MUSABBABI CHAPTER 10 BY HAJ HABIBA
MUSABBABI CHAPTER 10 BY HAJ HABIBA Amma kafin ta dawo din, sai da suka yi magana da kanwarta Hajiya Kubra, wacce kusan halinsu daya, don haka koda ta gaya mata kudirinta na hada Musaddiq da Hannatu aure da dalilinta, ba ta ji darr! Ba, ta amince, domin tana ganin duk karuwarsu ce. Hannatu za ta zama musabbabin kusanta su da arziki, don haka Hannatu ta tarkata kayanta ta yo Minna. Gargadi na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi mata, shi ne kada ta sake ta dora ma kanta son Musaddik, domin ta sa a ranta aure ne za su yi na wucin gadi, na dan lokaci, sai ga shi kuma ma an yi sa’a Musaddik din burge Hannatu kawai yake yi, amma babu sonsa ko kwayar zarra a zuciyarta. Sai dai ta ci-gaba da shishige masa tare da nuna masa kauna da kuma kokarin nuna masa ita yarinya ce ta-gari, sai dai ko kadan Musaddik bai ta6a sa ma ransa wai zai so Hannatu ba. Ko kuma tana yin abinda take yi masa, don ya so ta ne. Tsawon lokaci Hannatu ta share a gidan, amma Musaddik baya ko bi ta kanta, hidimarsa kawai yake yi…