CANJIN RAYUWA CHAPTER 14 BY HALIMA A K/MASHI
Alhaji Bishir ya Kosa ya isa gidansa don kai wannan albishir. Haka nän – Mimi ta kosa matuka Dad din nata ya dawo don ta sanar da shi labarin masoyinta Khalil. Momy Nafisa kuwa tana cikin damuwa, sannan tana ta tufka da warwara: a kan yadda za ta hada fitina tsakanin Mimi da Mahaifinta. A haka Alhajin ya iso gidan, cikin doki. Tun daga shigowarsa falon yake zuba kiran Nafisa! Nafisa ta fito cikin sauri tana cewa, “Alhaji ga ni. Lafiya kake ta kira na?” Ya ce, “afiya lau. Sai alheri.” Ta amshi jakar hannunsa da hularsa da malum-malum. “Muje ciki”Gabanta ya fadi. “Wani sabon kasuwancin ne?” ya ce, “wannan duk ya wuce nan.Sai da suka zauna, sannan ya ce,Abbas, ashe Mimi yake So?” Gaban Momy ya fadi. Ya ci gaba da cewa, “gaskiya nayi murna sosai. Burina zai cika.” Tayi dán yake, sannan ta ce, zai yiwu, za a yi murna. “gaskiya kam, da abin •’ Ya ce, “me zai hana shi yiwuwa? Daina fadin haka. Nafisa ta ce, dazun take sanar da ni cewa saurayinta zai zo daga Kaduna gaishe mu. Ya zaro ido yana kallon …