CANJIN RAYUWA CHAPTER 10 BY HALIMA A K/MASHI
tamkar ya hadiye ‘yar. Ya yi walima gagaruma, inda aka rinka sanarwa a Jarida, gidan Rediyo da Talabijin, sabon abu, Saudatu ta ga sabon abu kamar na fari. Wani abin da ya fi ba ta al’ajabi, tuni ya amshi renon jaririyar tamkar ba zai fita ba. Ya na burge ta har ta soma jin haushi, domin ba ya kula da ita yanzu kamar da koyaushe uwarsa Mimi, wai shi sam ba ya son jin kukanta, duk lokacin da ya ji kukanta, ya dinga fada kenan, ita kuma ga shegen kuka. Sannu-sannu Mimi ta soma girma, sai ta shiga yi ma kowa Kuya sai Dady, lokacin zama ta ke Amma in Dady yana gida ko Hajiya Sauda ba ta amincewa ta dauke ta. Hakanan zai iya barin kowa da komai ya lallasheta, in har tana kukan rigima. Haka ta taso cikin mugun gata da rigima ga shagwada, abin da ta ce, shi za’ayi, su Abba har suka soma jin haushinta, yayyanta kenan. Domin kirikiri za ta yi laifin da ya kamata a zane ta, amma sai a ce ko kallon banza ba za’ayi mata ba. Sannan. da aka tashi sanya ta a makaranta, sai aka sanya ta a wadda ta fi ta kowane yaro tsada a gidan, makarantar da duk wani mai ji da kansa a Katsina nan yake kai ‘ya’yansa. Sai wani babban abin takaici a gurin Hajiya Sauda yadda kirkiri Mimi ta ki Islamiyya.
Da ta dage sai an sa Mimi, hakan ya hakura aka sa ta, in ta je ba ta komai sai kuka da birgima. Rannan wani Malami ya dan dake ta, saboda ta ki yin shiru kuma ta ki. zama ta kage a tsaye, ai ko ya gane kurensa, domin ‘Yan sanda Alhaji Bashir ya kirawo wa Malamin. Lokacin da Mimi ta sanar da shi cewa Malaminsu ya duke ta,
‘yan sanda suka rufe shi, ya ce a rama wa
‘yarsa dukan da ya yi mata, domin shine mutum na farko da ya soma dukan ta.
Hajiya Sauda ta yi bakin ciki matuka, hakanan ita ce ta je ta yi belin Malamin tare da ba shi hakuri.
Tun daga lokacin ta kawo idanu ta zuba wa mijinta da ‘yarsa, ya ce ta daina zuwa Islamiyya, wai Sauda ta dinga koya mata a gida, ai ita tana da ilimi. Sauda tace, ai ba zai yiwu ba, a ce ba za ta yi Islamiyya ba, yaushe za ta san kanta bare addinita. Sai ya ce, ai ita mace ce, in ta iya na Sallah tunda ba wa’azi za ta yi ba, ba limanci za ta yi ba ya ishe ta. Sauda ta ce, ai kuwa a dai rayu cikin jahilci.
Tun daga lokacin Mimi ba ta Kara
Islamiyya ba, Hajiya Sauda sai ta dauki matakin tsare ta da bulala tana koya mata, in ta kiya sai ta zane ta. A kan hakan suka yi rikici, wai ba ta son Mimi, shi ko sai ya dauki matakin Tafiya da ita duk inda za shi.
Ta zama tamkar jaka, shi ke kai ta boko ya kuma dauko ta, ko da yana ofishinsa ne, lokacin tashi ya yi zai bar komai ya je ya dauko ta. Ta na gurinsa, sai zai bar ofis sannan su koma gida tare. In ko za shi wata kasa ko wata Jihar, to fa zai kashe mata makaranta, tana gefen damansa.
Hajiya Binta tana matukar bakin cikin abinda Mimi ke yi, tamkar ta kashe yarinyar ta ke ji. Cikin haka Sauda ta haifi
‘yan biyu duk mata, Hasana da Husaina, ta yi murna sosai, tana zaton tunda ga wasu yara matan ‘yan biyu ma abin sha’awa, to lallai mijin na ta zai rage son Mimi, za su ture mata gwamnati ko ta samu tayi mata tarbiyyar da ta dace, amma me? Sai yana cewa, Mimi fa dabam take, da duk wasu ya’ya da ya haifa baya da kuma wanda zai haifa nan gaba.
Haka Hajiya Sauda ta kawo ido ta zuba masu, wai sai da ta kai Mimi ba ta : maimaita kayan sawa, sai in ta yi ra’ayi, ci-banza-ci-wofi shine abincinta. Amma ba wai abincin kirki ba, wanda aka dafa ba, haka Hajiya Sauda tayi ta haihuwarta a kai-a-kai, ta yi Abdullahi sai Amen, sannan Umar da Sadik, a jere ta yi ta haihuwarsu, amma har lokacin Mimi ita ce ta gaban goshi. Lokacin da Hajiya Sauda ta samu cikin Husna, lokacin ne ita ma Hajiya Binta ta samu na ta rabon. Sauda ta yi mata
• murna sosai ita ma ta yi farin ciki matuka.
Kasan cewar wannan ne farko da za ta ga kwanta a duniya, lokacin da ta haihu an samu mace aka sa mata Zainab, kishin Mimi ya sa suke yawan rigima da mijin, ita wai dole sai ya ji da ‘yarta kamar yadda ya keji da Mimi.
A wannan lokacin ne ya gina wani katafaren gidan gona a Malumfashi, kuma ya gina wani gida a cikin garin Malumfashi, don haka sai Sauda ta ba shi shawarar ya maida daya daga cikinsu can tsakanin ita da Hajiya Binta, don ita kan ba ta son rigima, ta gaji da takalarta fada da Binta ke yi kan Mimi. Ya yarda kuma ya dauki hajia Binta ya maida ta Malumfashi, bayan Husna, sai cikin Hasina shima ba ta yaye
Husna ba ta same shi.
Wani sabon al’amari, wata Juma’a Sauda tana daki kwance guraren shadaya na rana, sai Jummai mai yi mata aiki ta yi sallama ta ce, Hajiya kin yi bakuwa. Ta fito ta ga mace wayayya kuma gogaggiyar ‘yar boko, daga ganinta kuma ‘yar masu halice, ko kuma mjinta mai hali ne. Sauda ta ba ta mazauni, sannan ta sa aka kawo masu abin sha.
Suka gaisa, Sauda ta ce, sai dai bangane ki ba fa? Bakuwar ta ce, suna na Nafisa kuma daga Abuja na zo nan, na san cewa ba ki sanni ba. Amma ni sai ta dan yi shiru, Sauda dai ta ji gabanta yana ta faduwa, cikin zakuwa, ta ce, ina jinki?
Bakuwar ta ce, za ki yi mamaki idan na ce miki ni matar mijinki ce? gaban Sauda ya fadi cikin daga murya ta ce, me ki ka ce?
Bakuwa ta ce, ni matar Alhaji Bashir ce maigidan nan.
Jikin Sauda ya soma bari ta ce, Karya kike yi, mijina ba zai yi aure ba tare da na sani ba wallahi. Nafisa ta daga mata hannu tare da cewa kar ki rantse, domin mun yi aure da shi shekaru bakwai kenan. Ta nuna babba daga cikin yaranta ita ce Na’ima kuma ita ce ‘yarmu ta fari. Sai wannan sunan ta Suhaila, sai kuma wannan Karamin Ahmad. Na’ima sa’ar Abdullahi ce danki, kuma inda Mimi ‘yarki tana nan za ta shaida miki, domin ita kadai kawai ta sanni, ta san yara na a duk lokacin da Alhaji ya je
Abuja Mimi tana zama a hannu na ne.
Na dade ina son ya kawo ni in ganku iyalinshi, ku sanni amma ya ki sai ya ce, zai kawo ni, sannan wai ba ya son ki ta da hankalinki, ni kuma na ga cewa akwai mutuwa. Shi yasa tunda ya sanar da ni zai tafi China ni kuma na dauri aniyar zuwa mu gana da ku saboda halin rayuwa. Hajiya Sauda jinta kawai take yi tamkar a cikin mafarki. Sai da ta lallashi zuciyarta sannan ta ce, shikenan ba komi. Ku jira shi a nan in ya dawo sai ku tafi, Nafisa ta ce, ni ma haka ne kudurina. Sannan ina son a nuna muga dangi, Sauda ta ce, babu damuwa.
Kwanan su biyu, Allah ya yi wa mahaifin Alhaji Bashir rasuwa a Masari, da ma ba shi da lafiya har Misira an fita da shi, amma da yake jikin tsufa sai a hankali. Nan suka tattara suka nufi Masari, shima dole ya bar komai ya nufo gida, shi da ‘yar lelensa Mimi, bayan an natsu Hajiya Sauda ta’ gabatar da Nafisa ga dangin mijinta Nan suka yi ta surutu bai kyauta ba, bai
” kyauta ba, wasu kuma su ce giyar kudice.
Ita kam Sauda cewa ta yi, ni haushi na daya, mene ne na kin fada mani, wa zai hana shi aure? Kuma da ya Ki kawo ta, inda ta Allah ta kasance a kanshi ta zo da yara ta ce ita matarsa ce za a yarda cikin sauki? Ita kuwa Hajiya Binta zagewa ta yi tana ta tsula rashin mutumci duk da cewa gidan mutuwa ne, karara ta nuna kishinta.
Shima duk da yana cikin ciwon mutuwa, ya girgiza da samun Nafisa a gidan, sam bai so ba. Dole ya hakura ya jure masifar da Hajiya Binta ta dinga yi masa son ranta, ta fada ma shi maganganu.
Ita kuma Sauda ba ta ce komai ba, sai rashin yin maganarta ya fi daga mashi hankali fiye da masifar da Hajiya Binta take yi. Sai da aka yi bakwai sannan kowa ya watse suka koma gidajensu.
Daga nan ya sa aka maida Nafisa
Abuja, sannan shi ma ya nufi Katsina.
Har cikin daki ya samu Sauda tana shirya yaranta za msu tafi Islamiyya, sai da suka tafi sannan ya zauna kusa da ita ya ce, Sauda na san na yi miki laifi, donAllah ina son ki yafe min, dama kullum cikin tunanin zuwan wannan ranar na ke yi. Ta kalle shi laifin me? Ya kasa ba ta amsa, ta tabe baki ba ka yi min laifin komai ba. Ya ce, ai ni na san na yi laifi, ki fahimce ni, sam banyi da nufi ba.
Tunanin halin da za ki shiga ne ya hana ni na fada miki, saboda na ga yadda muka yi ta samun matsala a lokacin auren Hajiya Binta, ni kuma ba na son bacin ranki sam. Ta ce, umm! ni yanzu lamuranka ba bu ruwa na da su, ya ce, don me ki ka ce haka?
Ta ce, na za ta ni da kai duk daya ne, ko mutuwa zanyi don kishi ai ka fada min in ya so in mutu. Kuma bayan ka yi ma, ai sai ka fada min. Ya ce, to na yi kuskure, ai lokacin auren ne ya zo babu shiri don Allah bari in fada miki yadda abin ya faru.
Lokacin ina son sayan wasu filaye a cikin garin Abuja, saboda ina son fara harkar gine-gine ina saidawa, to mahaifinta shine shugaba a ma’aikatar filaye, da safiyo, ni da lauya na muka je gidansa don ganawa ta musamman kamar yadda ya bukata, shine na ganta, amma har ga Allah ba sonta na ke yi ba. Don in samu saukin wannan harkan shi ya sa na nuna ina sonta, kuma Alhamdulillahi sai ya bani ita.Su Alhaji Isa Mani ne suka amsar
min aurenta, ban zaci zamu dade a cikin auren ba, domin na yi ne na wani lokaci,
amma sai mutuncin mahaifinta, da yanda
ya sakar min nake samun alherin filaye, shi ya sa na hakura. Abinda ya sa ta kara shiga raina shine yadda take son Mimi sosai har ma wani lokaci ina cewa a ce ita ce mahaifiyar Mimi, domin ba ta takura mata.
Hajiya Sauda ta ce, wato ita Mimi har da ita
a munafunta ta, ya yi mata kyau.
Ya ce, kar ki ga laifin ta, ta ce, kaima
ba cewa na yi ka yi laifi ba cewa, na yi don me ka boye min? Ai aure ba laifi ba ne, na isa in hana ka yi? Ya ce, ba zan Kara ba, tace, nan gaba in za ka cike ta hudu na roke ka, ka sanar da mu. Ya ce, ai na gama Sauda.
: Ta ce, uhum, haka dai ka ce, ni yanzu na daina yarda da kai. Ya shiga lallashinta da
fada mata maganganu, tsakanin mata da
miji sai Allah, nan dai suka sasanta tamkar ba su taba samun matsala ba, har ranta ta bar abin a kaddara. Tun da ya samu Sauda da sauran danginsa suka san da Nafisa, sai ya ga ba shi da matsala, tuni yake son ajiye Mimi a gurin Nafisa amma babu hali saboda ina zai ce ya kaita? Amma yanzun ga dama ta samu, tuni ya tattara ta ya maida ta, Mimin ma ta yi murna da hakan, don ta san Momy Nafisa na sonta. Lokacin da za su tafi kalma daya ta fada mishi,
Alhaji tunda kana ganin zaman
Mimi a can ya na nan, to babu matsala, amma ina son ka san cewa, duk iyayen da ba su sa dansu kuka ba, to wata rana sai dan ya sa su kuka ya ce, wannan kuma irin na ki tunanin kenan, ni dai zan maida ‘ya ta inda za ta samu ‘yanci ta kuma hutu Lallai
Mimi ‘yargatace, domin a
dankararren gidan da ya gina a Abuja Maitama, an tsara gidan sama ne hawa daya, amma saman na Mimi ne kowa yana kasa, dakin baccin ta komai pink don shine kalar da ta fi so. Dayan dakin kayan karatun ta ne a ciki, shi kuma dayan an gyara shi an rufe.
Lokacin shekaranta goma kacal, Momy Nafisa tana yin iya yinta don ganin ta danne zuciyarta ta kauda kanta ga abinda alhaji ke yi ma Mimi, ba don komai ba, sai don ta samu shiga da kuma abin duniya da yake sakar mata. Amma a badini ba ta son Mimi, ba ta kamar tana sonta, kullum burinta yanda za ta shiga tsakanin su, don ko makaranta da zai sa ta wanda ‘ya’yan jiga-jigan Abuja ke zuwa ya sa ta.
Wata rana za shi Katsina shi da Mimi»
ya ce bari su fara zuwa Malumfashi don ya ga su Hajiya Binta, ya kuma ga gonarsa su wuce, tunda Binta ta ganshi da Mimi ta hade
• rai, lokacin wayoyin hannu ba su yi yawa ba, sai ta ga Mimi da dankareriyar waya mafi tsada a wannan lokacin. Sai Binta ta bata rai ta shiga jero zantuka marasa dadin ji, tana fadin ma Alhaji cewa ya cika son kai, ba shi da hakki ya bambanta Mimi da ‘ya’yansa, nan fa ranshi ya baci an tabo rabin zuciyarsa ya ce, duk abinda za ta yi, ta yi mishi don shine ya auro ta, amma ta cire sunan Mimi a bakinta, nan fa suka yi kaca-kaca abin har ya kai su da yi mata saki daya, ya tattara yaranta guda uku suka wuce Katsina. Ran Sauda ya baci matuka, ta duddungure Mimin a gabansa, ya dai daure. fuska ‘amma bai yi magana ba, ta matsa mishi lallai sai ya dawo da Hajiya Binta, ta sa shi gaba suka je biko, bayan Binta ta dawo ne ta zo kwasar ‘ya’yanta amma sai Zainab taqi binta, saboda suna yin wasa da su Husna, ta yi-ta yi, yarinyar ta ki dole ta hakura ta barta.
Bayan Husna Hajiya Sauda ta sake haihuwar
Hasina wadda ta zame mata auta, don ta sha wahala a haihuwar tamkar ba za ta tashi ba, sai da aka yi mata aiki, Alhaji ya firgita sosai don haka ya ce da likita ahi masa taimako a tsaida haihuwar. Hajiya Binta ta kara biyu Naja’atu da Fadila su biyar kenan, Momy Nafisa ita ma ta Kara biyu Mas’ud da Aisha.
Bayan Mimi ta kammala secondary ta ce da Alhaji Bishir mahaifinta, Daddy ni fa na fi son in fita waje America ko England ko Spain. Ya ce, ba matsala ta zabi duk wadda take so, ya sayi hannun jari da sunanta, banda kamfanin da ya bude duk wata ribar tana shiga asusunta, sai da ya gama komai sannan ya samu Sauda da batun har yana Kara fada mata cewa za ta fita karatu waje, Hajiya Sauda ta ce duk ba ta yarda ba, sun yi rigima sosai, dole ta kyale shi.
Shi kuma in ta kushe kasashen turawa, sai ya ba Mimi shawara ya ce ta ta fi Dubai, tunda can garin larabawa ne, da kyar Mimi ta yarda ta tafi don yin karatun Law, zabin ta shine ta zama lauya, amma in a son mahaifinta ne ta yi karatu a kan kasuwanci, don ya dora ta a kan al’amuransa. Abba ya gama digree dinsa a kan mass com, ya samu aiki a banki, ya na Kaduna, kuma ya auri Samira wadda suka hadu a ABU Zariya, mahaifinta shine ambasadan Najeriya a Egypt. Su na da yaro daya, wanda suka sa mishi sunan Alhajin suna kiran shi Asraf.
Mukhtar kuma yana shekarar shi ta karshe, don karatun shi mai tsawo ne, likita ne fannin magunguna.
Shima Abdulkarim
shekarar shi ta karshe ya ke, Engineering ya ke karantawa. Ita kuma Mimi ta cinye shekarar farko ne ta zo hutu, za ta shiga ta biyu, wannan shine asalin su Mimi.
Tunda Ismail ya koma dakinsa ya ke mamakin Mimi, har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka? Shi kam ba maula ya zo ba, don haka ba ya zaton zai kaskantar da kanshi, ya kira layin Mahmud suka gaisa, Mahmud yana tsokanarsa, da cewa mutanan Abuja garin daula, Ismail ya ce, gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula.
Mahmood ya ce, ai mutumin nan ya shahara, to ya ya ku ka yi da yarinyar nan? Ismail ya ce, kai dai bari, nan ya sanar da shi duk yanda su ka yi, Mahmud ya ce kar ka ce za kayi zuciya, ka natsu ka danne zuciyar ka in tä shiryu za ka samu lada. Sannan mahaifiyar ta, ko don ita ya kamata ka jure.
Ismail ya ce shikenan, amma fa sai dai mu zuba.
Ita kuwa gimbiyar, wato Mimi, sintiri ta dinga yi a falon tana nazarin wannan mutumin wane irin hukuncin ya kamata ta yanke masa? Wata zuciyar ta ce, idon kin kore
Hmmm