SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 13 BY FATYMA SARDAUNA

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 13 BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 13 BY FATYMA SARDAUNA                     Www.bankinhausanovels.com.ng  Yana zaune acikin falon, taturo ƙofa tashigo bakinta ɗauke da sallama, cike da mamaki yake kallonta. “Bakije gidan Ƙawartaki bane?” ya tambayeta yana me tsareta da kyawawan idanunsa. Murmushi tayi haɗe da ƙarasowa cikin falon, zama tayi gaf dashi, haɗe da ɗaukan hanunsa ta ɗaura akan cinyarta.   “Naje nasamu batanan, kuma dama banaso nabarka kai kaɗai agida, shiyasa na dawo” tafaɗi haka tana me ƙara faɗaɗa murmushinta. Kansa yajinjina haɗe da ɗaukan goran ruwan dake  aje a gabansa, yakai bakinsa,  kallonsa take tanaso tafaɗa masa abun dake cikin ranta, amma kuma tsoro takeji saboda batasan taya zai ɗauki maganar ba. Matsewa kawai tayi haɗe da sanya hanunta ta saƙalo hanunsa,  fuskarsa takafe da ido kana tace “Yau nahaɗu da Zahrah” Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, cike da tsananin mamaki yace “Wace Zahrah?” “Zahrah wacce kasani, wacce kuma tunaninta ke maƙale acikin zuciyarka, babu dare babu rana…