SHU'UMIN NAMIJI CHAPTER 3 BY FATYMA SARDAUNA SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 3 BY FATYMA SARDAUNA Www.bankinhausanovels.com.ng Wani irin kallo mai ta da tsikar jiki Zaid yayi mawa Zahrah, still fuskarsa ɗauke da wannan sheɗanin murmushinnasa, sadda kanta ƙasa tayi haɗi da soma wasa da yatsun hanunta,, Sunanta yaƙira da wata irin murya mai kwantar da zuciya, bata iya amsa masa ba saima ɗago kanta da tayi ta kallesa, wani irin baƙon yanayi ta tsinci kanta aciki mai wuyar fassaruwa, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa masu kalar bacci haɗe da buɗesu a lokaci guda,, “Zantafi !!” yafaɗa daidai lokacin dayake ɗaura sit belt a jikinsa, kasa ce dashi komai tayi saima wani iri taji dayace zaitafi ita a sonta bataƙi su tabbata a haka ba, domin ganinsa kaɗai yakansa taji wani irin nishaɗi a cikin zuciyarta,, wata ƙatuwar leda mai ɗauke da tambarin wani makeken mall yamiƙo mata, sadda kanta ƙasa tayi haɗe da girgiza kanta, alaman bazata karɓa ba,, ɗan ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa ” idan baki karɓa ba bazanji daɗi ba, kuma k…