CANJIN RAYUWA CHAPTER 16 BY HALIMA A K/MASHI
Na’ima tana ba ta hakuri. Daidai lokacin Ismail ya shigo falon, don lokacin karatun sa ne da yara. Ganin Mimi cikin halin da take ciki, har zai koma sai ya tambayi Na’ima, “lafiya dai ko?” Banza ta yi da shi cikin salon wulakanci. Ya dan yi jim, can ya ce, “baiwar Allah kuka bai taba zama mafita ga bawan da musiba ta auka masa ba. Idan kina da bukata zan ba ki maganin damuwa da yaye bakin ciki. Kila ma ki cimma burinki.” Duk ba su tanka shi ba har ya fice. Mimi ta fi sa’a guda tana kuka har kanta ya soma ciwo. Na’ima ta yi lallashi ta gaji, don haka ta kira Momy Nafisa ta fada mata abin da yake faruwa. Momy ta yi ta kiran Mimin ba ta dauka ba, da yake tana kasa, wayar kuma na sama. Sai da ta soma jin jiri, sannan ta mike ta nufi saman. Ta jima a kwance kafin ta ji rurinta. Cikin sauri ta dauka. Tunaninta Khalil ne, ashe Momy ce. Ta dauka, muryarta can Rasa, ta ce, “Momy!” Momy ta ce, “Na’ima ta fada min komai. Ina so ki kwantar da hankalinki. Na fada miki ba za ki auri Abbas ba. Ta soma…