CANJIN RAYUWA CHAPTER 2 BY HALIMA A K/MASH

mata gaskiya ko dai ba ke ce ki ka haife ta : ba? Ya aje cokalin hannunshi, na rasa me take miki, ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba. Sai ta zo hutu irin haka, amma samba kya ko yin kewarta. Hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba, wanda ta hada masa, a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce, halin ta kawai za ta canza, in dai tana son soyayyata. Yanzu baka kalli shigar da ta yi ba? Tun daga Abuja ka sako ta gaba har Katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje, kayan jikinta duk sun dame ta, wai ita dole ta waye. Ya kalli Mimi sannan ya kalli Sauda, da dan murmushi, ina laifin kwalliyarta, ni ban ga aibun ta ba, haka ‘yan mata matasa irin ta ke yi. Ya kalli Mimi, ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?. Tsaki Hajiya ta yi sannan ta nufi dakinta. Sai lokacin Mimi ta samu damar yin mita, kaga ko Dad, sai da na ce ka barni can in gama hutu na, ka ce a’a sai na zo, ni daman na san Hajiya ba za ta taba so naba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta, shiga ta fa, mene ne aibunta? Ya kalle t…