CANJIN RAYUWA CHAPTER 12 BY HALIMA A K/MASHI
CANJIN RAYUWA CHAPTER 12 BY HALIMA A K/MASHI Tunda ya soma karatun danna wayarta ma take yi, ya gama ya dube ta, yanzun sai ki karanto fatihar in ji ke ma daga nan sai in dora miki daga bakara aya biyar-biyar za mu dinga yi duk kwana biyu sau biyu a sati. Sauran kwanakin kuma sai mu saka fikihu, hadisi da tauhidi. Ta ce, me ka ke fada ne? ni fa duk ban ji ka ba, ya ce, karatun na ce ki yi, ta harare ‘shi, yanzu fa ka ce, sai ka fara sannan zanyi, ya daga murya, kina nufin ba ki ji karatun da na yi ba? Ta ce, shine gaskiya, da ka yi ai da na ji, ya rufe kur’anin cikin takaici, ya zuba ma kafet din kasan idanu, shi kam ya gaji. Ta katse mashi tunani, a banza za’a ba ka dubu dari? Ya ce, in na fasa koyarwar fa? Ta ce, ka rasa, zanfi son ma ka ce ka fasa, don ni dole idanu na suke kallon fuskar ka, kuma ba na son in kore ka saboda Hajiya za ta yi min fada, amma in ka tafi da kan ka shikenan.Ya ce, yanzun zan kira Hajiyar in fada mata komai, gabanta ya fadi, ta yi shiru cikin fargaba. Ya ce, …