CANJIN RAYUWA CHAPTER 15 BY HALIMA A K/MASHI
kawai. ka wuce gurin kamar yadda na fada maka. Ya ce, “gobe za mu tattauna da shi. Amma Mimi ba ta isa ta ja min asara ba. Ta leko ta koma min kenan Ita kuwa Hajiya Sauda, wadda ba ta san komai ba, sai da Alhaji ya fada mata, amma ita ma yanzun laifin ya shafe ta, ta Kira Mimi. Can kasa-kasa ta ji muryar Mimi ta amsa sallamar Hajiyar. Hajiya ta ce ba ki da lafiya ne?” Mimi ta soma kuka,Dad ne wai sai na auri dan Minista, kuma mi ba na son sa. Hajiya Sauda ta ce, “ni dai in na isa in fada miki ki ji, to ki bi zancen Mahaifinki, ki auri wanda yake so. Yanzu ke wannan ba abin kunyarki ba ne, sauran ‘yan uwanki su ji kina takaddama da Ubanku? Mutumin da ya muna miki gata, ya yi miki duk abin da ki ke so, ya nesanta ki da duk wani abu da zai bata miki rai. Mimi na zaci ko wuta babanki ya hura ya ce, ki shiga, za ki shiga ba tare da kin tsaya dogon nazari ba. Ashe ba kya yi masa son da yake yi miki. Ki yi tunani sosai. kuma kiyi abin da ya dace. Shawarata kenan.” Ba tare da taji uzarin Mimin bat…