turare ya ce, ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko ya ya ne dai daga can zan wuce Malumfashi. In duba su Binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba. Sannan inda lokaci zan shiga Masari can ma na jima ban je ba. Kin ga sai na kwana kenan, gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo. Hajiya, Sauda ta ce, Allah ya tsare sai ka dawo din, amma batun tafiya da Mimi ne nake tunani a kai. Ya kalle ta, kamar ya ya? Ta ce, sai ka dawo dai Allah ya tsare, ya dan tabe baki amin.
Suna fitowa Falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi, ya amsa da daidai, sannan ya kalli Usaina, Mimi fa? Ta ce, tana kwance Dady,: ya: ce, shikenan za mu yi waya. Hajiya ta raka shi har mota, wannan ba sabon abu bane, haka ta saba tun suna da kuruciya.
Falon ya kacame, yaran suna ta karin kumallo, sai hayaniyarsu da Karar kofuna.
Mimi ta fito sanye cikin riga da wando masu dan kauri na barci. Sauri take yi, tare da fatan Allah Ya sa Dad dinta bai fita ba, don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba. Ta iso gurin Hajiya, fuskar ta babu annuri ta ce, ina kwana Hajiya? ba tare da ta dube ta ba ta ce, lafiya lau. Mimi ta yi tsaye shiru, tana son yin magana amma tana tsoro.
Hajiya ta dago ta dube ta, ga kayan shayi can a kan dining, na san ba kya shan kunu, ta ce, tam! Ehemm! Da ma zan gaida Dady ne, yana ciki ne? Hajiya ta ce, a’a ya tafi Malumfashi sai gobe zai dawo. Mimi ta zaro idanu ya ya Dady zai min haka ya tafi ya bar ni, ta kalli Hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce, Hajiya don Allah ina waya ta? Hajiya ta ce, sai za ku tafi sannan zan ba ki, don ni ba za ki yi mani wannan chatin din naki ba a nan, sannan ki karya ki je ki yi wanka, in malamin su Hussai ya zo za ki bi su, ki je daukar karatu a gurinsa. Ina sa ran ma Alhaji ba zai tafi da ke ba, nan zai bar ki sai kin san Addininki sannan za ki tafi, ko da za ki cinye hutun ki a nan. Cikin sauri Mimi ta koma daki cikin kuka sai da ta yi me isarta sannan ta shiga wanka, a fili kuwa fadi take, Allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa Katsinan nan.
Dolenta ta saka atamfa,riga da siket, a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wa su Usaina sai an yi mata. Ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi. Amma ko ta halin kaka ba za ta zauna cikin irin wannan takurar ba. Can ta hango wayar Hasana kan durowar ta. Cikin sauri ta tashi ta dauko, layin Dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri, cikin kuka ta soma Magana, bayan ya daga dad ka ga Hajiya ta dauke min waya ta, kuma wai ba zan tafi ba, ni-dai Dad wallahi ba zan zauna ba. Ya ce, yi shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma, yanzu me kike so? Ta ce, Phone di na, ya ce, shikenan zan ce ta ba ki, kin ci abinci? Ta ce, a’a, ya ce, to ki je ki ci zan sa ta ba ki wayarki kin ji?.
Ta na zaune a kan Dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam ba ta da hanzari, tana kallon lokacin da Hussaina ta kawo ma Hajiya waya ta ce, Dady ya kira, ta daga. Ta na jin lokacin da Hajiyar take cewa, tsaya ka ji Alhaji, sai kuma tayi shiru, da alama ya katse ta ne, ya hana ta Magana, don ta ga Hajiya ta yi shiru, amma ranta a bace yake. Sai kuma ta ce to Alhaji na ji zan ba ta, amma ba na son chatin din nan da ta ke yi. Mimi ta yi murna, a ranta ta ce Dady na kenan, ta nufi daki da murna.
Alhaji ya ce, kar ki damu Sauda,
‘yarki mai kamun kai ce. Ita da kowa ya shaida ko saurayi ba ta da shi. Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita, ya ba ta kulawa fiye da wanda take samu a guri na.
Hajiya ta ce,
umm! Allah ya taimaka, ai ni da na zaci ma ba za ka iya auradda ita ba (cikin gatse ta yi maganar). Ya ce, kash kin ji ki da wata magana kuma Sauda, in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta. Ina ma ki ka ga an tada , haka? Ke dai ki yi mana addu’a, ta ce, Allah ya taimaka, kun gama ganawar ne? Ya ce, eh, yanzu haka muna hanyar Malumfashi sai na dawo ta ce, Allah ya tsare, ka dawo lafiya, ya ce, Amin, ga dai uwata nan amana na ba ki, katse wayar ya yi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.
Ga zaton Mimi tana aje wayar Alhaji za ta zo ta ba ta tata, amma sai ta ji shiru. Ta sake fitowa falo nufin ta kila Hajiya ta ganta ta tuna, idan ta manta ne, amma sai ta ga Hajiya ta ci gaba da lamuranta. Yaran duk suka yi wanka suka fito, Husna da Hasina suka shiga falo da gudu suna cewa, ga malam nan ya zo. Ga mamakin Mimi sai ta ga duk yaran sun rude, wasu sun dauko Alkur’anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu. A ranta ta ce niko bari in ga wanene malamin, kai har na ji na tsane shi tun kafin in ganshi. A zaton ta nan zai shigo sai ta ga Abdullahi da Umar da Aminu da Sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai Zainab da Hasana da Hussaina suka fita.
Hasina da Husna kuma sun dukufa suna ta karbarma juna hadda, kafin a zo kansu. Mimi ta tabe baki tare da cewa, wahalar da kai, su ba su dade ba suka dawo
su. Su Hasana sun mike kenan Hajiya ta fito daga daki ta ce, ke ma tashi ki je, ta nuna
Mimi. Ta hada rai, sai dai ba ta da damar yin musu, don ba bu Alhajin da zai tare mata.
Hasana ta ce, yaya Mimi sai kin sako Hijabi fa, ta banka mata harara, ban dauko ba. Ina wasa da ke ne? In ki ka kara yi min magana
sai na mare ki.
Suka yi shiru suka wuce, ta warware
dan kwalin kayanta ta yafa, tana biye da su har falon baki, kafin su shiga sai da suka
kara gyara hijabansu sannan suka yi
sallama suka shiga. Ta tsaya tana mamaki wai malami ne sukeyima wannan bare-baren, malamin ma wai na Islamiyya, ita
malami ko na boko ba ta dauke shi wani abu ba, face bawan ta mai ci a karkashin su.
Bare wannan da ba za ta iya bambamce shi
da maigadi ko mai sharan gidansu, kosawa
ma ta yi ta shiga ta gani wane gaja ne?
Ta jingina da kofar, sannan ta kai
kallonta gurin shi, yana zaune kan kujeran zaman mutum daya sanye yake da jallabiya mai ruwan madara mai dogon hannu da maballi a hannu, sannan tare da kwala a wuyarta. Ga wani dan ado da zare mai ruwan kasa da aka yi a wuyar da hannun rigar, ba ta kai can kasa ba, irin dai shiga ta sunna, hular kanshi baka ce irin wanda ake kira minista. Ya na rike da Alkur’ani yana bude inda suke. Su kuma su Hussaina suna zaune a kasa kan kafet a gabanshi duk suna rike da Alkur’aninsu, Mimi ta tabe baki tare da harde hannuwanta a Kirjinta, tana kare masu kallo.
A ranta ta ce, tabdi, ai ba a yi mutumin da zai zo gidan ubanta sannan ta zauna a kasa yana kan kujera ba. Malam Ismail ya dago ya kalli bakin kofa da kyawawan idanunsa, duhun mutum ya gani, ya sa shi kallon gurin ya kalli Mimi da ke tsaye ta watso masa wani kallo da ba zai iya fassarashi ba. Ya mayar da kanshi ga abinda ya ke yi. Su Hussaina suka ci gaba da kawo masa hadda yana yi, masu ‘yan gyare-gyare, suka kamalla, sannan suka soma sauran littafai.
Ta shiga ta zauna tare da daukan rimote ta kunna TV, ya dago ya dube ta, tamkar zai yi Magana, amma sai ya fasa. Ya san da gadara ta zo, bayan su Hussaina sun kamalla, sai Hussaina ta ce, yaya ki zo mun gama, ta kalle su cikin harara, ku fita mana, suka fita suka je suka sanar da Hajiya ko mai. Ita kam suna fita ta mike tana tafiyar nan tata, ta isa kan kujerar gefen shi ta zauna.Ya dago ya dube ta, sannan ya mike tare da tattara littafansa, ya nufi fita, a bakin kofa suka ci karo da Hajiya za ta shigo, ya dakata ta Kara so suka gaisa, ta ce, har ka mata karatun? Ya ce, wace kenan? Ta ce, Mimi, bangan ta ba ai, Hajiya ta ce, a’a ta shigo cikin falon. Ta ce ga ta nan fa, ya dawo cikin falon, ok! wannan ce? Na ganta amma ban zaci karatu za a yi mata ba. Ita kuma ba ta fada min ba. Hajiya ta ce, ai ba za ta fada maka ba, saboda ba son karatun ta ke yi ba. Ka soma mata daga Fatiha don ba nazaton ta iya, don Allah Malam Isma’il kar ka yi mata da sauki. Isma’il ya ce, ba komai Hajiya, amma ta saka Hijabi ta ce, to ba komai bari in sa su Hasana su kawo mata, in ta ki yika dake ta ko ka kira ni.
Hajiya ta fita shi kuma ya kai duban shi gare ta, Mimi ta cika ta yi tam. Ya na zama Hasana tana shigowa da sallama, shine ya amsa, ta ce, yaya ga shi, harara ta watso mata, sannan ta ki amsa, Hasana ta aje a hannun kujerar da take zaune ta fita.
Ya kalle ta, malama ki saka hijabinki mana, cikin sauri ta dago kai ta dube shi duban tsana mai tsanani, domin ba a taba ci mata mutunci kamar yau ba a gaban kaskantacce irin wannan. Sannan ba a taba rena mata wayo ba kamar yadda shi din ya yi mata, ya ganta sarai, amma ya ce, bai ganta ba. Wannan abin ya yi mata ciwo fiye da abinda Hajiya ta yi mata. Ta harare shi sama da kasa sannan ta ja tsaki, malam Isma’il ba ya daukar reni, sabi da haka sai
ya hada rai tare da rufe Alkur’anin shi.
Ta ce, kai waye sunan da ake kiranka? Ina son ka sani na wuce ka rena min wayo kuma kai ba ka isa ka koya min karatu ba, sannan ya daga hannu tare da katse ta da cewa ke. Ba ki da ladabi ne?
Gaskiya ba tarbiyyar nan gidan ba ce, domin yaran gidan nan mazansu da matansu na yi shedar su gurin ladabi game da sanin darajar mutane, ke ma ina yi maki nasiha ki canza. Kuma ina son ki sani karatun nan in kin yi kin ma kanki ne ba ni ba, don haka ka da Allah ya sa ki yi, ya mike ya fita abinsa.
Yana jiyo tsakinta gami da cewa, talakan banza kanaci a karkashin mahaifi na sannan ka nuna ni da yatsa, to bari ka gani lokacin barin ka aiki ya yi. Har ya tafi ya dawo ke ma dukiyar da ki ke takama ba taki ba ce, ta mahaifin ki ce, sannan ina son ki sani ba ke ki ka dauke ni aiki ba bare ki sallame ni. Ba kuma maula nake zuwa yi a gidanku ba, ina son ki san wannan. Kafin’ta sake yin wata magana ya wuce ya barta cikin takaici, lallai wannan sai na yi maganin sa, shine mutum na farko a tun tasowar ta da ya tada fada mata abinda ya ke so, kuma tana son ya zama na karshe, takaicinta ma talaka ne shi, ba wani isashshe ba.
Daf da zai fita daga cikin gidan, Abdulkarim ya yi masa sallama, ya tsaya suka gaisa ta hanyar yin musabaha. Ya ce, ai ina ta sallama ba ka ji ba, ya ce, na ga fuskar ka ba walwala ko yaran ne suka hada maka zafi? Malam Isma’il ya ce, ko kusa ai yaran gidan nan ba su da matsala sam, sai dai wata bakuwa da Hajiya ta ce a koya ma ta karatu, amma ba ‘yar ta ba ce ko?
Abdulkarim ya sake matsowa kusa da shi, sannan yace, ba dai Mimi ba? Isma’il ya ce, kamar haka na ji an kira ta, gaskiya saboda ita zan iya daina zuwa gidan nan in har za ta dinga zuwa karatu. Abdulkarim ya ce, kai ma ta nuna maka halinta kenan, don Allah ka yi hakuri zan fada ma Hajiya, kuma ina zaton ma gobe za ta tafi, Isma’il ya ce, shikenan ba damuwa.
Suka yi sallama ya fita, Abdulkarim ya nufi ciki kai tsaye zuwa falon Hajiya, duk suna falon, Mimi kuma tana kujerar Dining, ranta cinkushe, ya kalli Hajiya, ke ki ka tura Mimi ta yi karatu gurin Isma’il, Hajiya ta ce, ta yi masa rashin kunya ko?
Abdulkarim ya ce, ta yi masa kenan tunda ya ce, matsawar za ta dinga zuwa gurinsa daukar karatu to kuwa zai daina koyar da yaran gidan nan.
Hajiya cikin fushi mai tsanani ta rufe
Mimi da fada, sannan ta ce, in ki ka sake na samu labarin kin yi sanadiyar koran malamin nan sai kin sha mamakin abinda zan yi miki, sai kin yi zaton ban sanki ba ma, sam bare ki tuna cewa nice na haife ki.
Don malamin nan ya fi min ke amfani, Mimi ta sa kuka, Hajiya ta ci gaba, tunda na lura karatun ne ba ki so, to sai kin yi shi, bari Alhaji ya dawo nan zai barki sai na yi maganin abinda ke damun ki a cikin kanki.
Mimi ta fada daki ta na kuka. Hajiya ta kira layin Malam Ismail tana ba shi hakuri a kan abinda Mimi ta yi masa, ya ce, ba bu komai ai yarinya ce.
Washegari misalin shadaya da rabi
Alhaji ya dawo. Ya iso cike tam, ya ce, a ba Mimi wayanta, amma ba a ba ta ba. Sai dai
yadda’ ya samu Hajiya rai bace kamar ma
har kuka ta yi, sai kuma ya juya da
tambayar shi kanta yana son jin abinda ya
same ta ciki da damuwa mai tsanani irin wanda bai taba gani a fuskarta ba, ta ce, ko
ka ji ba za ka magance mun abinda ke
damuna ba. Ya tausasa murya haba Sauda.
Ya ya za ki ce haka? Daga lokacin da muka
zama ma’aurata shekara talatin da bakwai
zuwa yanzu kin taba samun kanki cikin
matsala ban taimaka miki ba? Ta dube shi,
wannan karon na san ba za ka,,,,ya daga
mata hannu dole ta dakata ya ce, amsa mini kawai.
Ta ce, ban ce ba ka taimakamin ba
Alhaji, amma wannan karon na san zai yi
wuya, ya kama hannunta. Matsalar kudi ce? Ta ce, a’a ni da ‘yar gwal dinka ce Mimi,
ta kalli fuskarsa ya yi dan murmushi, ki ce abun me sauki ne, me ya faru?. Ta ce, ina son dai ka bar ta a nan saboda sam ba ta san
komai kan addininta na Musulunci ba.
Sallah har da kuka ta yi, saboda Allah a ce kamar Mimi shekararta nawa? amma ba ta yin sallah, malamin yaran nan Ismal’il don ance ta je ya koya mata karatu kurum, ta je ta yi masa rashin mutumci.
Sannan ta toge tana firan ka dawo ta ce ka kore shi. To ba zan yarda ba, ita kanta ma dole ta zauna ya koya mata karatu, don ba za ta koma ba ta yi ta zama cikin jahilci.
Ya yi shiru yana nazari. Ya san dai komai za a yi ba zai bar Mimi a gidan nan ba. Ta ce, ai dama na san zai yi wuya ka bar Mimi nan, to ina son tunatar da kai iyaye abin tambaya ne game da kiwon da aka ba su na ‘ya’ya a ranar gobe kiyama, ta mike ta fita abinta.
Ya fito falo. Hussaina tana yin Home work ya ce, ke ce da Mimi ta same ni a daki na. Itama cikin kuka wiwi ta cewa Dady,
•don Allah ka kori malamin nan wallahi na tsane shi. Tunda nake ba a tada yi mini abinda ya yi mini ba. Ina son in nuna mi shi talaka ba komai bane a guri na. Alhaji ya ce, uwata yi shiru ki daina kuka. Zauna, ta zauna a kan kujera shi kuma yana bakin gado ya ce, Mimi ina son ki bar batun koran
Hmmmm