CANJIN RAYUWA CHAPTER 10 BY HALIMA A K/MASH

CANJIN RAYUWA CHAPTER 10 BY HALIMA A K/MASHI tamkar ya hadiye ‘yar. Ya yi walima gagaruma, inda aka rinka sanarwa a Jarida, gidan Rediyo da Talabijin, sabon abu, Saudatu ta ga sabon abu kamar na fari. Wani abin da ya fi ba ta al’ajabi, tuni ya amshi renon jaririyar tamkar ba zai fita ba. Ya na burge ta har ta soma jin haushi, domin ba ya kula da ita yanzu kamar da koyaushe uwarsa Mimi, wai shi sam ba ya son jin kukanta, duk lokacin da ya ji kukanta, ya dinga fada kenan, ita kuma ga shegen kuka. Sannu-sannu Mimi ta soma girma, sai ta shiga yi ma kowa Kuya sai Dady, lokacin zama ta ke Amma in Dady yana gida ko Hajiya Sauda ba ta amincewa ta dauke ta. Hakanan zai iya barin kowa da komai ya lallasheta, in har tana kukan rigima. Haka ta taso cikin mugun gata da rigima ga shagwada, abin da ta ce, shi za’ayi, su Abba har suka soma jin haushinta, yayyanta kenan. Domin kirikiri za ta yi laifin da ya kamata a zane ta, amma sai a ce ko kallon banza ba za’ayi mata ba. Sannan. da aka tashi sanya ta…