CANJIN RAYUWA CHAPTER 8 BY HALIMA A K/MASHI

CANJIN RAYUWA CHAPTER 8 BY HALIMA A K/MASHI koshi, ya sha ruwa ya koshi. Daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba daga Katsina zuwa Abuja. Can da ya farka ya kalli agogo, sai ya ga lokacin sallah ya Karato, nan da nan ya tashi ya yi alwala, ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a gurin. Hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira, ya yi masu sallama, suka amsa. Ya ce, Hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci ya yi, Hamisu ya ce, ba a fa kiran sallah a masallacin nan, sai dai kawai kowa ya yi alwalarsa ya shiga ya yi sallah. Isma’il ya ce, saboda me? Hamisu ya ce, ni dai haka na tarar suna yi, to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar, ni da maigadi da mai shara. Ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba, ya fi yi a cikin gida. Yaron sa namiji daya, ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. Isma’il ya ce, ko ku uku za ku iya jam’i, don haka ni kam zan kira sallah. Isma’il ya shiga ya ga da abin magana da komai,…