CANJIN RAYUWA CHAPTER 15 BY HALIMA A K/MASHI

kawai. ka wuce gurin kamar yadda na fada maka.

Ya ce, “gobe za mu tattauna da shi. Amma Mimi ba ta isa ta ja min asara ba. Ta leko ta koma min kenan

Ita kuwa Hajiya Sauda, wadda ba ta san komai ba, sai da Alhaji ya fada mata, amma ita ma yanzun laifin ya shafe ta, ta Kira Mimi. Can kasa-kasa ta ji muryar Mimi ta amsa sallamar Hajiyar. Hajiya ta ce ba ki da lafiya ne?” Mimi ta soma kuka,Dad ne wai sai na auri dan Minista, kuma mi ba na son sa.

Hajiya Sauda ta ce, “ni dai in na isa in fada miki ki ji, to ki bi zancen Mahaifinki, ki auri wanda yake so. Yanzu ke wannan ba abin kunyarki ba ne, sauran ‘yan uwanki su ji kina takaddama da Ubanku? Mutumin da ya muna miki gata, ya yi miki duk abin da ki ke so, ya nesanta ki da duk wani abu da zai bata miki rai. Mimi na zaci ko wuta babanki ya hura ya ce, ki shiga, za ki shiga ba tare da kin tsaya dogon nazari ba. Ashe ba kya yi masa son da yake yi miki. Ki yi tunani sosai. kuma kiyi abin da ya dace.

Shawarata kenan.” Ba tare da taji uzarin

Mimin bata kashe wayarta. Alhaji Lawal ya kawo sadakin Zainabu duba dari kamar yadda lnnarta ta

fada musu, Kuma an kawo akwatuna an

kuma sa ranar bikin sati biyu. Zainabu na ta

kuka kuma har gidan su Mahmood ta je ta

fada masa, ta kuma bukaci ya ba ta wayar don Allah, ta kira Isma’il. Ya ce mata ai

kawai ta je ta bi maganar iyayenta. Isma’il

ba abin da zai iya tunda an rigaya an yi miki

miji. Shi ba ya so ma Ismalil din yaji zancen ma.

Haka ta tafi ba tare da ta cika burinta

ba. Isma’il kuma duk kwanakin sai yayi ta fama da muggan mafarkai marasa kai. In ya

kira Mahmud, sai ya ce masa kowa lafiya

Tun kwanaki da ya yi waya da Zainabu, Mahmud bai sake hada su ba. In ya ce masa don Allah ya je gun ta za su yi waya, saiya

ce masa ba lokaci. Daga karshe har ya ji

haushi, ya ce,

“na daina cewa ka kai mata

wayarka. Da na dawo zan sai mata in huta Mahmud yace, “ka taimake ni, don ba a son raina nake zuwa ba.” Ismail ya kashe wayarsa cikin takaici.

Kusan kwanaki uku, Ismail ya shiga gidan don koyar da Mimi, har lokaci ya cika ba ta fitowa, don haka sai ya Kuduri niyyar yau in Alhaji ya dawo zai sanar da shi. Haka kuwa bayan sun yi sallar isha, sai ya sanar da Alhajin. Alhaji ya ce zai yi mata magana. In ma ba ta fito ba kar ka damu. Ka Ci gaba da koyar da kannenta. Ismail ya ce shi ke nan. Alhaji ya ce in ta fito kuma, to don Allah ka dinga yi mata nasiha. Kaji ko?

Isma’il ya ce, insha Allah.

Momy Nafisa ita da Na’ima sun kulle kansu a dakin Momy tana sanar da Na’ imar yadda tsarin da ta yi yake tafiya yadda take so. Ta ce an kusa zuwa gurin kar ki damu.

Na’ima yanzu fa har Hajiya Sauda, Alhaji haushin ta yake ji. Ya zaci ita ce ke zuga Mimi. Shekaran jiya Mimin ke fada min wai Hajiyar Saudar ta ce lallai ta bi zabin Alhaji. Na ce mata Mimi kin san dai sai dai Mahailiyarki ta gwada min ta haife ki, amma ba ta kai ni son ki ba ko? Mimi ta ce

Eh. Na ce to kiyi duk abin da nace Ita kin

ga ba ta yi boko ba, ba lallai ta son ‘yancin kanta ba, bare naki. Mimi ta ce haka ne.

Nan da nan na zuge ta. Sai da na goge dan

tunanin data soma yi na danganar da Uwar ta sa tayi.” Naeema ta ce Momy ai naji dadi.

Yanzu Dad ya fi kula mu a kanta. Momi tace shegiya ba, ni ma na dan ji tsai, a yi nan

Dad dina, a yi can Dad dina, ta kwaikwayi

muryar Mimin, suka kwashe da dariya.

Na’ima ta ce, “to ba ki ganin Dad zai iya

daura musu auren, ni kuma fa? Tanda kin ce masa kawai su sa rana.” Momy ta ce,

*ina so ne a yi mai yiwuwa ne a gama. Shi ya sa nake son a sa rana. Ke dai duk abin da

na ce ki yi, to ki yi kokari ki aikata.

Na’ima ta ce, “an gama,’

Alhaji Akilu da Alhaji Bishir suna

zaune cikin ofishin Alhaji Bishir din, sun

zabi haduwa a nan ne don su tattauna batun

auren yaransu. Alhaji Bishir ya ce, ka san

ja’irar yarinyar nan wai ina fada mata sai take neman yi min gardama.” “Haba dai?!”

in ji Alhaji Akilu. Alhaji Bishir ya ce,

“Allak kuwa. Amma na san duk iyayi ne na yaran nan.

• Alhaii Akilu ya ce, “ka san

mata ba mamaki tana zaton mu ne muka hada su, ba shi ne ya ganta ya ce yana so ba.

“Ka bar ta kawai. Da zaran an yi

Qiyayyar mace ba ta dorewa. Sai dai in bata sama kula ba. Cikin jin dadi, Alhaji Bishir ya ce na gode da ka fahimci hakan. Yanzu wane

Lokaci kake ganin za mu sa?” Alhaji Akilu ya ce kar mu ja abin mu yi mu wuce gurin.

“Ni ma haka na gani, in ji Alhaji Bishir.

Mafi sauki mu saka sati uku ko hudu.

Alhaji akilu ya ce, “mu bar shi hudun, don na ji mata suna cewa za a fita Dubai ko Chaina hado kayan auren. Shi kuma Angon ya soma gyaran gidan nan nawa na Asokoro

Alhaji Bishir ya ce, *ka fasa sai da shi ke nan?”

Ya ce, ” ba dole in fasa ba,

tunda Abbas ya dage gidan yake so? Gidan yayi masa girma, amma shi wai tsarin gidan ya yi masa.” Alhaji Bishir yace a bar masa. Allah ya sa hakan yafi alheri. Alhaji Akilu ya ce,amin. Zan turo

waliyyan nasa, kanina da Alhaji Sa’idu abokina za su zo.” Alhaji Bishir ya ce, babu matsala. Ni ma zan yi wa nawa kanin da kuma Alhaji Kabiru magana. Yaushe ne za su Zo?”- Alhaji Akilu ya ce cikin satin nan.

Za dai mu yi waya.» Bavan sun gama

tsarinsu ne suka koma batun kasuwancinsu.

Abu kamar wasa, zance ya soma nuna, don an kawo sadaki. Kuma Momy Nafisa da wata kawarta sun shaki kudi gurin Alhaji sun nufi Dubai siyayyar kayan kicin, ta zage kuma tana ta zabar masu kyau da tsada, domin tana fatan su rikide su zama na Na ima.

“Tafiyarsu da kwana biyu, sai ga

Khalil da mahaifiyarsa har gidan su Mimi.

Yadda abin ya faru kuwa, Hajiya Amina ta ga danta ya shiga damuwa da tashin hankali ta rasa gane kansa, sai ta tsare shi a daki don ya fada mata damuwarsa. Ta yi ta lallashin saiya nuna masa cewa, ita ce ta fi dacewa da Ta san matsalasa, kuma ta magance masa, in har za ta iya. Jin haka ya sa shi koro mata komai. Ba ta yi kasa a guiwa ba ta sanar da Mahaifansa wanda hankalinsa yake kan siyasa. Nunawa ya yi wannan ba damuwarsa ba ce damuwarsa kawai Khalil ya yi karatu ba tare da zabin da ya wuce bai wa dan nata hakuri, gami da shawarar tsayawa kan karatunsa. Amma cikin. kwanakin sai ga yaro kwance warwas, ba ci ba sha, duk ya fita hayyacinsa. Ba arziki ta taso shi zuwa Abujan don rokon a bar masoyan su ci gaba da soyayyarsu har zuwa lokacin da za su hattama karatunsu, sai a daura musu aure.

Na’ima da ke falo ita ce ta amshi bakuncin nasu.suka gaisa. Ta ce, kun zo gurin Momy ce? Ga shi ba ta nan. Hajiya Amina ta ce, Mahaifinku fa?”Na’ima ta ce,

yanzun nan ya fita. Khalil ya ce Mimi fa?

Na’ima ta ce tana samanta; in kira ta ne?” Hajiya Amina ta ce, eh. Kudundune take cikin bargo. Yau tun safe zazzabi ke jikinta.

Na’ima ta yi sallama, ta shiga ta sami Mimi.

Baki aka yi. Sun ce in kira ki. Ta ce daga ina? Ki ce su hawo, ba zan iya sauka ba. Na’ima ta raka su har falon Mimi, sannan ta ce, “Sis ga su nan.” Mimi ta yunkura za ta tashi, ta kasa. Ta ce, tambaye su Na’ima, daga ina? Ba zan iya tashi ba.” Na’ima ta tambaye su. Sai ko Hajiya Amina ta mike mu je kawai, in yi mata bayani.

Ta zauna bakin gado, sannan ta kamo hannun Mimi, “*Yata ni ce mahaifiyar Khalil.” Da sauri, Mimi ta tashi zaune.

Sannu da zuwa Momy. Wa ya nuna miki gidan nan?” Ta mce, ga shi nan a falo, tare muke.” Da sauri Mimi ta sauko daga gadon don tabbatar wa idanunta Khalil dinta ne kuwa? Sabbin hawaye suka soma zubo mata. Ta je ta zauna a kujerar da ke kusa da shi. Cikin damuwa ya ce, “dubi yadda kika rame, don Allah Mimi ki yi hakuri. Ga Momy na nan na ‘kawo ta za ta yi magana da Momy dinku ko Dad.”

Mimi cikin kuka ta ce,

“ba zai saurare ku ba, don sun yi nisa da shirin aura min Abbas.” Hajiya Amina ta dafa bayan Mimi. Bayan ta zauna a hannun kujerar da take, sai ta ce,’

“kar ki damu ‘yata. Yaya za a yi in gan shi?” Mimi ta ce bari in gwada kiran sa ko zai daga, don yanzu bai damu da daga kirana ba.Sai a kira na biyu, sannan ya daga. Me ya faru Mimi?”

Abin da ya soma

tambayar take nan, bayan ya daga wayar.

Ta soma kame-kame,am, am da ma

wannan ne, baki ne suke son ganin ka.

Hajiya Amina ta amshi wayar, «sannu da kokari Alhaji.” Ya ce,yawwa, wace ce?” Ta ce, “sunana Hajiya Amina daga Kaduna. Kuma nice mahaifiyar

Khalil saurayin Mimi, wanda take so.

Haushi ya kama Alhaji Bishir, amma sai ya danne, ya ce,to lafiya?”Ta ce, “na zone ina son ganin ka don mu yi magana a kan yaran nan. Ya ce,

“babu bukatar wata magana domin na riga na ba da ta. Yanzun haka nan da sati uku ne bikin. Don Allah ki ba wa dan naki hakuri.”

Tace, “amma Alhaji kana sane cewa ba ta so ko?” Yace, “ba damuwata ba ne, kuma ke ma ba damuwarki ba ce. In kin zo nemawa danki aure ne, tuni ya kamata ki yi haka ba yanzu ba. Yanzu kam kun makara.

Na gode. Sai an jima.

” Ya kashe wayar. Ta yi shiru, ta rasa me za ta ce wa yaran, ga shi sun tsare ta da idanu. Ta ce, «ku hakura kawai. Tashi Khalil mu tafi.

Mimi ki bi zabin iyayenki.” Sai kawai ta ga sun soma kuka su duka biyu. Mimi ta riko hannunta, “don Allah Momy ku gudu da ni. Ba zan iya rayuwa babu Khalil ba. Zan mutu, don Allah.” Momy ta ce, “ba zai yiwu ba ‘yar nan rufa min asiri.

Shi ma ya ce, “Momy don Allah mu tafi da ita.

,.” Uwar ta kalle shi, lallai ba ka da hankali.” Ta dafa kafadar Mimi, “ki yi hakuri ‘yata. Mu yi addu’a Allah ya yi mana zabi na gari.

. Har kasa Mimi ta biyo su da

kuka, har gurin motarsu. Ma’aikatan gidan* wadanda ba su san me yake faruwa ba, sai kallon Mimi suke yi. Sun fi zaton ‘mutuwa ce aka yi gagaruma. Fatansu Allah ya sa ba.

Maigidan ba ne domin gudun tarwatsewar aikinsu.

Na’ima ce ta kama ta suka nufi cikin falon kasa. Ta zauna ta ci gaba da kuka,

Hmmm