MUSABBABI CHAPTER 7 BY HAJ HABIBA

MUSABBABI CHAPTER 7 BY HAJ HABIBA “A gaskiya Hajiya kin san tsakanina da ke babu cuta babu cutarwa, ba na kuma boye maki duk wani abu da na gani na dadi ko ma rashin dadi, don haka maganar auran Musaddik babu, abinda zai hana shi yiwuwa, sai dai mutuwar daya daga cikinsu” Hajiya Kilishi ta dafe Kirjinta, hankalinta ya tashi matuka ta ce “Yanzu babu wata hanya da za a bi a dakile lamarin, dole sai hakan ta faru?” Ya jinjina kai ya’ce. “Kwarai kuwa Hajiya. Dole sai wannan auran ya kasance, babu wata mafita, idan kuma ba ki yarda ba, to ki jesduk inda za ki je, amma ki sani, kudinki za su ci a banza babu biyan bukata.” Hajiya Kilishi ta kalli Hajiya Rakiya, duk jikinsu a sanyaye, sannan Hajiya Kilishi ta dawo da kallonta ga Mai Rakwacam ta ce “Na yarda da maganarka, ban kuma kasance me jayayya akan duk abinda ka fada ba, domin ina gain gaskiya a cikin aikinka, sai dai abu daya”. Ya ce “Menene shi?” Ta ce “Na saduda akan auran, amma ina son Musaddik ya dawwama akan halin da yake ciki, ko kadan…