Kai ba su da yawa ni yara na ishirin da biyu, mata na uku. Alhaji Akilu ya yi ‘yar dariya, ku manya ne, amma hakan ya yi kyau, dama ka yi Kokari ka cike, suka saka dariya, Alhaji Bishir ya ce, mu yi tare, kai ta biyu sai a yi rana daya. Suka kalli matan wadanda su ma dariyar suke har suna hada baki gurin fadin ku yi ta yi mana, ga dai yaranku nan, sun girma. Bayan sun gama gabatar da iyalansu sun dan yi wasa da dariya, sai kuma Mommy Nafisa ta ce, ya kamata mu je dining, nan fa aka hau kan teburin cin abincin.
Mimi ta kalli Na’ima cikin maganar nan ta ta a hankali ta ce, ki lura tun daga kan Aisha zuwa kasa ni zan ji da su Daddies, Mommies da Brother Abbas. Yanda ta yi maganar, iyayen suka sa dariya, haka ta yi ta zuba masu sai da kowa ya ce, ya yi, ita ma Na’ima ta kula da na ta gefen. Bayan an kammala aka koma kan kujeru, Mimi da ba son hayaniya take yi ba, sai ta kama hannun Aisha zo mu je sama na. Hakan ya yi wa Mommy Nafisa dad, har ma ta dauki wayarta ta tura ma Na’ima messege, inda ta ce, ga dama nan ta samu, ki lura da Abbas kuma ki ja hankalinsa.
A sama, Aisha sai santin falon Mimi take yi, Mimi ta kai ta ko’ina a saman ta, ta ce; gaskiya Mimi kin ji dadi, ke kam ‘yar gata ce, duk nan ke daya? A ina ki ke karatu? Mimi ta ce, Dubai, ai in fada maki Aisha Dad yana ji da ni fiye da zaton ki, duk abinda ni ke so yana yi min. Can kasa kuwa Mommy Nafisa
• ta ja Hajiya Bilkisu zuwa dakinta, Alhazan su ma tasu hirar su ke yi, kananan kuma sun bar falon Alhajin sun nufi na su, suna gaban damfareriyar talabijin din falon suna búga game,
Na’ima ta koma kusa da Abbas wanda ke ta latsa wayar shi ta ce Bros ya kokari, ya kalle ta, Alhamdulillah, ya makaranta? Ta ce, ai yanzu ina gida ne ban fara zuwa makaranta ba, ina son in je waje nima, amma dadinmu ya ce, ko Abuja ba zan bari ba. Ya ce, kila kina rawar kai ne, ta ce, a’a ra’ayinsa ne haka, sai kuma ta canza maganar da cewa in ga phone din ka bros, ya mika mata ga shi. Ta yi ta shiga nan fita nan ta dinga kallon hotunan shi lokacin yana karatu a waje, ya birge ta sosai. Ta ce, ka hade fa Bros, ya ce, na gode, ta saka lambar wayarta a ta shi ta kira lambar, ta fito a cikin wayarta ta ce, ga lamba ta nan, in maka saving din ta, ya ce, eh, ta ce, kana da me irin suna na? Ya ce, a’a ta saka sunan, sannan ta yi saving din ta shi. Kamar daga sama sai ta ji ya ce, sa min ta sister din ki, mene ne sumanta na gaskiya? Tace, Khadija, ya ce, ok sa min lambarta, da ta ta shi, sai ta canza lamba daya ta mishi saving ta ce, in kun ta fi sai yaushe? Ya ce, ku ya kamata ku kawo mana ziyara ai, ta ce, haka ne, za mu zo, muryar Alhaji Akilu Bala ta katse su.
Goma ta yi ku tashi mu tafi, Alhaji Bishir ya ce, tun yanzu? To sai mun zo mu ma, Alhaji Akilu ya ce, abinda zance kenan muna jiran zuwan ku, amma da rana za ku zo mana ko? Alhaji Bishir ya ce, in ka samu lokaci ka sanar da ni sai mu zo, ya kalli Na’ima, je gurin Mominku ki ce su fito, Alhaji Akilu ya ce, ka san mata da Kus-Kus.
Sun fito inda Mommy Nafisa ta cika Hajiya Bilkisu da kayan mata, Alhaji Bishir ya cika yaran da kudi, Na’ima kuwa Abbas ta yi wa kyautar turaruka masu kamshi, ita kuma Mimi kawarta Aisha ta yi ma kyautar irin kayan jikinta da takalmi da kuma turare, sannan suka yi canjen number,
Alhaji Bishir ne ya kira Mimi ya cê, su sauko, Abbas ya kosa ya sake ganin Mimi don komai na ta ya yi masa, kuma ita ce yake ganin zai zaba ta zama matarsa, tunda suka fito yake sake kallonta zuciyarsa tana Kara kurantanta. Sun raka su har bakin möta katuwa Jeep, direba ya na ciki yana jiransu, aisha ta rungume Mimi Sis sai na ji ki, Mimi ta ce, yawwa Sis Aisha sai kin jini.
Tunda suka koma gida, Abbas ke kiran layin da Na’ima ta sa mishi na Mimi, wani ke dagawa, duk ya damu sai kai kawo yake yi a gefen na sa, ji ya ke yi tamkar ya nufi gidan su Mimin ya fada mata ya na sonta.
A gidan Alhaji Bishir kuwa bayan sun yi bankwana da juna kowa ya shiga makwancinsa, Dad da Momi sun shiga na su makwancin, sai take ce masa, Alhaji naga kamar Na’ima da Abbas sun aminta da juna, ya ajiye rigarsa da ya dauka da niyyar sa wa ta bacci ya ce, haba!! Ta ce, (cikin dariya) da gaske kuwa, har canjin number ta ce min sunyi. Ya kamo hannunta Nafisa Allah ya sa haka ta tabbata da sai na fi kowa murna. Da Na’ima ta ga auren gata, ina son mu hada surukanta sosai, ta haka zan zama na gaba a cikin masu yin dillancin man fetur, buri na in zama na daya Mommy Nafisa ta ce, kar ka damu, zan kula maka da wannan alakar ta su, Insha Allahu har a kai ga yin auran, ya rungume ta, ke kanki kyautar ki daban ce, suka sa dariya.
Abbas ya samu Aisha a cikin falon su, ya sami waje kusa da ita ya zauna ya ce, Sis don Allah ba, ta ce ina jin ka, ya ce lamba za ki ba ni, ta kalle shi, ta wa? Ya ce kawarki, ta sa dariya, wacce kenan? ya ce, ta gidan da muka kai ziyara mana, na ga kun Kulle. Aisha ta ce, Ok, Mimi ko lallai ka samu ‘yar gaye, ka ga gefenta kuwa? Ta shiga ba shi labari, yana sauraronta zuciyarsa tana Kara fari. Ta ba shi number ya koma sasan shi, sai dai abin takaici ya kira ta kusan so biyar amma ba ta daga ba. Abinda bai sani ba, Mimi ba ta daga number din da ba ta sani ba, don haka tana kallon wayar ta na yi tana katsewa. Sake komawa ya yi hankali tashe gurin Aisha yana tuhumarta cewa ba ta ba shi lamba daidai ba. Ta ce, bari in kira ta da layi na, a ringin na hudu ta daga ta ce, Hello Sis Aisha ya ya aka yi? Lafiya lau in ji ta, Bros ne ya yi ta kira ba ki daga ba, shine ya zo ya tare ni wai na ba shi number ba daidai ba. Ta ce, ok dama shine? Ayya ban sani ba tsari na shine ba na daga bakuwar number, amma zan yi saving dinta yanzun nan, ta ce to zai kira ki,
Mimi ta ce babu damuwa ya kira kawai.
Sasan shi ya sake komawa, sanna ya kira ta, sun gaisa bai tsaya bata lokaci ba ya ce, Mimi kin tafi da dukkan tunani na, tun da na ganki na ji gaba daya na birkice, ke ce matar da su Dad su ka ce in nemo, lokacin da suke min maganar aure, ke kawai ni ke kallo a amaryar. Mimi ta yi shiru tana jinsa, sai da ya kai aya sanna ta ce kayi hakuri da abinda zan ce ya ya Abbas. Gaskiya ina da wanda ni ke so sosai, ban san adadin son da muke yi wa juna ba. Don Allah ka yi hakuri saboda gudun faruwar haka na bar falon don na lura da yawan satar kallon da ka ke min, amma ina me yi maka addu’ar samun wadda ta fi ni.
Sannan zan ba ka shawara ga kanwata
Na’ima, ba ta tare da kowa, kuma tana da hankali, ya katse ta, ki bani lokaci in zo mu yi maganar daga zaune. Ta ce kowane lokaci ina gida, ya ce, in zo yanzun? Ta ce a! haba dai mu barshi gobe. Sannan sharadi kar ka zo da batun so na ka zo da batun kanwata, ya yi
‘yar dariya, sai dai in na zo din, ta ce, shikenan.
Misalin shadaya Ismail ya nufi gurin karatunsa kamar kullum, ya jira sannan ta fito, haka nan ya bude kur’ani yana karantawa kamar yadda ya tsara. Ya gama ya kalle ta, gaskiya ya kamata yau ki karanto inji ko kina rikewa tunda kin ga mun kammala shafi biyu na suratul Bakara, sai ji amma a ce kullum ni zanyi karatu, ke kina danna waya don ban sa ran cewa kina ji ba. Ta ce, in fahimta, ko kar in fahimta ya shafi albashinka? Don haka ka yi kawai ina jin ka, dama aya biyar yake yi kullum, don haka ya karanto mata ko da ya gama ya dago ya kale ta daidai lokacin wayarta ta yi ringing, ta daga tare da cewa, Brother Abbas, ya na’am gani na zo fa, ta ce, Ok, ka shiga mana, Na’ima tana nan a falo ka ce ta kawo ka falon baki na ciki. Ya ce, Ok to, Ismail ya kalli agogo abin haushi yanzun shadaya da rabi saura minti talatin.
Bako ya yi sallama Ismail ne ya amsa da ya shigo, sai ya mika wa Ismail hannu. shi ma ya miko masa kenan za su gaisa Mimi ta ce, a ‘a Yaya Abbas, kar ka hada hannu da shi, Abbas ya dakata sannan ya kalle ta lafiya? Ta nuna ma shi gurin zaman, zauna kawai, Ismail ya bude Kur’anin shi ya ci gaba da karantawa a zuciya, sai dai kunnansa yana gurinsu. Ta ce, dan aiki na ne, kana dan minista za ka hada hannu da talaka? Ni da zai koya min karatu ma na ki ya ji karatu na don bai kai matsayin ba, sai kai ka hada hannu da shi, kodayake mu bar zancan shi, ka iso lafiya? Ya ce, lafiya lau, da farko ai na zaci shine na musamman din na ki, ta ce, shishshhh haba mana Abbas ka cuce ni, da ka hada Khalil da wannan, don Allah ka bani hakuri don ka cuce ni. Abbas ya ce, to shikenan yi hakuri, amma so ba shi da haka, kuma wannan din ban ga laifinsa ba, ta ce zan hau sama in kana irin wannan zancen, ka yi abinda ya kawo ka.
Abbas ya ce, Ok na san jan ajin ku ne na mata shi ya sa ki ka ce min kina da wani, kar ki damu da jan aji don kina da ajinkin Mimi. Tun ranar da muka zo ban kara sukuni ba don Allah ki duba ni. Ta ce, Yaya Abbas don Allah ka bar zancen nan, ni da Khalil mun fi shekara daya muna tare, shi ya sa tun jiya na ce kar ka zo da batun nan, ka zo in ba ka kanwata Na’ima. Ba laifi in ka ce mu zama abokai, mu dinga ba juna shawara, ya ce, Mimi ni dai ke ni ke so, ta sa yatsan ta a kan lebenta ta ce shhhh, don Allah bar zancan, ka amince da batu na, bari ka ga Na’ima, tana da kyau kuma ga hankali.
Kafin ya ce komai ta danna kiran layin
Na’ima, ba ri ka ganta da kyau, Na’ima daidai lokacin tana dakin Momi cikin damuwa tun Zuwan Abbas da ta nuna mashi falon baki kamar yadda Mimi ta umurce ta. Dakin momy Nafisa cikin damuwa tana fada mata cewa, Abbas ya zo, Momy ta ce dama na san zai zo, Na’ima ta ce ai gurin Sis Mimi ya zo.
Gaban Momy ya fadi ta maimaita cewa, gurin Mimi? Na’ima ta ce, suna ma falon bakl, Momy ta yi shiru tana tunani, can ta ce, ni wai yaya zani da wanna shegiyar Mimin? Wayar Mimin ce ta katse su ta dubi Momy, ga Mimin tana kira na, Momy ta ce, daga mu ji, Mimi ta ce, Sis Na’ima ki kawo ma Bros Abbas abin sha ta ce, ok, gani nan.
Ta kalli Momy, wai in kai masa abin sha, ta ce maza je ki kai masa, har ta fita, ta kwalo mata kira, zo Na’ima ta ciro wani turare a jerin turarukanta ta fesa mata sosai, sannan ta ce, je ki ko babanku na fesa turaran nan yana sa shi nishadi. A falo ta ajiye dan kwalin kanta, a ranta tana fadin in gashi ne ni ma akwai.
Da sallama ta shiga falon, nan ma
Ismail ne ya amsa, wanda ke zaune yana jin komai, ta shiga ta aje, sannan ta sake gaida shi, Mimi ta ce, zuba masa a kofi Na’ima ta zuba, sanna ta ba shi a hannu ya amsa yana ta kallonta, sai da ta tafi sannan ya ce, Mimi kuna da bambamci da yawa, kyau kuma ba iri daya bane, ina son ki don Allah. Mimi ta ce, in ba ka amince da Na’ima ba to ka tafi ka nemi wata, na yi haka ne don na san iyayanmu za su yi murna. Ya ce, ni da ke za su yi murna, ta ce, to abinda ya yi ni, shi ya yi Na’ima, ya mike, ke da ita akwai bambamci, zan tafi amma fa ban hakura ba.
Ismail dariya ya yi ta yi a daki tare da tausaya ma Abbas, don ya san menene so, in ya tuna Zainabun shi, qila ma in ya ci wata daya sai ya je Katsina ya ganta, ya sai mata waya don ya dinga jim muryarta kowane lokaci.
Mimi tana cikin damuwa, sam ba za ta so zancan nan ya kai gurin Dady ba, domin zai so hakan. Tun bayan tafiyar Abbas Mimi take sake-sake. Momy ta hau sama ta sami Mimi tana ta tunani ta ce, Na’ima ta ce min Abbas ya zo gurinki, Mimi ta bata rai, ya z0 ne ya dama min lissafi Momy, wai sona yake yi. Gaban Momy ya fadi, ta dan zaro ido, sai kuma ta wayance, mene ne, to ki amince kawai. Mimi ta ce, gaskiya Momy ina da wanda ni ke so, Momy ta ce, haba da gaske?
Ta ce, Allah, sunan shi Khalil, su ‘yan Kaduna ne, baban shine dan takarar da aka tsayar a Jihar Kaduna zai yi takarar gwamna.
Sunan mahaifinsa Usman Kaura, haifaffan Zariya ne. Momy ta ce, to shawarar da zan ba ki kiyi saurin sanar da dadinku kafin shi ya sanar da na shi mahaifin.
Mimi ta rike hannun Momy, don
Allah Momy ki taimake ni ki fada min yanda zan fada masa. Momy ta ce, kar ki damu in . ya dawo ki same shi ki fada masa, inda hali ma ki ce da yaron ya zo ya gaida shi. Mimi ta ce, ai tsoro na kar Dad ya ce masa ya turo iyayansa, to shi kuma karatu yake yi, gidansu ba za a yi masa aure yanzu ba, sai ya fara aiki. Momy ta ce, ba damuwa don wannan kin san dadinku bai son damuwarki, ba zai takuraki ba. Mimi ta dan ji sanyi a ranta, ta kuma yarda duk abinda take so, shi mahaifin take so. Abbas ya zauna kusa da mahaifinsa
Alhaji Akilu Bala ya ce, daddy na ga irin matar da ni ke so. Ya tattaro hankalinsa ga dan nasa, ‘yar gidan waye? Abbas ya sunkuyar da kai, gidan da muka je ziyara, gidan Alhaji Bishir Masari. Alhaji Akilu ya dafa kafar danshi, yaro ka yi abinda nake so, ka san buri na? Mu zama surukai da shi, Abbas ya ce, saboda me Daddy? Ya ce, saboda siyasa ta Abbas, duk dan siyasa yana son hulda da mutum mai jama’a. Alhaji Bishir babban dan kasuwa ne yana da mutane fiye da zaton ka, lokacin da ya bukaci hulda dani sai da na bincika, ka taimaka ka samo min soyayyar ‘yarsa mu zama surukai. Yana tare da mutanan da in suka goya min baya zai yi wuya ban dare kujerar shugabancin kasar nan ba. Abbas ya ce, na yi mata magana ta ce tana da wanda take so, amma ina zaton jan aji ne, don Allah ka yi wa mahaifin ta Magana, babbar na ke so, Alhaji Akilu ya ce, kar ka damu yanzu zan kira shi.
Sun gaisa da Alhaji Bishir ya ce, ka samu hutu kenan mu kawo ziyaran, Alhaji Akilu ya ce, danka ne nan ya fiti ne ni wai tun da mun ce ya yi aure, shi ‘yar uwarsa yake so Mimi, tunda muka kawo ziyarar nan ya kasa sukuni. Alhaji Bishir cikin matukar murna ya ce, masha Allah, ka fada masa kar ya damu, Mimi ta zama ta shi don na ba shi. Nan Alhaji Akilu ya hau godiya, cikin murna, Abbas cikin murna ya rungume mahaifinsa. Alhaji Bishir ya kosa ya iso gida don ya yi albishir ga Mimi da Momy Nafisa, lallai burin shi zai cika.
Alhaji Lawal ya kalli Direban shi, yarinyar nan ba za ta ba mu hadin kai ba, don haka ka yi min sallama da mamanta. Haka kuwa ya rangada sallama, kaninta ya leko ya ce, yawwa ka ce Alhaji yana sallama da mamanku, yaron ya ce, innarmu? Ya ce, eh, ka ce in ji Alhaji Lawal. Ba da jimawa ba, innar su Zainabu ta fito, tamkar marokiya, haka take ta yi wa Alhajin barka da zuwa ka iso lafiya, sannu-sannu. Ya fito ta durkusa, bari a yi shimfida a zaure, ta mike ta koma ciki da gudu. gani Alhaji wanna ‘yar raka yarima ce asha kida, ‘suka yi dariya tamkar ba direba da ubangida ba. To direba za a kira shi ko kawali, tunda shine me kawo ma Alhaii labarin mata. Suna zaune a kan tabarma zaure, Alhaji ya ce, Inna na zone muyi zancen aure, Zainabu ta ki ba ni hadin kai na turo manya na, sai fada min take yi tanada wanda za ta aura.
Inna ta cafke zancan da cewa, karya ne ba ta da shi, ka turo kawai, ya ce, to na gode. Ya aje daurin ‘yan dari biyar-biyar, Inna ga wannan kwa ci goro, kuma zan turo manya na gobe, ba na son bikin ya wuce sati uku. Ta ce, ai kuma lokacin ba mu shirya ba, Alhaji ka san sai mun dan nemi na gado. Ya ce, ina da komai Inna, mata nace ina so, kuma ita za a ba ni ba tarkacan kaya ba. Ta ce, to shikenan, in goben ka ke so za a daura, bare nan da sati uku.
Tirkashi!!!
Hmmmm