MUSABBABI CHAPTER 1 BY HAJ HABIBA
Fatima Muhammed wacce akafi sani da afrah a sakamakon sunan kakarta ta wajen uba da taci nagartacciyar yarinya ce kyakkyawa hafaffiyar garin minna Mai cikar kamala haquri juriya sune manyan halayenta na gari abin koyi sai kuma tsantsar ilmin islama da Allah ya wadata ta dashi domin tun tasowanta take kokari. Koyon addini har zuwa yanzu data mallaki hankalin kanta ta zama cikakkiyar mace domin tuni ta kammala karatunta na sakandire tana zaman jiran sakamako ne a yanzu idan akwai abinda ya ragi afrah a rayuwa to bazai wuce maraici ba domin ta dandana dacin maraici tun tana yar shekaru biyu kuma itace kadai yar da mahaifiyarta ta haifa tare da mahaifinta mal mahmud bayan rasuwar mahaifiyarta ne rikonta ya koma hannun matar babanta mama hauwa wacce a matsayinta na uwargidan mal mahmud tana da yayyi guda biyar biyu maza mansir wanda shi ne na farko, a yanzu ma’aikaci ne a hukumar wutar lantarki, wato (NEPA). Yana rike da babban mukami, ya yi aure har da ‘Yarsa daya, sai Kabir, shi kuma ma’aik…