Na’ima tana ba ta hakuri. Daidai lokacin Ismail ya shigo falon, don lokacin karatun sa ne da yara. Ganin Mimi cikin halin da take ciki, har zai koma sai ya tambayi Na’ima, “lafiya dai ko?” Banza ta yi da shi cikin salon wulakanci. Ya dan yi jim, can ya ce, “baiwar Allah kuka bai taba zama mafita ga bawan da musiba ta auka masa ba. Idan kina da bukata zan ba ki maganin damuwa da yaye bakin ciki. Kila ma ki cimma burinki.” Duk ba su tanka shi ba har ya fice.
Mimi ta fi sa’a guda tana kuka har kanta ya soma ciwo. Na’ima ta yi lallashi ta gaji, don haka ta kira Momy Nafisa ta fada mata abin da yake faruwa. Momy ta yi ta kiran Mimin ba ta dauka ba, da yake tana kasa, wayar kuma na sama. Sai da ta soma jin jiri, sannan ta mike ta nufi saman. Ta jima a kwance kafin ta ji rurinta.
Cikin sauri ta dauka. Tunaninta Khalil ne, ashe Momy ce. Ta dauka, muryarta can Rasa, ta ce, “Momy!” Momy ta ce, “Na’ima ta fada min komai. Ina so ki kwantar da hankalinki. Na fada miki ba za ki auri Abbas ba. Ta soma kuka, “kin yi min alkawari Momy?” Ta ce, “ko rantsuwa na yi miki, ba zan yi kaffara ba. Don haka na yi miki alkawari.
Ina dai sake fada miki, ki tsaya a kan ra’ayinki.”Ta ce, “shi ke nan Momy.”
Mimi tana tsave a windonta na falo, wanda yake kallon ‘boys quaters’ da kuma lambun gidan. Fararen tantabarunta take kallo masu yawa, wadanda Dad ya sai mata tun shekaru da dama da ta ce tana so.
Hamsin ya sai mata, amma yanzu sun fi guda dubu, duk da cin su da suke yi. Ta tuna ta yi kwanaki rabonta da zuba musu abincinsu. Sai masu aiki ke ba su. Duk da kayan barci ke jikin ta, haka ta sauka.
Naima tana cewa ina zaki?” ta ce, “zan duba tantabaruna ne. Tunda aka soma matsalolin nan ban je gurin su ba.
Ta kicin ta bi zuwa barandar baya, inda nan abincinsu yake. Ta diba taita watsa musu. Duk da ba safiya bace, yanzun lokacin da ta saba watsa musu, sai ta ga suna nan da yawa. Har ta yi mamakin hakan, domin da rana suna fita.
‘Kamar an ce waiga, sai ta hango
Malam Isma’il yana shanya a gefensu. Da alama ya wanke kananan kayansa na ciki ne. Take zantukansa suka fado mata. in kina da bukata zan ba ki maganin yaye damuwa da bakin ciki. Kila ma har ki cimma burinki. Ina ya san tana da wani buri? Kodayake shi Malami ne, kuma ta ji ana fadin Malamai suna yin magani. Ta tuna Mina kawarta ta taba ba ta labarin cewa kishiyar Mamansu ta yi wa Babansu magani, sai abin da ta ce. A fili ta ce, zan nemi taimakon Malamin nan, amma ta yaya zan yi masa magana?
Da wannan tunanin ta hau samanta.
Ta jima kafin ta yanke shawarar kiran Na’ima. Bayan ta daga ne, ta ce, ina son ki je ki amso min lambar Malam din nan mai koya mana karatu. Na’ima ta dan yatsina, ba ki san ba na son zuwa boys quaters ba sam. Bari in tura Polina. Mimi ta ce, a’a, ki sa Malam Hamisu kawai ya amso miki ki kawo min. Tace, ok.
Na’ima ta amshi wayar Mimi da ke hannunta ta saka mata lambar Ismail, sannan ta yi mata saving da Malam. Ta mika mata. Mimi ta ce, “aje kawai.” Har Na’ima za ta fita, sai kuma ta dawo. “Sis wai me zakiyi da lambarsa mimi ta kalleta kije kawai karki damu da sai kinsan dalili Tun fitar Na’ima, Mimi take tufka da warwara a kan kiran Malam Ismail. In ta kira shi me za ta ce masa? Kuma yaya ma zai dauki zancen nata? Wanan tinanin shi ° ne ya dauke ta har zuwa karfe takwas din. dare, wanda har lokacin ba ta tsai da:. matsaya ba.
Sallamar mahaifinta ne ya zaburar da ita cewa an bude kofar. Ta waiwayo, ta dube shi. Kwanaki kusan hudu ba ta sa shi a ido ba, domin yana fushi da ita. Cikin in-ina ta amsa sallamar, sannan ta dinga kallon sa cike da kewa. Ya zauna kusa da ita. Cikin sigar lallashi ya ce, “uwata ta kaina.” Ta dube shi, “Dad na yikewarka. Don Allah kayi hakuri a kan abin da na yi. ” Ya ce, “kar ki damu. Kina ji na Mimi, ki tashi ki je ga Abbas can ya zo don ku tsara irin shagalin bikin da kuke so lokacin bikinku, sannan ku zabi Kasashen da za ku tafi shakatawa.”
Mimi ta yi shiru tana tunani, kamar ta amince, sai kuma ta tuno zancen Momy Nafisa da ta ce duk runtsi ta tsaya a kan ra’ayinta. Don haka sai ta ce, “Dad don Allah ka taimake ni. Wallahi Dad ba na son shi.” Ya ce, “what?! Ina cewa mun gama wannan maganar.
» Ya rike kansa yana
tunanin yadda zai bullo mata. Can ya saki.
Ya dube ta cikin lalama. “Mimi ki yi nazari da kyau. Tunda kika fito cikin mahaifiyarki nake dawainiya da ke. Na fifita ki cikin
‘ya’yana. Na yi miki dukkan gata. Mimi zan
•tambaye ki, na taba neman wani abu gurinki?”
Ta ce, “Dad, ni ba ni da komai da za ka nema. Ni ma da kai nake takama.
Ya ce, “to yau ina neman alfarmarki, ki taimake ni ki min biyayya, ki auri Abbas.
” Ta ga kamar zai sauko ya runsuna mata. Sai ta yi sauri ta ce, “na amince Dad.” Ta soma kuka wi-wi. Ya rungume ta. “Na gode ‘yata. Ni da ma na san irin son da kike mini ba za ki ba ni kunya ba. Daina kuka. Ki share hawayenki. Ki je ku yi magana. In kun gama, ni ma ina son mu yi magana da ke. Za mu je store din wani abokina ki za6i kalolin gadon da kike so. Gidanki dakunan barci shida ne; gaba dayansu zan zuba miki gadaje na alfarma ‘yan Dubai da Chaina da Indiya. Sannan zan nuna miki wata mota da na yiwo miki oda. Ba ta Karaso ba, amma hotonta yana cikin laptop dina don ki yi yawon amarci in kun dawo shakatawa.
Tashi maza ki je kinji Mimi.”
Mimi ta mike cikin kasala ta nufi dakinta. Mayafi kawai ta dauko, sannan suka jera da Mahaifinta har kofar falon baki ya raka ta. Sai da ta shiga sannan ya dawo.
Ta zauna kujeri biyu tsakaninta da
Abbas. Ya mike ya dawo wadda suke daf da juna ya zauna. Sabon kuka ta soma. Abbas ya ce, “haba Mimi, wai ta ina Allah ya rage nine da kike ta ki na har haka?” Ta dago ta dube shi, “ya rage ka ta soyayyata. Abbas don Allah ka taimaka min ka rabu da ni. Khalil kadai nake so.”
Ya tausasa murya, “Mimi ki ba ni dama ni ma’ in nuna miki kalar tawa soyayyar. Na yi miki alkawarin zan koya miki sona har sai kin manta cewa an taba halittar wani da namiji a doran duniya in ba ni ba.
Ta ci gaba da kukanta. Ya ci gaba da fadin, “gobe karfe goma zan zo mu fita. Ki fada ma Kawarki Amina, zan zo da abokaina don mu duba guraren da za mu yi shagalinmu. Me da me kike son mu yi? Ni dai ina son dinner.”
Ta ja tsaki, “don Allah ka bar ni, ka shiga tsakani na da mahaifina.
.” Ya ce, “kin kasa yi masa biyayya ne Mimi? Me zai sa ba za ki yi wa mahaifinki sakayyar son da ya yi miki ba?”Ta mike, “zan je in kwanta,
kaina ciwo yake.” Ya ce, “ba ki ba ni amsa ba.” Mimi ta ce, “ba ni da amsar da zan ba ka. Amma ka sani in ka matsa cewa sai ka aure ni, nadama da dana sani sune Karshen lamarin.
Shi ma ya mike, “ban damu da su ba Mimi, saboda ban taba sanin su ba. Kada ki manta gobe karfe goma za mu zo. Fatana za mu same ki da kawarki.” Suka fito a jere. Ta. ce, “ban taba ganin mutum mai son kai irin ka ba.” Ya ce, “ban taba ganin mara tausayi irin ki ba. Ko barci fa ba na yi, amma ban damu sosai ba, da kin zama a gefena, zan rama duk barcin da na ci bashi.”
Tsaki ta ja,
“har yanzu ban taba hasashen hakan ba. kuma wannan ya nuna min ba zai faru ba.
Ko cikin mafarki aurenmu ba zai kasance ba, na yi ma kaina alkawari.” Daidai
lokacin suka iso babban falon, ya runsuna. ya yi wa Dad bankwana tare da sanar da shi
“cewa gobe za su fita don duba guraren da ya dace su yi bikinsu. Dad ya ce ba damuwa,-sai ka zo. Ya kalli Mimi wadda ke shirin yin samanta ya ce, “ki taka masa mana zuwa gurin mota.
“Ba ta yi gardama ba, suka fita.
Ya dube ta, nawa kika sa in auren ya kasance?” Ta ce, “in har auren nan ya kasance, na yi maka alkawarin halaka kaina.
” Ya waigo ya dube ta, “ni kuma na yi miki alkawarin hana hakan faruwa. Sannan zan yi kokarin ganin mun samu ‘yan biyu a haihuwarmu ta farko.” Rasa me za tace tayi, sai ta ja tsaki, ta koma ciki tana jin shi
yana cewa, “mu kwana lafiya.”
Dad ya ce, “zo Uwata zo ki ji.” Ya
bude laptop dinsa ya dinga nuna mata
kalolin kayan kicin din da Momy Nafisa ta siya ta turo masa ya gani. Ya ce, “suna da
kya” sunyi miki?” Cilin kosava tace eh.
Ya nuna mata motarta. Motar ta ja
hankalinta don ta shekara mai zuwa ce,
amma ga shi an sai mata cikin wannan shekarar. Yace, “bari ki ga fa irin gadaje da abokina ya turo min. Su ma sai kin zaba.”Ta kalle su, sannan ta kalli Dad, “sun
yi yawa.» Ya ce kar ki damu uwata. Zan yi miki duk abin da kike so. Zan kashe ko
nawa ne gurin auren nan ba tare da in cewa na yi asara ba. Ribar mai daya in aka ba ni
kwangilarsa, zan ribanya dukkan kudin da na kashe.” Mimi ta mike, “zan sha magani Dad, zan kwanta ne.”
‘ Ya ce, “to je ki kwanta. Ya fada miki za ku fita karfe goma ko?” Ta ce, “eh.” Ya ce, “to sai ku je har da Na’ima.” Ta ce, “ok A sama Mimi ke ta nazarin abubuwa. Zuciyarta ta fi aminta cewa ta bi umurnin Mahaifinta. Dubi duk daular da yake shirya mata. Gaskiya bai kamata ta bari a ji su ba, ita da Mahaifinta. Hakuri shine kurum mafitarta. Za ta huce haushinta a kan Abbas ne kurum, wanda ya dage cewa sai ya aure ta.
Har ta kwanta da nufin barci, sai agogonta ya buga sha daya. Kallon agogon ya zo daidai da ringin din wayarta. Khalil ne. Gabanta ya fadi. Shi da take tunanin shafe babinsa, amma ba ta iya share shi, don haka ta daga. Cikin sanyin murya ta ce, dear ina ka shiga na kasa samunka a waya yace nayi kokarin na haqura dake ne shi ya sa na kashe wayata, sai na ga ashe ba zan iya ba. Zan mutu Mimi. Don Allah ki fada min yaya za mu yi.” Ya soma kuka. It ma kukan ta soma yi. Sai kuma ta tuna da batun Malam Isma’il. Da sauri ta ce, «yawwa Khalil zan yi wa Malam din nan magana, ko zai ba mu magani. Ya ce ai ba
Hmmmm