TSINTACCIYA CHAPTER 8 BY NIMCY LUV TSINTACCIYA CHAPTER 8 BY NIMCY LUV Www.bankinhausanovels.com.ng Yana zuwa bakin ƙofar ya tsaya yana jiran fitowar Akeem, gently ya buɗe ƙofar ya fito idanunsa a lumshe ga yadda jijiyoyin kansa suke a mimmiƙewa fuskarsa tayi jajirrr da ita alamun har yanzu yana cikin ɓacin rai. Ganin Akeem cikin wannan halin wanda bai taɓa ganinsa a ciki ba yay saurin faɗin “Dr” idanuna da suke a Lumshe ya buɗe tare da sauke ganinsa akan fuskar Abbu,wani irin bugawa zuciyar Abbu tayi saboda wani irin jaaa da idanun Akeem sukai har wani ruwa suke fitarwa. Muryar sa na rawa yace “what… what happened to Akeem?” Lumshe idanunsa yay kana ya buɗe kamar wanda baya son yin magana ya buɗe baki da ƙyar yace “noting” yana faɗin hakan ya nufi shiga cikin gidan da idanu kawai Abbu ya bisa yana mamakin baƙar zuciya irinta Akeem. Girgiza kai kawai yay tare da nufar cikin gidan kai tsaye part ɗinsa ya nufa, Akeem na shiga Amani na ganinsa ta miƙe tana faɗin “Abbie na” bai ko kalli inda take ba sai hannu daya sanya yama …