CANJIN RAYUWA CHAPTER 8 BY HALIMA A K/MASHI
koshi, ya sha ruwa ya koshi. Daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba daga Katsina zuwa Abuja.
Can da ya farka ya kalli agogo, sai ya ga lokacin sallah ya Karato, nan da nan ya tashi ya yi alwala, ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a gurin.
Hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira, ya yi masu sallama, suka amsa. Ya ce, Hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci ya yi, Hamisu ya ce, ba a fa kiran sallah a masallacin nan, sai dai kawai kowa ya yi alwalarsa ya shiga ya yi sallah. Isma’il ya ce, saboda me? Hamisu ya ce, ni dai haka na tarar suna yi, to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar, ni da maigadi da mai shara.
Ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba, ya fi yi a cikin gida.
Yaron sa namiji daya, ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. Isma’il ya ce, ko ku uku za ku iya jam’i, don haka ni kam zan kira sallah.
Isma’il ya shiga ya ga da abin magana da komai, yana kwada kiran sallah daidai lokacin motar Alhaji Bashir tana kunno kai.
Ko da direban ya tsaya bai fito ba, sai da ya ji karshen kiran sallar, muryar tamkar balaraben Saudiyya. Maimakon ya shiga gida sai ya samu kansa da nufar masallaci, gurin da aka tanada don alwalla, nan ya je ya tattara hannun rigarsa ya soma alwalla. Su Hamisu suka tsaya suna kallonsa, nan dai Isma’il ya ja su Sallah, Hamisu ya yi masu Ladanci, sai dai Alhaji shi kadai ya tsaya a sahunsa,
Suna idarwa suka fito, Ismail ya gaida Alhaji, ya nuna masa jin dadinsa da sallar da ya kira har suka yi jam’i. Isma’il ya ce, Alhaji zan yi wata magana, amma in na bata maka rai ka yi hakuri, amma hakki ne a kaina in sanar da kai. Bai kamata ka tsaya ba a sahu ba, duk da cewa mu din masu nema a Karkashin ka ne, amma gurin Allah ba bu bambamci, musamman gurin sallah.
Sahu dole ne, na san Alhaji ya sani. Tuni kawai na yi masa, Alhaji ya ce, na gode ba komai, sannan ya nufi cikin gida. Sai karfe tara na dare, Kuku ya sake kawo masu abinci, da ya karba sai ya fito, sannan ya samu Hamisu shi ma yana cin na sa, ya aje ya ce, me zai hana mu rinka ci tare? Hamisu ya ce, ba damuwa Bisimillah.
Suna ci Hamisu ya ce, na ji mamaki da na ga kana magana da maigidan nan, wai me ka ce masa ne? Ismail ya ce, wata magana wanda bai dace in fito na fada ba, a takaice kuskure ne na yi masa tuni, Hamisu ya ce tabdi, gaskiya ka yi sa’a, ai maigidan namu mafadaci ne na gaske. Wanda bai son a shiga huruminsa, kuma yana da wata yarinya mara mutunci, wanda kowa ke tsoron ta, hatta matan gidan.
Sai dai gaskiya yana biyan kudi da tsoka, shi ya sa ka ga na jure, ni ne direban yaran gidan, don haka na fi kowa wulakanta. Isma’il ya ce, na san ta, kuma ni malaminta ne, na zo in koya mata karatun addini. Ne Hamisu ya dago ya kalle shi, sannan ya yi dan murmushi, lallai ina mai ba ka shawara, ka nemo duk wani hakuri da kau da kai, ka Kara a kan wanda ka ke da shi. Ismail ya yi ‘yar dariya, sannan ya ce, ta taba yi maka? Ya ce, to da wanda ta raina ma iri na?.
Ban san iya sau nawa ta zuba min miyau a fuska ba. Banda kalaman cin mutunci. Ismail ya ce, kai kuma sai ka tsaya kana kallonta? Hamisu ya ce, ya ya zan yi, tunda ina so, dubu talatin yake biya na a wata, ba ko’ina zan samu haka ba.
Isma’il ya ce, sannu da kokari, amma ni kam ba zan dauki wulakancin nan ba. Sun jima yana ba shi labari, kafin suka yi sallama.
Haka da asubahi ya kwada kiran sallar farko, Mimi wacce lokacin ta yi sallama da Kalil dinta wanda suke chatin tun misalin taran dare, ta bude idanunta tana jin sabon lamari a gidansu. Ta tashi ta sauko daga kan gado, ta kunna wutar dakin na ta, sannan ta nufi windo, ta yaye labule tana kallon masallacin, wanda dama saitin windon na ta yake. Tabbas masallacin nan ne, to wane ne wannan da karfin hali? Ita tunda ta taso ba ta tada jin an kira sallah a masallacin nan ba. Ta koma ta kwanta ta saki tsaki, za ta ga mai wannan kokarin na hana mutane barci. Ta fara barci ta ji an sake kiran sallar, aka shiga masallaci aka yi sallah, ba ita ta samu barci ba sai da aka idar da sallah.
Don haka ba ta farka ba sai shabiyu,. ta yi mika tare da hamma, sannan ta silalo kafarta kasa kan lallausar kafet. Tamkar sarauniya ta ke jan taku har zuwa bandakinta, wanda aka tsara shi da kalar pink, kalar da take bala’in so, bandakin da yafi na kowa tsaruwa a gidan, hatta mahaifinta. Ta shiga bahonta, bayan ta cika shi da ruwan dumi, sama da awa daya ta dauka a wanka, sannan ta fito. Gurin shafarta daya ne da kayan sawanta, ba ta cika yin Kyale-kyale a fuska ba, Hoda kadai sai jambaki bayan mai, amma tsadarsu ta ishi talaka jari.
Ta saka wando baki irin mai kama jikin nan, da riga ja, ta ja dogon gashinta ta kama shi da bakin ribbon. Sannan ta soma wanka da turaruka, ta nufi gadonta ta dauki wayarta tana dubawa, miss call kusan goma
Dadin ta, da na Dear Khalil, sannan Hajiya
guda biyu. Bakin gadonta zaune tana kiran layin
dadinta, ya daga tare da cewa uwata ya ya
aka yi? Cikin shagwada da muryarta din
nan wanda ke fid da sauti a hankali cikin salo ta ce, Dad, na ga miss call din ka ne fa?
Ya ce, uwata har na fita baki tashi ba,
lafiyarki kalau ko? Ta ce, eh Dad, emm,
yawwa dad wane ne jiya cikin dare ya hana ni barci da kiran sallah?. Ya ce, malaminki
ne, gabanta ya yi bala’in faduwa ta ce, Dad
shine da zuwansa zai canza mana tsarin
gidanmu? Mene ne nufinsa da haka? Ya ce, babu komai Mimi, kin san malamai da son Masallaci, yau nima na samu yin sallar asuba a kan lokaci, sannan makwabtanmu sun shigo mun yi sallar tare da su. Tace, kash Dad, yanzu gidanmu gurin tara
mutane kenan?. Ya ce, kar ki damu musuluncin
kenan, ina fatan za ki sauko domin daukar
karatu gurin malamin na ki. Ku yi amfani da falon baki, ko falo na kike so? Ta ce, a’a Dad ya tsaya can falon baki, ba falon ka ba, da wanna bakauyiyar kafar ta shi. Ya ce, shikenan tunda Na’ima tana gida ita ma ta soma karatun, in su Ahmad sun dawo da yamma sai ya yi masu, ta ce, shikenan Dad, bari in kira Hajiya na ga ta kirani, ya ce, ok ni ma yanzu muka gama waya, ki ce ina gaida ta. Cikin fargaba ta kira mahaifiyarta, Hajiya ta daga cikin lallausar murya ta yi sallama, Mimi ta amsa, sannan ta gaida ta, Hajiya Sauda ta amsa tare da cewa, ina ki ka bar waya? Ta ce, ina barci yanzu na yi wanka sai na ga miss call dinki. Hajiya ta ce, na zaci kin fita gurin karatu ne? ta ce, Hajiya ban san ma ya zo ba sai yanzu Dad ke fada mun.
In na yi Break zan yi yanzun, Hajiya ta ce, ki maida hankali saboda ki san abinda za ki bauta ma Allah mahaliccin ki. Suna yin sallama kiran Kalil ya shigo sai da ya yi daf da tsinkewa sannan ta daga, wannan wani ra’ayinta ne. Ta ce, hello Dear ya aka yi? Ya ce, ba komai ina son in ji muryar ki ne? Yanzu ki ka tashi? Ta ce, eh, ya ya hutu?
Ya ce, ga shi muna yi, don Allah ina son in zo gidanku wannan karon, ina jin tsoron kamar zan rasa ki, kar ka damu Dear na fada maka don juna aka yi mu, ina jin haka a jiki na.
Ya ce, Lovely har yanzu ban yi mafarkin haka ba ina ganin sai zancen ya je gurin manyanmu. Ta yi ‘yar dariya, ka san fa Dad naka ba zai yarda ka yi aure yanzu ba, ni kuma in Dad dina ya ganka guri na. kila yace, zai min aure, ka ga sai matsala ta samu.
Ya ce, na fahimce ki, ba na son na sha wahala a aurenki kamar yadda na sha kafin na samu amincewar soyayarki na garu.
Ta yi ‘yar dariya cikin salon maganarta ta ce, Dear ka manta da haka, bari na karya, ya ce, to shikenan sai in mun hadu online ta ce, tam. Cikin tafiyarta tamkar mai tausayin kasa take saukowa daga benenta, wanda ita kadai ce a sama ta ke mallakin katon falo da dakuna uku. Daya dakin barcinta daya kayan karatun ta, tun daga Computer zuwa kasa, dayan kuwa rufe yake duk da cewa shima da komai a cikinsa.
Momi Nafisa tana zaune tana kallon
Fim a cikin tafkeken TV da ke manne a bangon falon. Ta waiwayo, kin fito Mimi?
Ta kalle ta, na fito Momi an tashi lafiya? Ta ce, lafiya lau, Dadinku ya yi ta kiran ki ba ki fitoba, ta yatsi na fuska, mai kiran sallar cikin daren nan ne ya hana ni barci. Momi ta ce, ai malaminki ne, na ga Dad dinki ya yaba da hakan. Ta ce, na lura da haka a wayar da muka yi dazun. Ta isa gurin karin ta hada shayi tana sha, sannan ta dubi mahaifiyar ta su Na’ima fa? Ta ce, tana dakinta, ta dauki wayarta da ke kusa da ita, ta soma kiran layin Na’ima, tana dagawa Mimi ta ce, sis zo mana, Na’ima ta fito cikin riga mai gajeran hannu da wandon Jins damamme, kanta ita ma babu dankwali, ta kama gashinta da ribbon Blue.
Ta ce, sis gani, Mimi ta daga fararen idanuwanta ta kalli Na’ima cikin harshen turanci su ka fi yin magana. Ta ce, ki je gurin Folina a kicin ki gani ko ta gasa kifin, ta ce, sis mu je snacks store mana mu ci, Mimi ta harare ta, ki yi abinda na sa ki mana, ta daga hannu, alamun ban hakuri ta rinka fadin sorry sis.
Folina ta zo, ta shirya wa Mimi gasashen kifi tare da gasashen biredi, tana gamawa ta kalli Na’ima ina son a kira mini Malamin da ya zo jiya, amma ban san yaya zan yi ba, don ba za ki je ba, amma ki duba in kin ga direban ku, ko wani dai ya kira shi, ta ce, tam sis.
Lokacin da Hamisu ya sanar da
Isma’il cewa ya je ciki ana neman sa, sai ya ce, sai mun yi Sallah tukuna, don yanzu zan kira. Bayan sun idar sannan ya ce, ma Hamisu ya yi masa jagora zuwa cikin gidan.
Barandar kofar falon, nan suka danna ‘yar wata danja, jim kadan aka bude, Na’ima ce ta kalle su irin kallon da wasu ya’yan masu da shi suke yi wa masu yi masu hidima. Ta ce, wane ne Malamin? Hamisu ya nuna Isma’il wanda ke tsaye sanye cikin yadi mara nauyi, hularsa ta dace da yadin wandonsa a dage irin na Ahalil sunna.
Ta kalle shi sama da kasa, sannan ta ce, ina zuwa. Kamar minti biyu ta dawo ta ce, Sis ta ce, ka shigo, ya shiga dankareren falo wanda tsarin sa ya wuce duk tananin Isma’il ga sanyi AC ko ta ina. Ta waiwayo ta ganshi tsaye, ka bi ni mana, ya ci gaba da binta cikin zuciyar shi yana addu’ar Allah ya tsare shi daga sharrin da ke cikin gidan, alherin da ke ciki Allah ya sada shi da shi.
Wata Kofa suka shigo inda suka iske wani falon madaidaici, shima ya tsaru ta ce, ka jira ta a nan.
Kusan minti biyar, sannan Mimi ta shigo falon ba tare da sallama ba, rashin sallama yana kona ran Ismail, don haka bai ko kalle ta ba. Ta zauna tana kallon fuskar wayarta, ta fi minti biyar chatin take yi da Kalil dinta, labarin Karfin halin Malamin take ba Kalil. Ta ce, ni da zai ci a gurin Ubana, amma ni yake jira in ji da shi, Kalil ya ce, kin san talaka da girman kai. Ta dago ido ta kalli Isma’il wanda ya bude Alkur’ani yana karantawa a zuciyarsa. Ta ce, hamm mai neman taimako baya girman kai.
Ya dago ya kalle ta, kafin in ce komai zan soma yi miki nasiha, da saka hijabi don suturta jikin ki. Sannan ki koyi sallama yayin da ki ka zo gurin mutane, abu na uku, ba neman taimako na zo ba, ke na zo in taimaka ma wa, don haka yanzu sai ki dauko littafi mu fara daga huruful ija’iyya.
Ta ce, ba ka isa ka ce za ka taimake ni ba, don ba ka da komai, kuma ba zanyi sallamar ba, ba zan rufe jikin ba. In ba ka sani ba, bari in fada maka, na sa a kawo ka nan gidan ne saboda in tozarta ka, in nuna maka kai kaskantacce ne. Ya ce, don na miki wane laifi? Ta ce, kai ne mutum na farko da na tada yin sa-in-sa da shi. Wanda ya taba kallon cikin ido na ya fada min Magana, kuma ina son ka zama na karshe, wannan shine laifin ka. Isma’il ya ce, yanzu dai za ki yi karatun ko a’a? Ta ce, na ce ba zanyi ba, ya mike tare da kwashe takardunsa. Ta ce, ban sallame ka ba, ya yi tafiyarsa ya bar ta zaune. Mimi ta bi shi da kallo cikin mamaki, shi wannan da me yake takama, har da ba ya jin shakka ta, kamar yadda sauran jama’a su ke ji?. Ya san wace ce ni kuwa? Ya san wane ne ubana?
Ba wani ba ne uban Mimi fa ce
•Alhaji Bashir, dan asalin Masari ne,
Karamar hukumar Kafur Jihar Katsina.
Mahaifiyarsa ‘yar Dabai ce, su shabiyu mahaifiyarsu ta haifa, amma yanzun saura su biyar, bakwai sun rasu, Mahaifiyarsu ta rasu lokacin ya kammala Sakandire, yayyin shi mata uku ne, sai namiji daya da ke bin shi. Rakiya da Basira a Malumfashi suke aure, Saratu kuma tana cikin Kafur, Malam Aliyu mahaifinsu ya sake yin aure. Inda matar ta kasance mai son kanta game da son zuciyarta. Wannan ya sa ya bar Masari, ya soma shiga cikin garin Katsina don neman abin kanshi, maimakon noma da suke taya mahaifinsu, shi da Shafi’u kaninsa.
Ya yi sana’o’i kala-kala, tun daga kan kwandastan mota har zuwa dako, daga bisani ya soma bin wasu abokansa guda biyu da suka kama shago daya su uku, da Isa Mani da Kabiru Na’alla suna harkan
dabbobi. Tun yana karba yana saidawa ya
cire ribarsa, har ya zo ya samu jarin kansa.
Sannu a hankali sukayi zangonsu na
dabbobi, lokaci bayan lokaci yana zuwa
Masari ziyartar danginsa da Mahaifinsa,
kuma yana yi masu alheri. Kaninsa Shaffu har yayi aure matarsa ta haihu, don haka Mahaifinsa da
yayyansa kullun burinsu yayi aure. Wani
zuwa da yayi har mahaifinsa yana cewa, ga
‘ya’yan ‘yan’uwansa ya zo ya auri daya daga
cikinsu, sai basheer din ya ce, ya yi hakuri,
shi ba ya sha’awar auren zumunta, amma
duk lokacin da ya ga wanda ta yi masa, to
zai yi aure, amma a yanzu neman kudinsa
ya sa a gaba.
Ranar wata Juma’a Isa Mani ya tare
shi yana sauri za shi masallaci ya ce masa,
Bashir ga wadansu shanu can za’a saida su a
rugar Fulani nan Mashi. Bashir ya ce, har
Mashi? Gaskiya da kyar zan je, Isa mani ya
Mce, za ka samu alheri mutumi na, don jiya na dawo tafiya, ka sani da na saye su, amma ka
daure mu je in ka dawo masallaci. Hardon
rugar ne ke son zuwa aikin Hajji, shine zai
yi cikon kudi. Bashir ya ce, ni dai masallaci
na nufa ga shi ina jinjina zuwa Mashin nan, Isa ya ce, mu je dai Masallacin nan tare ma kawai, da zanje na karfe biyu ne, in ya so
daga can sai mu wuce. A masallaci suka
hadu da Kabiru Na’allah, inda suka nufi
Mashi dukkan su.
Sun je rugar Fulani, inda suka shiga
garken shanu don duba shanu. Ya nuna
masu, sannan aka shiga ciniki, an daidaita
kuma Bashir yayi alwashin kawo kudi
gobe, saboda kudi suna banki. Suna cikin
sallama ne idon Bashir suka kai kan wasu
‘yan kwailoli guda biyu, sun dawo daga tallar nono, dayar ya kure da ido, ‘yar similmila ta yi masa kyau, sai da ta bace ma
idanunsa, sannan ya bar kallonta. Har Isa
Mani ya gane, bayan sun bar gurin ya ce,
Bashir kana ta kallon ‘yar mutane saboda me? Kar dai ka ce min son wata ka ke yi daga cikinsu? Bashir ya ce laifi ne yin
Hmmmm