BABBAR YARINYA CHAPTER 4 Oum Aphnan
BABBAR YARINYA CHAPTER 4 Oum Aphnan
_Wasu Na cewa wai Anya Oum Aphnan Ιin nan Musulma ce kuwa? … To Tambayarku ta dawo gareni,saidai banda Amsarku A ynz ,Amma in kuna jin tantama zaku iya ΙabbaΖa mun kalma Asshahada sai kuga in zan karΙa._
Da Ζyar Islam ta yarda ta fito dinner ,bayan kiran da suka dinga mata a waya a cewarta tayi fushi dasu ,tinda suka bar Akram ya zauna basu hanashi ba to tabbas sun daina sonta.
A dinning wani shan kunu tayi tana cusa abincin kamar magani, taΖi haΙa ido da kowa ,saidai Hajiya zainab Ιin da Alhaji buban su kalli juna su guntse dariya.
“Baby” Alhaji buba ya kira sunanta a hankali ,kumburo kumatu tayi amma ta kasa magana
“Baby Girl” Hajiya zainab ta sake kiranta
Murya can Ζasan maΖoshi ta amsa da “Um” sannan ta caki Fried plantain taΙan gutsura tana taunawa
“Baki tambaye mu me ya kawo yayanki Akram ba?”
Saida ta juya Ζeya ta kalli Ιangare Ιaya ta babballara harara gamida murguΙa baki kafin tace “So who cares me ya kawoshi,sai yayi ta zuwa in yaso ya shekara anan…ni inma cemun akayi un bar masa gidan bari zanyi tunda kun daina sona” Ζwalla da ya soma taruwa mata a ido yasata shanyewa gamida yin shiru
Kannewa Hajiya zainab tayi “Oh yeag mu mun isa muce Ki bar gidan nan ke da yike mallakinki mufa dik zamanki muke ,Saidai shi Alkhairi da cigaba yake yunΖurin kawo ma rayuwar ki ,don zuwansa ma yace ya samar maki Admission a UK zakije ki karanta Home managements abun daΙin ma tare zaku tafi…”
Islam data kai glass cup baki ta kurΙi lemo kenan ta furzo shi waje
“What??” ta tambaya gamida zaro ido
Kafin suyi wani yunΖuri ta Ιaura da bala’i kamar wacce ta tasa Ζ΄aΖ΄anta a gaba
“Ni?…Ni dai Islam nine zan bi Akram UK da sunan wai karatu,kuma ma in rasa a abunda zan Ζare sai a mai koyan dafa abinci! Wannan shine abinda bazai taΙa yiwuwa ba ” tana kai aya ta ture kujeran da take kai baya ta miΖe ta bar masu wajen gabaΙaya
Waigowa Alhaji Buba yayi ya kalli Hajiya zainab
“Ko zaki ki Ιan rarrasota? Nifa dama shiyasa ban goyi da bayan tafiyar nan ba”
“Haba Sweet haba don Allah ,wannan fa abun na Islam yina neman yawa ,kar mutane suzo suga yanda take maltreating Ιin mu a fita da ita a baki da sunan bata girmamu muji kunya”
“To ai laifin kine ,ke kika sangarta ta”
“Haba Alhaji ni ko kai?” take suka fara musu ,kowa yina zargin Ιan uwansa da bada gudunmawa wajen lalacewar tarbiyyan Islam…Ζarshe dai Hajiya zainab ne ta janye maganar ta miΖe tai masa saida safe ,yasan tayi fushi ne amma kawai sai yayi burus da ita shima yayi hanyar samansa .
*****
Akram kam tun kafin ya bar gidan ya kira wayar drivern Office Ιinsa ya kwatanta masa Gidansu Islam yazo ya Ιauke shi.
A back seat ya zauna cikin motarshi GMC ,lumshe ido yayi ,yina tuno sanda Islam ta wani Ιaure rai gamida haΙe giran sama da Ζasa ,tana tambayarsa wai Anya har yanzu ma ka mallaki motar kanka?
Dariya ya sake fashewa dashi ,yina tuna yanda ta wani yi balance cikin fasuwan kai ala dole ga ita Babbar yarinya
Wayarsa ne ya fara Ιurari ,Kallar wayar yayi yaga baΖuwar number ce ke kira a kuma personal phone Ιinsa ba na wajen Aiki ba
Kamar zai Ζyale wayar sai kuma ya Ιaga tunda yasan duk wanda zai kira tanan tabbas family member Ιinsa ne.
Ζauka yayi ya kanga a kunne
Ta Ιayan sashen akace “Hello” Gwale ido yayi cikin mamakin muryar mace
“Assalamu Alaik,waccece?”
“Sorry durling dama na kira ne in tabbatar in numberne ashe kuwa shine ,Affa?”
Tsaki yaja cike da Ζuluwa “Wai wanene plz”
“Oh Mr. Man calm down na aza ko cikin muryoyin mata dubu zaka iya cankar muryata? Hmm karka damu to Khairy ce your cleaner”
Wani mitsiyacin tsaki yaja kawai ya kashe wayar yina jin ransa na tafasa ,shikam wa ya bata numbersa ? number ma na gida ba na wajen aiki ba?
****
Next day Evening
Islam kwance take akan bangajejen gadon royals Ιinta sai juyi take cikin barci mai Ιauke da mafarki mai tsayuwa a rai ,Dirkuwar motocine ,ya isheta a barci da Ιan hayaniyar mutane haka daga can tsakar gidan.
Cikin fushi ta miΖe ta kwaye cikinta daga cikin blanket Ιin ,ta sako Ζafarta Ζasa daga ita sai Ιingilar riga armless da ya Ιan gota gwuiwarta da kaΙan.
Zuwa tayi gaban windown Ιakinta dazayi hango mata tsakar gidan ta leΖa ,Wani Tsaki ta saki me cike da Ζuluwa ,Ζaga murya tayi ta Ζwalla ma guard Ιinta kira
“Amaka!!”
Guards Ιinta da suke zaune akan plastic chairs a Ζofar Ιakinta , suna hiransu cike da fara’a da NishaΙi ,ga alama dai sunajin daΙin zuwan wa’innan BaΖin ,A furgice wanda aka kira da amaka ya miΖe “Yes Ma!”
Ya Shiga Ιakin saidai a bakin Ζofar ya tsaya
“Barka da yamma”
Ζan yamutse fuska tayi
“Hayaniyar me nike ji? ,A waje?”
“Eh to ,dama Yaron Gomna ne Ishaq maga ,wannan babbar lawyan dake da kotuna a Ζasan Ingila ne yazo neman Aurenki shine kike jin jiniya!”
Wani tsawa ta daka masa “Oh sharraf!”
Da sauri ya Ιinke bakinsa
“Go and tell them to turn that blurdy Noisy Idiot off”
Zaro ido yayi jikinsa na Ιan rawa “Ehem hajiya?”
Ranta Ζara Ιaci yayi “Bakaji da kyau ne? Wuce kaje kace su kashemun banzan jiniyarsu inason inyi barci ,this is just 5:00pm “
Da sauri ya juya ya fita daidai nan ya haΙe da hajiya zainab ta nufi Ιakin Alhaji Buba da sauri ,shima ko bayanta yabi don ya faΙa mata abunda Islam ta aikesa yayi tunda gaskiya shi bazai iya zuwa ya faΙa ba.
Saidai yana soma kiranta ta dakatar dashi da hannu
“kaga ina zuwa ,munyi baΖi dakace ni kaΙan” tana maganar tana hayewa Ιakinsa
****
Jin An kwashe a Ζalla mintuna Biyar baa Ιauke Ζaran jiniyar ba ya sata harzuΖa ,a yanda take ta suri Room slippers ta fice a zafafen Ζarshe ,tana Ζwallawa su Amaka kira saidai bataga kowa ba ,hakan ya sata wucewa tsakar gidan , ta sa a dakatar da kanta amma a ranta tana kimtsa rashin mutuncin da zatayiwa su amaka Ζilan ma yau Ιin nan zata dakatar dasu a bakin aikin su ,don basu da amfani kasancewarsu guards Ιinta
Harabar gidan ta fito Sosai daidai Sojoji sun rufo masa baya cikin isa da shiga ta Alfarma
Wani haΙe rai tayi tamkar me jin amai,tana masa kallon raink wani lukuti dashi,shikam sai Ιan murmushi yike mata dukda ,daka kalli fuskarsa ba ma’abocin fara’ar bane ara yayi kawai ya yafa
RiΖe Ζugu tayi a bakin Ζofar da zasu shiga ma’ana inda akayi masu iso
Ζyar yike kallon suranta cikin lafaffen cotton Ιin rigar jikinta ,sosai ya yaba halittarta saidai baiji daΙin fitowarta a haka cikin mutanensa ba ,sam ba girmansa bane ,amma zaiyi mata uzurin yarinta ne da ya aureta zai gyara abinsa
Cikin tsawa da bala’i ta kallesu “Ashe ban aiko a kashe mun wannan lousy Noise Ιin ba ,kun gallaze ni ina barci wannan wani irin zaluncine ?”
Jikinsa rawa ya somayi ,da sauri ya matsa gabanta ,cikin sassauΖar murya irin na wanda basu saba Ιaukan kwaram Ιin jama’a ba yace “My love”
Tsawa ta daka masa gamida Ιaga masa hannu tana faman hura hanci “Oh shut that your dirty mouth up !…ka kawo mun Wa’innan Irresponsible Nonentities Ιin cikin gida saboda selfishness Ιinka duk sun hargitsa mana gida this evening an katse mun barci who dare you ,Da zakasa a kawo mun wannan Good for Nonthing Fools Ιin ehem?”
Ta Ζare tana Ιaga jijiyar wuya kamar ta samu Ιan cikinta
A hankali ya tako gabanta yina Ιan ware hannu ,yanda zai mata magana cikin sulhu
“Haba ke kuwan,karki kunyata ni cikin mutane na mu shiga ciki sai kiyi mun magana a tsanake,tunda kinga ko banza dai abun arziΖi ta kawoni da nufin mu Ζulla soyayya mai tsafta cikin Ζ΄an Ζalilan kwanaki mu angonce…”
Ras ! Taji gabanta ya faΙi ,take taji gabaΙaya ya koma mata baΖi wuluk a idonta ,rasama me zatayi masa tayi ,kawai Ζaga hannu tayi bai aune ba saidai yaji Ιauuuuu!! Ta dalle sa da mari wanda ya sashi razana gamida sakin baki shaye da tsananin mamaki ,a take lafiyayyun yatsunta biyar suka bayyana a kuncinsa
AsheΖeΖe ta kallesa tana jin yanda Ζirjinta ke kaiwa da komowa a zafafe,sannan cikin gatsali ta Ιaura da masa magana
“An faΙa maka ni ,Islam Kwantai nayi da zaka kawo mun wasu sillallun Ζafarka nan wai…(Ta shiga kwaikwayan yanda yayi magana) Abun ArziΖi ya kawoni da nufin Ζulla soyayya me tsafta dani dake fa !!” HaΙe rai ta kuma yi “Oh gerrout ,tsami kawai
Cikin zafin nama ta danno Ζofan sai ji kake kararaf ta kulle Ζofar ,ta barshi anan tsaye dafe da kunci kunyar duniya ya gama shansa ,ko motsi ya kasa yi bare har kuma ya iya Ιaga ido ya kalli guards dinsa da suke ganin kimarsa.
Post a Comment for "BABBAR YARINYA CHAPTER 4 Oum Aphnan"