CANJIN RAYUWA CHAPTER 14 BY HALIMA A K/MASHI

Alhaji Bishir ya Kosa ya isa gidansa don kai wannan albishir. Haka nän

– Mimi ta kosa matuka Dad din nata ya dawo don ta sanar da shi labarin masoyinta Khalil. Momy Nafisa kuwa tana cikin damuwa, sannan tana ta tufka da warwara: a kan yadda za ta hada fitina tsakanin Mimi da Mahaifinta.

A haka Alhajin ya iso gidan, cikin doki. Tun daga shigowarsa falon yake zuba kiran Nafisa! Nafisa ta fito cikin sauri tana cewa, “Alhaji ga ni. Lafiya kake ta kira na?” Ya ce, “afiya lau. Sai alheri.”

Ta amshi jakar hannunsa da hularsa da malum-malum.

“Muje ciki”Gabanta ya fadi. “Wani sabon kasuwancin ne?” ya ce, “wannan duk ya wuce nan.Sai da suka zauna, sannan ya ce,Abbas, ashe Mimi yake So?” Gaban Momy ya fadi. Ya ci gaba da cewa,

“gaskiya nayi murna sosai. Burina zai cika.” Tayi dán yake, sannan ta ce, zai yiwu, za a yi murna.

“gaskiya kam, da abin

•’ Ya ce, “me zai hana shi yiwuwa? Daina fadin haka.

Nafisa ta ce, dazun take sanar da ni cewa saurayinta zai zo daga Kaduna gaishe mu. Ya zaro ido yana kallon ta. Sannan ya ce, wane ne shi? Wannan ba gaskiya ba ne. Inda Mimi tana da wani saurayi, nine mütum na farko da zan fara sani, domin kin san babu wani abu da take boye min. Ba ta da aboki ko kawar da ta fini.

Nafisa ta ce, haka ne, amma jiya ta yi min zancen. Da alamu kuma tana son sa sosai. Ya daga hannun, alamun dakatarwa.

Sannan ya sa kai ya fita daga dakin. Kai tsaye saman Mimi ya nufa: Tana kwance a kan kujerarta, chatin suke yi da Khalil, tana bashi labarin halin da take ciki na damuwa. Shi ma duk hankalinsa ya tashi. A sama ta ji muryar Dad yana cewa, Uwata ta shi zaune da sauri! Tana fadin Dad ka dawo ne? Ban sani ba, ai da na sauko.

Ya zauna kusa da ita. Yau ina cikin farin ciki ne Mimi. Burina zai cika. Ya kama hannunta, kin san na dade ina addu’ar Allah ya kawo miki mijin da zai kula da ke ko? Gabanta ya fadi, ta ce, “eh Dad.” Ya ce, “tO ga Abbas dan gidan Minista. Mahaifinsa yake sanar da ni tsananin son da Abbas din ke miki. Wannan lamarin ya zo a daidai da burina na hada surukunta da Minista. Zai kawo ci gaban kasuwancina, musamman ta fannin man fetur.

Ta ce, “Dad akwai matsala. Shi Abbas din ai mun gama magana da shi.” Yace, “wace irin matsala kuma?” Ta ce, “Dad, ya zo ya ce yana so na. Na fada masa ina da wanda nake so. Lokaci mai tsawo muna tare da shi. Dad ya kamata in bar shi in koma wa Abbas?” kallon ta kawai Alhaji Bishir ke yi. Bai fara jin haushinta ba don yana sa ran zai shawo kanta. Ya ce,

“za ki iya barin sa, tunda bai nemi aurenki ba.

Sannan ban zaci za ki boye min komai ba, wai kina tare da saurayi tsawon lokaci ban sani ba. To ina son ki ajiye batun wani saurayi. Ki natsu kin ji Mamana?”

Ta yi shiru, ranta bace. Idanunta sun soma kawo kwalla. Ya daga fuskarta,

“mene ne abin kuka? Murna za ki yi. Allah ya yi miki zabi na gari.” Ta ce, cikin kuka,

“Dad ba na son sa ne. Ai ni Khalil nake so.

Zai zo yau ka gan shi. Irin mijin da zuciyata take so kenan.Ya daga murya,Mimi mun zo

lokacin da zan ce ina son abu, ke kuma ba

kya so? Mun fara jayayya kenan?” Yanzu

kam kuka sosai take yi. “Dad ba haka ba ne, amma bai dace a tsananta min in so shi ba.

Kar ka damu zan kira Abbas din in sake tuna masa cewa ba na son sa.”

Saukar mari ta ji fau! A fuskarta. Yace, “ba ki isa bal”

A fusace ya nufi fita. Ta rike kumatu tana kuka sosai. Momy da ke labe ta sauka da gudu, jin alamun zai taho.

Cikin dakinta ta shiga. Lallai tana cikin

farin ciki. Bari ta je ta Kara wa wutar kananzir.

Ta fito ta nufi dakin Alhajin, tamkar

. ba ta san komai ba. Ta yi sallama, Alhajin

ya amsa a ciki, yana ta zirga-zirga a cikin

dakin nasa. Cikin alaye ta nufe shi, “lafiya

Alhaji? Me ya faru?” Ya kalle ta, “Mimi wai take nema ta tona min asiri. Bakina da na Uban dan nan na ce, na ba su yarinyar nan, amma in zo mata da batun, ta ce, ba ta san zancen ba?”

Nafisa ta zaro ido, tare da dafa kirji,

“in ji Mimin?” “Haka ta fada. Yau har marintq nayi” Momy Nafisa ta ce, “a’a wasa take yi, kana ji ko Alhaji? Kiyayyar mace ba ta wani tasiri, sai dai in ba a yi auren ba. Ku tsai da rana. Kafin ta kammala makaranta ku daura musu aure. Bikin kwa yi in ta gama karatun.” Ya ce, “kina ganin hakan zai yiwu?” Ta ce, “sosai kuwa. Idan ta san cewa da akwai igiyar wani a kanta, dole ta rabu da kowa.

” Ya ce, “ke ma kin

kawo shawara. Amma zan so ki je ki dan Kara ba ta shawara. Ko don gatan da na nuna mata, ya kamata ta yi min biyayya.” Momy ta ce bari in je. Amma kafin in tafi, za a hada maka ruwan wankan ne, ko abincin za ka fara ci?” Ya ce ba na bukatar ko daya. Ya zauna bakin gado, “bari in kira Sauda, ko zan samu natsuwa.

” Ranta ya

dan sosu, amma ta danne. “bari to in je gurin Mimi din. Ka ce da ita ina gai da ta. Kuka sosai ta samu Mimi tana yi.

Don haka ta shiga lallashinta da cewa ta yi shiru, su yi magana. Ta zone don sama mata mafita. Bayan Mimi ta share hawayenta ne, Momy Nafisa ta ce, “ki ce masa ya turo iyayensa, shi Khalil din. Kila in Alhaji yaga magabatansa sun zo ya hakura.”

Cikin disasshiyar murya ta ce,

“Momy ba na fada miki ba karatu yake yi?

Iyayensa, yanzu ba za su saurare shi da batun aure ba. Da ma mun bar shi a kan sai mun gama karatu ne.” Momy Nafisa ta yi shiru tana tunanin mafita. Mimi ta kama mata hannun, “don Allah Momy ki fada min yaya zan yi?”

Ta rungumo ta, “kwantar da hankalin ki Mimi. Wannan Karamin abu ne. Kuma kin sam Dad dink yana son duk abin da kike © so. Shawarar da zan ba ki ita ce, ki tsaya a kan ra’ayinki na cewa Khalil kike so. Zai hakura. Amma in kika bi ra’ayinsa, ba za ki ji dadin zaman auren wanda baki so ba.”

Mimi ta ce, “to ni ba na son Dad ya ce ban ji maganarsa ba.” Ta ce, “Kar ki damu da haka. Yanzun nan daga dakinsa nake. Ya ce in ya ga kin dage zai hakura.” Mimi ta sauke ajiyar zuciya, sanan ta ce,

“shi kenan zan tsaya a kan ra’ayina.’

Momy Nafisa tace, “duk runtsi ki ce ba ki son Abbas. “Mimi tace, *shi kenan.

Alhaji kam, Hajiya Sauda ya kira yana labarta mata komai da ya faru, tun daga burinsa har zuwa yanzu. Sannan yace ina son ki kira ta ki yi mata fada, ta bar batun wani yaro, ta tsaya ga wanda ni na zaba mata.” Hajiya Sauda ta ce, “Alhaji ba zan shiga zancenku ba, kai da lelenka. Abu daya kawai nake ganin zan iya. Shine zan kira ta in ba ta shawara.

Ya ce ban gane ba za ki shiga zancenmu ba. Ta ce Alhaj ke nan. Yanzu ne da ta kwabe muku ka san da ni? Ina uwarta mai son ta wadda aka canza mata da ni, saboda ni ina takura mata ta yar abin da ya kamata? Shawara kawai zan ba ta ta yi maka biyayya, amma ba wai in takura mata ba: Idan ta ki yarda, sai ka yi mata abin da take so, kamar yadda ka sabar mata tun tana Karama.” Shiru ya yi, ya kasa magana. Sai kuma ya kashe wayar.

Momy Nafisa ta same shi cikin damuwa, yana ta tattauna maganganun Hajiya Sauda a cikin zuciyarsa. Ta zauna kusa da shi. “Alhaji na yi magana da Mimi.” Ya kalle ta cikin sauri, “ta amince?”

“Mimi ta ki sam Alhaji. Kuka take ta yi. Da na tsananta mata da lallashi, da nuna mata cewa ta yi maka biyayya, sai ta ce min don na ga ba ni na haife ta ba. In da ni na haife ta ba zan so ayi mata auren dole ba.”

Ya ce,

“haka ta fada? Kenan tana da daurin gindin Mahaifivar tata? Domin da na kira ta a kan tayi mata fada, ce min ta yi ita shawara za ta iyabata, ba fadaba.”

Momy Nafisa, cikin jin dadi ta ce,

“amma Hajiya Sauda ba ta kyauta ma kanta ba. Ta yaya za ta hana ‘yarka ta yi maka biyayya?”

Ya ce, shi ne abin mamakin.

Amma zan gwada musu su duka cewa ba su isa ba.

» Ta ce, “abin da ya kamata kenan.

Da ma ku zauna kai da Minista ku sa lokacin auren sati uku ko hudu, ku daura

Hmmm