WATA MACE CHAPTER 5 BY SANA S MATAZU

WATA MACE CHAPTER 5 BY SANA S MATAZU
WATA MACE CHAPTER 5 BY SANA S MATAZU                     Www.bankinhausanovels.com.ng  Kwanci tashi babu wuya wajen ubangiji, Yusuf ya sami sauƙi sossai. Har an sallameshi. Sai dai rayuwarsa ta sauya sossai, ya yi bala’in ƙara zama me sanyi fiye da baya. In kaga haƙoransa sun buɗe to murmushi ne amma ba dariya ba. Ita kanta Shukura ta ga sauyi sossai a tattare da shi na wasu ɗabi’un amma kuma shaƙuwarsu na nan. Lokacin da aka sallamoshi gidan mahaifinsa ak wuto da shi, domin ya ƙuduri aniyyar ya bar GIDAN MATARSA har abada. Dan haka ba shi da wajen zama da ya wuce baranda, kodai yana karatu ko kuma suna waya da Shukura. Wannan damar Labiba ta samu ta maida tagar dake ɗakin Amne ta sama wajen zamanta. Kodayaushe idanunta yana kansa, duk wani motsi nasa yana tafiya da yanayinta zuciyar n matsewa da wani irin abu da takasa fahimtar tausayine ko kuma ƙiyayya ce. Kamar kodayaushe yana zaune, ita kuma idanunta na kansa. Tunani take yi ta ya ya zata isa wajensa ta nemi yafiyarsa? Tabbas tana ka…