MUSABBABI CHAPTER 7 BY HAJ HABIBA
“A gaskiya Hajiya kin san tsakanina da ke babu cuta babu cutarwa, ba na kuma boye maki duk wani abu da na gani na dadi ko ma rashin dadi, don haka maganar auran Musaddik babu, abinda zai hana shi yiwuwa, sai dai mutuwar daya daga cikinsu”
Hajiya Kilishi ta dafe Kirjinta, hankalinta ya tashi matuka ta ce “Yanzu babu wata hanya da za a bi a dakile lamarin, dole sai hakan ta faru?” Ya jinjina kai ya’ce.
“Kwarai kuwa Hajiya. Dole sai wannan auran ya kasance, babu wata mafita, idan kuma ba ki yarda ba, to ki jesduk inda za ki je, amma ki sani, kudinki za su ci a banza babu biyan bukata.”
Hajiya Kilishi ta kalli Hajiya Rakiya, duk jikinsu a sanyaye, sannan Hajiya Kilishi ta dawo da kallonta ga Mai Rakwacam ta ce “Na yarda da maganarka, ban kuma kasance me jayayya akan duk abinda ka fada ba, domin ina gain gaskiya a cikin aikinka, sai dai abu daya”.
Ya ce “Menene shi?” Ta ce “Na saduda akan auran, amma ina son Musaddik ya dawwama akan halin da yake ciki, ko kadan ba na son a sami wani canji a game da rayuwarsa a dalilin auransa”. Ya yi dariya ya ce.
“Wannan ai babu canji, ko na yi aiki akai ko ban yi aiki akai ba, ba za’ a samu wani canji ba. Zai ci-gaba da zama a halin da yake ciki, auransa ba zai canja shi da komai ba.”
Hajiya Kilishi ta ce “Godiya na ke”. Ta balle jaka ta fito da kudi ta mika masa, ya amsa yana godiya gami da Kara Karfafa mata guiwa akan lamarin Musaddik, daga nan suka yi masa sallama suka fito.
Har sai da Hajiya Kilishi ta fara tuka mota, sannan Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce “Amma yarinyar da za ta auri Musaddik mahaukaciya ce ko?” Hajiya Kilishi ta ce
Ko daya da hankalinta ras!
“To idan ba mahaukaciya ba, me za ta ci da
Musaddik, wane jin dadi za ta samu daga gare shi, mutumin da ina ganin ko wanka ba ya yi, kullum yana wurin *yan daba yana shaye-shaye, yana kuma yawon bangar siyasa, ko dai suna tunanin za su sami kudi ne a hannunsa?”
•Ta girgiza kai ta ce “Ubanta ya fi kowa sanin
Musaddik baida ragowar sisin kwabo, ni dai ban san dalilin da mahaifinta yake son hada wannan auran ba da zai zama masifa da fitina ga ‘Yarsa, dama shi mutum ne me kafiyar tsiya, amma tabbas ba na son Musaddik ya auri ‘Yarsa Afrah”.
Hajiya Rakiya ta dubeta ta ce “To ki na ganin za mu gwada sa’ar wani wajen ne?” Ta girgiza kai ta ce “A’a Hajiya. A gaskiya na yarda da aikin Mai Rakwacam, kin fi kowa sanin
cewa tsawon shekarun nan, shi ne yake taimaka min, bai taba yimin aiki na ga rashin sa’ar aikin ba.
Idan kuma abu ba zai yiwu ba, zai gaya min, ba zai cin min kudi a banza ba, na kuma sha gwada wani wajen, idan ya ce ba zai yiwu ba.
Haka nan za’a ci min kudi kuma babu biyan bukata, shi ya sa yanzu idan ya gaya min abu ba zai yiwu ba, na kan hakura gaba daya na rungumi qaddara, kamar yanzu da na saduda na hakura akan maganar auran nasu.”
Ta nisa gami da hadiye yawu kafin ta ci-gaba da magana. Hajiya Rakiya ta ce «To ki na. da gaskiya, tunda kin yarda da shi, gara ki aje hankalinki waje daya”. Ta ce “Haka ne, amma na yi alkawarin ba zan taba barin Afrah ta sami kwanciyar hankali ba, dole sai auran ya fita a ranta, da kanta za ta nemi wajen gudu.
Hajiya Rakiya ta yi dariya ta ce “Kin ji ki da wata magana, za ki bata ma kanki lokaci, rashin kwanciyar hankali, har ya wuce wanda mijinta zai sakata a ciki? Halinsa kadai ya isa ya sa ta gudu ta bar shi, wa zai iya da Musaddif “
Hajiya Kilishi ta yi dariya ta ce “Kai Hajiya
Rakiya sai a bar ki.” Gaba daya suka kwashe da dariya. Sai dai fa ba haka Hajiya Kilishi ta so ba, har ga zuciyarta auran nan yana daya daga cikin abinda ta tsana a duniya, amma babu yadda za ta yi, tunda haka kaddara ta riga fata. Ta bangaren gidan Malam Mahmud kuwa shire-shiryen bikin Afrah da Musaddi& ya kankama, ita kuwa Na ‘ima tunda ta dawo gidan, take ma Allah godiya daya gajarce mata wahalar auran Musaddik.
Inna Halima da kanta ta sai ma Afrah gado da katifa da sauran tarkacen kayan kicin.
Kudin kuma da su Kabir suka ba mahaifinsu a matsayin gudunmuwa, su ne ya ba Inna Halima ta sayo kujeru kayan kallo da firij har da keken dinki da sauran duk kayan da ake bukata.
Duk da haka sai da kudin suka ragu, su ne ya yi amfani da su ya sayi kayan abinci. Mama Hauwa kuwa tunda ta fabimci Mansur da Kabir ne suka bada makudan kudin sayayyar Afrah, ta ji bakin-ciki kamar ya kasheta, don sai da ta kirasu ta yi masu kaca-kaca. Ta nuna masu matukar bacin ranta.
Shirye-shirye sun yi nisa, sun kankama, amma ga Afrah, al amarin ya fara ba ta tsoro, saboda tun daga ranar da Musaddik ya zo gidansu suka yi magana, bai kara dawowa ba.
Ba shi, ba labarinsa, dan ko ta je gidan Inna Halima ranar juma°a har ta gama kwanakinta ta dawo gida, ba zai zo ba. A zahiri abin yana damunta, tana matukar son ta san halin da yake ciki.
Ga shi ba ta san inda za ta same shi ba, balle ta nemo shi ta ji lafiyarsa. Haka zalika bata nuna damuwar komai a gaban kowa, musammam mahaifinta da Inna Halima, haka zalika koyaushe tana samun Karfin guiwa daga Ya Sayyadi Habib tare da addu’o’i, wadanda a yanzu su Afrah ta rike suka zamar mata garkuwa.
Idan ma akwai abinda ke damunta, to bai wuce habaici da maganganu marasa dadi da Mama Hauwa ke mata ba, tare kuma da nuna mata tana cikin jin dadi, don ganin rayuwarta za ta lalace, a dalilin auran Musaddik, amma da yake ba ta son damuwar mahaifinta, haka ta dage tana hadiye duk abinda Mama Hauwa ta yi mata ba tare da ta nuna damuwarta ba.
Har yau daya rage saura kwana shida daurin auran Musaddik da Afrah, da yamma Afrah na cikin wankin ragowar kayanta, gefe Malam Mahmud ne zaune tun dazu, da alama wani yake, jiran zuwansa, dai-dai lokacin Musaddik ya yi sallama ya shigo.
Afrah ta yi saurin dago da kanta tana kallonsa, ko don ta dade ne ba ta gan shi ba? Sai ta ga ya yi baki, ya rame duk bakinsa ya bushe kamar wanda ya shekara bai sha ruwa ba, tausayinsa ya kara kamata, amma shi kallo daya ya yi mata, ya dauke kansa ya wuce wajen Kawunsa, ya tsuguna a gabansa, ya gaishe shi.
Malam Mahmud ya dade yana Kure masa da ido cike da tausayawa ya ce “Musaddik ina ka shiga kwana biyu, duk inda yakamata a nemeka na nemeka, amma ba ka nan, wayarka kuma ba samu?” Ya dan numfasa, sannan ya ce “Kawu ka san idan zabe ya kawo jiki, ba ma samun wani zama, na dan jima ba na garin ne.” Malam Mahmud ya a girgiza kai, ya ce.
«Yanzu Musaddik don Allah ba za ka yi ma kanka fada ka fita daga harkar nan ba, bangar siyasa ba ta dace da kai ba, kana sane da irin wahala da zubar da mutunci da ku ke yi akan mutanen da su kansu ba su san darajar kansu ba, balle darajarar ku, ya kamata ace ka natsu Musaddik ka san inda duniya ta sa gaba
Musaddik ya dan sosa keyarsa ya ce “Sai hakuri Kawu, ayi ta mana addu’a dai har zuwa lokacin da Allah zai kawo mana agaji, a Kara hakuri da mu.” Ya gyada kansa ya ce. “Allah shi kyauta, ya kuma shirya”. Ya gyara tsugunnarisa ya ce Amin.”
Malam Mahmud ya dube shi ya ce “Ka na kirge da kwanakin da suka rage na auranku ko?” Ya gyada kai alamar eh, sannan ya ci-gaba da magana,
“To shine dalilin nemanka, akan maganar wajen da zaku zauna, ka na da wajen da za ku zauna ko kuwa?” Musaddik ya ce.Eh . Kawu, na yi magana da
Hajiya shekaranjiya ko za ta taimaka min da gidan da zan zauna aro, koda nawa ne na da, da na zauna da Hannatu, sai ta nuna min ai ba ta da iko da gidan, tunda na Hannatu ne, ba nata ba.
Ya dan yi shiru. Sannan ya dora da cewa “Shi ne ta ce sai dai ta taimaka min da daki anan cikin gidan namu, na kuma amince da hakan, tunda banda sauran wani zabi. Malam Mahmud ya yi shiru na dan wani lokaci, sannan ya dago da idonsa ya kalli Afra da ta ke ta wankinta tamkar ba ta jin abinda suke fada, a hankali ya dawo da kallonsa ga Musaddik, sannan ya ce “To shi kenan, Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri. Allah kuma ya daidaita zaman da ita”
Ya ce “Amin”. Daga nan ya tashi ya shiga cikin dakinsa, a nan ne Musaddik ya juya yana kallon Afrah, ita ma ta juyo ta kalle shi, fuskarta dauke da murmushi, cikin jin nauyinta ya dauke idonsa a kanta.
Zuciyarsa cike da mamakin irin zuciyar
Afrah, ya kamata ace ta yi fushi da shi, a dalilin rashin Kara waiwayarta da bai yi ba, amma babu alamar damuwar hakan ko tsanarsa akan hakan.
Dai-dai lokacin da Malam Mahmud ya fito rike da kayan sawa. Mama Hauwa ta fito daga daki ta tsaya ta kama Kugu ta rike tana kallonsu. Malam Mahmud ya zauna, sannan ya mika ma Musaddik: kayan, shaddoji ne da yadiddika masu kyau, akalla za su yi kala tara, ya ce “Na san ba ka tanadi komai ba, don haka ga kayan sawa nan, sannan ga wannan”
Ya mika masa Naira dubu goma. “Ban ce ka je ka kashesu a banza ba, na umarceka da ka aje su ka yi amfani da su a bikin ko wata harkar ta alheri.” Ya karba cike da godiya da yabo, ya yi ta godiya.
Malam Mahmud yana fadin.
“Ka daina yi min godiya, don ban ga dalilin yi min godiya ba, kai fa dana ne halas malas, don na yi maka wani abu, babu bukatar ka yi min godiya.”
Musaddif ya ce “Kawu karamcinka a gareni, ya kai duk inda ya kai, godiya ba za ta isa ba. Sai dai na ce Allah ya Kara girma.”• Zai yi magana kenan. Mama Hauwa ta amshe.Ai dole ka ce godiya ba za ta isa ba, gata mugun abu, aka ce inji wanda bai samu ba, wanda zai kawo kayan lefe, shi ake ba kayan sawa, wannan aure shine gallatiri, tunda na ke ban taba ganin irin wannan auran gatan ba.”
Ta juya ta kalli Afrah ta ce “Lallai Afrah ba za ki taba daraja a wajen Musaddik ba, don bai san darajarki ba, balle tsadarki, daga sama kawai ya sameki. Allah ya kyauta. Malam Mahmud ya daga mata hannu, ransa a bace ya ce “Na gaya miki, na Kara gaya miki, ki fita daga cikin duk abinda ya shafi auran Afrah, babu ruwanki, ki shiga taitayinki Hauwa”
Ta saki tsaki ta ce, a yayin da take shigewa dakinta “Kanku ake ji. Wai mahaukaci ya fada rijiya”
Malam Mahmud ya dawo da kallonsa ga
Musaddik, wanda fuskarsa ta nuna matukar damuwa da maganganun da Mama Hauwa ta fada ya ce.
“Kada ka damu Musaddik. Hauwa ce fa, haka take, ba za ta taba canjawa ba, don haka babu dalilin da mutum zai damu da dabi unta, kai ma ina umartarka da ka manta da zantukanta.Ya jijina kai ya ce “Haka ne Kawu, babu komai, na gode.” Daga nan Musaddik ya hada kayansa a cikin leda, wanda zuwa lokacin Afrah ta shige dakinta, ranta da hankalinta a tashe da maganganun Mama Hauwa.
Wanda hakika ta san gaskiya ne. Duk abinda ta fada, ba ta da wata daraja a wajen Musaddik ko ba’a kan rashin tsinana komai akan bikin ba, ko a
•cikin zuciyarsa, ta san ba ta da daraja domin daga dukkan alamu. Musaddik baya sonta, dole zai aureta, don Kawunsa, kamar yadda dele za ta aure shi, don mahaifinta. Malam Mahmud ya riga Musaddik fita daga gidan, don a tunaninsa zai tsaya su tattauna da Afrah, ita ma Afrah ta yi tunanin zai memeta su yi magana, musamman akan auran nasu, duk da ta san ba wani shirye-shiren da za suyi akan auran, amma ga mamakin Afrah, mahaifinta yana fita. Musaddik ya tattara kayansa shi ma ya fice, ba tare daya nemeta ba. Shin wane irin aure za ta yi? Me Musaddik ya dauketa? Wadannan tambayoyi. Afrah tana
matukar bukatar amsoshinsu, amma ba ta san inda za ta samo amsarsu ba. Saura kwana uku daurin auran. Afrah ta nemi hutu a Islamiyyarsu, a ranar Ya Sayyadi ya nuna matukar damuwarsa na rabuwa da yarinyar da zuciyarsa take muradi.
Iya yadda ya so ya boye damuwarsa a yau, hakan ya faskara, yadda idanun Afrah suke fitar da hawaye, haka idanunsa suka yi ta tsiyayar hawaye masu matukar dumi da kyar ya samu ya lallashi kansa.
Sannan ya ci-gaba da yi mata nasiha gami da shawarwari a game da zaman auranta da za ta fara da Musaddik, wanda ta ji dadin nasihohinsa, domin tabbas za su taimaketa.
Daga bisani ya ba ta enbilof a matsayin gudunmuwarsa. Ta karba ta yi godiya kwarai,
wanda sai da ta isa gida ta zauna,
sannan ta san abinda Ya Sayyadi Habib ya ba ta a matsayin gudunmuwarsa, kudi ne kimanin Naira dubu. ashirin. Ta kara tausaya ma Ya Sayyadi, ta kuma Kara tausaya ma kanta da wannan auran kaddarar daya gitto rayuwarta.
Hakika ba za ta taba mantawa da Ya Sayyadi ba, kuma ba za ta taba daina yi masa addu’ ar samun
Hmmm