BABBAR YARINYA CHAPTER 4 Oum Aphnan BABBAR YARINYA CHAPTER 4 Oum Aphnan Www.bankinhausanovels.com.ng _Wasu Na cewa wai Anya Oum Aphnan ɗin nan Musulma ce kuwa? … To Tambayarku ta dawo gareni,saidai banda Amsarku A ynz ,Amma in kuna jin tantama zaku iya ɗabbaƙa mun kalma Asshahada sai kuga in zan karɓa._ Da ƙyar Islam ta yarda ta fito dinner ,bayan kiran da suka dinga mata a waya a cewarta tayi fushi dasu ,tinda suka bar Akram ya zauna basu hanashi ba to tabbas sun daina sonta. A dinning wani shan kunu tayi tana cusa abincin kamar magani, taƙi haɗa ido da kowa ,saidai Hajiya zainab ɗin da Alhaji buban su kalli juna su guntse dariya. “Baby” Alhaji buba ya kira sunanta a hankali ,kumburo kumatu tayi amma ta kasa magana “Baby Girl” Hajiya zainab ta sake kiranta Murya can ƙasan maƙoshi ta amsa da “Um” sannan ta caki Fried plantain taɗan gutsura tana taunawa “Baki tambaye mu me ya kawo yayanki Akram ba?” Saida ta juya ƙeya ta kalli ɓangare ɗaya ta babballara harara gamida murguɗa baki kafin tace “So who cares me ya kawoshi,sai yayi …