SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA
SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA
Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna fita kuwa ta iske Baffa yayi Ιare Ιare agaban motar Dr Sadeeq sai washe haΖora yake kai kace anmasa kyautar Ζ΄an kuΙaΙe ne.+
Dakansa ya buΙe mata murfin motar Ιangaren gidan baya, cikin sanyin jiki ta shiga cikin motar, kaitsaye yashige Ιangaren driver haΙe da mawa motar key…
Tunda suka Ιau hanyar makarantar tasu Baffa ke faman zuba kamar wani kurna, yayinda Doctor Sadeeq ke amsa masa jefi jefi, domin hankalinsa gaba Ιaya yana ga Zahrah, wacce ke zaune tayi jigum a gidan baya, akai akai yake satan kallonta tacikin madubi..
A haka dai harsuka iso cikin makarantar tasu, dai dai bakin Ζofar hall Ιin da zasu gudanar da lecture yau, ya yi parking motar tasa, domin dama already ansanar dashi cewa yau a wannan hall Ιin zasu gudanar da lecture.
A hankali ta buΙe murfin motar ta fito kafaΙarta Ιauke da jakar makarantar ta, cikin takunta mai Ιauke da nutsuwa ta nufi cikin hall Ιin kai tsaye, ko wai gensu batayi ba, tanashiga hall Ιin kallo yadawo kanta, take taji wani irin muguwar faΙuwar gaba haΙe da karyewar zuciya, gani take tamkar kowa yana ganin abun da yafaru da ita rubuce akan goshinta.
Karab idanunta suka sauΖa akan Husnah wacce take faman aikin haΙa wasu takardu dake gabanta. wani irin sanyi taji zuciyarta tayi sakamakon ganin husnah, domin kaf makarantar bata mu’amala da kowa bayan husnah, da matuΖar farinciki Husnah ta rungume Zahrah, domin koda wasa batayi tunanin ganinta ba.
“Kamar mafarki nakeyi gaskia naji daΙi sosai Ζawata!” Husnah tafaΙa cike da tarin farinciki.
Zama sukayi a tare dai dai lokacin Sir Bature yashigo cikin hall Ιin, tsit haka ajin ya Ιauka ana ta sauraran lecture Ιin dayake yi musu, a zahirin gaskia tanajin abun da yake cewa, amma kwata kwata bata fahimtarsa, awa biyu suka Ιauka chur suna lecture, kafun daga bisani yafita daga ajin, gyara zama Husnah tayi haΙe da mai da kallonta ga Zahrah cike da kulawa tace ” Yanzu ina likitan yake ?”
Ajiyar zuciya Zahrah ta sauΖe haΙe da cewa ” Ba maganar Doctor bace damuwata Husnah, babban damuwata shine gani nake tamkar abun da Zaid yamin yana rubuce a gaban goshina, Husnah gani nake tamkar kowa yasan abun dake damuna !” Zahrah taΖare maganar cikin raunin zuciya.
” Kada kice haka Zahrah, babu wanda yasan abun da yafaru dake, kada ki Ιaga hankalinki Ζawata kinfasan kowa da irin tasa Ζaddaran, kuma zuwa yanzu na tabbatar kin mai da al’amuranki ga Allah, shima Zaid nasan kinbarsa da Allah “
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi mai ciwo Zahrah tayi haΙe da kallon Ζawarta ta, cike da Ζuna tace ” Banda wata hanya wanda tawuce barinsa ga Allah, nasan nan bada jimawa ba Allah zai bimikin haΖΖina ” taΖare maganar cikin raunin zuciya,
Hannayenta Husnah ta kama suka fice daga cikin ajin, kai tsaye cafeteria suka nufa don cin abinci. Balaifi sosai tasamu nutsuwa a yau Ιin domin kuwa Husnah bata barta tayi kaΙaici ba. Ζarfe 5 dai dai suka fito daga cikin lecture Ιin Ζarshe na ranan yau Ιin, kasan cewar ta kwana biyu bata zo makarantar ba, sai take jinta gaba Ιaya duk ta gaji, cikin nutsuwa take takunta yayinda kanta ke duΖe a Ζasa, ba abun da zuciyarta keyi banda bugawa, gaba Ιaya tsoron fita daga cikin school Ιin takeyi, gani take tamkar tana fita za’a kamata, da Ζyar take iya Ιaga Ζafafunta, dagani kasan bason tafiyar take ba. a hankali ta matsa gefe, haΙe da waigowa don ganin waye wannan ya matsa mata da horn Ιin motarsa, karab idanunta suka sauΖa akan sa, kasancewar gilasan motar tasa gaba Ιaya a sauΖe suke, sam batayi tsammanin ganinshi ba, murmushi yasakar mata haΙe da cewa ” Da baki matsaba ai dana take ki !” yafaΙi maganar cikin yanayin tsokana, Ιan guntun murmushi itama tayi haΙe da taΙe baki, “ai idan haka ta kasance zanfikowa jin daΙi ” Zahrah tafaΙi hakan da iya gaskiyarta.
“Shigo mutafi!” yafaΙa cikin tsare gida.
Saurin kallonsa tayi bakinta Ιauke da tarin tambayoyi, amma kuma takasa koda motsa bakinta ne balle ta furta wata kalman.
“Kintsaya kina kallona, ba dole idan bazaki bini ba, saina yi tafiyata!” yaΖare maganar yana mai niyar tada motar tasa.
Da sauri ta zagaya haΙe da buΙe murfin motar, gefen mai zaman banza ta shiga haΙe da tamke fuskarta tamau tamkar wanda yagayamata magana marar daΙi.
Da Ζyar ya iya Ιoye dariyan dake cinsa, domin kuwa tsoro ya hango Ζarara akan fuskar Zahrah, “NaΙauka ai zakijamin ajine, da sai na tafi na barki ba ruwana!” yafaΙi hakan cike da shauΖi.
Harara ta watsa masa haΙe da sake turo baki gaba, cike da shagwaΙa wacce batasan tayi ba tace “Nifa idan surutu zakamin ka sauΖeni nayi tafiyata”
Yanzu kam kasa Ιoye dariyarsa yayi saida ya dara kafun ya ce ” Bazan sauΖe kiba ai bani na Ιauko ki na saki ba, zaki iya fita da kanki ma, ai nasan ke jaruma ce zaki iya kare kanki ako da yaushe, har ma zaki iya shiga cikin ko wani abun hawa da Ζwarin guiwarki !”
Saurin kallonsa tayi domin kuwa sarai ta fahinci inda maganganunsa suka dosa, wato dai shima ya hango zallan tsoron dake kwance akan fuskarta.
“Shikenan tunda haka kace” tafaΙi maganar tana mai ΖoΖarin buΙe murfin motar ta fita.
“Haba Ζ΄ar Ζanwata, nifa wasa nake miki, kiyi haΖuri ki bari na kaiki gida kinji ko!” Doctor yafaΙi maganar cikin lallashi, domin yafahimci cewa saurin fushi ne da’ita.
A cikin zuciyarta tayi hamdala, sakamakon hanata fita daga motar da yayi, domin dama burga ce kawai tsoron dake cikin zuciyarta bazai barta ta iya tafiya ba, duk runtsi tafiso shiΙin ya kaita domin tafi yarda dashi fiye da kowa a yanzun..
Kwantar da bayanta tayi akan kujeran motar haΙe da lumshe idanuwanta, gaba Ιaya jinta take a gajiye, ga wani irin ciwon kai dake damunta, a hankali take buΙe idanunta, a zabure tatashi zaune sakamakon ganin da tayi Doctor ya nufi wata hanyar da ita saΙanin hanyar gida.
“Inazaka kaini !” TafaΙa a razane, kuma cikin yanayin tsoro,
“Saidake zanyi!” Yayi maganar babu alamar wasa akan fuskarsa.
“Dan Allah kayi haΖuri ka sauΖeni, ka barni naji da duhun dake cikin rayuwata, kada ka Ζaramin wani bala’in dan Allah!!” tuni hawaye sungama wanke fuskarta.
Wani irin kallo Doctor yayi mata haΙe da sakin murmushi bai kuma sake ce da ita komai ba, saima maida hankalinsa da yayi ga tuΖin da yake,
Yanzukam kuka mai sauti ta sanya haΙe da soma cewa ” Dan Allah kada ka sake cutar da rayuwata, zan iya amincema ka kasheni amma bazan iya jure wa ba, idan kaci mutumcina, wlh na yarda ka wurgani kan titinnan mota ta taka ni, amma dan Allah kada kamin komai!!” taΖare maganar cikin matsanancin kuka mai taΙa zuciya. Daidai lokacin suka iso gaban wani makeken mall wanda yagaji da Ζawatuwa,
yana parking motar baiko kalletaba yayi saurin ficewa daga cikin motar haΙe da dannawa gabaki Ιaya Ζofofin fita a motar luck, domin yasan dole zatayi ΖoΖarin fita daga cikin motar,
STORY CONTINUES BELOW
Kuka sosai Zahrah keyi haΙe da sanya Ζarfinta tashiga dukan glass Ιin motar, tana mai ihun neman taimako amma babu kowa a wajen balle tasaran za a temaketa, domin kuwa wajen parking space ne.
“Ashe duniya cike take da azzaluman maza, ashe itakam rayuwarta a haka zata Ζare? wayyo Allah itakam Ζaddaranta kenan” abun da take faΙa kenan acikin zuciyarta tana kuka mai tsuma zuciya,domin a zaton ta hotel ya kawota zai kuma lalata mata rayuwa.
Daidai lokacin Doctor Sadeeq ya dawo hanunsa Ιauke da manyan manyan ledodi guda biyu, yana shiga cikin motar yakuma danna mata luck haΙe da mawa motar key da gudun gaske ya hau titi.
Zahrah kam muryanta har ya dashe kukanma harya daina fita domin gaba Ιaya ta gama sadaukar da cewa yau ce ranar mutuwarta, kukantane yasoma tsagaitawa ganin sun nufi hanyar unguwarsu, a hankali hawayenta suka daina zuba, yayinda tashiga sauΖe ajiyar zuciya akai akai, bakomai yasa hakanba face ganinsu da tayi sun shigo cikin unguwarsu tsulum, a bakin Ζofar gidan nasu yayi parking cike da kulawa yajuyo da kallonsa ga Zahrah wacce take ta sauΖe nannauyar ajiyar zuciya, alamar taci kuka ta Ζoshi.
“Banga laifin kiba Zahrah, domin dole zakiji matuΖar tsoro, a iya tsawon rayuwata bantaΙa cutar da wata mace ba, kuma bazan fara akan ki ba, bazan taΙa iya cutar dake ba Zahrah, inaso ki yarda dani, ban kuma yi haka don na cutar dake ba, nabiya dake ta mall Ιinne don inaso muje kiyi sayayyan abubuwan dakikeso da kanki, amma sai naga gaba Ιaya kinfirgita, kiyi haΖuri na tsorataki ko Ζanwata !!” Doctor Sadeeq yafaΙi maganar cikin tsananin tausayawa da kuma lallashi ga Zahrah’n..
Kuka kawai Zahrah takuma fashewa dashi haΙe da cusa kanta cikin cinyoyinta, a hankali ya kama hanunta haΙe da matsewa a cikin nasa hanun, “Banason kuka Zahrah, bana ce kiyi haΖuri ba!” Dr yafaΙa cikin damuwa.
“Bakaine zaka bani haΖuri ba likita, nice zanbaka haΖuri, nayi maka mummunar fahimta, dan Allah kayi haΖuri, wlh tsoro nakeji banso wani abu yasake faruwa dani…!” taΖare maganar tana kuka sosai.
“Idan kinaso nayi haΖuri to kidaina kuka kinji Ζanwata!” yafaΙi maganar yana mai Ζare matse hanunta a cikin nasa hanun.
A hankali tashiga share hawayen dake ambaliya akan fuskarta, ji takeyi zuciyarta tayi mata sanyi.
“Bakya kyau idan kina kuka, kinfi kyau idan kina dariya, kije gida kiyi wanka ki huta, banso kisake zubar da hawayenki kinji Zahrah, ungo wannan ledan kishiga gida, akwai waya a ciki na samiki sim da komai, akwai games dayawa a ciki,nasan zai Ιebe miki kewa, banson ganinki cikin damuwa Zahrah, kije gobe zanzo na kaiki school dakaina, Allah yasa bazakimin gardamaba ” yaΖare maganar yana Ζ΄ar dariya.
Murmushi itama Zahrah tayi haΙe da ΖarΙan Ζatuwar ledan dayake miΖo mata, batare da tayi masa gardama ba, cikin rashin kuzari ta buΙe murfin motar tayi ficewarta, harsai da yaga shigewarta cikin gida kafun ya ta da motar tasa ya bar unguwar tasu..
Zahrah tanashiga cikin gida kai tsaye Ιakinta tawuce, jakarta da ledan da Dr Sadeeq ya bata ta ajiye. Kayan jikinta tashiga cirewa, zani ta Ιaura a kirjinta haΙe da sanya hijabi tafice daga cikin Ιakin, zaune ta taradda Inna a tsakar gida, sannu da gida kawai Zahrah tayi mata, haΙe da shigewa cikin bayan gida, tana fitowa a wanka ta bi lafiyar katifarta domin dama dai bata wani jin yunwa, ledan da Doctor yabata ta jawo haΙe da buΙewa, kyawawan dogin riguna ne suka bayyana acikin ledar saikuma dangin su snacks dasu choculate, kyakkyawar kwalin wayar da tagani acikin ledar taciro SAMSUNG GALAXY S10 shine sunan da ke rubuce ajikin kwalin wayar, wani irin faΙuwa gabanta yayi take nunfashinta yashiga gudu akai akai, bazata taΙa mantawa ba shima da haka yafara, daga Ζarshe kuma ya dasa mata babban tabo acikin zuciya da rayuwarta mai wahalan gogewa, saurin sake kwalin wayar tayi haΙe dayin watsi da kayan da suke zube a gabanta, talauci bahauka bane, bazata sake bari haka yafaru da’ita ba, hawaye ne suka shiga sauΖa akan Ζuncinta, haΖika soyayya bata mata adalci ba, kwanciya tayi lamo akan katifa tana nai sauΖe a jiyar zuciya, jin da tayi zuciyarta na shirin dawowa Ιanyea shakaf ne yasanyata tashi ta Ιauko littafi mai tsarki wato Al’Qur’ani tasoma karantawa domin rage damuwar dake damunta a zuciya….
STORY CONTINUES BELOW
“Salima kuma Hajiya?” Doctor Sadeeq yatambaya cikin muryar damuwa.
“Ζwarai kuwa Sadeeq, ko ita Saleema’n tana da wani aibune? Ζwarai nayaba da hankalinta dakuma tarbiyanta, saboda haka nagama yanke shawarata, gobe zanfaΙamawa Ζanin mahaifinku yaje yatambayo maka aurenta, idan ma a so nane banso bikin yawuce nanda wata Ιaya ” Hajiya tafaΙi maganar babu alamar wasa akan fuskarta.
Cike da sanyin jiki Doctor Sadeeq yace ” Shikenan Hajiya, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, amma dakin Ζara haΖuri, nan bada jimawa ba zan kawo wacce nakeso”
“Hmmm ai aikin gama yariga daya gama Sadeeq, nagaji dajin wannan zancennaka, koda yaushe haka kake cewa, to yanzu dai nagaji da Ζaululan dakakemin saboda haka natsaida magana,zaka iya tafiya”
Gaba Ιaya hukuncin da Hajiyar tasa ta yanke masa baiyi masa daΙi ba, amatsayinsa na Namiji bai dace ace anyimasa dole akan aure ba, shi sam Saleema ma bata Ιaya daga cikin irin tsarin matan dayakeso, amma yazaiyi tunda dai Hajiya ta kafe, yasanta da wuyar sha’ani, idan tace eh zaiyi wuya kuma tace a’a, jiki a mace haka yafice daga falonnata, kaitsaye Ιangaren sa yanufa, yanashiga cikin falonnasa direct friedge yanufa, goran ruwa mai sanyi ya Ιauko, haΙe da zama akan kujera, saida yasha ruwan fiye da rabin gora, kafun yashiga sauΖe ajiyar zuciya, wayarsa yaciro acikin aljihun rigarsa, kai tsaye lambar sim Ιin dake cikin wayar daya bata, ya danna wa Ζira, saidai yaji saΙanin tunaninsa, domin kuwa cemasa akayi wayar a kashe take, nannauyar ajiyar zuciya ya sauΖe, haΙe da aje wayartasa a gefe, “Maiyasa nadamu da’ita sosai ne?” yatambayi kansa, bayan kuma yasan baida amsa,
“Inatausayinta sosai,amma kuma bayan tausayi inajin wani abu na daban a ga me da’ita, menene wannan abun ? yazama dole nasan menene amma tabbas ina da burin inganta rayuwarta ” Ζaran wayarsane ya katse sa daga zancen zucin da yakeyi, ganin da sabon number ake Ζiran nasa yasa bai Ιauki Ζiranba, saima tashi dayayi yawuce cikin bedroom Ιinsa…
Washe gari.
Yau tunda safe takammala shirinta, tayi kyau cikin shigar ta ta atamfa riga da sket, yayinda lufayant dake jikinta ya kasance hot pink colour, sama sama tasha ruwan shayin da Inna ta dafa, tana kammala shan ruwan shayin ta Ιauki jakarta haΙe da nufar hanyar waje. domin batamaso likita yazo yasameta, tafiso tayi tafiyarta, sam bataso yanashiga cikin rayuwarta, takuma yanke shawaran gaya masa yafita acikin rayuwarta, domin sam baikamata tasake bawa wani namiji dama ba.
Turus haka taja ta tsaya, domin kuwa tsaye tagansa ajikin motarsa, yasha ado cikin wata blue Ιin shadda, sam batai tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacinba.
Murmushi yayi mata haΙe da soma takowa harzuwa inda take tsaye.
“Baki tsammaci ganina a dai dai wannan lokacin ba ko?” yatambayeta kansa tsaye yana mai kafeta da idanu.
Ζan Ζaramin bakinta taturo gaba haΙe da cewa “Ina kwana”
“Lafiya Ζalau, yakika tashi?”
“Lafiya” tabasa amsa a taΖaice, haΙe da sunne kanta Ζasa, domin hakanan taji yamata wani irin kwarjini.
“Muje kada kiyi latti ko” Doctor yafaΙa yana mai yi mata nuni akan cewa tashige gaba.
Bazata iya musa masa ba, domin kuwa yayi mata kwarjini sosai, don haka cikin sanyin jiki tanufi wajen motar tasa, shikuma yarufa mata baya, gaba Ιaya jitayi jikinta yayi sanyi, alΖawarin da ta Ιaukawa kanta nacewa zata faΙa masa yafita a rayuwarta gaba Ιaya ya ruguje, domin kuwa tanaganinsa taji bakinta yamutu murus, tana shiga cikin motar ta lumshe idanu, domin kuwa wani irin daddaΙan Ζamshi cikin motar keyi, cike da nutsuwa yake tuΖin nasa, yayinda jefi jefi yake satan kallon Zahrah, wanda gaba Ιaya hankalinta yana ga ababen hawan da suketa hada hada akan titin.
“Maiyasa ki kaΖi kunna wayar dana baki?”
Sunkuyar da kanta Ζasa tayi haΙe da soma wasa da yatsun hanunta, “Babu” tafaΙi hakan cikin sanyi murya.
“Ko kuma dai bakyason kyauta daga gareni ba “
Saurin kallonsa tayi, jin abun da yace, ai kuwa karab idanunsu suka haΙe a waje Ιaya, saurin sadda kanta Ζasa tayi, domin batason haΙa idanu dashi kokaΙan, “Bahaka bane, kawai dai banson rayuwata tasake cutuwa ne” tafaΙi hakan da iya gaskiyarta.
Kansa ya jinjina haΙe da cizon lips Ιinsa, “Eh ta wani wajenma kina da gaskia, amma ai bada wata manufa na baki ba, amma idan kinaga zaki takura to shikenan saikiyi abun da yadace” shima yayi maganar da iya gaskiarsa.
Daga haka dukansu basu sake ce da junansu komaiba, har suka iso cikin makarantar, yauma har gaban lecture hall Ιin su ya kaita, sai da kuma yaga shiganta cikin hall Ιin kafun yayi tafiyarsa.
Koda aka tashi yauma shiya zo da kansa ya Ιauketa, sai dai tunda suka kama hanya harsuka isa gida babu wanda yace da Ιan uwansa wani abu.
A daidai Ζofar gidan su ya tsaida motar, haΙe da juyo da kallonsa gareta ΖoΖarin fita tasomayi daga cikin motar, cikin wata irin murya mai sanyi yace “Inason magana dake”
Kallo Ιaya tayi masa ta kau da kanta gefe, “Wace irin maganace ?”
“Maganace mai matuΖar mahimmanci , amma kuma tana buΖatar ishashshen lokaci ” Doctor yaΖare maganar yana mai duban agogon dake Ιaure a tsintsiyar hanunsa.
“Inajinka” Zahrah tafaΙa a taΖaice,
“Bakina jina zaki ce ba, hankali da tunaninki nakeso kibani “
Gyara zamanta tayi haΙe da Ιan satar kallonsa, batare da tace komaiba.
Kwantaccen sajen dake kan kumatunsa ya shafa, haΙe da cewa ” No kada kiyi zaton wani abu zance, dama alluranki ne banΖara sa miki ba, kuma akwai matsala idan banyimiki su ayau ba!”
Gaba Ιaya idanunta ta Ζwalalo su waje, yayinda tsoro yacika zuciyarta, “Dan Allah kayi haΖuri wallahi na warke, yanzu banajin komai ajikina!” taΖare maganar lokacin da muryarta ke rawa, alamun zatayi kuka.
“A’a ni gaskia banyarda da cewa kin warke ba, saboda naga kina yawan sanya kanki a damuwa kuma jiya ma dana riΖe hanunki naji zazzaΙi a jikinki, don haka kawai zan Ζarasa miki yanzu” yaΖare maganar yana mai shirin buΙe wani Ιan Ζaramin drower dake cikin motar, take allurai suka bayyana, ai a Ιari Zahrah ta buΙe murfin motar haΙe da rugawa zuwa cikin gida, ko tsayawa Ιaukar jakarta batayi ba.
Dariya sosai Doctor Sadeeq yasanya, hadda riΖe ciki, shi dama burinsa yaga yanayin tsoronta, domin idan tana cikin wannan yanayin tsoron sosai take burgesa, Ιaukar jakar nata yayi haΙe da fita acikin motar kai tsaye yanufi cikin gidan. Yana sallama Inna ta tarbesa da fari’a, haΙe da cewa “Ai dama nasan tare kuke domin daganin yanda tashigo a guje nasan cewa ba ita kaΙai bace” Ιan guntun murmushi yayi haΙe da cewa ” waifa dan nace zanmata allurane, shine duk tabi ta ruΙe, kuma yau bazan bar gidannan ba harsai na mata alluran nan, ko yakikace Inna?”
Idanu Zahrah tasake gwalowa jin abun da yake cewa, gaskia ita daya mata allura gwamma yabata magani amma sam batason allura, kuma ita taji sauΖi, amma su sundage akan cewa wai bataji sauΖi ba, kafun ta gama zancen zucin da takeyi taji muryarsa a bakin Ζofar Ιakin yanacewa Inna ta Ιauko masa ita….Sake matse jikinta tayi ajikin bango, haΙe da turo Ιan Ζaramin bakinta gaba.+
“ZAHRAH!” taji muryarsa yana Ζiran sunanta, cikin tsoro da Ιar Ιar, ta buΙe Ζofar Ιakin nata, kallo Ιaya yayi mawa cikin idanunta yakau da kansa gefe, domin kuwa wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, gaskia Zahrah tana da abubuwan Ιaukar hankalin Ιa namiji da yawa a tattare da’ita.
Batare da yakuma kallonta ba, ya miΖomata jaΖarta dake riΖe a hanunsa, da sauri ta fusge jakar haΙe da komawa cikin Ιakin ta,ta kuma datse Ζofar, murmushi kawai Doctor Sadeeq yayi haΙe da girgiza kansa, kallonsa yakomar ga Inna, cikin girmamawa yayi mata sallama, bayan ya cika mata hanunta da alkhairi, cike da farinciki Inna tayi sallama dashi, don tsabar daΙi ma har kusan Ζofa ta rakasa, tana mai zabga masa godiya.
Tafiya yake amma shi kaΙai yake murmushi, sosai Zahrah take burgesa, yanason komai na yarinyar, fushinta, dariyanta, tafiyarta, nutsuwarta, dama duk wani abu nata, tabbas Zahrah tana Ιaya daga cikin irin matar da yake fatan mallaka a matsayin matarsa ta sunna, ko dai zai jarrabane ?” ya tambayi kansa, saurin dukan seterin motar tasa yayi haΙe da cije laΙΙansa, “Ka dawo cikin hankalinka Sadeeq, maikake shirin aikatawa ne haka?” yatambayi kansa a fili.
“No baikamata nayi haka ba, dole zanyi haΖuri !” yafaΙi hakan cikin karyewar zuciya, dai dai lokacin kuma ya iso gaban makeken gate Ιin gidansu, mai gadi yana gama wangale masa gate Ιin ya cusa motar tasa zuwa cikin gidan.
Saida tagama Ζaremawa wayar kallo kafun ta danna madannin da zai sanya wayar ta kawo haske, nannauyar ajiyar zuciya ta sauΖe, haΙe da jingina bayanta da jikin bango, “Yazama dole kikawo sauyi acikin rayuwarki Zahrah, kada ki bari abunda Zaid yayi miki, yazama sanadiyar lalacewar duk wani farinciki dake cikin rayuwarki” zuciyarta ta faΙa mata hakan cike da Ζarfafa mata guiwa, “Amma tayaya hakan zai kasance, bayan banda wani ginshiΖi dazai taimakamin ?” Zahrah tatambayi kanta, sake gyara zamanta tayi haΙe da Ιaukar wayarta, kai tsaye tashiga wajen dazai sadata da apps Ιin wayar, Word Charm shine game Ιin daya Ιauki hankalinta, duk cikin apps Ιin dake wayar, dama tanason game Ιin, don haka kaitsaye tashiga tasomayi, take taji kewa da kaΙaicin da take ji sun soma ragewa, a wannan rana dai Zahrah batayi wani dogon tunani da takura kanta ba, dazaran taji ta takura zata Ιauki wayarta tasoma buga game, idan ta gaji da buga game Ιin kuwa, sai ta shiga Instagram shima sosai yake rage mata kewa (nima haka, lol)..
STORY CONTINUES BELOW
Tayi kyau sosai cikin blue rover gown Ιin dake jikinta, wata baΖar lufaya ta sanya a jikinta wanda yataimaka wajen Ζarawa shigar tata kyau da armashi, batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, ta dai shafa man leΙe dakuma kwalli, amma duk da haka tayi kyau, dama mai kyau ko baiyi kwalliya ba kyawunsa baya Ιuya.
Kasancewar yau baza su jima a makaranta ba, yasanya bata Ιauki jakaba, sai wasu Ζ΄an littatafai da ta Ιauka a hanunta, sai kuma wayarta, koda ta fito tsakar gidan zaune a bakin murhu ta iske Inna tana tuyan Ζosai, wanda Baffa yace ayi na karyawa.
“Inna ni zanwuce makaranta” Zahrah ta faΙa tana mai ΖoΖarin gyara zaman lufayan dake jikinta.
“Bazaki tsaya ki karyaba Zahrah”
Baffa dake fitowa daga cikin Ιakinsa ya faΙa.
Ζan guntun murmushi Zahrah tayi haΙe da shafa cikinta “Banajin yunwa sosai Baffa, kuma ina tsoro kada na makara!”
“Eh kina da gaskiya, kinga kuwa tun Ιazu likita, yazo yana jiranki, bayanda banyi da shi ba akan yashigo, amma sam yaΖiya, don haka gwamma ki hanzarta, a dawo lafiya ” Baffa yaΖare maganar yana mai yunΖurin komawa cikin Ιakinsa.
“Ameen Baffa nagode!” Zahrah tafaΙa cike da farinciki, domin kuwa karo na farko kenan a rayuwarta da taga tsananin kulawan Baffa a kanta.
Tana fitowa yasakar mata kyakkyawan murmushinsa, ga mamakinsa sai yaga itama ta sakar masa murmushi, wanda yayi matuΖar taΙa masa zuciya, domin kuwa bakaΙan ba tayi kyau, da tana murmushin.
“Saiyanzu ki ka ga daman fitowa? kinshanyani kamar kin aje dutse” Doctor yafaΙi maganar yana mai turo baki gaba, tamkar Ζaramin yaro.
Dariya sosai Zahrah ta shiga yi, domin yanayin yanda yayi maganar yazama dole wanda ya gani ya dara, hangame baki Dr yayi yana kallon yanda take dariyan, abun da bai taΙa gani ba kenan, tun haΙuwar su da’ita, bai taΙa ganinta tana dariya ba sai yau, ashe ma duk kyawunta da yake gani, bai ga komai ba, domin da tana dariyan tafi masa kyau.
Hanunta tasanya ta toshe bakinta, haΙe da tsagaita dariyan da takeyi, kallonsa tayi haΙe da cewa “Bakaga yanda kazama yaro ba dakana maganan nan, tamkar Ιan shekara takwas!”
Murmushi yayi haΙe da jefamata hararan wasa, cikin yanayin da yayi magana Ιazu yakuma cewa “Shine kikemin dariya ko? sai na faΙaki da mamana!” ai kamar yaΖara mata fower’n da riyan nata ne, nan take taci gaba da dariyanta, hadda Ιan guntun Ζwalla a idanunta, wani irin sanyi da nishaΙi yaji yana huda zuciyarsa, tabbas bashida wani buri da yawuce yaga Zahrah tana cikin farinciki Alhmdlh, yau gashi ta sanadiyarsa tana dariya dakuma nishaΙi,
“Kayi haΖuri, bazan sake shanyaka ba, amma gaskia ka iya shagwaΙa da yawa!” Zahrah tafaΙa dai dai lokacin da tayi mawa kanta mazauni acikin motar, haryanzu dariyane kwance akan fuskarta.
“Wato dai yau mugunta kike ji dashi, dariya hadda hawaye!” Doctor yafaΙa cikin nishaΙi.
“Bahaka bane, kai Ιinne dai kawai kabani dariya!” itama ta basa amsa cikin nishaΙi.
“Dagaske kike, saboda ni kike wannan nishaΙin? ” Dr ya tambayeta cike da zaΖuwa, duk da kuwa cewa yasan sabo da shiΙinne take nishaΙin.
“Eh mana, saboda kaine, kasan kaban dariya sosai, kuma nasan bama ni kaΙaiba, duk wacce takalleka a irin wannan yanayin dole zatayi dariya”
Ajiyar zuciya Dr ya sauΖe haΙe da murza key Ιin motar, suka Ιau hanyar da zata sadasu da titi.
“Idan kina dariya kinfi ko yaushe kyau Ζ΄an mata na!” Dr yafaΙa cikin muryar nutsuwa.
Saurin maida kallonta garesa tayi, jin abun da yafaΙa tayi kamar wani almara, sai kuma taga yanayinsa tamkar bashine yayi maganar ba.
Yi tayi itama kamar bataji mai yace ba, mai da kallonta tayi ga titi, tana mai kallon yanda ababen hawa suke gudanar da hada hadansu.
STORY CONTINUES BELOW
“Maiyasa ki ka Ζi cin abinci? ko kinfiso ki zauna da yunwa ne?” Doctor ya jefo mata tambayar da batayi zato ba.
Kallo Ιaya ta yi masa ta kau da kanta gefe, “Banjin yunwa ne, sannan kuma banaso na yi latti”
tafaΙi maganar a taΖaice.
Baice da’ita komaiba, saima buΙe Ιan Ζaramin drowern dake jikin motar yayi, wani haΙaΙΙen cake dake cikin wani Ιan Ζaramin kwali ya ciro, haΙe da Ιaura mata akan cinyarta, ” Kici, kuma banson musu” yanayin yanda yayi maganar zai tabbatar ma da cewa, ba wasa yake ba.
“Nagode, amma zanci idan muka fito a lecture” itama ta faΙa kai tsaye.
“Yanzu nakeso kici, umarnine bawai shawara ba” yakuma faΙi maganar cikin yanayi mai nuni da cewa da gaske yake maganar.
Batason yi masa musu, domin koba komai yayi mata halacci a cikin rayuwarta, a hankali take gutsuran cake Ιin tana kaiwa bakinta, duk da cewa cake Ιin yayi mata daΙi.
Duk abun da takeyi yana lure da’ita, yanayin yanda take tauna abincin shiyafi komai burgesa.
Saida taci cake Ιin fiye da rabi, kafun ta dawo da kallonta garesa, “NaΖoshi” tafaΙa tana mai yatsine fuska.
“Dole sai kin cinye, domin kuwa ni idan nabawa mutum abuna, bai isa yacemin ya Ζoshi ba, dole sai yacinye koda kuwa ya Ζoshin”
Ζan guntun murmushi tayi haΙe da cewa “Dagaske nake naΖoshi, amma da alama dole kakeson min”
“Dolen dole ma kuwa” yafaΙa dai dai lokacin da yagama parking motar tasa, domin kuwa harsun kawo cikin makarantar tasu, hanu ta Ιaura akan murfin motar da niyar buΙewa ta fita, tuni ya dannawa Ζofofin luck, saurin kallonsa tayi domin bata fahimci hakan da yayi me yake nufi ba.
“Babu inda zakije, matuΖar baki cinye cake Ιin nan ba” yafaΙi hakan yana me jingina bayansa a jikin kujeran da yake kai.
ΖwaΙe fuska Zahrah tayi cikin sigar lallashi, tace “Kayi haΖuri, naΖoshi, idan naci da yawa, bazan iya karatu yanda ya kamata ba!”
“Um,Um, naΖi wayon, saura kaΙanne fa please kicinye shi mana Zahrah!” Doctor Sadeeq yaΖare maganar cikin lallashi.
“Um, Um, na Ζoshi, gaskiya idan naci zai cutar dani, zanyi Ζatuwa da yawa, ni kuma banaso nayi Ζatuwa!” cikin zallan shagwaΙa Zahrah tayi maganan.
Dariya sosai Dr Sadeeq ya sanya, domin kuwa maganar Zahrah ta bashi dariya, wai ita bataso tayi Ζatuwa hmm.
“To ai yaune kawai, kuma kinga bazakiyi Ζatuwa ba, nima banso kiyi Ζatuwa da yawa, amma inaso kiyi Ζatuwa kaΙan!” yanayin yanda yayi maganar kaΙai ya isa sanyawa mutum mutuwar jiki.
Batace dashi komaiba, domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, Ιaukan ragowan cake Ιin tayi, tashiga turawa acikin bakinta, tamkar wacce aka bawa guba.
Dariya Doctor Sadeeq yashiga yi mata Ζasa Ζasa, domin kuwa yanda takecin cake Ιin, dagani kasan dole a kayi mata bawai a son ranta bane. tana cinyewa ya miΖomata goran ruwa, ai kuwa ba musu ta karΙa ta shiga sha, domin dama duk cake Ιin ya shaΖeta.
Cikin yanayi na shagwaΙa da Ιata fuska tace ” Na cinye yanzu zan iya tafiya!”
Dariya Dr yayi haΙe da cire luck Ιin da yasanyawa Ζofofin motar “Zaki iya tafiya, amma kikula da kanki sosai, sannan idan kun fito a lecture wani zai kawo miki saΖo daga nine ki amsa”
“Wani saΖo?” Zahrah ta tambaya cike da Ιaurewar kai.
“Zakiyi latti,kiyi sauri kije” Dr yafaΙi hakan don kawar da tambayar da tayi masa.
Bata sake cewa komai ba tabuΙe murfin motar tafice, yauma dai sai da yaga shiganta cikin hall Ιin kafun yatada motarsa yabar cikin makarantar, direct shima asibiti ya nufa, domin yau yanada aiki sosai.
STORY CONTINUES BELOW
Sosai yau ta gane Lecture Ιin da akayi musu, saΙanin sauran ranakun da suka wuce wanda ba komai take fahimta daga cikin abun da ake koyar musu ba.
Fitowarsu kenan daga lecture, tafe suke su biyu, yayinda Husnah keta mita, wai jimawan da sukayi suna lecture, yasanya tanemi gaba Ιaya abincin cikinta ta rasa.
Dariya Zahrah tayi haΙe da cewa “Nikuwa kinga Ιigo na yunwa banaji, domin kuwa yau Ιure, a kamin dan dole na”
“Ιure kuma bestie? Amma badai Inna da Baffa bane sukaimiki Ιuren bako?”
“Doctor Sadeeq ne!” Zahrah tafaΙa a taΖaice.
“Doctor Sadeeq kuma? lallai kuwa Doctor yayi babban ΖoΖari, shiyasa na ganki yau kina cikin farinciki” Husnah tafaΙa tana mai ΖoΖarin gimtse dariyar da take ΖoΖarin taso ma ta, domin ita kam ta hango wani babban al’amari dangane da Doctor dakuma Zahrah.
“Maikike nufi?” Zahrah ta tambayi Husnah cikin tsare gida.
Husnah batakai ga bata amsa ba, wani mutumi ya Ζaraso garesu, hanunsa Ιauke da wata leda, sallama yayi musu suka amsa masa.
Kaitsaye ya miΖomawa Zahrah ledar dake hanunsa, haΙe da cewa “Gashi inji oga”
Take maganar da Dr yafaΙa mata Ιazu a cikin mota, cewar wani zai kawo mata saΖo, ya faΙo mata, cikin sanyin jiki ta amshi ledan, haΙe da ce masa ta gode.
“Saurin karΙe ledan Husnah tayi daga hanun Zahrah, haΙe da cewa “Allah yasa abun daΙi ne, domin yawuna haryafara tsinkewa, kinsanni ba baya bace wajen kwaΙayi”
“Wow special gift!!” Husnah tafaΙa sanda idanunta suka gane mata abun da ke cikin ledar,
“Amma ba haka naso ba, Ζawata naso ace wani abun ci ne kinga da sai na morewa bakina!” Husnah ta Ζare maganar tana mai Ιata fuska.
Dariya Zahrah tayi haΙe da sanya hannayenta ta dafa kafaΙun Husnah, cike da nishaΙi tace ” Allah Ζawata, ki rage kwaΙayi, yanzu idan abun ci ne, yazuba mana wani abu a ciki, mukazo mukaci, ya cutar da mu,kuma fa? kinga kwaΙayi ya jawo mana kenan,kuma bai mana rana ba”
“Dan Allah malama sakeni, nayarda da Dr nasan babu abun da zai Ιamu wanda zai cutar da mu, kedai kawai mugunta ne irin naki, bayan kinsan inajin yunwa, muje cafeteria muci abinci please!” Husnah tafaΙa tana mai daΙa kwaΙe fuska.
“Yi haΖuri Ζawata bani nakar zomonba, muje sai kici abincin ko” Zahrah tafaΙa cike da kulawa.
“Ungo kayan shafanki, domin kuwa cigaba da riΖesu ma, Ζaramin yunwa zaiyi” Husnah ta Ζare maganar tana mai miΖomawa Zahrah ledar dake hanunta.
Dariya kawai Zahrah tayi haΙe da amsar kayan, sarai tasan Husnah bata da haΖurin yunwa ko kaΙan.
Ice cream kawai Zahrah tasha, yayinda Husnah kuwa ta cika cikinta da shinkafa. Yau darasi biyu garesu kacal, don haka suna fitowa kowa ya yi ΖoΖarin kama gabansa.
Waige waige tashiga yi ko zata hangosa, amma babu alamar komai irin motarsa, wayarta ce ta soma Ζara alamar shigowar Ζira, Number ne ke yawo a kan screen Ιin wayar babu suna, dama kuma batayi tunanin Numbern zai fito da suna ba, domin batayi saving numbern kowa ba, wama ta sani da zatayi saving number’nsa.
Har saida wayar ta kusa katsayewa kafun Zahrah ta Ιaga Ζiran, “Zahrah! na gaji, da yawa, aiki yamin yawa, please ga nan driver na, zaizo ya Ιaukeki ya kaiki gida, kiyi haΖuri kinji Ζanwata!!” Dr Sadeeq ya faΙi haka cikin kwantar da murya, da gajin yanda muryansa take fita slow kasan cewa a matuΖar gajiye yake.
A jiyar zuciya Zahrah ta sauΖe haΙe da cewa “Shikenan kahuta lafiya”
“Yauwa Ζ³an mata na, ki kulamin da kanki” Ζit ya kashe wayar, ba tare da ya tsaya ya saurari mai zata ce ba.
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi kawai Zahrah tayi haΙe da girgiza kanta, “Hmm wai itace Ζ΄an mata, itakam yanzu ai ta wuce a Ζirata Ζ΄an mata saidai sauran Zaid” tafaΙi hakan a zuciyarta, take kuma taji idanunta sun kawo ruwa. Dai dai lokacin motar Dr Sadeeq ta Ζaraso inda take tsaye, kasan cewar yayi mata bayanin cewa driver’n sane zaizo Ιaukarta, dan haka batayi wani jinkiri ba, ta buΙe murfin motar tashiga, ko kallon inda driver’n yake batayi ba, “ZAHRAH!” muryan Dr Sadeeq ya daki dodon kunnuwanta, saurin maida kallonta inda taji muryan tayi, ai kuwa shiΙinne kwance a jikin kujeran gidan baya, idanunsa Ιaya ya kashe mata haΙe da Ιage giransa Ιaya sama, “Surprise!” yafaΙa fuskarsa Ιauke da murmushi.
Murmushi itama tayi masa, haΙe dayin Ζasa da kanta, domin yanayin yanda yayi mata maganan, yasanya taji jikinta yayi sanyi.
“Dawo nan muzauna, ki bar driver yayi aikinshi”
Ζata fuska Zahrah tayi haΙe da turo baki gaba, cike da shagwaΙa tace “Ni dai kabarni na zauna anan Ιin ma yayi!”
“Nace ki dawo nan muzauna ko!” yafaΙi hakan babu alamar wasa akan fuskarsa.
Cike da sakalci Zahrah ta dawo gidan baya inda yake zaune, ko kallonsa batayi ba saima langwaΙewa da tayi a jikin kujera. Har sukayi nisa a tafiyan babu wanda yace da Ιan uwansa Ζala, cikin shagwaΙa tace “Bakace min aiki yamaka yawa ba, amma mai yasa kazo?”
“Saboda ya cancanta nazo, ina da burin baki kyakkyawan kulawa a ko da yaushe, ko bakiyi farinciki da hakan ba?”
“Nayi farinciki sosai!” Zahrah tafaΙa kai tsaye, domin kuwa sam batason irin kallon da yake yawan yi mata a wasu lokutan.
Baisake ce da ita komai ba, shima sai ma komawa da yayi ya jingina bayansa da jikin kujeran motar.
A haka har suka iso Ζofar gidan su Zahrah’n, kallo Ιaya tayi masa haΙe da buΙe murfin motar tayi ficewarta, yana ganin shigewarta gida, yace driver ya ta da motar suje.
Bayan Sati Biyu….
Wani irin shaΖuwa ne mai Ζarfi yashiga tsakanin Doctor Sadeeq da Zahrah, kullum shi ke kaita mkaranta shi kuma ke Ιauko ta, sosai yake bata kulawa, baya son duk wani abu da zai Ιata ranta, ko ya sanya taji ba daΙi, Ιangaren Zahrah ma, sosai take kiyayewa dashi, tana iya ΖoΖari wajen ganin bata musa masa idan ya umarceta da tayi abu, ko kaΙan batajin wani abu a dangane dashi, tana dai yi masa biyayya tana kuma ganin girmansa, domin kamar yanda yace ta Ιaukesa, a matsayin Ιan uwa, to a matsayin Ιan uwan ta Ιaukesa, domin kallon yaya take masa, sannan kuma sosai wayarta take Ιe be mata kewa, yakanyi ΖoΖari wajen ganin ya Ζirata a waya, a kowani dare, sai dai hiran tasu bata tsayi suke sallama da juna, sosai rayuwarta tasamu canji, bakamar da ba, duk da cewa abune mawuyaci manta abun da ya faru da’ita, amma takanyi ΖoΖari Ζwarai wajen ganin ta gusar da duk wani damuwarta.
Tsaye yake a gaban tangamemen dressing mirror Ιin dake kafe a jikin bangon Ιakin nasa, yayi kyau sosai cikin riga da wandon shadda dake jikinsa, ba abun da jikinsa keyi banda tashin Ζamshi, hannayensa duka yazura a cikin aljihun wandon shaddan dake jikinsa, tabbas a kwai wani al’amari mai girma dake cikin zuciyarsa, haΖiΖa kuma akwai abun da yakeso ya furta,amma tayaya, baisan da wani manufa zata Ιauki zancen ba, baisan wani amsa zaiji daga bakinta ba, wannan shiya hanasa furta mata tsadaddan kalman dayake ta Ιoyewa tsawon lokuta, bayajin zai samu abun da yakeso daga gareta, bakuma yajin zai samu amincewarta, ya tabbatarwa kansa cewa, a yanzu lallashi take buΖata fiye da komai, sannan kuma bata buΖatar wata magana wanda zata zamo sanadiyar rugujewar Ιan farincikin da ta soma samu, sai zuciyar sa ta Ζarfafa masa guiwa, saikuma gangar jikinsa tayi sanyi laΖwas.
“Ba’asan jarumin Namiji da tsoro ba!” wata zuciyarsa ta furta masa hakan.
Ζwarai ya yarda da cewa shi Ιin jarumi ne, amma kuma gurin da yake da muradin isar da saΖonnasa wajene mai rauni, dole zai fuskanci Ζalubale guda biyu, rashin nasara, ko kuma, yin nasara, wayarsa ya Ιauka ya sanya a cikin aljihunsa, kai tsaye ya fice daga cikin Ιakin nasa, yana shiga cikin motarsa ya bata wuta, kai tsaye unguwar su Zahrah ya nufa, sosai ya yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, lallai yazama dole ya bayyana mata sirrin dake kwance cikin zuciyarsa, sai dai yasan balallai ta aminta da ΖuΙirinsa ba, amma zai jarraba ya gani.
A Ζofar gidansu yayi parking motarsa, haΙe da ciro wayarsa, ya danna wa Number’n Zahrah Ζira, sai dai harzuwa lokacin zuciyarsa fat fat haka take bugawa. tana Ιaga wayar yace “Ina Ζofar gidanku, dan Allah kizo ki sameni” banji mai tace masa ba, sai gani nayi ya mai da wayar tasa cikin aljihunsa, haΙe da sauke nannauyar ajiyar zuciya….Tana aje wayan ta Ιauko wani rover hijab Ιinta ta sanya a jikinta, koda tafito daga cikin Ιakin nata, zaune ta iske Baffa da Inna, a tsakar gida, domin dai dama dare yasoma rufawa, cike da ladabi tace ” Baffa Doctor Sadeeq yana Ζirana a waje”
Gyara zama Baffa yayi haΙe da cewa ” to naji Ζaran tsayuwar mota ai, ashe dai likitane yazo, to adawo lafiya”
Muguwar harara Inna ta jefamawa Zahrah, cike da masifa tace “Wato ni banza bankai matsayin da zaki tambayeni ba ko? wato Baffanki kaΙai kika gani a wajen?”
Cikin sanyin murya Zahrah tace “Kiyi haΖuri Inna, naga shi ya kamata na sanarmawa hakanne, tunda ya na nan!”
“Wuce kije Ζiran da yake miki kinji Zahrah’u, barta Salame yau masifa take ji dashi” Baffa yaΖare maganar yana mai wurgamawa Inna harara.
Bata kuma sauraran abun da Inna zatace ba tasakai tayi ficewarta daga cikin gidan..
Duk da cewa babu wadataccen haske a wajen, amma tana iya hango kyawun da kayan jikinsa sukai masa, “gaskiya Dr kyakkyawane shima” tafaΙi hakan a cikin zuciyarta.
Da sallama Ιauke a bakinta ta Ζaraso inda yake tsaye, cike da fari’a Dr ya amsa mata sallaman da tayi haΙe da cewa “Wato sai anjamin aji kafun a fito ko?”
Ζan guntun murmushi Zahrah tayi haΙe da cewa “Bawani batun jan aji, ni a hakan ma inaganin na fito da wuri”
Shima murmushin yayi haΙe da cewa “Kinyi kyau!”
Still murmushi tayi, cikin son kawar da zancen da yayi na cewa tayi kyau, tace “Lafiya kuwa naganka a dai-dai wannan lokacin?”
Gyara tsayuwarsa yayi haΙe da maida nutsuwarsa gareta “Maganar danazo miki da’ita Zahrah bata tsaye bace, yana da kyau mushiga mota, sai mu tattauna ko?”
Ζan jim Zahrah tayi, haΙe da cije lips Ιinta, “Shikenan amma inafatan bazamu jimaba, kafasan banson fitowa waje da dare”
“Insha Allah, bazamu Ιau tsawon lokaci muna magana ba!” Dr yafaΙi hakan lokacin da yayimawa kansa masauΖi a cikin motar tasa, bayan ya kunna Ζoyin wutar dake cikin motar take haske ya gauraye cikin motar.
STORY CONTINUES BELOW
Gyara zama Zahrah tayi, haΙe da tattaro duka nutsuwarta “Inajinka” tafaΙa a taΖaice.
Wani irin numfashi Dr yayi, haΙe da fitar da iska daga bakinsa, sai yanzu yakejin cewa, bazai iya furta abun da yakawosa ba, gaskiya yanajin nauyi, baisan tayaya Zahrah zata karΙi muradinsa ba, kada maganar da zaifaΙa ma ta yazamo sanadiyar rugujewar nishaΙin da yake gani akan fuskarta yanzu, “Ta’ina zanfara?” ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
“Lafiya kuwa, naga kayi shiru?”
Zahrah ta tambaya, cike da mamakin yanda yayi shiru, bayan yace akwai maganar da zasuyi.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauΖe, haΙi da maida kallonsa gareta, saida ya tattaro nutsuwarsa kafun yace…
“Yazakiji idan wani yazo miki da batun soyayya a wannan lokacin Zahrah?” abun da ya iya fitowa daga bakinsa kenan, domin a gaskia shikam yarasa ta’ina zai fara.
“So kuma? wani irin so?” Zahrah ta tambaye shi cike da mamakin kalaman nasa.
“So na Aure Zahrah!” yafaΙi maganar cikin Ιar Ιar.
“Au..r..e.. Kuma Likita? Aure fa kace, dama akwai wani wanda, zaiji kwaΙayi da sha’awar aure na ne? hmmm a gaskia bana tunanin haka, domin kuwa babu wani wanda zai so ni da rayuwata, a yanda nake Ιinnan!” Zahrah tafaΙi hakan da’iya ka gaskiyar ta.
“Kada kice haka Zahrah, akwai mata masu rauni da yawa irin ki, amma an auresu, kuma anzauna dasu, ke me yasa zaki yanke Ζauna da….”
“Dan Allah kadaina min wannan zancen Doctor, banjin zan sake son wani Ιa namiji a duniyar nan”
Zahrah ta katse shi da ga maganar da yakeyi, ci gaba tayi da cewa
“taya kake tunanin zansake kai kaina tarkon da ya ruguzamin rayuwa, shi So Ιin dakake faΙa yanzu, shine ya ruguzamin rayuwa ta, ya rabani da duk wani farinciki na rayuwata, shin idan kace min na sakeyin So, kamin adalci kenan? ” Tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.
“Kada kice haka Zahrah, kefa musulmace, kuma ke mace ce, nasan kina da sanin cewa, kyautatuwar rayuwar Ζ΄a mace shine aure, haka kuma rayuwar Ζ΄a mace bata cika hundred percent sai da aure, haka kikeso ki Ζare rayuwarki ba aure? ko kin manta cewa cikar mutumcin mace shine a ganta gidan mijinta? yin Aure shine burin kowacce mace ta Ζwarai, nasan kema wannan shine burinki, kada shaiΙan yayi amfani da abun da yafaru dake, ya ruguza miki rayuwa, ya hanaki aikata sunna!”
“Hakan shine burina amma ada, wa zai aureni a yanzu? waye zai Ιaukawa kansa duhu? waye zai Ιauki sauran da wani yaci ya rage, sauran da wani ya tarwatsa, ya zuba Ζazantarsa, acikin cikinta, waye zaiyi hakan? bazan yaudari kaina ba, nasan babu wani wanda zai aureni a yanda nake, bantaΙa aure ba, amma kuma niba budurwa bace a yanzun, ya cuceni yariga ya karΙe abun da nake burin bawa mijina na sunna, waye zai yarda da haka?”
“Nine nan Zahrah, Nasan komai a kan ki, kuma zanyarda da duk wata Ζaddaranki, nine wanda zan sharemiki hawayenki, kece damuwata bawai budurcin kiba, kiyarda dani dan Allah!!” Doctor Sadeeq yafaΙi hakan cikin jajircewa..
Kamar sauΖan aradu haka Zahrah taji sauΖan kalamansa a cikin kunnuwanta, cak ta tsaida kukan da takeyi haΙe da, da hangame baki tana kallonsa, gani take kamar ma baya cikin hayyacinsa, Ζaryane tayaya za’ace Namiji mai aji, kamar Doctor yace wai ya amince da Ζaddaranta zai aureta, wannan ba gaskia bane,
“Kada kiyi shakka ko kokonto, ba yaudara’nki nake ba, dagaske nake har cikin zuciyata, don Allah ki bani dama Zahrah, burina da fatana kawai ki amince min!”
Kai Zahrah ta shiga girgizawa, cikin tsananin Ιacin rai da danasin sauraransa da tayi tasoma cewa ” Nayi Babban kuskure, haka kuma na tabka nadaman baka daman shigowa rayuwata da nayi, ashe dukanku haka halinku yake, macutane ku azzalumai, ashe bazaku taΙa sanjawa ba, dama Ιaya kawai idan aka baku, sai ku nemi shigo da manufarku, kaicona da abun da Zaid yayi mini baikasance IZNAH ga rayuwata ba, kaicona dana sake aminta da kai, kaicon zuciyata, kafita a rayuwata dan Allah, kaje banaso nasake ganinka ko kuma jinka, katafi kayi nisa da ni, kabarni na rayu cikin salama dan Allah!!” gaba Ιaya hawayen Ιacin rai yagama wanke mata fuska, ΖoΖarin fita daga motar ta somayi, cike da tashin hankali Doctor Sadeeq ya riΖo hanunta, ko kaΙan baiyi zato ko tsammani ba, saijin sauΖar mari yayi akan kumatunsa, Zahrah ce ta Ιaukesa da lafiyayyen mari, babu abun da ke kwance akan fuskarta banda tsananin Ιacin rai,
STORY CONTINUES BELOW
“Koda wasa kada kasake ΖoΖarin taΙani, mayaudari, dama haka kuke bakuma zaku canza ba!!” fuuuuu haka Zahrah tafice daga cikin motar tamkar kububuwa.
Tamkar statue haka Dr Sadeeq ya tsaya, komai nasa daina aiki yayi, sai numfashinsa dake fita da sauri, ganin komai yake tamkar al’amara, wai yau shine Zahrah ta mara da hanunta, a hankali yasanya hanunsa ya shafi kan kumatunsa inda Zahrah ta wankesa da mari, ko kaΙan baiga laifin Zahrah ba, kuma baiji zafin marin da ta masa ba, babban damuwarsa da tashin hankalinsa, shine yanda yaga Zahrah tana kuka wiwi, sannan kuma ranta yayi matuΖar Ιaci, tabbas da yasan abun zai Ιaci har haka, to da baiyi gigin furta mata kalmar cewa zai aure ta ba, ko da na minti Ιaya ne bayason Ιacin ran Zahrah, yanzu yasan haka zata kwana tana kuka, maiyasa? maiyasa na kasa jurewa? ni nake burin faranta rayuwa da zuciyarta, amma sai gashi da kaina nasake ruguza farinciki’nta maiyasa? yatambayi kansa da Ζarfi, cike da haushin kansa ya sanya hanunsa duka biyu ya daki siterin motar tasa, wani irin haushin kansa yakeji, yayi dana sanin sanar da’ita abun dake cikin zuciyarsa, “mai yasa na yarda nazamo LOSER?” ya tambayi kansa cikin Ζunan zuciya, yakusan 10 minute yana zaune a cikin motar, da Ζyar ya’iya tada motar yabar cikin unguwar tasu…
Zahrah kuwa tana shiga gida, kaitsaye Ιakinta ta wuce, zamewa tayi a Ζasa, tashiga rera sabon kuka, lallai tayarda cewa Ζaddaranta mai girma ce, daga wannan sai wannan, bata taΙa zato ko tunani’n haka zai fito daga bakin Dr Sadeeq ba, ko da wasa bata taΙa ayyana wani abu a ranta ga me da shi ba, maiyasa zai zo mata da wannan maganar a daidai wannan lokacin? maiyasa zai sake maida ita uΖubar da tayi nasaran samun bakin fita daga cikinsa? tabbas yanzu kam tayarda cewa duhu yasamu mazauni a cikin rayuwarta
“Bawanda zai soni a haka, shima nasan ba sona yake ba, wata manufarsa kawai yakeson cimmawa, ashe Ζaddarorina suna da yawa?” ta tambayi kanta cike da ruΙu.
Sanin bata da amsar bawa kanta, yasanya ta cigaba da kukanta, ganin hakan bazai fishsheta ba yasanya ta Ιauro alwala tazo ta fara gabatar da salla, haΙe da miΖamawa mai kowa mai komai duka lamuranta…
Koda Doctor ya isa gida, baije koda Ιangaren mahaifiyarsa bane, kai tsaye Ιangarensa ya nufa, gaba Ιaya jiyakeyi duniyar ta masa Ζunci, saboda cimma muradinsa yasake sanya Zahrah a damuwa, kwanciya yayi lamo akan gado, zuciyarsa cike da tarin tunanuka kala kala, gaba Ιaya kalamanta ne suke yawo a ΖwaΖwalwarsa, babu kalman da tafi tsaya masa a rai kamar inda takecewa ” Natabka nadamar baka daman shigowa rayuwata da nayi, katafi ba naso na sake ganinka ko kuma jinka!!” wannan kalamannata sunfi komai Ιaga masa hankali, sam shikam ya ma manta da marin da tayi masa, saboda bai Ιauki marin a matsayin komaiba, shidai shiga damuwarta ne bayaso, baisan wani irin so yake mawa Zahrah ba, bayason ganinta a cikin damuwa, ba kuma yason Ιacin ranta, amma tayaya Zahrah zata fuskancin hakan? Yanaso ya aureta yakuma inganta rayuwarta, ba budurci’nta bane abun so a gareshi ita kanta ce abarsonsa, haΖiΖa kowani namiji yana burin auren mace yasameta a budurwa, shima kuma yana burin hakan, amma son da yakemawa Zahrah, yasanya zai iya karΙanta a yanda take.. Haka Doctor yayita saΖawa da kuncewa, da Ζyar bacci Ιarawo yayi nasaran Ιaukarsa.
Ζangaren Zahrah ma dai hakanne takasance da Ζyar ta’iya runtsawa a wannan dare….
*TURKEY*
*ZAID* ne zaune akan wata haΙaΙΙiyar kujera, sanye yake da riga long slive, white colour yayinda wandon jikinsa ya kasance baΖi, suit ne baΖi Ιaure a saman kayan nasa, sosai yayi kyu a cikin shigartasa, hanunsa riΖe yake da wani dogon kofi na glass, bakomai ne acikin kofin ba face giya, a hankali yake sipping giyar tasa, yayinda ya Ιaura Ζafansa Ιaya kan Ιaya, gefensa kuwa Abid ne zaune shima dai irin shigar Zaid Ιinne a jikinsa, sai dai shi nasa kalan sun kasance blue, “Lokaci fa yana tafiya Zaid, yakamata ace yau munkoma New York, amma bansan dalilinka nacewa muzauna anan ba, ni fa duk yanda instanbul takai ga haΙuwa da daΙin zama, batakaimin new york ba, kasan can akwai mata Ζ΄an harka, amma ni gaskia nan a takure nake!” Abid yakai Ζarshen zancennasa cike da Ζosawa.
STORY CONTINUES BELOW
Kyakkyawan murmushinsa yayi haΙe da maida kallonsa ga wani kyakkyawan ruwa dake gudana a gefensu,
“Inason zaman Instanbul sosai Abid, domin yanayin garin yanasawa inajin shauΖin abar sha’awata!!”
“Bangane shauΖin abar sha’awan kaba? wai meke damunka ne? kusan tsawon watanni kenan dana fuskanci sauyawa a tattare dakai”
“Sha’awa nakeji Abid, matsanancin sha’awarta nakeji!”
Zaid yafaΙa cike da tsananin shauΖi.
“Sha’awa? wacece ita?” Abid ya tambaya cike da zaΖuwa, domin shikam yarasa wace irin macece Zaid ya kejin sha’awa’rta haka, ko da yaushe cikin maganarta yake, kuma ita kaΙai yakejin sha’awa.
“ZAHRAH NA!” Zaid yafaΙa cikin wata murya mai Ιauke da ma’anoni.
Dariya sosai Abid yasanya, hadda riΖe ciki, “Zahrah fa kace Zaid, wannan villager girl Ιin, koba sugar baby’nka ba?” Abid yatambaya yana ΖoΖarin gimtse dariyar da ta tasomai.
” Tana da matuΖar mahimmanci a wajena Abid, bantaΙajin irin abunda nakeji akanta ba, inason kasancewa da’ita a koda yaushe, inaso tazama ita ce mace guda Ιaya dazanna yin sex da’ita dare da rana, sha’awarta tamun mummunan kamu Abid, kasan yanda nakeji kuwa ?” Zaid ya tambayi Abid cikin sigar rashin wasa.
“KokaΙan bansan ya kakejiba, amma kuma Zaid wannan ba sha’awa bane SO ne” Abid yafaΙi hakan da iya gaskiyarsa, domin shi abun da ya fahimta kenan.
Dariya sosai Zaid yashiga yi, haΙe da sanya hanunsa ya daki kafaΙan Abid.
“Shirmen banza, wai SO? menene SO Abid? kasan me kake faΙa kuwa, taya sha’awa zata zama SO, so fa kananufin wai inasonta ne, hahaha Abid ΖwaΖwalwarka Ζaramace, taya za’ayi nayi soyayya da’ita, sha’awace kawai kuma da zaran na sakeyin sex da’ita nasan komai zai wuce, tun farkoma danasan ban Ζoshi da’itaba, ai da banbari ta tafiba!!” yaΖare maganar yana mai Ιaga kofin giyarsa yakai baki.
Murmushi kawai Abid yayi, domin yafi kowa sanin cewa Zaid bayason gaskia, amma tabbas shikam anasa hasashen zuciyar abokinsa takamu da so, yana kuma da tabbacin idan har Zaid zaiyi sex da Zahrah sau Ιari, to wannan sha’awar bazata taΙa barinsa ba, saboda dama ba sha’awar bace So ne.
“Shikenan naji ba soyayya bane, sha’awa ce, amma kasan dai yanzu bazaka taΙa samunta ba ko, wataΖilama ta mutu, domin ina da tabbacin cewa baka shigeta da wasa ba”
“Dole zan sameta ne Abid, dole sai ta dawo gareni, kuma dole ta Ζara yarda da Ζudurina a karo na biyu, aure baya Ιaya daga cikin tsarina, amma idan taΖi yarda dani, saina aureta!”
Saurin kallon Zaid Abid yayi jin abun da yake fitowa daga bakin Zaid Ιin, “Aure kuma Zaid? Abid yafaΙa cike da mamaki.
“Ζwarai zan’iya aurenta Abid, Ζ΄an matan tana burgeni fiye da zatonka, inason komai nata, tana da kyau na fili dana baΙini, ni nasan mai naji a cikinta Abid, bakuma zanso nasake rasata ba, sha’awarta yasa koda yaushe cikin tunaninta nake, na kuma gama yanke hukunci, nan da sati Ιaya zankoma Nigeria, badon kowa ba sai don ita, nayi missing tattausan laΙΙanta masu zaΖi kamar zuma!!” Zaid yakai Ζarshen zancennasa yana mai lumshe idanunsa, da suka soma zama ja lokaci Ιaya.
Hangame baki Abid yayi yana kallon Zaid, “Anya kuwa ba aljana Zaid ya haΙu da’ita ba?” yatambayi kansa, tabbas baitaΙa ganin Zaid acikin hali makamancin wannan ba, gaba Ιaya Zaid ya sauya, yarage yawan yin sex da mata, a cewarsa wai bayajin daΙinsu, sannan kuma koda yaushe cikin tunani yake, to idan ba so ba meke da munsa ? Abid yakuma tambayar kansa.
A hankali Zaid ya buΙe idanunsa, haΙe da miΖewa tsaye kwalbar giyansa dakuma kofi ya Ιauka a hanunsa kai tsaye yanufi wani babban bene inda anan masauΖinsu yake, da kallo kawai Abid yabisa har ya Ιacewa ganinsa..
Yana shiga cikin Ιaki ya Ιaga kwalbar giyarsa ya kafa a bakinsa, saida ya shanye giyan tas kafun yayi wurgi da kwalba’r, kaitsaye ya nufi inda ma’ajin zane zanen sa suke, Caboard papers ne dayawa acikin wajen kuma duka Ιauke suke da hoton zanen fuskar Zahrah a jiki, wani ma iya bakinta kawai ya zana, wani ko iya idanunta ya zana, yana yawan yin zanen ne idan matsanancin kewa da sha’awarta ya da mesa, Ιaukan caboard paper’n dake Ιauke da zanen bakinta yayi haΙe da mannawa akan nasa bakin, wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, domin kuwa ji yayi tamkar itaΙince da gaske, zamewa yayi ya zauna a Ζasa daΙas, haΙe da warwatsa caboard paper’s Ιin akan jikinsa.
“Inakewarki Sugar Baby’na ,nayi missing komai naki, duk da cewa nasan kina fushi dani namiki da zafi, amma kiyi haΖuri wannan karon bazan miki da zafi ba, a hankali zan bi da ke tayarda zakiji daΙi har brain Ιinki, zakuma za ki saba da ni a sannu, na miki alΖawari zandawo gareki!, kina sona?” yatambayi zanen fuskarta dake jikin wani Ζaton caboard paper, “Nasan har yanzu kina sona ko Zahrah na?” still dai wannan zane yakuma tambaya, murmushinsa mai kyau yakumayi, haΙe da sanya hanu yashafi gefen kumatunsa.
” Kiyi murmushi Zahrah na, nakusa zuwa gareki, a yanzu zan iya sadaukar da komai na zuwa gareki, amma fa banso kina yawan fushi, duk da cewa idan kina fushi kinfi kyau !”
Haka Zaid yayita sambatun sa har bacci ya Ιaukesa a wajen.2
Kwance take akan Ζirjinsa, yayinda fuskarta ke ΙauΖe da murmushi, a hankali ya matso da fuskarsa daf da tata, cike da matsanancin sha’awa ya kamo lips Ιinta na Ζasa yashiga tsotsa a hankali, cike da Ζwarewa yake cusa harshensa cikin bakinta, cike da soyayya ta soma tsotsan harshensa tana mai lumshe idanunta, a hankali yayi Ζasa da hanunsa zuwa Ζirjinta, cikin salo yashiga shafa breast Ιinta, yanayin yanda suke sucking tongue Ιin junansu, shiyasanyasu suka fice a hayyacinsu lokaci guda, Ζasa yayi da kansa zuwa Ζirjinta, yana shirin Ιaura bakinsa a kan nipples Ιinta kenan, taΙace masa Ιat, dai dai lokacin yafarka a hargitse, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauΖe, duk da cewa sanyin A.C na aiki a cikin Ιakin amma shi gumi yake haΙawa, da Ζyar ya’iya miΖewa ya shiga bathroom haΙe da sakarmawa kansa shower.
ba yau yafara wannan mafarkin ba, amma maiyasa Zahrah take gudunsa acikin mafarki, takan Ιacewa ganinsa a daidai lokacin da yake matsanancin buΖatar ta….Yajima tsaye a gaban shower ruwa na dukansa, mafarkinsa na yau ne yatsaya masa a rai, duk da kuwa cewa ba wannan bane karo na farko, daya fara yin irin wannan mafarkin. Koda wasa baiyi niyar komawa America a yau ba, amma yanzu yaji ajikinsa cewa komawarsa can Ιin yafi masa, domin kuwa mararsa har Ζullewa take saboda sha’awa, gaba Ιaya kwana biyunnan da suka shuΙe baiyi sex ba. A gurguje ya shirya kansa, bayan yasanar da Abid cewa shima ya kimtsa zasu wuce America a yau. Suna zuwa airport basu wani daΙe ba, jirginsu yaΙaga zuwa sararin samaniya….+
Nigeria
Washe garin ranan da Dr yazo da dare yafaΙi muradinsa..
Tun tashinta takejin Ζunci a zuciyarta, hakanan take jin ta tsani komai na duniyar, badon lecture’n da zasuyi yau mai amfani bane, to tabbas da bazata je makarantar bama.
Doctor Sadeeq ne tsaye a tsakiyar Ιakinsa, yayinda hannayensa duka biyu ke sanye cikin aljihun wandonsa, shima kallo Ιaya zaka masa kafahimci cewa yana cikin damuwa, kallon sa yamaida kan agogon bangon dake saΖale ajikin bangon Ιakin na sa, Ζarfe 7 da rabi na safe kenan, tabbas yasan yau Ζarfe takwas suke da lecture, yanaji a jikinsa cewa yayi mata laifi mai girma, sannan idanunsa suna matuΖar son ganinta, to amma a yanda yakeji bazai iya zuwa gareta ba, “idan ma naje nace mata me?” yatambayi kansa. ” Nariga dana furta mata abun dake cikin zuciyata, dole zanbata lokaci domin samun dawowar nutsuwar ta” yafaΙi hakan a bayyane, wayarsa ya Ιauka haΙe da kutsawa cikin dialing call Ιinsa, numbern drivernsa yashiga Ζira kai tsaye, Ζara biyu wayar tayi, drivern yaΙauki Ζiran, kasancewar driver’n yasan gidan su Zahrah, yasan ya kai tsaye, bai tsaya yi masa wani kwatance ba, yace masa yaje ya Ιauketa ya kaita makaranta, da “to” kawai driver’n ya amsa masa, katse Ζiran yayi haΙe da cilla wayar tasa zuwa kan gado,
“Yasan balallai ta yarda tabi driver’n ba, domin yanayinta da yagani jiya, kaΙai ya isa ya tabbatar masa da hakan, amma burinsa ne ya bata ingantacciyar kulawa, shiyasa baiyi Ζasa a guiwaba wajen sa driver’n nasa kaita makarnta, saboda baiso ta hau wani abun hawa bayan nasa….
Ko kwalli, yau bata shafa ba, balle kuma uwa uba fawder, zumbuleliyar doguwar riga ta sanya, haΙe da Ιaura Ζaton hijab akai, kallo Ιaya zakayi mata kasan cewa tana cikin damuwa da Ζunci.
Koda tayi mawa su Baffa sallama, suma sun fahimci cewa yanayinta ya sauya, amma sai suka share babu wanda ya tambayeta.
Tana kai Ζofar gida zuciyarta tayi wani irin bugawa, sakamako’n ganin motar Dr Sadeeq, da tayi fake a Ζofar gidan nasu, tsayawa tayi cak ganin cewa driver’n sane yafito daga cikin motar, saΙanin shikansa Dr Ιin.
Cike da girmamawa Mudi driver ya Ζaraso inda Zahrah ke tsaye.
” Ranki shi daΙe barka da safiya! dama yallaΙoi ne yace nazo na kaiki makaranta, shi ba zai samu daman zuwa ba, wani aiki ne ya riΖesa, kawo jakar na karΙamiki” Mudi driver ya Ζare zance’n nasa yana mai ΖoΖarin karΙan jakar dake riΖe a hanunta. Saurin ja da baya tayi haΙe da fusge jakarta, cike da Ιacin rai tace.
“Kakoma kace masa bana buΖatar kulawarsa koda kaΙanne, ka kuma ce masa injini yafita a rayuwata, saboda bana buΖatarsa!” tanakai Ζarshen zancennata tasakai tayi tafiyarta.
STORY CONTINUES BELOW
Da kallo kawai Mudi driver yabita. “Uh ni naga bala’i, daga taimako kawai, to Allah ya kyauta” Mudi yafaΙa yana mai komawa cikin motar, key yayimawa motar haΙe da nausata kan hanya, tabbas zai koma ya shaidawa uban gidansa, duk abun da tace a faΙamai..
Cikin ikon Allah tana isowa bakin titi tasamu mai taxi, bawani Ιata lokaci tashiga yaja sukayi gaba, bayan ta sanar masa inda zai kaita.
Tun shigowarta cikin ajin, Husnah ta lura da mugun sauyawan da fuskar Zahrah’n tayi, domin kuwa kowa ya kalli idanunta, zai fahimci cewa tayi kuka har ta Ζoshi. kasancewar Zahrah’n na shigowa malami yashigo, yasanya Husnah bata samu damar tambayarta komai ga me da sauyawarta ta ba.
Koda aka fito daga lecture, kan dakalin da suka sama zama, yauma sukai mawa kansu masauΖi.
“Wai meke damunki ne Zahrah? gaba Ιaya kinsauya, bayan jiya ba haka muka rabu dake ba, sannan kuma na kula cewa, yau ba Dr bane ya kawoki, maike faruwa?” Husnah ta tambaya cike da kulawa, ga Ζawarta ta.
“Inacikin matsala Husnah! a she a yanzu babu wani, wanda zai taimakeka don Allah sai don biyar buΖatar kansa? na Ιauki yarda ta na basa, na Ιaukesa tamkar Ιan’uwa, na’aminta dashi, nayi saurin yadda haΙi da sakewa dashi, bantaΙa zaton haka zata faru ba, ashe shi abun dake cikin zuciya da ruhinsa daban ne, wani abune saΙanin tunani na!” Zahrah tafaΙa tana mai share Ζwallan daya gangaro daga cikin idanunta.
“Banganeba, kinsani a duhu, maikuma ya sake faruwa? ki faΙamin !” Husnah tafaΙi hakan cike da zaΖuwa, don ta Ζosa taji menene matsalar Ζawarta ta.
“Kinsan abun da yafaru dani Husnah, Zaid yaci mutumci na, ya Ζwaci budurcina da Ζarfin tsiya, ya halaka min rayuwa, shin kinaga akwai wani namiji dazai soni tsakani da Allah, bayan yasan abun da yafaru dani?” Zahrah ta tambayi Husnah.
“Haryanzu banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zaifi kyau ace kiwarwaremin komai!” Husnah tafaΙi hakan cikin rashin fahimta.
“Ba gaskiya bane Husnah, bai faΙawa kansa da zuciyarsa gaskiya ba, baizamanto gaskiya ba, soyayyar da yakemin ba gaskiya bace, Husnah bazan yaudari kaina ba, domin nasan babu tayanda za’ayi cikekken namiji mai aji da lafiya kamar Doctor Sadeeq, yace wai ni yake so ya aura! ina kokonto akan al’amarin !” gaba Ιaya hawaye sun gama wanke mata fuska, lokacin da takai Ζarshen zance’n nata.
Nannauyar ajiyar zuciya Husnah ta sauΖe, domin kuwa sai yanzu ta fahimci inda matsalar Ζawartata take, dakuma abun da ke damunta.
“Doctor da kansa yace zai aure ki Zahrah?” Husnah ta tambaya, bayan ta aza hannayenta duka akan kafaΙun Zahrah.
Kai kawai Zahrah ta’iya gyaΙawa, alamar “eh”
“Ba wasa bane Zahrah kamar yanda kika Ιauka, haka kuma ba yaudara bane kamar yanda kike tunani, har yanzu keΙin mai kyauce, kuma haryanzu keΙin haΙaΙΙiyar mace ce abar so ga kowani irin namiji, ba’akanki a ka faraba, baikuma dace ki Ιau hukunci mai tsanani gawanda baiji ba bai gani ba, kina tunanin Doctor Sadeeq yaudaranki zaiyi ?” Husnah ta tambaya.
“Ζwarai kuwa Husnah, ke kanki kinsani, namiji kamar Dr ba sa’an aurena bane, ko lokacin danake Ιauke da mutumcina yafi Ζarfina, balle yanzu danake fanko, inaso kisani wannan karanbani’n shi na tafka a karon farko, yazo yazamemin babbar matsala, domin kuwa nayaudari kaina, na sawa zuciyata soyayyar wanda har gaban abada yafi Ζarfina, yakuma yi mini rata, na yaudari kaina danaΖi amfani da tunanin cewa Zaid yafi Ζarfina, bazan taΙa yarda nasake aikata haukan dana aikata a baya ba Husnah!” Zahrah tafaΙa cike da raunin murya dana zuciya.
“So baitaΙa zama haukaba Zahrah, kada kicemin kin wulaΖanta Doctor saboda abun da Zaid yayi miki, kada ki yarda da tunaninki nacewa gaba Ιaya maza mayaudara ne, kowa da irin halinsa, kuma masu irin halin Zaid basa Ιoyuwa a kamanni da halaye, soyayyarsa ce kawai tarufe miki ido, har ki ka kasa hango mummunar manufarsa a kanki, yana da kyau ki nutsu kiyi tunani, inada tabbacin cewa Dr Sadeeq, ba zai taΙa cutar da rayuwarki ba, kema kuma yakamata kisan hakan, kada tunaninki ya gushe ki kasa tantance fari da baΖi, wlh ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq ba mutumin banza bane, bakuma zan Ιoyemiki ba, tabbas idan kika tsaya wasa da damarki, to zata miki mummunan suΙucewa, haΖiΖa Dr Sadeeq haΙaΙΙen gaye ne, wanda ko wacce mace zatayi fatan samunsa a matsayin mijin aurenta, nasan idan nace miki kiyi soyayya yanzu na haΙaki da babban aiki, amma zai kyautu ace ki koyawa zuciyarki soyayyar Dr Sadeeq, shawara nake baki Zahrah, idan kuma har kikayi amfani dashi, bazaki taΙa danasani ba, dan Allah Ζawata kiyi tunani mai kyu!” Husnah tafaΙi hakan cikin son Ζarfafawa Zahrah guiwa.
STORY CONTINUES BELOW
Hawayen dake zuba daga cikin idanunta ta sanya hanu ta share.
“Bazan iya ba Husnah, bazan iya taΙa sake son wani ba a cikin rayuwata, kada ki ga laifina, nasan Dr Sadeeq yafi Ζarfina, yana da asali, yana da Ζ΄an uwa, yanada gata, yana da kuΙi, yanakuma da Ζ΄ancin da zai zaΙi matar aure wacce ransa keso, nikuma fa? idan kikayi dubi da tushena, to ban cancanta da zama inuwa Ιaya da shi ba, nifa yanzu banda wani Ζ΄ancin da zan iya zaΙin mijin aure da kaina, sbd akwai nakasa acikin rayuwata, dole sai mai tawakalli ne zai iya aure na, to maiyasa zansanya kaina a cikin wahala? balallai farincikin da Dr Sadeeq ke ΖoΖarin bani yakasance dauwamemmeba, nafaΙamasa yafita a rayuwata Husnah, a yanzu bana buΖatar kowani namiji, zaifi kyautuwa a gareni nayi rayuwata ni kaΙai, nayarda da Ζaddarata, amma kuma yazama dole na kiyaye sake jefa kaina a haΙarin soyayya!”
Rungume Zahrah,
Husnah tayi ajikinta, sosai tausayin Ζawarta ta ya kamata, haΖiΖa Zaid yacutar da rayuwar Zahrah, ya rabata da duk wani sukuni nata, amma a kwai Allah.
“HaΖiΖa dole zakiji ciwo Zahrah, amma yana da kyau ki zurfafa tunani, ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq auren ki yakeso yayi bada wasa ba, amma abun da kikayi masa baki kyauta ba, ki basa haΖuri, koda kuwa bazaki auresa ba, yayi babban ΖoΖari acikin rayuwarki, kiyi nazari, amma kuka ba naki bane, kuma yana da kyau rama halacci da alkhairi !”
Gaba Ιaya Zahrah jitayi jikinta yayi laΖwas, take marin da ta shararawa Dr Sadeeq akan fuskarsa ya dawo mata, wani irin faΙuwar gaba taji, ko kaΙan batayi tunanin zata iya kai hanunta jikinsa da sunan duka ba, amma a daren jiya Ιacin rai yasanya idanunta rufewa, harta iya ta mare sa batare da tayi tunanin komai ba, tabbas komai yayi mata bai cancanci mari daga gareta ba.
Gaba Ιaya kasa sakewa a cikin makarantar Zahrah tayi a wannan ranan, dole ta tattara yanata yanata ta dawo gida.
Zaune take jigum akan tabarma yayinda hannuwanta ke dafe da Ζuncinta, idan da za’a ce za’a kasheta idan bata faΙi, tunanin me take ba, to tabbas da sai dai a kashetan, amma ita kanta batasan tunanin mai take ba.
Inna da fitowarta kenan daga bayi, hanunta riΖe da buta, kama Ζugu tayi, haΙe da maida kallon ta zuwaga inda Zahrah ke zaune tayi jigum.
“Wai lafiyanki kuwa Zahrah? meke damunki ne? tun safe haka kike sukuku, yanzu kuma kinyi tagumi tamkar wacce akamawa mutuwa, kodai halinki na da, kike son dawowa dashi ne? to wallahi bazan Ιau wannan iskancin ba, tun wuri ma kisani!” Inna taΖare maganar cikin faΙa faΙa.
“Ko Ιaya bahaka bane Inna, narasa taya zan Ιullowa matsala ta ne!” Zahrah tafaΙa cike da sanyin murya.
“Matsala! wace irin matsala kuma?” Inna ta tambaya cike da son jin gulma.
“Inna wai Likita ne yace zai aure ni !” Zahrah tafaΙi hakan cikin sarΖewar murya.
“Likita yace zai aure ki!” Inna ta maimaita maganan cikin Ζaraji haΙe da sanya duka hannayenta biyu ta dafe Ζirjinta.
Kai kawai Zahrah ta’iya gyaΙa mata domin zuwa lokacin har Ζwalla sun soma cika mata ido.
Wani irin guΙa Inna tasa, haΙe da sake kama ΖuΖu, “Lallai kuwa, wannan babban al’amari ne, mai Ιauke da tarin farinciki, Allah yasa dai kin amince masa?” cike da zaΖuwa inna taΖare maganar.
“Bazan iya ba Inna, kuma ma ni yanzu babu batun aure a tsarina,zan zauna kawai naΖare rayuwata cikin Ζaddarata!” Zahrah tafaΙa lokacin da hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa.
Salati Inna ta sanya, haΙe da soma tafa hannaye.
“Amma kedai Zahrah anyi shashar banza, sokuwa marar wayo, ashe dai baki da hankali, yanzu a yanda kike Ιin nan, kin samu ance za’a aure ki a haka, kice wai baki amince ba, lallai yau nasake tabbatar mawa da kaina cewa ke wawuyace, to wlh baki isa ba, baki isa Ιarar mana da alkhairan da zamu samu ba, aure dole ko kina so ko bakya so, wato kinfiso kita zama damu, goΙo goΙo dake ba aure ko, to kisa aranki cewa aurenki da likita ba fashi, dole!”
“Babu wanda zai mata dole!” Muryan Baffa dake shigowa cikin gidan yakaraΙe kunnuwansu.
“Maikake shirin faΙa ne malam, kakosan me ta aikata kuwa, Likita fa yace yanason aurenta amma taΖi?”
“Ζwarai kuwa duk na saurari zancen ku, magana ta gaskia Salame, baza’ayiwa yarinyar nan dole ba, yanzu lokacin ta ne, yakamata a bar rayuwarta tasha iska hakanan!” Baffa yafaΙi maganar sanda yayi mawa kansa masauΖi akan wani Ιan dakali dake tsakiyar gidan.
“Laaaa shikenan kuma, kakosan abun da kake cewa? kana nufin zuba mata idanu zamuyi, ba mu isa mu sata dole ba? wani shan iska kake ΖoΖarin samawa rayuwarta, sanin kankane cewa babu wani wanda zaizo yace zai jajiΙeta a yanda taken nan, don kawai likita ya rufa mata asiri yace zai aureta, saikayi ΖoΖarin hure mata kunne.”
“Tashi ki koma Ιakinki kinji Zahrah, kiyi tunani mai kyau, idan kin yanke hukunci to kisanar dani!” Baffa yafaΙa cike da kulawa.
Cikin rashin Ζarfin jiki haka Zahrah ta koma cikin Ιakinta, yayinda take jiyo bala’in Inna a tsakar gida.
Jingina bayanta tayi da bango, haΙe da lumshe idanunta, saiyanzu take jin cewa bata kyautawa Doctor Sadeeq ba, amma kuma shima baikyautu ace yazo mata da magana mai nauyi kamar wannan ba, ko da wasa bata taΙa kawowa a ranta cewa wani zai sota anan kusa ba, gaba Ιaya ta cire soyayya a tsari da jerin rayuwarta, tabbas sai dai ta yaudari kanta, amma tasan bazata taΙa Ζara son wani Ιa namiji ba a rayuwarta, ta yarda da shawaran da Husnah ta bata, amma kuma abune mawuyaci, tarayyanta da Dr Sadeeq yazama mai Ιorewa, shin dagaske aurenta yakeso yayi koko shima wata manufartasa yakeson cimmawa? tatambayi kanta tambayar da bata da amsa, “Idan bakiyi aure ba, haka zaki dawwama Zahrah?” wata zuciyarta tayi mata wannan tambayar. hawayene suka shiga gudu akan fuskarta, lalllai akwai babban Ζalubale a gabanta.
Zaune yake akan derny table Ιin dake tangamemen falon Hajiyar tasa, plate Ιin abinci ne aje a gabansa, yayinda yake juya spoon Ιin dake cikin abincin dake gaban nasa a hankali, kusan mintuna 10 kenan da kawo masa abincin, amma yakasa koda kai loma Ιaya ne na abincin bakinsa, gaba Ιaya hankali da tunaninsa baya garesa.
Cike da tuhuma Hajiya da tun Ιazu take kallon sa tace
“Wai meke damunka ne Sadeeq? gaba Ιaya yanayinka ya sauya, kowa yaganka yasan cewa kana cikin damuwa? gashi nace kaje gidan su Saleema, amma kayi banza da maganan bakaje ba har yau”
Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauΖe haΙe da maida kallonsa ga mahaifiyar tasa.
“Inada damuwa Hajiya!” yafaΙi hakan cikin sanyin murya.
“Subahanallah! damuwa kuma Sadeeq, damuwar me?” Hajiya ta tambaya cike da kulawa, Allah yasani tana matuΖar son Ιan nata.
“Nasamu wacce nake so ne Hajiya!” Sadeeq yafaΙa cikin Ιar Ιar, don baisan ya Hajiyar tasa zata Ιauki al’amarin ba.
“Kasamu wacce kake so? wani irin magana ne wannan, wato so kakeyi kamai dani Ζaramar mace ko, to wallahi baka isaba, bazai taΙa yiwuwa ba, nariga dana gama magana da iyayen Saleema, har Ζanin mahaifinka yashigo cikin lamarin, saboda haka wannan batun kama dainasa tun kafun ranka yakai Ζololuwa wajen Ιaci, banason shirme!” Hajiya tafaΙi maganar a fusace, haΙe da tashi tabar masa falon.
Tabbas dama yasani ko da Zahrah ta amincewa aurensa, to balalle ne Hajiyarsa ta amince masa ba, amma yasan cewa yanamawa Zahrah so mai tsanani, kuma insha Allah, zai aure ta ya rayu da’ita har zuwa Ζarshen rayuwarsa, domin yaji hakan a jikinsa.
Post a Comment for "SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 6 BY FATYMA SARDAUNA"