MUSABBABI CHAPTER 8 BY HAJ HABIBA
mace ta-gari ba, wacce ta fi ta komai. Ta dade tana tunanin yadda za ta yi da kudin, domin dai ba za ta iya kai ma mahaifinta kudin ba, don ba ta son ya san cewa akwai wani da namiji da take so a cikin rayuwarta.
Don ba ta son ta sa masa damuwa na tunanin ya hanata abinda take so. Ya hadata da abinda zuciyarta ba ta tabaso ba, don haka ta adana kudin, ta boyesu da kyau da tumanin bayan bikinta, za ta san abinda za ta yi da su.
Washegari daya kama sauran kwana biyu daurin auran. Inna Halima da yayyin Afrah, Naja’atu da Sakina da ‘yan-uwan, mahaifiyar Afrah su biyu su ne za su je su yi ma Afrah danki, amma kafin su tafi, sai da Malam Mahmud ya ja kunnen Inna Halima akan duk abinda Hajiya Kilishi ta yi masu, kada su biye mata, ko su tanka.Su yi abinda ya kai su kawai, su dawo, domin ya san Hajiya Kilishi, ya san halinta. Inna Halima ta yi masa alkawarin babu abinda zai faru, daga nan suka dunguma tare da motar kayan zuwa gidansu Musaddik.
Amma ga mamakin Inna Halima, sai ta ga
Hajiya Kilishi ta yi masu kyakyawar tarba har da lafiyayyen girki, wanda ya ji nama, ga lemo kala-kala, ga sakin fuska da suka samu
Wannan lamari ya ba Inna Halima mamaki, ya kuma ba ta sha’awa. (Boys Quarters) Hajiya Kilishi ta ba Musaddik mai dauke da dakuna biyu da bandaki, sai kicin, an yi ma Afrah dankinta, daki ya yi kyau matuka.
Domin ita kanta Hajiya Kilishi ta yi mamakin
‘irin kayan da ta ga an malala ma Afrah. Babu makusa. Hakika Malam Mahmud ya yi matukar kokari, wai ma ina ya sami kudin daya fitar da Afrah kunya?
Domin dai ta san bai aje ba, bai ba wani ajiya ba. Bayan komawarsu gida, cike da jin dadi da farin-ciki Inna Halima ta ba Malam Mahmud labarin irin karamcin da Hajiya Kilishi ta yi masu.
Wanda shi ma ya yi mamaki, ya kuma ji dadi tare da addu’ar Allah ya sa har cikin zuciyarta ta gyaru, ta kuma amshi auran Afrah da Musaddik da zuciya daya.
Ita ko Mama Hauwa a lokacin da Naja at ta gaya mata irin kyakyawar tarbar da suka samu a , gidansu Musaddik, gaba daya sai ta ji bakin-ciki da bacin rai ya cika zuciyarta, ko kadan ba ta so hakan ba.
Sai washegari wanda ya rage saura kwana daya daurin auran, sannan Musaddik ya zo ganin Afrah, shi da wasu abokansa guda hudu marasa kyan gani, don da ganinsu ka san shaye-shaye ya gama da su, banda wari ba abinda suke yi, hakan ya sa Afrah ba ta dade a wajensu ba, tayi karyar za. ta koma ta Karasa aiki. Haka suka tafi babu wani abin arziki.
Afrah na komawa gida, ta shige daki ta kulle
Kofa ta shiga rusar kuka tamkar ranta zai fita, ba ta taba ganin irin wannan auran ba, wanda miji da mata duk ba sa dokin sa, auran da ko kawarta daya ba ta gayyata ba, auran da ko dan-kwali miji bai kawo gidansu a matsayin lefen ta ba.
•Anya kuwa ta yi ma kanta adalci? Na karbar auran Musaddik? Sai dai ta bangaran zuciyarta daya tana Kara karfafa ma kanta guiwa akan auran, don ba don farin-cikinta za ta yi ba, don farin-cikin mahaifinta za ta yi, kuma biyayya ce tasa ta sadaukar da farin-cikinta ga mahaifinta, don haka tana addu’ar Allah ya ba ta ikon cinye wannan jarabawa.
Ta tashi ta goge hawayenta, ta bude kofa ta fita, ta je ta dauro alwala ta shiga gabatar da sallolin nafila, domin samun natsuwar zuciya da kuma yayewar bakin-ciki.
• Dai-dai agogo ya nuna karfe daya da kwata na dare. Afrah na kishingide kan darduma, tun bayan da ta gama nafilolinta, barci ya kwasheta.
Malam Mahmud ya tura kofar ya shigo a hankali, gami da sallama, ya dan jima tsaye a kanta yana kallonta, kafin ya kira sunanta. A gaggauce
Afrah ta tashi ta zauna tana kallon mahaifinta. “*Ki natsu Afrah, magana zan yi da ke”. Ya
fada a lokacin da yake zaunawa a gefen katifarta,
ita ma ta gyara zamanta, tana kallonsa. “To Baba,
ina jinka”. Malam Mahmud ya numfasa cike da
tsantsar damuwa, ya zuba mata ido, sannan ya fara magana.
“Na kwanta, amma barci ya gaza saceni, iya
yadda na ke boyewa tare da danne damuwata a
wannan daren, na kasa, domin damuwata kullum,
kasancewar gobe ita ce ranar da zan rabu da ke, ita
ce rañar da za ki kafa sabuwar rayuwa a wata
duniyar”
Ya kara nisawa, sannan ya dora da cewa “Ina
matukar Kaunarki fiye da duk “Ya’ yan da na haifa,
a dalilin ke ma kin fi su kaunata, na kuma fi samun
kulawa da mutuntawa daga gareki. Afrah ina son ki
sani, har ga Allah ba irin auran da na ke kwadayin kiyi kenan ba.
Kamar yadda ba mijin da na ke miki mafarkin
ki aura ba kenan, amma babu yadda za mu yi da
Kaddara da kuma abinda Allah ya hukunta a kan mu.
Afrah ina son ki sa ma ranki cewa auranki da
Musaddik jihadi ne, ki kuma sa a ranki cewa kin yi
domin Allah ne, domin kuma taimakon rayuwar
dan-uwanki.”
Hawayen idanun Afrah suka balle ta shiga
zubar da hawaye, tamkar an bude famfo. Malam Mahmud ya muskuta, damuwarsa ta Kara fadada, a hankali ya ci-gaba da magana.
“Afrah na rokeki don girman Allah ki yi hakuri da dukkan hali da dabi’ un Musaddik, na san ba mutumin kwarai bane, amma muna da tabbacin da ikon Allah halinsa na da zai dawo gare shi, ki yi hakuri, ki yi juriya, sannan daga Karshe ina rokonki da ki yafe min’
Afrah cikin kuka, ta ce “Haba Baba me ya sa ka ke neman gafarata? Babu komai, na riga na daukar ma kaina yi maka biyayya akan duk abinda ka ke so, na kuma yi imanin cewa Allah zai taimakeni, na cinye wannan jarabawar.
Kuma can a allon Kaddarata, babu sunan kowa a matsayin mijina, sai Yaya Musaddik, saboda haka na karbi wanna daddarar da hannu biyu”
Malam Mahmud ya ce “Allah yayi miki albarka. Allah ya ba ki abinda ki ke nema duniya da lahira. Allah kuma ya: tabbatar da alheri a rayuwarki “
Afrah ta ce “Ameen Baba, na gode.” Daga nan ya yi mata sallama, ya tashi ya tafi, jikinsa a matukar sanyaye, yana fita’ ta kara rushewa da kuka har ta ba uku lada. Hakika dole ta sa ma kanta hakuri da dangana, domin ba za ta taba ba mahaifinta kunya ba, ta san babu son Musaddik a zuciyarta, amma ta yi alkawarin za ta ba shi dukkan kulawa dà kariya, za kuma ta yi zama na so da kauna tare da mutuntawa da Musaddik, za kuma ta dauke shi shugabanta, kamar yadda addini musulunci ya koyar.
Washegari kuwa Karfe biyu da rabi alkawarin ya cika akan Musaddik da Afrah, domin kuwa an daura auransu a kofar gidan Malam Mahmud, akan sadaki Naira dubu goma kacal!
Bayan daura auran. Afrah ta ci kuka har ta gaji, musamman da Inna Halima ta shigo dakin nata, ta sa ta gaba da nasihohi da shawarwarin yadda za ta zauna da Musaddik.
Har zuwa lokacin da za’a kai ta dakinta, wanda abin takaici hatta motar da za’ a kai ta dakin mijin nata, da motar. yayan ta Mansur aka kai ta.
Inna Halima da ‘ya’yanta su Naja’atu da matar
Mansur. Sai dangin mahaifiyarta su uku su ne suka kai
Afrah dakin mijinta, nan ma Hajiya Kilishi ta yi kokarin wadata su da abinci har suka bar gidan, ba su yi kuka da komai ba.
Sun tafi sun bar Afrah ita kadai. Da kanta ta tashi ta zazzaga dakin nata, hakika ta yaba ma mahaifinta, domin dai dakinta ya kawatu, kamar na kowace ‘yar gata, tabbas an fit da ta kunya. Bayan ta gama ganin ko’ina ne, ta dawo ta zauna tana tsammanin shigowar angon nata.
Amma shiru, har zuwa lokacin da agogon bangon ta ya buga Karfe daya na dare, ba Musaddik, babu alamarsa, ta tashi cikin matukar damuwa ta kulle kofar dakin, sannan ta wuce bandaki, ta dauro alwala, ta kyautata niyyarta ta shiga yin sallar nafila, zuciyarta cike da tsantsar damuwa.
Afrah ba ta gushe tana sallah ba, har aka fara kiran sallar farko na asubah, dai-dai lokacin Afrah ta ji ana bugun kofa da karfin gaske, tamkar za’a balle kofar, ta mike a gigice zuwa bakin kofar.
“Afrah ki bude kofar.” Muryar Musaddik ta daki dodon kunnenta, da sauri ta bude kofar, tana budewa, ya fado dakin a buge yake, koda Afrah ba ta san warin giya ba, to tabbas Musaddik tsamin giya yake, da sauri ta matsa, ya fada kan doguwar kujera yana sambatun surutai.A sanyaye ta maida kofar ta rufe, ta dawo ta tsaya a gabansa tana kallonsa, hawaye a malala daga idanunta, ya dago da idanunsa jajir! Wadanda ba su buduwa duka, ya ce “Kin tsaya a kaina, ki matsa ki ba ni waje.Da sauri. Afrah ta koma kan
daya kujerar ta zauna, tana goge hawayenta masu dumi. Da kyar ta samu ta tashi ta yi sallar asubahi, wanda kafin ta idar Musaddik ya gama wanke kasan dakinta da aman giya, me matukar wari, tana
Idarwa, ko addu’a ba ta gama yi ba, ta tashi ta shiga aikin goge aman, tana kuka me dauke da sautin ban tausayi.
Bayan ta gama gyara wajen ne, ta taimaka masa ta janye shi daga falon zuwa uwardaka. Ya bata wandonsa da fitsari, ya bata rigarsa da amai, duk da tana cike da jin nauyinsa, haka ta taimaka masa wajen cire kayansa, ta sa masa wasu, sannan ya koma kan gado da kansa, ya kwanta, cikin rashin dawowa hayyacinsa. Bayan ya kwanta ne. Afrah ta fice ta koma falonta, ta zauna ta dasa wani sabon kukan, gaba
daya har jikinta ya yi dumi, shin wace irin mummunar rayuwa ta shigo a daranta na farko a gidan mijinta?
Bata fara da komai ba, sai da aikin kwasar
aman dan giya da aikin gyara wajen fitsarinsa, shin haka rayuwarta za ta kasance tare da Musaddik?
Idan ko har haka ne rayuwarta ta riga ta kare babu sauran wani abu na farin-ciki ko na jin dadi daya rage a gareta. Kaiconta, kaicon wannan mummunar rayuwar, hakika ta yi sadaukarwa me girma.
Karfe takwas Afrah ta yi wanka, ta gyara kanta, sai dai kallo daya za ka yi mata ka san tana cikin tashin hankali da matsananciyar damuwa, domin kuwa har ta rame idanunta sun zurma ciki, fuskarta ta yi fauu! Idanunta ma’abota girma da haske, duk sun Kaskance, a sakamakon kukan da ta ci, har zuwa lokacin Musaddik barci yake yi ko motsi baya yi.
A dalilin hakan Afrah ta janyo hijabinta ta sa ta fito zuwa cikin gidan, domin ta gaida. Hajiya Kilishi. A katon falonta ta tadda ita zaune da me aikinta Amimi, tana ta kaiwa da komowa wajen shirya abincin karyawa akan tebur, cikin sallama Afrah ta shiga falon Hajiya Kilishi. Ta dago ta kalleta gami da amsa sallamar can cikinta.
Har kasa Afrah ta zube tana gaida ta cike da girmamawa da mutuntawa. Hajiya Kilishi ta amsa ba yabo, ba fallasa, rai a bace kamar wacce aka yi ma wani laifi, hakan ko ya ba Afrah mamaki.
Domin sanda aka kawota gidan a jiya, ba haka ta karbeta ba, ta karbeta cikin kyautatawa da kauna, to mênene yanzu? Me ya yi zafi? Za ta ga canji nan da nan, ko daman Hajiya Kilishi tana da. dalilinta na yin duk abinda ta yi ne a baya ne? “Ya kwanan amarci?”
Tambayar Hajiya Kilishi ta katse Afrah daga tunanin da take yi, ta dan kalleta kadan, ba tare da ta ba ta amsa ba.Hajiya Kilishi ta ci-gaba da cewa “Na san kin yi kwanan amarci me dadi, domin ina da tabbacin angon naki ya ba ki kyakkyawar kulawa da dawowa akan lokaci dai-dai sallar asubah, na san kuma ya zo maki da kyakkyawan sakamakon kaiwa asubah a waje.” Cike da mamakin maganganunta. Afrah ta dubeta idanunta sun kada sun yi jajir!
Hajiya Kilishi ta gyara zamanta gami da yi mata wani sakaran kallo, sannan ta ce “Afrah na yi mamakin da ki ka amince da auranki da Musaddik a matsayinki na yarinya mai natsuwa, mai kuma ilimi, na yi zaton za ki yi Kokarin girmama kanki, ki samu rayuwa ta-gari.
Wacce za ta amfaneki, ta kuma amfani
‘ya yanki, sai ga shi kin buge da watsa ma kanki rayuwa da kanki. Meye riba ko amfanin auranki da mutumin da bai san inda rayuwarsa tasa gaba ba.
Me za ki samu?”
Ta Kara kura mata ido ta ci-gaba da cewa.
«Shi mahaifin naki daya hada auran ku, ya san cewa Musaddik bai dace da ke ba, idan kuma don abin duniya ya aura miki shi.
Ya san cewa Musaddik baida ragowar komai na gadonsa, asalima inda kuke zaune yanzu, a matsayin alfarma ce, taimaka maku nayi, alfarma : nai maku, na ba shi aron wajen da ya aje ki. Idan na so sai na ce yaje ya nemi wajen zama, amma na taimaka masa, domin Allah.”
Anan ne Afrah ta dago da idanunta, da tuni suka fara zubar da hawaye ta ce “Mahaifina bai taba tunanin ya aura ma Yaya Musaddi ni saboda tunanin fanshewa daga wani abin duniya daga gare shi ba, ya aura ma sa nine, saboda Allah ya riga ya rubutani a cikin matan da Yaya Musaddik zai aura.
Ita kuma Kaddarar Ubangiji babu wanda ya isa ya kauce mata, don haka a shirye na ke da na na karbi kaddarar, zan kuma rike Yaya Musaddik da daraja fiye da yadda kowace mace take daukar mijinta.
Hajiya Kilishi ta saki tsaki ta ce “A hakan har wace daraja Musaddik yake da ita? Ke kam! Ki na da babban aiki a gabanki, na zama da dan iska, dan giya a matsayin miji Afrah ta yi dan murmushi ta ce “Ba komai.
Allah ya ba ni ikon ci-gaba da zama da shi a hakan, domin ta nan zan sami aljannata.”
Tana gama fadin hakan, ta mike, ta ce “Dama na zo na gaisheki ne, bari na koma, kada ya tashi barci ba na nan’Tana gama fadin haka ba ta saurari komai ba, ta fice, a yayin da Hajiya Kilishi ta bi ta da wani mugun kallo, zuciyarta a zafafe, lallai yarinyar nan zuciyarta a dake take, yanzu duk abinda Musaddik ya yi mata à jiya ba ta gani ba?
Mai-gadi ya tabbatar mata da cewa sai asubah ya dawo gida, kuma ya dawo a buge da giya, ace ango yayi ma amaryarsa haka a daren farkonsu, ai ya isa dalilin da za ta nemi kashe auran ma, amma kalleta ko a jikinta. Hmm! Rashin sani, ya fi dare duhu, domin Hajiya Kilishi ba ta san dalilin auran Afrah da Musaddik ba kenan, don ya sami me taimaka masa, tare da tallafa masa da kuma kokarin maido da shi hanya madaidaiciya, don haka duk halayensa ba baki bane agun Afrah, ta sani, asalima halayen nasa su ne suka sa ta aure shi.
Afrah na shiga daki, ta tadda Musaddik zaune a bakin gado, ya yi tagumi hannu biyu, tana ganinsa a haka, ta yi saurin korar damuwar da ke fuskarta cike da fara’a, ta karasa inda yake, ta ce.
“Ka’ tashi?” ya dago fuskarsa cike da damuwa, ya kalleta a hankali cike da kunya, ya dauke kallonsa daga gareta, sannan ya ce.
“Afrah don Allah ki yi hakuri, ki yi min afuwa”. Ta dan yi murmushi ta ce “Me ka yi da ka ke neman afuwata?”
Ya numfasa ya ce “Kin fi kowa sanin abinda na yi, domin ko ni da na yi, sai dai na kintaci abinda na yi, na tuna, dan abinda zan tuna, amma sanin komai, sai ke da na yi a gabanki, don haka ki yi hakuri, koma me nayi a daran jiya, ina neman yafiyarki, don Allah”
Ta jinjina kai ta ce “Ya wuce, babu komai, amma ka san wani abu?” Ya girgiza kai yana kallonta. “A’a”
Ta dan gyara tsayuwarta ta ce “Ina yi maka kallon me ilimi wanda ya san abinda Allah ya fada akan giya da kuma me shanta, ban tada tunanin zan tadda kai a cikin shaukin shan giya ba, bayan ka san giya ita ce uwar kabairai.
Komai za ka iya aikatawa, idan ka sha giya, to me zai sa ka sha, me zai sa ba za ta zama abar tsana a gunka ba, sai dai abar kauna, sannan ka rasa lokacin da za ka sha, a daren auran ka. Yaya Musaddik? Me ya sa za ka yi haka?”
Musaddik ya runtse idanunsa, ya bude, sannan ya ce “Ba za ki taba ganewa ba Afrah, ba za ki gane ba”. Yana gama fadin haka, ya mike yana kokarin shiga bandaki. A frah ta yi kokarin maida
hawayenta, ta ce “Ya kamata ka fara yin wanka ne kafin ka yi sallah, bari na kai ma ruwan wankan.
A hankali Musaddik ya dawo da baya, ya koma ya zauna a bakin gadon, a yayin da Afrah ta yi gaggawar fita, ta hada rishonta, ta dura kananzir ta kunna ta dora masa ruwan wanka, cikin kankanin lokaci ruwan ya yi zafi, ta juye ta kai masa. Ya yi wankan, ya yi kuma alawala, bayan ya fito ne ya kintsa ya yi sallar asubah. Dai-dai karfe tara da rabi, zuwa lokacin ta gama abin karyawa. Domin Malam Mahmud ya yi kokarin hado
Afrah da garar abinci, hatta kananzir da garin two, sai da ya hadota da shi. Musaddik yana gama karyawa, ya fice. Ko kadan babu dokin auran a ransa, balle har ya yi tunanin ya zauna a gida na dan lokaci tare da matarsa. Haka ya tafi ya bar ta cikin matsananciyar damuwa. Domin duk yadda ta dauki abinda sauki.
• Ta ga ba haka bane, hakika akwai katon aiki a gabanta.
WAIWAYE, ADON TAFIYA.
Alhaji Mansur Musaddik Mai Fata shahararre ne, kuma hamshakin dan kasuwa, wanda ya mallaki manya-manyn kamfanoni na sarrafa fatu, sannan bayan hakan yana safarar fatun zuwa Kasashe makwabtan Najeriya.
Hakan ya sa kasuwancinsa ya kara fadada, ya kuma sami karbuwa sosai, mutum ne me saukin kai, me addini tare da son kyauta ma “yan-uwansa, duk da ya taso cikin matsananciyar tsana ta yan-uba a dalilin maraicin uwa da uba da ya yi gaba daya, amma duk da haka bai hana shi taimaka masu ba.
Bayan da Allah ya azurta shi. Hajiya Kilishi ita ce matarsa ta farko, auren saurayi da budurwa, mace ce me ji da kanta, fadin rai da daukar kanta madaukakiya.
tanda matsanancin kishi, wanda hakan yasa take ganin Alhaji Mansur ba zai iya yi mata kishiya ba, musamman idan ta yi la’akari da irin son da yake mata, ta haifa masa ‘ya’ ya har uku mata.
Hassana da Hussaina, sai Amina. Bakin-cikinta daya a rayuwarta, shine yadda ba ta da da namiji, ga hailuwarta ta tsaya mata, gashi tana da gamshahshen sanin cewa babu abinda mijinta yake nema ido rufe irin magaji da namiji, don haka kullum addu’oi’nta. Allah ya ba ta haihuwar da namiji, amma ba ciki ba dalilinsa.
Hakan ya sa a lokacin da Alhaji Mansur ya furta mata maganar Karin auransa da Harirah hankalinta ya yi masifar tashi, hauka ne kawai ba ta yi ba, haka zalika ta yi kokarin lalata auran ta hanyoyi da dama.
Domin ta yi ta asarar kudinta a wajen
Malamai da Bokaye, don dakatar da auran. Amma da yake kaddararran al’amari ne. Allah ya riga ya kaddara Harirah sai ta kasance uwar dan Alhaji Mansur, sai da Allah ya tabbatar da auransu.
Sai dai Hariral ta zauna cikin kunsar bakin-cikin Hajiya Kilishi, domin kuwa ta kankane komai a gidan. Harirah ba ta da wani Karfi a matsayinta na matar gida, komai sai Hajiya Kilishi ta amince, ta kuma sa baki sannan yake yiwuwa.
Koda ta bangaren Mai-gidan ne, domin Hajiya Kilishi ta riga ta gama mallake shi ta hanyoyin sihirinta. Hakan ya sa Harirah ta ci-gaba da zama a wulakance a kaskance a gidan mijinta.
Har zuwa lokacin da Allah ya yanke mata wahala, ya dubi hakurin da ta yi a dalilin. cikin daya ba ta, tunda ta sami cikin, kadarin Hajiya Kilishi ya karye, domin yadda Alhaji Mansur ya dauki son duniya ya dora akan cikin, ga kuma wata
Hmmm