CANJIN RAYUWA CHAPTER 1 BY HALIMA A K/MASH

Hajiya Sauda tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, ‘yar kimanin shekaru arba’in da bakwai zuwa da takwas, amma ba tayi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu. In an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya, kyakyawa ce mai cikar mutunci. Wayarta da ke gefe samfurin Nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar. Kamar yadda ta za ta, Maigidan ne, domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba. Sallama ya yi, ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce, Hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. Cikin taushin murya ta ce, shine ba ka fada mini ba tun safe? Cikin lallashi ya ce, na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce, da ka nemi ta su Usaina, kila Network ne domin waya ta kunne ta ke, ya dan murmusa, ba mamaki zan iso da yunwa fa, don haka a tarbe ni, ta yi ‘yar dariya, wace irin yunwa? Shi ma ya yi ‘yar dariyarsu ta manya, duk wata yunwa ta, da ita zan zo, ta ce, kar ka damu Allah ya kawo ka lafiya, ya ce, …