Zuciyarsa cike da tunanin maganganun da suka gama tattaunawa da Innarsa. Washegari da yamma
dawowar Afrah daga makarantar Islamiyya kenan, tare suka jero da Sayyadi Habibi, hira suke cike da annashuwa da kaunar juna har zuwa kofar gidansu.
‘Anan suka tsaya, domin su yi sallama, dai-dai lokacin Musaddik ya tsaya shi da dan acaba, daga shi har wanda ya goyo shi, babu mai kyan gani, idanu jajir! “
“Ka jira ni yanzu zan fito”.
Musaddik ya gaya ma abokin tafiyar ta sa, sannan kai tsaye ya nufi cikin gidan, murya a sanyaye Afrah ta gaida shi, ya amsa yana kallonta
“Afrah ya gidan?” Ta ce “lafiya lau”.
. Malam Habib ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya shige cikin gidan.
A yayin da Malam Habib ya dawo da
• kallonsa ga Afrah, wacce duk fuskarta ta canja ta shiga damuwa, ya ce “Afrah me ya faru ki ka canja
fuska?
Ta yi dan yake ta ce “Ba komai Ya Sayyadi.”
Ya girgiza kai ya ce “Hmmm! Da komai mana, Afrah duk abinda ki ka ga ya faru da bawa, to rubutacce ne akan allon Kaddararsa, ko kadan kada ki sa damuwa akan lamaria Dan-uwanki, bai kamata ba, addu’a kawai ita ce magani, ita ce kuma za ta taimake shi.
Domin duk wanda Allah ya batar, babu wanda ya isa ya shiryar da shi, haka zalika duk wanda ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar da shi. Idan ki na tuna haka, ba za ki taba. samun damuwa ba. Da ba haka yake ba, don haka a yanzu ma wata kaddarar ce ta hau kansa, wacce sai addu’a.”
Afrah ta gyada kai cike da jin dadin nasihar malaminta, wanda hakan yana daya.
daga cikin dalilan da ya sa take matukar sonsa, ta ce, “Na ji ya Sayyadi, na gode kwarai da nasiharka, na kuma yarda da duk abinda ka fada, sai dai ina rokon kai ma ka dinga sa Dan-uwa cikin addu’arka da bakinka me cike da ambaton Allah kullum”.
Ya yi murmushi ya ce “Zan sa shi a cikin dukkan addu’oi na Afrah. Allah ya shiryemu gaba daya.” Ta amsa “Amin, na gode”
Hayaniyar da Afrah ta jiyo tana tashi daga cikin gidan, ya tilasta mata yin sallama da Malam Habib, domin ba ta son ya fahimci akwai matsala a cikin gidan, bayan sun yi sallama. Da sauri Afrah ta shige cikin gidan hankalinta a tashe.
“Na gaya miki ki yi shiru ko Na’ima ya ta ce, ina da damar da zan aura mata duk wanda na ga dama ko da dan kashin kasuwa ne, Karewar lalacewa, ke wace ce da za ki dakatar da ni?”
Cewar Malam Mahmud da yake tsaye ransa a matukar bace. Musaddij na tsugunne a gabansa. Mama Hauwa na dogare a jikin katanga, ta yi zufa ta yi kasharban saboda tsabar masifa. Afrah na shigowa ta jingina da jikin Kofar dakinta, idanunta sun cika da hawaye.
Don ta tsani damuwar da take gani a idanun mahaifinta, kamar yadda ta tsani muzantar da ta ga Musaddik ya yi a tsugunne. Mama Hauwa ta ja
tsaki ta ce,
“Duk abinda za ka fada, sai dai ka fada, amma ba zan taba nade hannu na zauna nasa maku ido ku na Kokarin nakasa rayuwar ‘yata ba, don haka Musaddik ka tattara ka tafi.
Duk abinda Kawunka ya fada, ka watsar da shi, don ba mai yiwuwa bane, zan kuma yi mummunan saba maka matukar ka masa sai ka auri *yata, babu ruwan biri da gada, don haka ina mai gargadin ka da ka dauki maganar da na ke gaya maka, don ita ce hanya me bullewa a gareka.
Ka koma can gun tsohuwar matarka da ta talautaka ta kuma gudu ta bar ka, bayan ka zama abinda ka zama. Wacce ta sa ka zabeta, ka bar Sakina, iya rashin kunya yau ina ganinta, to ba dai Na’ ima ba.
Idanun Musaddik jawur! Ya dago ya dubi
Malam Mahmud ya ce “Kawu na gode kwarai da niyyar da ka yi, amma ina ganin duk abinda Mama Hauwa ta fada gaskiya ne, ba ni da wata cancantar daya kamata ace na sami mata me cikar kamala, bayan ni ba ni da wannan cikar kamalar, gaskiya ne ko wace uwa tana bukatar farin-cikin “yarta, don haka Mama Hauwa ba ta da laifi don ta hangi rashin farin-ciki ga ‘yarta bayan ta aureni”.
Ya Kara kallonsa, bayan ya ajiye numfashi, sannan ya ci-gaba da cewa,
«Saboda haka abar
wannan maganar, ni aure ma baya gaba na, kuma ba zan boye maka ba.
Ba ni da sha awar yin aure a yanzu, domin babu yarinyar da na ke bukatar na cutar da rayuwar ta. Zamana ba wani a karkashina ya fi min kwanciyar hankali, don haka Kawu abar maganar nan kawai.”
Kalamansa sun yi matukar ba Afrah tausayi, nan da na hawayen da take kokarin mayarwa suka balle a Kumatun ta. Mama Hauwa ta dubi Malam Mahmud daya sandare a tsaye, komai ya tsaya masa cak! Don bakin-ciki da damuwa. Mama Hauwa ta ce.
“To ka ji yaro, ashe akwai sauran tunani a kansa, abin mamaki ma sai na ga yana neman ya fi Kawun nasa zurfin tunani, domin duk abinda ya fada gaskiya ne.
Don haka ya rage naka, kai ma ka’aje makaman yakin naka”. Tana gama fadan hakan, daga nan ta juya a fusace ta shige dakinta dai-dai an fara kiran sallar magariba. Malam Mahmud ya yi kasa shi ma ya durkusa a gaban Musaddik yana kallonsa, ya dagoshi gaba daya’ suka tashi tsaye, yana kallonsa ido cikin ido.Musaddik ya ce “kada ka sa ma kanka damuwa Kawu, ka bar maganan nan, komai lalacewata, ina da tabbacin ba zan rasa wacce za ta iya sona domin
Allah ba.”
Malam Mahmud ya girgiza kai ya ce. “Ina nan fa akan bakata, na riga na yi alkawarin sai na aura maka ‘yata a cikin wannan halin da ka ke ciki, kana bukatar kulawa ba daga bare ba, daga ‘Yar-uwa, don haka kada ka yi tunanin zan tashi akan maganata, yanzu ka wuce ka yi alwala, mu je _masallaci mu yi sallar magariba, sannan ka tafi gida, zan nemeka
Da sauri Afrah ta goge hawayenta ta wuce da sauri ta dauko buta guda biyu ta cikosu da ruwa ta zo ta aje, daya a gaban mahaifinta, daya a gaban yayanta. Malam Mahmud ya dago ya zuba mata ido a hankali ya ce “Sannu Afrah.” Shi ma Musaddik din kallonta kawai yake ba tare da ya ce mata komai ba, ya ja butar ya fara alawala.
Ita ma ta wuce a hankali zuwa dakinta, kasancewar tana fashin sallah, hankalinta a tashe yake tana matukar jin tsoron rayuwar duniya, musamman idan ta tuna yadda Musaddik yake.
Tana matukar nin tsoron rayuwar duniya, mussaman yadda Musaddik yake a da da yadda mata ke kokuwar kawo kansu gare shi, amma yau saboda canjin yanayi, mace daya da za ta so shi ta zauna da shi, ya rasa.
Shi kansa Musaddik bai tada bata lokaci ya tsaya ya yi tunanin rayuwarsa da makomarta ba, irin daran wannan rana, ya dade yana nemar ma kansa amsar dalilin canjawar rayuwarsa, amma har yanzu ya rasa amsa, da ba haka yake ba.
Babu kuma dalilin da zai sa ya koma haka a yanzu, shin wace irin rubutacciyar kaddara ce Allah ya rubuta masa? Sai dai duk da haka yana addu’ ar.
Allah ya ba shi ikon cinye wannan jarabawa.
Washegari tun hantsi Mama Hauwa ta kwashi jiki zuwa gidan Inna Halima da kashedin ta fita harkar ta da ta da “yarta, anan ma Inna Halima da Mama Hauwa sun kwashi ‘yan kallo, don babu wanda ya raga ma wani a tsakaninsu, kaca-kaca su ka yi cikin diban albarka.
Mama Hauwa ta bar gidan Inna Halima, tana komawa gida ta shirya Na’ ima ta ba ta kudin mota ta ce ta tafi can garinsu, wato Suleja, gidan kakanninta ta zauna can, sai ta gama da lamarin Malam Mahmud.
Sai ta tabbatar ya sauko daga maganganunsa, sannan ta dawo, ai ko nan da nan Na’ ima ta shirya ta tafi abin ta, ba tare da Malam Mahmu! ya sani ba
Har sai bayan ya dawo daga sallar Issha”i
Inna Halima ta zo ta gaya masa duk wulakanci da diban albarkar da Mama Hauwa ta je ta yi mata har gida. Kwarai da gaske ran Malam Mahmud idan ya yi dubu ya baci, a fusace ya kira Mama Hauwa ta fito, tana yamutse-yamutse ta dogare a tsaye ta ce
“Ga-ni menene?”
Malam Mahmud ya dubeta rai bace ya ce
“Wai ke Hauwa me ki ke mufi da ni ne, meye matsalarki, shin Na’ ima ‘yar ki ce ke kadai, don me za ki tayar mana da hankali, kin hanamu sakat! Don kawai nati nufin Kulla alheri…?”
Ta yi karaf, ta katse shi ta ce “Ka yi niyyar kulla sharri dai, kuma ba dai da ‘Yata ba, banda maugunta, ai ba Na’ima bace kadai ‘yarka da ba ta yi aure ba.
Don me ba za ka canja ba, sai ita, don ba ka kaunarta.” Ya jinjina kai ya ce “Na ji, to meye ya kai ki gidan Halima ki ka yi mata wulakanci?
Wannan abin ai tsakanina da ke ne, don me za ki sa
‘yar-uwata a ciki?”
“Saboda na san duk kulle-Kullen ta ne wannan, saboda ba ta kaunata, shi ya sa take bakin-ciki da kwanciyar hankali na, don haka ka gargadeta ta fita harkata da ‘ya’yana”. Inna Halima ta dubeta ya ce.
“Kin ci sa’a a gaban yaya muke, duk abinda za ki fada, ba zan iya maida miki a gabansa ba, don
yana da daraja da kima a guna.” Ta tabe baki
«Wannan ke ki ka sani kuma.’
Malam Mahmud ya daka mata tsawa ya ce
“Ke Hauwa ba ruwanki da Halima kuma idan ki ka
Kara taka gidanta, ki ka yi mata abinda bai kamata ba, sai kin yi mamaki na, don ki sani, ba tsoranki na ke ji ba, kin kusa kai ni bango, ki fita a cikin lamarina”
Ya bude baki ya kwala ma Na’ima kira.
Mama Hauwa ta dube shi ta ce “*Wace Na’ imar? Na riga na turata inda ya kamata, ba kuma za ta dawo ba har sai ka janye wannan mummunar maganar.”
Malam Mahmud ya fiddo da idanu waje ya ce
“Ina ki ka turata ba tare da sanina ko izinina ba?” Tace “Ba dole bane ka sani, izininka kuwa dama ban nema ba, don na san ba zan samu ba, shi ya sa na yi gaban kaina”
Malam Mahmud ya ce “To shi kenan, na ba ki daga wannan daran zuwa gobe, ki tabbatar Na’ima ta dawo gidan nan, ko kuma ki tattara ki bi-ta”. Inna Halima ta ce “A yaya kada ayi haka, ka fita harkar Hauwa, don na lura tana jin dadin cima mutane mutunci, ka bar ta, duniya ma ai makaranta ce
Mama Hauwa ta ce “Kada ma ya bar ni, ba kuma za ta dawo ba, ni ma ba inda zan je, zama daram! Idan kuma neman kwanciyar hankali ku ke, to ku janye batun auren nan, shine kawai maslaha a tsakanin mu.” Daga nan ta juya fuuu! Ta shige dakinta gami da rufe kofa.
Inna Halima ta juyo tana kallonsa ta ce “Yaya ina ganin maganar Na’ima a bar ta, saboda abinda muke kwadayi, ba za mu samu ba, hakuri da juriyar zama da Musaddik ba za ta iya ba, koda mun tursasa an yi, to ba za mu samu hadin kanta ba. balle ta ba mu gudunmuwar dawo da rayuwarsa kan hanya, tunda ba ta so, mahaifiyarta ma ba ta so.
Domin tashin hankalin Hauwa ma kadai, ya isa ya hana su zaman lafiya da kwanciyar hankali, koda ita ma Na’imar tana so.
Balle bisa dukkan alamu ya nuna tana tare da mahaifiyarta, tunda har suka iya shirya ta gudu.
Allah ya ga tunanin mu, ya kuma ga niyyar mu.
Allah ya ba mu ladan niyya, shi kuma Musaddik Allah ya kawo sanadiyyar shiryuwarsa, ko da ba ta dalilin auren ba.
Malam Mahmud ya saki ajiyar zuciya ya ce
“Kai babu wata jarabta ga da namiji irin rashin sa’ ar mata ta-gari, shi ya sa ba zan taba mantawa da marigayiya ba, wacce ta so-ni, ta yi min biyayya har me rabawa ta rabamu, na yi kwadayin ace ita ce ta cika min gida na da “ya ya kafin rasuwarta, amma duk da haka na san ta bar min daya tamkar da dubu Afrah”.Inna Halima ta gyada kai ta ce “Haka ne,
Allah dai ya jikanta”
Ya ture hularsa keya ya ce “Amin, kuma ina nan akan bakana na hada Musaddik da ‘yata aure.”
“Amma ta yaya, ina za mu iya da tashin hankalin Hauwa?”• Ya ce “Ba komai, akwai wata
mafitar da na fara hangowa, ki tashi ki tafi gida dare ya yi sosai, zuwa jibi idan na gama tunani zan nemeki”
Ta jinjina kai, ta ce “To Allah ya kai mu, ya kuma kara maka hakuri da juriya akan zama da Hauwa”. Ya ce “Amin Halima.
Daga nan ta tashi
ta yi masa sallama ta leka dakin Afrah wacce duk’ abinda ke faruwa tana zaune akan katifarta tana jinsu, nan ma sallama ta yi da Afrah.
Sannan ta wuce zuwa gida, zuciyarta cike da tsanar Mama Hauwa da jin haushinta. Yau alhamis ba makarantar Islamiyya, tun safe Afrah ta kwashe wankin mahaifinta ta wankesu tsaf! Ta shanya, sannan ta shiga dakinsa ta gyara tsaf!
Kamar yadda ta saba duka ranar alhamis, haka zalika duk wani aikin gida, babu wanda Mama Hauwa ba ta, ba ta ba, duk kuma ta yi ta gama, har zuwa yanzu da ta hada wutar guga ta goge kayan mahaifinta.
Ta kammala kenan, ta kwasa za ta kai masa daki, ya dawo, ya shigo yana kallonta dauke da kaya ya ce “Afrah, yanzu bayan wanki har guga ki ka sami damar yi min, bayan aikin da na fita na bar ki da shi a gaba?” Ta yi murmushi ta ce “Eh Baba, ai har ma na gama, sannu da zuwa” Ya ce Yauwa, Allah ya yi miki albarka,
Allah ya ba ki -kuma masu jinkanki,
masu taimakonki gadda ki ke taimakona”. Ta ce “Amin Baba.” Daga can nesa inda Mama Hauwa ke zaune ta saki tsaki ta ce.
“Ayi dai mu gani.” Ya yi mata wani irin kallo, sannan ya shige dakinsa ba tare da ya tanka mata ba. Ita ma Afrah ta bi bayansa daukè da kayan a hannunta.
Tana shiga dakin ta tarar da Malam Mahmud zaune akan kujerar da ita kadai ce a dakin, ya yi
tagumi
hannu biyu, fuskarsa dauke da matsananciyar damuwa, bayan ta aje kayan ne, ta juyo ta dora masa ido, zuciyarta ta dagule ta shiga damuwa, domin ganin mahaifinta cikin damuwa.
Tana matukar so ta zauna su tattauna damuwarsa, amma ba ta da yadda za ta yi, domin bai nemi hakan daga gareta ba, ta juya a hankali za ta fita, har ta kai kofar dakin, muryar mahaifinta ta dakatar da ita daga fita, ta hanyar kiran sunanta, ta amsa da sauri, lokaci daya ta dawo ta durkusa a gabansa ta ce “Ga-ni Baba:
Malam Mahmud ya dawo da kallonsa gareta, ya fara magana. “Afrah ina cikin wani hali na tsaka mai wuya, na daukar ma kaina alkawarin da na ke neman na gaza a kansa, na shiga wani hali da banda wani zabi da ya wuce na roke ki a matsayinki na wacce na ke tunanin tana da maganin matsalata.”
“Ya dan numfasa, sannan ya ci-gaba da cewa «Musaddik Dan-uwanki ne, idan rayuwarsa ta gyaru, na yi imanin za ki zama daya daga cikin masu jin dadi, ko kadan ba ni da nufin Kara ma rayuwarki damuwa, saboda maraicin ki da kuma irin hannun rikon da ki ka taso. Hakan ya sa na ke miki kwadayin samun miji na-gari wanda zai taimakeki, wanda zai rikeki da mutunci, wanda kuma za ki sami dukkan gata daga gare shi.
Shi ya sa ban yi tunanin hadaki aure da
Musaddik ba, don na san duk abinda na lissafa, ba zaki taba samu daga Musaddik ba, shi ya sa na yi tunanin hada shi da ‘Yar-uwarki Na’ ima.
Ya numfasa gami da gyara zamansa, ya kurama Afrah ido, wacce take tsugunne, banda faduwar gaba ba abinda take yi, ya ci-gaba da cewa.
“Ba sai na gaya miki matsalar da na ke fuskanta daga Hauwa ba.
Tunda na furta maganar hada auran nasu, domin na san kin ji, kin kuma ga irin cin mutuncin da Hauwa ke min, karshe ma ta dauke Na’ ima ta boyeta, ban san inda ta kai ta ba.
Don haka Afrah ina rokonki da hannaye na biyu, ki taimakeni ki share min hawaye, ki sadaukar da farin-cikinki saboda farin-ciki na, ki yi min biyayya kamar yadda ki ka saba, ki amince ki auri
Musaddik don Allah.
Da sauri Afrah ta dakatar da shi “Don Allah
Baba ka daina rokona, wace ce ni da har sai ka rokeni, don na yi maka biyayya, duk irin so da kauna da ka nuna min ace sai ka rokeni don kawai za ka aura min Dan-uwana.
Har kullum ina fatan Allah ya kawo ranar da za ka nemi wani abu daga gareni, domin ba ni da abinda zan saka maka ko na biyaka daga irin rikon da ka yi min.
Ta yi kokarin maida hawayen daya cika mata ido, sannan ta ci-gaba da cewa “Saboda da haka zan sadaukar da da farin-ciki na, kamar yadda ka bukata, zan auri Yaya Musaddik, zan kula da shi tare da kokarin sanya shi a hanya madaidaiciya,
Allah kuma ya shirya shi.”
Son ‘Afrah tare da tausayinta ya Kara kama Malam. Mahmud, a yayin da farin-ciki ya cika zuciyarsa, amma daya kalli cikin idanun Afrah, sai ya ji wani bakin-ciki ya kama shi, domin a yadda Afrah ta’ so ta boye damuwarta, to ba za ta taba boye ma Malam Mahmud ba, hakika bai hango son Musaddik ko son auransa a kwayar idanunta ba.
Abinda ya hango daya ne, shine tsantsar biyayya da kaunar faranta ransa, ya nisa gami da jinjina kansa sannan ya ce.
“Ki yi hakuri Afrah, ba haka na so rayuwarki ta tafi ba. Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki
‘ya’ ya masu jinkanki, Allah kuma ya albarkaci duk abinda zai shigo rayuwarki. Allah ya juya wannan al’amari ya kasance alheri a gareki, da mu baki daya, domin Allah ya ga kyakkyawar niyyar mu akan wannan auran, na gode, na gode”
‘Afrah ta danyi murmushi ta ce “Baba ka na sa ni jin nauyi, idan ka na min godiya, don Allah ka daina min godiya
». “Allah ya yi miki albarka Afrah,
tashi ki tafi.” A hankali ta mike ta fita, gabanta na matsanancin faduwa.
Tana shiga dakinta ta fada kan katifarta, kuka take riris! Komai ya kwance mata, meke shirin faruwa da ita? Ko a mafarki ba ta taba kwatanta
Hmmm