MUSABBABI CHAPTER 10 BY HAJ HABIBA
Amma kafin ta dawo din, sai da suka yi
magana da kanwarta Hajiya Kubra, wacce kusan halinsu daya, don haka koda ta gaya mata kudirinta na hada Musaddiq da Hannatu aure da dalilinta, ba ta ji darr! Ba, ta amince, domin tana ganin duk karuwarsu ce. Hannatu za ta zama musabbabin kusanta su da arziki, don haka Hannatu ta tarkata kayanta ta yo Minna.
- Gargadi na farko da Hajiya Kilishi ta fara yi mata, shi ne kada ta sake ta dora ma kanta son Musaddik, domin ta sa a ranta aure ne za su yi na wucin gadi, na dan lokaci, sai ga shi kuma ma an yi sa’a Musaddik din burge Hannatu kawai yake yi, amma babu sonsa ko kwayar zarra a zuciyarta.
Sai dai ta ci-gaba da shishige masa tare da nuna masa kauna da kuma kokarin nuna masa ita yarinya ce ta-gari, sai dai ko kadan Musaddik bai ta6a sa ma ransa wai zai so Hannatu ba.
Ko kuma tana yin abinda take yi masa, don ya so ta ne. Tsawon lokaci Hannatu ta share a gidan, amma Musaddik baya ko bi ta kanta, hidimarsa kawai yake yi.
Hakan kuwa ya fara tayar ma da Hajiya Kilishi hankali, ta rasa mafita, don haka ta nemi aminiyarta Hajiya Rakiya, domin neman shawarar yadda za’a bullo ma lamarin, ba tare da wani dogon tunani ba. Hajiya Rakiya ta bada shawarar a hada lamarin da Malamai, domin, a hada soyayyar Musaddik da Hannatu ta karfi da yaji, wannan shawara ta yi dai-dai da tunanin Hajiya Kilishi, don haka ta bukaci rakiyar Hajiya Rakiya zuwa wajen amintaccen Bokanta.
Wato Mai Rakwacam, suna isa tun kafin su fadi abinda ya kawosu. Mai Rakwacam ya gaya masu dalilin zuwansu, ya kuma tabbatar masu da cewa auran Musaddik da Hannatu tamkar an yi, an gama ne. Ya yi ta surkullen ayyukansa, daga bisani ya ba ta kwallin da Hannatu za ta sanya a idanunta, suna hada ido da shi. Shi kenan, sai turare da za ta shafa a jikinta, ya ji kamshin, sai kuma wani garin magani da za ta zuba masa a cikin abincinsa da zaran ya ci, shi kenan bukata ta gama biya. Bayan dawowarsu daga wajen Mai Rakwacam ne. Hajiya Kilishi ta ba
Hannatu duk abubuwan da za ta yi amfani da su.
Na sawa a abinci kuwa da kanta take sanya masa, kuma sai ta tabbatar ya ci, sannan take barin wajen, kwanaki uku kacal! Tsakani. Musaddi§ ya haukace akan soyayyar Hannatu. Bai sami sukuni ba, sai da ya gaya mata, ta kuma amince.
Da kansa ya sami Alhaji Mansur ya gaya masa ya sami matar aure, wato Hannatu. Alhaji Mansur ya karki abin na sa babu yabo, ba fallasa, don dai a so samunsa ne, ya sami wata wacce ba ta da alaka da Hajiya Kilishi. Amma tunda abinda dansa yake so, shi yake so, ya sa ya amshi zabin na sa, hannu biyu ba tare daya bari ya gane zabin na sa bai yi masa ba.
Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ta sami jin dadi, farin-ciki da kuma natsuwa, domin hakarta ta kusa cimma ruwa, nan da nan aka shiga shire-shiryen biki, kasancewar Hannatu marainiya, mahaifinta ya rasu, ya sa Alhaji Mansur ya dauki nauyin komai nata.
A ranar da Musaddik ya je ya gaya ma Inna
•Halima, Hannatu ya zaba a matsayin matarsa ta yi masa fatan alheri tare da sanya ma lamarin albarka, daga gidan Inna Halima, gidan Malam Mahmud ya wuce, a ranar ya tarar da Afrah tana wanke-wanke cike da mutuntawa ta gaishe shi. Ya amsa cikin nuna yabawa da lamuranta.
Domin dai duk cikin ‘ya’yan Kawunsa, babu yarinyar da haka nan yake ganin girmanta tare da kaunar dabi’unta irin Afrah, yarinyar gaba daya rayuwarta daban ce, ba ta da hayaniya.
Bayan ya gaisa da Kawunsa da Mama Hauwa, yake sanar da Malam Mahmud maganar Hannatu.
Malam Mahmud ya yi murna, ya kuma sa albarka.
Maimakon Mama Hauwa da ta hade girar sama da ta kasa, idan ranta ya yi dubu, to ya baci, ta dubi Musaddik ta ce “Amma Musaddik ca na ke soyayya kake da Sakina?” Yai saurin kallonta ya ce “Soyayya, kamar yaya?” Ta ce “Irin yadda na ga taku ta zo daya, sai na ke zaton ko soyayya ku ke yi, ka ga shi kenan tuwona, maina, sai ayi hadin zumunta kawai
Musaddik ya girgiza kai ya ce. “Mama
Hauwa kin fahimta a bai-bai, domin gaskiya ba soyayya muke yi ba. Asalima ni ban tada dasa ma kaina tunanin zan so-ta ba, daya wuce soyayya ta
“yan-uwantaka. Hannatu dai ita ce na ke son na aura.
Mama Hauwa ta yi turus! Tana kallonsa cike da takaici, a yayin da Malam Mahmud ya ce “Kyale ka ji, neman zance ne da ita kawai. Musaddik Allah ya sanya alheri, ya sa Hannatu abokiyar arzikinka
Ya amsa da “Amin”. Daga nan ya zaro kudi
‘ya aje masa, ya yi godiya, sannan ya tashi zai tafi, dai-dai inda Afrah take, ya tsaya ya danko kudi masu yawa ya ba ta, ganin irin kallon wulakancin da Mama Hauwa ke yi masa, ya sa ya fice ba tare daya ba ta ko sisi ba. Yana fita, ta dasa ma Malam Mahmud gwanjon bala’i, wai yana da damar da zai sa Musaddik ya auri Sakina, amma ya ki sa baki, illa ma goya masa bayan auran Hannatu da yake yi.
Daya gaji da sababi da bala’inta ne ya kakkabe rigarsa ya tattara ya bar gidan. Bayan auran Hannatu da Musaddik, a katafaren gidan da Alhaji Mansur ya ba shi ya tare, babu wanda baya sha’ awar rayuwar Musaddik. Allah ya rufa masa asiri, amma baya wulakanci.
Baya kyamatar talaka, ga taimako da son shiga duk abinda zai daukaki addini, ba Alhaji Mansur kadai yake yaba da halayen dansa ba, har sauran jama’a suna matukar ganinsa da kima da daraja, domin dai Allah ya tabbatar da natsuwa a cikin rayuwarsa. Musaddik Mansur Musaddik kenan.
Duniya ba matabbata ba. Watanni biyu kacal!
Da auran Musaddik. Allah ya dauki ran jigo kuma gatan Musaddik, wato Alh. Mansur, ya yi rasuwar farat daya a dalilin hadarin mota a hanyarsa ta zuwa Kano daga Abuja, domin halartar wani taron *yan kasuwa da suka gayya ce shi.
Sai gawarsa ce ta dawo Minna, inda a nan ne akayi masa suttura aka rufe shi. Fadin tashin hankali da kuncin da Musaddik ya shiga, bata lokaci ne.
Nan da nan ya rame, ya fige, ya fita hayyacinsa. Rasuwar mahaifinsa ta yi mummunan taba shi, hatta abinci baya iya ci. Duk wani me imani, dole ya tausaya masa, domin ya fada mawuyacin hali. Haka Inna Halima da Malam Mahmud suka yi ta Kokarin dawo da shi hayyacinsa tare da yi masa addu’ ar samun dangana. Ita kam Hajiya Kilishi duk da rasuwar mijin nata ya taba mata zuciya, to fa maganar abinda ya mutu ya bari, ya fi damunta, bakin-cikinta daya ne na kaso mafi tsoka da Musaddik zai samu, domin dai ta san kason ‘ya’ yanta mata biyu. Musaddik zai ci.
Idan da akayi abinda za ta fi shi da shi, to bai wuce tumunin takabarta ba da kason ‘yarta daya, ta san kuma babu abu daya da ‘ya yanta za su bari a hannunta, tunda sun riga sun mallaki hankalinsu.
Suna kuma tare da mazajensu, don haka ta san da kasonta kadai za ta tashi, shin ya za ta yi? Ta san dai ba ta da damar hana Musaddik gadonsa, domin ya san ‘yancinsa.
Abinda ko take gudun ne ya faru, domin bayan fitarta takaba, aka yi rabon gado, ba gidan Musaddik ba motarsa ba kuma kamfaninsa na siminti a cikin rabon.
‘Domin Alhaji Mansur ya rubuta a rubuce cewar duk wadannan abubuwan ya ba shi su kyauta ne. Hakan koya tada hankalin Hajiya Kilishi, ga
“abu a rubuce, balle ta ce karya ne.
Sannan da aka yi rabon gadon. Musaddik ya tashi da kaddarori da kudade makudai, amma duk. ba sune a gabansa, ba su kuma burge shi ba, ya fi ‘bukatar mahaifinsa fiye da komai a duniya. Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa gaba daya tunaninta ya tafi ne akan dukiyar Musaddik da tunanin yadda dukiyar za ta zama nata, watau ta mallake ita daya.
Abu na farko da hajiya Kilishi ta fara yi, shi ne Kokarin mallake Musaddik, ta taimakon Bokanta Mai Rakwacam, ta kashe makudan kudi kafin bukatarta ta biya, domin kuwa ta sami mallake Musaddik, komai zai aikata ko zai zartar akan duk abinda ya shafi rayuwarsa sai da saninta, sai da kuma amincewarta.
Yana matukar jin tsoronta tare da tsoron bata mata rai, sai daya zamana duk duniya Musaddik gani yake baida kowa sai Hajiya Kilishi, hatta dangantakarsa da su Inna Halima duk ta ja baya, domin ko kafin ya je gidanta ma aiki ne. A yayin da Hannatu take tsiro da halayen wulakanci da musgunawa ga Musaddik, sam ba ta ganin mutuncin ko darajarsa.
A yayin da shi kuma ya dora ma kansa tsoronta da shakkarta, gaba daya lamuran Musaddik
•suka dagule, rayuwarsa ta shiga cikin gigita da dimauta, wannan lamari shi ne tushen
lalacewar rayuwar Musaddik. Domin dai baida tunani nasa na kansa, sai wanda Hajiya Kilishi da Hannatu suka kaga masa, haka zalika baida ta cewa, sai cewarsu. A hankali Hajiya Kilishi da Hannatu suka fara zare dukiyar Musaddik, ya zama wanda da sun ce, bai samun sukuni, sai ya aikata masu. Haka Hajiya Kilishi ta yi ta sa Musaddik yana sa hannu akan kadarorinsa na tabbatar da cewa ya mallaka mata,
• wasu kuma ya mallaka ma Hannatu.
Daga Inna Halima har Malam Mahmud babu wanda ya san wainar da ake toyawa, balle su taimaka masa su yi ma tufkar hanci tun nesa da kofa.
Hatta kamfanin ya daina zuwa kullum yana gida, hakan ko ya fi komai yi ma Hajiya Kilishi
•dadi, inda ta fara tura Hannatu kamfanin tana shiga ofis dinsa hakan ko ya janyo cece ku ce a kamfanin a tsakanin ma’ aikatan, daga bisani Hajiya Kilishi
“tasa Musaddik ya yi ma ma’aikatansa bayanin
- Hannatu ce za ta ci-gaba da daukar nauyin kamfanin, domin shi ayyuka sun yi masa yawa.
Sannu a hankali cikin dabara da ta hanyar
Bokaye da Hajiya Kilishi ta saba ta sami nasarar kwace kamfanin daga hannun Musaddik, inda ya sa hannu, aka kuma kafa shaidu akan cewa ya bar ma matarsa kamfanin halas-malak. - Wannan lamari ya daga hankalin abokin
- Musaddik kuma (Cashier) na kamfanin Murtala.
*Domin ya fara zargin tamkar Musaddik baya cikin hayyacinsa, tamkar bai san abinda yake yi ba. Da kansa ya sami Musaddik ya tunantar da shi muhimmancin kamfanin a gare shi, ya kuma tambaye shi meye dalilinsa na barin ma matar da bai tada koda haihuwa da it ba irin wannan dukiya? Anya kuwa yana cikin hayyacinsa.
Musaddik ya numfasa yana kallon Murtala, sannan
ya ce.Ni fa babu abinda ke gabana, ko yake min dadi gaba daya rayuwar ma ni ta fita kaina, don haka duk wata dukiya, ni ba ta gabana. Kuma Hannatu matata ce, ko ta haihu ko ba ta haihu da ni ba, zan iya yi mata kyauta, saboda haka don Allah ka tsaya a matsayinka na aboki na, ka daina kokarin shiga abinda bai dameka ba.Haka Murtala ya bar Musaddik cike da mamakin irin magangarun daya gaya masa, domin dai ya san ba haka Musadik yake ba a da, don haka bai ji haushi ba.
Ya yi alkawarin zai ci-gaba da fahimtar da shi illar abinda yake aikatawa, har ya fahimta, ko ya nemi wani shakikin Dan-uwansa ya sanar da shi abinda ke faruwa ko za su iya taimakawa.
Sai daya zamana Hajiya Kilishi ta gama zare komai, domin hatta gidan da yake ciki, ya mallaka shi ga Hannatu, a lokacin ne Hajiya Kilishi ta ga ya kamata ta dauki mataki na karshe na karasa lalata rayuwar Musaddik. Domin ba ta kaunar dük wani sanadi da zai sa Musaddik ya farga ya dawo hayyacinsa, ya fahimci irin mummunar barnar da ta yi ma rayuwarsa, ko kuma hankulan mutane da na dangin mahaifiyarsa su ankara da halin da ta jefa Musaddik.
Don haka ta fara neman shawarar aminiyarta
Hajiya Rakiya yadda za su yi da Musaddik. Hajiya Rakiya ta yi shiru tana nazarin lamarin, a nan ne Hajiya Kilishi ta dubeta ta ce “Ni fa Hajiya Zuciyata a bushe take akan Musaddik ko kadan ba na. Kaunar yaron nan, musamman idan na tuna ni fa ba ni da da namiji, sai na ji tamkar na raba Musaddik da doron kasa”
Ta dan hadiye yawu gami da kallon Hajiya
Rakiya da take sauraron ta, sannan ta ci-gaba da cewa.
“Kamar yadda a yanzu na gama tunanin lokaci ya yi da zan raba Musaddik da duniya gaba daya, domin duk wani amfani da zai yi min, ya riga ya gama yi min, kuma ina ganin mutuwarsa ita ce kadai hanyar da asirina zai rufu akan dukiyarsa, domin babu wanda zai tuhumeni..
Hajiya Rakiya ta yi gaggawar dakatar da ita, tana yi mata kallon ko kin haukace ne? Ta ce “Haba Hajiya. Shin rashin imaninki har ya kai ki fara tunanin daukar rai, bayan duk irin ta’asar da ki kayi masa na raba shi da arzikinsa mallakarsa, duk wannan bai isa ba, sai kin kashe shi? Kai! Abin zai
Hmmmm