CANJIN RAYUWA CHAPTER 6 BY HALIMA A K/MASH
kace haka ka ban mamaki, kai da na sani dakakke mara tsoro na ga ko a nan a Islamiyya da muke koyarwa duk yaran masu da shi din ne, amma shakkar ka suke yi. Isma’il ya ce, ba za ka gane ba, ita fa wannan ya rinyar ina zaton irin tabararrun nan ne ko da ban sani ba dai, amma na ga alamar kamar uban bai son a takura mata, ga ta da alamun ta tsani talaka ba ta dauke shi wani abu ba, ni kuma duk sun san hali na, ba na son raini. Shi ya sa ba na raina mutane, dalili kenan da na ke ta tunanin ya ya koyarwar tamu za ta kasance? Mahamud ya ce, shawarata a nan kawai ka aje duk wani waswasi kai dai ka amshi kudinka ka cika burinka. Ka tuna da karatun da muke son yi, kai ko yau Jami’ar Madina suka kira ka za ka bukaci kudi. Ga yarinyar nan da ka dauki son duniya ka dora mata, Zainaba, kar ka manta da abinda mahaifiyarta ta ce, sadakin ‘yarta dubu dari, akwatin ‘yarta me shida ne, Ismail yace, da na tuna wadannan abubuwan ni ke jin cewa ya kamata in jajirce in je, yanzu dai malam nake son gani in ne…