Hajiya Sauda tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, ‘yar kimanin shekaru arba’in da bakwai zuwa da takwas, amma ba tayi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu. In an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya, kyakyawa ce mai cikar mutunci. Wayarta da ke gefe samfurin

Nokia tayi ruri, cikin

natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar.

Kamar yadda ta za ta, Maigidan ne, domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba.

Sallama ya yi, ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce, Hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. Cikin taushin murya ta ce, shine ba ka fada mini ba tun safe? Cikin lallashi ya ce, na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce, da ka nemi ta su Usaina, kila Network ne domin waya ta kunne ta ke, ya dan murmusa, ba mamaki zan iso da yunwa fa, don haka a tarbe ni, ta yi ‘yar dariya, wace irin yunwa? Shi ma ya yi ‘yar dariyarsu ta

manya, duk wata yunwa ta, da ita zan zo, ta ce, kar ka damu Allah ya kawo ka lafiya, ya ce, Amin.

Ki sa ayi wa uwata farfesun kifi tare za mu zo, take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta, ta ce, Alhaji don Allah kar ka zo min da Mimi. Ya ce, saboda me? Ta ce, ka san komai, Alhaji Mimi in ta zo gidan nan sai ta addabi kowa, ba yaran gidan ba, ba ma’aikatan gidan ba. Ta sani, na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta canza halin ta ba, ba na bukatar ta. Ya yi shiru domin ranshi ya baci, kusan minti daya duk sun yi shiru.

Sannan ya ce, Sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda ki ke yi wa Mimi ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta Mimi. Allah! In ji Hajiya Saudatu, ta sake tausasa muryarta, ban san-lokacin da za ka fahimce ni ba Alhaji, amma ka yi hakuri. In dai don mu za ka zo, to ka zo kai daya zan fi son haka. Cikin dan zafi ya ce, Sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum, ki fada ma duk ‘yan gidan wanda bai son ganin ta zai iya barin gidan har sai ta tafi, sannan ya kashe wayarsa.

Ta dan ciji lebe tare da lumshe ido cikin takaici, ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so. A fili ta ce ni kan ba na son zaman Mimi garin nan, na tsani halin ta, a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda take so. Ta mike tana nunke sallaya.

Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure, sannan ta yi tsaki, Abdulkarim ya ce, lafiya Hajiya? Alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da Mimi.

Abdulkarim ya ja tsaki, don jin an ambaci sunan Mimi, sannan ya ce, ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu gaisa kawai Hajiya in sabi jaka ta, ai a wannan satin ba ni da darasi kamar yau, sai na sake dawo wa.

Hajiya Sauda ta yi ‘yar dariya tare da fadin haba Abdul, ka taho tun daga Zariya har Katsina sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda Mimi? Ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba. Dauki jakarka kawai ka wuce sashin ku, ka watsa ruwa. Bari in sa mutuniyarka Tabawa ta kawo maka abinci na san yanzu sun gama na rana. Ya ce, ai ni ba na son rainin wayonta ne Hajiya, a ce yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo, ba dama ka yi magana. Ni kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta.

Hajiya ta ce, a’a kar ka soma, ka san halin Alhaji. Ina fatan ba ka manta da yadda yayanka Abbas suka kwashe ba, in ka tuna zungure mata kai kurum ya yi, amma ta inda Alhaji yake shiga ba ta nan yake fita ba. Tsawon wata shida ya ki amsa gaisuwar Abbas. Sai da bikin shi sannan Alhai ya sauko, shi ma sai da abokan Abban suka taro abokan Alhajin aka hadu ana ta ba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan ‘yarsa.

Abdulkarim ya yi ajiyar zuciya cikin takaici, sannan ya ce, ban manta ba. Hajiya shi ya sa na ce, zan koma, tace ka hakura tunda ka zo, iya ka dai kar ka shiga harkanta. Ya ce, gaskiya Alhaji ba ya yi mana adalci, a ce cikin ‘ya’yansa mu ishirin da biyu, amma ya zabi daya rak ya ce, ita ce

Star don kawai tana da sunan mahaifiyarsa. Allah Hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa, amma ko shawara da ita sai abinda ta ce a Family

Hajiya Sauda ta ce, ku yi ta hakuri, dadin abin ita dai ta mace ce, duk abinta ai dole ta yi aure ko? Abdulkarim ya ce, tabdi, wannan ‘yar jin kan? Ya zauna a kujera, sannan ya ce, Allah ya sa ta saurari wani.

Hajiya ta ce, ayya Abdulkarim dole ta yi aure. Ba dai mace ba ce? Shi kanshi zai so a bar masa ita a gabansa? Abdul’ ya yi ‘yar dariya, sannan ya ce, kila ya ce mijin ya dinga biyo ta nan gidansa. Hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi’yar dariya, ta ce ba su lokaci kawai. Ni dai ina ta fada ma Allah, ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta, bare wadanda ba nice na haife su ba. Abdul ya mike tare da saba jakarsa, bari ni kan na isa dakinmu, Hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin.

Hajiya Sauda ta tafi gefen babban kicin, ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari, tun daga waje za ka san cewa mamallakin gidan ya tara abin duniya ba kadan ba. Ta isa babban kicin din, mata uku ta samu a ciki suna ta aiki, suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa, ta amsa da sannunku da aiki cikin girmamawa, ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce, Baba Tabawa me aka yi da rana?.

Tsohuwar ta ce, Taliya ce ke kan layi da rana, da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar danyen kubewa, ga taliyar nan ma yanzu na sauke.

Hajiya ta ce to, a canza na daren a yi mana dan waken garin dawa sannan a yi shi da wuri. Baba Tabawa ta ce, Maigida yana nan shigowa kenan? Hajiya ta ce eh, suna tafe, suka hada baki gurin cewa, Allah ya kawo su lafiya. Hajiya ta ce amin. Sannan ta kalli Jummai muna da kifin ruwa ko?

Jummai ta ce eh, Hajiya ta ce yawwa ki dafa kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafarnuwa.

Sannan ki kula kar ya dagargaje na

Mimi ne. Dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da Mimi ne za a zo? Jummai ta ce, Allah ya fishe ni yin kuskure. Hajiya ta ce kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in ta zo, ku kawar da kai duk abinda za ta yi kun ji ko? Cikin karyayyar murya suka ce to shikenan, Tabawa ta kalli Jummai kar ki sa mata tafannuwa, wancan zuwan da ta yi Maman Sani daga sa tafannuwa shikenan ya zama sanadin korarta. Jummai ta ce, zan kula insha Allah.

Hajiya ta kalli Ramma ta ce, da safe me muke da shi? Ramma ta ce, Shayi ne, Hajiya ta ce, to a canza zuwa Kosai da kunun gyada, ta ce to Hajiya. Tabawa ta ce,

•akwai Kafar sa fa ko wannan karon ba za’ayi ma Alhaji ba? Hajiya ta ce, a dora zan

dinga zuwa ina dubawa, na zata babu ne, sannan Tabawa mutumin ki fa ya zo Abdul, a kai masa abinci, ina magajiya? Tabawa ta ce Allah sarki Abdul ne ya zo zan kai masa ma da kaina maigida sukutum. Hajiya ta juya tana dariya tare da fadin kowa ya duba abinda babu sai ya zo ya fada min.

Da kanta ta nufi wajen me wankinsu yana ta gugar kayan yara, ta ce masa ka je ka fadawa mai gadi da mai kúla da fulawa cewa Mimi za ta zo anjima, sannan Ya’u direba ya same ni a falo. Ta sakè cewa, Danladi na fada maku ne don ku kiyaye ba na son ana korar min ku, Danladi ya ce, zan fada masu. Danladi ya nufi gurin mai gadi, ya turo mata direba ya sanar da su zuwan Mimi nan, suka dinga tattauna rashin mutuncin Mimi, ya same ta tana zuba nono a cikin Firiji. Domin tasan al’adan shi ta shan furan dare.

Direba ya yi sallama cikin girmamawa, Hajiya ta amsa, ya gaida ta sannan ya ce, ga ni Hajiya ta ce, malam Ya’u da ma ina son sanar da kai ne, yau Mimi za ta zo na san ba ka santa ba. Amma ka samu. labarinta? Cikin in’ina ya ce eh na ji gurin su Danladi. Ta ce to ka tafi filin Jirgi’ tun misalin hudu da rabi, gara ka jira su, domin da jiran da suka yi ne wancan direban namu shine sanadiyyar korar shi da Mimi ta sa Alhaji ya yi. Ya ce zan kiyaye insha Allah.

Tun hudu Ya’u ya nufi filin Jirgin, jiran zai fi masa sauki da haduwa da fushin Mimi. Biyar da minti talatin suka iso, Alhaji Bashir Aliyu Masari ya fito daga cikin Jirgi, Mimi tana biye da shi, sanye cikin riga da wando masu kalar pink sun dame ta tsam. Sai after diress baka mai sheki, sannan ta gaba an ratsa pink hakanan rigar ba ta kai kasa ba. Don haka ana ganin wandonta, dan siririn mayafinta ba shi da girma shima pink bai rufe dogon gashinta ba.

Kafarta sanye cikin takalmi shima

• pink dinne, da ratsin baki marar tudu mai igiyoyi, purse din hannunta da wayoyin ta kirar Nokia duk kalar pink ne. Can saman goshinta za ka iya kallon wani katon gilashi irin wanda wayayyun ‘yan mata masu jin kansu su ke sakawa. Da gudu Ya’u ya nufe su domin duk da bai san Mimi ba ya san maigidan na su. Cikin ladabi ya yi masu sannu da zuwa, sannan ya amshi jakar hannun Alhaji, Alhaji ne kawai ya amsa,

Mimi kan ko kallon shi ba ta yi ba.

Ya bude kofofin motar sannan ya sa jakar Alhaji a kujerar gaba, bayan sun fito daga filin yana hawa titi zai raraka da gudu, Alhaji ya ce tafi a natsuwa Mimi ba ta son gudu, Ya’u ya ce, to ranka ya dade.

Shi kanshi mai gadi a waje ya tsaya yana jiranzuwan su, yana hangosu da gudu ya nufi ciki ya wangale get din, kamar yanda Mimi ke so, don ba ta son jira. Ko da direba ya tsaya ya bude masu sannan ya cire jakar yabi bayan su Mimi ta kalli gidan sannan ta ce,

Dad gidan nan yana son

fenti ya yi datti, ya yi ‘yan kalle-kalle, sannan ya ce, na lura da haka za a sabun ta shi da fenti. Direban ya ajiye jakar a kujera sannan ya kalli Alhaji, na barku lafiya ya fita. Alhaji ya so ma kiran Hajiyata-Hajiyata, ta fito, dankwali a hannun ta, domin lokacin ta gama saka kayan, ta yi adonta cikin super kalar Blue da ratsin yellow sai kamshin turare take yi.

Ta kalli mijinta, sannu da zuwa

Alhaji, ya ce, yawwa, Sauda ta dubi Mimi wadda tunda suka shigo falon ta natsu, saboda duk iya-shegenta tana tsoron uwarta, ta san Hajiya sam ba ta daukar reni.

Ta dago ido cikin fargaba ta kalli mahaifiyarta Sauda ta ce, sannu Hajiya, Hajiya Sauda ta amsa yawwa, ya Mominku Nafisa da kuma sauran Kannenku? Ta ce, kowa lafiya, Hajiya ta ce, masha Allah, ta dauki hular Alhaji da jakarsa da kuma malun-malun dinsa ta nufi dakinsa tana fadin za a hada ruwan wanka ko? A’a rabona da abinci tun safe shima ba wani abinci na ci mai nauyi ba coffee ne, ta karasa dakin ta aje kayan hannunta ta fito tana fadin mu je Dining.

Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna, ya kalli Mimi zauna mana uwata. Ya mayar da kallon shi ga Hajiya Sauda, an yi mata farfesun kifin? Hajiya ta kalli Mimi cikin daurewan fuska, sannan ta ce, an yi,

Mimi ta turo baki tare da hada rai.

•Hajiya tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow, ta janyo wani plate din tana zuba masa farfesun kafar sa, sannan ta tura gabansa tana fadin Alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba? Ya kalle ta cikin yar zolaya ya ce, duk ganin ki ne ya mantar da ni. Ko da dai na’ san zuwa yanzu suna Islamiyya ko? Ta ce eh, yau kam ma da murna suka fita, don na gaya masu cewa kana tafe, ya ce, ga shi ban riko masu tsaraba ba. Amma bari in sa direba ya sayo masu, ta ce, a’a zai fi kyau ka fita da su don yaran nan ba sa samun kulawarka, kamar fa sam ba su shaku da kai ba.

Ya kalli Mimi wacce ta jibga tagumi, ya ce, zan gani ko da lokacin, kin san fa ko acan ba samun zama na ke yi ba. Shiru ta yi don ta san kome za ta ce ba fahimtar ta zai yi ba, ta jima tana yi mishi nacin cewa, ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki. Ko su da suke matansa ba sa ganin shi a kan lokaci, sai ya yi wata ko sati uku in kuma ya zo kwana biyu yake yi, nan gurin ta ya kwana daya yaje Malumfashi wajen Hajiya Binta ya kwana daya.

Tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar Mimi menene uwata? Na ga duk kin bata ranki? Ki ci kifinki mamana. Ya kalli Hajiya Sauda ina kifinta? Hajiya ta nuna kular da cokali, ga kular kifin nan gabanta? Ta dauka mana ko a baki zan ba ta? Mimi ta sake tura baki tare da kallon mahaifiyarta, ni na koshi, Hajiya Sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki abin, yanzu ki ce ba za ki ci ba, saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan na san ba ki so zuwa ba, ko Katsinar ce ba ki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare miki can.

Sauda! Alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni ba na son abinda ki ke yi, a ce ke da ‘yarki ta cikinki amma ba ki kaunarta?. Hajiya ta ce, ba kaunarta bane ba na yi, halinta ne ba na so. Kuma in har ta ga mun zauna inuwa daya da ita to ta tabbatar ta canza halinta, in ko ba ta canza ba to sai dai ta nemi wata war ko da yake tana da ita.

Ya tausasa murya ai ba maganar fada bane, amma gaskiya ba zan iya kallo kina mata irin wadannan kalaman ba, kullum tana yi mini korafin ba ki sonta, ita in fada

Hmmm