CANJIN RAYUWA CHAPTER 12 BY HALIMA A K/MASHI
Tunda ya soma karatun danna wayarta ma take yi, ya gama ya dube ta, yanzun sai ki karanto fatihar in ji ke ma daga nan sai in dora miki daga bakara aya biyar-biyar za mu dinga yi duk kwana biyu sau biyu a sati.
Sauran kwanakin kuma sai mu saka fikihu, hadisi da tauhidi. Ta ce, me ka ke fada ne? ni fa duk ban ji ka ba, ya ce, karatun na ce ki yi, ta harare
‘shi, yanzu fa ka ce, sai ka fara sannan zanyi, ya daga murya, kina nufin ba ki ji karatun da na yi ba? Ta ce, shine gaskiya, da ka yi ai da na ji, ya rufe kur’anin cikin takaici, ya zuba ma kafet din kasan idanu, shi kam ya gaji. Ta katse mashi tunani, a banza za’a ba ka dubu dari? Ya ce, in na fasa koyarwar fa? Ta ce, ka rasa, zanfi son ma ka ce ka fasa, don ni dole idanu na suke kallon fuskar ka, kuma ba na son in kore ka saboda Hajiya za ta yi min fada, amma in ka tafi da kan ka shikenan.Ya ce, yanzun zan kira Hajiyar in fada mata komai, gabanta ya fadi, ta yi shiru cikin fargaba. Ya ce, zan fada mata komai don kar ta zarge ni, ta ce, bari in riga ka fada mata, ga mamakinsa sai ya ga ta saka wayarta a handsfree ta kuma kira layin Hajiyar, ba ta jima tana ringing ba ta daga. Sun gaisa sannan ta ce, ya ya kuwa karatun ki na yi? Ta ce, eh! Hajiya yanzun haka ina kan yin karatun, na kira ne na yi miki godiya, sannan kiyimA malamin godiya in kun yi waya. don ina fahimtar karatunsa, ta ce, ai Ismail yana da himma Allah ya taimaka, ta ce, Amin, suka yi sallama.
Ta kalle shi, ka gane nufi na? na san yanzun dai za ka ji nauyin ce mata ba na karatu, tunda na ce ina fahimtarka, ka ga kenan sai ka nemi dalilin ka na kin koyar da ni da za ka yi, ya yi banza da ita ya ci gaba da kallon agogo minti goma da suka rage sun yi mishi nisa, sai da ya ga saura minti biyu, ya kalle ta, tana ta chatin, ya ce, ki yi amfani da lokacin ki tun kina da Kuruciyarki, ki nemi sanin addininki sannan ki bauta ma Ubangijinki kafin lokaci ya Kure miki. Ta ce, kai har ka samu sake da yawa irin haka ne? ganin ka ka kai ka dinga fada min magana son ranka ne? ya yi murmushi, in kin gaji da kallon kyakyawar fuskata zan tafi, don lokaci ya cika, kin san lokaci baya jira.
Ta mike tsaye, shima ya mike tare da kwasar littafansa, ta ce, har wani kyau ne da kai? Dube ka, yace, sosai kuwa, don na san na fi ki nesa ba kusa ba. Ta ce, karya ka ke yi, na sha jin mutane suna gulmar kyau na, ban da wadanda suke fada a gabana. Ya yi ‘yar dariya, da son ya cusa mata takaici, sanna ya ce, ina zaton suna tsoron ki ne, ko jin nauyin ki, ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau su fada maki tsakani da Allah. Ya kalli agogo, kash har na kara minti biyu, ya fice. kafin ta kai ga cewa wani abu, ranshi kar, ya san cewa ya guma mata, don ya san mata ko ba su da kyau, sun tsani a fada, shi kuma ya yi ne kawai don shakar da ita, bai yi nisa ba, ya ji ta saka kuka, sauri ya Kara ya fice daga gefen na su.
Mommy Nafisa ta fito da sauri jin kukan Mimi, abinda ta dade ba ta ji ba, ta ce, mene ne? Mimi ta ce, Mommy kalle ni sosai da gaske ba ni da kyau? Mommy ta ce, inji wane makahon? Mimi cikin shagwaba ta ce, wancan talakan malamin mana, Mommy Nafisa ta ce, barshi kawai karya yake, Mimi ta ce, bari Dad ya dawo dole ne malamin nan ya yi kwanan Cell, Mommy ta ce, ki share shi ne kawai, Hajiya Sauda ba za ta ji dadi ba, in har ki ka kai shi gurin ‘yan sanda:
Mimi ta yi samanta cikin matsananciyar damuwa, kai tsaye dakin ta ta wuce, sai gaban madubin ta na jikin sif dinta, don shine zai nuna mata siffarta tun daga sama har kasa, ta dinga juya kowane gefen ta tana kallo, zantukan malamin suna yi mata yawo a cikin kai. Ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau, su fada maki tsakani da Allah, wadannan kalaman sun sa ta a cikin rudani, ta dauki wayarta, ta kira layin Na’ima, bayan ta daga ta ce, ki je ki ce ma Hamisu direba zamu fita, Na’ima ta ce to Sis, ni ma zan bi ki, cikin tsawa ta ce, a’a ki je aike na kawai.
Gidan su Amina Dakingari ta nufa, Mina ta yi mamakin ganin Mimi ba ko sanarwa, bayan sun shiga daki, Mimi cikin kuka ta ce, Mina don Allah ki fada mun gaskiya tsakani da Allah. Mina ta dafe Kirji, me ya faru Mimi? Mimi ta ce, ni dai ki fada min, Ina da kyau?, Mina ta ce, ko makaho ya shafa, Mimi ya san kina da kyau sosai ma. Wai duk me ya kawo wannan tambayar?
Mimi ta ce, hum! wannan malamin ne talakan banza nan dai, Mimi ta sanar da ita yanda suka yi. Mina ta yi tsaki, na zata ma wani na kirki ne ya ce miki haka, ya fada ne kawai don ya ba ki haushi. Ke to me zai dame ki tunda ba Khalil ba ne ya ce ba ki da kyau? In duniya za a taru a ce ba ki da kyau, na tabbata Khalil ba zai ce ba. Mimi ta sauke ajiyar zuciya, sännan ta isa gaban madubin Mina tana Kallon kanta, ta ce, Mina cewa fa ya yi kawai ana dai jin tsoro na ne ake cewa ina da kyau, Mina ta zo ta dafa ta, kar ki ruda kanki Mimi, dube ki fa doguwa fara sal ga gashi harbaya, idanuwanki masu haske. Mimi hatta
hakoranki abin birgewa ne, so kar ki damü. kanki. Mimi ta dauko wayarta ta somakiran” layin Khalil, ta zauna daidai lokacin da ya daga ta ce, zan tambayeka wani abu, ka fada min gaskiya. Ya ce, ina jin ki, ta ce, kana so na? Ya tausasa murya, haba Khadija wannan tambayar ai kin dade da sanin amsarta, amma in ki na son in sake maimaita mikine, sai in ce ina sonki, ina sonki sosai fiye da yanda ni ke son kaina, ta ce, saboda me ka ke so na Khalil? Ya ce, abubuwa da dama Khadija, amma daga ciki akwai halinki da kuma kyawunki, Mimi ta ce, hali na kuma?
Khalil ko dai gaskiya ne mutane ba sa son fada min gaskiya? Ban taba jin wanda ya yabi hali na ba, daga Daddy na sai Mommy Nafisa, sai kai yanzun, ta kashe wayar, hawaye na zuba mata.
Mina ta ce, Mimi kin cika son sa ma kanki damuwa, wani banzan talaka ya rikitaki duk ki damu kanki, ki dawo hankalinki mana? Wayarta ta soma ringing ta duba ta ga Khalil ne ta jefar da wayar. Mina ta ce, shi kuma me ya shafe shi? Mimi ta ce, tsakanin da Allah Mina kin taba jin wanda ya ce, ina da hali mai kyau? Hatta mahaifiyata kullum fada take yi min in gyara hali na. Ke ma in na yi wani abu, kina ce min irin halin nan ba shi da kyau, amma yanzu Khalil yana fada min wai yana so na don hali na.
Maganar malamin nan ta zama gaskiya, kenan masu cewa ina da kyau ba su fada min gaskiya.
Mina ta ce, oh my God, don Allah ki daga wayar Khalil, in kowa zai ce halinki ba kyau, Khalil ba zai gani ba, don so yana hana ganin laifi, ka da ki dama ma kanki lissafi, shawara ta ki kori malamin nan ki huta mana. Mimi ta ce, kina nufin Khalil iyaka gaskiyar shi ya fada min? Mina ta ce, kina dai karatun English Novel na soyayya, da ma ba ki fahimtar komai? Mimi ta yi shiru tana nazari, can ta yi ajiyar zuciya, sannan ta dauko wayarta daidai lokacin Khalil ya sake kira, wanda ba ta san ko kira nawa kenan ba.
Ta daga muryarta tana rawa ya ce,
Khadija fada min gaskiya na yi miki wani laifi ne? ta ce, a’a na ji ka ce kana so na don hali na, ni kuma kullum kowa ce min yake ba ni da hali, fada min gaskiya. Ya ce, ni halayen ki sun mini, ko da ba su yi ma kowa a duniya ba, zan iya yin komai a kan sonki, ki yi min izini in zo Abuja mu yi magana a cikin tsanaki. Ta ce, na fada maka Dad dina ba zai so ya ga ina hira da saurayi bai san lokacin da muka hadu ba, ka bari na ba shi labarin ka, sai ka zo ku gana. Ya ce, ko wani guri daban sai mu je, in na zo sai mu yi maganar kin ji?
Don Allah da ma ina son ganin ki, ta yi shiru, can ta ce shikenan, gobe ka zo, amma zan turo maka address din gidan su Mina sai mu hadu a can, ya ce, shikenan sai kin turo, ki kwantar da hankalin ki kin ji? Ta ce, babu komai
Mina ta riko mata hannu, kar ki damu da sauraran shi, sannan ki kore shi kawai.
Mimi ta ce, ba ni da damar yin haka, don dazun na Kara daure kaina na fada ma Hajiya dewa ina jin dadin karatunsa ina fahimta, in na ce a kore shi bisa ga wane dalili? Mina ta ce, kin hadu da alakakai, ta ta shi, bari in je gida, duk da haka. zan nemi shawarar
Mommy Nafisa a kan shi.
Lokacin da ta iso gidan Mommy
Nafisa, Mommy Nafisa suna dakin Na’ima suna tattaunawa a kan matsalarsu, wato Mimi, Mommy ta ce, Na’ima ai. na ji dadin zuwan malamin nan, saboda na jima ina son in ga ran yarinyar a bace, sai dai ni ba ni da damar in bata mata. Na’ima ta ce, don Allah Mommy kar ki bari ta kore shi, ai ni ya birgeni da yake yi mata abinda take yi wa mutane. Kiran da take yi wa Mommymomy shine ya sa ta yin sauri ta fito daga dakin, ta ce, ya ya ne Mimi, kin dawo? Ta ce, eh, ni Mommy kina ganin ba zaifi kyau in kori malamin nan ba? Mommy ta ce, a ‘a ba na son Hajiya Sauda ta zarge ni, don haka ki yi hakuri ‘ya ta, bari in sa Folina ta kira shi, in gargadeshi, don kada ya ci gaba da fada miki Magana, ta ce, shikenan, amma ina son a yi ma shi fadan a gabana don ya san ni ba sa’ar shibace.
Haka kuwa Folina ‘yar aiki ta kira
Ismail, a gaban Mimi ta yi mi shi gargadin kar ya Kara cewa ba ta da kyau. Ya ce; Insha Allahu, ko ba komai dai Ismail ya ji dadin bata mata ran da ya yi.
A Katsina kuma kwana biyu da tafiyar
Ismail, Zainabu ta soma yin tallar ta, kuma a ranar ne ta had da wani Alhaji, babban mutum ne a shekaru haka kuma a aljihu.
Direban shi ya tura ya tsaida ita, ya tambayi sunanta da kuma gidansu, ba ta boye ba don mahaifiyarta ta shirya mata cewa, ta saurari duk wanda ya zo, tunda Ismail ba ya gari, a nan ma za su samu kudin siyan mata kayan kicin. Zainabu tana son Ismail sosai, don haka ta yarda tana son ta ji ana yin zancan auran su. Alhajin ya zo da dare kuma ya tura uwar da kanta ta dinga gyarawa Zainabu kwalliya har zaure ta rako ta, tamkar ta bi ta wajen a yi hirar da ita, tunda ‘yar ta ba ta labari, ta ji a jikinta cewa irin wanda take so ne ya zo. Alhajin ya ji dadin fitowar Zainabu, don yarinyar tayi masa, ya ce mata auranta zai yi, shi sunansa Alhaji Lawal, ta ce, ta yarda, da zai tafi nan ya cika su da kudi masu dama, wanda suka sa mahaifiyar rawa, ta kuma yarda cewa ‘yarta ta samu miji.
Washegari da safe Ismail ya kira
Mahmud ya roke shi don Allah ya kaima Zainabu wayarsa, don yana son su gaisa ya ji muryarta. Mahmud ya ce, shi fa ba ya son yaje ne a raina mishi wayo. Ismail ya yi ta rokon shi, da kyar ya yarda, ya ce, zai je da yamma. Suna gama waya ya mike ya debi takardu don zuwa cikin gida koyar da ‘yar mulki, sunan da ya fi kiran ta kenan in zaiyi maganar ta da Hamisu direba. Ta fi minti talatin sannan ta fito, tunda ya ga hakan ya san yau akwai matsalar da ta fi ta kullum.
Alkur’ani da ma yake karantawa tun kafin ta zo, ta kalli inda yake, sannan ta ja tsaki ta zauna, ya kai aya sannan ya dube ta barka da shigowa fatan ki na lafiya? Ta zaro ido, ba ruwanka da lafiya ta, ko kai likita ne? bai ce komai ba, amma idanunsa suna kallon ta, tá ja tsaki tare da fadin aikin banza shishigi kawai. Ya ce, ki na jina ko? Yau ba neman fada ni ke yi ba, don Allah ki tsaya mu yi karatun nan shine ya kawo ni garin nan, ni na roke ki kin ji? Ta ce ba zan yi ba, ya ce, to zan kira mahaifiyarki in fada mata gaskiyar komai, sannan ni kuma in tafi abina, na soma gajiya da zama haka. Ta ce, zan so haka, na fi kowa son ka tafi don na tsani kallon fuskar ka, amma bai kamata in barka ka tafi haka nan ba, ya kamata ni ma in yi maka abinda ba za ka mance ba. Kamar yanda kaine mutum na farko daka soma cusa min bakin cikin da ba zan manta da shi ba. Ba a taba bata min rai ba tunda ni ke sai kai, ya yi shiru, don shi ya gaji da wannan wasan
-kwaikwayon, Ya ce, to in na ba ki hakuri fa?
Ta ce, karike kar ka bani don ba zan karba ba, ka barni in rama. Ya ce, ba laifi, daga nan ya yi banza da ita, sai kuma ya mike tare da kwasar littafansa, ta ce, na sallame ka ne?
Lokacin ka bai cika ba, ya ce, ba amfanin zaman, tunda ba karatun za’ayi ba ya ta fi abinsa.
Yana zuwa dakin shi ya kira Hajiya
Sauda da nufin ya fada mata komai, suna gaisuwa sai ta soma yi masa godiya har ya kasa fada mata, suka yi sallama, ya kwanta yana tunanin abin yi
Haka suka yi ta yi har ranar lahadi, wacce ta kasance ranar da Alhaii Bashir zai amshi bakuncin sabon abokinsa, ministan man fetur. Karfe takwas zai zo, amma tun shida an hana kowa sakat a gidan. Girki an yi shi ya fi kala goma, ban da nau’in kayan sha na kanti, ga busassu tun daga kan goro dabino, kayan marmari ma gasu nan kala-Kala. Takwas zai iso gidan, don haka zuwa lokacin kowa na ta shiri. Ya kira Alhaji Bashir ya ce, Alhajin Allah zan zo fa da nawa iyalan ne, Alhaji Bashir ya ce, na yi murna sosai, ina yi maku maraba.Ya fito daga dakinsa yana kiran
Nafisa, ta fito cikin sauri tana cewa, sun iso ne? Ya ce, a’a da iyalansa zai zo, ta ce, Allah ya kawo su lafiya. Cikin azama ta shiga dakin Na’ima ta same ta tana yin kwalliya, sai ta ce, yawwa Na’ima ki yi gayu sosai, da iyalansa zai zo, inda namiji ki yi kokari ki ja ra’ayin shi. In ba namiji ko ministan din ne ki ja ra’ayin shi, ta haka ne za ki samu shiga gurin dadinku. Zai so ki fiye da Mimi, Na’ima ta ce, ya fada ne? Mommy Nafisa ta ce, a’a ba ya fada bane, kin san yana son zama kut-da-Kut shi da minista, in surukanta ta shiga tsakanin su yaya ki ke gani? Na’ima cikin murna ta ce, zan yi kokari, amma in shi kanshi ne mommy ai ya yi tsufa. Allah ya sa yana da yara maza Mommy, Nafisa ta ce, ina ruwanki da tsufansa? daura shi za ki yi a wuya? Kudin muke bukata, ballantana a ce kin haihu, randa duk ba shi mu sha gado, ga gata gurin dadinku, Na’ima ta ce, Insha Allah za ta yi hakan.
Mimi tana daki tana shirin ta, ita ba gwanar shafa abubuwa rakwacan ba ce, amma man ta da hodar ta zuwa turare tsadarsu ta isa. Jambaki kurum ta shafa pink ta saka riga da wando damammu bakake a sama ta dora pink din shimin kayan ta zo mata gwiwa, ta tattare gashin kanta zuwa gefe ta kama shi da pink din ribom Kasa-kasa, ta fesa turaranta na yau da kullum, don ta fi son turarukan Arabia, takalmin ta flat baki mai ratsin pink.
Ta dauki wayarta daidai lokacin da wayar ta soma ringin, ta daga Dad ya ce, uwata sauko sun iso, ta ce to Daddy. Lokacin da ta sauko falon kasan babu kowa, sun tafi tarbo bakin, ba ta bi su ba, sai ta samu kujera ta kame. Suka shigo da sallama, ta tashi ta nufe su, matar ministan ce suka shigo tare da Mommy Nafisa, sannan su Alhaji Bishir din, sai wani saurayi sannan Na’ima da wata budurwa sa’ar Mimi, sannan Kananan suka shigo tare da su Ahmad. Kan kujerun falon Alhaji suka zauna, sun gaisa inda suka gabatar da junansu, ko in ce Alhaji Akilu ya gabatar da iyalansa. Ya nuna uwar, ga madam dina Hajiya Bilkisu, sai yaro na na farko Abbas ga shi nan ina ta fama ya yi aure yaki.
Ya gama karatunsa, yanzun yana aiki da Central Bank ne, Alhaji Bishir ya ce, ya kamata kam a yi aure. Abba zai shekara talatin ko? Alhaji Akilu ya ce, talatin din ce kuwa, Alhaji Bishir ya ce, sa’an Abba kenan dana na fari. Shi kam yayi aure har sun yi min takwara, Alhaji Akilu ya ce, ka gani ko abinda ni ke buri kenan in ga ‘ya’yan. Alhaji Bashir ya ce, ka kokarta ka ji dana? Abba cikin murumushi ya ce, Insha Allahu.
• Ya nuna ta mace, waccen kuma Aisha ce tana shekarar ta ta farko a jami’a ta kasar Ghana, sai Samira da Azima da Jamil duk
‘yan primary ne da J.S.S. Alhaji Bishir ya ce, masha Allah, Allah ya yi masu albarka. Kai
Hmmmm