SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA

SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA                     Www.bankinhausanovels.com.ng  Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi ɗare ɗare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haƙora yake kai kace anmasa kyautar ƴan kuɗaɗe ne.+ Dakansa ya buɗe mata murfin motar ɓangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige ɓangaren driver haɗe da mawa motar key… Tunda suka ɗau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba ɗaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya, akai akai yake satan kallonta tacikin madubi.. A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu, dai dai bakin ƙofar hall ɗin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall ɗin zasu gudanar da lecture. A hankali ta buɗe murfin motar ta fito kafaɗarta ɗauke da jakar makarantar ta, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa ta nufi cikin hall ɗin kai tsaye, ko wai gens…