CANJIN RAYUWA CHAPTER 9 BY HALIMA A K/MASHI

CANJIN RAYUWA CHAPTER 9 BY HALIMA A K/MASHI hakan? Isa ya ce, a’a bance ba, sai dai ka bani dariya kawai, duk ‘yan matan da ke cikin garin Katsina? amma ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan ‘yan ruga mitsi-mitsi da su?. Kabiru Na’allah ya ce, in dai fulanin nan ne ma, ba su son baiwa bare ‘ya’yaansu. Bashir ya ce, ku yi min addu’a, in rabo na mce za su bani, don gaskiya naga wacce na ke so. Suka sa mishi dariya. Abin ya wuce da tunanin Bashir, domin ranar da tunanin ‘yar fulani ya kwana, ya kosa ya je su kai kudin shanu, don haka tun tara ya shirya ya nufì banki ya ciro kudi, daga nan suka nufi Mashi. Ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, amma har suka bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota, amma baiga giccin wani da Ya kama mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai, da sauri ya fasa shiga motar ya nufi gurinta. Sallama ya yi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga sama, ganin mutum sai ta amsa cikin dariya.…