CANJIN RAYUWA CHAPTER 13 BY HALIMA A K/MASHI
Kai ba su da yawa ni yara na ishirin da biyu, mata na uku. Alhaji Akilu ya yi ‘yar dariya, ku manya ne, amma hakan ya yi kyau, dama ka yi Kokari ka cike, suka saka dariya, Alhaji Bishir ya ce, mu yi tare, kai ta biyu sai a yi rana daya. Suka kalli matan wadanda su ma dariyar suke har suna hada baki gurin fadin ku yi ta yi mana, ga dai yaranku nan, sun girma. Bayan sun gama gabatar da iyalansu sun dan yi wasa da dariya, sai kuma Mommy Nafisa ta ce, ya kamata mu je dining, nan fa aka hau kan teburin cin abincin. Mimi ta kalli Na’ima cikin maganar nan ta ta a hankali ta ce, ki lura tun daga kan Aisha zuwa kasa ni zan ji da su Daddies, Mommies da Brother Abbas. Yanda ta yi maganar, iyayen suka sa dariya, haka ta yi ta zuba masu sai da kowa ya ce, ya yi, ita ma Na’ima ta kula da na ta gefen. Bayan an kammala aka koma kan kujeru, Mimi da ba son hayaniya take yi ba, sai ta kama hannun Aisha zo mu je sama na. Hakan ya yi wa Mommy Nafisa dad, har ma ta dauki wayarta ta tura ma Na’ima messege, i…