TSINTACCIYA CHAPTER 8 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 8 BY NIMCY LUV

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yana zuwa bakin ƙofar ya tsaya yana jiran fitowar Akeem, gently ya buɗe ƙofar ya fito idanunsa a lumshe ga yadda jijiyoyin kansa suke a mimmiƙewa fuskarsa tayi jajirrr da ita alamun har yanzu yana cikin ɓacin rai.

Ganin Akeem cikin wannan halin wanda bai taÉ“a ganinsa a ciki ba yay saurin faÉ—in “Dr” idanuna da suke a Lumshe ya buÉ—e tare da sauke ganinsa akan fuskar Abbu,wani irin bugawa zuciyar Abbu tayi saboda wani irin jaaa da idanun Akeem sukai har wani ruwa suke fitarwa. Muryar sa na rawa yace “what… what happened to Akeem?” Lumshe idanunsa yay kana ya buÉ—e kamar wanda baya son yin magana ya buÉ—e baki da Æ™yar yace “noting” yana faÉ—in hakan ya nufi shiga cikin gidan da idanu kawai Abbu ya bisa yana mamakin baÆ™ar zuciya irinta Akeem. Girgiza kai kawai yay tare da nufar cikin gidan kai tsaye part É—insa ya nufa, Akeem na shiga Amani na ganinsa ta miÆ™e tana faÉ—in “Abbie na” bai ko kalli inda take ba sai hannu daya sanya yama ture ta kai tsaye upstairs ya nufa yana dafe kansa yana jin yadda Amani ke kuka amma yau banza da ita, Didi dake zaune tayi saurin faÉ—in “Au! Yarinya ba sai dai kiyi tayiwa Ubanki istigifari ba, daÉ—in abin ko kashe ki yay shine ya haifa a toh” Aleema ce ta kama hannunta tana rarrashinta kasancewar weekend ne duk suna gida. Akeem na shiga side É—insa rest room ya nufa cire farar jallabiyar jikinsa yay tare da saÆ™ale ta a hanger, fure fresh skin É—insa ta bayyana wani irin

ƙwantaccen baƙin gashi ne a saman mararsa mai matuƙar ɗaukan hankali jikinsa a sanyaye ya nufi cikin tube tare da shigewa ciki, wani irin sauke numfashi yay a hankali kuma ya ƙara nutsewa cikin ruwan dake cike har bakin tube ɗin, zafin da zuciyarsa ke masa ya sanya gaba ɗaya yama mance a cikin ruwa yake, idan ya tuna irin faɗan da Ummi da Abbu sukai masa sai yaji wani abu ya tsaya masa a ƙirjin, cikin ficewar hayyaci da kuma zallar damuwar dake ransa ya ƙara nutsa kansa cikin ruwan a hankali kuma ruwan ya fara shige masa cikin baki da hanci.

A hankali wata baÆ™ar mota mai Æ™irar Audi RS5 ta fara shigowa ciki Nasarawa daga farko farkon Nasarawa harya gifta sai kuma ya dawo baya a hankali yana zare baÆ™in glasses É—in dake idanunsa,  saurayi ne É—an kimanin shekaru 27 yana sanye da wani farin voyal wanda yay masa kyau sosai kasancewar sa farin bafulatani kana ganinsa Kasan cewar kuÉ—i sun zauna masa, a hankali yake tafiya da motar zuwa baya kasancewar shike driving É—in ganin hakan yasa wanda ke kusa dashi yace “Ajmal me kake haka ne?”shiru Ajmal É—in yay domin baya jin akwai abinda zai iya faÉ—a, a hankali ya gama tsayar da motar  tare da buÉ—e murfin motar ya fito ganin hakan yasa Karim yay saurin fitowa yana faÉ—in “wallahi kaifa ba hankali gare ka ba, kana ganin aikin dake gabanmu dole ne a wannan satin mu samu mu shawo hankali duk raguwar jama’ar” ina Ajmal baya gane yaran domin tuni idanunsa suka sauka akan fuskar Akeela dake kwance a Æ™asan wata bishiya wallahi wallahi a wannan lokacin duk wanda yaga Akeela dole zuciyarsa ta buga domin ba zaka taÉ“a cewa Æ´ar hausawa bace, tana kwance kanta na zubda jini saboda wata muguwar faÉ—uwa da tayi gaba É—aya kayan baccin dake jikinta sunyi wani bala’in yin datti gashinta ya wargatse yay É—ai É—ai, tsaye Ajmal yay akan Akeela yana jin zuciyarsa na bugawa, a hankali kuma ya tsuguna a gabanta dai-dai lokacin da Karim yake Æ™arasuwa wajan cikin sauri yace “wai Ajmal meke damunka ne? Baka tsoran abin cutarwa ne? Kilama ba mutum bace Aljana ce, ina ka taÉ“a ganin mace mai gashin wannan?” Banza Ajmal yay masa domin yadda idanunsa suka sauka akan fuskarta yasa baya fahimtar komai dukkan wani abu na kansa sai da ya kunce, hannunsa ya miÆ™a tare da tattare sumar data rufe mata fuska cikin sauri ya rufe idanunsa yana faÉ—in “Ohh God”  Karim yay saurin faÉ—in “is she died?” Girgiza masa kai kawai Ajmal yay yana Æ™oÆ™arin sanya hannunsa ya É—auke ta Abbu dake Æ™arasuwa wajan yace “Akeela! Allahamdulillah”

Da sauri ya sanya hannunsa ya É—auke ta tare da kallon Ajmal yace “thank you son, wallahi tun jiya mukai missed nata yanzu na Æ™ara fitowa ne, kamar daga sama na hangeka ji nai kawai ina son ganin Meke faruwa cikin ikon Allah kuma naga Akeela thank you” jinjina kai kawai Ajmal yay yana shafa wuyansa sosai ya gane Abbu amma shi Abbu sam bai gane waye Ajmal ba, kamar bazai magana ba sai kuma yace “Dad! A nan kuke ne?” Kallon Ajmal Abbu yay yana karantarsa sai kuma yace “eh cikin Railway quarters no 112” idanunsa akan fuskar Akeela yace “ok Thank you” yana faÉ—in hakan ya nufi cikin motar tare da zama wajan driving ba ganin hakan yasa Karim shima ya shiga cikin motar da gudu Ajmal yaja suka bar wajan, mai makon yaje inda zashi sai kawai ya juya kan motar ya nufi hanyar gida da Mamaki Karim yace “wai Ajmal Meke damun ka ne?” Cikin É“acin rai Ajmal yace “ban sani ba, banza shege munafuki kawai haba” ya faÉ—a cikin É“acin rai yana Æ™ara sharara gudu.

Abbu shima cikin farin ciki ya nufi motarsa bai yadda ya ajjiye ta a back seat ba a nan saman jikinsa ya barta key yaywa motar ya juya zuwa gida tun a hanya ya kira number Ummi da sauri tai picking call É—in tana faÉ—in “Something news?” Cikin Æ™asa da murya yace “I’ve seen her Ummi on my way yanzu” Murmushi tayi tace “Allahamdulillah”

A wahala Akeem ya É—ago kansa daga cikin ruwan yana sauke wahalallan numfashi a hankali kuma ya buÉ—e idanunsa da sukai wani mahaukacin ja, ya jima cikin ruwan kafin ya fito ya É—auki  bathrobe ya sanya a jikinsa, ruwa na zuba a jikinsa ya fito kai tsaye ya nufi cikin wani special bedroom É—insa Yana zuwa ya rufe Æ™ofar da key, derect bed ya nufa yana zuwa ya faÉ—a tare da jan duvet ya rufe jikinsa tass domin wani mugun bacci ya keji, kamar yadda ya saba haka yanzu ma ya jawo pillow ya rungome a tsakanin Æ™irjinsa yana sauke numfashi a haka bacci ya É—auke sa da tunanin yadda zai rama abinda akai masa akan wannan yarinyar.

Ummi da Didi ne suka miÆ™e lokacin da Abbu ya shigo da Akeela a hannunsa, kai tsaye part É—in su Aleema ya nufa da ita, Ummi na biye da shi Mami ko motsawa ba tayi ba idanunta akan cineme,  yana zuwa su Afaf suka miÆ™e fuskarsu É—auke da farin ciki, kwantar da ita yay cikin nutsuwa Ummi tace “bari na duba ta” gefe Abbu ya koma yana jin kamar ya kori kowa ya jata jikinsa ya rungome ya lallasheta da kansa amma no way ahlinsa na wajan dole yaja da baya da yaga yana neman zama wani uncontrol sai kawai ya fice daga part É—in, a hankali Ummi ta zauna idanunta akan Akeela tace “Afaf jeki kawon warm water a bowl with towel” “ok Ummi” bathroom tayi ta shiga haÉ—a ruwan zafin kana ta fito É—auke da towel É—in “drop it and leave and you too Aleema” ficewa duk sukai gently Ummi ta zamewa Akeela rigar jikinta babu ko bra a jikinta cikin tausayin ta Ummi ta shiga goge mata Jikinta da ruwan zafin, sosai ta kasa mata Jikinta ta shafe ta da robe kana ta sauya mata kaya zuwa Sleeve Bodycon mai sauÆ™in nauyi saboda zafi ake da alama akwai Æ™aramin hadari a Æ™asa, kwantar da ita tayi ta rufe da duvet gudun a.c ta Æ™aro mata ba mai cutarwa, fuskarta tabi da kallo ganin yadda take sauke ajjiyar zuciya a jajjere, fita tayi daga bedroom É—in a Parlo ta samu su Afaf É—in suna buga game ficewa tayi daga part É—in nasu baki É—aya.

Ummi na fita Akeela tai wani irin juyi tare da buÉ—e idanunta abinda basu sani ba idanunta biyu kawai har yanzu mutanan na kanta ne irin aljanun nan ne masu mugun abu wanda sai ansha wahala kafin suyi magana ma. Parlo Ummi ta dawo kusa da Mami ta zauna ba tare da tace komai ba, a hankali Abbu yake tafiya cikin tafkeken bedroom É—insa hannunsa goye a bayansa sai numfashi yake fitarwa, gaba É—aya yama rasa yaya zai yi baya jin daÉ—in komai burinsa kawai yaga fuskar Akeela, wani murmushi yay yana jin daÉ—i domin sai yanzu ya tuna da Ƙofar dake bedroom É—insa wacce kai tsaye hanyar tayi har parlon su Aleema, jikinsa na rawa ya buÉ—e Æ™ofar tare da fita su Afaf na tsaka da buga game su kaga Abbu kamar daga sama kallonsu yay yace “bari na mata magani” jinjina kai kawai sukai, bedroom É—insu ya nufa jikinsa har wani tsuma yake tana zaune ta tura kanta cikin tsakiyar cinyoyinta, Æ™arasawa yay tare da faÉ—in “Babyn Abbunta zo nan gani nazo rarrashin ki” shiru bata motsa ba hakan yasa ya Æ™arasa inda take yana zuwa ya jawota jikinsa yana shafa kanta tare da faÉ—in “Babyna” jajayen idanunta ta É—aga ta kallesa cikin wata kakkausar murya tace “Abbu Akeem” zuciyar Abbu ce ta buga da Æ™arfi cikin damuwa yace “me Akeem zai maki” kuka ta sanya masa ko kuma aljanun suka sanya masa cikin wata iriyar Murya mara daÉ—in saurara tace “Akeem muke son gani Abbu” sai a lokacin Abbu ya fahimci ba ita take Maganar ba, shafa kanta kawai yay yana faÉ—in “sorry Babyna kina shan wahala ko? Dana aureki zan bar Æ™asar dake” wani irin kallo tayi masa tace “kai ma baka da lafiya Abbu Meye Wannan a jikinka?” Bai tsaye jin zan canta ba ya É—ura bakinsa a kunnanta ya shiga yi mata addu’a, miÆ™a ta fara yi kafin kuma a hankali jikinta ya saki bacci mai nauyi ya É—auke ta, Murmushi Yay yace “Babyna zaki sanya zuciyata bugawa idan kina kiran sunan Akeem, Tabbas ni kaÉ—ai zaki so nasan Akeem bai taÉ“a cewa yana sonki amma yadda kike da mugun kyan nan masu kawo maki hari suna da yawa, ni kawai zaki so zaki zauna dashi, zan koyar dake zallar so da kuma Æ™auna ta Akeem kuma duk yadda za’ai a watan nan sai na tura shi Germany zai nesa dake sai yay Shekaru masu yawa lokacin tuni kin zama tawa zai dawo” ya faÉ—a yana shafa kanta a hankali ya sumbaci goshinta..

*Singapore*

Khoo Teck Puat Hospital

A hankali motar tai parking Meema ce a gaba sai mahaifinta President Ahmad Adil yana Cikin Wata dakakkiyar shadda dark blue mai kyau sai sheÆ™i yake, yayinda ita kuma take cikin wata milk É—in abaya da red É—in Stones tayi rolling kanta da vail tayi kyau sosai, hannunta riÆ™e da waya ga wasu manyan guards  kai tsaye cikin female sugical world suka nufa shiru asibitin saboda asibiti ne na masu kuÉ—i babu hayaniya ko kaÉ—an, cikin sauri Meema ta buÉ—e Æ™ofar office É—in Dr É—in ba tare dako permission ba, yana zaune yana duba wasu files Meema ta shiga tana faÉ—in “Dr what happened i saw your miss call” Murmushi yay yace “Na kira na faÉ—a maki yau za’a buÉ—e fuskar Æ™aninki” wani daÉ—i taji da sauri ta rungome Dad tace “Dad bana faÉ—a maka ba” hannunta ya riÆ™e yace “ok be careful” MiÆ™ewa Dr yay cikin so much respect ya shiga gaisar da Dad kafin yace “follow me” binsa sukai a baya har suka nufi wani room 11 buÉ—e Æ™ofar akai Dr na gaba Meema na baya sai Dad, cikin sauri ta zame hannunta ta nufi inda yake a kwance da kayan marasa lafiya Murmushi tayi tana riÆ™e hannunsa, É—umin hannunta daya ratsa tafin hannunsa yasa yay sauri riÆ™e hannunta domin yau gaba É—aya ba tazo hospital É—in ba kamar yadda ta saba, kayan aiki Dr ya É—auko Meema jikinta har rawa yake domin ta matso ta ganshi, cikin nutsuwa Dr ya fara ware masa bandejin fuskarsa yana cirewa, bakinsa ne ya fara bayyana mai É—auke da jajayen laɓɓa, sai kuma hancinsa a haka har aka gama buÉ—e masa fuskar, idanunsa a rufe ruff fuskar Abbu kwance a saman nashi fuskar Dr ne yace “Congratulations now open your eyes” slowly ya shiga buÉ—e idanunsa kai tsaye ya sauke ganinsa akan fuskar Meema babu ko kifta idanu, cikin farin ciki Meema tace “Bro na” shiru yay mata bai ce mata komai ba ganin hakan yasa ta kwaÉ“e fuska tace “why baya magana?” “Ai sai ya koyi komai ba, kinga aiki ya sameki” Dad kam tunda aka buÉ—e fuskarsa yaji gabansa ya faÉ—i sosai ya san me fuskar amma mene haÉ—in Meema da wannan gske har ta sanya aka sawa wani ita? hannunsa Meema ta kama tace “I’m your sister” cikin kwaikwayon Abinda ta faÉ—a yace “I’m your sister” wani irin Murmushi Meema tayi tace “A’a ba haka za kace ba” kallon Dad tayi tace “Dad his name please” buÉ—e baki Abbu yay yace “Asheer” “Wow! Nice name” Meema ta faÉ—a tana faÉ—in “as from today sunanka Asheer amma zanna ce maka Bro ni kuma kace Sister” dry Dr yay yace “tab kina nufin a yanzu duk zaki koya masa komai? Mudai nan kafin ku tafi zamu kuya masa wanka,Sallah, cin abinci komai” Asheer kuwa tunda ya É—ura idanunsa akan Meema yaÆ™i É—aukewa domin tsoran kallon mutanan wajan ma yake, miÆ™ewa tayi zata É—auko masa mirror da sauri ya riÆ™e hannunta yana juya idanunsa, da Æ™yar dai ya sake ta lokacin da yaga kansa a madubi kansa ne yay wani irin sarawa da sauri ya saki madubin a Æ™asa ji kake tasssss ya fashe a Æ™asa cikin sauri kuma cike da tsoran abinda yayi ya É“oye fuskarsa a bayan Meema..

Today is Monday yau Akeem ya tashi da azumin Litinin da Alhamis kamar yadda ya saba, rabonsa da ganin Akeela wajan sati guda kenan, domin ko zama yanzu ba yayi a Parlo, a hankali ya fito daga motarsa lokacin ana ta kiran sallar magrib kai tsaye pampo ya nufa tare da É—aura alwala, ko cikin gida bai shiga ba ya nufi cikin masjid É—in, lokacin daya isa ana jiran zuwan liman amma Shiru ganin an rasa wanda zai ja sallar sai kawai yay gaba tare da tada kabbara, nutsuwa kowa yay a hankali cikin zazzaÆ™ar muryarsa mai daÉ—in gaske ya fara fidda kira’a yana fidda makarijil huruf, a can gida kuma Akeela na zaune domin ita sosai azumin ya wahalar da ita kuma ta saba tana yinsa ne, idanunta ta buÉ—e jin sautin Muryarsa ya daki kunanta rabon da taji Muryarsa haka harta mance, MiÆ™ewa tayi saboda wani sanyi da jikinta yay a hankali ta nufi bathroom ta É—aura alwala kana ta dawo tayi sallah ji tayi jikinta babu daÉ—i sai kawai ta zame hijab É—in ta nufi bathroom, cikin sanyin jikinta ta buÉ—e Æ™ofar ba tare data rufe ba ta fara kwaÉ“e kayan jikinta ruwan zafi ta sakarwa kanta tana sauke ajjiyar zuciya.

Bayan an idar da sallah Akeem ya fito Abbu na bayansa a haka suka nufi gida babu kowa Parlo duk Sallah suke, part É—insa ya nufa Akeem kuma ji yayi yau babu abinda ya keso sama da zuma yasan kuma Didi kawai ke Shanta, part É—in ta ya nufa a hankali ya shiga lokacin tana Sallah, wani daÉ—i yaji domin baya son masifar ta a yanzu, fridge É—inta ya nufa gaba É—aya robar zumar ya É—auko Didi kam banda zare ido babu abinda take da taga abin bana wasa bane sai ta fara “ehem! ehem!” Ko Kallonta bai ba ya nufi waje ai da sauri tace “Assalamu alaikum” miÆ™ewa tayi tana faÉ—in “Muhammadur Rasulullah s.a.w Audil sata Æ™iri Æ™iri Ubangiji dai yau ya nuna min É“arawon zumata” jin tana kiran sunansa kuma ya tabbatar part É—insa zata bisa cikin rashin makamar yi kawai ya faÉ—a part É—in su Aleema ga mamakinsa sai yaji tana faÉ—in “Munafikin ai na ganka” da sauri ya juya yana duban inda zai É“oye ganin Æ™ofar bathroom a buÉ—e ya wani faÉ—a ciki da sauri yana murzawa Æ™ofar key…..