ki da matsala, in dai nice, ki sha kuruminki”

Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa akan lamarin. Washegari. kuwa da taimakon rakiyar. Hajiya Rakiya suka tafi rugar Mai Rakwacam dauke da bukatunsu, da fatan samun dacewa. Mai Rakwacam ya dauk tsawon lokaci yana bincikensa, kafin ya dubi Hajiya Kilishi ya ce, “Aiki zai yiwu, bukata kuma za ta biya, ki aje Naira dubu dari biyu da hamsin, za’a sayi kayan aiki.”

Nan da nan Hajiya Kilishi ta balle jakarta ta aje masa kudin, ya Kara kallonta ya ce “To ku tashi ku tafi, jibi goshin magariba ki dawo.” Hajiya Kilishi ta yi godiya, suka tafi.

biyu tsakani goshin magariba kamar yadda ya bukata. Hajiya Kilishi da Hajiya Rakiya suka isa rugar, sun tadda Mai Rakwacam ya kammala duk aikin.

Ya dauko wata bakar laya da ta ji surkulle, ya ce ta sami kasan jiiyar bishiyar kuka ta binne hade da wani dan Karamin kasko daya ji daure-dauren bakin zare, duk jikinta an zaneta da sunan Musaddik, ya ce ta hada da layar ta binne, da zarar ta binne aiki ya kammala.

Babu wanda zai raba Musaddik da shaye-shaye da lalacewa, sai ranar da aka tono wannan layar da kaskon. Don haka ta san yadda za ta binne da kuma inda za ta binne.

Ya Kara da cewa, ba zai karbi ko sisi ba, sai aiki ya ci. Daga nan za ta dawo ta cake masa Naira dubu dari uku cif? Haiiya Kilishi ta karbi komai ta yi godiya tare da alkawarin dawowa ta ba shi hakkinsa da zarar bukata ta biya, daga nan suka dauki hanyar gida.

Suna cikin’ tafiya ne. Hajiya Kilishi ta dubi

Hajiya Rakiya ta ce “Yanzu ina za mu samu bishiyar kuka, inda za mu binne wannan asirin?”

Hajiya Rakiya ta yi murmushi ta ce.

“Dadina da ke mantuwa, a ni tunda ya ambaci bishiyar kuka, na ji na sami kwanciyar hankali, kin manta rikakkiyar bishiyar kukan da ke bayan gida na, abubuwa nawa muka binne a

• Kasanta? Hajiya Kilishi ta fashe da dariya ta ce “Godiya na ke da samun aminiya, mai share hawayen kuka na, yanzu kawai mu wuce gidan naki mu aiwatar da aikin.Sun isa dare ya yi, gari kuma ya yi duhu.

Hajiya Rakiya ita ce me haska ma Hajiya Kilishi bakin bishiyar da hasken wayarta. Hajiya Kilishi kuma na aikin haka, sai da ta haka rami me zurfi.

Sannan ta binne kaskon da layar. Babu wanda ya gan su har suka gama, suka tafi.

Kwanaki biyu tsakani, sai ga Hannatu hajaran-majaran tana gaya ma Hajiya Kilishi ba za ta koma: gidan Musaddik ba, domin jiya kwana ya yi yana shaye-shaye, ta ce dama ya iya shaye-shaye ne? *

Mutumin da ko taba bata taba ganin ya sha ba, .amma rana tsaka ta gan shi cikin wannan mummunan halin.

Hajiya Kilishi ta fashe da dariya, ta mike ta yi rawa, ta yi juyi, ta daga hannu tana yi ma Allah godiya tare da yi ma kanta kirari na sharri. Hannatu ta yi galala tana kallonta cike da mamaki ta ce “Ya na ga ki na murna Inna, wannan fa magana ce ta lalacewar rayuwar Musaddik da ni kaina”

Hajiya Kilishi ta koma’ ta zauna, tana fadin

“Lalacewar rayuwarsa dai, ina ruwan ki, ko kin manta tun farko ma gaya miki wannan aure ne na dan lokaci, aure ne kuma na samun arziki, ko kin yi kuskuren fara sonsa ne?”Hannatu ta girgiza kai ta ce

“Ban fara sonsa ba, sai dai na fara tausayinsa.

» «To shi ma tausayin ki yi gaggawar cire shi a ranki, domin daga tausayin ne ake samun soyayya, auranki da shi kuma ya kusa zuwa karshe.

Don rayuwarki dama ba ta dace da ta sa ba, dukiyarsa da son cikar burina su ne musabbabin auranku, kamar yadda cikar burina, zai zama musabbabin rabuwarku.”

Hannatu ta mumfasa, ta dade tana ganin mata marasa imani, ciki har da mahaifiyarta, amma ba ta taba ganin mara imani irin Hajiya Kilishi ba, a duk lokacin da ta yanko wani sharrin. Hannatu ta kan tambayi kanta, anya ko wai hajiya Kilishi ba shaidaniya bace? A nan Hannatu ta ci-gaba da zama, ba ta koma gidan Musaddik ba.

A yammacin ranar kuma Hajiya Kilishi da

Hajiya Rakiya suka dangana da wajen Mai Rakwacam, ta cake masa Naira dub dari uku gami da godiya, a hanyar su ta dawowa kuma ta ba Haiiya Rakiya Naira dubu dari biyu kyauta. Ta karba cike da jin dadi da godiya.Dukkan bukatu Hajiya Kilishi sun gama kammala sun cika, yau ta mallaki komai na Musaddik, sannan. ta maida rayuwarsa lalataciya.

Matakin Alh. Mansur na samun magaji na kwarai ya rushe. Lamarin Musaddik ya taba66are, masu jin wai wai sun gani da idonsu, ya daina zuwa masallaci, baida wajen zama sai wajen dabar shaye-shaye, bai da abokai sai ‘yan daba.

Surutai sun yi yawa, sai zagayawa suke yi ko’ina. Inna Halima da Malam Mahmud suna daya daga cikin wadanda lamarin ya fi tayar ma da hankali, sun yi fadan, sun yi nasihar. Amma babu wani canji. Kowa gani yake mahaukaciyar dukiyar da aka bar masa ne, ta canja masa rayuwa.

Shi ya sa arziki ga matashi, wani lokacin fitina ne Wasu kuma suna ganin wata kaddara ce kawai ta fada masa, domin dai Musaddik ya samu kyakyawar tarbiyya, da ba wani kudi da zai iya canja shi.

Idan aka yi la’akari da cewa lallai cikin gata da kudin ya taso, to me ya sa tun farko ba su bata shi ba, sai yanzu da ya kamata ace ya kara samun natsuwa, dalilin shine magajin Alhaji Mansur, bayan rasuwarsa.

Ai mutunci ya kamata ace ya jawo masa, ba kaskanci ba. Kasancewar a cikin aikin da aka yi har da rufe bakunan jama’°a daga magana, ko Hajiya Kilishi tana da sa hannu a cikin lamarin Musaddik, shi ya sa babu wanda hankalinsa ya kai kanta balle ma a zargeta.

Hajiya Kilishi ta kira taro tsakaninta da

Malam Mahmud da Inna Halima akan zaman Hannatu da Musaddik har kashi biyu tana ikirarin

•Hannatu ba za ta iya zama da shi ba.

A dalilin ba ta jin dadin zama da shi, yana kuma wulakanta ta. Malam Muhmud hakuri dai suke badawa tare da Kara yi ma Musaddik fada, amma dai ba wani canji, kullum abin gaba yake yi.

Musaddik ya koma tamkar wanda bai. taba rayuwa’ a cikin daula ba, ya zama abin tausayi.

Motar da yake hawa, wacce ita kenan ta rage masa, ya daga ya sayar ya sa kudin a gaba da yaran banza, suka cinye, abokinsa Murtala ya shiga damuwa yayi kokarin jawo Musaddik a jiki, amma ya ki yarda, domin a yanzu ba irin abokan da yake bukata kenan ba.

Murtala ya rasa dalilin wanna bala’i, dole ya hakura ya ci-gaba da raka shi da addu’a da kuma taimaka masa da kudin kashewa, a duk lokacin da ya hadu da shi. Haka zalika tuni ya bar aiki a kamfanin, kasancewar Hajiya Kilishi ta daga shi ta sayar, ta watsa kudinta a banki.

Iya lokacin da Hajiya Kilishi ta diba na auran

Musaddik da Hannatu na cika, ta kira Musaddik ta ba shi izinin ya saki Hannatu, ba tare da musu ko jan magana ba, ya rubuta takarda saki biyu, ya ba ta. Washegari kuwa ta kira Malam Mahmud da Inna Halima, sai Musaddik da Hannatu, ta nuna bacin ranta kamar ba ita ta bukaci rabuwar ba.

Ta nuna ma Malam Mahmud takardar sakin da ya rubuta ma Hannatu, su ma ba su ji dadi ba.

Amma sun san babu wata mace da za ta iya hakurin zama da shi a wannan hali, idan kuma aka takura ma Hannatu a maida auran, to ba’a yi mata adalci ba, don haka addu’a kawai suka yi. Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri a tsakanin su.

Anan ne Hajiya Kilishi ta gyara zaman ta, ta ce, “Sai dai na ga ya kamata ku sani, ga Musaddik nan, a cikin dukiyarsa, akwai wanda ya mallaka ma Hannatu, sauran kuma ya zuba su a kasuwa ya sayar ya yi shashancinsa da su, don haka Na ga ya dace ku sani, tunda kun san sun rabu, ina ganin ya kamata ya karbi komai nasa daya mallaka mata”. Ta Karasa maganar tana kallon Musaddik, wanda ya yi gaggawar yin magana kafin, Malam Mahmud ya yi magana.

“Hajiya. Ya za’ayi Hannatu ta dawo min da abinda na ba ta, bayan na riga na ba ta, kuma ni ba rabuwar tashin hankali muka yi ba, don haka ni duk abinda na ba ta, na riga na ba ta rabuwar mu, ba zai sa na karba ba.

Abinda Hajiya Kilishi take tsammanin ji daga bakinsa kenan, kuma bai ba ta kunya ba, hakan ta ji Malam Mahmud ya dubi Inna Halima, ita ma shi take kallon, sannan ya ce.

“Maganar Musaddik haka take, babu dalilin karbar wani abu daya ba Hannatu, tunda ya riga ya ba ta, kamar yadda ya fada, babu komai”

Inna Halima ta mumfasa ta ce. “Allah ya kyauta, ina ganin ya kamata mu tafi yaya, zaman mu baida wani muhimmmanci, tunda duk abinda ake gudu shi ne ya faru, sai da kuma ya farun.

Sannan muka sani, ka ga ba mu da wani abin yi kenan.

Ta fadi maganar ne cike da zargin Hajiya

Kilishi tare da jin haushinta, domin tana ganin har da sonta a rabuwar auran Musaddik, tunda ta bukaci hakan ba daya, ba biyu ba. Hajiya Kilishi ta yi mata wani kallo ta ce. “Shi aure ai rai ne da shi. Ranar da ajalinsa ya sauka, babu wanda ya isa ya hana hakan farusa. kuma ai Hannatu ma ta yi kokari da ta iya zama da Musaddik na tsawon wannan lokacin, kuma idan Musaddik bai canja mugun halin da ya dora ma kansa ba, ba na zaton zai sami matar da za ta zauna da shi a haka.”

Malam Mahmud ya ce “Ni na rasa irin wannan fitinar haka nan, ka ari wata banzar rayuwa ka dora ma kanka abinda ba ka yi ba da, ace shine ka ke yi yanzu, duk mutunci da darajarka Musaddik ka watsar, don me?”

Musaddik ya yi kasa da kansa cikin matsananciyar damuwa, domin ya san ya fi kowa damuwa da halin daya tsinci kansa a ciki. Ya zama wani da ake sarrafa rayuwarsa tamkar ana yi masa wahayi daya aikata, shi kuma sai ya aikata.

Malam Mahmud ne dai yake ta kidansa yana rawarsa. Inna Halima ba ta cewa komai, ita ce ma ta matsa su bar gidan. Haka zalika har suka kai gida korafi Inna Halima take yi akan ba ta ga dalilin daya sa Musaddik zai ba Hannatu wasu daga cikin

•kaddarorinsa ba, me ta tsinana ma rayuwarsa da har zai ba ta wannan damar? Malam Mahmud ya nuna mata tsakanin mata cewa.

“Mata da miji sai Allah. Sanda zai ba ta ma bai sani ba, mu dai duk ba mu damu da wata dukiya ba, rayuwarsa da martabarsa ita muka fi damuwa da

Hmmmm