SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 14 KARSHE BY FATYMA SARDAUNA

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Two years Later!+

Acikin shekaru biyunnan da suka wuce abubuwa da yawa sun faru, ciki kuwa hadda haihuwan Husnah, da kuma Æ™arin girman da akayiwa Doctor Sadeeq a wajen aiki, Zahrah kuwa tazama lecturer acikin jami’ar da tayi karatu. Abubuwa dayawa sun faru acikin waÆ´annan shekarun.

Tsaye take agaban wani babban table tana haÉ—a wasu takardu dake gabanta, ajikinta sanye take da Abaya gown, maroon colour, wanda jikinsa yaji adon duwatsu da kuma flowers masu kyau,  yayinda  Abaya Vail É—in dake yafe saman kanta, ya sauÆ™o har zuwa Æ™irjinta,   babu wani kwalliya akan fuskarta, lipstick ne kawai sai kuma kwallin data sanya acikin É—ara É—aran idanunta,   sosai taÆ™ara kyau, cika da kuma wayewa, duk da cewa a Æ´an shekaru biyun da suka wuce itaÉ—in ba baya bace wajen kyau, amma ayanzu komai nata yaÆ™ara ninkuwa akan nada, yanzu tana amsa sunanta na cikakkiyar mace.  Kallonta ta maida kan agogon dake É—aure akan tsintsiyar hanunta.   “4:30 pm” ta faÉ—a tana É—an waro idanunta, da sauri tacigaba da tattare takardun, wasu tasa acikin jakarta, wasu kuwa ta sanyasu acikin wata drawer dake cikin office É—in. Wayarta da jakarta ta É—auka, kana ta nufi hanyar fita daga office É—in.

STORY CONTINUES BELOW

Motarta Æ™iran  Corolla LE  tashiga haÉ—e da bata wuta, ta fice acikin jami’an..    Bata wani jima sosaiba ta isa sabon gidansu wanda suka koma babu jimawa.

Da sallama É—auke abakinta ta kutsa kanta cikin falon, babu kowa afalon, sai TV Plasma É—insu dake ta aiki shikaÉ—ai.  Direct wani É—aki dake cikin falon ta nufa,  tsayawa tayi ajikin Æ™ofar É—akin tana sakin murmushi, idanunta nakan wani yaro da shekarunsa na duniya bazasu wuce uku ba, ya nata  Æ™iriniyansa  shi kaÉ—ai, yaron kyakkyawane sosai, gashin kansa kuwa kamar na larabawa.  Cikin sanÉ—a tashiga takawa harta Æ™arasa wajen dayake zaune, murya a hankali tace.

“Babyy!”    Jin muryar mahaifiyarsa acikin kunnuwansa yasashi juyowa da sauri, yana ganinta, ya tafi ya faÉ—a jikinta, yana dariya, itama dariyan tayi haÉ—e da manna masa kiss akan bakinsa, cike da kulawa haÉ—i da Æ™aunarsa.  

“Aunty Sannu da dawowa” cewar Haulat me yi mata rainon yaron, idan zata aiki.

“Yauwa Haulat sannu da gida” Zahrah ta amsa mata fuska a sake.

ÆŠaukan yaronnata tayi suka fice daga É—akin, direct sama ta haura inda anan bedroom É—inta yake.

Aje yaron nata tayi akan gado haÉ—e da durÆ™usawa agabansa, chocolate irin marar zaÆ™i sosai É—innan ta ciro ajakarta, kana ta É“are ta basa a hanunsa, da murna Asad ya karÉ“i Chocolate É—in,  matso da fuskarsa yayi daf da tata, kiss yayi mata akan kumatunta haÉ—e da cewa “Thank you Mummy!” yayi maganar ne cikin muryarsa dake É—auke da tsananin yarinta.

Murmushi tayi kana taÉ—anja kumatunsa, miÆ™ewa tayi ta wuce cikin bathroom acan ta cire kayan jikinta haÉ—e da sakarwa kanta shower. 

Koda ta fito sama sama ta shafa mai domin yanayin garin ana É—an busa zafi,    wani dogon skin tight  baÆ™i ta sanya, wanda yayi matuÆ™ar bayyana surar jikinta, bama kamar hips É—inta da suka sake cika,  wata riga mai  net tasanya, irin fitted É—innan, sosai rigan tayi mata kyau,  Æ™irjinta ne kawai yazamana a rufe, amma gaba É—aya jikinta daga cikinta zuwa bayanta a bayyane suke, haka tsarin rigar yake.

Da Body Spray É—inta me daÉ—in Æ™amshi ta feshi jikinta,   dogon gashinta dayasha kitson kalaba, ta kama ta É—aureshi da  ribbon,  direct gaban É—an madaidaicin fridge É—in dake É—akin ta nufa,  buÉ—ewa tayi ta É—auko goran Yoghurt, buÉ—e murfin goran  tayi tasoma sha ahankali.

Shigowarsa É—akin kenan, amma kuma kokaÉ—an bataji motsin buÉ—e Æ™ofarsa ba,   yana sanye da riga da wando na Suit navy blue colour masu kyaun gaske,  tabbas ya sauya daga kamanninsa nada, yaÆ™ara haske da kyau, ga lallausan sajensa da ya kwanta luf akan fuskarsa,  yazama wani na musamman dashi, me tafiya da hankalin Æ´an mata, yaÆ™ara zama Handsome, dagani kai kasan kuÉ—i sun zauna masa..

Dariyan Asad da taji ne yasata waigowa ta kalli yaron, atunaninta ko ɓarna yakeyi mata, gani tayi idanunsa nakan ƙofar shigowa ɗakin, saboda haka itama ta maida idanunta wajen, da taga Asad ɗin na kallo.

Idanunsu ne suka sarÆ™e a cikin na juna, wani irin murmushine ya Æ™wace mata, haÉ—e da lumshe idanunta, ta kuma buÉ—esu alokaci guda, shima murmushin yayi mata, kana ya buÉ—e duka hannayensa, alaman ta taho garesa,    babu musu ta Æ™arasa garesa, haÉ—e da faÉ—awa cikin jikinsa, atare suka rungume juna, tare da sauÆ™e ajiyar zuciya.

Hanunsa yasanya yashiga shafa bayanta, haÉ—e da soma hura mata iskan bakinsa, cikin kunnenta.  Luf tayi acikin Æ™irjinsa, tana mai jin daÉ—in abun da yakeyi mata, idan har tanajin iskan bakinsa acikin kunnenta, sosai take samun nutsuwa acikin ruhinta.

Sun kusan mintuna 10 a haka kafun tace dashi cikin sanyin murya.    “Sannu da dawowa!”

Bai amsa mata ba, saima hannayensa daya É—aura a gefe da gefen cikinta, yashiga shafawa a hankali,  shiru tayi aÆ™irjinsa tana sauÆ™e numfashi.  ÆŠayan hanunsa yasanya ya É—ago haÉ“arta, suka jefa idanunsu acikin na juna, wani irin kasalane ya dirar mata alokaci guda, sakamakon tozali da kyawawan idanunsa da tayi.  lumshe nata idanun tayi, tana sauÆ™e numfashi a hankali, matso da tasa fuskar yayi gaf da tata, harsuna iya jiyo hucin numfashin juna,  bakinsa ya buÉ—e haÉ—e da kamo lip É—inta na Æ™asa, yasoma sucking a hankali,  tsikar jikinta ne, ya shiga tashi, take wani shauÆ™i yasoma ratsa ta,  kusan mintuna 6 yana sucking lip É—inta, kafun ya tsagaita yashiga maida numfashi.  Ganin haka yasanya ta sanya hanunta akan wuyansa, haÉ—e da sanya bakinta acikin nasa, ta laluÉ“o harshensa, tasoma masa shan sweet,   yanda take sucking É—insa tausassun laɓɓanta na kai komo cikin bakinsa shine abun da ya Æ™ara hautsina tunaninsa,  tsananin sha’awarta ne yasake ninkuwa acikin zuciya da jikinsa.  Hannayensa yasanya yana Æ™oÆ™arin buÉ—e gaban rigarta. Kukan Asad ne ya katsesu daga duniyar da suke Æ™oÆ™arin faÉ—awa, gaba É—aya su sunma manta da cewa yana É—akin. shikuwa Asad chocolate É—insane yafaÉ—i Æ™asa, shiyasa sa fashewa da kuka.

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri Zahrah ta Æ™arasa garesa haÉ—e da É—aukan chocolate É—in  ta danÆ™amasa a hanunsa, dawo da kallonta tayi ga Doctor dake tsaye idanunsa sunyi ja. Murmushi tasakar masa, tare da takawa ta Æ™arasa garesa, hanunsa ta kama ta zaunar dashi akan gado, kayan jikinsa tashiga rage mai, saida ya rage dagashi dai dogon wandon suit É—in dake jikinsa.    Bathroom tashiga ta haÉ—a masa ruwan wanka.  saida taga shigansa wankan kafun ta É—auki Asad suka fice daga cikin É—akin, wajen Haulat tamaida Asad, itakuma ta wuce kitchine. Milk Shake tahaÉ—a masa, haÉ—e da É—aukan wani tray na tangaran me kyau ta yayyanka kayan marmarin aciki.   É—aukan É—an madaidaicin tray É—in tayi, tare da cup É—in da  milk shake É—in ke ciki, ta nufi É—akinta.

Harya fito a wankan yana zaune akan gado, dagashi sai long jeans ajikinsa,  tanashigowa cikin É—akin, ya kafeta da  tsumammun idanunsa,  É—an madaidaicin stool ta jawo ta É—aura kayan hanunta akai, zama tayi akusa dashi. Da kanta tasoma bashi fruit É—in abaki.  Yanacin fruit É—in amma gaba É—aya hankalinsa na ga breast É—inta da suka bayyana kansu ta saman rigar dake jikinta.  Sarai ta kula da cewa hankalinsa naga breast É—inta, hakan yasa da gangan ta kuma saÉ“ule wuyar rigan don yagani da kyau.  Tana kammala bashi fruit É—in, aka soma Æ™iran sallan Magriba,  alwala yayi haÉ—e da É—aura brown É—in jallabiya akan wandon dake jikinsa yafita zuwa masallaci, itama alwalan tayi, ta gabatar da sallah, bata tashi akan sallayan ba har saida tayi sallan isha.   Wanka takuma yi, yanzu kam wata fitinanniyar sleeping gown ta sanya wacce iyakarta guiwa,  turarenta da tasan yana tafiya da imaninsa tashafa, haÉ—e da É—aukan wani wanda Æ™amshinsa ke haifar da kasala, tashafa aÆ™asan breast É—inta dama duk wani lungu da saÆ™o na jikinta. 

Tana tsaye agaban dressing mirror É—in yashigo cikin É—akin, dawowarsa daga masallaci kenan.

Lumshe idanunsa yayi haÉ—e da buÉ—ewa,  idan yabiyewa Zahrah zata zautar dashi ne kawai, gaba É—aya yawani zama soko akanta, kullum Æ™ara kyau da cika take, sannan kuma duk kwanan duniya Æ™ara fito da wani sabon salo take, wanda take rikitasa da su,  ga tarin soyayyarta dake Æ™ara wanzuwa acikin jini da jikinsa, shikansa baisan wani irin so yakeyi mata ba, amma yayi amanna da cewa, bayan Zahrah babu wata,  ita kaÉ—aice bata da tamka, ita ta musammance acikin matan duniya. baisan wata mace ba aduniyarsa bayan ita, amma kuma yanaji ajikinsa cewa, yayi dace, yakuma samu gamdakatar wanda bayajin akwai wata wacce zata kama Æ™afarta.

Ƙarasowa yayi gaban mirror ɗin ya rungumeta ta baya haɗe da kwantar da kansa abayanta, yana sauƙe ajiyar zuciya, iya ƙamshin dake fita ajikinta ma kaɗai, ya isa yasanya masa feeling, ina kuma ga ya taɓa lallausan fatar jikinta.

Hanu tasanya ta shafi gefen fuskarsa, haÉ—e da É—an zame jikinta daga nasa.  Hijab É—in dake aje kan gado ta É—auka, haÉ—e da zurawa ajikinta.

“Hubby Nasan Babyna yayi bacci, banaje na dubasa” tafaÉ—i haka tana me nufar hanyar fita daga É—akin.

Bai iya ce mata komaiba harta fice.

Tanazuwa É—akin Asad É—inkuwa tasamu yayi bacci akan lallausan gadonsa,  yayinda Haulat mai kula dashi itama tuni tayi bacci, zama tayi ta tofeshi da addu’a, haÉ—e da gyara masa kwanciyansa. Rage musu hasken wutan É—akin tayi kana ta yi ficewarta.

Tana shiga tasamesa tsaye dagashi sai towel É—aure a Æ™ugunsa, yayinda jikinsa ke É—auke da danshin ruwa, da’alama ruwa ya watsa wa jikinsa.    Cire hijab É—in jikin nata tayi, ta nufo inda yake,   atare suka sakarwa juna murmushi,    jawota yayi haÉ—e da mannata da Æ™irjinsa,  hanunsa yasanya acikin gashin kanta, murya asanyaye yace.

“Nayi kewarki dear, muna gida É—aya amma yau two days kenan banji É—umin jikin ki ba!”  yaÆ™are maganar yana me cusa kansa acikin wuyanta.    Lokacin da sajensa ya taÉ“a fatar wuyanta,  saida taji wani yarrrrrr ajikinta,   hanunsa yakai kan cikinta, ya warware igiyan da tazamo mahaÉ—in rigar dake jikinta, aikuwa take rigar ta buÉ—e ta gaba, hannayensa duka yasa ya juyo da ita suka zamana suna fuskantar juna.    kallon juna suka shigayi cike da shauÆ™i, hanunta ta É—aura akan chest É—insa tana shafawa a hankali, lumshe idanunsa yayi haÉ—e da laluÉ“ar fuskarta ya haÉ—e bakinsu waje É—aya.   A hankali suke sucking lips É—in junansu, suna fidda wani irin numfashi mai sauti,   cike da nutsuwa ya zame gaba É—aya rigar jikinta, tayi Æ™asa,   hannayensa yaÉ—aura abayanta yashiga shafawa yana yawo dasu ahankali har ya gangaro zuwa kan Æ™irjinta, still bakinsu na haÉ—e dana juna suna bawa kansu hot kiss.   Saida sautin numfashinsu dukansu ya sauya, alokacin da hanunsa suka shiga yawo akan breast É—inta, cire bakinsa yayi acikin nata kana ya gangaro da bakinnasa zuwa wuyanta,  tsotseta yake son ransa, yana fidda wani irin numfashi dake nuna yana cikin tsananin mayen sha’awa dakuma sonta.   Æ™afafunsu ne suka soma gazawa wajen É—aukarsu,  tana acikin Æ™irjinsa suka nufi kan bed.  MaÆ™alewa tayi ajikinsa, ahankali take goga masa breast É—inta akan chest É—insa, hakan kuwa sosai ya ruÉ—asa,   tana kwance aÆ™asansa yayinda shikuma ya yi mata rumfa da faffaÉ—an Æ™irjinsa, sukansu basusan awacce duniya suke ba,  gaba É—aya sun zauce,  alokacin daya gama ratsa cikin jikinta, sai da wasu hawaye masu É—umin gaske suka gangaro daga cikin idanunta, sam hawayen  bana baÆ™inciki ko damuwa bane, wannan hawayen sukan fitane alokacin daya dace, lokacin da mutum yakasance baya acikin duniyarsa, irin wannan hawayen sukan fitane, alokacin da mutum wanda ke acikin tsananin magagin sha’awa da kuma so yasamu abun dayakeso a lokacin daya kusa zautuwa,  wannan hawayen na musamman ne, wannan hawayen sukan fitane alokacin da mutum yasamu cikar muradinsa.

Yanayin da suka samu kansu aciki, yakasance me daÉ—i agaresu,  gaba É—aya daren sun Æ™are shi ne cikin soyayya, yayinda Zahrah keta zuba masa shagwaÉ“a shikuma ya dage sai lallaÉ“ata yake, koda sau É—ayane bayason abun dazai É“ata ranta.  Gaba É—aya yagama shagwaÉ“ata, yamai da ita saikace wata Æ´ar 7 year.    Yanzuma shagwaÉ“an tagama zuba masa,  tana kwance luf acikin Æ™irjinsa, yayinda shikuma ya kafeta da idanunsa, dake É—auke da mayen sonta.   Kissing É—inta yayi akan goshinta, haÉ—e da maida duka hannayensa cikin Æ™irjinta, har yau jinta yake kamar sabuwar budurwa, koda yaushe Æ™ara shiga zuciyarsa take, sannan babu wani abu na jikinta daya sauya daga mai kyau zuwa marar kyau, breast É—inta har yau sunanan a yanda suke babu wani abu daya samesu,  hakan nema yasa ako da yaushe yake nanuÆ™e mata, ya murzata son ransa, atunaninsa bacci  take saboda haka yayi Æ™asa da kansa zuwa Æ™irjinta, wani numfashi ta sauÆ™e alokacin da taji hucin numfashinsa, na sauÆ™a akan Æ™irjinta ahankali,   dama baccinta baiyi nisa ba,  duka hannayenta ta cusa acikin gashin kansa, tana yamutsawa slowly,  ahaka har bacci ya É—aukesu  dukansu..

(Nima bacci nakeji, kuyi haÆ™uri typing É—in dare nayi,  yanzu nagama kuma dare yayi sosai, saboda haka da safe idan Allah Yakaimu zan sake muku shi. Please kubani Vote sosai a wannan page É—in, Inason wannan page É—in, da wanda zanyi gaba sufi kowanni page na baya yawan vote, next page na Zaidun mune.)

Rayuwa tana tafiya ne da gudu gudu batare da wani mai rai ya ankara da hakan ba, akullum kwanan dunia shekarunmu Æ™ara Æ™arewa suke, sannan Æ™ara girma muke, sake kusantar mutuwa muke.   Daga kwana É—aya anzarce kwanaki daga kwanaki anwuce satuttuka daga satuttuka anwuce watanni daga watanni anÉ—arawa shekaru. Haka yake ako da yaushe, acikin waÆ´annan kwanaki da shekarun kuma abubuwa ne masu yawa suke faruwa  suke kuma shuÉ—ewa, wani yasamu cigaba wani kuwa yasamu naÆ™asu, wani ransa yayi baÆ™i wani kuwa ransa yayi fari Æ™al.  To hakance takasance acikin labarin ZAID da ZAHRAH,  shekaru sunja rayuwa ta haÉ“aka,  shekaru sama da biyar kenan yanzu,  har lau kuma rayuwa suke cike da farinciki….+

“MY SOUL!  MY SOUL!!  MY SOUL!!!”    muryarsa daketa kwaÉ—a Æ™iran sunan MY SOUL ta Æ™araÉ—e ilahirin farfajiyan gidan, tundaga cikin katafaren falonsa, keta kwaÉ—a Æ™iran har ya kawo compound É—in gidan.

Sanye yake da wando track suit sai kuma wata farar t-shirt Æ™afarsa sanye suke cikin wani takalmi mai igiyoyi.     Tsayawa yayi haÉ—e da sanya hannayensa akan Æ™ugunsa yana fesar da numfashi, yayinda yaketa baza idanunsa, ko zai hango wacce yake nema.   Babu wani abu daya sauya ajikinsa, sai ma kyau da hasken fata daya Æ™ara, ga wani haÉ—aÉ—É—en Æ™asumba daya daÉ—a Æ™awata kyakkyawar fuskarsa, lallai shiÉ—in namiji ne cikekke, wanda zai É—auki hankalin duk wata mace data gansa, ya haÉ—u sosai da sosai, duk da cewa shekarunsa sun Æ™aru akan nada, amma duk da haka yana nan ayanda yake, kyawunsa da kwarjininsa suna nan,  haryanzu shiÉ—in mutum ne mai tsananin son gayu, sam bayason Æ™azanta,  komai nasa me ajine.  ZAID kenan namijin dayazamo abun kwatance acikin sauran mazaje, namijin daya iya jure dakon soyayya me tsananin zafi, namijin daya zamanto sadauki, akan soyayya.

Sake gyara tsayuwarsa yayi, haɗe da ƙara furta ƙiran sunan

“MY SOUL”

Da gudun gaske wata kyakkyar yarinya wacce bazata wuce 6 year ba ta Æ™araso tsalle É—aya tayi ta haye bayanshi,   lumshe idanunsa yayi, alokacin dayaji an É—ale kan bayansa, yasan babu wani ko wata da zaiyi masa wannan aikin idan ba MY SOUL É—insa ba.    Hanunsa yasanya ya jawota daga bayansa, zamewa yayi akan guiwowinsa haÉ—e da É—aura duka hannayensa akan kafaÉ—unta. 

“MaÆ™oshina saura kaÉ—an yafashe My Soul duk kuma akanki ne, kinaji inata Æ™iranki shine kikaÆ™i ki amsa ko?”  tamkar wani Æ™aramin yaro shagwaÉ“aɓɓe haka ya faÉ—i maganar.

Dariya  fara kyakkyawan yarinyar da yanayin fuskarsu ke shige da tata tayi, haÉ—e da sanya hanunta akan dogon hancinsa. 

“I’am Sorry My Papa luv, ina cikin garden ne, kuma na amsa amma bakaji ba” yarinyar tafaÉ—a tana É—an juya idanunta.

STORY CONTINUES BELOW

Murmushinsa mai kyau yayi mata haÉ—e da jawota jikinsa ya rungume.

“Bazaki daina juya idanunki idan kina magana ba ko?” yatambayeta yana me shafa bayanta ahankali.

“Papa luv banice fa nakeyin hakan da gangan ba, nima banasanin najuya idanuna idan ina magana!” tafaÉ—i haka a shagwaÉ“e hartana É—an buga Æ™afafunta a Æ™asa.  

Lumshe idanunsa kawai yayi yana maijin Æ™arin Æ™aunar Æ´artasa na ratsa jini da tsokan sa,   sosai yanayinta ke kama dana Zahrah babba, haka kuma É—abi’ar Zahrah ne wani lokaci idan tana magana takan juya idanunta, to itama wannan haka ta keyi,  sau da dama idan tana abu, kallon  real Zahrah kawai yakeyi mata,  domin kuwa yanzu da ta Æ™ara girma kamanninta da Zahrah sai ya sa ke fitowa,   baisan wani irin soyayya yakeyiwa  ZAHRAH Æ´arsa ba, gaba É—aya soyayyan da yayiwa Zahrah itace ta dawo kan yarinyar, wani irin so yake yi mata da baida misali, jinsonta yake ako ina na jikinsa,  Zahrah Æ´arsa itace rayuwarsa, itace Hasken sa, itace madubinsa, wacce idan ya duba ransa keyin sanyi, samunta yafiye masa komai aduniya, samunta wani alkhairi da ginshiÆ™i ne acikin rayuwarsa, domin kuwa tunda yasameta, arzikinsa suka yalwata akan nada, shikansa ayanzu baisan iya adadin dukiyarsa ba,  itakanta yarinyar kamfanoni masu tarin yawa ya buÉ—e mata, sosai yake samun alkhairi adalilinta.

“Papa Luv!”  yarinyar ta Æ™irasa murya a sanyaye.

BuÉ—e idanunsa yayi ahankali haÉ—e da sauÆ™esu akan babyn ta sa “Na’am My Soul” ya amsa mata.

Ya mutse fuska tayi haÉ—e da cewa “Yunwa nakeji Papa Luv banyi breakfast ba”

Waro kyawawan idanunsa yayi haÉ—e da  miÆ™ewa tsaye ya sungumeta suka nufi inda zai sadasu da babban falon gidan. 

Tana tsaye agaban dining area tana nunawa hause girl yanda zata shirya musu dining É—in,  tasha adonta cikin wani jan lace me kyau da burgewa, taÆ™ara cika ta zama babbar mace, dagani kai kasan tana murza naira son ranta, domin wani haske ta Æ™ara tayi fat da ita.     Shigowarsu cikin falon suna dariya yasanya ta maida hankalinsu gareta, batasan wannan wace irin soyayya bace ke tsakanin Zahrah da Babanta Zaid, soyyace irin ta bugawa a jarida.

Tana tsaye tana kallonsu suka Æ™araso dining area’n kujera yaja ya zauna akai kana ya É—aura Zahrah akan kujeran dake gefensa na dama, dama kuma haka suke zama koda yaushe.

Murmushi Afrah tayi haÉ—e da cewa “Nashiga É—akinka banganka ba ae, sainayi tunanin kana wajen yin gym, ashe ma kuna tare da Zahrah”

Murmushi kawai yayi haÉ—e da sanya hanu ya shafi kan Zahrah, baitankawa Afrah ba saima duban Zahrah da yayi cike da so yace “Me zan zuba miki?”

“Duk abunda zakaci Babana nima shi zanci!” Zahrah tafaÉ—i haka tana kashe masa idanunta É—aya.

Dariya suka sanya atare haÉ—e da bata hanunsa suka tafa,  abinci yasoma zuba musu da kansa, acikin plate É—aya, dama kuma a yanzu baya taÉ“a cin abinci saida Zahrah, zaiÆ™i ci da kowa amma zaici da ita, kujera Afrah taja ta zauna itama, haÉ—e da soma yin serving É—in kanta, don ta lura babu wani wanda yake ta ita, daga Zaid É—in har Zahrah, su dama kansu kawai suka sani. 

Shida kansa yaciyar da Æ´artasa, itama haka ta dinga basa abincin abaki har ya Æ™oshi,   sama sama suke hira da Afrah, nan ma itace take jansu da hira, amma daba haka ba bazasu kulata ba, ita har mamakinsu ma take, Zahrah sam bata damu da ita ba, kamar ba itace ta haifeta ba, zancenta baya wuce mahaifinta dakuma Momyn Friend É—inta, wanda suke makaranta É—aya dashi.

Tana gama goge bakinta da tissue ta kalli Papa Luv É—innata ashagwaÉ“e tace.    “Please Papa luv yau muje shan ice cream mana!”

“My Soul yau inada aiki, mubari sai gobe mana, kinga fa next week zamu koma U.S.A, akwai abubuwan danakeso nayi kuma kafun mu koma” yafaÉ—i haka bayan ya aje kofin tea É—in dake riÆ™e ahanunsa.

STORY CONTINUES BELOW

Sake shagwaɓewa tare da narke fuskarta tayi, ɗan ƙaramin bakinta taturo gaba haɗe da cewa

“Ae Dan Allah Nace Papa Luv, inaso naje ne!”

“Shikenan zo muje na shiryaki” yafaÉ—i haka yana mai miÆ™o mata hanunsa.

Tsalle ta doka haÉ—e da faÉ—awa jikinsa ta rungumesa, cike da farinciki ta kai masa sunbata akan Æ™uncinsa. 

“Thank You Papa Luv”

ÆŠagata yayi caÉ—ak akan kafaÉ—unsa haÉ—e da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan table, direct suka wuce É“angarensa. 

Kai kawai Afrah ta girgiza haÉ—e da cigaba da cin abincinta, sam abunsu baya damunta, tasaba da hakan, koda yaushe haka suke, kamar tip da taya basa rabuwa.

Shida kansa yayi mata wanka yashiryata cikin wasu riga da wando na jeans masu matuÆ™ar kyaun gaske, naÉ—e mata dogon gashinta yayi a tsakiyar kanta, da wani babban ribbon,  lokaci É—aya kyawunta da tsananin kamaninta da Zahrah suka sake bayyana, shima wanka yayi kana ya shirya kansa, cikin wasu riga da wando masu kyaun gaske,  sosai yayi kyau sai tashin Æ™amshi yake,  Little Zahrah dakanta saida tayaba kyawun da Papa Luv É—inta yayi.  

Yana riƙe da hanunta suka fito harzuwa falo, kallonsa ya maida ga Afrah wacce ta mato akan kallonsa.

“My Wife bazaki zo kirakamu bane?”  ya tambaya.

Murmushi kawai tayi haÉ—e da lumshe idanunta, akasalance tace “Kuje kawai Dear nikam inanan, amma ku tahomin da nawa ice cream É—in”

Hanu Zahrah ta É—aga mata alaman bye bye kana suka fice daga cikin falon.  

Barinta yayi awajen sayan kayan maÆ™ulashe irinsu chocolate da sauransu shikuma ya nufi wajen turaruka.    Tana tsaye ta Æ™urawa wani babban ledan chocolate dake can sama idanu, so take ta É—aukoshi ta sanya acikin kayanta amma kuma wane ita, ya É—arawa tsayinta,  jitayi anrufe mata idanu a hankali,   a iya saninta mutum É—ayane keyi mata hakan,  saboda haka yanzuma tasan cewa shiÉ—inne, dariyan farinciki tasaka haÉ—e da cewa “ASAD!” 

Dariya yayi haÉ—e da sake mata fuska ta juyo zuwa garesa, kyakkyawan yarone wanda bazai wuce 7to8 year ba, yarone fari tas dashi tamkar ajinsin larabawa yafito,     tsallen murna Zahrah tasanya haÉ—e da rungumesa, shima rungumeta yayi cike da jin daÉ—in ganin Æ™awartasa wacce rabonsa da ita yau tsawon sati uku kenan, tun da aka basu hutun makaranta rabonsa da ita..

Cike da É—okin ganinsa Zahrah tace.    “Laaa Asad dama zanganka anan? kaida waye kukazo? nidai nida Papa Luv É—ina mukazo, aibansan zamu sameka anan ba da munzo tunda wuri”

Hanu yasanya ya É—an murÉ—e bakinta cikin halayyarsu ta yara yace “Baki gajiyawa da Surutu Soul ina Papan naki?”  yaÆ™are maganar yana me baza idanunsa.

“Asad me kakeyi anan, bacemin kayi chocolate zaka É—auka kazo ba?”  

Daga Asad har Zahrah atare suka juya suna kallon mai maganar.     Kyakkyawar mace wacce ta amsa sunanta mace mai aji da kamala, sanye take da abaya gown black colour ta yane jikinta da mayafin abayar, komai nata na burgewa ne, kallo É—aya zaka mata, kakuma son sakewa domin ba irin Æ™ananan matannan bane, duk da cewa bata da wani jiki, haka kuma bata wani sanja ba, har yanzu  tana nan da kyawunta mai fusgar hankali.

“Itace Mamanka?” little Zahrah tafaÉ—i haka Æ™asa Æ™asa tana kallon Asad.

Kai Asad ya kaÉ—a mata alamar “Eh” 

Da gudunta ta Æ™arasa wajen Momyn Asad ta rungumeta,  cikin surutunta daya zame mata sabo tace.

“Oyoyo Mom Asad, dama inataso mu haÉ—u dake, amma bakya zuwa school É—inmu, Dad É—in Asad ne kawai yake zuwa,  ni da Asad abokaine sosai, kuma dan Allah kudawo U.S.A kunji, muma kunga can zamu koma” tunda little Zahrah tafara zuba bata tsagaitaba sai yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

Hakanan Zahrah taji yarinyar ta burgeta, durÆ™usawa tayi agaban yarinyar haÉ—e da sanya hanu ta shafa fuskarta, hakanan taji bugun zuciyarta ya Æ™aru, “Idanunta ne ke mata gizo kokuwa dagaske kamanninta take hangowa akan fuskar yarinyar?” tambayar da tayiwa kanta kenan, cike da son sanin amsa.

Murmushin da Little Zahrah tayiwa Mom Asad ne yayi sanadiyar kusan rugujewar zuciyarta.    “ZAID” tafurta sunan acikin maÆ™oshinta da kuma kan laɓɓanta, sai dai kuma amon sauti baifito ba.

“My Soul”

Taji wata murya dabazata taɓa mantawa da ita ba tafaɗa.

Dagudu Little Zahrah takamo hanun Papa Luv É—inta dake tsaye.

“Yauwa Papa zokaga Momyn Friend É—ina Asad, wacce nafaÉ—amaka tana da kirki, tana bawa Asad abun daÉ—i, shikuma yana bani.” 

Idanunsa ya sauÆ™e akan bayan wata mace dake durÆ™ushe a Æ™asa tabasa baya,   cigaba da jansa little Zahrah tayi harzuwa inda Mom Asad ke durÆ™ushe amma bata É—ago fuskarta ba.

“Momyn Asad, ga Papa Luv É—ina nima, tare dashi mukazo” little Zahrah tafaÉ—a cike da kauÉ—i.

Ahankali ta É—ago manya manyan idanunta ta ta kalli mutumin da Zahrah ke cewa shine Papa Luv É—inta.

Atare bugun zuciyarsu suka tsananta, take wani irin abu ya tsarga jiki da jijiyoyinsu.

Da Æ™yar ta’iya daure zuciyarta ta Æ™aÆ™alo murmushi.

Shima murmushin yayi haɗe da sunkuyar da kansa ƙasa.

Hanun Asad ta kama jiki asaɓule ta juya daniyar barin wajen.

“Asad” taji muryar Zaid yaÆ™ira sunan yaron.

Tsayawa sukayi cak amma ita bata juyo garesa ba,  takowa yayi har inda suke ya durÆ™usa haÉ—e da kamo hanun Asad. 

“My dear ya hutu?”  yatambayi Asad.

“Lapiya”  Asad yabashi amsa yana murmushi.

Kallonta yayi haÉ—e da cewa “Dama Asad É—anki ne?” 

Kanta kawai ta jinjina masa alamar “Eh” gaba É—aya ta Æ™osa subar wajen shikuma yakama Asad ya riÆ™e Æ™am.

Murmushin dake Æ™arawa  fuskarsa kyau yayi haÉ—e da cewa “Fine boy, natayaki murnan samun wannan kyakkyawan yaron,  amma kuma saidai inajin tsoron abunda zai faru anan gaba,  Asad abokin Zahrah na ne, idan nan gaba yasan nayiwa mahaifiyarsa laifi mai girma yakike tunanin zai É—auki abun?” 

Kanta ta girgiza masa haÉ—e da É—anyin murmushi.  “Kada kace haka Zaid, abu idan ya wuce yana da kyau amantasa, afuskanci gaba, banafatan Asad yasan abun da ka aikata agareni” É—an numfasawa tayi tare da kama hanun Asad.     “Sauri nake zanwuce gida”  kallonta ta mayar ga Little Zahrah da ta Æ™ura mata idanu tun É—azu, murmushi Zahrah tayi mata, haÉ—e da shafa kanta, sosai taji son yarinyar acikin ranta.

“Allah ya albarkaci rayuwarki Rabin raina”    Tana faÉ—an haka taja hanun Asad suka bar wajen.

Saida ta É“acewa ganinsa kafun yasaki wani murmushi haÉ—e da cusa duka hannayensa acikin aljihun wandon jeans É—in dake jikinsa.   Little Zahrah ce tataho zuwa garesa haÉ—e da maÆ™alewa acikin jikinsa, murya asanyaye tace “Papa dama kasan Mommyn Friend ne?”

Murmushi yakumayi akaro na sau babu adadi,  hanunta yakama suma suka bar wajen, batare daya bata amsar tambayar da tayi masa ba.

Tunda suka shiga mota batace da yaronnata Æ™alaba,  shima baitanka mata ba, domin dama shi hakanan yake ba mutum ne mai son yawan magana ba, yana da miskilanci wani lokaci.  Ganin da yayi cewa kamar Momyn nasa na cikin damuwa ne yasanyashi gyara zama haÉ—e da cewa.

“Momy wani laifi ne Papan Friend yayi miki?  naji kamar yace wai bayaso muji ko mu sanine oho”

STORY CONTINUES BELOW

Harara ta watsa masa, hakan yasashi yin gum da bakinsa, shidama gulmace ke cinsa, da yasani ma da baitambaya ba.

Tana isa gida tasamu Husnah da Areefa matar Asad, sunzo suna jiranta, sam basu sanar da ita zuwansu ba,  batayi mamakin ganinsuba kamar yanda tayi mamakin  ganin yanda aka sauya mata tsarin falonta, aka mamaye gaba É—aya falon da decorations masu kyaun gaske,  tsayawa tayi tana Æ™arewa falon nata kallo.

“Happy Birth Day to you my dear Wife!!!” 

muryar Dr.Sadeeq ta karaÉ—e ilahirin kunnuwanta, kallonta ta maida inda taji muryartasa na fitowa.

Fitowarsa daga É—aki kenan yasha ado cikin riga da wando na jeans masu matuÆ™ar kyau.  Murmushi tasakar masa,  gaba É—aya ita tamanta da cewa yaune birth day É—inta.

Hanunta yakama suka nufi wani É—an keÉ“eɓɓen waje dake cikin falon, sosai aka Æ™awata wajen da decoration’s  mai kyau,  kusan suman tsaye tayi alokacin dataga irin hidiman da mijinnata ya shirya mata, manya manyan cake masu kyau da tsada yasa akayi mata har guda uku, ga kayan ciye ciye dana shaye shaye, tsananin farinciki da Æ™aunarsa ne suka mamaye zuciyarta, juyawa garesa tayi ta rungumesa, haÉ—e da cusa kanta acikin Æ™irjinsa tana shaÆ™an daddaÉ—an Æ™amshin jikinsa.  

“Thank you so much my lovely husband!!!” tafaÉ—a cikin sanyi yayinda Æ™aunarsa ke Æ™ara ratsa zuciyarta.

“Babu godiya atsakaninmu My Wife kina da babban matsayi a wajena, keta musamnan ce, inasonki da duka zuciyata!” Dr.Sadeeq yafaÉ—i haka yana Æ™ara matseta acikin Æ™irjinsa.

Kwantar dakanta tasakeyi ajikinsa cike da Æ™aunarsa, haÆ™iÆ™a tasamu duk wani abu da takeso, farinciki, soyayya, da kuma zaman lafiya, sosai Doctor ke bata kulawa, bayason É“acin ranta ko kaÉ—an,  yana Æ™aunarta har acikin jininsa, itama kuma tana Æ™aunar mijinnata sosai, ayanzu yafiye mata kowa da komai,  yabata farinciki haka kuma yabawa iyayenta, yamantar dasu komai na É“acin rai da talauci, ya wadatasu da komai na rayuwa, bata da wani  TAURARO sama da shi, shiÉ—in na musamman ne arayuwarta, koda sau É—ayane bata taÉ“a yin danasanin kasantuwarsa amatsayin mijinta ba, ko da kowa aduniya zai juya mata baya, tasan banda Mijinta Haskenta Abun Alfaharinta.    Rayuwarta tayi mata daÉ—i akoda yaushe saidai tace ALHAMDULILLAH..

***

Yana tsaye agaban dressing mirror  yayinda little Zahrah ke tsaye agefensa, tana shan chocolate, Afrah ce tashigo cikin É—akin hanunta É—auke da kofin coffee wanda take haÉ—amasa kullum daren duniya.

MiÆ™o masa kofin coffee É—in tayi, ya amsa yana murmushi, aje kofin yayi haÉ—e dasanya hanu ya jawota jikinsa ya rungumeta, bakinsa ya kai dai dai saitin kunnenta, ahankali yace “Inasonki Æ´ar lukutar matata!”  

Dariya Afrah tasanya haÉ—e da cewa “Nima inasonka É—an lukutin mijina” 

Murmushi kawai yayi haÉ—e da sanya hanu yashafi kumatunta.

“Nima inasonka Papa na!!”  little Zahrah dake tsaye a gefensu tafaÉ—i haka da Æ™arfi.

“SON SO nake miki farincikina, idan babuke acikin rayuwata, to babu wani haske dazan sake gani, Allah yarayamin ke na aurar dake ga miji na gari!!” yafaÉ—i haka yana dariya, acikin zuciyarsa kuwa, har yau tsananin danasanin yanda halayansa suka kasance a baya yake,  yayi danasani sosai, har gobe kuma akan danasani yake, bazai kuma taÉ“a daina Istigfari ba har Æ™arshen rayuwarsa.

Duk da Little Zahrah  bata fahimci me maganganunsa ke nufi ba, amma tasan cewa mace da namiji suna aure, domin wancan satin daya wuce ma sunje auren Æ™anwar momynta.

Dagudu taÆ™araso ta rungumeshi,  Æ™asa Æ™asa tace  “Nidai ko zanyi aure bakowa zan auraba sai Friend, aishima yanasona ko Papa?”

DurÆ™usawa yayi agabanta cike da soyayyarta yace “Yanasonki mana, ai aduniya babu wani wanda zaiÆ™i me wannan kyakkyawar fuskar, ke É—in ta musammance My Soul!”

DaÉ—ine yakama Zahrah, sake rungume mahaifinnata tayi, aranta tana Æ™ara Æ™aunar papan nata, domin adunia tasan bayan shi babu wani wanda zaiyi mata irin wannan soyayyar dayakeyi mata a yanzu……

*** *** ***

Duka ahali biyun rayuwarsu ta miÆ™a komai suna yinshine cikin farinciki da jin daÉ—i, akowacce rana ta duniya Æ™ara Æ™aunar junansu suke, saidai muce  MASHA ALLAH.

*Alhamdulillah anan nakawo Æ™arshen labarin SHU’UMIN NAMIJI ina fatan zakuyi aiki da abun dayake dai dai aciki, inda nayi kuskure kuma Allah Ubangiji yayafemin, nagode sosai da sosai masoyana, haÆ™iÆ™a kunbani haÉ—in kai nakuma ji daÉ—in haka Allah Yabar Ƙauna,   waÆ´anda na É“atawa rai don Allah kuyi haÆ™uri, balaifina bane, haka labarin yake, haka kuma Æ™addaran  ZAID  da ZAHRAH yake, babu wanda ya isa sauya Æ™addaransa.

*Ku ci gaba da bibiyana Insha ALLAH Zakujini da labarai kala kala wanda ina da tabbacin zasuyi muku daÉ—i, Ina muku SON ƘAUNA!!!  Insha ALLAH Ina zuwa muku da wani sabon labarin wanda zai É—are ma Shu’umin Namiji, ina kuma da tabbacin cewa zaku ji daÉ—insa sosai, na katse muku labarinne saboda wani babban uzuri.*