SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA
SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA Www.bankinhausanovels.com.ng Two years Later!+ Acikin shekaru biyunnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda haihuwan Husnah, da kuma ƙarin girman da akayiwa Doctor Sadeeq a wajen aiki, Zahrah kuwa tazama lecturer acikin jami’ar da tayi karatu. Abubuwa dayawa sun faru acikin waƴannan shekarun. Tsaye take agaban wani babban table tana haɗa wasu takardu dake gabanta, ajikinta sanye take da Abaya gown, maroon colour, wanda jikinsa yaji adon duwatsu da kuma flowers masu kyau, yayinda Abaya Vail ɗin dake yafe saman kanta, ya sauƙo har zuwa ƙirjinta, babu wani kwalliya akan fuskarta, lipstick ne kawai sai kuma kwallin data sanya acikin ɗara ɗaran idanunta, sosai taƙara kyau, cika da kuma wayewa, duk da cewa a ƴan shekaru biyun da suka wuce itaɗin ba baya bace wajen kyau, amma ayanzu komai nata yaƙara ninkuwa akan nada, yanzu tana amsa sunanta na cikakkiyar mace. Kallonta ta maida kan agogon dake ɗaure…