MUSABBABI CHAPTER 8 BY HAJ HABIBA

MUSABBABI CHAPTER 8 BY HAJ HABIBA mace ta-gari ba, wacce ta fi ta komai. Ta dade tana tunanin yadda za ta yi da kudin, domin dai ba za ta iya kai ma mahaifinta kudin ba, don ba ta son ya san cewa akwai wani da namiji da take so a cikin rayuwarta. Don ba ta son ta sa masa damuwa na tunanin ya hanata abinda take so. Ya hadata da abinda zuciyarta ba ta tabaso ba, don haka ta adana kudin, ta boyesu da kyau da tumanin bayan bikinta, za ta san abinda za ta yi da su. Washegari daya kama sauran kwana biyu daurin auran. Inna Halima da yayyin Afrah, Naja’atu da Sakina da ‘yan-uwan, mahaifiyar Afrah su biyu su ne za su je su yi ma Afrah danki, amma kafin su tafi, sai da Malam Mahmud ya ja kunnen Inna Halima akan duk abinda Hajiya Kilishi ta yi masu, kada su biye mata, ko su tanka.Su yi abinda ya kai su kawai, su dawo, domin ya san Hajiya Kilishi, ya san halinta. Inna Halima ta yi masa alkawarin babu abinda zai faru, daga nan suka dunguma tare da motar kayan zuwa gidansu Musaddik. Amma ga mamakin Inn…