CANJIN RAYUWA CHAPTER 6 BY HALIMA A K/MASH

kace haka ka ban mamaki, kai da na sani dakakke mara tsoro na ga ko a nan a Islamiyya da muke koyarwa duk yaran masu da shi din ne, amma shakkar ka suke yi.

Isma’il ya ce, ba za ka gane ba, ita fa wannan ya rinyar ina zaton irin tabararrun nan ne ko da ban sani ba dai, amma na ga alamar kamar uban bai son a takura mata, ga ta da alamun ta tsani talaka ba ta dauke shi wani abu ba, ni kuma duk sun san hali na, ba na son raini. Shi ya sa ba na raina mutane, dalili kenan da na ke ta tunanin ya ya koyarwar tamu za ta kasance? Mahamud ya ce, shawarata a nan kawai ka aje duk wani waswasi kai dai ka amshi kudinka ka cika burinka.

Ka tuna da karatun da muke son yi, kai ko yau Jami’ar Madina suka kira ka za ka bukaci kudi. Ga yarinyar nan da ka dauki son duniya ka dora mata, Zainaba, kar ka manta da abinda mahaifiyarta ta ce, sadakin ‘yarta dubu dari, akwatin ‘yarta me shida ne, Ismail yace,

da na tuna wadannan abubuwan ni ke jin cewa ya kamata in jajirce in je, yanzu dai malam nake son gani in nemi shawararsa. Da ya amince zan Kara samun kwarin gwiwa.

Haka kuwa yana unguwar har aka yi Isha’i, lokacin ne Isma’il ya samu magana da Malam, ya yi masa bayanin komai, Malam ya ba shi goyon baya tare da karfafa masa gwiwa, cikin farin ciki ya nufi gidansu.

Dakinsa da ke Soro ya bude ya shiga ya kunna wuta haske ya gauraye dakin, ya zauna bakin katifarsa ya cire hularsa da agogo tare kunna wayarsa ya dora a teburin da ke gefen katifar mai dauke da tarin littafai, ya ciro kudin da Alhaji ya ba shi, da ma ya ba Mahamud dari biyar daga ciki. Ya dauko wani littafi wanda a cikinsa ya ke ajiyar kudi ya dora su a kan kudin da yake ciki, ya mayar da su ya rufe, sannan ya mayar da shi a mazauninsa. Ya dan kwanta rigin-gine gurin Zainaba yake son zuwa don zuciyarsa ta matsu da son ganinta, amma yana jin jikinsa ya gaji. Wayarsa ta soma ruri, yana daukowa ya ga Hajiya ce.

Ya daga tare da sallama ta amsa ya gaida ta. Ta ce, ka yi hakuri na kira ka cikin dare. Ya ce, ba komai Hajiya. Ni ma na so in kira ki, sai na ga bari dai in bari sai da safe.

Ta ce, daman na kira ka ne in sanar da kai cewa Alhaji sun tafi dazun da Mimi, ina son don mu karkare maganar ina son in sanar da shi. Sannan ka fada min albashinka, yaushe kuma za a kai ka Abujan? Saboda ku soma karatun da wuri. Isma’il ya gyara zama,

Hajiya batun albashi dai ni ba zan iya cewa ga shi ba, ta ce, yauwa ni ma ba na son ka ce ma shi kaza ne.

Don Alhaji in mutum yana son ya ci moriyar shi to ya biyo shi ta haka. Zan fada mishi cewa ka ce duk abinda ya ga ya yi, na san zai nemi shawarata. Ni kuma na san abinda zan ce masa. Labarinka da ka bamu a jiya na tausaya maka, kuma na tabbatar kana bukatar taimako, yanzu ka yi magana da malamin naku? Ya ce, eh? Gobe zan je gidajen da nake koyarwa in sanar da su. Ko zuwa jibi sai mu tafi Abuja din. Ta ce shikenan Ismail sai ka zo jibin, ya ce to na gode, Hajiya ta ce ba komai. Sun yi sallama Hajiya Sauda tana ji a zuciyarta Ismail tamkar danta. Washegari kamar yadda ya alkawarta ya sanar da duk wanda ya kamata cewa, gobe zai yi tafiya zuwa Abuja, ya sanar da su Zainaba kadai ta rage masa ya je su yi sallama.

Da yamma la’asar ya shirya zuwa gurin Mahamud don ya raka shi zuwa gurin abar son sa, su yi sallama. Yana isa Islamiyyar da suke koyarwa ya samu Mahamud ya fito daga ajin da yake koyarwa. Bayan sun gaisa Ismail ya ce mu je ka raka ni gidan su Zainab in duba ta da

jiki, daga nan in yi sallama da ita. Ko ta zo Islamiyya?

Mahamud ya bata fuska,

gaskiya Ismail ka je kawai. Ka ga ba a ma ta shi ba. Yace amma ka fito aji ai, wai me ya sa ne Mahamud ko yaushe idan na ce muje gidan su Zainab sai ka ce min a’a? Yau dai dolenka mu je, kuma gurinka zanbar amanar ta. Mahamud ya ce, mu je dai, amma ba ruwa na da wata batun amana. Suka jera a hanya ya kalli Mahamud, ban san me ya sa ku ke jin haushin yarinyar nan ba. Haka yaya Amina kullun sai ta yi min korafi.

Mahamud ya ce, ai ban boye maka dalilin ba. Yarinyar tana da Karancin tarbiya, sannan ‘yar mace ce. Ga shi uwar ta dora dogon buri a kanta. Isma’il ya ce’ ina fadi maka ni wannan ba wata matsala ba ce a guri na.

Ni dai ina sonta don Allah ita ma tana so na, in ta zo hannu na ba sai yadda na yi da ita ba? Mahamud yace, haka ka ke fada. Suna isa kofar gidan suka aiki wani yaro ya kira ta. Ya fito ya ce an aike ta, Isma’il yace jikin ya yi sauki kenan, ya kalli yaron, je ka ce nesa ne ta je, ko kusa ne, mu jira ta? Yaron ya koma, Ismail ya kalli Mahamud, in nesa ne sai mu tafi mu dawo da daddare. Mahamud ya ce ka dawo dai ni kan ba zan zo ba.

Yaron ya iso tare da cewa da nisa, suna juyawa da niyyar tafiya, sai ga ta cikin

dauke da tiren goro, ta tsaya cikin daburcewa irin ta marasa gaskiya. Sam ba ta tsammaci zuwan su ba, don bai cika zuwa da yamma ba. Ransa ya yi matukar baci. Ya ce, dama har yanzun ki na zuwa talla, duk da irin yarjejeniyar da muka yi?

Da ma karya ne lafiyarki lau, ki ka daina zuwa Islamiyya? Zainab cikin in-ina ta ce, dama gidan wata tsohuwa kadai na kai, amma ba na zuwa talla. Ya ce, karya ki ke yi, in mutum daya za ki kaima wa, ya ya ba ki sa a leda ba?. Sai ki dora tire a kai, bayan kuma na fada miki ba bu abinda na fi tsana irin in ganki da wannan tiren a kai.

Kuma na fada na sake fada, ba na son talla. Kun dora min dari uku kullum, na yarda, kuma ina ba ku, shine za ki munafunce ni? Ta sassauta murya ta ce, ka yi hakuri, ya ce, ke malama ba wani hakuri je ki yi min sallama da innarki, don ba zan tafi in bar baya da Kura ba. Ta nufi ciki tsaki Mahamud ya yi, sannan ya ce, kalli irin gidan da za ka nemi aure. Wannan ce uwar da za ta yi wa ‘ya’yanka tarbiya? Wai kyan take birge ka ko me? Ismail ya ce, don Allah Mahamud ka bar ni in ji da abu daya. Kalli wannan wulakancin, sama da wata takwas duk sati biyu sai na ba su dubu biyu da dari daya ko dari uku. Ko da ba zan ci ba, ba zan sha ba, sai na ba su kudin nan.

Don kawai ta daina talla, ashe suna nan suna yaudara ta ne. Mahamud ya ce duk kai ka so, yaran mata ga su nan a fadin garin Katsina masu tarbiyya da ilimi, ka kau da kai a gurn su, na san dai ka san cewa, in ba ka nema wa ‘ya’ya uwa ta gari ba, zai yi wuya ka samu ‘ya’ya na gari. Isma’il ya ce, ba za ka gane ba, ina yi wa yarinyar wani mugun so ne, ba zan iya rabuwa da ita ba. Mahamud ya daga kafadunsa guda biyu . tare da fadin ruwan ka. Daidai lokacin Zainab ta sake fitowa ta ce, shigo daga soro (zaure), nan suka tsugunguna. Ita ma innar ta tsuguna. Suka gaishe ta, sannan Isma’il ya soma magana cikin fushi, inna na zone na yi wa Zainab sallama zan tafi Abuja, sai kuma na ganta da tiren goro, bayan na san mun jima da wuce maganar talla. Eh, ni na ce ta zaga da goro tunda tun shekaranjiya ya kamata ka aiko da kudin amma shiru. Isma’il ya sake shaKar takaici, cikin sauri ya ce, amma inna ko na sati biyu na tara ina badawa ko?

Ya ci gaba, gaskiya bai kamata a saba mun ka’ida ba. Inna in na bar garin sai yaya kenan, bai da ce fa a saba mun alkawari ba.

Inna ta dago ta dube shi, aikin Gwamnati ka samu a can Abujan? Ya dube ta, sannan ya sunkuyar da kai yace, a’a koyarwa ce. Ta ja tsaki sannan ta ce, ana nan dai. Ta mike ya ce, inna zan ba ta kudin ta kawo, ni dai roko na ka da ta dinga daukar tallar nan. Sannan ina hijaban da na dinka mata ne, yau na ganta da gyale?

Ta daga masa hannu, dakata kai

Isma’il, bafa ka ba da sadakin Zainab ba ne da za ka yi ta sa mani dokoki iri-iri a kan ‘ya ta, kuma ba zan gaji da fada maka cewa ba zan bayar da ‘ya ta inda za ta sha wuya ba, kamar yadda ni na sha wahalar talaucin ubansu. ‘Ya ta tana da kyau, ba zan maida ta baya ba. Ismail ya mike shi dama Mahamud tuni ya kai waje. Ranshi ful takaici, zuciyarsa tana tafasa.

Zainab da ke cikin gida kusa da soro ta leko cikin damuwa ta ce, innarmu don Allah ki daina wannan zancen, wai ke kullum in za ki yi magana sai kin sako babanmu? Isma’il ya sa hannu cikin aljihu, Zainab zo in ba ki sako, innar ta koma cikin gida. Zainab ta kalle shi, malam don Allah ka yi hakuri, ya ce, Zainab ni dai rokon da zan miki, don Allah ki rike min amana.

Ya sake yin kasa da murya, kin dai san ina sonki ko? Ta kalle shi da manyan idanunta na sani malam. To ki kula min da kanki, ya sa hannu cikin aljihu ya. ciro dubu uku, ki cire kudin sati, sai ki rike sauran. In na dawo zan saya miki waya saboda mu rinka gaisawa, sannan zan turo iyaye na. Ta ce, to ni ma zan fi son ka turo din, sannan don Allah ka yi kokarika dan yi kudi ko da ba masu yawa ba ne, saboda innarmu ta daina yi maka haka.

Ya ce, kar ki damu shi arziki na Allah ne, yana bayar da shi ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so. Muna rokon shi ya ba mu na halas, ta ce amin. Yawwa a gidanku wace ce Fatu? Ya ce, me ya faru? Ya tattara hankalinsa gurinta, sun hadu ne a gidan wani biki can kofar marusa, shine take cewa innarmu wai kar ta yadda ka aure ni, wai wuya zan sha ba ka da komai, sai dan daki daya da ka gada a zaure.

Ba ka da aiki, sai Kalallahu, Kala rasulu. Isma’il ya lunshe ido na dan lokaci, sannan ya bude tare da furzar da huci mai zafi. Ya ce, Zainab don Allah ki toshe kunnuwanki, wadannan abubuwan duk kafin in mallake ki ne. Da zarar kin zama mata ta, dole kowa ya zura mana ido. Ta ce, to shikenan amma wace ce Fatu din?. Ya ce, matar wa na ce, kar wannan ya dame ki, ni zan tafi ta ce to shikenan. Sai yaushe? Ya ce. sai dai na zo, don sai na je na ga yanayin gurin, har ya kai bakin kofa ta ce, malam don Allah kar ka manta ka samo kudin. Bai iya cewa komai ba. Ta shiga cikin gida shi kuma ya je ya samu Mahamud suka wuce.

Mahamud ya kasa yin shiru, suna tafe ya ce, Ismail don Allah dubi irin

Hmmm