Ta dubi wayar cikin bacin rai tana ganin sai tayi kasa da kai kamar munafuka
Kinyi sallar ne? Cikin tsawa taji maganar mini tayi shiru tace bakijini bane? Tq girgiza kai tare da fadin banyi ba
Hajiya ta rufeta da blfada ban gane bakiyi ba
Anya ma kinayin sallar kuwa ta kalli hajia cikin sauri tare da fadin inayi mana hajiya tace karya ne kalli kalli agogonki karfe nawa ne yanzu? Da har zuwa yanzu bakiyi sallar magriba ba bare ishai inna lura musulunci baya burgeki islamiya kin daina duk wani abu da islma yazo dashi komai na addini kin mayar dashi kauyanci ke ga yar boko ko? Mimi dai bata dago kai ba
Hajiyq tace nasan in ko za,a kasheki yanzu daqar idan zaki iya kawo cikakkiyar fatiha
Kin zauna kinata danne dannen waya in baki sani bane gara ma ki sani kina cutar kanki ne rayuwar da kika daukar ma kanki bamai dorewa bace don haka bata dace dake ba ki tashi kiyi sallar yanzunnan,sakarya marar hankalil Simi-simi
Mimi ta tashi ta nufi bandaki, Hajiya tace tunda ‘abin naki ya soma nisa haka, wayewar ta ki har ta kai ki da gudun salla, to nan gidan zaiki kare hutunki. Kidaukaratu gurin malamin yaran nan, sannan ki koyi salla tun da bani da tabbacin kinayi Bari baban naku ya shigo, ta juyata fita da wayar a hannunta. Mimi daga cikin ban daki, kuka wiwi ta dinga yi ita kam ba zata iya zama har ta gama hutu cikin wannan takurar ba a silent Hajiya ta saka wayar Mimi taja durowa ta jefa. Mimi tana kuka ta yi sallar, su Hussaina, suna kallonta, ta idar ta fada kan gado taci gaba da kuka, Don ita amshe, mata wayar da Hajiya tayi ya fi bata mata rai fiye da fadan, don jinta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayar
Misalin shabiyu saura-Alhaji ya shigo yake ta neman layin yar lelan tashi, amma saita yi ta ruri har ta yanke ba a daga ba. Hajiya ta shiga ta sameshi tana cikin shirin barci ya kalle ta da wayansa a hannu, Mimi fa? Ta kalle shi, in Kira maka ita ne? Ya lura cikin gatse ta yi masa maganar, don haka sai ya ce, a’a dama inji ko ta yi barci ne, saboda ina ta kiran
*wayarta ba ta dauka ba. Cikin in haushi Hajiya ta ce oho. Na zata ita ma nan za mu kwana tare don kar wani abu ya cinye ta. Ya mike tare da kama hannunta,
Sauda kin canza sani na ba haka ki ke ba.
Yanzu kin zama mai saurin fushi. Ta kalli fuskarsa, kai da ‘yarka ku ka canza ni. Ya ja hannunta, to zo mu zauna in ji mai zan samu. Ya basar da wancan zancen. Ita ma sai ta biye masa da cewa, duk abinda ka ke so. Ya tallabe fuskarta kin san mene ne Sauda? Ta girgiza kai kullum na kalli faskarki sai natuna ranar da muka fara haduwa, ranar da idanu na suka fara kallon fuskarki. Rana mai tarihi a guri na. Hajiya:
Sauda ta ce, ikon Allah ni kan da a ce wannan kalmar karatu ce, da sai in ce, tuni na haddace ta, tun muna da Kananan shekaru.Ya yi ‘yar dariya ina jin dadin tuna
baya, wani lokacin sai in ji tamkar in mai do lokaci. Ta lumshe ido, ai Alhaji kuruciya cike take da shirme, in ta wuce sai ayi ta kewarta, ni kaina ina son tuna baya,
rayuwa stana da sauri, duk da haka in muna tare, sai in rika jin kaina tamkar’ yar kasa da shekara ishirin. Yayi dariya, a haka ni ke kallon ki Sauda, kullum na kance, lokaci na sauri. Ta kwantar da kanta a kafadarsa. Allah ya kara mana tsawon rai da rayuwa
mai amfani. A kunne ya rada mata amin. soyaya ba ta tsufa, sai dai masoya su tsufa,
Allah ka yi mana mai kyau.
Katfe bakwai Alhaji Bashir ya nata Shiri cikin sauri, Hajiya Sauda tana taimaka masa gurin saka kaya, rokonsa take yi ya dan sa wani abinci a bakinsa, ta ce, don kai na sa a yi kunun gyada da kosai, saboda nasan kana so. Ya kalle ta, ta na saka masa links a hannun riga ya ce, ki yi hakuri mata ta,, na yi alkawarin zan gana da wani mutum ne, wanda na fi wata guda ina neman damar ganinsa.
Ta ce, duk da haka ka karya zai fi. Yace sai na dawo, domin inna samu damar, da ni ke nema a gare shi, kasuwanci na zai ninka, in ko haka ta samu ya ya ki ka gani? Ta ce, umm! kai dai da ma kullum, saurin ka bai wuce kasuwanci, a kasuwanci inane ba a sanka ba, duk fadin Afirka ina ne sunanka bai kai ba? Wane irin kudi, ne ba kamalaka ba, kullum ciikin samun riba kake.Ta mika masa hularsa, me ya kamata ka nema kuma Alhaji? Yanzu bayan Aljanna? Murmushi, ya yi, ba tare da, ya bata amsar duk tambayoyin da ta jero masa ba. Ta ci gaba, ni dai ba zan gaji da ba ka shawarar, cewa, kamata ya yi zuwa yanzu ka yi murabus ka bar Abba da Mukhtar su jagoranci kasuwancinka. Ya ce, nikuma fa? Ta ce, kazo mu zauna mu huta, mu karasa rayuwarmu, yan. Kananan уaranmu su shaku da kai. Ya saki dariya, tare da cewa, Sauda kenan. Inki ka fadi wata magana sai ki tuna mini tadinmu na farko da ke. Ta ce, au kana nufin, wannan maganar, ma, dana fada shirme ce? Ya ce,kusan haka kina cewa inbarmasu. Abba ragamar
Hmmm