CANJIN RAYUWA CHAPTER 9 BY HALIMA A K/MASHI
hakan? Isa ya ce, a’a bance ba, sai dai ka bani dariya kawai, duk ‘yan matan da ke cikin garin Katsina? amma ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan ‘yan ruga mitsi-mitsi da su?. Kabiru Na’allah ya ce, in dai fulanin nan ne ma, ba su son baiwa bare
‘ya’yaansu. Bashir ya ce, ku yi min addu’a, in rabo na mce za su bani, don gaskiya naga wacce na ke so. Suka sa mishi dariya.
Abin ya wuce da tunanin Bashir, domin ranar da tunanin ‘yar fulani ya kwana, ya kosa ya je su kai kudin shanu, don haka tun tara ya shirya ya nufì banki ya ciro kudi, daga nan suka nufi Mashi.
Ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, amma har suka bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota, amma baiga giccin wani da
Ya kama mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai, da sauri ya fasa shiga motar ya nufi gurinta. Sallama ya yi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga sama, ganin mutum sai ta amsa cikin dariya. Ya ce, ‘yan mata ya ya sunanki? Ta kalle shi ta ce, suna na? ta kau da kai, taci gaba da abinda take yi. Isa ya kwada masa kira daga nesa, Bashir ka zo mu tafi mana, Bashir gani ya ke idan fa ya tafi ya bar damarsa, ya ma rasa ta kenan, shi mutumne da bai son matsalar da za ta sa shi damuwa.
Don haka da ya ga abinda zai dame shi, nan da nan zai yi maganin abin, in har zai iya, musamman in na kudi ne, tunda yanzu ba laifi yana samu.
Sake komawa ya yi ya sa aka yi masa sallama da Ardo, wanda ya tafi don ya adana kudinsa. Kabir ya zo gurinsa, zo mu je in ya so mu sake dawo wa, Bashir yace, ba a haka da ni, ka san ni in ina son abu, zan yi duk abinda zan iya in kuna sauri ku yi gaba zan zo. Kabiru ya gane fusata ta sa Bashir fadin haka, sai ya yi dariya, sannan ya yafito Isa Mani da hannu, suka zo su ukun suna jiran fitowar Ardo.
Ya ce, da muna daki daya da ku, duk ku ka yi aure ku ka barni, dole ku yi min dariya. Duk yadda suka dauki lamarin da zafi gurin Ardo, ma’ana ba sauki sai suka ga akasin haka. Ardo yana da ilimin addini, ya fahimçe su, kuma ya yi masu bayanin cewa lallai sun yi dace, domin har an bayar da ita, sai wanda aka baiwa din Allah ya yi masa rasuwa wata biyu kenan. Ya Kara da cewa, in yana son ta ta amince ya nemi soyayyarta, in ta amince gurin shi babu wata matsala.
Kwana biyu tsakani Bashir ya Sake yi wa rugar fulanin tsinke, cikin ado aljihu dam da kudi.
Sannan Isa Mani ya sa shi yin tsarabar sarka da ‘yan kunne, wai mutanan ruga suna son abin ado mai kyalkyali. Bai samu Ardo a gida ba sai babban dansa Jabiru. Sun gaisa inda ya yi masa bayanin cewa, Ardo ya je cikin gari maganar tafiyarsa aikin Hajji. Sai dai yayi wa Jabiru alheri, sannan ya ce, masa yana son ganin Bengel, kamar yadda ya ji Ardo ya ambata rannan. Sai Jabiru ya ce, oh! Sauda? Ai Saudatu sunanta, Ardo kadai ke fada mata Bengel, na gode bari in turo ta, domin yanzu za su fità tallar nono.
Yana tsugune Sauda ta isko shi, tana sanye da koriyar atamfa da kuma farin mayafi mai kyalli. Duk da fuskarta babu walwala farin ciki gurin Bashir ba ya misaltuwa. Ta tsuguna can nesa da shi, sannan ta gaishe shi, ba tare da wata kwana-kwana ba ya ce, Saudatu kina so na? Rufe fuska ta yi da gefen mayafinta sannan ta ce, Ardo ba za ya ba da ni ga wanda ba bafulatani ba. Ta yi magana cikin hausar da ba ta goge ba. Ya ce, kar ki damu Ardo ya san da zuwa na, ya amince in nemi soyayarki.
Saudatu yarinya ce ba za ta wuce sha uku-sha hudu ba, sai kyau tamkar balarabiya. Ta ce, in na amince me zai faru?
Ya ce, aure ne zai faru, ya fada cikin kwaikwayon muryarta, ya lura akwai kuruciya gurin yarinyar. Ta ce, kamar ya ya? Yanzu da na amince sai a kama aure? Ya yi dariya, to me za a jira? Zan turo iyaye na su gana da naki, zan bayar da sadaki da duk abinda ku ke yi na al’ada, sai a daura mana aure. Ta sake kallon shi, sai me daga nan?
Ya ce, a kai ki gida na, ta ce, ina? Ya ce, cikin gari, tace, daga nan sai me? Kuma me zanyi a gidanka? Ko kaima kana da shanun ne da zan dinga tatsar nono ina kaiwa kasuwar ku.
Ya ce, a’a abinci kawai za ki dafa min, sai in kin haifa min yara ki kula min da su. Ta rufe fuska, zan tafi yace, haba da sauri haka muna hira mai dadi? Ta ce, Sa,ada ce ke jira na za mu je talla. Ya ce, wace ce Sa’ade? Tace, ‘yar’uwa ta ce, kanmu daya, ya ce, tare za’ayi maku aure?
Ta ce, ni kan zan tafi ta fada tare da rufe fuskarta. Yace, ba na son tallar nan, ta ce, ni kan ina son zuwa talla, don na ga kasuwa,. kai kam, me ya sa ba ka so? Ya ce, ina tsoron kar wani ya kwace min ke.
Ya ciro tsarabar sarka cikin gidanta ya ce, ga wannan, ta amsa da murna tana godiya. Ya sake fiddo da sabbin kudi ‘yan naira goma-goma ta yi ta godiya yace, mata zai dawo Jumma’a ta ce, sai ka zo, cikin abinda bai fi wata daya ba ya mallaki zuciyar ‘yar fullo. Iyaye sun shiga, inda aka tsayar da rana, sai Ardo ya dawo daga aikin Hajji.
Su biyu aka hada bikinsu da Sa’ade, ita an kai ta wata Rugar Fulani da ke kusa da su. Ita kuma Saudatu can Masari aka yi da ita, inda mahaifinsu ya ba su daki. Satinsa guda ya koma Katsina, a nan Tudun wada ya nemi daki, ya koma ya dauko ta, ya saka ta Islamiyya saboda ya lura tana da Karancin ilimin addini. Ta kasa fahimtar cewa shi din fa mijinta ne, fa di take, yadikko, ta ce, ka da ta bari najimi ya taba ta, balle ma jikinta, ita kan ba ‘yar iska bace.
Sai da ya lura ta saka hankalinta a karatu, kuma tana fahimta, sai ya samu malamin ya sanar da shi matsalarsu, nan malamin ya cire minti biyar kullum yana
• yin nasiha ga dukkan dalibansa don akwai me irin matsalar Addini bai rufe komai ba, don haka bayani filla-filla ya dinga yi masu ya yin nasihar. Sauda ta fahimci komai, kuma ta mika wuya ga mijinta game da
neman gafarar sa, lokacin watannin su goma da aure, shi kam ya yi ta ji da ita tare da kara son ta tamkar ya ba ta kanshi. Sunyi shekara uku, kafin ta samu
cikin farko, ta sauka lafiya danta namiji, yaci, sunan Mahaifinsa Aliyu, suna kiran sa Abba, kullum Kara son Saude ya ke yi, saboda biyayyanta da ladabi.: A wannan lokacin mahaifinta Ardo ajalinsa ya sauka,
sun shiga tashin hankali, domin damuwarta
ta tayar da hankalinsu sosai.
rugarsu har ta yi sati biyu da kyar ya lallabe
ta sula dawo Bayan iyayensu sun fita takaba, sai aka yi masu rabon gado, Sauda ta samu shanu tara da raguna, saboda su biyu ne a
gurin Ardo, Bashir ya ce, ta ba shi aronsu ya
saida, zai fadada kasuwancinsa, in komai
ya daidaita zai maido mata da shannunta ko
kuma kudinsu. Amma ta je ta yi shawara da
yadikkonta, yadikko ta ce, ki ba shi, in kin san zai ba ki. Sauda ta ce zai ba ni, ta ce, to ki ba shi, Sauda ta tattara komai da ta mallaka ta damka ma mijinta.
Allah ya sama abin albarka, inda kasuwanci ya bunkasa ya fadada, ta hanyar. buden manyan shagunan kayan” masarufi, kayan abinci, shaddoji da zannuwa, ba a fi shekara ba ya soma fita irin’ su Kwatano, Togo da dai sauransu. Kafin shekara biyu ya fara shiga China da Dubai. In ya sayo kaya sai ya raba ma ‘yan kasuwa. Daidai lokacin ne ta sake haihuwar danta na biyu, inda aka rada masa Muktar.
Bayan ta ya ye, shine suka je aikin Hajji, shine ya biya masu ita da shi, da wata shekara ta zagayo kuma ya biya wa mahaifinsa. Shekara daya ya bude kamfanin kansa da ake sarrafa robobi da katifu.
Shekarar ne ta sake haihuwar danta na uku, aka sa ma shi suna Abdulkarim. Lokacin ne ya soma nuna mata maitarsa ta son ‘ya mace. Ya ce, Sauda ban taba fada miki ba tun cikin Abba na ke son haihuwar ‘ya mace. In kina da ciki koyaushe ina cikin addu’a, ta ce, mu ci gaba da addu’ar Allah ya ba mu ‘ya mace amin. Sai in sa mata suna Khadija, sunan mahaifiya ta ce, Allah ya ba mu masu albarka.
Abdulkarim ya shiga shekaru uka, amma ba ta samu wani ciki ba, lokacin ne Alhaji Bashir ya hadu da Hajiya Binta a Saudiyya, bazawara ce, mijinta ya mutu, ya bar mata dukiya, amma ba ta taba haihuwa ba. A girme za ta girme Sauda, a boye suka yi ta soyayya, don ya rasa yadda zai yi ya fada ma Sauda, sam ba ya son bacin ranta. Wani dare bayan sun gama mu’amalarsu ta ma’aurata, sai ya rike hannunta yana me sake jaddada mata cewa, sonta daban yake a cikin zuciyarsa. Matuka take jin dadi a duk lokacin da ya yi irin wadannan kalaman, ta ce, ai tuni ta san haka, kuma ta yarda da wannan. Ta kuma fada masa cewa, bafa sama da shi a rayuwarta, amma in an cire yadikkonta. Ya yi murmushi sannan ya ce, kin san aure mukaddari ne ga kowane bawa ko? Ba tare da ta fahimta ba ta ce hakane.
Ya ce, zan Kara aure, da farko ta dauka wasa ne, amma jin yadda ya kuke yana ta zayyana mata inda suka hadu, da inda maganar ta tsaya a halin yanzu, sai ta mike cikin fushi ta nufi dakinta. Kishi kenan, kumallon mata, rigima sosai suka yi har ta bukaci kudinta. Ba da bata lokaci ba ya maido mata, sannan ta dauki matakin Kaurace masa, ya yi ta lallabarta amma ta ki. Ta kai kudinta gidansu, inda za a sai mata filaye da shanu. Wannan ne karo na
– farko da ya taba kai Karanta gurin kannin mahaifinta. Har gida Baffa ya zo ya yi mata fada da nasiha, ta ci kukanta ta hakura dole.
Anyi biki inda aka kawo amarya sabon gida da ya gina masu a sabuwar unguwa. Katon gida mai tsari, sai da zama ya soma yin nisa, a nan Saudatu ta gane lallai mijinta ya fi son ta. Don haka ta saki ranta ta zauna dasu zuciya daya. cikin wannan zaman ne ta samu cikin Mimi, haihuwar Mimi ta zo masa cikin nasarori, randa aka haife ta, rannan ya bude kamfaninsa na fulawa a Kano. Da ya dawo ya ga ‘ya mace kyakyawa, mai kama da abar son shi wato mahaifiyarta, ya yi murna
Hmmm