ABUNDA KE BOYE BOOK 1 CHAPTER 3 HAUSA NOVEL

kowa yasani, prof zayyanu is very sensitive and over reactive akan yarsa zainab arifah gani yake kamar gwal ce daga sama Allah ya sauko masa dashi, ya




 kowa yasani, prof zayyanu is very sensitive and over reactive akan yarsa zainab arifah gani yake kamar gwal ce daga sama Allah ya sauko masa dashi, yanzu ko tsawa kama Zainab arifah taje gida tana kuka sai ya zamo muku babban case da shi, da suka gaji da irin cin mutunci da baqaqen magana dayke fetsa musu idan sun mata gyara yasa kowa ya ja baya da ma zainab din gyara aka bar masa yarsa msmn ma dayasha gaya ma bappa zaidun cewa duk sanda ya takura ma yarsa da wa'azin karya wallah sai ya

kulleshi.


infact haryau zarginsu yake da cewa tunda Allah ya bashi yarsa suke neman hanyar da zasu rabashi da ita dan inya mutu a kwashe arzikinsa akawo musu..


Duk da rakin hajiya haka bappa zaidu ya dakatar mata yafara tuna mata wayannan maganganun saida tay shiru


yace mata duk cikinsu babu wanda yake son yay fama da kazafi da zargi, ynxu qaddara wani abu yaje ya same zainab a gidan nan toh dole ne su zaa kama a kulle, kuma faɗar da gaban cikin gida ne, ..babu abunda zai jawo musu face zubewar kima da mutunci awaje, tunda yace abar masa yarsa saidai in ita zata iya masa mgn bazasu hanata ba...

atsakiya hajy mairon ta sakasu tanata bori cewarta babu abunda zai hanata itade ta gayawa zayyanu gaskiy bayan sunsan yanxu kusan shekara bakwai kenan basuy waya dashi ba



Bangaren zainab din kuwa tana saukowa daga kan steps nacikin babban palourn gidan ta miqe Inda taga Babu kowa 


Dan tsayuwa tayi cikin nazarin Inda zata soma duruwa Can saiga sautin saukowar maheer ahnkli yake saukowa he is wearing dis calm coffee-brown T-shirt da Khaki trousers da sneakers sanye da wireless ear piece a kunnensa yana amsa waya, tana ganinsa da sauri ta taho tanamai tareshi


Shikuwa sanda ya Gama amsa wayarsa tsaf sann yaji kmr zai saurareta suna hade ido tahau murmushi tana kankance voice tace "whats up Big bro",


maheer ya hade rai,tana dan murmushi tace pls tmbya nake ko kaga Inda sauran mutanen gidan nan sukayi?..cos I came down here but no one is available..Idanunshi nakan wayarsa a hnkli yace "I don't know...


Kallon sa ta cigaba dayi shikuma baisan yawan kallo

yace Asali Wai wakike nema ne? bude baki tayi kamar zata amsa taci Karo da fararen idanunsa masu asalin kyau da daukar hnkli, wani kafeshi tay da ido tsaban yadda taji wani maqudan bugun zuciya na taso mata in her mind she was like dis guy is damnn hot too har wani kama taga ykeyi da dad inta musmn inya hade ransa, too many hot choices around here saidai haryau bataga wanda yazo mata kusa da irin kyauwu da ajin ibaad ba ji take har duniyarta yanade bazata ga wanda yakai ibaad ba


jin ta bace shiru yasashi dagowa ahnkli yace in su hajiya kike nema Suna can dakinta, And U can check out the rest atacan sashen anty safeera..Da Dan Murmushin ta tace mai ok thanks, shareta yy kamr badashi tayi ba ya juya kansa abunsa, ta kyabe baki batama jira ba ta bar wajen tanufi falon ahnkli tana takawa Kan matakalar da zai sadaka da ta wajen cikin sauki



Dan madaidacin falon sama ne mai Dan uban kyau da tsari wanda ba acika mai tarkacen kwalliya ba daga yan flawowi sai sofas da na asalin round glass table Wanda aka kawata shi da fararen kujeru masu dauke hankli


Wani salon taku take tana Jin yadda iskan Acn wajen ke famar hudata saidai harta karaso wajen su fuskrta ba asake ba ganin yadda yaran gidan gabakiya suka mamaye mujaheed ya sake yana zabga dariya acikin yar hirarsu da su sultana da su ayaanah safiya ce kawai  ta kafe idonta a tv tana kallon indian series a star life da alama ko jinsu bayi takeyi ba..


Tana shigowa wajensu ayaanah tayi shiru ta yanke hirar da sukeyi har Arifahn ta soma masa magana cikin kayataccen salon data shirya tazo dashi, yadda bata musu sallama ba yasa sauran yaran duk basu daga ido sun kalleta ba kowa yay shiru face khultum datake da taurin kai ta cigaba da maganarta abunta kmr bata san wata ta shigo wajen ba


zainab arifah dake Kansu tana tsaye cikin yar sautin murmushinta mai tafe da yaudararren salo tace ma mujaheed "mjay can I sit with u guys? yace ok. ta karaso cikin tafiyar yanganta mai sanyi ta zauna ata dayan bangaren Agefe dashi kowa na satar kallon kalar shigarta amma ita ayaana kawai take kallo..


Da dan Jin haushin yaran aranta musman nakin basu waje tace"I hope I'm not interupting anytin? da Basu amsata ba ta cigaba, tace"..so Mr south africa Wani hirar akeyi bandamu kaifa kamata yayi ace hutawa kakeyi ba surutu ba,..right girls?Ta mayar da tambayar Kansu sultana Wanda suka dago cikin sauri suka mata kallon raini..


A hnkli ayaanah ta miqe kamar zata bar wajen ya mata Ido akan karta tashi


Sosai Hakan ya bawa zainab arifahn haushi dan ji take kamr jininta sam bai hadu da yarinyr ba amma a fuska murmushi kawai take tamkar bahakan take rayawa aranta ba,gyaran muryan sa daya fito a hnkli yasata bada hanklinta kanshi..


wasu irin damning question tafara masa akan ayaanah 

musmn ma akan kauyensu waye babanta, tana so dai ta dawo da batun kmr almajira aka dauko musu aka kawo


feeling iritated da hirar yasa kulthum ta miqe tsaye tana kallonsu ayaana tace  i think I'm gonna go inside inkun Gama hirar Kusameni aciki..


tun basu amsata ba mujaheed ya ganota cikin hade rai yace aa, babu inda zakije zauna kawai baga wata antyn taku tazo tayaku hira ba


..Hade rai kulthum tayi batace uffan ba ta zauna kusa da ayanah tana mata alama da ido akan kartay fushi, sama sama ake hira, har saida aka aje talla style life sann safiya tajuyo ta gaishe da zainab arifa ta amsa ta a dakile dan sosai ta lura da yaran gidan kmr suna da raini sosai .



satar kallon ayanah take trying to figure her out taga dai fatar jikin a wanke yake da haske irinna buzaye but with this unique smooth like Ethiopian looks, idonta manya, gashinta idonta dogon gaske bataga dai  alamann wani extension ba nd she cant just get enuf of her sai ta tuna ashe ance daga kauye ma hajiya mairo tazo da ita hala bata iya turanci ba.



wani abu taji yana dan motsa mata a zuciya ta fetsar da numfashi me cika da isa tana kallon Ayanah sama da ƙasa.


suna hade ido tace “you… what’s your name?dagan gan ta yi magana da harshen turanci cos she just want to embrass ayanah awajen nd make fun of her.


Ayanah ta juyo kaɗan tay shiru jin kowa yay shiru saita kalle xainab din cikin idonta tace “My name is Ayanah,”ta amsa cikin smooth clear English.


Zainab Arifah tay jim dan tayi tsamanin yarinya daga ƙauye haka ai ba za ta iya sanin haka ba but anyways dats a simple one


Ta kalli dogon gashinta ta ɗan ja igiyar jelarsa a hankali tace “is your real hair? Or is it attachment?” ta na jan jelar ayaanahn faɗa da murmushin rainin wayo....wanda ko safiya ma barin kallonta tay ta juyo tana kallonsu tana Allah Allah ayaanah ta kwafsa ta fashe mata da dariya


Ahankli ayaanah ta janye jelar gashintan daga hannun zainab  Arifah tabari ya sauko bayanta kamar an sake ruwa sabida yana da yauqi irin silkness na korean hair in nan acikin kwanciyar hankali tace malamin mu yace mana "attachments is haram acan garinmu kowa ai yana da gashinsa.. 


kulthum tay smirks ganin yanda zainab din tay wani iri da fuska tace “so, its REAL?”


da azarbabi sultana ta janye small veil din ayana ta kara warware mata gashin tace "yeah it is u want to feel it?

dagangan ta warba mata ajiki

tay saurin yarfawa Yaran suka yi dariya kaɗan. anty Zainab yakikaji laushi? hararar sultanan tay tayi shiru da alaman taji haushi, Hankalinta ya fara tashi sosai cikin basar da batun gashin ta kalli ayanah "well, i am just quiet suprise u speak good English..innocently Ayanah tace “Yes. I go to school. har wannan lokacin kallon ayaanah mujaheed yake tay yanajin ta burgesa ganin sunata fafatawa confidently take amsa zainab batare da tsoro ba.


can dayaga zata fara mata slangs yay sauri yace “Zainab, ke fa ba size ɗinta ba ce. Ki yi halin manyan mana ki kyaleta


zuciyarta na tafarfasa taciki tace "ure ryt, i think i just lost my drive to talk barinje dakin anty safee i need to be alone tana fadin hakan ta mike ta haura sama, wani dan uban karar dariyar su kulthum da sultana taji nabibiyarta abaya


safiya ma sosai taji mugun haushi saita bata shiru a falon ta kara kafe tv da ido


surutu ne ya kaure sultana ta rike kafadun ayana tana dariya tace i knew u knw how to speak english, duk na miki magana da turanci kina jina shine mu baki taba mana bako? kulthum tana kyalkyala dariya tace "gashi yau tay a inda yake da amfani,.yaa mujaheed amma kasan anty zainab dai tana mata turancin ne danta kunyartar da ita ko?? 


dariya kawai yakey yaki ce musu komi..yabarsu sunata making fun din abun har saida sukaji sallamn maherr  kafin nan suka nitsu 


daga nan har akaci abincin rana zainab arifah tana can sama bata kara fitowa ba har saida yamma yay aka kusa zuwa daukar ta snn ta fito ko kallon su batay ba taje neman ibaad, a kofar masjid ta samesa suka gaisa sama sama he notices how her eyes was a bit red sabida ɓata mata rai da akayii agidan yau amma dake abune da bai shafasa ba sai baice mata komi ba har drivernta yazo ko sallama batama hajiya mairo ba ta wuce gida abunta, bayan tafiyar zainab arifah gidan was calm nd quiet for a while, can wajajen bayan magrib kulthum ta fito daga wajen maheer da qur'ani hannunta tana isowa falonsun ta tsinci koina shiru batayi wata wata ba tahaura sama dakinsu ta same both ayaana da sultana suna kkrin idar da sallah atare


kallon sultana tayi daga kan sallaya ta budi baki a mamaknce tace"..oh my god siss wato ke sallah ma kikeyi bakima shirya tafiya bako? toh wallah kinsan yaa ibaad bazai juri jiranki kuma nasan anayin isha zaa ce ki fito kutafi gida.


 ..sultanah batace uffan ba taƙare mata kallo dan bakaramin kyau yau kuthum din tayi ba musmn dataje wajen maheer ta sauya kaya tasaka pure atamfa dinkin fitted na riga da sket takuma yi lullubi tafito zak arewa beauty masha Allah. 


cikin kif kifta ido da kankance murya tace "toh nikuma shirin me zanyi bayan next week ma zamu kara zuwa kinga ni wallhy gidanmun nan ya ishe kamar karna tafi, ayanaah dai batace musu komi ba kulthum tana ta kallon bakin sultana datake turowa gaba gaba cikin mita batasan sanda tyi dariya ba"sis wallhy ure sooo funny ke kenan kullum zaki tafi gidanku kinta fushi kenan ko toh ki shirya dai yaa ibaad ne zai jaku a mota..kuma kinsan dai kika batamai mood yau ba kyaleki zaiyi ba dan wallh bakiga daukar wankan da yay bane yay wani fresh yay kyau, keeeee!! wata mayyar Plain black polo yasaka with this Ash-grey pants da wata irin blck sneakers da Silver wrist watch, mehnnn gashi ta dan kamashi guys kuzo kuga wankan swags, wallh nikaina saida naji kamar in sace shi, he is damn hot....


tuntuni su ayaanah sai kallon ta sukeyi tana rau rau da ido can sultana tace sis are u okay kuwa?ko kinsha wani abu a hanya ne yaa ibaad  fa is always gushing hot kowa ya sani


tace "yeah i know" ta ai naga mutumiyarsa ta gudu gida ne, ayaana ta kunyata sheigya..ta fada kan gado tana dariya..


sultana ma tafara dariya Dan Allah dagaske kike ya shirya?

tace..."ohh u think im crazy, okay ki dan leka side din ammi karama ki tabbatar ma idanun ki..


cikin yarfa hannu sultanah tace niki kyaleni kar yaje ya wanka min mari kinsan dai daga ganin irin wannn wankansa anty zainab taje shagala taje takamo da sonsa kuma ai kinga karshen ta baiyu kyau a hannunsa ba...mugun haushi take bani tana wani abu  kamar wata kucaka innine shi har abada bazan so ta ba


atare suka fashe da wata muguwar dariya ganin ayaanah bata saka bki a hirar ba da muryan tsokana kulthum  ta jawo sumanta ahnkli cikin kwaiwakyon zainab arifah tace "hey. is ur hair real? or is it attachment? sanda ayaanah ta fara dariya ma bata sani ba

sultana ma tafara mimicking

sukaci dariya


tace"i dont knw what her problem is oo nifa na lura kamar tazo ne tay embrasiing dinki ayaanah, ...ahanki ayaanah tace toh ai ni bansanta ba..


quiet seriously kulthim tace ai kuwa yanxu zan baki labarinta ta kama hannun sultana tay da ita gaban mirror tace toh zauna na gyara miki hair dinki saiki fara shiryawa nikuma ina bawa ayaana kanun labarai


suna farawa kulthum ta kalle ayaanah tace yaya ibaad, yaya ibaad, hmm yaya ibaad the dangerous mupper. majinan bango ahauka a zame kahau mutum kazauna dai dai wani uban dariya suka fashi 

dashi mai ƙarfi harda tafawa ita da sultana. 


nn ta kalli ayaanah tace sis  ingaya baƙaramin drama akayi a gidan nan ranar ba, nikaina naci dariya kamar inyi yaya amma fa saida naje harr schl dinmu nayi dariyan indan

a gidan nan ne da bakizo kin sameni ahakan ba hala da an kaƙƙarya ni.


ayaanah tace why meyafaru? dariya ya riga yaci ƙarfin kulthum amma hakanan ta fara bawa ayaana labari tace  anty zaina  ce mana da uban rawan kanta ranar bansan wani shaidan ne ya shiga jikinta taje ta cewa yaa ibaad wai tana sonshi....haba mana

daga nan sultana ta saka baki suka fara bata labarin irin tsuge zainab din da akayi da wayar wuta, word to word har kukan datayi yadda kulthum take mimicking wayyo Allah daddy kazo ka ceceni yasaka abun ya zama so funny


....magana kawai takeyi amma tuni idanun ayaana already ya cikko da ruwan hawaye tsabar taci dariya dan har ƙasa taga su sultana sukakai tare suna kyakyatawa kamar wasu sabbin mahaukata. 


sai can da kulthum tsagaita tace wow u guys are really fun to be with zan masifar missing dinku wayyyo kamr karki tafi


sultana tace sis ya isa haka karki yaudare ne.. snn yakamata mubar hirar nan haka kar wata rana yajimu yace muna gulman shi a mana ciki da bai irinnna anty zainabuuuu..kara kwashewa da dariya sukayi


tace thank God sunzo sun dan shirya yanxu but rlship dinsu is so weird nd funny yana son fushi ita kuma shegen naciya

..gata da iya barazana hargara ynxu ma naga yana tsayawa ya kulata amma dacan hmm ko gaisawa baya shiga tsknsu


...sultana tace "maybe fa ansashi sun sasanta ne, dan ranar babanta ne ya aika aka kirashi yaje gidansu daga nan kuma naga ta dawo da rawar kanta tanakan bibiyarsa kamr wata jela har ynxu..


wannan hirar suka dingayi tun ana raha ana dariya har abun yafara sakama ayaanah tashin hankli acikin ranta batare da tasan dalili ba. 


musmn dataji sultana tafara kawo magann ai iyayen ne sukeso su hada su aure hala shiyasa yaa ibaad yanzu baice mata komi yake kyaleta


within no time har kulthm tagama tayata shiryawa ta tattara kayanta duka suka shirya tsaf ta saka black abayah mai mugun daukar ido da mayafinshi nayin rolling..


ayaana kuma wani designer turkish skirt ne ajikinta da riga mai dogon hannu ba wani design mai yawa bane ajikin shi face golden beats da stripes da akayi striping tawajen wuya da hannun rigar din dashi aka zagaye shi da stones fari masu kyalli, kwalliyar ta nayau  was more lighter than ever kwalli kawai ta saka a idanunta kulthum tay working mata eyes dinta da ghost shades lines idon ya zama so sexy nd natural,eye balls dinta suka fiffito suka bada yanayin luiiii shape din tamkar kuma nata ne na asali, man bakin data shafa was very shiny hakan ya saka tayi lining dinshi da pitch lipstick so her face was shining bright and fresh as hell.. suka fetsa perf ana kirar isha suka jero sukayi isha'in su atare.



suna idarwa suka fara parting junansu with goodbye speech dan babu karya cikin kwanaki sha hudun nan da sukayi tare a dakin kulthum bakaramin shakuwa da junansu suka kara yi ba musmn ma ayaanah da ta fara sabawa dasu sosai 


cikin salo kulthum ta riko hannun ayaana ahankli tace sis, i am very proud of u for speaking up agaban anty zainab arifah karki bari dan anaga kinzo daga kauye ana rainaki, snn karkiga muna ma anty zainab arifah ki rainata dariya wallah daurin gindi take dashi ko su baba basu iyawa da ita, saishi wanda take so din wato yaa ibaad..duk gidan nan shine kawai yake mata abunda yaga dama kuma still kiga tana binshi..but dont be scared of her. if not walalh zata ci miki mutunci ai kinga abunda taso ta miki yau. da sanyin murya ayaanah tace hakane, duk dama ni bansan haka take nufi dani ba amma nagode sosai sis.. feeling sober sultana ta dafata tace "i will leave u in good hands ga kulthum zamu na waya da phone inta you guys shud stick togethr har sai sartuday in nazo.


suna ciki wann maganar aka wani bangaje kofar da karfi

suna daga ido suka ga safiya da blue hijabi atsaye tahade ranta sosai kamr zatay kuka


haushi ya kama sultana tace ke kuma meye haka. 


da mugun rashin kunya ta harare sultanan tace toh ana kiranku wai inji hajiya waiku maza maza ku fito.


da sauri sultana ta miƙe ta cakomota cikin dakin kamr zasuyi dambe tace "toh mu sa oinki ne da bazaki mana sallama ki gaya mana aikan ahankalce ba saikizo kan mutane kina musu gatsale wallah kika kara murguda min baki saina fasa miki baki


batace komi ta fauce hannunta ta fita a dakin da gudu tana bambami


masifa sultana take tana cewa nifa rainin yarinyar nan ya fara isata ba kuma dan taga muna mata shiru ne shiyasa take kara hawa kai..but i wll show her dat i am not her mate

..mtwss. suna cikin fadin lefin safiya suka lura da yadda ayaanah tay shiru


kulthum ta dafata tace "what? kema safiyan tamiki wani abu ko? i saw the way she look at u sumtimes kamr wani zata dake ki


ayanah tace "aa, bata min komi ba. kawai ranarne naji ammin sultana nacewa wai ku aikun girme ni safiya itace age mate dina ka fa wata rana nay wani abu nima kuce ina raina ku..i dnt want us to fight kunga bansan kowa anan garin ba.


sunajin haka suka gane me take nufi da tausayi a idonsa suka dawo jikinta suka zauna dukansu kusa da ita sosai sigar lallashi


sultana tace" damu da safiya we all sisters ayaanah, nd yes akwai age gap tsakaninmu sosai, aiko kulthum na girme ta da watanni amma it doenst mean dat zamu taware  junanmu base on silly age gap issures saidai base on charcters, ke kanki kinga bhvrs din safiya, in ana right ita tana left, is like she just hate every body, asalin ta fitinanniya

ce...nd ure nothing like her dats why i choose u to be our forever friend, kituna kin rufa min asiri nd u took blames for me...nd u even agree to sleep here with us a dakin kulthum for her sake duk dama baki gama saninta ba..kinga ai bazaki hade halinki dana safiya ba...


abunka da yaranta dan hakan da suka gaggaya mata sai taji hanklinta ya kara kwanciya da su sosai. daga nan suka rungume juna nd they promise each other to be friends nd sisters forever.


suna gama maganan suka tattashi suka kimtsa kowacce tay kyau snn suka dauki kayan sultanan sukaje sukay sallama ma anty safeera har daki kafin nan suka sauko sashen ammi karama suka maida kayan duka a akwatin sultanan ammi karama ta rako su har waje tabawa sultana cookies da su dambun nama dayawa acikin take away roba.


bayan anyi sallama da kowa ammi babba ta nace saida bappa zaidu ya dauketa ita daya a motarsa suka wuce


kulthum ma bata wani tsaya sosai ba tunda maheer yace taje tay karatu sai ta koma ciki, ya rage daga ammi karama sai ayaanah da sultana da mujaheed


har mota suka sakata suna mata bye snn dukansu suka juya ciki mujaheed yaja ayaana suka koma dakin kulthum suka same ta harta fara karatun su kuma suka zauna agefe akan sofa still yanata mmkin yadda akay ta iya smooth turanci 


tambayoyi ya dinga mata da english tana bashi amsa har yazo ya gane cewa inganttcun malamai da coppers daga kudu ake yawan kai musu chan kuma dama basuda yawa amma dake tasaka bokon aranta shiyasa ma ta dage har ta iya turanci harma fiye da addanta inayah


daga harabar gidan kuwa maheer na zama agaban motar ibaad ya zago ya miƙa masa key yace masa suje gidan kawai shi sai gobe da safe zaizo kuma ya riga ya gayawa bappa zaidu har kuma ya amince..


jin hakan yasa saida maheer ya fito, suka tsaye agefe yafara matsa masa yagaya masa dalili duk ya dauka wani issures aka samu da ammi babba, dakyar snn ya sanar da shi cewa yana so ne yay magana da hajiya akan karatun ayaana nd he want it to be privtely shiyasa ma zai kwana.


da maheer har ya budi baki zai tambayesa why privately tunda sun saba komi atare sukeyi

saidai sanin cewa asali yay niyyar bazai gaya masan bane kawai yasa yay shiru, dan yasan da inda yana da niyyar fada masa plan dinsa akan ayaana da tuntuni sunyi mgn da shi an wuce wajen


,..gyada kansa yay yace masa babu komi sede daga ganin yadda ya bawa ibaad din amsar cikin attitude kasan  har ransa baiji dadin hakan ba, da wani abu aransa ya koma motar daga shi sai sultana suka wuce gida kai tsaye


Direct ibaad ya koma cikin gida bai tsaya a ko inaba sai cikin personal room dinsa dake sashen maman nasa yana zama yafara cike ciken forms da files yanabi yana saka hannu nd reading tru each rules nd schdule throuhly daga na bokon harna islamiyan.


yana gamawa ya ajesu akan desk dinsa snn ya rage kayan jikinsa  ya zauna yay karatu for like 3 good hrs both na club dana asalin schll wajajen 11.30p. na dare ya gama yashiga bayi yay wanka ya hado da alwala, yana dawowa dakin yazo ya samu mamansa har ta aje masa hot herbal tea aka desk dinsa, murmushi me sanyi yay kafin ya dauka yay bismilla ya zauna ya shanye kafin nan ya kimtsa kansa cikin pjamas me kyau ya kwanta kafin kace wani abu bacci ya daukesa.


tsabar doguwar hira da english da ayaanah sukayi da mujaheed yasa still anan dakin kulthum din ta kara bingerewa da bacci suka sha baccin su atare. 


washe gari da sasafe suka tashi sukayi ibaadansu har sukay karatun qur'ani saidai haryau irin wnn momnt na dago mata tashin hankali sosai musmn inta y wani abu data saba yinsa sa inaayah sai taji gabaki daya zafin mutuwar ya kara dawowa mata sabuwa


kusan abunda ya saka ta tsiri yin baccin safiya kenan duk dama dacan bata saba ba dake yau sunday dama rnr hutu ne babu wanda yazo ya leka dakinsu sai MJ shima sama sama ya lekesa da asban snn ya wuce room dinsa daga nan basu kara ganinsa ayaana tafara bacci sosai harda minshari


dagata bangaren maheer kuwa har saida suka idar da sallahn frh da babansa snn ya same sa da complain dinsa akan yadda ibaad yafara waresa akan magann rywar ayanah


bappa zaidu yay shiru yana jinsa har saida ya gama complain dinsa snn acikin lumana yafara warware masa abunda ake ciki...


yace masa ayaana ai ba marainiya bace, kuma bawai an basu ita kyauta bace. shiyasa komi acikin tsari zasu bishi dan kar wata rana asamu  bacin rana, snn tunda hajiya tace musu mahfiyarta acan tazabi ibaad din yay ma yarta jagora arayuwrta ai kamata yay su suzage  suna bashi goyon baya bawai duka ataru ana rarraba masa hanklinsa

kashi kashi ba, .he told him alot of things da bai sani akan case din ayaanah ba, musmn part din baqin halin babanta ayadda haj mairo ta gaggaya musu, har dai yazo ya fahimce shi sosai.



Sai wajajen 9am su ayaana suka farka a bacci as usual sukayi wankansu fess sunje gaishar da anty safeera ta kamasu adakinta ta musu kwalliya mai kyau harda shafa musu jan baki. ayaanah slwys feels awkwad da abun amma zuciyar yaro data ga anty safeera tana son mata kwalliya sai abun yafara shiga ranta kadan kadan duk dama bata saba dashi ba. wani irin gyara mata gashinta tay da gel ta mata donut me kyau tasa mata kwalli da lip gloss akan pink lipstick she looks very fine har ta musu hoto.


dama can sultana ke zuwa dauko musu kaya dake yau bata nan tun ahanyar dawowa daga dakin anty safeeran sukay sallama da kulthum akan zata koma wajen ammi karaman kawai 


kulthum ta rakota har kofa snn ta koma, sashen was soo quiet nd cold banda uban qamshin tureren wuta masu sanyaya zuciya bakajin komi


kai tsaye ta wuce dakin su da safiya, ta samu safiyar tana matse akan sofar dakin tanata karatun qur'ani kana kallonta kasan na dole akasata idonta ya cika da ruwa ita dayane a dakin amma ayaana ta lura jikinta na rawa rawa. kallon kallo sukama junansu batare da sunyi magana ba ayaana ta cire hijabin kulthum dake jikinta ta jawo akwatinta ta fara cire kayan sawa half gown da wandonsa me dan fadi ta saka already anty safeera ta tattale mata sumanta da pins da ribbons sai batasha wahalan yafa gyalen kayan akanta ba.


ganin yadda tay kyau sosai yasa safiya taja mata wata arniyar tsaki me kara itade batace mata uffan ba ta shafa turarenta sama sama yadda taga su sultana sukeyi ta kama hanya ta fita gaishe da ammi karama.


tana fita ko dakinta bata karasa ba ta sameta kitchen tana kan soya kayan miya zatay musu spagheti


Sallama tay da sanyin murya suna hade ido da ammi karama ta karaso ciki da wani irin sanyin ladabi tabita durkusa kasa kanta na kallon can can kasa tace"ina kwana ammi..ammi tay murmushi me sanyi tace "lafya.. ayaana kin tashi lafya? tace lafya kalau, uhm..akwai aikin da zan taya ki dashi ne? 


murmushi ammi ta karayi tace "tashi akasan nan tukuna,. mikewa tay tsaye snn ammi tace mata ga waje can kije ki zauna,, tana zama akan chair ammi ta kawo mata tea me masifar kauri ta bata tace mata tasha, duk irin kunyar ayaana da sauri ta karba sabid wani irin qamshin dadi da tea din yakeyi


tafara sha kenan ammi tace" ayaana, i knw u will be lonely sultana ta koma gida amma karki damu akwai safiya da kulthum. they are ur sisters. u can play with them suma yan uwanki ne,..snn zuwa anjima idan munyi breakfast zanxo dakin naku sai kema k shirya kayanki a wardrob dinki dake da safiya will be sharing the room, amma zanso ace kowa yana kulawa da kayansa

..banda kuma kazanta banda fada ku zauna lafya da juna kinji ko? acikin ladabi ayaanah tace naji in sha Allah zany duk abunda kikace din ammi na murmshi tace good girl gashi kin sha kyau safeera tana ji daku fa..karamin murmushi tay tun batace wani abu safiya ta karaso kitchen din haway faca faca a face dinta ta kalle ayanaah da tsawa


tace "keeee...wai kijje yanxun nan yaa ibaad yana kiranki a dakin sa tana fadin haka ta rushe da wani irin kuka bakinta harna fitar da jini..


sosai gaban ayaana ya fadi taji tsoro ya rike mata zuciya ....


ammi tama ayaanan ido akan tashi tatafi waajensa kawai ayaanah bata kuwa bata lkci ba ta mike tafita a kitchen din da wani irin fargaban ibaad din a zuciyarta sosai...


tana ficewa ammi ta kalle safiya tace ke kuma meya hadaki dashi again??.......zata yi magana ammi ta kara kai mata duka tace koma miyene maganin ki kenan bake kin zama shedaniya baki tashi kiy sallahn asubah ba?ai dagangan naki gaya miki cewa xai kwana agidan nan tunda ke bakijin maganan uban kowa, bakima tsoron Allah sai tsoron yayanki ko? toh aiko kasheki agidan nan zaiyi bazan kara hanashi ba..just see the way u're talking to this girl now, ure so mannerless...kina wani mata tsawa kina hantararta ke din uwartace..uban metake miki ehh?dada rushewa da kuka safiya tay cikin sheshska tace ammi dan Allah dan Allah kiy hakuri kibashi haquri wallah bazan kara kin tashi sallah ba...


idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[26/11, 19:24] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE.💫

arewabooks@surayyahms


⏯️3️⃣0️⃣



ammi taja tsaki tace Da Allah tafican sau nawa kina sani ina rokonsa cewa zaki canza hali haryau kin canza ne?toh wallah safiya ki shiga hankalinki, dan babu ruwana a case dinki da ibaad kuma wallah yau bazan karbeki awajensa ba..kawai ki fita kiban waje..


Da wani irin kuka ta juya tafita da sanyin jiki saidai tana kaiwa kofarsa ta hadiye kukan tay shiru ta tsaya cak tanata kkrin share hawayenta dan tasan inta shiga masa da kukan banza zai iya tattakata.


ata bangaren ayaana kuwa already a tsorace da ganin yanayin daya fasa bakin safiyan ta taho tunda tay sallama gabanta yake faduwa sosai.


kanta na kallon kasa ta shigo cikin niimtaccen dakin wanda ko kadan bazakay tsammanin wai safiya bane dan wani irin tattalashi da akayi da tsafta, koina is sparkling clean, raɓar Ac dana turaren wuta daya qama sashen ya gaurayu da tsadadden turarensa xerjoff naxos har wani bacci bacci rairaiyi raitayi taji atmosphern dakin yana neman sakata.


tunda suka hade ido ya amsa sallamarta ko sake kallonta baiyi ba, ita kuwa harta karaso kallonsa take yadda ya mugun tafiya da imanin ta id just past nine amma har ya cancanda kwalliya wata calm Burgundy short-sleeve shirt ne da Black jeans da classy black men Bracelet a hannunsa yana zaune akan kujera akame kmr dan sarki..


tamkar wacce bata mumfashi ta taho gabansa ta tsuguna

asanyaye tanamai hana kanta jin wann uban feeling din dake janta atacikin ranta duk dama batasan na meye bane amma sai take jin matsanancin tsoro kar ta shagala itama abunda ya faru anty zainab arifah ya faru da ita.


cikin tattaro makanta nitsuwa da wani irin sanyin murna tace "ina kwana??....bai amsa ba saida yaja minti biyu snn yace "you dont knw my name?kara fadi gaban ta yay tay shiru, muryan sa a dakile yace"ki sake memeta abunda kika ce wann karon karki kara gaisheni kamar wani masinjanki... tana budan baki taji muryanta na rawa rawa hawaye taji zasu xubo mata tay saurin shanyewa ahnkli tace uhmmm iina kwana" idonsa ya zaro  yace ina kwana what?i dont have a name in dis ur tiny little mouth wato dan nace miki kidena cemin me mota shine kike neman rainimin hankli ko?


da sauri ta girgiza kai tace "aa fah,...yace okay say my name'

hawayen datake dannewa ya zuba mata ta kara sunkuyar kai snn tace ina kwana... yaya..i..i...tay shiru,"saida ta runtse ido tace yaa ibaad"


..yaja tsaki a masife yace "Ohhh dama kinsan sunana kike zuwa gabama gatsau kice min ina kwana? kika kara cemin uhmmm, ko ina kwana zakiga abunda zan miki..


batace mishi komi ba ta cigaba da hawayenta har ya miƙe tsaye ya dauko duka papers din yazo ya zauna agaban ta tare da su


karamin shiru ne ya ratsa wajen har saida ya tabbata tagama share hawynta ta nitsu kai tsaye yace"...yau sunday gobe monday kishirya zanxo nakai ki interview a sabuwar school dinki


wani irin garas taji saukar maganan ji datay yazo mata a kunneta kamar doka da oder.


yacigaba da cewa a new schedules dinki akwai zuwa islamiya, da lessons 4 times a week the remaining 3 days zaki amfani dasu ki huta snn kiy revising me kika karanta..


yana kaiwa nan ya miƙa mata papers din da biron sa ya nuna mata inda zatay signing one after d other tana gamawa yayi kasa da idonsa suna kallon juna with more gentler but no nonsense voice yace.."ai ynzu kingane me nake gayamiki ko? 


tsabar rudewa duk dama ta ganen amma ta girgiza kai tace aa bangane ba yaaya..


..gyara zamansa yay yace dago ki kalleni,babu shiri ta dago idonta ta zuba anashi suna hade idon yace zan sakaki a makaranta domin ki cigaba da karatunki anan, mmnki ta rubuta sako aciki duk gayamin dede inda kika tsaya akaratu, baza a maidake baya ba anan zaki cigaba ne daga dede inda kika tsaya shiyasa ma zaa miki interview me tsauri gobe...,kobakici ba kuma dolene zakiy wani makarntar daban..dan haka kisani der no time for jokes arnd here dan nan bakamar can garinku bane,zaki hadu da kalubale dayawa but i dont care..you must produce the best result to ur ability inbadai dama karya malamnku nacan sukeyi suna biye dolancinki ba..if ure truly smart like they  said then prove it here, duk gidan nan babu dolo..so..u eida come first or nothing. doka ta na farko dake kenan tunda har naji cewa kike zakiy talla dan tsabar sakalci da rashin tunani wato yarke innan harkin manta da alkwarin da kika ma mamanki da addanki ko? toh in sha Allah kika sake kika kawomin batun talla ko wasa akarantunki ranar na lahira sai yafiki jin dadi agidan nan..ahnkli yake magn amma bakaramin rawa jikinta yakeyi ba hawaye na zubowa a idonta kamar ruwa ta rasa abunda yake mata dadi..


muryansa na fita ahankli yace "u can cry a u want amma bazaki saida wani abinci agarin nan ba snn kuma na riga da nagaya miki sauran dokokin tun acan gidan so once kika fara schl kowani rana nazo zan iya tambarki abunda kikay aji, inba baki gaya min gaskiya ba ina da lambar kowani malmnku zan kirasu awaya inji, no watching tvs or using any gadjet untill ur home work are complte. ur lesson is very compusory..nd at end of the week zaki gaya min me dame kika koya..pls do not test my patience. da sauri ta gyada masa kai


yace gobe idan mun fita zakiga drivernki, kuma ai kinsan fuskokin yan gidan nan duka ko? ahnkli tace ehh yace toh inba daya acikinmu bane yazo daukarki a schll karda ki sake kice musu kinsanshi koda kuwa yace miki nina aikosa koda ya ambace sunanki dana mamanki da babanki dont u eve follow him.


cikin sanyin jiki tace toh nagode yaa Allah ya saka da alheri, naji abunda kace zanyi karatun..


daga nan yay shiru baice mata komi ba can ya dan jingina bayansa da kujera ya zuba mata duka idanunsa yana jin wani irin rauni rauni da kasala musmmn yadda fuskarta dayaji ssnyar kwalliyar yay caba caba da ruwan hawaye harsuna ɗiga akan dan karamin cute lips dinta like a molten ice, cikin lumshe ido da budewa yace give me those papers...


miƙewa tay jikinta a mugun sanyaye ta fara isowa kurkussa dashi qamshin turarensa yana wani irin bugar da ita ga wani irin dan iskan kallon dayake mata dats piercing direct into her small heart, idonta na kallon kasa ta iso gabansa tana kuwa miƙa masa pprs din taji ya kamo harda hannunta izuwa anshi ya fixgota jikin shi lkcin ji take kamr zata saki fitsari sai taga yaciro hankynsa me kyau 

yakai karamin bakin ta ya goge lipstick da duk wani make up dake wajen ya rarrage mata powder wanda tsabar tsoro suna kallon juna amma ji take kamar zata shide yadda ya mannata a jikinshi a sosai 


muryn sa na fita ahnkli yace 

"ranar bana cemiki wnn abun fuskarkin baya miki kyau ba? in kuma neman maza zakiyi kigayamin saina maidake kauyenku kije kiyi aure acan, but not now..kibari se kin girma kinsan me kikeyi nd if u truly want to seduce me to marry you saikita sakawa..


wani kuka me tafe da kunya da batasan daga ina ya fito ba ta fashe masa dashi dan batay tsammnin zai furta mata haka cikin shagbabben kukan tace "yaa, ammin kulthum ne fa takemin ni bance inaso ba ai banma iya ba..yana kallon idonta yace "amma ai kinsan zaki iya kuma ai kina so toh kiyi hakuri bayanxu ba sabida bazai amfaneki da komi ba. this make up thing isnt even for children inde baneman maza kike ba toh duk sanda tace zata miki kice mata kinfison fuskarki ahaka..


da sauri ta gyada masa kai da hankyn still ya goge mata hawayenta tass tana kkrin sauka ajikin shin caraf safiya ta bude musu kofar har saida ta shigo snn ta mannu a bango da rawan murya tace salam alaikum warahmatullah 


Da sauri yabi ya daga ayaanah ajikinsa yanamai doka ma safiyar harara zatay magana kenan yanuna mata hanyar wajen a mugun tsawace yace" sheigiya..fita..ure banned frm entring dis room...kije kijirani awaje naga alaman baki daku bane..


tana fita ya kalle ayaanan yace "ke kuma ga duka kayan schl dinki acan ki kitattara su kije can kinunawa ammi zata nuna miki yadda ake amfani dasu

..nd dont forget if u need anything kigyamin ko ki gaya ma ammi zata gayamin kinji ko..


cikin ladabi ayaana ta amsashi da toh yaya.. kyaleta yay anan ya fice ya samu safiya akofa

batasan me yace ma safiyar ba, tana fitowa da kayan kofa taga safiya ta hau karba tana tayata kwashewa suna kaiwa tare wa ammi karama


suna kaiwa duka kayan ammi tace su bari sai anyi breakfst an dawo tukuna zasu bude su gaggani. har kuwa akaje aka ci abincin safe a sashen hajiya mairo ayana bata nuna wa kowa alaman tay kuka ba banda make up da ya zama babu a fuskan ta yanzu. 


immidietly ana gama breakfst din ibaad ya fice agidan abunsa..


tun bayan fitarsa su ammi suka tattaro kayan karatun ayaana sukaxo falon hajiya dashi daga ita sai safiya da ayaanahn aka fara bude kayan daya bayan daya wanda tun daga kan uniform suka gane a schl dinsu sultana akasa ayaanah.


hajy ta gama bambaminya tay shiru tana mitar waimesa ba asaka ta tare da safiya anan kawai ba, dakyar ammi ta ganar da ita ai nasu safiya da kulthum ba ahade yake da courses din islamiya ba shiyasa..kominta na yar gayu yar gata masha Allah, sosai safiya ta kasa boye kishinta ta dinga bori ma hajya wai itama saidai asaya mata irin jaka da takalmin ayaana kuma ai bata da stationriees na zamani da yawa haka..tun abun be dara ayaanah but dataga borin da safiya tay tasan cewa lallai bakarmin kashe mata kudi akayi ba...


wani irin dadi taji aranta na hudata asihirince haka su ammi suka sakata ta gwada komi ajikinta, masha Allah sun masa chass chass sai can da yamma bayan ammi tay mata arranging kayanta a wadrobe kafin kulthum tazo ayaanah ta nunna mata sabhin abubuwan schl inta duk dama bataso da akce ayaana batare da su zatay schl ba.


dake tun da ibaad ya fice da safe bai dawo gidan ba hanklin kowa akwance yay bacci akan kayan schll din nan har yanxu safiya taki ta mata magana


early morning 5;30 on d dot suna tsaka da bacci sukaji an buga musu kofa jin muryan ibaad yasaka safiya tay wani irin firgitaccen tashi..


tana jin muryansa ta kalle ayaanah datake kkrin farkwa da kyar, da karfi ta zage ta maka mata mari ayaanah tana mikewa zaune tace "Allah ya isa min munafuka kawai aida bakizo gidan nan ba da yaa ibaad bazaina zuwa yana takura ma rayuwa na wallah sai kin bar gidan nan..


Hanklin ayaana sai ya kara tashi dataga yadda safiya take kukan tun daga kasar zuciyarta harta sauka akan gadon cikin toshe muryan kukan da karfi tace yaa fa mun tashi..tanaji yaja tsaki yace start geting ready for school


 ...hawaye na zuba a idonta tace tohh ...yana barin wajen ta kalli ayaanah ta kara fashewa da kuka tace Allah ya isa..ni wallh sai kin barmin dakina..ai nan ba gidan ubanki bane zaki jawoshi yazo yay ta takura ma mutum shiken bazan yi bacci ba


itade ayaanah batace mata komi ba, tana zaune akan gadon har safiya ta gama wanka ta fito tafara salla,itama sai ta tashi tashiga tay wanka taga babu sabulu sabida gabaki daya safiya ta kwashe abubuwanta ta boyesu tsabar baqin hali, tana gama watsa ruwan ta doro har da alwala 


zaman kurmaye sukayi a dakin kowa na abunda ke gabansa can ayaana ta bude wani waje ta hau tattaro nata sabulan da su man da ibaad ya tsiya mata safiya nata kallonta har takai wajen wanka ta ajesu agefe ta jerasu


confidence din yarinyar da saurin gane abu har  mamaki yke bata har cikin aranta tasan dai duk tsiya bazata jima tana mata isknci ba duk alama yanuna mata cewa yarinyar nan zata waye ta kuma bude ido da wuri badajimawa



jim kadan suka gama duk wani shiryawan da zasuyi zuwan kulthum dakin dan ta dubata yasa ayaanah taji hanklinta ya dan kwanta dan wani irin tunanin addanta take yi aranta haryanxu, she cant belive it cewa zata koma karatu kuma a binni amma babu  addanta inayah atare da ita,.she deeply hides her tears in her heart sabida batason tafara kuka akan haka ibaad yaji haushi ya mata fada agaban mutane, kusan tare suka fito wajen cin breafst da kulthum kowa yay kyau acikin unform dinsa na su ayaanah cambridge grey ne da fari nasu sultana kuma turquoise da fari, hanklinta duk atashe yake har aka gama gaisuwa aka ci breakfs kowa yana ma ayaana murna da nasiha wanda duk bama jin me suke cewa tay ba, her heart was busy drenching with grieve yawan surutun hajy mairo tare da kara sako mata zancen ummanta da ayaanah saiya zamana rauni ya riketa ataciki sosai. 


har anty safeera da su mujaheed suka gama mata hotonan first day at schll da wayoyin su basu gane kanta ba, they all tot dat shirmen yara ne najin tsoron first day at schll dinsu kusan babu kalar rarrashin ta da mujaheed baiyi ba amma batace masa komi ba sai gyada kai har ya gaji da surutun yay shiru


uncle moh ne bai wani ji dadin abun aransa ba sai bai nuna ma kowa ba har saida ibaad ya taso yaran agaba kowa ya wuce makaranta 


shidakansa ya dauke ayaanah, driver kuma ya aje su kulthum da safiya. bayan wucewr su bada jimawa ba uncle moh ya taho kamar xai same hajia da maganan sai kuma yay wani tunani ya fasa, in his imagine slight yaso ace asa ayaanah a schl din da matarsa safeera ta tay dacan, which is one of the loudest british schools a kano wanda yaran yan karya ne aciki sai kuma ya tuna cewa in yay hakan baida wani kwakkwaran dalili da zai gaya ma hajy mairo na saka ayaanah a schl din dayafi na sauran yaran gidan tsada sosai tunda kowa yasan duk salon koyarwn dayane wancan din dai suna yake dashi sosai har kasar waje...one of the few reason dayaji yana son safeera kenn sabida duk wani abu datay a rayuwarta na gani na fada ne na krya na nuna arziki, safera first class slay queen ce he is proud dat she attended the best schlls, travel abroads dai duk rayuwar karyan nan tay su datake karama nd he sumhow want to push ayaana to the same fate sabida tay matching level dinsa sai yaga kamr hakan kuma bazaiyu ba 


share batun yay ya wuce wajen aikinsa kafin kace wani abu gidan ya dauka da shiru


dataga fannin su ayana kuwa suna isa gate din schll din taga ibaad ya tsaya daga gefe basu shiga ba yay parking a bakin hanya wayarsa yana kara sauka ya barta aciki yaje ya same wani mutum suna magana dacan har ta dauke kanta sai kuma taga kamar tagane mutumin sosai...


kara saka idonta tay ta madubin motar taga ashe malamin science dinsu nacan anguwar tudu, duk sai taji mamaki ya cikata tanata tunanin a ina ibaad yasanshi


batace uffan ba har ibaad din ya sallamesa ya dawo motar da wani farar takarda snn ya  karasa da su cikin makaranta da bata taɓa ganin irinsa a fadi da girma da kyau ba dan ko da suka sauka ji tay kamar wani duniya nadaban take tsaya..


gaba yay da jaka abayansa tana bibiyarsa abaya baya har suka shiga wani katon building dake gidan sama ne security ne yamusu jagora inda ake interview duk taji ta rude dataga har da turawa kowa yana latsa computersa kuma duk turanci akeyi awajen babu hausa


wajen zama aka bata ta zauna ibaad kuma ya shige cikin wani office 10 mins later wata mata sanye da dark blue uniform tazo da murmushi da harshen turanci tace ma ayaanah tabiyota suje ciki .. ayaanah taki motsi ta zuba mata ido, matar tana murmushi ta mika mata hannu tace "haba yan mata muje ciki..karkiji tsoro ure safe here. da sanijn murya ta girgixa kai ssn tace yayana yace min karna biki ko ina ai bansanki ba.."Dariya matar tay tace" very good girl hmm ure security cautious.. to shkna  badmuwa bari naje na kirashi" 


ayaanah ta gyada kai, sai can data gansa tare da matar snn ta jawo jakarta tazo ta samesu suka karasa cikin office din atare..


tunda tazauna kusa da ibaad yabon wayon ta kawai mai interview din yakeyi sosai


..already bappa zaidu ya nema musu alfarma againts the normal school protocals dan basu daukar dalibi haka kawai musm ma daga kaskantaccen mkrnt na kauyr suyi admiting dinsa kuma a ajin daya baro. dakyar da ɓarin kudinsu snn suka samu duk wata alfarma wa ayaanah dan kar a maidata can can baya 


 Dan haka ne ma yasa ibaad yay going thru nooks nd cranies har saida yay tracing ya same number malamin science din su na tudu yabiya kudi aka bashi previous duk wani info da result transcripts da recomendations na duka perfomances inta na karatu abaya.


mai inteview yana ta mamki yadda taga komi na boko tanaci sosai babu faduwa islamiyan ne take baya bata yi nisa sosai ba kuma bata kkri akansa kamr na bokon


da can exams zai mata sai ya fasa, da turanci ya mata few question akan english, elmntary science,mathematic, civic education, da few other topics yaga ta amsasu sosai with her clean village girl english babu wani slang ajiki yadda ake koya musu haka takeyinshi corectly nd smoothly kuma confidntly


basu yi 20 minutes ba ya gamsu da potential inta sosai, yace za'a saka ta ne on trial admission idan akaga ta miƙe tay kkri wann sesssion din

kawai za'a kyaleta ne ta cigaba. islamiya ne aka mata repeating aji daya aka buga musu acceptance letter da rules da schll ajiki dayan matar ta karanta ma ayaana komi ta mata bayaninsu sosai snn aka sata tay signing. she was a bit okay face saida taga ibaad ya fara musu sallama zai tafi tafara jin hanklinta ya tashi


shiru tay har aka gama komi suka bar wajen interview suka sauko ya damkata ahannun caretaker dinsun wacce itace zata kai ayaana class.


yana juyawa kuwa ayaanah tafashe da kuka sosai matar ta kasa gane mata tun ibaad baikai ga tada motarsa ba tay gudu har tana haki takirawosa.


kirjinsa na buga ya biyota duk ya dauka wani abu ne, zuwa yay yasamu ayaanah ta zauna akasa tanata kuka dan guntun masifar daya taso masan ya danne acki ya karaso gabanta yace "me aka miki kike kuka?? 

shiru tay ya saka hannun ya fizgota tsaye yajata gefe yace

"Bakison makrntar ne?asanyaye ta girgiza kai a masife yace "then what? da muryan kuka tace "nifa tsoro nakeji, ai kace zanga sultana anan kuma banganta ba.


cikin lunshe ido da budewa yace dama dan ita kikazo karatun? tace aa..yace "ke bani son sakalci. waye kikaga yana kuka anan dan ankawo sa makaranta.. wato kin saka talla aranki ko? da shagon hajy nakaiki yanxu zakiy kuka ne?hawayen na zuba tace a'a kawai nifa tsoro nakeji..cikin harara yace "kinzo a tsakiyar term, kuma kinji sunce miki ure on trial admission..ayaanah idan baki dage wann karon ba zasu maidake ajin baya kuma shine zakice min kinajin tsoro..did u want me to slap you? a sanyaye tace "no, da muryan kukan daya kara zuwa mata bazata tace..toh dan Allah kayahakuri mana yaaya ai gani nay zaka tafi kabarni


..ajyn zucy ya sauke cikin sasauto da muryansa ya kara riko hannunta cikin nashi suna kallon juna cikin salon yaudara da lallami ya fara tuna mata wahalar da ummanta zatasha in bata nitsu tay karatu ba, kuma yace mata ta tana tuna addanta, she shud read to make them proud. haka ya dinga lallabata har saida yaga ta nitsu sosai snn ya rakasu ita da care takern har bakin ajin ta shiga ta zauna akan seat dinta

snn ya juya ya wuce schll da sauri dan bakaramin latti ta sashi yayi yau ba.


half of the time a schl din she was just thinking about his words in her head taga dai bata da wani mafita na jin rauni kasancewarta ita daya anan binni dolene tay karatun sosai.


gashi yan ajin sai kallonta kowa yakeyi dan seat dinta ita daya aka bata batada seat mate duk da yawan kallo sai batace ma kowa komi ba dan abune data saba dashi tun tuna kauye ake mata irin wnn kallon


kwata kwata schll din bai mata dadi ba har saida aka tashi break suka hadu da sultana dadi kamar zai kashe ta she was soo happy dataji wai schl dinsu daya da ayaanah, altho she is one class ahead of her tunda aka fito a break taje ta nuna mata wajaje acikin schl din har kamar karsu rabu



ata fannin ibaad kuwa har saida ya fito sallhn azhr kafin suka hadu da maheer acikin masallci maher bai kuwa boye masa fushinsa ba ya kuma gaya masa abunda bappa zaidu ya gaggaya masa.. ibaad baice masa komi ba face har sanda suka kama hanyar zuwa dauko su sultanan a schl snn yake sanar dashi labarin duk abunda ya faru dashi a tudu da duk wani abunda ya samu ayaanah,...


wa shi kawai ya gaya wa abunda ke cikin takardan wasikan tawuure, hannun maheer haka ya dinga rawa akan steering dan bai tabaji irin wann abun arayuwarsa ba..


jiki a sanyaye ibaad yace kafin ayaana taga mahaifyrta zai dau lokaci sosai dan acikin wasikar taawure ta gaya masa cewa matsafan majiya sun mata mummunn jefar daya fi karfin tsarin dayake jikinta, wanda ba ciwo ya sakamata ba amma duk inda taje zata zauna dan ataimaketa baqaqn aljanu zasu kona wajen da wuta kurmus


tace masa gidan kawun ta dataje a jigawa kwana uku kawai tay gobara ya kama gidan ya cinye musu gidansu kurmus, da suka gane ajikinta ne sihirin shine suke koreta. ynxu haka ta shiga wani duniya na neman maganin wn sihiri har saita samu taimako snn zata dawo wa yarta ayaanah

ynxu haka bazata iya muamala dakowa ba face har sai aljanun wutan nan sun dena bibiyarta inba haka ba duk wanda ya taimketa wuta zai masa asarar dukiyarsa ko rai, yan daidaikon abubuwa ne acikin wasiqar bai gaya ma maheer ba sabida ya shafi privacy tsakaninsu

..

gabaki daya jikinsu duka yay sanyi jikin maheer din na rawa banda salati babu abunda yake furtawa


sai yanxu yagane cewa babu shakka safetyn ayaana ya danganta ne da zama datakey a karkashin kulawan ibaad dan in har zasu iya ma taawure da tsafi zai ita yuwa suna lura da rayuwar ayaanah.


altho taawure ta gaya masa nan da shekara zasu iya dauke idonsu akansa inhar bai batar da ayaanah to bazasu sake nemansa ba..


hakuri maheer ya dinga bashi da judging dinsa da yayi har suka isa schl din hanklinsu duka tashe jikin maheer kuma bai bar rawa rawa ba.


dayaga ayaanah sai ya dada jin tausayinta ya mugun kamashi dakyar ya iya shanye hawayen sa suka kai su gida sharply sultana aka fara saukewa, snn suka kai ayaana gida ta samu ma har su kulthum sun rigata dawowa ranar hirar schl suka dingayi a dakin hajiya ayayinda ita kuma ta fara batun hidimar komawa shagonta da zasuy wnan asabar din


tsakanin ayaana da sultana monday friday ne kawai basu islamiya 1, 12. haka suke tashi a normal schl hours, but tues wed thur duk sai karfe 3 ake tashin su su dawo gida suyi lesson  4:30 to 5.30pm agida amma malaminsu daban daban.


farko da bata saba da kowa bakaramin hawaye ta dingayi yi ba,duk tabi ta dagawa mai kulawa da ajinsu hankli,yara yan uwanta sai kallon shirmen ta sukeyi.


Aranar harsanda aka kaita gaban shugaban makaranta

,dake mace ce harta dauka ko ayaanahn batada lpyane take yawan kuka, amma daga tace zata kira ibaad saitaga tayi shiru ta nitsu..


Tunda shugaban makranta ta fahimce hakan, ana zuwa da case din cewa ayaanah tana kukan banza da wurwuri zatazo da waya tace zata kira ibaaaf shikenan kuma anyi maganinta Ahaka haka harta zo  ta sake jiki tayi abokai a ajin ta saba da karatunta ta mance da batun kuka kullum a break suna tare da sultana kamar yan uwan jini haka suka shaku da juna




After 2 months.


Fara zuwan makarantar ayaanah sosai yafara sauya mata hali tadawo bata ma da kwakkwaran lokacin hira da su kulthum agidan dake ibaad was on her neck duk da baida lokacin kansa amma haka yake takurawa don yaga ayaanah ta nitsu tay karatu, acikin wata biyun nan kusan kullum saiya xo gidan ya zakwalota ta masa bitan karatun da tayi a makarnta

...both islamiya da boko, gashi tana bala'in jin tsoronsa bata iya yin garaje musmmn ganin yadda yake casa safiya da bulala kamar jaka.


...within no time halayyar ayaanah gabaki daya suka soma sauyawa suka dawo masu kyau gwanin ban sha'awa, duk son ta da su mujaheed da anty safera haka taja baya dasu, bata sakewa amata kwalliya inba ranar asabar da kowa yake nan ba.. basirarta da ilminta da tarbiya da nitsuwarta kuwa sosai suke dada fallasuwa tareda karfin jajircewan ammi karama akan tarbiyanta sosai


yanzu haka inkaje gidan zaka dauka ayaanah ce asalin yar cikin ammi karama, tana mata biyayya sosai bata da kwuiwa koda ammi tahanata aiki zaka ga tazo ta nace sai ta tayata ahaka ahaka har take ganin yadda ammin take abinci abin yana bata sha'awa sosai saidai bata da lkcin koya sosai..


GOBE SASSAFE ZAN TURO WANI PAGE INNAGA COMENT

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[27/11, 10:38] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabook#surayyahms



⏯️3️⃣1️⃣

rayuwa na tafiya ne daban daban akowani bangare mafi akasari kusan kowa yana yin abubuwan dake gabansa ne wasu abubuwan ma ba a sanin faruwarsu sabida hajiy mairo da workers dinta duka yanxu ne suke ta kkrin suga sbwr wajen sana'arsu ya tsaya, sai tay sati bata dawo cikin family house ba musmn ranakun da take jimawa ashago toh a  gidan bappan zaidu kawai take kwana wekdns sai ta dawo gida,wanda sanadiyar haka ya saka ammi babba samun kwanciyar hankli da sauki wnn kishin jigilar da bappa zaidu yakeyi a family house kwana nan yaragu mata sosai, ynxu kusan 50-50 akey, inba hajya mairo tana can ba sam ammi babba bata barin shi yana zuwa inda fatima take haka kawai batare da sunje tare ba dan haryanxu tanakan zargin fatima tana kan aikata wani abu ta hanyar bawa mijinta abinci dan ta kwace matashi.



daga bangaren zainab Arifa kuwa wannan tunanin yarantar dake yawan damunta na tunanin cewa mahaifinta zaisaka ibaad yajuyo ya fara asalin sonta cikin ikon da babanta yake dashi ahnkli komi yafara gushewa..


zatazo weknds din amma banda kwasar raini da iskancin su sultanah babu abunda take sha,kusan hardly ibaad yake samun lkcinta a wknds din ma musmn ma ayaana ta fara karatu, all the time tazo zata samu in one way or the oda lamarin ayaanah ne kawai ke gabansa, tun bata noticing cewa yana bawa ayaanah attention fiye da kowa har tafara ganewa sosai,wata rana in taga yana ma ayana tsauri akan karatu ko hira acikin mutane sai taji dadi ta dauka kmr yadda yake ma sauran itama hakanne.. but as time goes on, taga kmr komi yana canzawa ahnkli, sam sam ibaad baison ataba ayaanah,, but she neva tells, ko labari zata bayar tafi dauko wajen da babu dadi just to convince herself dagata fara bawa kawayenta labari yadda yake ma ayaanah tsauri wajen karatu dan su kara kwantar mata da hankli, sai kuma kawarta rukky tafara mocking inta tana cewa ai wann kulawa ne na musamman bawai tsanar ayaanah yayi ba. 


tunda rukky tafara mata wann gorin abun ya dinga damunta, dake tana da ilimi duk yadda taso ta karyata abun acikin zuciyarta within few weeks datake zuwa gidan kowani wkkend tana lura dashi sai taga kamar batun rukayyan gaskiya ne kmr ibaad is over protective nd sensitive akan duk wani abu daya shafi ayaanah haka kawai sai taji hushin yarinyar datakeji aranta ya fara dawowa tsana me tsanani.


last weeknds datazo abun ya fara nunawa a fuskarta sosai...tafara kushe halin ayaana awajen mujaheed tana ce masa yarinyar bata da kunya bata nitsuwa kuma ana barinta tana aikata abunda taga dama ibaad baiya mata komi.


Duk yadda mujaheed yaso ya kare halayyar ayaana kuwa saita kusheta, ta dawo tana iya magana da kowa ayaran gidan amma koda ayana ta gaisheta bata amsawa, ita kuwa ayaana dataga hakan su kulthum suka kara zugata ta dena gaishetan me gabaki daya, this week datazo weknd da haushin hakan takoma gida, monday tana zuwa schl takasa gane komi kawayenta suka ce mata ai yanxu ne daidai takai kararta wajensu hajiya ko ta hada mata wani mugun sharin da zai ɓatata awajen ibaad snn ta nuna ma yarinyar matsayinta awajensa. abudai sukayi a shirme da yaranta tanata Allah Allah asabar ya sake zagowa.


ata fannin uncle moh kuwa

duk dama yasaka ayaana a list dinsa na future wife amma babu abunda yake sakashi duba lamarinta face sai yaga wani abu dabazaizo dede da ra'ayinsa ba yake saka baki,


sai aukin janta ajiki da abun duniya idan sunzo su da kulthum gaishe sa tare da anty safeera, haka zai bata kudin wankan kowani juma'a da su kayan kwadayi kowa ya dauka tausayi ne da sassauci irinna manya

 

saidai haka kawai bai taɓa suggesting wani abu babba na kawo cigaba a rayuwarta ba,saidai ya zuba ido, idan bappa zaidu ko ibaad sunyi yaga abun bai masa saikaji yafara korafe korafe yafara burgan zai kara kudi ayi har abunda baima yaran cikinsa ba saikaji yana mgn ama ayaanah  


yana balain jin haushin da ibaad yake da cikakken iko akanta, wanda ko anje gaban hajy mairo sai yaga tabi bayan ibaad din. gabaki dayansu basu gano uncle mohd ba duk sundauka kawai kowa yana iya bakin kkrinsa sbida rike amana da biyayya ga hajya mairo basusan uncle moh kkrinsa makansa kawai yakeyi ba.


dakyar da wahala ya dena wasu abubuwan, yaji haushi ya fita a sha'anin rayuwar ayaana yafara saka karfi da karfe wajen neman kudadensa sabida manya manyan construction contract din hanyoyi da gidaje yake yawan samu na qwmanti bakaramin millions yake dauka ba...



Daga haka ayaana ta fara samun sauki daga fitinarshi saboda batajin dadin yadda yake ware yan uwanta harda yar cikinsa wajen mata kyauta, ita kuma yayta bata kyautan kudi da kayan kwamulashe wanda har yau bata sake ibaad yasan da haka ba sabida tanajin tsoronsa masifarsa sosai.


washe gari asabar wanda monday me xuwa su ayaana zasu fara exams akwai tulin pressure akanta na son taga taci exams dinann gashi ita atsakiyar session din dama ta datsa kuma she need to pass bfr she fully gain her seat in her class,iyaka farin jininta a schl yasaka ta samu masu sanar da ita abunda aka musu abaya intazo gida sai tay ta koya da taimakon lesson teachernta mr samuel sede wasu abubuwn duk da lesson teacher yana mata amma dake a kuraren lokcine kuma akwai anxiety na fear of failure sai bata ganewa sosai


daren jumaa dakyar tay bacci huge space ne tsakaninta da safiya dan haryau kamar wuta da auduga suke zama wani baya taba kayan wani kullum safya ta kalle fuskar ayaana sai taji duk duniya babu wacce ta tsana kmr ita dan gani take sanadiyar ayaana ne yaa ibaad yake yawan zuwa gidan

yake casata


babu abunda yafi kona mata rai kamar rabonta da kallon series ynxu takai wata guda kenan sai dai tay aboye sai ta dawo batama gane komi, dum lefin rugujewar jin dadin rayuwarta agidan ta dorasa akan ayaanah, duk takuri da masifar yaa ibaad kuma bata taba ganin ya taɓa jikin ayaanan ba, sai tana ganin kmr fifita ayaanan shima yakey akanta kmr amminsu shiyasa ko kadan bata kaunar ayaana ita kuma ayaanah ko ajikinta sabida kulthum tana yawan dauke mata kewa in basu komi


sassafe ranar sartuday din kowa ya hallara a family house, saidai wnn wknd din was very boring nd quiet hatta

mujaheed yana kkrin yin exam ne kowa kansa yay zafi dake gidan duk guraye ne kowa na takansa anata karatu a dfrnt spot manyan ne kawai suke ciki sashen hjy mairo


hidiman shago was very overwhelming musmn ma da yanxu aka fara tadashi, ammi karama ma tuni ta koma bakin aikinsu na foundation kowa dai kansa yay zafi.


as usual kusan bayan asr wann karon zainab Arifa taxo amma bata tashi zuwa ita daya ba sai tazo da kawarta nala dan tafijin dadin harka da nala dake kusan ita tafi bata shawarar masu tsauri ita kuma rukky wata rana takan gaya mata gaskiya koda bata son shi musmn akan ibaad shiyasa sam bata fiyeson yawo da rukkyn ba.



sunsha kwalliyarsu na kece raini sunyi kyau kamar ba yaran scndry ba, suna zuwa kuwa cikin cin sa'a suka same su safiya a waje tana wanke fuskrta a famfon waje babu yabo babu fallasa ta gaishe su suka amsata da sakin fuska kamr basu ba, kai tsaye suka tambayeta ina ibaad tace musu ai yana falon amminsu shida yaya mujaheed yana koya masa wani abu tace mata toh shikenan, yau ko sashen hajy basu leke ba sabida dressing inasu kawai suka wuce ashen anty safeera


falon babu kowa face book din safiya da alama ita dayane anan zainab arifah ta kalleta tace safiya pls kije kiramana yarinyar kauyen nan ta kawo mana ruwan sha ynxun nan


itakanta safiya ta sha mamaki da request din amma dake abu ne dazai walaknta ayaana sai ta amsa da toh ta haura sama da sauri taje daki ta samesu dukansu akan gadon kulthum kowa da book dinsa agabansa dakin yayi wani irin shiru sunata karatu..


motsinta kawai sukaji abayansu sukajiyo suna hade ido ta bata rai tace ayaanah wai inji anty zainab arifah ki sauko ki kawo mata ruwan sha taxo da bakuwa..


da dumbin mamaki kulthum tace what? wata ayaanan


 ..sultana tace bar fitinniya wallh zaki samu karyatake ita aika taxo tace ayaana


safiya tace shikenan kiyi tazama Allah yasa taje ta gaya ma yaa ibaad ankiraki kinki xuwaz hala munafurcin dakike min ne yaukema zakiji irinsa ajikinki Allah yasa ya miki shegen duka aikinsan budurwansa ko??


ayaana tay kamr zata sauka taje ta gani ma idonta sai kulthum ta rigata sauka da sauri taje ta leke tagansu zahiri tanaji safiya tana ce musu anty zainab arifah nagaya mata amma zagina tay tace min munafuka wai kuma ace miki bazata kawo ruwan ba baki da hannu ne ko bakida kafa...


da sauri kulthum ta dawo tace 'guys ashe dagaske ne...gashi sultana taje tanata gunduma miki wani mugun sharri wai kin zageta kince bazakizo ba..


sultana tace to sai me? dama ayaana ta saba debar mata ruwan sha ne? ai akwai masu aiki agidan nan,..ita safiyar mesa bataje ta debo musu ba

abeg ayaanah stay here koma miyene kin fada din..itade ayaanah batace komi ba.


daga falon kuwa safiya tasha mamaki dataga zainab arifah bata dau zafi ba, cemata tay kawai taje kasa ta kira yayanta ibaad tace masa he is needed urgently here karta dake ayaanahnsa yaji haushi


safiya tana fita suka haura sama ita da nala sukayi kane kane abakin kofar kulthum


ayaana ta mike tsaye batace musu komi ba su kulthum ma basuce musu uffan ba kawai nala tana shigowa ta fixgo ayaana tana cewa kece ayaanah ko? waye sa'anki acikinmu da har xamu aike ki kice mana bazaki xo ba


nan zainab arifah ta cabe magana tafara zaginta da turanci 'are u stupid?mani xaki na gayawa wann maganan dan nace ki kawo mana ruwa akan ban isa na aike ki bane komi

 ..baku san matsayina agidan na ba ko? toh ko wanda yake daure miki gindin a karkashina yake, inadan ibaad ne yasa kike ganin kamar kinfi karfin kowa..by the time kikasan matsayina awajensa u will know ure nothing kiwuce kije kideba mana ruwa...nala ta zugereta tanan, arifah ta tureta tacan..


ran ayaana ya baci sabida jan jan hannun ta da sukey da karfi ta fauce hannunta tace niki sakeni bazan je ba.


tace fada dani zakayi did u knw who i am..? u dont knw who i am i bet..toh kije ki tambaya ibaad din zai gaya miki i am his future wife 

nd u ure just a village girl dayake taimakawa agidan nan


ayaana tafara kuka idonta a rufe tace Eh din yataimekeni wnn ba karya bane kekuma ai kowa yasan matsayinki

bakice kikace kinason shi ya tsumage ki? ni ai bansan wani matsayinki wajensa face haka ba..


da tsawa zainab Arifah tace kikace mene?


da bacin rai kulthum tace anty zainab stop shouting at her wai meta miki ne zakixo kina zaginta kina ture ta???


nala takai ma kulthum mari atsawace tace you...just shut up. ana magana kina saka magana kiga min yaran nan fa


sultana tasa ihu tace wallah kufita mana a daki inba haka sainaje na gaya ma hajiya uban waye ne bawanku da xa'aje adebo miki ruwa baza a debo din ba ai gaskiya ne yaya ibaad bayasonki, bamusan matsayinki ba sabida baki dashi..nd we dont care... toh wai ma ina ruwanki da ayaana kuma meta miki?


xuwa nala tay xata mari sultanan ita da kulthum din duka suka wani irin tureta akasa sai datay rolling suka tumu akanta suka fara kai mata duka..


ayaana ta razana sosai

tasa kuka me kara cikin firgice zata fita taje ta kira su ammi wani caraf zainab arifa ta riketa abkin kofa ta shakureta ayaanah tafara ihu tana cewa "kisakeni"..wani muryan makirci zainab arifahn tasaka tafarace mata ki memeta abunda kika gaya min...inke kin isa marar kunya...


tunda safiya takai sakon kan ibaad ya daure, yanata mamki meye kuma zai hada zainab arifah da ayana da zatace zata bugeta, da har kamar zai share tasharsu yaqi zuwa dakyar mujaheed dayasan zainab arifah bata kaunar ayanaah yay convincing dinsa suka taho sashen wani irin ihu da tirka tirkan fada da sukaji ya cika sashen yasaka safiya zamewa da gudu taje kiran su hajy mairo


da sauri suka haura sama zuciyar ibaad kamr zai fashe dayaga irin matsar da zainab arifah tama wuyan ayaana kamr wacce xata kasheta mujaheed yay sauri ya raba su ya ficcike zainab din ayana tafadi kasa tanata kuka


saiwani fixga xainab arifah take tana ɓarin karya tana cewa "wallh saikin memeta abunda kika gayamin" .mujahd yana riketa tana turashi tana cewa mujaheed let me go..inta cika marar kunya ta memeta abunda tagayamin can you imagine? har rainin yaran nan yakai su gaya min haka kawai ta fashe dawani irin makritccn kuka


ibaad tunda yaga haka yagane koma miye ne karya takeyi


he remain calm yaki sam yay ma kowa tsawa, dakin ya shiga direct ya samu su sultana har sun yaga ma nala riga cikin daka musu wani irin mugun kallo yace musu maza su fito waje..dakyar suka bambaro ajikinta kowa na hawaye suka fito daya bayan daya...jiki a sanyaye ayaana ta mike itama ta bisu suka sauka 


kowa jikinshi a turmushi zainab arifah sai wani irin kukan makirci takeyi mujahedd yana riketa tana sake jiki ita da shi da kawartan da jikin ta duk yay tsami suka sauko kasa tare..


suna saukowa falon duka ibaad ya saka su ayana dukansu uku kneeling atsakiya..dede shigowar su hajiya kenan da ita da ammi babba da anty safeera


meye ke faruwa anan?

sultana? kulthum..kee ayana..me kukayi haka mezan gani


anty safeera tay sauri taxo jikin zainab arifah dake kan rabza kuka kamr ita aka taro aka daka


ammi babba already harta yanke hukuncin hakan ne ma

suka yanyane zainab arifah


anty safeera tace arifah what happen? meya hadaku fa yaran nan kike kuka haka.


da wani irin kukan makirci ta nuna ayaana tace anty safee kawai yarinyar nan nagani a falo tana kwance bata komi nace ta kawomin ruwan sha fa nida nala..shine taja min tsaki taje daki, shine fa nagaji muka bita saman dan muga whats taking her soo long daga tambayar yaran nan duka suka hargitso suna xagina...dede nan ta kara fashewa da kuka.. 


anty safee daga tambayar ruwa meya kawo maganan wai ibaad baya sona ya bugeni? kawai suka kama kawata suna dukanta..kuma wallh laifin yarinyar nan ce, ita bakuwa ma amma wai itace me bakin zagina su sulthana kuma suka goya mata baya mena taba musu...was i ever bad to u guys??


da wani irin bacin rai kulthum tace wallah karya kikeyi, kiji tsoron Allah kisan zaki mutu anty zainab wallah karya kike mana..sultana ta fashe da kuka sosai...ayaanah bata ma iya dago kanta ba tay shiru tana hawaye sosai....


surutu ne ya cika falon ammi babba ta dau xafi ant safeera ma tafara ma kulthum questions but only to judge her with it..


majazen basuce komi ba dake duk sunsan waye me gaskiya, shide ibaad mamaki ne ya fara rufesa da fargaba dan bai taba kawowa cewa zainab arifah zata fara saka ma rayuwar ayaanah zuƙa ba.. 


yau yafara sanin cewa dolene akwai wani abu aran zainab gameda ayaana wanda bai sani ba nd he must find out sabida ko da wasa bazai sake haka yafara shiga tsakaninsu ba


hargitsi da cece kuce ya kaure sultana da kulthum babu bayanin da basuyi ba haka safiya ta karyata su ta gaskata zainab arifah tace ai komi agabanta akay, ammi babba ta inda take shiga bata nan take fita ba tace ai dama ta lura da su ukun nan banda gulma da iskanci da raini bau abunda suke koya ynx


wani baqar magn ta dinga gasa ma ayaana akan batun zainab arifah da ibaad tana ce mata ita asuwa? ina ruwanta da wnn magann inba raini da gulma yaushe tazo cikin su dahar zata buga kirji ta gaya ma zainab arifah maganan banza inba gulma ba..



saida kowa yagama musu iya fadan da zai musu kafin nan ibaad yace musu subawa zainab arifaah din haquri


..bakaramin kuka su kulthum sukayi ba wanda badan ibaad bane dakansa yasa baki da wallah bazasu taba bada hakurin ba haka kuwa kowaccen su tace mata anty zainab kiy hakuri...kafin zuciyarta yay sanyi.


wani dan uban dadi taji da ya musu fada akan karsu sake fada ko cacar baki da wani ko wata babba agidan idan ba haka ba zai dauki mataki akansu.. bai wani zafafa ba yace musu su tashi su tafi yana furta hakan shima ya fita


sultana da kulthum kowacce ta hau dokin zuciya da tsananin bacin rai da fushi suka haura sama kmr iska


ayaana ce bata koyi motsi ba tana tsugune tana kuka sosai hajy mairo sai surutu take mata akanta tamata fada sosai ...


Ammi karama batace komi tana shigowa wajen tazo ta daga ayaanahn akasa tare da kama hannunta suka bar falon. hjy mairo ta bisu abaya tana masifa duk lefi tana so ta dora shi akan ayanahn sabida duk abunda safiya tafada,

mujaheed yay sauri ya tsareta sukaje sashenta tare dashi aka bar ammi karamn da ayaanah..


daga nan falo kuwa wani sabuwar tantin sharri suka bude anty safeera ce kawai bata gane komi ba, ammi babba kuwa sai kara ma sharrin wuta takey zainab arifah tace musu ai ta jima da gane cewa ayaana tana da raini da baqin hali shiyasa jininta bai hadu da yarinyarba kuma tay ta gaya ma mujaheed sai suta karyata ta toh gashinan yau asirinta ta tono.


ammi babba tahau bambami tace ai ammi karama ce take daure mata gindi..kuma ibaad yana tsoron ya batawa mum dinsa rai shiyasa basa hukunta ayaana ita dama ta jima da sanin yarinyar bata da hankali.. haka suka ta murda maganganu kowa yana fadin nasa har sukasa anty safeera ta soma yarda da su..


maheer yana dawowa ya samu mujaheed yana kan fada ma hajiya akanta dena saurin yanke hukunci kowa yasan ba haka halin yaran nan yake ba kuma bazasu taba zagin zainab arifa akan wannan maganan ba sabida dukansu suna tsoron ibaad...


tace sam ai safiya ta bada shaida ita yar uwarsu ne na jini ai bazata musu karya ba


harsaida ta maimata ma maheer magann snn ya nitsu ya warware mata karyan dake ciki dalla dalla kafin nan ta yadda har tay shiru..



Ammi karama ta dinga rarrashin ayaanah ita duk tsoron haduwar su da ibaad takeji sosai, bataso ya tuhumeta akan maganan sabida tasan ta furta ma zainab arifah hakan kuma bazata iya masa karya ba

..ahaka har ammi ta rarrasheta tay bacci



6:pm ibaad ya gama lailaya abunda ya farun aransa ya fito waje zai yi alwala knn sai ga nan zainab arifah da kawarta nala tun daga nesa yafara jin converstion dinsu suna magana kasa kasa suna dariya "i just cant wait to tell rukky ur one billion dollar story..suka kwashe da dariya" tace "kinga next time none of them will mess with me "nala ta kara kashe murya tace..amma kin bani mamaki how did come up with that story sharply nd babe u need to get that safiya girl a gift, she relly help dan naga gogan naki kamr fa bai wani yarda da storyn ba saida safiyan nan ta saka baki..

"tace'yeah ai dama bazai yarda ba, haka yakeyi akan yarnyr baya ganin laifinta, but i cant deny her back up was really useful." kinga muyi sauri muje gida kar wani yajimu cos ur cloth are even torn yarannan fa sun jibge ki wallah...tsaki nala taja bakiga cixon da dayan tamin bane dole naje nayi tetanus ai naji dadi da aka sa suka baki hakuri marasa kunyar yara kadan sukagani dahaka zaki koya musu hankli


tana gama rufe baki sai caraf suka hango ta bayan ibaad ata inda suke din saidai bai musu alaman yaji su ba dake sunga baiko juya ba, wani cakkk suka tsaya da kokontun hakan aransu, suka dan kalle juna, nala ta mata ido akan ta sauya fuska izuwa na tausayi..


aikuwa atake tay hakan

suka taho kamr ruwa ya kwaso su daf kusa dashi suka tsaya ahkli cikin muryan tausayi tace"..hey...ashe kana nan..i and my freind ar just leaving nd i am very sorry abt what happen..mu zamu tafi!


baice komi ba har saida ya gama alwalansa snn ya miƙe ya kalle nala yace "can u excuse us?wani murnushi tay tace yess da wani irin sauri ta bar wajen taje jikin motarsu ta tsaya driver na ciki yana zaune.


nala tana barin wajen kamar kiftawar ido da bisimillah taga fusknsa ya wani irin canzawa kmr na mala'ikal daukar rai

da wani irin cold voice yace" u were saying??


ajiyan zuciya tay mai nauyi adan tsorace tace "listen ib..aad..nasan abunda ya faru aciki is not pleasant but you knw it hurts me duk lokacin da akay amfani da abunda kamin dan nace inason ka ana zagina dashi, coming frm our younger ones is very disrepcful. 


cikin katseta yace harke kina maganan respect? havent u disrespect urself enuf to lie againt those kids zaki kalli tsabar idona kimin karya ynxu? what did u think i am, a fool..?


bakinta na rawa rawa tace "bangane ba? ya zakace ina maka karya but you saw what happen ryt..


zata fara kuka yace kee karki sake ki tara min jama'a i am not in the mood  to embrass you nd ur little lie today".. i will ask ayaanah she will tell me the truth kuma zan yarda da ita sabida bata batamin karya ba snn nasan kinsaka safiya ta kareki agaban mutane amma bazaki iya sata tamin karya ba..i can call her here ryt now to spit it in ur face if u daubt me....but unfurntly keda kawarki kun riga kun fada yanxu kuma duk naji...how u fake d story, how u hate them how u want to bribe safiya with gift? ke..bari nagaya miki bakida ilimin da zaki min wani karya koda bana wajen i knw dos kids dint start the fight, u intentionally ignite it  u planned this whole thing nd dats why u sent safiya to call me. kinjima kinajin cewa kinada wata power akan komi amma kisani bafa akan kowa powernki zaiyi aiki ba, bana tsoron babanki bare ke.


magana da nake miki da duk kulaki danake its bcos i respect my uncle dat asked me to vist ur house in d first place for sake of ur health, inda kuma nace masa bazan je ba da babu abunda ya isa ya min saidai ki mutu da duk abunda ke damunki azcyrki, snn kisani inkin mutun shikansa babanki bazai iya min komi ba..so, next time u want to feel like u have power to come to this house and lie againts my sisters have it at the back of ur mind that i can withdraw all the privilaged respect i gave to my uncle dats is sharking your empty skull najin cewa zaki iya yimun duk abunda ki kaga dama..bazaki iya ba..dont deceive urself ure not my type..stay the fuck away frm my sisters nd this will be the very last time da zan gaya miki haka..kije kicigaba da jin wanda suke zugaki kiyi wnn haukar amma ranar da kika sake taba yarinyar nan, zainab.. i promise u.. that will be the last time u will ever get the chance to call me yr brother or what eva

..cos i will hurt u so bad that u will hate me, nd i really wanna see u try ba takamar ki shine mahaifinki ba?kije kiyi duk abunda zaki yi nd i will shock you!!


tunda yafara maganan wani irin hawaye takeyi suna sauko mata zurrr kamar an kunna ruwan rafi, jiri taji ya rufeta batamasan yaushe har ya gama ya juya yabarta awajen ya nufi masallaci bata iya ko motsi ba har saida nala tazo ta jawota da karfin tsiya kafin nan tadawo hayyacinta...


suna hade ido da nala ta rushe da wani irin kuka..jikinta na wani irin kyarma nala ta jawota taturo ta aciki motar da karfi tace ma driver ya tukasu da sauri ko bari gidan basuyi ba tafara numfashi sama sama...tana rabza kuka kwakwalrta a birkice tana cewa nala ibaad yace zai rabu dani...pls tell me what to do na shiga uku..what i have i done? rarrashinta nala takeyi amma inaaaa kuka kawai takey kamr zata cire ranta...he knws i am lying nashiga uku


hanyar gidan sun driver  yay dasu tamasa tsawa tace masa aa kawai ya kaisu gidansu nala dan batason babanta yasan abunda ya faru..



tun bayan faruwar hakan ayaana ta jima acikin fargaba tanata tsammanin ibaad zai kirata ya mata fada da dare kafin su koma gida saitaga baiko kulata ba, bacci ma tay batama san meyafaru ba ta farka ta samu safiya sheme shema akan gado jikinta yay rada rada da zanen bulala 


akace ammi karama ce ta mata shegn dukan kawo wuka, ibaad yay contrling tempersa bai ko tabata ba shi ya kirata agabantan ya gayama mamansun duk abunda yaji su zainab din suke fada akan safiyan, sai ya kyalesu, wani irin duka yau safiya ta sha awajen ammi karama wanda ko hajy mairon dake kkrin bin bayanta ma bata karbeta ba.. abkin sultana maheer yaji duk kan labarin bata boye masa komi ba .


har sai washe gari snn gaskiyan labari ya fito acikin gidan, har jikin anty safeera yay sanyi dan yadda su zainab da ammi babba suka dinga kara wuta har itama ta yarda dasu, tun jiya kulthum taki taci abinci kuma batace mata komi ba duk tarasa me yake mata dadi...


ranar bakaramin drama akayi agidan ba har saida yamma can da maheer yazo wajen uncle moh kafin aka tara su duka duk ya sansantasu

...kowa ya gane kawai zainab ce take nemansu da mgna har maganan ya wuce


afannin zainab arifah kuwa ko tashin hankli da kukan data sasu ayaanah baikai wanda ita tay ba dan duk yadda sukaso sunemi mafita da rukky tazo taji maganan tace mata ai maganinta kenan databi shawarar nala yanxu ibaad bazai sake yarda da ita ba


...saurayin da baka sameshi a tafin hannunka inakai da yin munarfuci akan sisters dinsa da sunansa..rukky tace mata mafita daya ne, ta dan dauke kafarta agidan, sai can daga baya taje ta fara jan yarinyar ajiki inta dawo friendly da ayaana ko bata shi haquri zai  hakura, gasu dai duk yara ne amma kullum sai rukky ta gaya mata cewa bazata iya samun soyayyar ibaad da ikon babanta ko ikon makirci ba dolene saita iya siyasa..


dake duk a tsorace take atake yau tay naam da wannan shawarar rukkyn ranar sunday very early in d moring ta bar gidan su nalan ta koma gida taje tanata tunanin shirmeb data aikata



ranar monday su ayaanah suka fara exams dinsu kusan kowa hanklinsa nakan abu daya ayaana ta fara jan jan baya da abubuwa dayawa musmn inya shafi anty safeera sabida ta lura tana tare da zainab arifah da ammi babba sosai..zainab kuwa data dauke kafarta agidan anty safeeran kawai take kira akai akai..


kowa na harkan karatun exms dinsa safiya ce kawai take agalabaice dan tun da aka fara exam, cikin ruwan sanyi ibaad yake cin ubanta da wani irin wicked silent treatment wanda ita dakanta tafara yanke hukunci ficewa kawai aharkan ayaanah gani take ai duk akanta yaa ibaad yake walakanta kowa 


har suka gama exams

itace kawai takejin wahala agidan duk wani hanyar jin dadi ta ya katse har aka basu hutu bata fita bata kallo ya katse mata komi zainab Arifah kuma bata kara lekowa gidan ba


Haka rayuwa ta kasance musu har na tsawon wata guda ranar monday da yamma sunakan kallo ita da ammi karama 

kulthum tazo sashen ammi karaman ta same ayaana da murna tace mata ynxun nan sltana ta kira tace mata ai result din schll dinsu ya fito itama ta shiga dash board inta ta duba....


...wani irin fargaba taji ya lullumeta Ammi tace mata karta damu zata duba mata awayarta....


tsabar fargaba ji tay kmar tace musu a'a ammi ta shiga schl portal din tace nafa taje ta dauko reg numberta da paswd atake taje ta kawo tanaji zuciyarta kmr zai fashe dan fargaba... mannuwa tay da jikin ammi tunda aka login suna budewa suka fara ganin As da Bs..A inta biyar bs inta hudu nd she came 4th


...kulthum tay wani irin tsallen murna ta rungumeta, tace oh my god congratulations ayana atsakiyar term fa kikaje??? da mamaki ammi tace masha Allah, wwoow my doter i dint expect this ayaana gaskiya kinyi kokari sosai 

..zare ido kawai ayaana take tana musu yake duk tarasa dadi zataji ko fargaba she can clearly rmber how he said is 1st or nothing...suna cikin haka taji muryansa a kofa da wani irin sauri ta kankame jikin ammi karama tareda boye fuskata abayanta harya shigo ciki......sai taga bashi kadai bane, mujaheed yana zuwa ya kalleta yace "ayaana baban mu yana kiranki..come fast..



#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[28/11, 20:20] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

Arewabook@surayyahms.


⏯️3️⃣2️⃣


Ayaanah ta ji zuciyarta ta tsaya cak lokacin da Mujahīd ya furta come fast din..sai Kafin ta ce komai, Kulthum ta kama hannunta cikin murna, Ammi karama kuma na murmushi, hanklin Ayaanah da zuciyarta gabaki daya baya jikinta duk murna da jin dadin sakamakon nan da akayi kalmar da ta tsaya mata a kunne guda ce “First… or nothing wanda ta san batakai ba,Sharadi ne, kuma ka’idarsa ce.


satar kallonsa takey har ya karaso ciki Kamar kullum, shigowarsa na ɗauke da nutsuwa da kamiya babu hayaniya, qamshin turarensa me tsada atake take ya mamaye wajen da sanyin dadinsa.


idonta na kallon kasa ayayinda kulthum ke rike da hannunta A hankali sukace mai "sannu da shigowa yaa."kallo daya yay musu ya amsa da kai snn ya wuce dakinsa, asulale suka bi bayan mujaheed kai tsaye suka wuce sashen anty safeera wanda bata saka komi aranta face harsaida suka isa..


mujaheed dake shirin wucewa dakin anty safeera yace "kuje falonsa a sama ki sameshi, kulthum zata raka ki..cikin sanyn nitsuwa ayaanah tace "toh" kulthum ta rakatan kuwa har sama cikin karamin falonsa da sallama me sanyi suka bude wata shirgegen green labulen ayaanah tay maza ta ɓoye fuskarta ata bayan kulthum jin yadda uncl moh ya kira sunanta da "ayaanah Dear" da wani irin fara'a tun kan su karaso..


suna gabatowa ta lura da akwai wani baƙon abu a tare da shi wanda box ne madaidaici an nannade shi da ribbon mai launin ruwan toka.

Baiwani tsaya ba bai kuma kalli kowa sosai ba sai Ayaanah.


tana dan dago kai Idanuwansu suka haɗu dajuna na ɗan daƙiƙa kaɗan, ganin tana jin nauyinsa da kunyarsa yasa ya ɗan kauda kai yana murmushi tamkar nawanda yake jin mugun tausayinta tareda jin daɗi alokaci ɗaya.


Har zata zauna kasa tafara gaishesa yace "aa karki zauna kasa zauna anan mana dear .ya mata nuni da soft chair da ke kurkusa danashi, respcfully ta zauna kanta na kasa ahnkli tace uncle ga ni nan naji kace na zo,kulthum ta matsa gefe, yana mai dan murmushi ya turo box din gaban ayaana" Ki buɗe,” kawai ya faɗa. ta kalle shi da mamki sai taga kulthum tana dan noding mata kai, hannunta na rawa ta bude gift box din ahnkli taga wani hadadden fancy set ne na Art supplies  kmr colours, sketchbook, glitter pens da wani irin tsadadden Cute hair accessories da small girlish puzzle game aciki da wata nice hoodie dark red colour shima acikinn fancy kwalinsa.


..abunka da zucyar yaro tuni taji abun ya bala'in burgeta ta dago kai da sauri ta kalleshi taga yana murmushi ahnkli yace congratulations my dear result dinku ya fito ko? ahnkli tace eh amma...cikin katseta yace ai ni ban damu da nasara ajikin takarda ba, dake kawai na damu dan haka Ki kula da kanki snn ki ƙara dagewa kifi haka..ahnkli yace "kina da daraja fiye da wannan my dear.


shiru tay cikin rasa sanin me xatace mai dan ji tay kamar maganan nasa sun mata nauyi sosai, can ta dago da ladabi da jin nauyinsa a muryanta tace uncle nagode sosai Allah ya saka da alheri,in sha Allah zany kkri sosai nan gaba


yana murmushi...yace"nine da godiya..ya kalle yarsa dake tsaye yace nd you too baby kin yi kkri ko, i neva daubted you ure the best amma wnn karon gift na ayaanah ne ita kadai. da murmushin jin dadin kalamansa kulthum tace thank you soo much baba ai tay kkri mid term taje fa. ,yace yes she tried baby, dan shiru ne ya ratsa wajen after a while kafin nan ya sallamesu..


duka suka fito suna murna dakin kulthum suka nufa suka zauna akan gado suka hau bubbude gifts din for a while harta mance fargaban ibaad dake damun kwakwalrta suka kira sultana a waya sunata surutu kowa yay ma ayaana murna sukasa taji cewa ai bakaramin kkri tay ba haka ta rarraba musu wasu abubuwa daga ciki amma tace sai ta nuna ma ammi kafin ta kawo musu kowa tabashi, kulthum tana ta murna dan dama jan rigar sanyin ne yafi tsole mata ido kuma shi ayaana ta bata kyauta,.


harsaida suka gama kallon duka gifts din duka snn ta tarkatasu duka ta dawo dashi sashen ammi karama. xuwa tay ta samu ammi na zaune a falo ita daya da tulin murnan ta tazo da box din tace "Ammi..Ammi kigani uncle ne ya bani yace wai nay kkri...da fara'a ammi tace masha Allah ahh uncle dinkun nan ya kyauta mugani, da murna ta mika mata, ammi ta bude ta gaggani tace masha Allah, ayaana u tried, in sha Allah anjima zan miki abu me dadi kici ina fata kuma next time Allah yasa ki fi haka kkri, dan kwanciya tay ajikin ammin da murmushi me yawa tace Ameen ammi nagode in sha Allah zanzo first" daga nan ammi tajata suka je wajen hajya mairo dake kan shiri gobe jumaa zata kwana agidan bappa zaidu ana nuna mata result itama tay murna harsaida tasa ayaana kuka tana ce mata ai da tudu kike da ba haka ba..kinyi kkri sosai ayaana am, waye ma zaiyi tunanin zaki rayu batare da yar uwarki da mahaifyarki ba

..haka tasaka ayana tafara hawaye dakyr ammi karama ta rarrasheta, ana daf za'a kira magrib suka rakata kofa drivern bappa zaidu yazo ya dauketa ta wuce can gidan su ammi babba.


dawowarsu ciki bada jimawa ba tazo ta dauki rigar sanyin takai ma kulthum har dakinta acan tay sallahn magrib da isha suka sha nutella da cookie suna ta hira can kafin tafara tunanin gamuwarta da ibaad sai taji atake komi ya tsaya mata cak


mikewa tay tace ma kulthum zata tafi kawai sai gobe, agurguje ta sauka cikin sauri ta dawo sashensu dan karya kasance bayan isha zai tafi gida...


gabanta na wani irin faduwa ta shigo jin babu motsin kowa a sashen yasa fargaban ta ya karu tana kuwa lekowa ta kofarsa ta tsaya cak jin kamar an danna mata remote, ganin safiya tay a kasa a kofarsa ta waje tanakan kneeling tsabar tagaji hannun sai reto yakey a sama tanata matse hawaye


da saurin fargaba ta juya zata gudu taje wajen ammi karama

tana juyawa kuwa taji sautin muryansa frm no where...a adake yace"kee, ina zaki je.., a kangare ta juyo jikinta na rawa ganin fuskrsa ne kawai ya leko 


suna hade ido yace" what are u doing here"..bakin ta na rawa rawa tace dama..dama..nazo

ince...ince..."cikin katseta da tsaki yace "just come in"..Da sauri ta gyada kai ta karaso da tsananin fargaba ta bude kofarsa a karo na farko dataga saman table dinsa a wargaje

ya aje katon white A4 ppers yana drawing wasu abubuwa ajiki


jikinta na rawa rawa ta taho dan tasan na biyu safiya tazo, ahnkli tabi ta tsare sa da ido baiko kalleta ba sai har da ya aje pencil din snn suka hade ido yace "what? cikin hadiyar yawu ta rusuna kadan da sanyin murya tace "Dama kulthum ne taxo dazu tace min wai result dinmu ya fito..yace "and so? kmr zatayi kuka tace "shine nazo na gaya maka" yace okay...did u come first?.

maqudan hawayen datake dannewa ya sauka a raunace tace "a'a..i came fourth"yace "hmm 4th, shine akace kizo kimin kuka? xatay mgnan cikin katseta yace.. naji.. naji.."uve tried. but not enuf to receive a congratulation from me


..adan shagwabe tace but i will try hard next time i promise.


girarsa na sama adage yace karma kiymin alkwarin da bazaki iya dauka ba i told u, u were not dat smart saidai a can kauyenku , u came mid term nikuma i came 2 weeks to exams in my schll but i came first, kije ammi zata nuna miki ai zaki gani..kinzo kin same wanda suka fiki ilimi ko? hmmm uve a long way to go yarinya...hawaye na kan zuba a idonta cikin turomai baki tace"i will try next time... yace okay, then dont come to my room nd cry again untill u come first i dnt walk with not sooo smart ppl. 


duk da serious face din dayasa har ranta she knw he is just teasing her...saidai sosai mgn nasa yasaka takarajin dolene ma ta dage ta zo na daya kodan ta kureshi...


shirun datay tana kan raya hakan aranta yasa ya juyo suna hade ido yace "inkuka kikazo yi anan ki tashi ki tafi kiban waje...dama uban  waye yaje miki kije kizo na hudun


mikewa tay jiki a sanyaye taxo daf dashi da wani irin sihirtacn narkakken murya tace toh kay hqri mana yaaya..ainace zan gyara.  


yace 'naji"..ya dauki hankynsa ya bata yace "share hawayenki sai ki tayani tattara wannn papers din saiki tafi .


hakan dayafada yasa taji zuciyarta yay sanyi sosai, dan tagama tsammnin tsawa da hukunci me tsauri zai dauka akanta  sai taga ba haka ba, duk gidan ma shine kawai yasaka taji kmr she is deeply challenged to do better next time sosai tasa aranta zatay kkri nan gaba. tana gama share hawaye da hankyn taji gabaki daya ta dawo tana qamshi irin nasa.


cikin sanyin nutsuwa tafara tayashi tattara drawing dinsan kallonta yakeyi amma bazaka taba sanin kallonta yake ba, her cute eye balls were fixed on his bold italic fine hand writing dinsa wanda da alama ya dauke mata hankalinta sosai...


har saida suka gama snn ta daga ido suka kalle juna sai kuma taji bakinta yay mata nauyi tana son tagaya masa abunda uncle moh ya bata amma tsoron me zaice mata yasa ta kasa iya bude baki. har ya dauke idonsa akanta ya tattara jakarsa yazauna ya saka takalminsa ya gyara room din sharply ya kamo hannunta suka fice atare..


suna bude kofa safiya dake kneeling ta dinga satar kallonsu baki bude dan tagama daukawa yau zaiy ma ayaana dukan tsiya,sai taga har wani kama hannunta yay suka fito atare, wani gulluton baqin ciki taji ya rike mata wuya, ita fa na biyu taci akasata kneeling din nan bayan uban masifa da zungurin data sha. ko kallonta baiy ba kuwa suka wuce ta da ayaanan, suna kaiwa falon ammi ya sake mata hannu ahnkli yace "go to bed" ni zanje gida, hawaye taji na nemn cika mata ido sai ta shanye tace "okay..gud nite.. cikin kwayar idonta ya kalla yace "thanks" kafin ta dauke idonta anashi sukaji motsin ammi da sauri ta juya ta wuce daki har ammi ta karaso sukay bankwana da shi ya wuce ya tafi.....


tun bayan tafiyarsa harta koma dakinsun ta kwanta tunanin kalamnsa da fuskansa kawai takeyi jin wani birkitaccen shauqin yadda zuciyarta ya riƙeshi da muhimmaci wanda ita kanta bata san ya zata fassarashi ba batamasan meye takeji ba

...har tay bacci safiya bata shigo ba sai wajen around 11;30 na dare da ammi tazo ta sameta a tsugune dan tsabar tsoron ibaad datake ji har yanxu tanakan gyangydi wajen datake kneeling din bata tashi ba fitowar ammin ne yasa ta fatattaketa ta wuce daki taje ta kwanta


da tsaki ta shigo dakin dan tsabar haushin ayaanah datakeji haryau bata taɓa bari sun kwana kurkusa da juna ba kowa baccin sa yakeyi acan can edge din gado da safe ma suka tashi basuce ma junansu komi ba inba wani rikici ne ya hadasu ba. yau sosai tsanan datake mata yakara zafafa dan haryau batagama jin haushin yadda sultana take makalkale ma uwarta ba yet ayaana is just another pain in her ass, sai takeji kmar ma gara sultana, soyayyr uwarta kawai ta karbe mata, lamarin ayaana yafi ci mata rai cos it pains her alot to deeply feel in her heart that yaa ibaad yana bala'in fifita ayaana fiye da kowa, inba haka ba ranarfa ta musu laɓe taji duk sharudan daya saka mata akan karatu, amma yama za'ay ta karya sharadinsa na zuwa first snn ace bai dake ta ba harma ya wani kamo hnnunta su fito waje tare...wann abun sosai yayi ma safiya zafi har saida tay kukan baqin cikin ayaana kafin tay bcci.


bayan faruwar haka gidan bai kara zama lively ba sai ranar asabar tunda ayaana da kulthum da sultana suka hadu duniya yay dadi. gashi ranar ne aka kawo sabbin dinkuna na atamfofi da laces 20 pieces masu shegen kyau da tsada da ammi karama tay odersu wajen mum ramlat collection duka aka dinka ma ayaana


ranar asabar din tamkar ranar sallah haka taji aranta ganin yadda kawayenta suka mamayeta suna ta gwada sabbin kayanta a dakin ammi karama kowa yana mata murna suna dariya kmr sun mugun jimawa da sanin juna. she bacome so overwhelmed with joy da dan uban gatan da ammi karama ta nuna mata. wknd din yay ma su ayaana dadi, kowa yazo anci abinci anyi raha zainab arifah ne kadai haryau bata zago ba wanda hakan sosai ya fara sosa ma hjy mairo zuciya duk ta dauka ko akan ayaana ne zainab din tay fushi.


haka ta tursasa anty safeera ta kira mata ita awaya wanda dakyar ma ta dauka suka dan yi magana ta dinga ja mata aji amma ko ajikin ta tsohuwar nan tay ta bata haquri akan karta yanke zumuncin su sabida abunda ya faru tsakaninta da ayaana, bata kuwa wani bata kwakkwran amsa ba har suka gama wayar


monday nayi kowa ya shirya aka wuce schll wanda ya kasance sabuwar yanayi ga ayana dan da wani irin karfin gwiwa tafara wnn term din duba da har anyi aproaving admission inta within next four month zata samu sabuwar uniform na jss class itama. suna farawa ta dukufa tare da bada hanklinta kawayenta na schl din ma tafara baya baya dasu sai in ayi break su hadu da sultana kawai suci abinci.


satin gabaki daya was fun face saida sultana tabata labari cewa ai uncle moh yakama kulthum da hoodie data bata kuma ya mata fada sosai yace kar ya sake bawa ayaanan kyauta snn yagani ajikinsu..


bakaramin sanyin jiki hakan ya bawa ayanah  anar suna komawa da driver ko sashen ammi karama bata wuce ba ta nufi bangaren anty safeera


samu tay dukansu biyu suna zaune kulthum tanacin abinci da alama itama shigowartan kenan, tunda ayaana tay sallama ta gaishe da anty safeera duk sai ta rasa me zata gayawa kulthum, face saida kulthum din ta haura sama taje ta dauko mata red hoodie in da sakin fuska tace "dama innay wanka ne zanxo 

nakawo miki rigarki kiy haqri baba na yace min kar ya sake baki abu na karba..muryan ayana kmr na wanda zatay kuka tace "kai kulthum amma ai kyauta na baki meyasa bakigaya masa haka ba dazu

hakama fa sultana ta dawo min da ribbons dina wai baku so, tana fadin haka hawayenta ya fara xuba a idonta.....cikin sakin murmushi anty safeera ta jawo hannunta tace "haba ayaana, karki dauki abun haka mana  meye na kuka, ai bawai sunki abunki bane nima fa ina bayan babansun this gift is specially for you...su ai anjima ana siya musu, bekamata su karbi naki ba shiyasa ma yace musu su dawo miki dashi...


jiki a sanyaye kulthum ta dafata, ganin ayaanan na hawaye sosai tace haba ayana na ai zan dinga sawa aro kinji! fadin hakan da kulthum tay yasa ayaana taji dama dama tace toh shikenan zan aje miki


shafa kanta anty safeera tay cikin lallashi tace "ure very kind my dear...yanxu kije ki cire uniform kici abincinki karki damu babu komi kinji? hawayenta ta share ahnkli tace toh anty sai anjima..ta gyada kai,suka bata red hoodie in ta karba..da kallo suka bita tana wucewa saiga mujaheed ya sauko ganin yadda sukay zugum da tausayin ayaana ya saka ya tambayesu what is going on, anty safeera ta hau gaya masa, kyabe baki yay baice komi ba cos if feels odd for him da babansu yafara behving haka, dan gaskyr shine ko su yayansa baiya saya musu kyauta..saidai dake suna zuwa first din kowani lkc yakan bada anty safeera kudi ta saya musu duk abunda suke so amma bai taba shida kansa yaje kasuwa ya siyo musu kyauta ba. da tausayi anty safeera tace musu ai ayana tamkr marainiya ce tunda babu uwa babu uba ynxu atare da  ita, tace hala shiyasa babansu yake son yamata abubuwa da zaisaka taji kamr ba a wareta agidan ba,..da wann furucintan yaranta duka suka kara fhimtar haka aka bari acewa tausayi ne da kuma taimako yasaka yncle moh yake ma ayaana abubuwa nadaban.



after few days komi ya dawo normal ata ko wani bangare, karatun ibaad yanamai kara zafafawa, har ya kaiga an fara rage musu hours da sukeyi a private club dinsun dan ya dinga samun cikakken nutsuwa. basu kara jin duriyar zainab arifah agidan ba har saida tacika wata daya har da sati snn ta shirya ta sako wata abaya me kyau na mutunci taxo gidan wkends daga ita sai driver, tun ahanya ta dinga kkrin kawo duka tunanin irin magnganun da suke yi da ruqayya insunje makaranta wanda  badan ruqayya tayta bata shawara yadda zatay ta dawo da mutuncinta agidan ba da kwata kwata bata san ya zatay ba.


mahaifyar ruqayyar yar siyasa ce babba,gata dai yar 14 going to 15yr amma tunanin manya ne da ita sosai tafi nala nesa bakusa ba dan nala banbamcinsu da zainab Arifah kawai dan gata ne da kuma albarkan daukaka da karfin power da sunan familyn al-mansur suke dauke dashi, al-mansur kusan suna ne dayake iya bude kowani irin kofar, snn ya durkusar da kowani irin sarki, hakama yan kasuwa da yan siyasa mahaifin zainab arifah yana da wani irin strong ties da international gvnt nd secret organisations saikaga mutum komin ikonsa da kudinsa ba son shiga harkansa bare ayi wasa dashi shiyasa golden dotersa zainab aarifah ta zama sananniya acikin makarntar wanda  haryau shugabannin ta da malamnan cikinta gani suke kmr babban alfarma prof zayyanu yay da ya kawo yarsa karatu dasu...



yau shigar mutunci tay kamr yadda ruqayya ta gindaya mata, sashen hajy mairo ta wuce direct ta samu kowa ya taru yaran ne kawai ba sa wajen kowa nata mamkin ganinta hjy mairo ta rungumeta tana murna ahh ahhh zainabu  lale marhaba kaga yarinyar kirki ashe ba xuciya da mu kikayi ba, murmushi kawai tay bata amsa ta ba ta wani narke ajikinta d shigar sakarci ta gaishe su da bappa zaidu da sauran matanen," su ammi babba sai shige shige suke mata duk dama ta balain basu mamaki da sukaji tace ai bada hakuri tazo ta bawa su ayaanah tace ai kawarta nala ce ta shirya komi ita babu ruwan ta aciki shiyasa ma zata basu hquri. falon ya cika da kace kacen mata kowa yana yabon ta anty safeera kuwa abun bedaina bata mamaki ba.


can dai suka nufi sashenta tasamu su kulthum suna zaune a regular spot dinsu a falo su da yayansu mujaheed  yasaka musu puzzle game duk wanda yaci zai bashi kudi ayanah ce kawai bata wajen taje debo musu ruwa marar sanyi


yaran suna ganinta suka harxuka zasu bar wajen anty safeera tace musu aa suzauna, a tsomare suka zauna suna watsa mata harar kasa kasa zainab arifah duk ta daure ta sharesu dan ruqayya ta gaya mata tadinga tuna cewa in bata daure tay hakan ba duk bazata samu kan ibaad ta sauki ba, nd ji take kmr zata iyayin komi inde ibaad zai yafe mata su dawo suna magana kmr dacan dan dakayr tay surviving kwana biyun nan data basanya shi a kwayar idonta ba


da wani irin makircitacn salo ta kalle su sultana tace" hi sisters..suka amsa ta ciki ciki, confidently da wani irin rigima tace "girls, abunda ya faru lets put it behind us tunda nazo nabaku hquri yau. by d way, it was all my frnds idea so i hope dai ya wuce...shiru suka mata jin yadda take kan laka komi akan kawarta basuce komi ba saiga nan ayaanah tana dawowa da goran ruwa

guda biyu a hannu


suna hade ido da zainab arifah din ta tsaya daga can gefe zainab din tafara mata wani irin murmushi kafin ta mata magana ayaana ta aje ruwan akan table agaban mujaheed da sauri ta doshi kofar waje ta kama hnyar sashen ammi karama da sauri duka suka bita da kallo...


anty safeera har ta budi baki  zata kwala mata kira akan ta dawo zainab arifah tace


"its okay, karki damu

anty safee..ai zanje sashen nasu.


ta kalle su sultana tace "so, guys are we cool ryt now? tun basu amsa ba anty safeera tace haba dont mind them they are cool, ai suma da lefinsu tunda kema ai elder sis dinsu suke rainaki..


cikin hade rai tace kulthum sultana oya kuma kubata haqri maganan nan ya wuce haka itace babba kuma taxo ta baku haqri ai sai kuyi hakuri...kusan atare suka ce "ya wuce anty zainab ..we are sorry too..dan karamin murmushi mujaheed yay yace good girls toh kusha hannu,abasu so suna qi haka ya saka duka suka sha hannu da zainab arifah kafin nan tabi anty safeera sama kowa na mamakinta, anty safee babu yadda bataso dan tasha cikin zainab Arifah ba amma tay kyam taki gaya mata komi 


tace bata so ne kawai babanta yaji maganan na ya hanata zuwa cikin yan uwanta kuma nd she is bored na zama agida..she refuse to admit sabida ibaad ta dawo bada hqri amma sosai anty safeera ta ganeta.


nasiha ta mata akan ta rika kama kanta da shiga harkan yaran msnm ma ayanaah da kowa yake jin tausayin ta ana taimaka ma rayuwarta, anty safeera tay ta bawa zainab arifah labarin yadda ayaanah ta taso, har mutuwar sisternta inaya, da rabuwarta iyayenta da zuwanta nan birni da duk wani temakon da su ammi babba suke mata kai har kayan da aka siya mata da kudin da su ammi karama da bappa zaidu suke ɓatawa akan lafyarta da welfare inta da wanda ibaad yake kashewa akan karatun ta da komi sai data warware ma zainab a tunaninta wann bayanin is enuf to make zainab arifah sympathetic nd to understand the situation of ayaana agidan fully, danta dafa gane cewa yarinyace datake bukatar kulawa da taimako da gata sosai bawai haka kawai ake mata abubuwa ba..


saidai anty safee batay tsammanin a baibai zainab take jin labarin ayana datake batan ba all she hears is a story of a helpless, poor, sick village girl with broken parents dataxo cin arzikin ibaad dinta..

dan dai bataga dalili da za'ace dan mahaifyr yarinya ta damka yarnya a hannun ibad shikenan kuma sai yazamo tamkar ubanta ba.


amemakon taji imani da tausayi sai taji matsancin kishi da haushi dan bakaramin irritating inta labarin ayaanahn yay ba..


har anty safeera tagama mata bayanin kom batace uffan ba sai ayyah, eyyyah, so sad..so sad... ko nuna wani alaman wani abu aranta batay ba har suka gama maganan ta sauko kasa direct ta wuce sashen ammi karama, lkcin ayanaa tana kitchen tare da maheer tana nuna masa inda coconut juice din ammi yake ibaad ne kawai a falo ya gama cin irin tsiren tsinken nan kenan sai gata nan ta shigo .


tunda ta yaye labulen ta kallesa taji duniyarta gabaki daya yay haske tamkar wanda dacan acikin duhu take ynxu ne dare ya waye, dan tabbas wann maqudan son datakeji akan ibaad bata tunanin natural ne, ji take kamar Allah ne dakansa ya diga mata kaunar ibaad aranta, tunda ta dora idanunta akansa taji duka jijyin xuciyarta sun tsaya cak 


ganin irin dressing din dake jikinsa oh my god irin mayun american urban fitters dinn ne

simple shirt creame colour, da wata matured suade tailored trousers he look old money classic, very smart nd groomed, tsaftarsa duk yafi tafiya da ita.


mancewa tay ana sallama ta shigo da dan rawan jiki da murmushi me sanyi tace "hi,ganin ya daga ido da sauri alamn baisan da shigowartan ba yasa tace ohhh..my bad

"salam...wani irin kallo ya mata a dake yace "wasalam

and who are u looking for?

..dan kadan ta lumshe ido tace "no one". cikin dauke kai yace "okay..daga nan ya cigaba da abun da yaky baikara kulataba, har tagama tsayuwarta ta taho ta zauna a kusa dashi cikin sauke ajiyan zuciya ahnkli tace "ive come to apologise..i am sooo sorry for what i did to ur sisters ibaad. it was childish dan Allah kay hakuri, suma na basu hakuri..i just want u to give a scnd chance kaima fa kasan ba hali bane, wallh baran kara bari wata kawa ta zugani ba...pls lets put this behind us..


yana jinta har ta gama tay shiru baice komi ba har ya gama tauna naman dake bakinsa ya dauki ruwa yasha snn ya dau tissure ya goge bakinsa  da hannunsa he used almost 10 pieces of sheet na tissure, wajen ya dauke da wani irin shiru,shi be kalleta ba baikuma ce mata uffan ba, har tafara kokonton ko ma baiji me tace bane amma kuma taga kusan daf da chair dinsa take zaune 


hawaye taji ya cika mata ido kirjinta yay nauyi ta kara juyowa ta kallesa taga kmr wayarsa ma yake shirin dauka muryanta na rawa na rawa tace are u listening to me at all?saida yaja kadan snn yace "yeah, apology ryt?toh, good for you!! now what? kallonsa take bata ko kiftawa dan duk duniya babu wanda yake bata mugun wahalar sha'ani kmr ibaad, the way yadda yake basar da ita yake ja mata aji da sauran su is deeply killing her, cos all her life ppl are made to worship, and serve her, rana daya kaje gidan su kaga yadda ake mata duk wasu hidiman rayuwanta acikin tsananin biyayya da nuna gata da sakalci har abada bazakay tsamanin zainab arifah zata taɓa budan baki tabawa wasu haquri dan kawai ta samu attention dinsa ba, bata dena kallonsa ba face saida taji hawayenta ya kusa zubowa ahnkli tace "are we cool now?? dede nan su ayaana suka fito tana daga idon ta kalle ayaana cikin dauke kai ta dafashi da wani irin shagwabben murya tace ibaad, i...missd you, nd i am sorry..pls say sumtin. mamaki ya cikashi kafin yace wani abu ta miƙe tana wani irin hawaye batace ma maheer komi ba ta kamo hannun ayaana da karfi ta jawota gabansa tana makalkale wuya tace "you see i wll apologise to her now..nide dan Allah ibaad kayi haquri wallh bazamu sake ba..


akaro na farko da ayaana tafara jin wani irin abu na rike mata zuciya zainab arifah ta fara kallonta tace hey little girl kiyi hquri kinji? i wll neva do that to u again kingama  ai agaban quardian inki na fada

toh ki mance da komi kinji


kafin ayaanah tafara sakin hawayenta yace musu ya isa haka..just let her go..anji ..ni wnn surutun na damu na. ta ki sake hannun ayaana, da tsaki ya sa hannunsa ya raba yace ma ayaana "leave. da sauri ta wuce ciki ta wuce dakinsu bata kara lekowa ba, itama znab din zatamai magana cikin daga mata hannu yace 'its okay..just leave. thanks! cikin lumshe ido da budewa ta mike ta dauki jakrta ta fita da fushi..


maheer ya girgiza kai ya karaso har saida ya zauna snn yace"..yarinyar nan fa dagaske ne take sonka..


runtse idonsa yay alaman baison jin wann maganan

ahnkli yace "maheer kaina yanamin ciwo wallh..virus inda ta samin a brain ina ma kabarni dasu is enuf


maheer yana murmushi yace hmm wata rana zakace na fada maka dan abunda zaisa zainab tazo ta bada haquri ai babban abu ne.


ibaad yace ohonta, kaga ni bawai na gama yarda da ita bane... i knw she is upto sumting kawai dai abarsa ahaka but will defnatly keep my eyes on her...


dariya maheer yay baice komi ba har suka bar maganan ya wuce haka, jim kadan yamma yay, bappa zaidu yace sam yau magrib ma agida zasuyi dan haka kawai kowa ya fito su wuce. yay tsammnin ayaanah zata fito kmr kullum suyi bye amma sai yaga har sukabbar gidan tun bayan data shiga dakin bata kara fitowa ba.



Bayan faruwar haka bada jimawa sosai ba rayuwa ya dawo normal tun suna dar dar da zainab arifah har suka saki jiki suna respcting inta normal, babu wani hayaniya..tunda ta lura kmr intana gefen ibaad ayaana bata magana yasata tafara wasu sabbin over caring bhrvs akan ayaanan masu ban haushi.


tay tay ibaad ya budi baki yace mata itama zata iya kula mashi da ayaana amma ina haryau bai taba kulata akan suggestion din datake kawo masa akan rayuwar ayaana ba. dataga kmr ta hakan bazata samu shiga ba kawai ta fara matsawa akan islamiya sabida yanzu haka tasan bazatakai wani cikakken 2yrs a nigeria ba, dan she is sure a kasar waje zatay duk wani sauran karatun dake gabanta ryt frm degree uptil level of PHD. dan sungama shiryawa da babanta cewa she is going to become a business icon, with a grade one major professorshp ryt frm (fin.tech, msc inta kuma a enterprise risk management, phd in financial economics) duka kuma a columbia univesity na manhattan dake birnin new york zatayi, is her best top ivy leaque unversities na duniya datake mutuwar son taga ta kasance acikinsa all her academic life wanda in few months zata fara shirye shirye. 


mai bawa babanta shawara yace tafara rubutu essays da exam na TOEFL dinta tana submitting tun yanxu sabida koda bata ci a farko ba ta samu daman sake rubutawa kafin ta gama scndry schl inta tunda tazo kurkusa.


da duk wann bayanin ta dinga damun ibaad da yawan kira da zuwa gidan akai akai har saida amminshi ta masa fada akan kawai ya amince mata tunda  dakanta take cewa zatay karatun addini yanzu. shide sharadin tan ne kwata kwata bai masa ba, cos he cant 

take care of ayaana snn ya kula da wata agefe ga nashi, karatun.


dakyar ya shawo kan amminshi ta barshi yace ma zainab din zaina kawo wani malami har gidansu yana mata karatun atleast 3 times a week

wednes, thur nd sunday. jin yace har gidansu zaina kawo malamin yasa ta amince atleast she get to see him 3 times a week da wuri wuri ta amince taje ta gayawa babanta har wani falo na musmn aka shirya mata na karatun agidansu the following week batare da bata lokci ba ibaad ya kawo malam jameel har gidan prof ana biyansa 200k a month yana koyawa zainab arifah karatun islama agidan wanda duk iyayen ta sun dauka abun bazai taɓa daurewa ba sabida sun san yarsu da sakalci da tsabar kwyuwa, da abun mamaki kuwa sai gashi har anci wata uku da wani abu zainab arifah tana zama tay karatu muddin ibaad ne zai kawo malami, kai wasu abubuwan ma da iyayen basa iya saka ta sai ga shine kawai zai ce mata tay kuma sai suga tay.


wanda memakon hakan yasa sudinjajin dadi aransu sai yana cusa musu tsananin  baqin ciki da fargaba,hajy hamida kullum zargin su bappa zaidu sukeyi akan sun tsafe ibaad ne shiyasa yarsu ta haukace akansa dan yagama musu da yarsu da soyayya sai su kasheta suhau kan gadon ubanta, she belive son da zainab arifah take ma ibaad  ba ordinary ba ne kullum tana wajen malamai  tana bayarda bincike haryau kuma anace mata ba aga komi ba.


shikuma prof yafi bada himma akan kashe masa yarsa kawai ake so ayi dan antsanesa

daga familysa kullum yana saka ido, duk abunda ibaad yake yi kuma haryau bai gama aminta sosai dashi ba duk dama ibaad bai taɓa ko awasa ya tambaye abun hnnunsa

ko ya nemi taimakon sa ba. sumtimes sai yace girman kai ne, wani bin komi yace munafurcine.


ata fannin ayaana kuwa duk dama ta saka kanta akan karatunta sosai saidai abubuwan da ya soma canzawa tsaknin ibaad da zainab arifah kuma tanaji kullum hajiya mairo sai tay ta hiran abun a falo, tayi ta fadin maganganu, tana cewa aiko rokon ibaad zasuy ya aure zainab sabida rayuwarta ya gyaru, ita batamasan meye ake ji a soyayya bare aure amma sai taji gabaki  bata kaunar ana hada ibaad da zainab arifah musmn akan batun aure


most of the time she looks normal amma daga ta ga zainab arifa tana rawan kai tana bada labarin islamiyta da ibaad sai tanajin rashin nitsuwa, this week suka fara exams a schll kuma tay karatunta sosai amma most of them bata san metake yawn rubutawa ba, har suka gama aka basu hutu, kwata kwata 3 weeks holidays sukayi agida sakamakonsu ya fitovkowa yana tsammnin ayaana zata yi gaba tana kara dubawa taga

4th din ta sake zamowa ranar kuka ta dingai a daki safiya kuwa ta rinka mata dariya kai kamar zata tashi sama tsabar dariyar mugunta..


dakyar ayaana tazo ta gane cewa kmr yawan jin labarin zainab arifah da yaa ibaad da hajya take damunsu dashi kmr fa shine yafara dauke mata hankli. kowa yay mata jaje, still taga ibaad baice mata komi ba..koda ta kai masa result din yace mata bazai gani ba har sai ta ci first. uncle moh km ko ajikinsa haka ya kara jajibo mata gifts ya bata sabida jss class zata shiga. duk ta shiga damuwa...ranar tana zaune a falo tay tagumi mujaheed yazo, da kyar ya lallameta ta gaya masa subject din da duk bataci ba, yace mata babu damuwa da daddare inbata komi tanazuwa wajensa a falon zaina koya mata iya wanda suke bata wahalan tunda tana lessons. kamr da wasa ayaanah taji dadin wnn maganan ranar monday suna komawa schl aka mata promotion zuwa side din manya jss da new uniform, duk ranar da babu lesson ta kan zo  ta same mujaheed yana koya mata extra lesson wanda sosai yajanye mind inta daga zuwa wajen hajiya tana jiyo abubuwan dake dama mata tunani


the funy thing was she cant even explain it, kawai dai bata so taji ana cewa yayanta zai auri anty zainab arifah ne, she doenst knw why but it alwys felt intensed in her small hrt


rayuwa yafara canzawa sosai da taimakon mujaheed wnn karon ayaana tazo na biyu

shima bata wani ji dadi ba duk dama ibaad ya dauki sabon wayar iphone13 me kyau ya bata sabida kowa acikin yaran gidan daya ya shiga scndry ake basu waya sabida saukaka cmuncation da asigments dake ma ana mugun saka musu ido, ya bata wayar nan baiko saka lambarsa aciki ba su mujaheed da sauran yan gidan suka karba suka  sasska nasu aciki sai can daga baya ta dauki lambar gogan awayan amminsa tay saving, shikansa bai sani ba saidaya ga ammin sa ta turo masa tex da wayar, murnan ayaanah daya da harynxu islamiya haryau itace take zuwa na daya sabida tuno da addanta datake yawan yi intana karatun qur'ani cos karatun addini was the best part of inayah's life tana da memries dinsu na hakan sosai saiyana sata tana tunata duk sanda take koyan karatu. bokon datake mutuwarso ne kuma ynxu yafara bata tsoro sosai, dan saida tay term kamr uku kafin nan finally Allah ya bata ikon cin nasarar zuwa na daya, ranar kam bakaramin murna tay ba, gashi a tsakiyar sati ne ibaad baizo gidan ba 

uncle moh da tuntuni yake boye kishinsa na ganin ibaad ne yafara saya mata waya bashi ba, yau anace mai ayaana tazo first baizo gidan ba saida yay oder wata tsaddyar apple detachble tablet me dan karan kyau da tsada it cost almost 1.4 million sabida limited edition ne. 


agidan kusan babu wanda baisha mamakin wann kyautar ba, ayayinda yara still thinks is very normal, anty safeera kuwa atake tasoma jin kamar kalamansa akan ayaana wnn karon yafara mata nauyi.. 


cos he alwys say things

agabansu kamar irin “Ayanah ba ‘ordinary’ bace. ko yace maata wai kowanne abu da ya fito daga wajen ayana yana so ya zama abin da zan iya alfahari da shi....har ta fara tunanin ko zai amshi ayanan ne gabaki daya ahannun su ammi karama da bappa zaidu da ibaad shi ya zame mata tamkr uba sai kuma tarasa da wanne kalma zata saka magann ya zama daidai

ahaka dai hartazo ta share abun aranta



tun wednesday uncle moh ya bata wann girgicaccen kyautar she spend much time da mujaheed da kulthum suna koya mata yadda ake amfani dashi, tsabar kyan tablet din yasa the more suna using the more har hanklin kulthum ya fara dawowa kai taji kmr itama tanason a siya mata.


 washe gari koda ta gaya ma uncle mohd itama ya siya mata irinna ayaanah da mamaki taga ya haura mata da fada sosai har yace mata wai tafara kishin yar uwarta ne kawai bawai ta rasa abun duniya agidan ba,


bai taɓa mata tsawa ba dan haka taje daki tay ta kuka wanda hakan still ya kara dagawa anty safeera hanklinta sosai. 


babu yadda anty safeera batay wajen tuhumarsa dalilin yima kulthum wann uban tsawar ba sai yace sam sam lefinta ne ai kishi da ayaanan take so ta koya shikuma bayason wnn halin. dakyar ta lallemesu duka tacewa ko bai saya mata ita zata siya mata tukun nan maganann yazo ya kare batare da kowa yaji ba. 


ranar friday bayan an dawo daga schl ayana tay wanka ta saka hadadden custard yellow atampa peplum nd strght skirt ne daya kama dirin jikinta tsaf tsaf, tsabar dikin ya  mata kyau haka yauma anty safeera ta musu light juma'a make up

suka zauna a falonta suna video da pictures


da yamma liss ta dawo sashen ammi karama unxpectldy ta same yaa maheer da wasu friend dinsa guda biyu sunzo


har kasa da ladabi ta gaishe su, tana Allah Allah ta tashi sabida tasan dolene da ibaad sukazo da batagansa anan ba tasan yana dakinsa, zucyr yarinta ya debata tay maza taje ta dauko result din taje room dinsa ta same yana waya, ta jira har ya gama snn ta gaishe shi ta miƙa masa ya gani she had all flat As yace 

tay kkri, snn ta masa tex da duk abubuwan datakeso zai siya mata anjima da dare amma sai gobe in sunzo wknds zai kawo matasu.


wani dadi taji tana ta murmushi just as  she was planning to  tell him uncle moh ya siya mata expensive tablet wayarta ya fara ringing...ibaad ya kure ta da ido, tana ganin sunan dake jiki taji tay wani irin freezing dan har ga Allah batasan yaushe tasa wnn sunan ma altho banda hjy mairo da da ruthy, da sultana da yaa ibaad sauran kusan kowa shiyay saving nasa dakansa. tarasa waye  yasaka mata.."BIG DADDY"kuma da capital letter...hannunta taji ya fara mata nauyi tana shirin daukawa ibaad ya fixge wayar calmly ya kalle screen din ya kyabe baki bai jira ko scnds daya ba ya saka hands free lokcin ji tay kmr kirjinta zai fashe 


muryan uncle mohd sukaji" hello, ayaanah dear. yaya kike. baima jira ta amsa ba yace

"karki manta i promised u an ice cream spree after those gifts bansan ko zaki tuna ba dear, so yanxu zan fita, amma bayan isha idan na dawo zamuje tare ko?yay murmushi, toh saiki gayawa amminki zamu fita anjima tare karsuzo suna nemanki.


ahnkli ayaanah ta sauke kanta kasa


uncle moh yaji shuru yafara hello hello, ibaad baice komi ba a hello na ukun ya katse wayar ya wani irin watsa mata mugayen kallo yanaji kamr zai hadiyeta cikin lunshe ido da budewa yace hmm..snn ya mata jefa da wayar ajikinta ransa a bace kusan dakyar ma ta cabe kafin ta dago tagansa yay sauri zai fita, da gudu ta tsaresa muryan ta na raw a rawa tace "yaa ibaad, pls wait...da wani irin bacin rai a fuskarsa ya juyo yace wait nd do "What??? numfashinta atake ya tsinke ta dan matsa baya da sanyin murya me cike da rauni tace "i dint save his number like this..


ransa a bace yace

 ...i dint ask u abt that.


shiru tay hawayenta masu tsananin zafi da tsoro me yawa suka fara zubowa kmr an kunnasu


dahar yay zuciya zai fita ya kara dawowa kanta ya tsaya yace "gifts? since when?? dakyar ta dago ta kalleshi tace "since..since ...tun ranar da aka fara bamu result ne fa ya bani wasu abubuwa..sai ranar, sai shekranjiya.. nd " i was about to tell you now...


nade hannunsa yay a kirji yace really okay, go on tell me...


wani irin rawa jikinta yafaray tsoro ya rike mata zuciya ahnkli ta share hawayenta kanta na kallon kasa tafara masa bayanin duk abunda uncle moh ya bata wanda bata gaya masa ba..


wani irin dan uban masifa yakeson yaga ya mata amma kukan datakey a mugun tsorace kuma araunace yasa bai iyayin masifar ba.


cikin hadiye tulin fushinsa a kirji yace "he bot u all those expnsive gifts kuma bai saya ma yaransa ba kuma kika karba? ke kadaice kika ci first agidan nan ko? kulthum is always coming first tunda take bata taba zuwa 2nd ko 4th ba meyasa bai bata tablet ba wato sai kece marar tarbiya ko zaki na karban abu anyhow ko toh ai yamiki kyau...give me your phone ryt now..


hawaye na kan sauka a idonta ta mika masa har tagama cire rai akai, ta dauka tafiya da abun sa zaiyi, duddubawa yay kirjinsa har yana bugawa da karfi dayaga baiga wani abu aciki ba ya shiga contact dinta ya ya canza sunan daga big dady, ya dawo mata dashi uncle muhammad. ya canza na mujaheed ba ya sa mata yaa mujaheed..


ya koma call logs dinta yaga daga sultana sai wata schl mate inta Aisha suke yawan waya, danna kan layin uncle moh yay ya saka a blocked. snn ya kashe wayar me gabaki daya da tsananin fushin da baisan yana dashi ba ya kalleta yace"...no calls today,..kije ynxun nan kiyi sallah kiy bacci. bazan ce miki kidena karban wayann abubwn awajensa ba aikinsan babu kyaune shiyasa kika ki gayamin tun farko but since ure hiding it ,continue. yana gama furta hakan ya damka mata wayar ahannunta ya fita cikin sauri..


#

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[30/11, 00:07] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫.

arewabooks@surayyahms.



as usual, extra-ordinary beautiful nd hilarious comments nd hypes from different angles.thank you my kind readers❤️uncle moh loves u more soyayyar karfi dayaji..duk wanda yaji haushi munsani, dan bamu cemai dear ko mun siya masa ice cream bane toh babu yadda aka iya damu. #team uncle moh #big zaddy khaalidina feeha abadan🤣🤝.


⏯️3️⃣3️⃣


kallon kofar da ibaad ya rufen tadingayi tana hawaye masu sanyi daga tsaye, wani irin sanyi jiiknta yay duk sai taji karamin zuciyarta ya bala'in rikicewa a lkci guda, zama tay a bakin gadonsa hawaye na zuba a idonta, ta rasa meke mata dadi, tajima anan cikin dakinsan bata fita ba har saida taji alamar sunfita sallan isha kafin nan itama ta fito


ammi karama dake tattara falon tabi ta da kallo ganin irin sanyin da jikinta yay da kalan jan zuciya datakey sai batace mata komi ba dan tasan bazai wuce case ne tsakaninta da ibaad ba, ayaaana bata gane komi ba har taje room dinsu

tay alwala tazo tay sallahn magrib, nan inda tay sallan tazauna tana karatun qur'ani har akayi isha'i ta tashi tayi


Tana cikin sallah ta kara jin surutunsu a falo da alaman sun dawo yaa maheer da abokasan da yaa ibaad din suna cin abinci they are all gisting about football anata hayya hayya akan E football nd  most of maheer's frend basu san wai ammi karama ba mamansa na asali bane dan all this time gani suke kamar ma duk duniya yafi sakewa a rayuwarsa da ita bai taba kai abokai gidansu can ba saboda yasan mahaifyrsa ammi babba ta bala'in tsanan ganin baqi.


ayaanah tana idar da sallanhta akan sallayan ta zauna tareda cigaba da nitsuwa tanamai rero karatun qur'ani haddanta take ta nanatawa dan ya zauna mata dakyau a kwkwalwa, ita dadi ma taji da suka kasance a falon basu tafi da wuri ba ita kanta saida ibaad yay mata fada tafara gane kamar abunda ya fadin gaskiya ne kawai it will only be better in zaina siya musu abu da yaransa atare amma ba yana wareta yana bata abubuwa masu shegen tsada ba.


daga falon kuwa irin wajajen 9:30pm abokan maheer har sun fara tunanin tafiya gida ibaad ya biyo ammi har cikin dakinta da maganan


duk dama ya nuna mata cewa baison wann abun gifts da outings da uncle moh yake son farayi sa ayaanah ammi bata wani bashi fuska akai sosai ba. 


tace masa ya kwantar da hanklinsa bazata taɓa barin ayaana ta fita agidan da dare ba, but der is nothing wrong with gifts..kawai saidai in ace uncle moh din yana daurewa ya musu da yaransa tare, sabida ko ayaanan ma ai bazatana jin dadi ana wareta ba, amma in sukace uncle moh kwata kwata yadena bawa ayaana abu zai dawo musu babban case agidan harma agaban hajiya tunda yarinyan nan dai respnsibtyn gidan sun ne gabaki daya...


ganin kamar ibaad bai wani qamsu ba tafara masa fada tace batason ya jawo mata abun magana kawai yasaka ido akan ayaana amma kar yace zaihana wani agidan muamala da ita bare ma uncle moh ai kawunsa ne, yana da yaran da suka girme ayaana dan haka bazai cutar da ita saidai ayi masa gyara kawai..


bada son ransa ba yabar maganan, sun fito daga kitchen dn kenan saiga mujaheed ya shigo, ya gaishe da ammi da ladabi, snn suka gaisa da ibaad kai tsaye yace ammi ayaana fah? tace"ohh yanzu dai na leka dakinsu naga tana kan haddanta a daki amma bari na duba maka hala ta gama tay bacci naga goma saura..


yace okay, dama babanmu ne yace inbatay bacci ba tazo ynxu..wani irin dauke wuta ibaad yay atake yace "kaje kace masa tay bacci. its late!

mujaheed ya juya atake ya kallesa, ganin inda ya mugun hade rai sai baice komi yace "okay, ammi sai goben inta farka sai ki gaya mata wai her phone is still off ..da kai ta amsa masa yana barin wajen ta juyo da kallon tuhuma ta kalle ibaad tace meye hakane kam rayyan?ayaana is awake

meyasa zakace masa haka


hade ransa yay bai amsa ba sai can ahnkli snn yace amma ammi ai dare yayi, its almost 10, yakamata ma ai kisa musu light out mana pls ammi

....10ck sai karsu bar dakinsu suje koina they are still kids ynxu ne suke bukar bacci...


tace rayyan i know what ur problem is, kuma nace maka zan masa magana. but this isnt a boarding house bazaka hana yaran nan fa walwala ba, amma tunda kace light out ne aishikenan, amma bazan dai hanata zuwa sashen safeera akan wann maganan ba,..gobe kuma zan samu muhammad din, i will talk to him abt the gifts, dan naga kmr kai baka yarda da kowa bane ko?? shiru yay baice komi ba, muryanta kasa kasa tace" kasan ya riga yasaka aransa cewa kana da raini shiyasa jinin ku bai hadu sosai ba tun kana karami, ni wallah gaskiya banason wani hayaniya ya shiga tsakanin ka dashi akan ayaanah, i dont have energy for all this family feuds rayyan pls ka rufamin asiri..i promise u ayaana will be fine innaga wani abu da zai cutar da ita i wll even solve it myself. zai magana cikin dakatar dashi tace " ya isa haka babana muje kawai gobe in kazo wknds zakaji komi. 


gyada mata kai yay a ladabce har suka shigo cikin sauran mutanen dake falon ammi duk tay sallama da abokan maheer within few minutes suka watse gidan ya dauka da wani irin shiru....



washe gari da safe ranar asabar ayaanah tana idar da sallah ta fito sanye da hijabin datay sallahn ajikinta ta wuce dakin ammi karama da sanyin ladabi ta tsuguna tace mata "ina kwana ammi" ammi dake zaune akan sallaya da mrmshi tace "lafiya kalau ayaana har antashi? how was ur night tace fine alhamdullh. "toh yanxu dai kije kiyi wanka jiya uncle dinku ya aiko a kiraki da dare ina dai ba wani barna kuka masa acan bako?ambaton hakan da ammi tay yasa ayaanah ta dago kai da mamaki tace"a'a..ban masa komi ba. sounding curious ahnkli ammi tace" jiya akace min kin kashe wayarki ne ma shiyasa bai sameki acan ba, ayaana, kifadamin gaskiya karkiji tsoron kowa kinga bana son dan yana baki kyauta yaje ya dawo miki wani abun tashin hankali da yan uwanki ko a gidan nan in akwai wani abu dake faruwa bansani ba ki gayamin kawai ynxu..


kan ayanaah na kallon kasa tace" Ammi babu komi, dama jiya ne kawai ya kira awaya kuma sai yake cewa wai na fito zai kaini wajen ice cream wai bayan ishai sai yaa ibaad yaji wayar sai yaji haushi ya kashe wayar gabaki daya..amma wallh ammi bani nace masa inason haka ba. nifa babu ruwana bance yana bani abu ba. 


ammi karama ta dan yi shiru tace "its okay, nasan ban taba gaya muku ba amma once is 6:ockpm henceforth babu fita agidan nan. duk wani ice cream ko wani ciye ciye da zakuyi duk ayishi da rana banda dare 10pm kuma naga kowa acikin dakinsa, snn dik abunda ya baki ki tabbata kin gaya mana sabida kar wata rana azo wani matsala yataso akanki ace bamu sani ba kinaji na ko?


ahnkli tace eh inaji ammi

tace good toh kije kiyi wanka, bansan meyasa yake nemanki ba amma in kin gama sai kije ki gaishesu saikiji ki dawo maza ynxun nan.. tace toh. ammi karama ta sallemeta ta fita, tana komawa dakinsu wankan safiyar tay ta canza kaya tasaka riga da skirt da mini hijab ta wata danlop sleeper akafarta ta fito


kai tsaye ta wuce sashen anty safeera bata tare da tasaka komi aranta face fargaba da rudewar tunani


Har ta isa Allah Allah take taga koda mujaheed ne amma ina wajen gabaki daya is silent kamar babu mutane aciki, sai taji tsoro ya kamata bazata iya zuwa dakinsa ita daya ba, kai tsaye ta wuce zataje kofar kulthum tana kama handle tun bata bude ba taji anyi gyaran murya ata bayanta adan tsorace ta juyo caraf suka hade da uncle moh wani irin murmushi taga ya mata daga can nesa yace ayaana dear karaso nan mana..ai jiya na aika a kiramin ke aka ce mi kinyi bacci.


kamar wacce kwai ya fashe mata ajiki ta sake kofar kulthum din ta dawo ta wajensan tana tafiya ahankli ahankli kamar bazatyi ba harta karaso kuwa bai daga idanunsa akanta ba 


yarinya datake jss 1 kam gani yake girmanta bazaiyi wuya ba within few years to come ne kawai zata zama ready  sexually, physically nd mentally, sann ya aureta ta zamo nashi, bama sai takai 18 ba tunda hatta ammii karama ma yasani sarai batakai 18 din da ake fada ba aka aurota agidan nan so ba akansa za'a fara auren karamar yarinya agidan ba.



daf da wajen hadadden coridorn sashensa inda yake tsayen ta tsuguna cikin ladabi da fargaba tace ina kwana uncle.. da wani irin murya yace haba tashi mana dear karki rusuna min haka, wayarki ya baci ne ko? jiya na kira ki sai naji kamar bakiji na har na dawo gidan kuma ina kira naji akashe..


girgiza masa kanta tay ahnkli tace "a'a bai baci ba, ina karatu ne,.. da safe ne ammi tace min wai ya mujaheed yazo yace kana kirana shine nazo... ganin yadda tay saurin saukaka mgnn nervously yasa yaji arnsa kmr ko tsoronsa takeji yasa bataso ta sake jiki dashi


..cikin kame kansa yace okay, dama ice cream dinki ne nakawo miki toh muje dakina nabaki yana fridge saiki karba ki koma kije kiyi baccin ki dan naga kamr bacin bai sake ki ba..


batace masa komi ba kanta na kallon kasa yana wucewa gaba ta tsaya cak daga bakin kofar dakin har ya shiga ciki ciki ya dauko katon ice cream bags guda uku manya daga cikin fridge dinsa daga waje ya daga ido ya kalleta yace"dont stand dere my dear karaso ciki mana ki karbi abunki.


..tunkafin ta amsa ya wani taho da sauri yajawo hannunta ciki gani datay yana kkrin kmr zai mannata da jikinsa danya shafata yasa tay saurin fixge jikintan anashi muryan ta na rawa rawa sosai tace" uhmm uncle ammi tace na dawo yanxun nan, zan iya sha dani da su kulthum dasu safiya ko


ganin kmr she is starting to get scared of him sai yay maza ya dawo cikin senses dinsa cikin dedeta nitsuwarsa da normal voice nasa yace "toh toh badamuwa kije to kusha tare mana ai naki ne nidai nacika miki alkwari ne kurum.. 


kanta na kallon kasa tace nagode uncle..


kansa adan daure da yanayin ta yace its okay dear dama shikenan u can leave.. yana gama furta hakan ta gyada masa kai da mugun sauri ta fice a dakin tanamai jin tsananin fargaba.


shidakansa kuma daya zauna abakin gadonsa ya sauke ajiyan zuciya yafarajin kmr abunda yakeyin is bit off nd shameful. duk dama babban abokinsa alhaj Amir ne yake yawan bashi wnn tabbataciyar shawarar na akan cewa ya dage akan ayanah, kar ya zuba ido yay shiru yace saita girma ne zai sako kai, tun yanxu ne da ayaanan bata dawayo zai jawota jikinsa sosai, ya dinga bata gifts, snnan yana kyautata mata akai akai sabida kowani zuciya yana son me kyautata masa, snn ya dinga spending time da ita sosai yana dan janta da harmless physical touch, uwa uba yana spoiiling inta da ababen kwadayi sosai, Alhaj ameer ya tabbatar masa cewa inhar yayi hakan, tamkar yana trainer zuciyar ayaana ne da sonshi kuma ahaka ta girma, natural love ne zai ginu aranta akansa, snn koda wata matsala zai taso agaba da matarsa safeera by then sunyi shakuwa da ayaana da bazata taɓa iya rabuwa dashi ba.


shawarar sosai tay making sense amma sai gashi nan yafara aiwatar abun yana masa wani irin gashi kmr ayaana tafara jin tsoronsa.. doguwar tunani yayi akan haka kafin ya mike ya shiga wajen wanka.


dakin kulthum ayaana ta shiga ta sameta a nannade acikin bargo kanta namata ciwo da alaman period dinta ya fara sako kai, da mmki ta dago ta kalle ayaana ganin jikinta na rawa rawa har ta zauna kusa da ita suka gaisa tace "sis what happen meye wann kikazo dashi a leda...ayanaa ta tattaro nitsuwarta dakyar tace "abbanku ne ya siya mana abu dukanmu dani dake safiya shine kawai na kawo ki aje mana..ni kinga dama yaa ibaad yace min karna sha abu me sanyi da sasassfe sai kawai kusha abunku. mikewa kulthum tay tace toh mugani.. da sauri taga ayaana ta mika mata, ta karba ta bude tace wow..toh thanks, kinsan wani abu sis? mama na tace zata siya min irin tablet dinki gobe, cikin gwalo ido ayaana tace alhamdullh dama ji nake kamar in baki nawa kyauta

..suka fara dariya.."kinsan ai baba yahanako? kawai ki rike abunki..in nima mama ta saya min sai muna koya abu aciki..

ayanah ta gyada kai tana murna...hira kadan sukayi me sanyi sann ta kama hanyarta ta dawo sashen ammi karama batare da ice cream din ba, koda ammi ta tuhumeta batun kiran bata boye mata ta gaya mata komi dayace mata saidai bata san ya zata fadi abun a sigar da zaisaka ammi taga abun kamar yana damunta ba,...


...haka akay taron wknd din kowa ya hallara saidai sam hanklin ayana baiya jikinta saboda daure mata fuska dataga ibaad yay ranar sosai wanda yasa ta dadajin ta damu atake kuma tsoron karban abun hannun uncle moh din yafara kama zuciyarta, duk da ammi karama taxo ta samesa a mutunce ta tuhumesa aka batun ware sauran yaran da gifts, saidai dake ya raina age dinta yana ganin kamr ko shinan ya girmeta, dama can da irin rainin kanin mijin nan aransa kuma gani yake kmr ba asalin age dinta su hajy mairo suke fada a fili ba, kuma he is very very sure yama girmeta sai bai wani bata kwakwkarn amsa ba ya shanshantar yace ai shirmen yara ne dan haka akyalesa zaiyi duk abunda yay niyya ma ayaana


tun tadaga haka tasan ba fahimtar ta zai yi ba,  sosai ta rike alkwari ma ibaad she make sure ta saka ido, duk sanda ya kira ayaana gefe sai ta kuma tambaye ayaana ya sukayi.


bai kuma fasa kawo abubuwa time to time yana bata ita daya ba, har yasa ayaana tafara  fitowa fili ta nuna masa  alaman bataso, ya zamana kullum kota kashe wayarta kota ki zuwa sashen nasu gabaki daya musmn in aikowa yay taje.



bayan faruwan hakan da kamar sati uku komi ya fara lafawa su ayana suka koma 2nd term insu na jss1 ibaad kuma yana kkrin shiga 2nd smtr na level two dinsa a medicine.


wann satin ne suka samo wani babban cigaba a gidan, inda da wasa da wasa mahaifin anty safeera dake matsayin tsohon ministe da sukaje wani confernce ya saka hannu awani takarda har aka budewa uncle mohammed wani babbn intl connection ya samu wata contract da wata construction firm na larabawa, ita kuma hajiy mairo mai tuwo babban shagonta ya samu state award na fastest growing  traditional restaurant a kano haka akay taro  yan kasuwa kala kala suka kawo investmnt akan zasu adada wajen ana so ajonashi ayi prof. catering school na koyarda abincin zamani dana gargajiya...


satin gabaki daya ayaana sai taji sakat sabida hanklin uncle moh ya koma ga shirye shiryensa na tafiya kasar dubai zaije yay kamr 1 month kafin ya dawo.ranar alhamis da safe wajajen karfe 10.00am saura ibaad ne kawai baije schl ranar ba sbd abubuwa da suka masa yawa, kuma hrga Allah yafi gane advanced private club lesson dinsu akan normal schl lectures dinsu ynxu sai gabaki daya yau ya dauki karamin hutu da zai harhada ppr works da assigment dinsa na club dan sunyi nisa sosai a field, ga vsiting doctors turawa wasu larabawan egypt din nan duk ana turowa suxo sumusu practicals da lectures on a short visit, school lectures dinsan gabaki daya kmr masa revision ne. past exams result dinsa was incredibly awesome shine wide margin topper a ajinsu sede abun baya darashi sam kuma haryau bai yi aboki ko abokiya a ajin ba, shide bazaka taɓa gane masa ba dan ko mahaifyrsa baiya son nuna mata result in yaci saidai suji ana yabon kkrin dansun a bakin professor ciroma dake abokin bappa zaidu ne.


ibaad will alwys keep his successes private nd his problems even more quieter, asalinsa baison yawan samun attention ko yabon kowa da kowa ko kadan kawai abunda ke gabansa yakeyi most time.



tun daya dawo daga sallan fajr yake kan calculations da su drawings da sauran lissafe lisafen chem. compounds acikin dakin sa. yana gamawa kenan ya shiga ya fito  wayarsa ya fara kara bappa zaidu ya kirasa tareda umartansa kawai yay akan tunda yana nan yaje fmily house ya dauko ma hjya mairo me tuwo wani envelope a dakin ta yakai mata shago ynxun nan. tun da ya gama wayar daukar lokcinsa yay me kyau ya shirya kansa kamr wanda zaije wani waje mai muhimmaci.


he wore a complte set of gentle men set data masa mayen kyau, this clean white short-sleeve polo me aji da wata Light grey chinos, paired with Clean white sneakers and a simple brown leather wrist watch hade da Fresh haircut dinsa dat look brushed neatly. snn ya shafa hadadden turarensa na naxos. ya dauki wallet dinsa da wayarsa it took him 30min snn ya fita ya dauko baqar lexus din bappa zaidu dake parke a tsakiyar gidan ya taho family house dashi.


gidan was quiet yara duk sunje schll ammi karama taje aikinta ya rage anty safeera ne kawai ta aje komi nata danta taya mijinta shiryawa


da safe ne but they have this wonderful intimate sex kafin ta shiryasa tsaf ta rakosa har waje kagan shakuwa da irin soyayyarsu bakata taɓa tsammanin uncle moh zai daga ido ya kalle wata ya mace a duniyar nan ba.


suna fitowa gaban motarsa sai ga ibaad harya dauko file din a hannunsa zai wuce yana sauri anty safeera ta kwala masa kira ya dawo ta wajen sun ya gaishesu...


uncle moh dama ya jima yanaji aransa ibaad baida ladabi sosai atake ya fasa shiga nasa motar yace tunda ibaad fita zaiyi da babban mota kawai shi yakaisa aiport din ya saukesa. duk yadda ibaad yay dan ya doje haka yaki sam yace he cant drive  nd make calls kawai suje ya bawa hajiy aikan ya kaisa aiport. ibaad ya hakura baice komi ba ya amshi jakarsan yasaka masa a booth har yaje ya zauna a driver seat uncle mohd bai gama tsotsar bakin matarsa ba duk dama yasan ibaad yana iya kallonsu ta madubin mota. saida ya gama duk iskancinsa da zaiyi sann ya zo ya bude motar ya wani hakimce a owners coner yana zama ya fara zabga kiraye kiraye yana hira da wasu aboknsa yana kyakywtawa da dariya kamr wani drivernsa ya daukosa har suka isa shagon hajy mairon ibaad baice masa komi ba,yay parking ya sauka yakai mata aika yana dawo wai sai a sann uncle moh ya sauka shima yaje, ibaad  try his best not to react dan yasan uncle moh is alwys trying to provock him to anger, dan sam sam baya treating maheer haka wani bin ma kamr frnd yake daukar maheer amma shi sam jininsu bai gama haduwa ba.


after like 10 min of waiting ya dawo yana shiga motar ya cigaba da wayarsa banda tadin sirrikan aurensu dana yan matansu awaje babu abunda yakey da abokansa..


wht seem like a few minutes jouney bcome endless for ibaad sabida surutun banza da uncle moh yake yi a baya, 11:30am suka kawo aiport, haka yaki sam ya rike troly ko ya bayar a dauka mai a moving vehcle yace sam sai ibaad ya sauko ya bishi dashi ciki, suna tafiya ciki yanakan wayarsa kamar bazai gama ba. he is busy bragging na yadda zai kara samun kudi dat will make him do what ever the hell he want in his life. ibaad yay baya baya dashi yabarsa yay gaba shi yana tahowa daga karshe, tun suna cikin harabar arivals idonsa ya sauka akan wata dattijuwar mata wacce daga ganin shigarta kasa msulmace she is walking alone nd slow, da tsadadden hand woven gucci bag a hannunta bana kananan masu kudi ba,saidai abun da ya fara dauke masa hankali da yanayinta shine wannan shortness of breath din daya hango atattare da ita


she was heading for her luggage nd exit he tot to himself she will be fine tunda arival ne, sai ya dauke idonsa har suka iso inda uncle moh zai tsaya ahnkli ya aje masa bags dinsa yakama hanyarsa ya tafi baiko cemai sai anjima ba.


Da sauri ya shiga mota dan ya koma gida, dan da yamma can yana so yaje shi gym, maheer barely have time now sabida karatunsa yay zafi sosai. yana kama hanya dede gate din fita daga cikin aiport wata katuwar jeep ta tsare masa gabansa tana tuki ahankli ita bata matsa gefe ba kuma bata bashi space din wucewa har suka hau kan hanya yana horn amma mai motar bai bashi hanya ko ya matsa ba, tun yana iya dabara yana kkrin over taking har yaji ransa ya fara baci da matukin motar. sundau mintina suna tafiya a slow har saida suka danyi nisa kafin hanya yay fadi ya samu ya kara wuta ya wuco gaba caraf kuwa idonsa ya sauka akan wann matar da dazu ya gani, she was driving very very slowly nd shaky kamr wata me blurry vision can kuma yaga tafara breathing fast like she can’t catch air tadanyi Resting dayn hannunta akan chest dinta while trying to breathe, 


kasa wuceta yay ya sauke windonsa yafara mata horn saida yay kamar sau biyar kafin yaga dakyar ta juyo ta kallesa yana shirin mata alaman ta tsaya yaga da sauri ta sauka akan shoulder ta tsaya da motar dake shirin kwacewa a hannunta a mugun girkice take nishi kmr wacce heart attack yke neman kamata atake.


agaggauce yay parking ya sauƙa ya iso gaban motar ya tsaya yafara kwankwasa mata windon yanacewa "excuse

me ma'am are u okay?...tana numfashi sama sama ta bude kofa suna hade ido tace dan samari ...pls.. help me," help me karna mutu na bar yaro na pls help me..kafin yace wani abu tafara kkrin dago wayarta zata bashi tana jan nmfashinta dakyar tana cewa" i will call my doctor..pls help me ta..lk ..to him.. kusan duk wani symptom na heart attack atake ya fara bayyana ajikinta all this cold sweat, visible Chest discomfort ga wani irin shortness of breath mai dauke da Chest pressure sai yaga kmr jaw dinta yana mata ciwo shima.


his insticnt was almost driving him crazy  bai san sanda ya bude motar ba, yana budewa yay turning off ignition ya bar kofar motartan a bude, ya maida seat dinta baya, ya cire mata seat belt dan ta zama she is lying down flat godiyan Allah ma dayaga she is still uncoucious hannun ta na rawa tana mika mai wayar yafara magana da doctorn ta, docton yace masa maza maza kafin tafara loosing counsiouness ya kawota asibitinsu na rahama international private hospital yanxu he wll send emergncyy on the way too,. 


ibaad yana daga wayar a kunne ya ga doc har ya turo location...ya koma car dinsa da sauri saurii ya kulle, snn ya dawo ya samu matar is still very much councious nd breathing, saidai the more tanayi the more yana raguwa the more suna bata lkci the more lamarin yana kara lalacewa baiyi wata wata ba ya shiga motar yafara janta yana tukin yana mata magana just to keep her awake ita kuma sai rokonsa take akan yay hqri ko sunje asbitin kar ya  kyaleta har sai yaronta yazo, snn duk tsiya kar ya bari wani ya shiga inda aka kaita in ba mutumin sunan shi jamal ba, har suka karyo kwanan shiga gari bai gama gane nufinta ba, wanda tun basu karasa asibitin ba motar paramedics na asibitin suka tardasu a take atake aka dauketa aka kwantar da ita flat aka bata nitroglycerin bcos she is still very much coucious snn aka sa mata oxygen mask

within few minute suka iso rahma intenational hospital aka wuce ciki da ita aka fara bata taimakon gaggawa.


yana asibitin ya tura tex ma mujaheed ya masa kwatance inda spare key yake dan ya dauka yaje ya dauko masa car

daya bari a hanya dazu.


saida har yaga mujaheed ya amsa shi da okay snn yaji hanklinsa ya kwanta kamr yadda matar ta rokesa haka nan ya zauna for almost 2hrs har aka kira azhr ya samu wani security yay tipping insa snn ya ce masa kar yabar kowa ya shiga ciki inba wani me suna jamal ba.



after few minute ibaad ya idar da sallah ya dawo kenan ya hadu da securityn da ya bashi gadi awaje suna hade ido yace masa ai matar ta farka tana nemansa haryace mata yaje sallah so zai iya shiga ciki..


cikin sauke ajiyan zuciya tare da yin hamdala dan dama a dame yake ya koma gida ya doshi dakin.


tun a kofar yake jin sautin magangnu kmr ba ita daya bace aciki, saida ya dan kwankwasa kofar snn yay sallama kusan atare suka amsa shi ya shigo ciki cikin nitsuwa, inda atake suka hade ido da wani hadadden cute guy dat look handsome nd exctly brazillian sabida skin colour da dark red lips dinsa da wani irin baqin suma.


ya saka suit baki me dan karan tsada wanda a ido kawai dao bazaka ce kusan age mate na ibaad bane, sabida sense of responsiblty da maturity dake lullube a fuskar yaro...kallom juna sukayi na dakikan lkci kafin murmushin matan ya katsesu tace dan samari shigo mana ya ka tsaya daga kofa


ibaad baice komi ba ya karaso daf da ita yace "how ur feeling maam ya jiki...da hawaye a idonta tace nagode Allah "Alhamdullh, Allah ya maka albarka. nagode yaro na. you are a god sent you saved my life kumaka rike min alkwari.. what is your name? yace "Ibaad" ..tace "masha Allah ibaad, i am hajiya maryam moriki. mutane sun fi kiran da lady Diana. this is my only son jamal moriki.


atake jamal din ya mika ma ibaad hannu har ynxu jikin sa yana rawa rawa muryansa kamr nawanda zaiy kuka yace"..thanks men. thanks for saving my mother's life it means alot.. pls how can we repair you can ask for anything

...karamin scof ne ya kufce ma ibaad yace "no. pls..i just did what i tot is ryt.. Allah ya bata lafiya. gayen ya gyada kai with so much gratitude in his eyes yace "Ameen"..ibaad  ya kalle matan da karamin murmushi yace can i call u lady?tay dariya kadan tace ye.. yace" okay lady, i think i will leave you two now..Allah ya baki lfya


card dinta ta ciro ta mika masa da hawaye a idonta tace "pls dont say no my dear..call me anytime aikoda baka buktr komi awajena zamu iya gaisawa bcos ure a very kind person.. bai musa mata ya karbi card in ya kalli jamal sukay sallama suka dinga masa godiya sosai.


yana ficewa a dakin ko titi baikai ba yaji ana kwala masa kira ata bayansa yana juyowa sa mamaki yaga jamal ne ke biyosa yana riskansa, ibaad yace hey, i hope everything is okay? jamal yana haki yace "yeah yeah..na manta ne ban karbi contact dinka. ibaad yace is der really need for that..

..jamal ya kalli cikin kwayar idonsa yace u did not only save my mum frm dying u waited for her nd protected her...pls let me be ur pal or wat eva, by the way i am new in nigeria, taki jirana na nw gama meeting tazo ita daya, jirgi na kuma yazo 1nd half hour bfr hers..aiko gaisawa zamuna yi maybe we cud even hang out sumtimes.. 


cikin kyabe baki ibaad yace

"alryt, gayen ne ya fara ciro wayarsa wata golden plated iphone tana shining wanda saida ibaad ya mata kallo biyu, irin customise phones din nan ne sa ake saka musu highly encrypted security codes, ibaad ya saka masa numbers atake yay saving ya masa flashing ,ibaad yay saving numbarsa snn suka rabu.



Bayan faruwar haka sa kamar wata guda bai kara ji daga wajen su jamal ba, kuma shima bai sake nemansu ba kowa yafada harkan rayuwarsa


uncle moh ya dawo nigeria  daga dubai gabaki daya harkalla ya balain bude masa kudade da budi tazo masa atakota ina


wani irin sabuwar salo yazo dashi mai ban mamaki, giyar kudin daya karayin na balain debarsa, yanxu ya dawo kusan kowani karshen sati saiya bawa ayaanah kudin kashewa ko tana so ko bataso, harhada tactics dinsa yakeyi da hajiya mairo me tuwo dan kawai ayaana tana karban abun duniya a hannunsa, lamarin da gabaki daya ya jawo mata rashin nitsuwa sabida yadda ibaad yake yawan fushi da komi dake faruwa...


dakyar uncle moh yazo ya fara yana hadawa da sauran yaran a kyautatwarsa, but still sai yay ma ayaana wani abu na daban, ko ya bata nata kyautar yafi na kowa ko ya saya mata nata kalar daban.


banda ammi karama data hana sam ayana tana fita daga zarar mgrib yay ko side in anty safeeran bata kyaleta taje da dare yanxu.


kafin ayana suyi exam na shiga jss 2, wani irin silent war ne ya dinga gudana tsakanin uncle moh da mutanen gidan musammn ma ibaad 


dan uncle moh nuna musu yakey shi babba ne, kuma yasan me yakeyi, wani bai isa ya dakatar masa ba, nd he is always manipulating anty safeera with big big gift, ya canza mata cars and soo much money koda kuwa sunyi magana akan wasu abubuwan dayake bawa ayana sai yace sam ba haka bane sai kaga kuma ta yarda dashi, ga hajiya mairo ita kam bata gane komi ita duk daukawa tay danta muhammadu yana da tausayine kawai sosai


kan kace wani abu ayanah tana da exotic watches, abaya na dubai, da expensive bags da kuma expensive jewerie kala kala daya siya mata duk wai tsarabar dubai duk sanda yaje koda na kwana uku ne sai ya kawo tsaraba na ayana kuma me shegen tsada yake kawowa.

 


silent war dake tashi atsakanin ibaad da uncle moh din yasaka ayaana a wutar tsakiya,  ibaad ya dawo yana mata tsauri, akan tsafta, bacci, ko ana kallo zaizo ya koreta acikin yan uwanta ya hade rai yace taje bacci, dole tay karatu hadda zai takurata wani bin tanayi bakinta na bari. duk sai ya zamo bata samun sauki face wajen mujaheed.


har karya takeyi ma uncle moh dan karta karbe abun hannunsa dan ta samu sakin fuska awajen ibaad koda rana dayane amma sam sam yaki shidakansa saiyaje ya bawa hajy mairo yace ai abu kazan nan na ayaanah ne a ajiye mata ita kuma da zuciya daya take daukar abun haka zata kira ayana tasata karba dan dolenta babu yadda ta iya msmn ma da yanzu yafara hadawa da yaransa yana siya musu duk dama baikai wanda yake bawa ayaanah a idonsu, da kuma bayan idonsu ba.


abubuwan dake faruwa sunyi affecting din ibaad sosai,

musmn daya gane cewa wann ƙarin daukaka da sabon budin da uncle moh ya samu na kudaden larabawa shine ya saka izgilinsa ya karu sosai yake yin abunda yagadama

,ynxu duk gidan babu wanda ya isa ya hanasa yay abunda yaga dama koda sau nawa ammi karama zata masa magana baya daukar maganan ta da mutunci a idonsa bare kuma matarsa da tunda ya samu karin daukakar yake balain manipulating inta da soyayya yana baza mata bakin aljihunsa busines dinta tana wasa da kudinsa aciki duk ya rudeta ta zama koda taga abu marar kyau bata wani daukar abun serious kuma daga yay mata bayani kadan sai ta shashantar. hakan sosai ya kashe ma ammi karama gwiwa, ita kadanta tasan cewa ayaana kwata kwata batason komi dayake faruwa tskaninta da uncle moh, amma ganin ya rufe ma matarsa da yaransan ido duk basu korafi tarasa ya zatay, gashi alkwari tay bazata kyale ibaad ya tunkare case din ba, dan tasan duk randa tabarsa yay magana akan ayaaana bala'in da uncle mohd zai kunce agidan basu san karshensa ba...sam sam bataso ibaad yay fada da uncle dinsa musmn akan ayaana gani take kamr zaiy affcting abubuwa dayawa agidan.


ibaad ya shiga wani yanayi wanda har yakany amusing din zainab arifa, wani bi, she enjoys the bully da takurin  dayake ma ayaana,dan duk sanda taga ayaana tana takure ko tana kuka sanadiyar masifar ibaad bakaramin dadi hakan yake mata aranta ba.


within 2 months it became so clear that uncle moh yana opressing din lamarin ne da kudi, dan yasan ata nan ne kawai ibaad ko wani agidan bazai iya taka mai burki ba. 


business din da ibaad yake cewa saiya gama 2nd  semester  dinsa ne zaiyi sai yaji yafara shiga ransa cos he feel he had to do sumting to get ayaanah out of that complicated situation da uncle moh yake kkrin cusata aciki



 yana cikin wann nazarin suna daf da fara shirin exam  zainab arifah ma tafara nata makircin, inta zo gidan taga ayaanah atakure tana karatu ita daya ko an hanata fita sashen su anty safera sai tadinga cewa ai ayaana tana bata tausayi, haka zata bita har daki tana pity petting inta, wann wkdn din ana zuwa tazo ta same ibaad da kinibibi tafara ce masa yadda take takura ma rayuwar ayaana ynxu tana bata tausayi dan haka tana so ya bata permission zasu je shopping hala ta samo mata farinciki acan" he was so pissed wai har da ce masa tausayi yarinyar take bata..yace atleast she is grounded. zainab tace but she is just so vulberable i kind of pitying her.  yace you dont pity urself da everything u want weda good or bad u must get it? tace excuse me how is dat a bad thing?


yace  mata abar tausayi ai itace wanda aka traineta batasan darajar kanta ba. maganan ya mata zafi sosai ranar da fushi ta koma gida. ranar gabaki daya ransa a mugun bace yake, ayaana tana lura dahshi yau ko abinci baici ba...wani tunani tay, can da yamma bayan ishai kafin su wuce gida, taje kitchen ta debo abincin ta kawo masa har dakinsa, wanda dakyar da wahala ya kulata. haquri ta dinga bashi ita kanta bata san asali meyasa take bashi hakurin ba. dayaga tay masa kuka sosai kuma yasan hanklinta sam ba akwance yake kwana biyun nan ba sai ya hakura ya sauko sun jima a dakin nasa yana mata nasiha cewa kwata kwata tadena amshar wani abu awajen wani namiji koda shine yake bata abu excessively haka kartana karba sabida one day wnnan abun zai zamo mata trap ko wani abun gori. har ransa baiso da ya gaya mata hakan a fili ba duba da age inta, amma ji yake kamr uncle moh ba tsakani da Allah yake mata wasu abubuwan ba. kuma yana amfani ne da matsayinsa akansu yake yin abunda yaga dama dan yasan yana da bakin da zai iya magana hajiya mairo ta amince dashi kai tsaye.


kusan ma akan uncle moh ya mata fada amma da wayo kuma sosai ta fahimce shi duk da ma bai ambace suna ba. since that day datay shagwaba ta rarrashe yayanta suka dawo dede ya dena fushi, a satin gabaki daya sai ta fara wani irin silent rashin kunya, daga zaran uncle moh ya saya mata abu kai tsaye sai tace masa  atambaye yaa ibaad in yanaso ta karba...


tunda tafara masa haka na daya na biyu dayaga abun nata dagaske ne tuni yaji ya fara mugun hatsala, ranar jumaa da sassafe ana fita a sallan fajr ya kada jallabiyarsa ya wuce sashen hjy mairo da zimman kai karar ibaad game da wann magana da ayaanah take furtawa....

# atattauna monday in sha Allah zamu tashi da zafin tsiya.....💋❤️

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[01/12, 11:42] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️3️⃣4️⃣

Tun gari bai gama wani washewa ba uncle moh ya karaso cikin sashen hajiya mairo, lkcin ita kadaine azaune acikin sashntan tamike sawun kafafunta akan wata lallausar sallaya, tafin kafar nan ya gama jin bakin lalle asalin na gagajiya sai sheqi yake yi,cikin sashen banda qamshin turaren sandal balls babu abunda ke tashi koina ya dau tsafta da qamshi


lazimi take bugawa da katon carbi a hannunta tana Allah Allah tagama tajawo wann hadadden herbal tea dake tashin kayan qamshi gabanta da surkuwnta fatima ta kawo mata a flask yanxun nan, tana cikin wann yanayin taji an doka mata sallama..


"salama alaikum


jin muryan autarta ne yasa maza ta gyara zama tun bai karaso ba tace"muhammadu??


sai da har ya shigo da baqin jallarbiyrsa snn yace naam hajiya nan take ya zube kasa ya zauna da ladabi yace "hjy an tashi lafiya? tanata kallon murdadn fuskansa tace "kalau, mohammadu yaya kake, yaya kuma yan jikokina? tun be amsa ba cikin kyabe baki tace jiya anan nan yarka kulthum tazo ta shanye min madara na kuma nace mata bata isa ba wallah saita biyani, wai haka kuka rainesu ne in zasu sha conflaks sai sun zuba kusan rabin kwankwanin madara a kofi? yara basu san maleji ba, basu gaida me maleji, hm yyl haka kawai ana zaman kalau bazaku turo yaranku suna kassara ni bazai saku ba


..cikin karkadai tare da katseta ahnkli yace "wai har kayan madarar taki ya kare ne mama? tace o,o nifa bance maka yakare ba wnn tsakanina da jikokina ne kasan dai fada baya karewa amma dai ya kamata ku koyawa yarku kulthum maleji wani shegen namijin ne ynxu zataje gidansa tana masa irin wann barnan madaran baikoroto ba hmmm.. 


yaja ajiyan zuciya cike da ji dakansa yace koma yaya ne zuwa anjima zansaka akara stocking miki kayan shayi tunda ke da jikokin naki kike sha, mama in kulthum bata sha madara yanxu sai yaushe zata sha? ..kyabe bakinta tay tace toh toh shikenan, ai yarka ce banawa ba. kudai dake barnan kudi dama baya muku wuya..ohhh ni mairo Allah na tuba yaushe ma aka kawo wnn din baifi sati biyu ba inbanda shegen kwadayin yara inama nake da lkcin shan wayanann abubuwa,.. hmm toh ya aikin naka kuma ince dai komi lafya? 


fuskarsa ba asake sosai ba yace lafya kalau hajiya...bari na zuba miki shayin ki kisha dan wata magana nake tafe da shi kuma sauri nake zanje na shirya naje aiki .


cikin kwalo ido game da dafe kirji tace tohhhh..ince dai ba wani aure zaka jajibo mana ba muhammadu..ku fa maza ba dama kuga matayenku sunyi bulbul suna walwala agida caraf saiku kawo batun mata kishiya..yaushe ma safeeran ta gama haifa maka yaya da har zaka fara batun dankara mata kishiya kai jama'a..


jawo flask din yay yanakan zuba mata shayin a cup a nitse yace "hjy bance miki fa aure zanyi ba dan Allah karki kaini gaba..


tace amma ai zakayin ko? nifa uwarka ce duk naga take taken ka wallah..


dan karamin murmushi yay yace ehh tohh idan zaku bani mata agidan nan ba..


dan dariya tay tace "mata agidan nan? kaji wani maganan banza yo safiya yar cikinka zaka aura,.. ko kuma waye kagani ya dace dakai agidan nan, zaidu dai ya rigaka furtamin sunan fatima..kai da Allah gayamin meke tafe dakai kawai bana son shashanci.


sauke ajiyan zuciya yay ya kalleta with serious face snn yace "hajiya bawani abun tashin hankalii bane..kawai dai yadda abubuwa suke tafiya agidan nan ne basu min dadi, kar nay magana ace na tsane wani yaro wani ina fifita shi Dan haka gaskiya ni zan gaya miki abunda ake min agidan nan bana jin dadinsa dan na lura kamr yaran nan gabaki daya basa ganin girmana kuma iyayensu mata ne ke daure musu gindi...inba haka ba harnine za'a dinga min gadara agidan nan,wai ace na bada yarinyarnn kyautar abu sai taki karba tace wai sai wani wawan yaro agidan nan ya bata izini akan shi waye ne? zaman aure ne a tsakaninsu ko kuma shine ubanta, ni sam bana so na ja wata magana, amma tun da yarinyar nan dai jikarki ne, kece zakiyi masa magana dan duk gidan nan wallh babu wanda zai iya dukana acikin yaran nan, dan haka banaso akaini bango na harzuka na ci uban yaro acikinsu babu wanda yafi karfin duka wajena.


aje kofin shayi tay cikin

katsesa tace kai kai kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun haba haba haba muhammadu..wai kai da waye haka kake wann masifa da boye boye, banason mita kmr matar mamaci kawai fito fili, waye ya rainaka? waye kuma tantirin marar kunyar acikin yaran nan da suka hada meeting sukace zasu bugeka suna hauka ne da zasuce maka zasu casaka? wai waye yay maganan nan gaya min nikaina saina ci ubansa


cikin harde ransa yace hajiya aikinsan waye ne basai nakama suna ba amma inhar kinaso na kama sunan shikenan akan ibaad da ayaanah nake magana.


rike baki tay cikin sassauto da murya  tace tohh shikuma rayyanun meyay maka muhammadu Allah sarki naga bayama shiga harkan ka meye hadinsa dakai kuma


adan hatsale uncle moh yace" a'a..hajiya dakata min, dan Allah karki wani fara bin bayansa da wann irin pretence din dan ko ke nan kinsan anjima ana nuna min ban isa da yarinyar da kika kawota gidan nan ba, yakaiga maman safiya saitana tsare ni dawasu irin maganganun banza kamar tamaidani yaro bansan menakeyi ba dan ina bawa ayaana kyautuka ya zama ana kallona kamar mutumin banza, duk sabida ke nake yin hakuri na shareta sann ina bata girmanta kasncewarta ex matar yayana amma bafa tsoronta nakeji,  bana son raini, bazan kuma lamunci raini musmmn daga wajen marar kunyar Ɗanta dake neman shiga harkata akan yarinyar nan ba..wai tukunma ma ni a'ansa ne? gaskiya hajiya kija masa burki, ya kyale yarinyar nan tunda shi ba ubanta bane kuma ba aurene tsakanin su ba..kar ya kara hanata karban abu awajena idan ba haka ba wallah agaban yarinyar saina ci masa mutuncin da bzai kara iya daga ido ya kalleta ba bare ni...


cikin hade fuska tace  kai subhanallah toh ya isa haka

..shi rayyanun ne yace ma ayaana tadena karban abu awajenka baki da baki  ya gaya maka haka?


yace "aa baifada min baki da baki ba,amma ai kullum nabata abu sai tacemin wai inje intambayesa kenan shine yahanata karba, nifa wallah munafurci ne banaso...a fito fili mana, inkema bakisone in saka hannuna akan yarinya ne akigaya min saina san anware ni, saina bar muku yarku dama ai gwaninta ni bai karbeni ba, wani abun da akeyi agidan nan na rainin wayo ai ba isa ayi ma yaa zaidu ko yaa zayyanu ba saini da aka raina ma wayo


juyowa tay ta kallesa tace kai muhammadu wallah kafiye fadin rai abu kadan saika fara hada kanka da yayunka shi zayyanu ma ina ruwansa shidaya tsine ma uwarsa? zaidu kuma kasan baya mita girma ya kamashi kaine dai kake halinku na yan auta haryanxu..


...shikenan kaje, naji korafinka bari shi rayyanun yazo ni da shi zamuyi magana kaima sai akai zuciya nesa. banason ayi abun kunya yadda rayyanu yake zuwa gidan koyan dambe (gym) yana dada buduwa yana kato kowani rana, ai da kuyi abun kunya dashi gara duka kawai ahakura da rainon abarmin yarinya kawai zan maidata ma zaidu sai shiya riketa agidan sa, dan wallh haka kawai bazaka kama dambe da yaran cikinka ba..Allah na tuba wallah dukanka rayyanu zaiyi kaine dai baka kallesa da kyau ba  toh wallh ahirrrrr dinku nahana wnn magana, wanda yake zuwa gidan dambe kam bazaimin asarar haihuwa ba gara shi uwarsa bata tsufa ba koyau tay aure zata iya sake haihuwa.


da dan bacin rai a fuskan uncle moh yace "Allah ya kiyaye ya dake ni, ohh ashe dama tsoron sa kikeji kenan ko hajiya? zatay masa magana a zafafe yace toh wallh ba'a isa dai akan dan wnn maganan a daga yarinyar nan agidan nan ba..kawai ki masa magana inba wai tsoronsa kikeji ba..ko so kike ki gwada ma duniya maganan da ake fada game da ke akan uwarsa fatima ya tabbata gaskiya, dama ance kwata kwata baki kaunar lefin fatima kusan kowa ya san da haka

..toh wallah bazaiyu ba, akan shi waye...?


cikin daga mai hannu tace "toh naji. yanxun nan zan kirashi zaizo zan masa magana kuma koma miyene zakaji ayi hakuri akai zuciya nesa.


daga haka suka karkare maganan bayan ya dan zauna da ita na wani lkci ya ciro cheque na kudi wanda ya shirya tun jiya ya bata yace toh ga goron jumaa hajiya"..daukar cheque din tay tagani kudi ne meyawa tana murna tafara saka mai Albarka daga nan ya tashi yakoma sashensa domin ya karya ya shirya ya fita.


Tun bayan haka hajiya bata sake dago wnn maganan ba, har saida taje shago ta zauna kafin ta dinga kiran ibaad awaya yanata ringing bai dauka ba karshenta basu hadu ba sai har washe gari ranan asabar, kowa ya taho, su ibaad ne farko farkon zuwa gaisheta aka gaisa lafiya ana zama kenan tafara dago maganan acikin mutane. ga bappa zaidu, gasu maheer da mujaheed da su anty safeera, kananan yaran ne kawai basu nan


kamar maganan arxiki tafara nasiha cewa tana alfahari da kokarin kowanne acikinsu, sai kuma ta murda zancen ta dawo cewa ita bata dauke ma wani kyautatawa ko kulawa da jikarta ayaanah ba, dan haka karda hakan ya zamo silar da wani zaiy gadara ma wani. tay dogon wa'azi akan kyautatawa..tunda ta fara maganan ibaad kallonta kawai yake da mamaki..


dan yagama lura da cikin gidan gabaki daya, bama hajy mairo ba, kusan gani suke kamar tsaurin da yake ma yaran akan tarbiya da karatu kawai takurawa ne da mugunta. kowa ya tofa awajen shi baice komi ba


hajiya tace wai a saukake ma jikokinta su more zama agidan adena tsorata su bakowani dispcline bane akeyi da zafi da tsauri, bataso taji ana yawan duka, ko ana hanasu hutu, tunda duk suna kokari snn duk abu na kyautatawa da nuna gata indai agidan nan za'a basu kyauta ba nawaje ba kar ana hanasu tunda gidan nan duk ba cutar dasu za'a yi ba.

 

yanajin yadda uncle moh yay maza ya haura kan maganan harcewa yake su ibaad din ma ai tarbiya da nitsuwa bai gama ishensu ba dan haka basuyi girman da suma zasu takura ma na kasa dasu ba...


kusan kowa ya tofa albarkacin bakinsa atakaice dai hjiya mairo da uncle moh suka justifying komi which sunhow make sense to odas, sabida kowa gani yake toh meye lefin da ana bada ayaana ko wata yarinya kyautuka agidan nan, ibaad yay shiru ransa ya gama bashi cewa uncle moh ne yakai kararsa wajen hajya sai bai tanka kowa ba har aka sallamesu dukansu uku suka fita..


maheer yay kmr zai fahimce abun amma kuma sam ibaad yaki ya bashi fuska suyi maganan, mujaheed ne ma yaso shima yay korafi da dabiar baban nasa, saidai sanadiyar maganan nan sai shima ya dada zulmuwa yafara ganin abun as normal tunda dai gidane kuma babu cutarwa acikin kyautatawa.


kin cewa komi da ibaad yay yasaka maganan yay sanyi kowa ya cigaba da abunda ke gabansa har yamma yay, da zasu wuce gida hajy mairo ta kirasa uwar dakinta tafara masa magana privtly shikadai akan maganan rayuwar ayaanah


she din't even ask him what is hapening kai tsaye tay assuming cewa murdadden halinsa yasa yake so lallai ayaanah tadena karban abu daga wajen yayanta...sai cewa take inda muhammad ba dan cikina bane da sai nace kareta kakeyi, toh yaushe kuma alheri ya zama mugunta? ynxu inba shi ba waye agidan nan yake saya mata kayan gayu. wallh har tausayi muhammadu yake bani ka dubafa yadda yake nuna ma ayaana so da gata, harma fiye da yayan cikinsa, wnn ma ai abun alfahari ne garemu, kuma haka Allah yake son mutum yaso dan wani kamr yadda zaiso nasa toh ahir dinka rayyanu da nemansa da fitina nide bana son tsugudidi da tashin hankli...kaji na gaya maka kenan


tunda tafara maganan latsa wayarsa yakeyi idonsa na kallon wayar har ta gama baice mata uffan ba kuma bai dago ya kalleta ba. har saida

tay shiru ya miƙe tsaye ahnkli cikin danne abun aransa yace "toh, hajiya kiyi hakuri..inkin gama ni zan wuce gida kaina na min ciwo!


yanayinta wani iri tana kallon daurarren fuskarsa tace ahhh dakata min, wai yanaga kana wani daure fuska kana amsa ni daddaya rayyanu? wato kai badama amaka mgna kenan sai kay fushi? toh bari inazuwa ka jira ni anan..tun be amsa ba ta fita fuuu bada jimawa ba saigata nan ta dawo da ammi karama tana cewa hajy lafya? harsaida ta kawo ta ciki sann tace"fatima ga danki nan, wai daga namasa magana akan abunda yakey marar kyau shiknan fa ya fara kumbura.

....fisabililllah ynx meye laifin muhammadu dan yana nuna ma ayaana gata... shin ita ba mutum bace da zaina daure fuskansa yana hanawa?


cikin lumshe ido da budewa while stilll maintaining his temper yace "Hajiya cewa fa nayi kiyi hakuri ai banmiki wani musu ba, tunda naji maganarki shikenan..kuma na baki haquri kusan akaro na biyu kenan saidai kuma inkinaso shima naje na bashi hakurin ne toh..


hawaye tafara saukewa cikin raki tace fatuma kinjishi ko? 


ahkli ammi tace hajiya dan Allah kiyi hakuri..tunda yace yaji in sha Allah koma miyene ya wuce.


tace aah ah fatima kin haife rayyanu amma ashe kekam ma bakisan ainihin halinsa ba, ai ni gwammaci yamini masifa akan dayamin shiru, hakafa anan ya barni inata magana baice uffan ba wai sai cemin yay inyi hakuri kamar wani na zalunceshi? yo meye laifina anan dan nagaya masa gaskiya, yarinyar nan fa ba uba ne da ita agidan nan ba..meye ne aciki idan muhammdu yana bata gata na uba da zaina hanawa ni gaskiya bangane ma rayyanu mutum sai kace kafurin farko?


cikin lallashi ammi karama tace yi hakuri hajiya.  maganan ya wuce haka i am sure ya ji. kuma in sha Allah hakan bazai kara faruwa ba. dama fa yana maganan ne sabida kar abun yay yawa tazo ta lalace ko

kuma yan uwanta da ba amusu irinnata abun yay affecting dinsu, aike kinsan yadda yara suke tunani amma bawai ya hana bane Allah ya huce zuciyarki mama


tsabar ransa ya baci baisan sanda idonsa yay jaaa awajen ba..yarasa ma me zaice caraf kuwa sai wayarsa yafara ringing baiko daga yaga waye bane muryansa kasa kasa yace ammi zan wuce inaga maheer ne yake kirana suna jirana zamu wuce gida dare yayi.


gyada masa kai tay da tausayinsa a idonta cikin taushin murya tace "toh, inka isa gidan saika kirani..har zai wuce tace rayyan toh kay ma hajy saida safe mana..fuskrsa a daure yace"...hajiya sai da safe' baijira ta amsa ba agaggauce yabar sashen yanajin ransa na wani irin tafasa...


ringing biyu wayarsa yay ya dauke bai duba ba har saida ya shiga mota ya same maheer yana dubawa kuwa da mamaki yaga kiran jamal ne baibi kirar ba dan kusan tafiyar kurmaye sukayi a motar sabida in ransa na bace bai fiye son yin wata magana..


har suka kai gida kowa ya nufi dakinsa ransa na dagule dan gabaki daya abunda ya faru ayau yay masa zafi sosai saidai bai bata lkcinsa wajen yanke hukunci koyin wani tunani meyawa akai ba

kayan jikinsa yacire kai tsaye ya shiga bathrum ya kunna cold shower ruwan sanyi yana sauka a duka ilahirin jikinsa yajima ahaka kafin yaji ya dawo cikin hayyacinsa bacin ran yay sanyi, wrpping towel yay around his waist, snn yay brush a agaban sink, yana gamawa yay alwala yadawo room dinsa yay yan shafe shafensa ya shirya kansa cikin wata clean short marar nauyi bai saka riga ajikinsa ba ya dau ruwan gora ya zauna daga bakin gadon sa yanasha cikin lumshe ido da budewa yaji duk abubuwan da su hajiyan suke fada nadawo masa kansa, at some point yafara jin ya gaji dakomi dake faruwa, he even started to blame himself for caring, sai kuma ya tuna ita ayaana babu ruwanta, she is just a naive little girl yasan dai duk wann maganan banzan bazai wuce uncle moh bane ya tada shi, yay tunani duniyan nan na yadda zai kyale musu ita yayi abunda ke gabansa



saidai wani bangaren ransa kuma gabaki daya yaqi sam ya amince masa da batun fita sha'anin ayaana msmn inya tuna content din dake cikin wasiqar mahaifyarta, ji yake kmr idan yayi sake rayuwar ayaana ya lalace tmkar yaci amanar mamanta ne data rokesa with all the emotion i  her heart cewa yasaka mata ido sosai akan rayuwar yarta ayaanah sabida mahaifinta juma ya riga yamusu mmunan baki bataso yarta tazo binni ta lalace. idanunsa a lumshe yana cikin lisafin yadda zaiyi ya warware wasu abubuwan, wayarsa ya kara katseta da kara, da sauri ya bude lumashen idonsa duk ya dauka ko jamal din ne yana dagawa saikuma yaga mahaifyarsa ce


cikin sauke ajiyan zcya me sanyi yadauka tun beyi magana ba da sanyin murya tace rayyan nima fushin kayi dani ko?dazu nace kana isa gida ka kirana shine har yanxu shiru..


dan karamin numfashi ya saki ahnlki yace "kiy hakuri ammi wanka nay yanzun nan nake shirin innagama saina kiraki


tace its okay..kun isa lafya? yace alhamdullh kai tsaye tace "rayyan, pls dont take all this to heart. i knw it pains alot to be misunderstood kuma dama abunda nake ta guje maka kenan shiyasa bana son ka dauki zafi akan lamarin ayaanah..dan Allah nide karkace zakay fushi da ita da kuma sauran yaran nan. sumtimes hajy tana magana ne in favour of her son's emotions, kasan dai ita uwace, dama bazataga kusukuren danta haka kawai ba. amma tunda sunce maka kabari toh kwata kwata kadena shiga harkansa.


cikin katseta yace ammi nifa bance ma yarinyar nan tay masa komi ba. kawai nasiha na mata akan yawan karban abubuwan masu tsada da takeyi a hannunsa, .anyways, nide maganan nan ya kare

kuma ba fushi nayi ba, nide in ina takura ma yaranku kuyi haquri i will amend my ways.


dan shiru tay muryanta wani iri tace rayyan pls nide karka yanke wani danyen hukunci dat will make you to abandon ur sisters, inba dan kai ba bansan yazanyi da safiya ba. i truly truly understand you. dont blame urself for anything kaji?? kawai dai shi kawun ka muhammad din ne nakeso kafita a harkansa....


a nitse yace toh ammi..kema ki kwantar da hanklinki i am okay..wani kira yana shigowa wayata can we call it a night?


tace okay ayi bacci lafya. karamin murmushi yay mata yace u too maa.


tana katse wayar ya ga jamal ne cikin sauri ya dauka dan karya yanke da calm voice dinsa yay sallama, suka gaisa..

yace kwana biyu..nan da nan jamal yafara bashi haquri yace urgent meeting ya maidani U.S i cudnt call you men i am so sory..ibaad yace babi komi nima i was pretty much occupied, toh yajikin mum dinka, da fara'a jamal yace alhamdullah ta warware sosai

..hira kadan sukayi jamal ya fara sugesting ko dazasu hadu acikin sati su gaisa tunda shima ya dawo kanon yanzu kuma zaiyi kamar hutun wata biyu yanan nan


ranar wednesday da yamma suka yanke zasu hadu kafin suka karkare kowa yay bacci


washe gari sunday tun bayan sallahn fajr ibaad yakashe wayarsa gabaki daya sassafen suka fita gym shida maheer basu dawo ba sai wajajen 10pm sukay wanka suka ci abinci dats packed with healthy protein, maheer ya wuce wajen harkan secret investment ventures dinsa da already yanzu ya farayin karfi dan ya jima da fara abunsa a boye.


wani irin baccin huta gajiya ibaad yayi duk jikinsa saida ya samu nitsuwa, but with what is happening arnd him yaga kamr shima is high time kawai yay puting business tots insa into action tunda yana da kudin nan, ga uban gadon filaye da millions of naira da babansa ya bar masa me yawa dake babansa surgeon ne amma kuma yay running Big rice farming business ya tara silent arxikin nan saidai shi humble and simple life yay baya show off kwata kwata bakamar na prof ba  dama kuma maheer yasha matsa masa akan yafara kafa source of income insa da wuri basai karatun sa ya rikesa sosai ba. he tot abt it for while, sai kuma ya rasa ta ina zaifara sabida baida wasu kwakkwaran circle na abokai inba frends circle na maheer da mujaheed ba, besides, mujaheed  is a sport nd tech guy kuma shine karaminsu a mazan gidan sai gabaki daya baifiye son shigewa jikinsu sosai ba sabida field of interest dinsu yay hannun riga in bawai suna gida duka atare ba.


Da wannan tunanin aransa yake zama har ranar  wednssday yay suka hadu da jamal moriki a wani waje da shikansa bai taba sanin akwai irin wajen a kano ba.



THE BLACK MINARET


inside wani huge walled villa acikin nasarawa GRA blacl minaret yana dauke da wata matte-black metal gate with the emblem of a small eight-point star. Only members na wajen sukasan address snn ba a iya shiga saidai wani dan wajen ya kawoka ciki.


special waje ne da boyayyun Business magnates, young heirs of wealthy families,Oil & real estate families, crown princes, nd Private bankers da

many Diaspora billionaires suke zuwa when they’re in kano town.


Jamal ne dakansa ya fita waje ya jawo ibaad ciki, just few members wanda kowa abunda ke gabansa yakeyi ne awajen


waje is god damn private nd breathtaking, All-black marble floors Gold trims, silent lounge with dim amber lighting ga lumtsa lumtsan Leather chairs, da private conference room da kuma babban library with only business and philosophy books sai cocktail bar da suke cema Mirage Counter...


duk wayewar ibaad saida yajishi kamar ba a kano state yake ba, sai kuma ya tuna taken garin wai koda me kazo an fika nd na today he don confirm dat statement.


wani hali guda daya jamal moriki yake dashi wanda shine yake balain tafiya da ra'ayin ibaad wato humbleness da bala'in saukin kai ga iwa uba aji da yin magana acikin nitsuwa bada jiji dakai ba.


jamal ba irin gayun nan bane wanda arxiki da daukakrsu ke rufe musu ido su raina wani ko suyi girman kai ko show off, kyakkwan tarbiya ce mai rai da lafya ajikin yaron he is calm, jovial and classy..


royal blue suit yasa me balain tsada amma bamai hayaniyan design ba,tunda ibaad yazo suka zauna su biyu a mirage counter suna shan mocktail, anan yafara introducing kansa properly ma ibaad


jamal moriki yaro ne ga wani shahasharen me kudi da ya rasu kwanan nan, bada jimawa ba. he is the only son of his mother lady diana, after suffering in court da kawunsa akan arxikin babansa daya rasu shine harya samu aka 

damka masa ya hau kai at this young age dan da wata biyu kawai yagirme ibaad a shekaru


saidai yanayin yadda yake maganansa da tulin kamiya da kuma nitsuwa tareda ilimi u cant just deny his early maturity aura.


a yale uversity dake U.S yake kan karatunsa, while still tryng to run his fathers business conglomerate in the U.S and Dubai. maman sa ne kawai take saka masa ido akan komi shiyasa baya son ya rasata dake tana da boyayyen ciwon zuciya wanda a sanadiyar mutuwar babansa ne akasan ma tana dashi

....sunxo kano ne sabida anan ne shima aka haifesa asali ma anan ya fara tasowa a family house din maman sa gidan mahaifinsa ne kawai yake abuja.


wasa wasa suka sha hira dan ibaad  baiwani sha wahalan bayyana masa kansa ba dan yana ambatar sunan familynsu na almansur jamal ya cankosu  yace masa ai tun suna yara sukasan kawunsa prof zayyanu sabida ta hannun prof din marigayi baban jamal alhaj moriki yake samun wasu intnl contract da kudadensa ta sauki.


it became so easy for them to trust each oda at first manly date dinsu,..daga haka jamal yay requesting ko zasu dawo abokai sabida baisan kowa a kano ba kuma bazai iya trusting cousins na jikinsa ba duba da suna nuna maitarsu akan arzikin da aka daurasa akai yanxu..



ibaad baiwani bashi fuska a farko sosai ba, harsaida suka dan dau lokaci suna yawan hanging out tare suna hira suna dada fahimtr juna within 3 weeks ibaad ya fara sakan jiki dashi musm ma da har cikin family saida jamal ya kaisa, nd jinin mum din jamal din bakaramin haduwa yay da na ibaad ba, wnn sanyin aji da yadda yake kame kansa yasa ta jima da ganewa tabbas ba karamin tarbiya aka bashi ba hala bazai cutar da danta ba. 


dama shi sabo ga maza

bawani abu ne mai daukar lokaci ba nez musmmn irin nasu na yaran masu shi, they are always talking about bigger things, educations, cool adventures, da abunda duniya ke ciki..busines jamal yake karantawa. most time zaizo gidan bappa zaidu da yamma ya jira ibaad a masallaci, ko ibaad ya same sa acikin black magnet a regular hangout dinsu....

#DONT BE SHY FINE GEH OYA POST UR COMENT SABIDA DA DARE A SAMU BONUS



idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[01/12, 20:47] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: 💫💫💫BONUS


Dagata fannin family house kuwa tun bayan abunda ya faru ibaad bai sake kuwa shiga harkan uncle moh ba duk dama ayan satikan nan yayita nemansa da magana musmn yadda yake wasu abubuwan with full authority, yanzu kam ma baya neman permission,..

ko ayaana bata son abu zai siyo ya raba, snn yabata me kyan ciki ya bama sauran yaran yan dede, safiya ta hada harda haushin hakan ta dawo kamr kishiya ga ayaana ya zamo sam basa magana, bata kaunar kuma taga ayaana ta  shigo daki musmn da wani abun duniya da bata dashi. 


tun kowa yanasa ido yaga ko ibaad zai dauke kansa akan yaran gidan yahau fushi ya dena kula kowa sai suka ga ya kwashe tashar kowa ya watsar, normal yake rayuwansa kamr yadda ya saba, saidai haryau bai kara budan baki yace ma ayaana komi akan gifts dinta da uncle mohd ba,. zaizo zasu gaisa zai duba karatunta he will even challenge her to do more as usual abu dai inya shafi uncle moh ne kawai baya tsoma musu baki aciki wanda

tun ana  nemansa da magana a gidan har kowa ya gaji ya kyalesa..


adan kankanin lokaci kusan duka schedules na rayuwarsa ya fara canzawa sanadiyar tarayayyarsa da jamal dan jamal bai cika 6 weeks a kano ba suka yi wani irin shakuwa da ibaad, they hang out alot to private clubs,sport, libarary, gym shikuma maheer gabaki daya karatunsa da business dinsa yanxu yana balain hanasa yawo dasu sosai duk dama ibaad yay introducing dinsu ga juna. sati biyu kacal ya rage ma jamal ya koma aiki da kuma schl dinsa a united state, hakanan yadinga matsa ma ibaad akan suje su abuja atare suyi sati guda su dawo, 


sabida yawan zama da juna da sukeyi tare kowa yafara fahimtar capacityn brain in kowa nd he despreately want ibaad to meet his oda childhood friends sabida akwai abu mai muhimmaci dayake so ya saka ibaad din aciki wanda baison ya masa na sauri ko kai tsaye face harsai ibaad yaje yaga yanayin abokan nasa acan.


ibaad bai wani saba da wann rayuwar ba saida ya tattauna da maheer, da mamaki yaga maheer ya kara zugashi akan yaje, sabida ya gama lura da cewa jamal moriki yana da strong business netwoking  yana mutuwar so ibaad yaje ya leko musu yagan wani irine..


abun bai wani shige ran ibaad ba haka maheer yajashi na dole sukaje yaje ya gaya ma bappa zaidu cewa zaijeshi abuja da abokinsa jamal, akan ya rokesa suje family house dinsa suyi sati zasu dawo


...dake bappa zaidu has been obseving jamal most times inyazo gidan a masallaci suke yawan zama tare da su sai kawai ya kyalesa yace masa yaje amma kar ya wuce sati guda din daya roka.. few days bayan bappa ya bashi go ahead din yaje family house yay sallama da mahaifyarsa

wajajen 10am na safe suka bi jirgi suka iso garin abuja tun daga airpot kusan convoy na security uku ne sukazo aka kaisu wani katon mansion na mahaifin jamal a maitama cikin abuja


da kadan gidan yafi na bappa zaidu a girma da tsayin gatanga, daga su sai uban securities sai masu aiki kala kala, cikin awani luxurious suite mai manyan dakuna aka sauke ibaad snn aka musu tarba mai kyau, bayan sunci abinci sun huta jamal ya nunna ma ibaad cikin gidan nasu.


yace masa nan ne asalin gidan mahaifinsa, insunxxo abujan ne kawai suke sauka anan musmn in suna da wani meeting ko hidima. asalin family house dinsu kenan saidai basu fiye zama aciki ba tunda mahaifinsa ya rasu.


they understand each odas pain easily sabida duk yara ne da suka rasa ubanninsu tun suna kananan shekaru, bayan sun gama zagawa ya bawa ibaad key din wata fancy sport car shima ya dauke nashi suka sha wankansu suka fara zaga garin abuja, kusan kwana biyu sukayi agarin suna zallan yawo hanklinsu akwance saidai ibaad yay waya agida nan kam masu aiki ne ke musu komi.

 

a kwana na ukun ne da yamma sosai bayan isha'i jamal ya gaya masa cewa ai childhood abokansan gabaki dayansu sun hallaro yanaso suje suyi spending darensu nayau atare dasu.


ibaad baisaka komi aransa, he dress simple classy and casual kamr yadda ya saba, at around 9pm sai gasu agaban wata irin hadaddiyar under ground club na manya


suna shiga jamal ya bada membership card dinsa aka bude musu kofa suka nufi wani waje inda babu wani hayaniyan manyan mutane, acan sama regular joint dinsu inda babu music babu komi sai expnsive phones, laptops da tab, shisha pots wasu gayu ne su biyunsu a zaune all dressed up in their respective sophiscated designer regal wears.


kowannen cikin su bazakamai kallo daya kaji qamshin talauci ko kauyanci ajikinsa ba snn kowa da irin kyan da Allah ya zuba masa


kujera na farko by his ryt was graced by a guy named prince hassan zarko, the youngest son of zazzau emirates shine dan auta agidan su na sarautar zazzau, shi irin chocolate skin colour dinnnan ne amma akwai shi da wani irin sanyin kyau da fararen manyan idanu masu mugun daukar hankali, yasaka white royal heard scarf me tsada akansa untop his designer casuals, kalar royal scarf dinsa daya yake da booth din dake kafarsa wanda shikansa booth din ma abun kallo ne.


daga gefensa wani caramel skin tone guy ne, kana kallonsa kaga pure hausa fulani guy, baida fara'a sosai siffarsa is sumhow huge nd he is a bit matured looking, sunansa farhan bello murya, he is the only son of a private bank owner in sydney. sai kuma jamal moriki da ibaad almansur da suka shigo cikinsu yanxu.


daga nesa zaka ce bakaramin girman kai yaran zasuyi ba amma suna kallon jamal dukan su suka mike tsaye farhan ya fara kawo hannu suka tafa yace "hey men, suna gaisawa ya mika ma ibaad hannu suka  gaisa, jamal da prince hassan suka rungume juna suna dariya yace "so good to be back bro..."yana daga ido yace "ibaad ryt?..a nitse ibaad yace "yes..mika masa hannu yay suka gaisa yace welcome to the crew nd u guys shud have a seat muma bamu jima da shigowa ba...suna zama farhan ya kira wata waiter ta kawo musu ababen sha masu sanyi...


kai tsaye jamal yakara musu re-introducing ibaad as his only trusted frnd in kano state

wanda sunriga sunji labarin sa 

sai basu wani cika sa da questions ba, dake ba group bane na kananan magana, atake suka fara vibing da juna, sosai farhan ya zama addicted to shisha sauran kuma basa son shan koda hayakin dayake fitarwa.


sun jima a wann waje getting to knw each oda amma dake irin halin su suga kamar ibaad din yake dashii 100% snn suka yanke hukucin spending kwana biyar din daya rage musu a abujan atare. what ibaad tot it will be soo boring nd distant sai yaga kamar ma abokan jamal din sunfishi ilmi da saukin hali, komi acikin aji da ilmi sukeyi, musmn prince hassan daya kasance da jinin sarauta ajikinsu, bambancinsu da ibaad shine iyayensu sun bala'in sake musu suna duk wani abunda suka ga dama da kudi, they can sleep wherever they want, suna da security shikuma ibaad kudin gidansu is a classic quite wealth, a al'adr gidan su  basu nuna kai basu show off da arzrki amma duk inda sukaje ansan sunan gidansu da babban gnrational wealth legacy na ahalin al-amansur. 


cikin kwana biyar din nan sunyi yawo A abuja kamar wanda aka korosu agida, they have alot of fun su hudun, replays of introductions da kuma sharing comon intrest, suka exchangin contact da ibaad suna cika sati kuwa da yamma ibaad da jamal moriki suka dawo kano shikuma farhan ya tafi kasar waje, prince hasan dinne kawai ya wuce gida..koda ibaad ya dawo gida maheer ne kawai yake sanin abunda yake ciki da new circle of friends dinsa, wani bin koda yaso ya ja baya dasu saikaga maheer ya hanashi sam coa he believe one ryt network of connection is better than many years of hardwork. da ikon Allah kuwa yaga su farhan din ne ma suke yawan nemansa a waya duk da basa kusa amma ana gaisawa sosai..one week bayan sun dawo daga Abujan ibaad ya raka jamal airpot ya koma united states shima ya zamana time to time haka suna yawan communicating su hudun, within few weeks suka bude group chat su jima suna hira on diffrent topics. suna kuma sharing videos na moment na rayuwarsu, ibaad was busy quietly observing them har ya gane cewa gayu ne masu tarbiya da hankali da they don’t dress loud. they don’t speak unnecessarily, no girls, no party talks, infact their presence alone is status.


rayuwa ya kasance musu haka har sukayi kusan watanni shida suna tare da juna, lkcij ayaana tagama jss 2 zata fara jss 3 inta, time to time abokan ibaad suke dawowa ahadu a kano ko abuja, they spend time together family visits, private football games,snookers, boys dinner. book clubs, da library ayi musu, ayi dariya, adawo daidai.. mutum dayane acikin su yake busa hayaki farhan wanda abune dayabi jikinsa sosai sabida zaman kasar waje dayakey all his life sabida abokaine ma kadai yake zuwa nigerian badon komi ba.


tun da suka aminta halayyar da junansu kowa ya fara qamsuwa da juna prince hassan da jamal suka fara kawo joint busines proposal wanda daga grup chat hirar ya fara haryazama regular topic idan sun hadu..


ibaad yana samun hutun da zai kaisa ga shiga aji uku lkcin kuma maheer zaije ajinsa na karshe, maganan kulla alakar busines din ibaad da abokansa ya fara yin zafi, A  garin abuja suka hada secret meeting a daya daga cikin exotic villa na mahaifin prince hassan, su hudunsu suka hallara for good 3 days suna abu daya,..


they are all intelligent,wealthy, and serious tareda wannan dan uban damuwar dake cikin ran ibaad na ganin yadda uncle moh'd kullum yake amfani da girmansa da kuma kudinsa yana baza mulki agidansu musmn akan ayaanah.


abun yana masa ciwon da har baisan ya zai iya misaltawa ba dan sosai dabiar uncle moha din ya fara jawo ma ayaana kananan baqin jini, ko anty safeera yanxu bata wani fiye janta ajiki kamar da can ba,kotazo sashen sai dai ta tsaya awajen kulthum ko suyi extra lesson dinsu a falo tare da mujaheed, shikuma the more yanaganin ayanahn tana murjewa tana wankuwa sai yafara jin feeling na soyayya aransa na ginuwa akanta sosai... 


daga koyar da karatun da suke yawan yi ya fara koya mata poems na soyayya, sai suna tsaka da karatu sai yace a warwashe brain, amma harga Allah all those poems dayake rubuta mata are meant to express what he feels for her bacin ita batama san meyakeyi ba.


kulthum ne kawai comfort zone dinta a gidan, kawancen su da kulthum har yaso yafi nata da sultana duk dama suna yawan haduwa da sultana kullum a school da islamiya duk da bambamcin ajinsu they became real frend nd sisters, shakuwarta da kulthum ya samu nasaba ne da tana balain son jin labarin zainab arifah abaki kulthum din dan taga zainab arifahn sunfi kusa da anty safeerah


kwana biyu dataga ibaad baya fiye zama dasu agidan sosai ta fara saka kishinsa meyawa  aranta, tace ko zainab arifahn ne ke dauke masa hankali yake kin zuwa gida dake ko zaije abuja zaizo ya duba lafyarta ya bata kudin kashewa amma daga bappa zaidu sai maheer sai mamansa suke sanin baya gari..abubuwan sosai suke damun ayaana acikin ranta bana kadan ba, kuma tanata tsammanine ko zainab arifah ce ke son rabata da inuwar yayanta..



tsabar freedom da yaran gidan suka samu yanxu har zuwa shagon hajy mairo sukeyi da yamma haka acikin sati suna haduwa da ruthy har sai can dare snn ake dawowa dasu...


tamkar da wasa ibaad da abokansa suka fara harhada tattaunawa akan long term busines empire da zasu gina dan su dada karfafa alaqarsu..


Duk da sunyi meeting na kwana uku a abuja, it still took them series of calls, facetime, group chats, spies, routings, and research kafin suka hada kansu a tsakiya.


suka bawa business empire din suna _Q4 Sovereign Group Ltd_ each of them had agree to fund 25% of finance kafin suka nitsu suka fidda structure, aka yi dividing roles base on power da kowannen su yake dashi..


prince hassan ne Executive Chairman sabida Diplomatic access, royal network da kuma social intelligence na gidan su


sai suka bada farhan bello murya Managing Director, dan he is a very social guy shine musu kamar clients Charmer, negotiator,deal-maker..snn aka bawa jamal moriki COO wato chief operation office sabida he is already running his dad's companies yana da Practical brains, buzz logistics, da kuma execution plans, ibaad kuma aka bashi CFO chief Strategy Director nd also he wll be the  risk manager, nd mastermind behind all finances ups nd downs...


abune ya dauke su tsawon watanni suna shiryawa wanda ayayin da suke hakan fahimtar juna da shakuwa yake dada shigewa jikinsu sosai, har suka dawo aminai tamkar tsinsiya madaudrnsu daya, just like the name of thier company the Quadrant four sovering group just like a strong brotherhood pillar.


Duk da dukiya da kuma tarin daurin gindi da royal and poltical connection din da iyayensu suke dashi abubuwa bai musu sauki ba, musmn ma ibaad dayayi komin sa aboye, wnnn  karon maheer ne kawai ya san da komi shine ma yake taimaka masa da private legal adviser nasa, cos each of them must provide one for registrations nd all the legal documentions. step by step sukay drafting duka wasu core documents, sukayi kyc da aml, sukacire duk wani board of gorvenance, da strictt rules

suka bari a cewa business dinsu is a quiet jouney, No public announcements kuma

All investments dinsu is via Q4 subsidiaries only, da sauransu, 


bayan sun gama haka saida aka koma school akay one full semester snn suka dawo nn suka sake zama suka fito da duka operational moves dinsu lokcin kudin kowa ya shigo hannu 25million each suka hada each making it100million to avoid risk suka tsaya akan abu uku wanda zasu fara kawo musu riba within 3-4 months  kuma kasuwanci ne bamai hayaniyar da za'a jisu ba.suka zuba 40% a Agro-Supply & Farm Input Distribution, sai kuma 35% a Cold-Chain Beef Processing & Packaging amma shi acan kasar Waje suka kai inda akwai stable demand da electricity, sai Land Banking irin Buy & Hold na filaye innan, suka zuba masa 25% shima to enable them venture  into real estate in the future.


dukansu suna karatunsu na University kowa yasan bazai samu lokci ba dan haka suka using duk wani vector power na iyayensu sukay hiring competent operators da managers sanda har suka dage suka daure sukayita securing komi nasu legally kafin nan kowa cikinsu ya samu cikakken nitsuwa..



ata fannin ayaanah kuwa tin baya data cika shekaru 12 tafara ganin al'adanta tana kuma samun kulawar tsafta da tarbiya sosai awajen ammi karama saidai halayyar uncle mohd na jin kanshi haryau bai canza ba amma takanji da sauki duk ranar da ibaad ya bata lkcinsa, ya kulata, dan kwata kwata Girma baizo mata da sauki ba sabida tun a ynxu 

Komi nata ya soma bayyana kmar su budewar kugunta da kuma kirgen dangi daya soma nunawa boro boro akan kirjinta


..,bayan uban kyaun fuskanta dayake dada fitowa shape din jikinta shima sosai yake kokarin bayyana kansa sosai.


A makranta haka maza da malamai zalamammu suke takura wanda sam sam bata kulawa da suitadai abinda yakaitakawai shitakeyi inya dameta ne saita gayawa Ammi karama komi dominta ta bata shawara akan yadda zatayi.


sauki data zo tafara samu da aiki yafara ma uncle moh yawa akasar waje, yanxu yana yawan ficewa kasar wajem saidai duk ya dawo ya dinga takura mata da kiraye kiraye kenan kullum yanaso tazo ta sameshi suyita hira.



AFTER 2YEARS...


...

rayuwa yaja yau da kullum ta wuce wasa, abubuwa dayawa sun faru amma mafi akasari na cigaba ne da kuma kawo gabar da kusan rabi daga cikin yaran gidan zasu shiga wani sabuwar qarni na rayuwa..


just few month ago maheer ya kammala law dinsa already yana jirar yay passing bar dinsa ne snn yaje shi nysc dan bappa zaidu ya riga yagaya masa cewa zai turashi can (UOf T) wato University Of Toronto a canada zaiy 1yr msc LL.M yadan kara karatu duk dashi aure ma yasaka aransa sosai ynxu..


dan wann shakarar ne su sultana da kulthum suke ss3, nd in like 9 month time zasu cika 16-17yrs zasu gama secndry schl dinsu baison yaje karatu a wata kasa ace bai dawo da wuri ba sabida yar uwarsa kulthum din yake so ya aura...


kamar yadda ya saba kullum ma ammi karama kawai yay ma bayanin qudurinsa ta ita kuwa bashi shawara akan cewa ya daure yay passing bar, yay nysc dinshi, yaje canada ya dawo by then kulthum tama kai na auren nd what he need to do shine kawai ya tabbata da cewa sun samu fahimatr juna akan haka kafin ya tafi inyaso kafin ya dawo angama batun aurensu acikin gida, as usual this advice sits very well with him. ya bari aransa kawai hakan zaiyi tunda already yaga da alama kmr kultthum din ma tana sonshi sosai saidai kawai da ba abarinsu su nuna ma juna a fili..amma haryau shi kadai take kulawa.


ko sultana da ta fara saurayi kusan a boye take chat kawai sukeyi, His name is ahmed waziri dan gidan sarauta ne a kanon kamr mamnsa itace first wife na wani tsoho sarkin kano da ya rasu da jimawa. tunda suka hadu da sultana a school yazo daukar jnr sistrnsa yabi ya makalkale mata sosai itakuma bakaramin tsoron yayunta su kamata tana hulda da namiji da sunan soyayya takeji ba.



dagata fannin ayaana kuwa dan subucewar tazarar kulawa da uncle moh yay creating na karfi da yaji tsakaninta da ibaad yasa along the years ta samu dama daga wajen hajy mairo duk ranar da bata da islamiya ko lesson takanje shagon hjiya ta samu ruthy wacce ta gama buduwa tay katuwa kamar ba age mate dinsu sultana ba.


ayaanah intaje bata saida abinci dan tasan ibaad ya jima da hanata amma sosai take tursasa kanta tana koyan abubuwa da ake musu acikin catering school din musmmn da professionals aka kawo wajen suna koyarwa, gashi ruthy tazo ta gamu da mazan kano tawani irin bude ido ta zama yar gayu sosai, ita kanta ayaana mamakinta take sha, most of the time ita dayanta take zuwa shagon ta dan jima tare da ruthyn tanamai koyon wasu dabarun girki na zamani dana gargajiya sabida su kulthum sunakan shirin su waec da su jamb dinsu, gashi ko first term ba'ayi ba tukuna.



yanxu haka ss1 ayaana ta shiga ta zama big girl now amma Girma yazo mata da kalubale kala kala sabida wann matsanancin slim shady coca kola shape din da jikanta ya fitar dashi, yakasance kamr ita ta jera halittar jikinta dede wa deda,nononta da suka tashi fitowa so full nd round, hips dinta yadan baje dakyau yabata perfect curvy model shape, kyanta ya kara bayyanna sosai dake tana balain samun kulawa. ..


wani irin silent soyayya mujaheed yake nuna mata wanda haryau bata dago ba, haka a wasa wasa zata ga zai tura mata morning nd evening tex kuma ta amsashi itama duk da tunanin cewa sabon da sukayi da kirkinsa ne kawai yayi yawa ba komi ba.


hakama duk takuri da shige shige da wahalan saye sayen kayan duniya da unclle moh yadage yake kan mata Allah baisa ta dago meyake nufi da ita ba, itade tasan duk gidan babu wanda yakaishi bata kudi da kashe mata kudi..daukawa tay Haka Allah yay shi da son kyauta. hatta wayar da ibaad dinma ya siya mata yanxu kusan sau biyu kenan yana canza mata da latest iphones ynxu haka dai kowa dai ya zuba masa ido ne ba acemai komi...ko ibaad ma saidai ya kalla abun ya dauke idonsa duk dama haryau komi ayaanah zatay arayuwanta sai tazo ta tambayeshi shide kawai harkan uncle moh ne baya sake ya shiga dan ynxu ko ya gaishesa da kyar yake amsashi..



wani boyayyar haushi uncle moh yake fama dashi, dan ya jima yana lura da yadda  ayaanah take bala'in daraja interest in ibaad at heart..


Zata ki sam tazo jikinsa amma bai taba ganin taji kwuiyar ko kunyar yima ibaad wani abu ba


sabida schl da business na Q4 yasaka ibaad bai samun time na kowa amma duk abunda yakeso sai yaga shi kawai ayaana take koya, duk wani fav food dinsa ta san recipe dinsa awajen ammi karama, nd she love to be the one to take food to him inyazo koda bazaici ba zata kai masa har daki, dan zcyarta yana cikene  da uban damuwar canzawar dataga yayi ayan shekarun nan musammn bayan matsalar su da uncle mohd sai bata gane komi ba.


saita rike cewa lallai hala zainab arifah ce take dauke masa hankali tunda tasan ana ma zainab islamiya a gida

...hakan kuma take rayuwarta da wann tulin fargaban ta dora ma zuciyarta akab zainab arifah.


girma da gogewa yasa zainab Arifah din ta zanca itama, inzatazo gidan wani irin kure adakar wanka takeyi, musmn ma da ynxu ta gama secndry schll ita dinta next week kuma ake shiri zaa musu grand ceremony snn nan da sati uku zata bar kasan nan.


ayanah na makale da murnan zainab zata bar kasan ta kyale mata yayanta, batasan itama zainab arifah din itama adame take da rashin samun kan ibaad da takey arayuwarta kwana biyun na ba.


dukan su they are woried abt canzawarsa amma kuma kowa yana zargin kowa batare da sannin su ba shikuma yana can baima san sunayi ba dan daga harkan schll dinsa sai business dinsa daya sako agaba musmn ma da yanzu suka dawo sun shaku da su jamal sosai...


business dinsu da suka fara tun a watanninsa na biyar suka fara samun agro revenue amma dukansu basu taba ba, awatan su na tara suka fara small cold chain distrubution shi dake a dubai ne jamal ne yake dubawa sosai nd all the land da suka siya sunyi securing, kusan komi dai ya tsaya da kafarsa saura kawai yay karfi. 


1rs year suka fara samun return na kudadensu they make 39million naira each cos of the transction na cold chain in dollars yake zuwa musu, sunay suna reinvsting har saida suka bude rep. office a dinsu a dubai, snn suka fara karban monthly flow divisions kowani wata kowa kudi yana shiga acct dinsa ...


uncle moh da harka ya buda masa sosai yakan siya ma ayaanah abubuwa nagani ma fada, haryau shine gadgets,

jeweries ne,kudi ne duk zai bata.. amma haryau baisan cewa ibaad ne ke siya mata duk wani abunda take amfani dashi me matukar muhimmci a matsayinta na ya mace ba, ryt skin nd hair cares, sanitary pad, inner wears, da school items komi shiyake siya mata ammi karama kuma suke saya mata kayan sawa da duk wani abu daya shafi zaman gida most time kuma bappa zaidu ne ke biyan mata kudin  makaranta ita da sultana gabaki daya atare, bacin nan duk wani kananan abubuwa ibaad ne yake mata quietly snn yay guiding inta.



Dagata bangaren zainab Arifah kuwa wani irin grand shiri ake yi na graduation event dinsu dake tsarukan su ba iri daya bane dana sauran makarantu, dan sungama makarantar da kusan watanni kenan har result dinsu duka sunfito amma yanxu ne ake shirin musu gagarumin graduation ceremony


saboda kebetaccn makarantar masu shi ne sai sunyi shiri sosai sunyi gayyatan manyan 

mutane both daga cikin gida dana waje..


Bisaga labarin fitowar result, is no longer a news a gari cewa Zainab Arifah is the e best ever graduating student of her set, asalin madarar guruwa ce by karfi da naci, duk dama gidansu sunyi gadon ilimin amma kokarin da zainab tay a karatu ya samu nasaba ne da yadda take mutuwar son taga ta faranta mahaifinta ransa ta dorasa a wani babban matsayin da dolensa ne ya alfahari da ita


tunda aka san cewa result dinta sunyi kyau wokers din gidan su  basu kara samin duwawun zama ba


her pink yar gata graduation dress har kasar MILAN akaje wajen wani designer dinkawa, the whole week was spent on shoping, satin da za'a shiga na spa ne dan haka ta katse komi tun anan aka sallame malamin islamiyarta aka cemai aikinsa ya kare kenan dan ana yin graduation partyn kominta is ready zata wuce karatunta a kasar waje. yadda kasan aure zatay haka suka dau abunda zafi, amata wann, amaya wancan.


a week din spa din nata ne Ibaad yasamu wata urgent call daga wajen mahaifiyar jamal moriki 


wani lamari dayazo musu da babban abun mamaki, duk dama suna sane da cewa a satin nan jamal was supose to celebrate his birthday In the U S, sai kuma katin marriage engagement dinsa yazo musu abazata..he is  going to be engaged to his childhood sweethrt dinsa mufeeda Bilal yar gidan babban lawyer na babansa dayay musu fighting har suka samu arxikinsu da komi nasu  ahannu. His pained gold digger uncles suna kan pushing narritve din cewa jamal har yanxu karamin yaro ne bazai iya running babban kamfanoni ba wasu abubuwan sunaso ne lallai abasu karfi da yaji dan su kwace arzikiin yaron nan., the judge advice them to get him married, cos in the state samunka da stable relshp ko aure yana iya hana wasu kananan premature legal actions yayi aiki akan namiji ko mace and this was the only way for jamal. dan haka atake atake aka shirya aurensa da mufeeda bilal cikin satin nan. 


farhan dake sydney shiya fara isa, kafin nan su ibaad da prince hassan suka zo daga nigeria. kwana uku sukayi a U.S aka yi auren jamal kamar da wasa biki yay dadi sosai, it was in a very private nd luxurious way kuma dama can suna son juna sai akay small lovers event acikin private yatch.


bayan sungama supporting abokinsu to the fullest, washe gari suka dawo gida kamr ba ayi ba, kusan jakan designer guda suka dawo dashi na wedding souveniers shi ko bude nasa ma baiyi ya bawa amminshi duka kyauta  baisan ma ma waye ta raba ba.


duk yadda ake shirin hidiman graduation din zainab arifa ko kadan bai dara ayaana ba, ta dai ga su kulthum sunyi spa, sun gyara gashi an zabe special kaya..ita da kuma dake Allah Allah ma take zainab din ta bar kasar nan ta kyale mata ibaad sai abun baiwani darata ba.


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[03/12, 17:20] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️3️⃣5️⃣

Graduation day:

Wayewar gari ce mai sanyi iska tana kadawa ahankali kamar ana masa umarni ya nutsu yaurana kokadan bata fito ba tukuna amma dakin Zainab Arifah ya riga yayi wani irin haske da grandier decorations tareda tsadadn fitilu da kyawawan akwatunan kyautuka da aka jera mata a dakin tun jiya da daddare ayayinda take bacci batama sani ba.White nd gold boxes, ga manyan bouquets ga su sabbin bags, heels, sets na jewelries,har ma da wani babban frame da aka rubuta OUR PRIDE, OUR STAR. Congratulations on your Graduation zainab Arifah al-mansur.”Duk dakin ya dauka da sheƙi kamar gift room na royal palace.


yau Waking Moment dinta ma daban ne hajiya hamida ne tazo da dakanga da wani irin expenisve botle of champaing da sassafe cikin tsananin farinciki tay poping fasss a sama tace baby girl… wake up. its ur day!!! Da tsananin farin ciki Zainab tabude idonta a hankali ta tsaya cakkk ta yi blinking sau dyawa saboda dakin nata ya canza tamkar magic land with all the light, dolls, and gift boxes sorrounding her, atake Tsigar jikinta ya tashi ta mike zaune cikin wani irin sautin murna tace "yeeeyy...finally, i am a graduate! awn nd dis is All for me?hajy hamida tay dariya softly tadan shafa kanta tace yess Everything for you, my daughter. You earned it. Today is your special day.” 


tun bata amsa ba sai gan nan prof zayyanu ya shigo cikin dakin sanye da farar jallabiya yana murmushin farin cikin wanda bai iya boyewa,with this strong i am proud of u energy yace heyy "look..my princess is up! top of her class,best in the whole set Zainab Arifah Ina alfahari dake sosai, Wannan ba ƙaramin abu ne, zamu iya yi komi don nuna miki yadda mukeji princesss u can name anything in this world today nd i prmise u it will be yours..


da tsananin murna ta dora kanta akan kirjinsa ta dada rungumesa sosai tana jin wani irin sinadarin sonshi yana lulluɓe ta. da wani irin shauqi a muryanta tace i love u dad

...you are best man in this whole world. zan iyayin komi dan nasaka farinciki..dad..all this success is dedicated to u ...


idonsa kamar zai zubar da hawaye yace "Thats my girl.. i love u too my princess..ure my world. ta kara kankamesa ssai hajiya hamida ta dinga kallonsu feeling sober tanata murmushi sosai


jim kadan manya manyan kawayenta su Nala da Rukky suka iso gidan suka kawaye ta yadda ake ji da zainab din kowa ma zama yay sunai mata kallo kamar wata real princess. 


professional yan kwalliya su biyu ne suka mata special makeover aka saka mata Wani shimmering italian pinkish gown da gold shoes, kayan ya kwanta a jikinta tamkar anzana ne ajikinta her Hair was styled neatly, aka mata subtle make up mai kyau irin nasu na masu shi, kawarta Rukky tana tsaye a gefe tana tahowa kasa da excitement. tun daga can tace “Nalaaaaa, yaufa akwai bura uba anyah kuwa arifah bazata makantar da yaran makaranta yau ba? Nala ta ce, we run d town remeber? Wallahi the whole school will bow for her today, Dukansu suka yi dariya.



at arnd 9.30 am aka gama duk wani shiri suka fito tare da ita iyayenta da kawayenta dukansu suka sakota a tsakiya suna masu yagalgalata, a cikin wata exotic convoy na mercedez bunker Jeeps guda hudu suka nufi wajen hidima cikinsu babu wanda bai tsokalo wankan kyau na fitan hankli ba.



Wajajen karfe tara da rabi suka isa babban conference hall inda venue graduation in yake security ne kaca kaca a school din har da surveillance drone


tun daga waje manyan motoci keta hayaniyar parking sabida ingancin karatun da ake samu awajen yasaka wasu masu kudin marasa girman kai suka kawo yaransu schl din duk dama basufi daidaiku ba.


Drivers suna gama parking ahalin prof sauka suka karasa ciki her family arrival was chaotic dan kafin ma su iso cikin aka fara zunde ana nunasu saiji kake ana ambatar the almansurs, ihun rans dinta kakeji "O.M.G its zainab Arifah almansur"top student! she broke the school record! kusn kowa idonsa nakanta  suna takowa hannunta makale dana babanta tana wani irin yngatcn murmushi ana musu confetti har inda zasu zauna lokcin zuciyarta acike yake da farin ciki danji take kmr wa ita kadai akay shirya wann taron bama sauran dalibai ba.


decoration din wajen yayi balain kyau yaran masu kudin nan are all dressed like met Gala red carpet event, basu saka wani graduation gown ba kawai sai aka rabawa kowa expensiv silk graduation banner kowa yamakala wuya like a parade prince nd princeses.



Bangaren su hajiya mairo kuwa dake yau asabar ne tun jiyan ta dinga jadadda ma kowa fitowa da wuri dan zuwa wajen hidimar nan dan bawai zainab Arifah zataje ta gani kadai ba harda ma zumudin son taga zayyanu duk dama ya raba kansa da ita amma still akasar ranta tanaso koda fuskansa ta gani. haka tasaka aka tashi sassafe, tun 6 am aka hau shiri, dama kuma anyi odern abinci da kayan snacks anyi packaging insu in d best way possble duk na kaiwa graduation ground domin taya zainab arifah murnan gama makaranta.


kulthum da sultana suka saka designer gowns dake ynxu sunyi tsayi duk angirma sai bakaramin kwalliya me aji suka sha ba classy french gown ne ajikinsu amma na sultana mint green, na kulthum kuma calm champainge gold da duk wani matching accesories bakaramin kyau suka yi ba...


ayanaah ce kawai taki sakin jiki ta shiga ribibin hidima dan tafi dmuwa da abunda zai je ya faru acan,haka kawai takejin kwata kwata bata son tana ganin yayanta da anty zainab arifah, kuma wann intense feeling din sosai yake ginuwa acikin zuciyarta bana wasa ba. kowa na zumudin zuwa amma banda ita dan normal make up inta tay ta shafa kajol, tay lining lips dinta ta bishi da shiny lipgloss sai kuma yakara sakawa tay masifar kyau din harma fiye da wanda suka tsaya cancade make up tashirya tsaf cikin atampa exclusive green da pattern din yellow da baki, dinkin yayi mata kyau sosai, skirt ne with peplum blouse mai three quarter hannu, ba a sa komai a jikin rigar ba sai patterns din atamfar aka yi mata aiki dashi, dan kunne kawai ta saka bata sa sark'a ba, agogon gucci ta dauka ta mak'ala a hannunta tay dauri me push back kadan snn ta yafa veil me sharara tagama shirinta ta fito.


ayaanah tayi wani irin kyau, gashi tay tsayi zaka rantse su sultanan ma age mate nata ne, karfe tara da rabi kulthum suka fito daga dakin sukayi dakin anty safeerah, tana ganinsu tace "Masha Allah sisters dina kunyi kyau" kulthum na murmushi tace "not as much as you, sultana tace aikece beauty queen a dan shashance ayaana tay dariya kasa suka sauko suna jiran mujaheed mai kaisu yazo dan Already hajiya mairo da su ammi sun fara yin gaba, daga su yaran sai anty safeera ne ynxu agidan dake maheer akace ya tukasu su hajiy kowa yasan aransa ibaad ma yana tare dasu..jerowa sukayi awaje harabar gidan sunata daukar hotona da selfies da wayoyinsu.



agaggauce anty safeerah ta kulle dakinta wayar ta a kunne tana cewa haba mujaheed yanxu da kabisu maheer din uban waye kake so ya kawo yaran nan bayan ni anbarmin aikin tahowa da abinci 

..maganan datake y kenan har ta sauko tana fitowa babban falo tana jan tsaki daga can kasa ta hango ibaad daga stairs har ya canja kayan dake jikinsa ya saka casual ralph lauren shirt da sweat pant ajikinsa kafanshi sanye da slippers din Fenty, babu ma alamar zaijeshi wani waje, hanyan waje taga yabi zai fita ba tare da ya kalli palon ba rike da makullin motar da wani irin sauri tace "ibaad, don Allah ga su kulthum nan ko zaka ajiyesu a awajen su hajiya  tunda kai ma fita zaka yi pls dan Allah kawaye na ne har sun iso babu wani space a motar kuma bana so suyi driving da kansu, bai juyo ba saida yaji ta gama  cikin ransa yace hmm wato dai yau shi yazama driver wa yaran nan,cewa kawai yayi "toh" snn ya sa kai ya fita. anty safeerah ta sauke ajiyan zuciya dan batay tsammanin ma zai amince da wuri haka ba.


hasken rana daya fara fita ya haska fuskar ayaanah dago kanshi yayi zai duba ko sun fito idanunshi suka sauka kanta tsayawa yayi yana kallonta da gashinta da yasha gyara da yadda take murmushi ahankli. wani abu me karfi kamr sihiri yaji yana fizgarsa, cikin sauri ya dauke kai basu ma lura dashi ba saida ya shiga motar ya danna horn da karfi.


sultana ce ta farga ta fara zuwa kafin kulthum tabi bayanta ta shiga suka zauna a gidan baya da ido suka dinga ma alama ma aayana signal akan ta zauna agaba dan karma yace sun maidashi drivernsu ganin babu yadda ayaanah ta iyane yasa ta shiga gaban  har zai tada mota jin dadin turarenta ya bugoshi ya dakata ya dubesu su biyun abaya ya daka masu tsawa yace "ina kuke tunanin zan kaiku haka da gashi a bude kmr wasu dolaye ku fice min a mota kuje ku rufe kanku da kyau kuma kar wacce ta ɓata min lokaci...da wani irin speed suka sauko suka wuce cikin gidan da sauri fargaba yasa ayaanah jin kmr itama ta sauka ta bisu tana kama handle din motar ya kwace ya rufe kirjin ta taji ya buga idonsu sakale dana juna yace "where did u think ure going to? muryanta a rarrabe tace "kace...muje...cikn katseta yace "not you..suda bantaba gaya musu bane nace suje ke ai nasha gayamiki kidena tula kwalliya a fuskarki bakiji ba..u wanted me to see it ryt? toh nagani! cikin matsanancin jin nauyinsa ta sunkuyar dakai kasa muryanta na fita ahnkali tace "nifa ba kwalliya nayi ba, amma bari zanje na canza toh.

...dan dauke kansa yay cikin basarwa yace"i dont have that time.. just use ur veil nd cover it up banason irin wann dresing in da zai nuna wani part na jikin ki awaje.. jan veil din ajikinta tay ahankli ta kara rufe jikinta dashi, yana kallonta da wutsiyar ido yace "not like this, sake hade ido sukayi dashi ya mika mata hannu idonsa nakan veil din ajikin sanyin kunya ta zare veil din ajikinta ta mika masa ya rike duk qamshin ta ya buleshi

cikin lumshe ido da budewa ya kare ma jikinta takaitaccen kallo snn ya tattaro makansa nitsuwa carefully yay placing veil din above her head, ya dan rufe mata sama sama daga inda sumanta yake nunawa ta gaba she look abit matured now tamkr wata matar aure


kanta na kallon kasa har ya gama kafin ta dago ta kalleshi da sanyin murya tace "nagode"..ido ya zuba mata baice komi ba, taga ya daga wayarsa yana latsawa ko minti daya bai gamayi da wayar ba sai ga su sultana sun dawo babu dandanin gashinsu da ke nunawa a fili.


suna gama shiga ya kunna motar, ya saka karatun qur'ani at medium yadda babu daman suyi magana da juna. har cikin makarntr su zainab arifahn ya kaisu spot din da familynsan suke yana ajesu suka sauka yana kkrin juyawa kenan hjiy mairo ta hangosa ta karaso wajen tafara masa masifa akan dalilin dayasa shima bai shirya yaxo nan din ba aikuwa ko kulata baiyi ba yaja motarsa yay cikin gari. haka nan ta dinga surutu dakyar da wahala tasaka ammi karama ta kirasa awaya harsaida ya amsa cewa zaizo tukun hanklin hjy mairo ya kwanta..


daga gefe kuwa kulthum da sultana banda tsokanar ayaana babu abunda sukeyi kowa nace mata tay kama da matar aure duk dama wasa ne she keep wondering why xai saka mata veil dinta ahakan..

can anty safeera taxo tare da kawayenta su biyu sai ruthy da hajy mairo tace axo da ita zata na rabawa jama'a abubuwan souverniers da sukazo dashi..


kusan kowa ya hallara face bappa zaidu dan shi baidama lkcin wann shirmen banxan, uncle moh ma daga baya ana daf xaa shiga yaxo aka basu speacial seat a VIP zainab arifah dake can sama wajen graduant kamr xata hadiye ranta ko ta tada aljanu data gan kowa yana wajen face ibaad.


gashi har camera me tsada na msmn tazo dashi wanda zata dauke zallan memories din graduation inta dashi, wanda intaje U.S ta dinga kallo tana tunawa da wnn ranar a matsayi ranar farincikin da bazata taba iya mantawa dashi ba



Shiru hall in yayi ana sauraron speech in da Principal keyi da ta gama ne sauran members in High table suma suka karba mic suna yiwa graduating students in Nasiha game da sabuwar rayuwansu wanda zasu fara a university sai da aka gama speech ne aka fara presenting dinsu short litreture drama professional band perfomance da wasu abubuwan na nishadi da al'adu.



Ana gamawa aka fara kiran best graduating students domin su karbi certificates dinsu Mc na cewa Zainab arifah hall in ya cika da ihu fa tafi bayan ta mike masoyan ta ne ke ihun kai hatta malamai sai da sukay mata tafi cos she was such an excellent student duk da tarin chaos din datake jawowa na nuna classims acikin dalibai.


ihun da aka sane ya sa ayaanahn jan tsaki mai tsayi a hankali batare da tasan ma tay ba


zainab arifah ta sauƙa daga kan kujeran da take ta karasa stage ta karbi certificate inta daga hannun principal a hankali tace mata " Thank you maam" bayan yan hotuna da aka dukesu da ita ta koma inda sauran mates dinta ke tsaye lkcin kawai ibaad ne a mind inta tafarajin wani irin baqin ciki atake kar ruwan idonta yafara canzawa.. 


haka aka ci gaba da kiran sunayensu har sai da aka kira duka students din sannan aka yi musu standing ovation tareda tafa musu dukansu a kan stage in kowannensu ya tapping bannersa suka sa ihu ana musu hutu, bayan nan kowa kujeranshi ya koma bayan nan, lokacin ne aka fara presenting beautiful prizes for the best overall graduating students lkcin kirjin kowa na bugawa da fargaba.


Itadai rashin zuwan ibaad kawai takeji aranta dan taso ace yana nan xa'a kirata sama a karramata haryanxu batasan wani irin baqinciki zataji acikin zucyarta ba in ibaad baizo ba.


Principal ce dakanta ta taso ta tsaya tana kallon Zainab Arifahn kamar shining diamond cike da alfahari ta amshi mike tace “Ladies and gentlemen…presenting our exceptional star… the one nd only pride of this honourable Academy… Zainab Arifah Almansur.”


memakon taji farinciki duk ta tuna ibaad baya nan sai ta fashe da kuka saida babanta ya tashi yaxo ya rike mata hannu,.tahowa yayi da ita zuwa stage Gown dinta yana sharar kasa gashin kantan nan dayaji gyara yana baza kyalle wajen duk ya kaure da tafi kuma kowa ya mike tsaye aka bata Standing ovation.


Ayayinda zuciyarta ya cike da duhu wann rana na farinciki yadawo mata na kuka babu wanda yasan akan ibaad take kuka an dauka ko kukan murna ne da nuna godiya


Daga nan aka karanta achievements nata Best Overall Student, Winner of School Math Olympiad, Honorary Award for Leadership, Outstanding Academic xcellence...Principal ta dauko award plaques masu kyau har guda biyar duka ya mika wa prof zayyanu sai kuma muryar announcer kawai.“By the request of her parents, family, and the school board, Zainab Arifah almansur is presented with the Elite Scholar Crown, the award given once in ten years...raf raf aka fara tafi..tsabar kuka taki sam ta karbi awards din.. wa baban nata aka mikawa crown dn yasa mata akanta lokacin tafi da kuma camera flash ne ke haskawa ta kota ina


duk da kukan da zainab takeyi still prof yanaji ne kamar duk duniya shine kawai ya haifi ƴa me ilimi, hajy hamida kuwa har tana zubda hawaye, har sai bayan angama snn Zainab ta mike a hankali ta kama mic for her speech kusan kowa yasan ta tsaurin ido amma yau sabida absence din ibaad muryanta na rawa rawa hartana jan majina tace “Today… is more than graduation to me. It is proof that no background, no doubt, no challenge can stop a girl who sees herself as capable to win..“Thank you soo much dad. Thank you to every single person who believed in me nd who care to come..dede nan ta kara fashewa da kuka me zafi dakyar tay controlling kanta tace"I promise… this is only the beginning..


Wani irin tafi aka mata kafin nan Music ya fara cike wajen kawayenta su Nala ta daga ta sama tana ihu, zainab “ZAINAAB!!! Zainab Arifah became the name the whole school will never forget amma awajenta is almost the worst day ever tunda ibaad baixo mata ba.


haka aka ci gaba da bawa sauran dalibai prizes, but asif today is her day alone har gifts na most most obedient,

uwa uba itace neatest, punctual..snn akaba dukka prefect kyauta


Dj ne ya kunna ma zainab din wakan champion mates dinta sunata mata murna suna zagayeta dan kuwa tafi kowa karban prizes a wajen Kowa na admiring dinta koma wacece ita Masha Allah tayi kokari sosai.



haka aka ci gaba da bidirin daga karshe aka rufe da addu'a,tun suna ciki suka fara daukar hotuna da yan ajinsu har suka fito waje,all eyes was on her kowa ma hirarta yakeyi sabida karramawar data sassamu da kuma irin kukan dataci.



Daga nan Kowa wajen family members dnshi ya wuce hajiya mairon ta fara rungumewa ta kara fashewa da kuka tun kafin tafara complain hajiya tace mata zainabu Allah yasanya Albarka,Allah ya taimakeki yasa kifi haka",tace Amen hjy amma meyasa bakice ma ibaad yazo ba gaskya hajy bakimin adalci ba. baki bude hajiya tace ikon Allah dama ba kukan farinciki kike yi makanki ba akansa kike wann uban kuka toh wallah ki koyi gode ma Allah zainabu kaji min yar goguwa wato namiji ne ma aranki ko?


Daidai lkcin prof yake karasowa tawajen tare da su hajy hamida da wasu friends dinta..


suna xuwa hajy mairo ta dauke wuta tay tsinin baki, murya kasa kasa hjya hamida da frnds intan suka tsunguna ta gaida hajiya mairo, itama ta amsa ta a dakile. sabida idon mutane yasa prof ya karaso gabanta yafara gaisheta, jin yanace mata mama mamaki abun yake bata..kallon idonsa tadingay da fushi bata amsashi ba har ya tashi ya bata waje....zainab Arifah ta dawo kamar wacce aka mata mutuwa koina taje ta tsaya saita tambaya mesa ibaad baizo ba duk saida tasa iyayenta suka damu, prof ya dinga kiransa layinsa a kashe. maheer yana tare da kulthum, ita kuma tabi ta nanike ma mujaheed da question har ya rasa abunda zai ce mata.


can can bayan har angama gaishe gaishe anata rarraba abinci snn ibaad ya karaso

ahakan ma disturbing text message din daya gani a dayan layinsa da amminshi ne kawai tasani yasaka yabar abunda yake yay wanka yasaka black kaftan da hula ya taho.



yana sauka a mota out of emotions zainab arifah ta wani je da gudu ta rungumesa saida tasa yaji kunya idon mutane sosai, it was hard for him to maintain his face yayo saurin raba jikinta dashi fuskrsa a dore yace "ke lfyarki kuwa ya zaki wani cakumo ni cikin mutane kamr wata babban mahaukaciya are u insane?? cikin kufula ta kallesa zatai magana cikin katseta yace" ke da Allah matsamin karko sake min haka..am not ur mate" dan turata gefe kadan yay ya wuce wajen su amminshi tay saurin biyosa abaya da fargabn kar ace mutane sunga abunda ya faru


she kept following him duk inda ya tsaya within few minute ta dawo dede tadena kuka sai kuma ta bude chapter kinibibi...bata ma bari babanta ko su hajiya sun tuhumesa ba sai tana karsehi tunda dai yazo shikenan...dacan ayaana tana zaune da su anty safeerah da su sultana ne saidai tunda aka kafa chapter zainab arifah taga kowa yana cewa ai kukan datakey sabida ibaad baixo bane bla bla bla tunda yanxu ta gama schl kawai ayi kkri amusu aure karta shiga wani hali kowa yana kawo dfrent opinion hanklin yaana sai ya fara tashi sosai..


she was watching duk yadda zainab rifah ta makalkaleshi batajin kunyar idon kowa kamr wutsiya take binshi tama mance batun iyayenta agefe


ga hajiya sai hirarsu take 

ma uncle moh itama maganan kenan ayi ayi musu aure..


ruthy ne kawai tagano cewa ayaana ba kalau ba, Agindin wani bishiya ruthyn taja hannun ayaanah suka zauna ta inda ba'a kallonsu, tun kan tace mata komi taga ayaanah tana hawaye tafara rarrashin ta tana bata hakri har sanda taji nauyin dake kan zuciyarta yay sauki snn Ta tambayeta meye ne damuwarta?


Dacan tay shiru kmr batasan mema zata fara furtawa sai can kuma Ahankali ta sauke ajiyar zuciya saboda fargaba da tashin hankalin da zuciyarta ke ciki wani tsiririn numfashi taja hade dayin kasa kasa da kanta dan sam bazata iya kallon kwayar idanun ruthy a wannan lokacin snn tay mata karya ba.


Ahankali tasoma magana muryanta kasa kasa cikin sanyin jiki tace"yaya na ne" daga nan shiru ta danyi tana fidgeting fingers dinta kanta asunkuye take idanunta suka kara tara wasu sabbin ruwan hawaye tanajin wani sabuwar feeling din tsananin tsoro dake dabaibayeta,a cikin shagwabbiyar yanayi tanamai takune fusknta da sakalci tace,'..toh Bashi ba ne saiyana ta fadomin acikin raina kuma ynx kowa yana cewa zai auri anty zainab..


...shiru ta kumayi tana dago kanta sai zirrrrr hawaye masu rauni suka sauko mata bisa kuncinta, kara fashewa da kuka tay mai tsanani cikin kukan take cewa "ni wallhy bana son ya aureta..kawai bata dace dashi ba..kuma baice zaiy aure ba. Jawota jikinta ruthy tay ta rungumeta ganin kukan nata yafarayin yawa tace kai ayaanah kiyi hakri dan Allah...kinga za'ay ta kallon ki kina kuka anan wajen...kiyi shiru kinji?


Da kyar ta dena kukan ta dago kai tanajan shesheka ruthy tana dan shashare mata fusktanta cikin sigar lallami har sanda ta danne kukan tas snn ta riko hannayen ta suna fuskntar juna da sanyin murya tace "i knw how u feel..hajiya tace min he is ur quardian, wai shiya kawoki nan garin ko? its natural for u to feel attached to him nasan duk inda yake ai shima hanklin sa nakanki

..koda bansani ba ai alama ya nuna yarinyar nan ce take sonshi..kimasa uzuri kinsan idan mace tanason namiji irin wann bazaki iya gane komi ba.


Ta dafa gefen fuskarta acikin nitsuwa tace ki kwantar da hanklinki ki karkisa damuwarta aranki if she is not good for him zakiga bazai aureta ba kinsan mata masu throwing kansu ma namiji maza basu daukarsu da daraja i assure u he is not going to fall into her traps


jiki a sanyaye ayaanah tace haka ne, sai kuma tay karamin murmushi tace "i dont even knw why it bothers me. sai inaji kamr i am intimadetad by her. i mean, ruthy look at her she is a rich princess, classy nd intelligent..kuma tana sonshi sosai..sai naga kamr dai with time zakiga zata aure shi din dan banga wani abu data rasa ba.


cikin dafata ruthy tace 'ayaanah amma kinga kanki kuwa har kike hada kanki da wancan kucakar...ayaana tace what?ruthy tace yes kinjini gayyar kudi ne da kyale kyale 

amma wallah ko kusa dake bata kai ba. if da ace kece a matsaynta ma da ba haka ba. besides, kema me kika rasa? iyaka ta nuna miki bude ido kema da kinaso da tuni na nuna miki hanyar zamowa big girl dede da yayanki..


da mamaki ayaana tace bude ido as how?? cikin rage murya ruth tace "like getting to knw alot of big girls stuff mana. kmr yadda wancan din takeyi. she have her gang, fashion taste, nd can drive cars. halama tazaga duniya tay socializing ke fa zama kawai kike a waje guda kuma yadda kike kyakyawan nan koshi yayankin yaga kina leveling up bazai kalle wata zainab arifah ba.


shiruuu ayaana tay for a while kafin can tace " i dont knw what to say..amma zan miki magana innayi tunani akai.. 


karamin dariya ruthy tay tace " its just leveling up babe. wai bakiga yadda na dawo bane? just to knw how things work.. what attract men..no matter what dai dik macen da bata san kanta ba bazata iya mulki a duniyar namiji ba. itama wann din da tana da aji da tuni yafara sonta...cikin katseta ayaana tace its okay...zan kiraki amma bari nagama ss1 dinnan dai cos i dont want to be lagging behind..


ruthy tace anythime kika shirya kawai kizo wokers estate ko mu hadu a shago i wll teach u some things..


da fargaba aran ayaanah tace okay...daga haka suka bar hiran, bayan ayaana ta gyara fuskarta sukazo wajen daukar hoto.


Tunda akay na family tay dasu sultana da kulthum sai bata kara shiga wani ba dan yadda zainab arifah take makalkale a inuwar ibaad yana balain bata haushi

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[03/12, 18:12] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️3️⃣6️⃣



Neman waje tay ta zauna akan wani chair bata jima da zaman ba cikinta yafara murdawa which explains the sudden mood swing da anxiety datake fama dashi saiyanxu ta gane ashema period ne yake shiriin xuwa mata shiyasa ita kanta ta gane kanta..


tunkan ciwon ciki yay nisa ta mike cikn sauri zataje wajen mujaheed ta rokesa suje gida tunda anma gama komi tana dosowa sai kuma tagansa tare da xainab arifah suna magana portrait juyawa tay da ssuri bata karasa wajen ba, agefe kuma kwata kwata bataga su kulthum da sultana da yaa maheer ba da alaman sunje can ta wajen prof xayyanu tare da anty safeerah da uncle moh ana gaggaisawa batamasan meyake gaya musu acan ba


tana juyi ta hango hajiy mairo tana zaune da ruthy tana sharo kwana zata zo wajensu taji inuwar mutum ata bayanta kirjinta taji yana bugawa da balain karfi tana juyawa kuwa suka hade idanunsa waje guda


...ganin yadda idonta yay wani irin jaaa ahnkli yace ina zaki je? muryanta na fita da sanyi kafin ta amsa shi taga ya kamo hannunta "come lets sit over der nima nagaji..kafin tace wani abu taga ya jawo hannunta ahankli take binsa abaya har suka isa gaban wani chair a garden suka zauna inda babu hayaniyar mutane sosai


suna zama ta sauke ajiyan xuciya ya xuba mata ido fuska ba yabo ba fallasa yace "are u okay? hawayen da batasan da su ba ya ciko idanunta da sauri

ta girgiza kai ya hade rai "toh mesa kikaje can kika xauna da wata kina mata kuka? da mamakin jin hakan daya furta ta kallesa cikin sanyi tace

cikina ne dama yake min ciwo.

.".dan shiru yay kdan yana kallonta cikin kyabe baki yace

"nd u dint tell me? toh toh ince ta baki drugs awajen kinsha

...hawayenta datake dannewa ya fara zuba ta girgixa kai ahnkli tace lokcin ai kana tare da mutane ne ni bazan iya zuwa nagaya maka ba


yace ni bana tare da kowa its just zainab ko bakisan ta bane...cikin turo baki da shagwaba tace but she is talking to u all the time shiyasa.


..yace shiyasa me? u have no businss with her talking to me da zakiy fushi..cikin makale wuya tace "ni ba fushi nayi ba..da wutsiyar idonsa yadan harareta yace i dont believe you sau nawa kina ciwon ciki bakaiy kuka ba saida kika ganni da mace..kara tuluwa hawayenta yay tace nifa ba haka bane i dont want to cut u ppl off kuna magana kartaji haushi ai naji ana cewa ita zaka aura kuma..


karamin dariyar bazata yay yace.."aure? ninace miki haka..zatay magana yace look..in abunda ke damunki kenan why wont u do sumting abt it..go nd tell xainab dat ure once my wife shikenan zata kyale miki ni hala. hawayen tafara sharewa ahnkli kafin ta san amsar da zata bashi sai ga zainab din tana tahowa ta wajensu da sauri ganin yadda suke zaune kurkusa da juna kuma akebence da wani irin hararar kasan ido ta kalle ayanaah tace 'ashe kinzo? ai ban ganki ba..dakyar ayaana ta amsa tace ehh..shide mamaki take bashi. zainab ta dawo da idonta kansa tace hey, ynxu photographer da zai mana portrait zaizo just give me 5min dan Allah zan je na dan kimtsa fuska na zo nace mai ya same mu anan...tana fadin hakan batajira jinshi ba ta juya da sauri ta bi kawayenta dan agyara mata fuska cos she want a very big portrait of them wanda zatay masa enlargement ta aje a dakinta


tana barin wajen bada jimawa ba kuwa photograper yazo

irin professional din nan to kowa yana jiransa shikuma baisan waye zainab arifah  ba he tot ko ayaanah ce..yana zuwa yafara cewa small madam kidan kara matsawa kusa dashi..sir can u place ur hands around her, yawaa..bai bata lokci ba ya daudauka musu hotona masi shegen kyau..yana barin wajen ibaad yace tashi muje gida tunda cikin ki namiki ciwo kar yay tsanani..batace komi ba ta miƙe tsaye ta fara binsa batare da kowa ya lura da su ba ya bude mata gaban motar dayaxo dashi ta shiga ta zauna snn ya zagayo yana shiga ya tukasu suka bar schll din suka nufi gida.


yana sauketa ya juya ya koma gaban wata eatery ya shiga, nan ita kuma ta wuce daki dan tay wanka ta saka pad, ta gama har ta fito kenan tazo taga ya aje mata ledoji guda biyu, daya na drugs daya kuma kayan cime cime ne aciki..tun bata bude ba taji qamshi na bugata  bari tay ta kimtsa kanta ta saka simple riga da wando marar nauyi ta zauna  ta jawo ledan ta ciro fruit salad na ciki ta sha saida taji daidai snn ta fara cin su plaitain eggs da su pper chicken dake ciki...katon ice cream dake ciki tasha kadan ta aje sauran a fridge at around 2pm ta tura masa text snn ta kwanta nan wani bacci me nauyi yay awon gaba da ita..



bata kara jin meya faru ba sai can wajajen 4 data farka takeji labari abakin kulthum yadda zainab arifah ta dinga ma photographer hauka a fili...in short the whole graduation dat was suppose to be joyous was just a grand mess kowa saida ya wuce gida da gulmanta a makaranta. 


bayan komi ya lafa 2 days bayan graduation din aka kawo ma zainab arifah pictures insu har gida ta gaggani bayan ta yayyaga nasu ibaad din tasa wuta ta ƙonasu kurmus, gashi tun jiya tay tay ta rokonsa ta text message akan su sakeyin hoto baiko kulata ba harynxu..


dakyar ta cire batun hoton aranta ta dukufa shirin zuwa karatu duk wani abu na yar gata an mata har saida ya rage kwana biyu kafin ta wuce snn tazo gidan ta musu sallama, kowa a shashensa. anan ta nace musu wai saidai ayaanah ta karbi wayarta ta mata hoto 

ita da ibaad, ayaana kuwa ta karba ta musu pictures guda biyu, zama tay awajen tana editing din hoto dan ya kara kyau bayan ta gama ganin ita daya ne anan ta miƙe kai tsaye ta shiga room dinsa bataga kowa aciki ba har da zata juya kuwa sai caraf taga hotona guda uku half opened acikin envelope akan table dinsa da sauri ta bude taga the same pictures ne nashi da ayaanah data yayyaga sune anan batama san ya akayi ya samu copies dinsu ba..


kirjinta atake ya fara mata zafi tay sauri ta fara cusa su a envelope din da alama zata dauke taje ta konasu agida har tagama tattarawa zata saka a jaka kenan taji mutum akanta tana dagowa taga ayaana ta kura mata ido fuskarta ba asake ba tace "anty zainab in kin gama gani kibani yayana ne yace inkawo masa pictures din zai tafi dashi gida kuma sauri yakeyi...


ranta bai so ba ta miƙa mata..

ayaana ta bude hotonan tana kalla agaban zainab arifah tana murmushi basuce ma juna uffan ba, har ayana ta gama ta juya wani dan uban tsaki zainab arifah din taja ta fito batace ma kowa komi ba ta wuce wajensa sai taje ta same ayaanah still tana tsaye ajikin motarsa suna magana bata san me suke fada ba


haushi yasa kawai ta shiga nata motar ta daka ma driverta tsawa basu ma lura da ta bar gidan ba. koda da taje gida sosai haushin ayana ya kara tuluwa aranta tana jin kamar duk duniya babu wanda ta tsana kamr yarinyar nan ynx


bata daddara ba ranar da zata tafi haka tasa babanta ya kirashi wai shi zai kaita airpot duk da hakan ya faru har ta wuce U.S hanklinta a tashe yake akan alaqar sa da ayaanah. gashi sunyi da babanta cewa bazatana dawowa gida ba sai once in a while bayan ta samu dogon hutu, tun a jirgi kuma tafarajin inaaa hakan bazai taba yuwa ba, tun bayan graduation innan she bacome so insecured abt ayaanah sai ta fara jin dole ne ma tana dawowa gida akai akai sabida bazata sake yarinyar tagama kwace mata ibaad ita tana can tana karatu ba


tana isa gidanta a manhattan sukay waya da kawayenta iyaka maganan datake musu kenan sai kuma taji duk sun bi bayanta akan tana dawowar kawai in tana zargin ayaanah acewar rukky ai ayaanah tafita komi da komi is only fair if she marked her territory.


bayan kamar wata biyu da wucewar zainab arifah kasar waje daga nan nija kuwa ayaana tafara sauya kalar rayuwarta gabaki daya

schdules na karatun ta da skin care da skills inta na girki duk ta kara kaimi akansu bana wasa ba. dacan bata fiye kashe kashen kudin da uncle moh yake bata ba but the more ruthy tana gaya mata yadda rayuwa take a america the more tana gogewa anan itama. ruthy tana harka da wasu gang ne ita kanta batasan a ina ruthy ta samesu ba they know almost everything abt life kullum tazo shago anan suke haduwa, haka zasuje wajen hair dressing, latest designer da ake dinkin zamani da sauran abubuwa na gyaran jiki na mata tana daf xata y final exams na ss1 aka fara shirin graduation din su kulthum da sultana ranar da suka gama su final exams dinsu aka musu hadadden walima a ranar ne kuma kulthum ta gaya musu cewa yaa maheer yace mata zai aureta but she dont knw what to tell him yace dai taje tay tunani..they kept it as secret basu gaya ma kowa ba saidai su bata shawara, har maheer yay passing bar dinsa yay register nysc.


acikin yan kwanakin nan ibaad yafara batun exams insa na 500lvl yafara clinicals daga lkcin ne kuma ya lura da sudden canzawar da ayaanah tay sosai wanda harshima yasha mamaki irin seriouness da karatu da kuma yadda take bala'in yin wayo tana wayewa harma kamr zata fi su sultana sanin rayuwr kwalisa da kwalliya yanxu. while uncle moh is busy faving ways yana spoiling dinta with gifts dan wata rana har schll dinsu yake zuwa mata da suprise, tuni ruthy ta fara gaya mata cewa ai uncle moh sonta yake yi,ita kuma duk bata dauki abun seriius ba damuwarta yadda zata dawo macen kanta ne ta dan kwace ibaaad a hannun zainab arifah.


first time da zainab ta fara zuwa hutu iyayenta basu so ba amma ta nuna masa bazata iya zama acan haka ba babu yadda suka iya suka kyaleta, kullum tazo gidan she will only provock the situatuon na wann silent jealousy war dake tsakanin ta da ayaanah, zainab tana ji dakanta cewa tana da komi na duniya, ayaana kuwa tana amfani da wann daman tana dada shaping brain da sense of fashion inta.


kafin ayaana takai ss2 maheer ya gama nysc da zai wuce karatunsa aka hada harda hidimar birthdaynsa akayi masa home walima me dadi ranar haka sultana da ayaanah suka zuga kulthum har saida ta amshi batun aurensa yabata kyautar axurfa ring me shegen tsada few weeks after that ita da sultana suka fara level one a bayero university shikuma ya wuce canada karatu...


rayuwa ya zamana basa wani haduwa sosai da ayaana inba agida ko wkends ba wanda yasa ynxu ayaana tafi shakuwa da ruthy sosai sabida suna spending much time insu atare a shago da kuma cikin kawayen ruthyn da suke nuna ma ayaana wani duniyar yan matanci da batasan dashi ba.


she is almost 16 amma sosai jikinta ya habaka  silent rival competition dinsu da zainab arifah har sai ya baka dariya

musmn da zainab taxo ta fara jin kamar kanta zai kunce idan ta dawo taga canji ajikin ayanah,kmr yadda akata ririta ilimnta haka taji ana ririta na ayaanah, nd nala is alwys trying to copy ayaanah's fashion sense. gashi dai normal laces da atampa take sawa amma yadda take zagewa tay styling dinsu da dinkin zamani yabi jikinta yasa suka fara kishi da ita sosai


ya zamana ko zainab tana school a can america amma

hanklinta sam baya kwanciya, she was so intimadated da ayaana, professional gym din datake zuwa acan U.S tana gyara shape na jikinta duk sai taji ya fara kasa mata, yadda take ganin jikin ayana yana transforming into hour glass shape dake itama suna fita gym din time to time haka da su ruthy. ita kuma tay tay nata ya canza amma inaaa.. she started to think abt cosmetic surgeries. inda zata biya millions of naira agyara mata shape inta ya dawo me kyau fiye da na ayaanah, still duk wnn bai isheta ba har gidan su tasaka mum dinta hajiya hamida akan lallai ta kirawo mum ramlat collection itama aka siya mata atampopi da leshuna irinna ayaanah. babu abunda basu siya ba aka bawa fashion profesionals suka mata dinkunan zamani yet still duk hanklinta bai kwanta ba.


within dis time business din su ibaad yay flourishing sabida they are well connected and highy marketed by strong business routes he bot his first personal cars ayayinda yake kan kkrin shiga final year yana xuba kudi me yayiwa ma mum dinsa hidima snn ya kuma bude ma ayaanah clothing line online business tana saida imported gowns wanda ko ammi karama ma bata gayawa mata komi da komi akai ba dan harga Allah bataso uncle moh yaji labari bare yay wani abu akai, kanwarsa safiya kuma ya bata kudade itama tanayin nata beaded bag business din agida.

 

hanklin uncle moh ya fara karkata sosai wajen batun fayyace ma ayaana sirrin dake zuciyarsa da zimman next year tana gama secndry school sai aurensu, haka kawai ya tsira nunawa anty safeerah wata kalar soyayya me ratsa zuciya kudinsa yake zuba mata har kamr baisonsu trying to trap her dan kar yazo ya kawo batun aure ta kawo masa matsala dan ji yake babu amount of borin da zata masa da zaicanja shi ya fasa auren ayanah musmn ma yanxu dayaga ta bude ido ta wayewa sosai


the same week ayaana tafara lura da wasu dabiun ruthy da bata gane musu ba, dan dacan dai ta dauka kasancewarta ba musulma ba yasa take harka da maza but now is becming totally difenrt wasu irin mata da gayu take harka dasu kmr yan cult, nd it feels like she is sleeping with both of them. saidai abune da ta kasa samun wani evidence akansu dan ruthy bata sakewa ayaanah tazo dakinta ga tana aikata wasu abubuwa da ba daidai ba. ita ta koya ma ayaana abubuwa da da wuyane akoya mata su a gida kmr su amfanin saka jigida, full nd elaborated explanation of what female libido is, vaginal care,art of seduction da sexual feelings,har yadda ake aski na maza, she will alwys tell ayana ai intay aure wyann abubuwan zasu mata amfani musmn ma da ynxu da iyawa matan bariki suke kwace zuciyar mazajen wasu, ruthy ta jima tana so ayaanah ta fito fili ta bata labarin alaqarta da uncle moh in aurensa zatay dagaske saita nuna mata hanyar da zatay handling babban mutum dan tunda suke da ita ta lura kmr shine yake yawan bata kayan duniya da kudi amma kuma haryau sai taga ayaanan kmr hanklin ta ma bai kasan gabaki daya. 


ayaana bata wani jin maganan kowa inba na ibaad ba, ruthy ta kasa gane mata sam gani take kamar game dinta agefe amma kuma tafi damuwa da wani daban wanda yake da budurwansa da zai aura.


Har ila yau, Rayuwa sosai ta sauyin bazata wa ayaanah. wanda ya santa a shekaru biyu da suka shude bazai taba yarda da cewa ita din bace yanzu cikin sauki dan kuwa wayewar da tay ynx ya bala'in amsar tsarin jikinta ya saka mata kamiya da nitsuwa da kwanciyar hankali, ko fatar jikinta ma dayaji isashhen kulawa, motsa jiki hutu,da ingantaccun Abinci tuni jikinta ya warware ya dau wani irin haske da kyalli kibane kawai batayi sosai ba amma babu wani abu ajikinta na girma da bayyana ba


Wani irin tsabar kyaunta na tun usuli shiya soma hargowan fallasa kansa a fili kamar wanda dama a matse yake daya fito sarari,ba aufi tun tana ss2 din tan tasoma dawowa babban mace cikin cikakkiyar  hanklinta Dadin karawa da yanzu ta cire tunanin komi da kowa aranta takuma dora dammaran kai rayuwarta gaba shikenan taji rayuwa yana mata sauki,bayan tallafawar tarbiyansu ammi karama karatun novels din da takeyi shima ya balai'n taka rawa sosai wajen cire ma zuciyarta tsoron tunkarar rayuwarta na nan gaba duk dama Labarin novels baicika zamtowa gaskiya ba amma yana taimka mata wajen social nd mental awarenesss da samun ilimi game da wasu rudaddiyar matsalar dake addabar rayuwar ya mace koma na wani daban na kusa dashi, Hatta kulthum saida ta komo baya tana shan mamakin irin tarin ilimin ayaanah yarinyar a mugun nitse take,kuma tana kkrin perceving knowledge dinta in a very sensible and matured manner sam sam batada ragon azanci, wanda za'a iya alakanta yiyuwar hakan,a sababin challenges din da tacikaro dasu masu nauyi da wuyar dauka a rayuwa. ko ita dakanta batayi tsammanin zata kai wayann shekarun batare da taga mamanta ko addanta ba.



kwance tashi babu wuya karatu ya fara rike zainab arifah sosai yawan dawowarta nigeria duba ibaad sai ya ragu sosai, dan akwaita da son taga tafi kowa ilimi kuma can columbia university na manhattan kusan makarant ce da ake ji da ita a duniya mostly geniuses da gifted student ne kawai ke iya zuwa can dan haka kusan dolene yasata nitsu danta faranta ma babanta ransa kamr kullum


...all this time tun bayan graduation din xainab sau daya tall prof xayyanu yaje shago ya gaida hajiya mairo wanda rabi hayaniya kawai suka kare dashi, koda ta masa maganan yan uwansa da shiga dangi sai yace mata ita ta wareshi kuma yan uwansa dama arxkin sa suke so bashi ba, duk nasihar da zata masa ahaka maganan nasu yake karewa, shine me lefin amma yafita playing victim card da kyar da wahala ya turo hajiya hamida tazo ran juma'a da goma na arziki ta gaishe da hajy mairo agida wanda tun daga ranar basu kara dawowa gidan ko sun kirata awaya ba.


rayuwa ya cigaba da haka ibaad yana kammala exam yafara batun housamnship ayaana tana kkrin zuwa ss3 saiya bude personal business dinsa a kasar waje him nd his friends are lowkey conjuring 400+ millions every month his life had completely changed u cant even recognise him ryt now, wasu harkan ma ta wajen connectiomn dinsa yake samar wa bappansa upper hand a international business. 


it was miracolous how life can completely change with the ryt ppl, ryt netwking, nd ryt connections batare da ansha wahala sosai ba. kudi yake dashi ynxu wanda shikansa bai nitsu yasan nawa ya tara ba


da shi da abokansa sun dawo wasu kala na daban irin hot gentle guys dinnan da zakama ji tsoron hada hanya da su, farhan yay gemu all over his face yana kuma kitso shima yana managing wani branch na bank in babansa acan sydney yanxu, prince hassan kuma shima this year zaiy aure yana tech business personally ya bude kamfani fin tech, jamal is already running companies nd fathering a 1yr old baby boy da matar sa mufeeda ta haifa masa. ibaad had this upgraded john abrahams body structure not too big and not close to skinny kuma shi yana da tsayi, he is a bit muscular and very strong shi baiya tara gemu me yawa kamr na farhan saidai sajensa is alwys neatly caved, kansa a low cut yake bari. his skin is as smooth nd clean like a baby. duk ranar dayazo gidan haka kulthum da sultana zasuyi ta hot body crushing akansa while ayaanah had deeply fallen in love with him..


duk dama babu wanda yake kulawa da rayuwarta kamr shi, ita dai haryau bata cire tsoro da fargaban zata iya rasashi wa zainab arifah ba..


kwance tashi ayana da sultana da kulthum suka dawo hadaddun yan mata kuma haryau safiya bata sakewa ta hada hanyarta dasu, soyayya me sanyi da dadi kulthum sukey da maheer d distance make them addicted to each oda on phone, video calls, chat, kuma duk abunda takeso yana tura mata sultana tafara kula saurayinta ahmed waziri sama sama wanda a schl ne ma kadai suke haduwa. 


this year zasu shiga 200 level, ayaana kuma tana first term ss3 ranar asabar anzo wknds kwasam bappa zaidu ya shigo ma hajy da su uncle moh da maganan auren kulthum da maheer kai tsaye tunda bazai jima ba zai dawo dan yasamu ma wani aiki a malaysia already


 ..kamar da wasa aka fara maganan uncle moh bai damu ba da murna yace in har kulthum ta amince toh shima ya amince dan yafi aminta ma da maheer sosai...


cikin kankanin lokaci su anty safeerah suka ji ta bakin kulthum har saida aka gamsu da komi snn aka fara batun aure, it was like the smoothest weding proposal agidan kowa is okay with it dan hannu biyu ammi babba ta amince sanin cewa anty safera da uncle moh suna dashi, kuma kulthum din yar gata ce she have noting to loose kwata kwata wata uku su bappa suka saka rana nan aka fara shirye shirye, kawayen amarya su ukunsu sukayi meeting aka bawa sultana babban kawa ayaana kuma itace incharge na girls bridal shower event da zasu hada as usual ruthy ta kira tana tayata siye siyen kayan bridal shower da kayan da zasu saka, while sultana suna shirye shiyen kayann amarya na dinner, kamu da su dinki da su anko da sazu saka a hidiman biki...


Tunda aka fara ma amarya shiri ta koma yawancin zamanta tare da hajiya mairo a nan family house, in ana zaune kullum cewa take gidan zaidu yafara fin karfinta dan tunda aka saka ranar auren maheer ammi babba ta kunce ma bappa zaidu salo salo na shafin hauka, kullu yaumin sai tay zage zage ta kirasa munafuki, kai hatta maheer dinma zagin shi takeyi tana cewa ana munafurtan ta, badon komi sai gani datay kusan rabin shirin auren da ammi karama akeyin komi, ita kuma ko kadan batason fatima ta shiga mata hidimar auren danta, shikuma maheer yasan ammi babba sam bata iya muamala da jama'a ba baison ranar aurensa yaji kunya shiyasa ya nace dole dole sai ammi fatima ta shige masa gaba, koda tazo taji labarin cewa ma da shawara ammi karama maheer zaiy auren nan bakaramin zage zage tay ba..


iya bakin kkri hajy mairo tay wajen sasanta su amma ina haryau ammi babba a haukace take tana jin haushin kowa dan haka tace lallai lallai itace za'a barmata batun hada akwatunan aure


haka ta tara gang din kawayenta su hajy ramatu haka maheer ya siya boxes dinsa snn yafara turo mata kudi tana sayan abubuwa wasu abubuwan oder yakeyi ya saidai taga an kawo. tsabar zugin kawaye wani irin kayan fitar hankli suka dinga sawa sabida kar ace fatima tafita ko ita bata dashi..haryau bata gama warkewa da dumbin baqin cikin datake shaka awajen bappa zaidu ba cos she knew shine yake sponsoring din rayuwar fatima da kudadensa ta rasa wani irin asiri fatima tay ma mijinta dan ko ita baiya kashe mata kudaden dayake kashewa fatima a boye.


hajiy mairo dataga bazata iya solving wann case din ba yasa ta tattaro ta dawo family house domin shirya amarya Saidai shirin tasu ba irin tamu ta zamani bane,irin shirintasu ce ta al'ada ta yadda za'abi salo salo wajen kakkabo da ni'imar ya mace wanda basai an shashsha wani wahalar banza wajen shaye shayen maganin mata ba.


Tun cikin wnn watar farkon acikin watannni ukun nan da ya kama hajy mairo ta sauya ma kulthum routine din cin abincinta,yanzu kaff abin cinta sun dawo na asalin fresh fresh ganyayyaki da kayan marmari da hadaddun kunun daƙa asalin dakan tsakar gida na turmi,vgero,waken suya,gyada mai yaya, Ridi,alkama da makamantan su kala kala masu nunnuƙe da kayan yaji kanun fari masoro,kajiji harda busasshen dankwalin hausa, domin hade jikin mace,da tsassafo da ni'ima da kuma bulbulo da komi najikinta ciki da waje.


yanzu kusan awajen hajya mairo kulthum ta take wuni safe da rana wani bin bacci ne kawai ke kawo ta cikin gida


anty safeera batace musu komi sabida ta lura wann ba huruminta ba ne haryau da akwai wnn kunyan bata son ta wuce iyakarta akai. Gefe kawai tay itama tana nata shirye shiryen ata gefen ta kyale kulthum da hajiya mairo


Babban aminiyar hajy  mairo wato hajy hajara wanda kusan kullum tana zuwa gidan suyi budurin su akan kulthum atare babbar mace ce datasan ilimin al'ada irin tsoffin matan nan ne da anga jiya anga yau..ansan komi.


Dan tunma kafin su fara shirya amarya ita tasoma kawo shawararin cewa abi da yarinya a sassafa sassafa acewarta takurawar da akeyi ma ƴa mace inzata gidan aure a dura mata wann abata wann shine babban makasudin dayake jawo mata matsala acikin zamantakewar auren ta a nan gaba musamman ma wann zamani da yawancin kayan gyaran na emrgency ne bana din din din ba,in yay ne yayi lasting zuwa wata uku wata shida,ko shekara guda amma daga an haihu kuma shikenan komi ya lalace kenan sai anyi dagaske asake dawowa zam zam Kafin nan kuma sai kaga yarinya har ta shiga damuwar ganin sauyawa atattare da mijinta Batare da yin la'akari da cewa shidan adam in ya samu dadi, anan gaba na wanda yafi dadin da ya samu abaya zai nema ba.


Hakan yasaka amfani da magungunan mata batare da karato hikima da basira aciki ba yake da mummunan hatsari ga rayuwar ya mace 


daga zarar miji yaji zaƙinki tun kina amarya, bazai karayin la'akari da yau da gobe ba a kullum bukatarsa shine kirika kara masa zaki yau yajiki fiye da jiya gobe ma yajiki fiye da nau wann shine burin kowani da namiji.


Dan haka yasa suka dauki hanyar bida jikin kulthum ta hanyar da baza akai ga wann matakin ba,babu wani maganin mata da suka siya face yan tarkacen hade haden su na wanke infection,da dumama cikin jiki da farji da kuma duk wani matakin da zai kauda zubar ruwan gaba 


Sirrintaccen hadinta na furen tumfafiya da aka wankeshi tas aka dakashi da mazrkwala masu kyau kamar falle

Guda biyu,sai dabino shima mai kyau kamr rabin gwangwani haka da kaninfari maiqamshi cokali guda da citttan ta daidai misali Duka wannan hadin aka dakesu lugwi suka dawo gari. In za'tay mata amfani dashi sai an gurza kwakwa snn a jika a ruwa ta jiku sosai snn sai tace ruwan kwakwar a kofi,toh da hadin wannn garin da ruwan kwakwar za'a tafasu daga ya dan huce kadan sai bata ta sha.


Wnnan hadin mai tasirine mai saka mace taji tana hadewa tana matsewa taciki,yana matukar kakkabo da sha'awa da niima shiyasa Bai wuce sau daya sau biyu suke mata acikin sati ba.


Sai yan tarkacen markaddan kankana dabino da gwanda da zuma,ko markaddden ayaba a zubamai zuma aciki abata tasha.


Ta hada kayan sauko da ni'ima da kara dadin wajen daban wanda dama hade haden yayan itacuwa na fruits su suka taka muhimmayar rawa aciki sede wasu fruits din ba kasafai aka cika samun su ba saita sha wahalan aikawa a jos ko can ta wajen inyamurai sannan sukanyi excises din jikin ta sosai,sai yan daidai kun supplements kamr su sweet root of peruvian viagra da asalin tsumin goron tula.


To Tasan yarinyarta virgin ce duk dama da sauran sit bath da hajiya hajara ta riga ta bayar wanda tasan zasu matseta amma anan hajy mairo saita ragesu wasu abubuwan xuwa nan gaba Aganin ta in kulthum ta matse sosai abunfa bazai zo ya musu kyau ba dan haka kayan matsi basuda da yawa acikin kayan gyaran ta.


..kuma duk wani abu na amfanin mata me kyau na zamani duk ta dan siya mata na tsuguno na wanka duk ta sata agaba, Shirin datake mata irin wanda za'aji tane zam zam bakamar ko wacce mace ba. sauran kuma aka dan tarkata aka mata guzuri dasu.


mujaheed was so busy a ranakun yana taya mamansa abubuwan shirye shiryen biki

kusan ibaad ne yake yin komi gameda fannin ango duk wani hidiman kayan sawa and all what is needed na ango shi kadansa yakey tareda shi da prince hassan zarko dake sukadaine ynxu a nigeria farhan da jamal kuma suna kasar waje sai lkcin biki zasu taho.


ata fannin kawayen amarya kuwa abubuwa basuyi ma ayaana tsauri ba dake tana tare da ruthy suna aiwatar da kominsu atare wata rana har kwana sukeyi atare agidan ko taje ta jima a dakin ruthy.


ana shigowa month din bikin shiri yay nisa amincewa da shakuwa yafara shiga tsakanin sultana da saurayinta ahmad waziri yadda taga ana ma kulthum yasa itama tafara jin kamar bazata wani jima ba zatace masa yes kawai ya turo itama tay auren nan. he is very calm and loyal to her, duk wani yawace yawace da saya sayen biki yana makale da ita duk dama yaa ibaad ya saka mata ido ya hanata hirar dare ko yawo da sauri a mota anyhow yawanci abu sai taje school suke samun daman yinsa hankali kwance.


Burnt Orange da,Chocolate Brown da,Gold aka fitar kalolin biki dana anko dana komi ba kawaye ne zasu daka burnt orange da golden head, iyaye kuma zasu saka golden attires da chokolate brown head, maza da sauran tarkacen famiy kuma they stand btwn gold nd chokolate brown....


3 weeks to the weding ne birthdayn saurayin sultana yace mata kaninsa usman ne zai shirya masa cake cutting party kyma yana so ta halarci wajen koda na 5 minutes ne a farko bata amince ba amma dataga ya nace  sai kawai ta amince masa cewa sai ta tambaye gida in anbarta taje kwana a wekdns family house zata iya fita da dare batare da kowa ya sani ba..


sabida aminta da son datake ma ahmad ta roka bappa zaidu ya barta akan zata kwna takai ranar sunday a family house, sartuday night ne birthday partyn daga kulthum sai ayaana kawai ta gayawa gaskiyar inda zataje..


bayan anzo wkends an watse around 8pm sultana ta shirya zuwa birthday ayaana da kulthum suka rakata waje batare da anganosu ba...30 min kawai tace musu zatay by 9.30-10 dai suka saka ran zata nemesu suzo su shigo da ita amma inaaa


9.30 ya wuce 10 yay har ya wuce akazo kan 11 ayaanah ta dinga kirar layin sultana yana ringing amma ba adauka ba hanklinsu in yay dubu ya tashi suka rasa abunda yake musu dadi, tana kira kulthum tana kira wasa wasa har 2pm na dare basu ga sultana ba karshe ma sukaji wayarta akashe tsabar sun damu har kuka sai da sukasha subiyunsu a daki tsoro ya gama cika zuciyarsu...da har sun yanke hukuncin cewa kafin asubah zasu fito su gayawa ya mjaheed sai caraf suga text message dinta na cewa tana waje...da wani irin speed suka fito cikin sanda hanklnsu bai kara tashi ba saida su ganta babu takalmi babu dan kwali daga ita sai wayarta jikinta na rawa sosai. kafin su iso dakin gabansu ya gama faduwa, saida sultana tasha kuka snn ta fara basu labarin cewa ai set up ne, kaninshi faisal ya saka musu kwaya a drink ya dauke hotonan su akan gado half naked awaya yana threatning dinsu akan zai watsasu..


how they both wake up confuse tayita kuka harta fasa masa kai da flower verse ta zazzgeshi shima yayita kuka... she told them how he confront his bro har ya masa duka agabanta saishi kuma ya fadi gaskiya cewa ai mum dinsa ne tace ya lalata masa rayuwa sabida kar azo a bashi sarauta

 ...she was recording cos she was shocked of the betrayal yadda ahamd din ya saka yaron aransa sosai


iya abunda yasa su ayaana jin relieve kenan but they are scared, angry nd confused.  ta basu labari har inda ahmad ya rakota waje yana bata hakri yana mata bayani and how she  regret trusting him while he let his family problem push him to black mail her kawai ita bata son ta sake gann fusknsa, she came home cold nd crying  she even played the audio recoding for them. sukayi ta kuka then she demand they kept it as secret har saita samu mafita satin gabaki daya basa cikin hayyancinsu dan har vaginity test sun rakata tayi.


kullum ahmd zai kira ta amma bata daukawa, he came one time ana daf da bikin kulthum, dakyr suka roqeta ta kulashi nd he told her yayi bincike akan magana anma kama mum din faisal tana zuba asiri ma sarki she is custody now..nd he want to ask for her permission ko zai iya fadan abunda ya faru tsakaninsu ma sarki koda baza abashi aurenta ba he want to get justice for her since his bro is trying to expose them to get his mom out..


yace gara ace shiya fara kai maganan da kaninsa yakai yadai kalallameta she was just crying, then later told him koda yakai karar tan will it be enuf to save her dignity? baya tunanin idan iyayenta suka sani, ko yayunta sukaji ta fita da dare taje wajensa zasu kasheta, she put her self at risk ne sabida ta yarda dashi nd she loved him so much...kamar xai kuka yale amsata with more intense love duk agabansu ayaana akayi suma suna hawaye yadda ahamd din ya dinga rokon sultana yana bata haquri


sai can ayana ta jawota sukayi magana agefe suka tattauna posble out come nd plans. then they decide akan tace masa zuwa anjima she wll make her decison nd call him


bayan tagaya masa yana tafiya sukaje daki suka karasa tattaunawa, then da dare ta tura masa text saiya kirata tace tana da solution da zata basa na kare kansa daga sharrin faisal bro din, amma sai ya mata alkwarin cewa he wll only use that to keep him silent..amma bawai ya tona musu asiri ba..he beg nd gave her his word....dacan ma harta fasa sabida tsoro daga baya kuma da safe saita tura masa recording audio da video..she blocked him a chat din ryt away, yakira ma bata daukawa but he still send her text every day da kyar su ayaana suka ta rokonta akan tabashi snd chance musmmn ma since the plan was succesfl kuma faisal da mum dinsa ma ansaketa an kulleta shikuma yabar kasa. dakyar sultana ta iya yafe maganan ya rufu and ever since shima ya fara batun zai turo asan dashi agida tace masa bayanxu ba sai angama auren yayanta tukuna...


case din daya dauke musu hankli a satin kenan basu ma san da cewa zainab arifah itama ta dawo nigeria domin halattar biki ba


dacan anata cewa baza'a tara jama'a kafin kace wani abu satin biki anfara cika musu gida dan Acikin mutanen da anty safeera ta sanar da su iya wanda suke close da itane sosai,sai relations yan uwanta na nesa da kusa da kuma few colleques dinta na wajen aiki da suke kud da kud


hajiya mairoce dai ta taro mutanen ta birni da kauye,dan wasu na kusa da itan ma a sashen ta suka tare tun ana saura sati daya hidima ana shirye shiryen bidirin biki.


Tun abu na kamar wasa saida yan uwan anty safeera sukazo sukasaka shirye shiryen ya wuce tunanin jama'a abu yana nema ya dawo wani babban hidima dan kuwa bakaramin naira ake ta narkawa awajen tsare tsaren hidindimon da za'ayi ba.


Programes kala uku wanda ba'aza somayin su ba sai ana saura kwana uku da zuwan ango nigeria,dan hakama yasa aka buga invitation card tun wuri aka babbawa wanda ake son su hallici wajen taron wanda mafi akasari mata ne

,mazajen da aka gayyata basufi a kirga ba yawanci ma abokan mahaifinsa ne da wanda ake mutunci dasu sosai.


Day one na budirin bikin da wankan amarya aka fara tradional bridal wash colour of the moments was brown nd gold, akayi decorating cikin gidan aka kawata shi da ado irin na al'adun indiyawa ga tabarman alfarma masu shegen kyau Inda sisters da anties din anty safeera kowa ya dauki nashi sashen hidiman da zai kula dashi.


Ranar wankan amarya aka gayyato tradional beauty nd spa artist dinta tundaga ƙasar sudan saidai ita irin asalinta yar buzuwa ce din nan, hadin gambizar niger da kuma ƙasar sudan din,itama da mukrabbanta tazo gidan aka tara mata ana yan raye raye na al'ada akayi ma amarya traditional spa,waxing etc,snn aka mata wankan madara da caramel dilka, da wani irin kwabin skin mask Bayan an gama wanka har 12 dare aka kai ana mata tsumi da kayan qamshi.


Tun ba aje ko ina ba jikin kulthum da kawayenta ya fara fidda wasu irin rikitattun qamshin turaruka tun daga tsakar kanta qamshi hartafin kafafunta qamshi ne mai tsananin dadi yake fitarwa.


Washe gari sassafe haka aka sake taron bridal sitting inda aka tsantsara ma amarya lallen heena ja da baki a hannu da kafafu masu mugun daukar hankli, duk wanda yazo wajen shima saida aka zana masa nasa a hannunsa..


Tun daga rana na biyu manyan mata da antys suka fara ma amarya nasiha da hudubar zaman aure da wani dan karamin Al'adan su da sukeyi kamar budan kai,wanda saida yammacan akayiwa mata kwalliya ta saka golden chantilly lace dinta mai matching color design na amina muaddi heel cover shoes da purse dinshi,an mata kwalliyarta nude kamar dai yadda take so mai daukar numfashi taji gwalagwalen nan wuya da hannu bakaramin kyau tayi ba.


Wani babban mayafi mai sharara dogo aka mata rufi dashi duk inda tabi qamshine mai ratsa zuciya yake ragowa awajen,few schl mates dinta data gayyata wanda basufi su uku ba su suka dan tssattsaya mata akayi program din kamar budan kai.


Yan uwan miji bayan sun mammana mata kudi suka kawo mata kyautuka Snn aka bude fuskanta a sarari kowa ya kalla.


daren ranar maheer ya dawo suka zauna a wani babban hotel, both his freinds and ibaad's friends su goma cass

aka kwana tare.


Washe gari Ranar juma'a ne randa aka saka ranar daurin aure, da dare kuma sai dinner early morning 11:30 saturday za'ayo budan kai snn akai amarya.


yauma bakaramin kyau amarya tayi ba makeup artist sun tsantsara mata wani nude nd breathtaking kwalliya bakinta na wani irin shining da lipsgloss, ta saka wani tsadadden white lacy flowing weding gown mai cuts nd ruffle neck da dogon hannu

,kayan is so decent nd damn classy mayafinshi shima transparent ne har kasa yakeja yana sharar kasa,bayan nan komi na jikinta da akayi pairing silver colour ne...


angwaye suka saka grizzly sand colour shaddoji amma gare dukansu suka dinka ango ne kawai yasaka pure white ana gama daurin aure sukayo wata gawutacciyar liyafa acikin wani babban hall inda duk wasu mazajen da uncle moh ya gayyato suka hallara aka ci aka sha aka babba da souviernies wa baki


can angwaye suka rako shi gida yazo yay gaisuwa kafin nan aka fito da amarya da kawayenta sunsha kyau bana kadan ba,ayaana da kulthum sukasa chokolate brown colour aka musu nasiha bayan manya sun fita aka barsu duk wani surutun ango da amarya da akayi ayaanah bata dago kai ba hakama ibaad baice uffan ba har suka gama suka fita, he was just noticing yadda mujaheed yake ta daukar hoto da ayaanah, lkcin abokansa duka suna falon hajiy mairo anata surutu zainab arifah tazo ta zauna acikinsu dan bata taba ganin abokan ibaad ba sai yau and she is dying for him to introduce her to them to shikadaine bayanan anan, yana can sashen amminsa shikadai a daki ya cire garensa yana business call, yana gama kammala wayar cikin sauke ajiyan zuciya ya rubuta text ya tura ma ayaana akan ta kawo masa abinci daki yanxun nan. 


ganin text din yasa ta raba kanta da fitinar mujaheed tace masa ana kiranta aciki, tajuya zata koma ciki kenan cikin sauri sai ga safiya suna hade ido tace " ke..uncle moh yana kiranki acan falonsa waikije yanzu nan yana tare da abokansa acan...


Tun safiya bata gama rufe baki ba ayaanah tace kije jice masa baki ganni ba  tana fadin haka tay sauri ta wuce cikin gida, 


sashen Ammi karama ta nufa tana tafiya tana gyara zaman veil dinta dan irin dinkin me fallen neck dinnan aka mata mekyau batasaka komi a wuyarta ba


wani irin shiru sashen ya dauka dake ammi tana tare da sauran jama'u a sashen hajya mairo ga frend in ibaad dana maheer an cika wajen da surutu zainab arifah ce kadai acikinsu kafin mujaheed shima ya jonasu...


jin shirun yay yawa kai tsaye ta nufi dakinsa dan ta duba shi, ahnkli ta turo kofar kirjinta na bugawa ahnkki ta tsaya cak daga kofa tana hango fara kal din singlet dinsa ya kwanta adan rigingine dagashi sai singlet din sai doguwar wandon shaddansa na daurin aure da bai cire ba.


kai tsaye wannn qamshin jikinsa me ratsa zuciya ya danne nata qamshin duk dama jiya wuni sukayi ana musu turare cikin daidatu makanta nitsuwa tay sallama me sanyi ahnkli taga ya juyo suna hade ido irin sihirtaccen kallo daya bita dashi yasa tabi ta sunkuyar dakanta kasa da sauri...ya amsa sallamar 

ya zuba mata ido gabanta na faduwa ahnkli ta karaso gaban gadon har zata tsuguna yabi ya saka hannunsa ya fixgota bazata tajita azaune kusa daf dashi...


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[04/12, 20:36] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahms.



To All my group members i heart you❤️💋



⏯️3️⃣7️⃣

tanajinta daf dashi atake wani irin sihirtaccen ajiyan zuciya ya kufce mata inda atake qamshin jikinsu ya gaurayu dana juna yanamai fidda wani irin shauqaqqiyar qamshi me kara sautin bugun zuciya... 

tsikar jikinta duk suka miƙe, jin nauyin mayun ruwan idanunshi daya kafa matasu akanta yana wani irin kallonta camly da kasala atattare dashi, tareda browsing halittar jikinta da  sassanyar ruwan idanunshi masu masifar kashe gabobin jiki da jefa zuciya cikin wani duniyar garari..


bugawa kirjinta yake kamar zai ballo waje, gabaki daya taji ta kasa daga ido ta kalleshi dan kusancin dake tsakanin su yasa take jiyo yadda kirjinsa yake bugawa da karfin gaske..


karamin gyaran murya yay muryansa na fita kasa kasa yace malama sai yanxu kikaga aikan nawa?da kyar ta iya dago rikitattun idanunta ta kalleshi ta marairace murya tace"..i was thinking abt what u may like to eat shine yasa banyi sauri ba..dan karamin scoff yy da cute kamemmiyar smiles dinsa yace okay, toh Deceive me mana!! i knw ure not thinking abt me,ure just busy with ur friends!hmm su, kawar amarya manya! dada sunkuyar dakanta kasa tay cikin turo mai baki ahnkl tace "yaa toh me zan kawo maka kace kanajin yunwa..atakaice yace mata 'something fresh, pancakes or anything but freshly made ko kina wani abune na katseki..da sauri tace "a'a..i am, sai tay shiru, ahankli kuma akunyace tace...anything for you! tana fadin hakan ta miƙe tsaye ganin har yanxu mayun idon sa nakanta tace "i wll be back in 7minutes,..adan kasale ya gyada mata kai..


..wayanta ya hango kusa dashi kmr zai ce mata ta dauka but somthing deep in his hrt force him to keep quiet haka ta fita batay noticing cewa tabar masa wayarta a gefensa ba....


tana fita ya jawo wayar yanayin haske wani hadadden hotonta yagani akan screen din wanda yadau lokaci idonsa na kan hoton baiko kifta ido ba


daga kitchen kuwa ayaana tana shiga ta bude inda ammi take ajiye kayan su hadin pancakes din cos ammi has almost everything in stock wai indai na dafa abinci ne is like cooking is one of her favourite thing a duniyan nan, within minutes ayaanah ta gama kwaba cinnamon pancake with all the love in her heart


batay amfani da sugar ba tasaka masa pure honey da melted butter da asalin liquid milk da wani mayen vanilla flavour. sharply ta fitar da like 6 flaps of pan cakes a wuta, tana gamawa tasaka banana slices akai, tajera chocolate drizzle akn banana slices din carefully snn tabi kansu da pure honey in a stylish wavy drizzles, cikin nitsuwa ta jerasu akan wani white clean plate, atake cikin gaggawa ta dauki juicer ta zuba frozen straw berry ta hada fresh straw berry mint splash with just mint, lime da ice cubes cikin kankanin lokaci tasaka komi akan karamin tray tazo musu dakin nasa dashi...



karamin sallama tay lokacin hanklinsa yay nisa akan wayatta baima ji sallamn ta ba bare ya amsa ta, after 2-3 password trials he sumhow manage to use his name nd open her phone babu inda kuma baishiga ya leka ba sumtings make him go utterly speechless wasu kuma anan ne yagani yake shan mamakin su, like the amont of money da uncle moh yake tura mata, da flirt nd love text messages da mujaheed yake tura mata kowani safiya.



tunda ta leka ta bayansa taga wayarta ne a hannunshi gaban ta ya fadi kadan, how he opens it remain a mystery to her but dake tasan zucyarta awanke yake sai bata damu ba ta karaso, da karamin gyaran murya tace yaa ur food is ready ..qamshin pancake din yaji ya daga kansa suka hade ido ya mata wani irin kallon kishi daya dan tsorata jikinta a dan sanyaye ta taho gabansa ta aje plate din tanajin sautin saukar ajiyan zuciyarsa har yanxu baice mata komi ba da ido kawai ya mata alaman ta zauna kusa dashi tana zama yace" can u help me out with the food..ya nuna mata wayar dan ta gani dakyau.. yace i am busy here..karamin ajiyan zuciya tasauke ahnkli tace "sure...wanke hannunta taje tay ta dawo ta zauna kurkusa da shi, tana daukar pancake din tafara bashi a baki ahnkli yakeci har saida yacinye guda daya snn ya karbi abunshi ya fara ci dakansa yabi ya xuba mata ido yana kallonta da abubuwa aranshi yana tauna pancake din batare da ko kiftawa ba ayayinda ita kuma ta sauke kanta kasa tay shiru da fargaban me zai biyo ba in yagama karewa wayatta tanadi


Ya cigaba da tauna pancake ɗin a hankali every minutes zai juyar da ruwan idanunsa a kanta kamar wani mai karanta cikin zuciyarta


he was busy debating in his hrt, wani abu nace masa kodai ya kama kanshi ne ya basar, ko kawai ya fadi abunda ke cinsa acikin ransa, abazata kuma ya ajiye sauran bite din dake hannunsa a gefe yana jin bazai iya shiru ba, still yana kallonta da irin kallon nan da ya daɗe bai yi mata da wannan zurfin ba.


A hankali ya miƙar da hannunsa ya riko nata hannunn tare da jawo ta kurkusa da shi har saida taji saukar hucin numfashinsa yanamai malala akan kyakyawan fuskarta.


Muryarsa a kimtse yace

..“Ayaana…tana daga ido kafin ta amsa shi cikin kafeta da kallo yace meyene ke faruwa atsakaninki da mujaheed?


tambayar taji ya fado mata a jiki kamar an watsa mata ruwa mai sanyi. ta daga kai a hankali kamr tana son ta yi magana saikuma taji kalmomin da zata furtan duk sun makale mata a maƙoshi.


matsowa ya karay idanunsa tattare da wani irin launin kishi mai hade da rikitaccen kallo

yace“ madam i’m asking you 

“Ki fada min… why is he messaging you good morning my heartbeat every day?..


Ayaana ta rufe idanu tana jin jikinta nayin wani kalar rawa rawa taciki da wani irin shagwabben murya ta buɗe idonta a hankali tace yaaa i dont know..kasan he loves to jokes abt things, ni kuma harga Allah babu abunda ke tsakanina dashi....Ta ɗan yi shiru, tareda matsawa kusa ɗashi sosai nan ya lumshe idonsa ajiyar zuciya mai nauyi yanamai kufce masa ya kura mata ido kamar zai shige cikin ta...ahnkli yace “So ke kince min baruwanki da kowa ko? let me ask you, if he was the one dat ask u to make this for him will you come nd give me? da sauri Ayaana ta girgiza kai a hankali tana dan wasa da yatsun hannunta duk ta kasa kallon cikin idonsa sai ya miƙa hannunsa ahankli ya ɗago fuskarta yasa ta kalleshin na dolen-dole. snn yace “Ayaana.”


kirjinta na bugawa tun kan yay magana tace " i swear babu wani abu dake tsakanina dashi yaya wallh dagaske nake.


A hankali ya janye numfashinsa daga can cikin zuciyarsa ya ce“if u cant give him this pancakes bcos is mine, then stop giving him nd other men what belongs to me for exmple like ur time. yana fadin hakan ya saketa Snn ya ɗauke pancake ɗin yakai bakinsa yana taunawa ahnkl cikin wurga mata wani irin kallon mallaka mai nunnake da shauƙin soyayya me narka jiki da zuciya.


ji tay kamar zata nitse a wajen dan kunya takasa cewa komi wani irin ruwan shauqaqiyar soyayyarshi taji ya lullumeta daga sama har kasanta yana mata yawo duka ilahirin sansanin jininta da jjiyonta yana mata rawa har acikin kwawalwa.


batace masa komi ba face murmushi datake sakewa a kunyace yana gama tauna na bakinsa ta dauki mint splash din ta bashi ya karba yace "thank you" ta gyada kai..yana sha yay hamdala yace..madam take ur phone..tana karba kasar wuyarsa yace nd pls stop cheating nd deceiving me okay..


karamin dariya ya kufce mata cikin sanyin murya tace yaa i am not cheating or deceiving u.


yace hmmm..toh naji..ya kalle agogon sa yace tunda na koshi yakamata muje waje ko


gyada masa kai tay ya miƙa ya jawo rigarsa ya saka itakuma ta tafara tattara empty dishes din.. kafin ta gama ya bude closet dinsa ya dauko wata karamar box dan karamin abun wuya ne aciki dats made of pure gold amma irin mai round neck innan ne kuma rare design me masifar kyau


bakaramin dacewa da kayan jikinta yay ba idonsa nakanta yace "hey..turn around.. tana murmushi ta juya masa, ahnkli

ya matsar da jelar suman ta yabi ya samata abun wuyar wanda ya zauna mata damas akan wuyanta yamata mugun kyau bana kadan ba....


gaban madubi tay ta tsaya tanamai admiring har ya karaso daf da ita yace"did u like it?da sanyin murna a muryanta tace "its perfect

..tana fadin hakan ta ciro wayarta batare da ya shirya ba ta musu mirror selfie cikin basarwa tay kmr bada niyyar ta sakoshi a aciki tayba, irin hoton bazatan nan ne dayay mugun kyau, cos he is wearing his grizzly brown shadda ita kuma chocolate brown material nd they look absoltely perfect nd in love. daga nan har suka fito musu sukeyi akan hoto tace mai sam abun wuyanta kawai ta dauka bashi ba..yayi ta nuna masa taqi sam har ya gaji ya kyaleta.


suna fitowa sarari kuma kamar basu ba, his face remain stiff nd emotionless ita kuma normal take tahowa agefensa dede kofar sashen falon hjya mairo ya tsaya ya leka ciki yace guys ya kamata mu wuce ko..


one by one su jamal sukay sallama da ammi karama, lkcin zainab arifah tashiga daki kara shafa powder sabida ji datay suna maganan wucewa tasan dolene ibaad zai fito she really want him to introduce her to his gangs of frends dataji sun bala'in burgeta sabida wankan ajinsu da swags dinsu na wealthy background


kafin su gama sallama da ammi karama su fito already ya sako ayaana agaba har sunje waje ta gaban motarsa suka tsaya...friends dinsa suna isowa wajen su taji ya kama hannunta calmy ya dada pulling inta by his side yadda zai basu clue she is his special sumone batare da ya furta ba, da sigar tsokana jamal ya kare musu kallo ganin dacewarsu a fili yasa yay murmushi me shegen sanyi yace "ohhh wow finally", da sanyin fara'a ayaana ta fara gaishe su, each one of them with calm respect kowa yagaya mata sunansa da kansa..kai tsaye yace mata these are my best frends..nd guys this is ayaanah...dariya me sanyi farhan yay yace "you mean 'the our ayaanah..ibaad yadan hararesshi prince hassan yace she is perfect!!

hajiya ayaana we are hoping to come for ur own celebration soon..mune kirjin biki aiko..

...murmushi me sanyi tay tadada boye fuskarta ata gefensa abazata tareda kankame hannun ibaad din nata cikin nata hannun sosai..


the air almost stand still nd heavy ayayinda uncle moh da taragon abokansa suka fito waje shima yafito rakasu atake atake yanayinsa ya canza dan baima iya basarwa ya bi ya tsaya cak yadan kuresu da ido, wutar kishi kamar zai fasa kwayar idonsa daya ga yadda ayaanah ta wani irin rike ma ibaad hannu shyly and lovingly kuma tana tsaya daf daf dashi kamr ma zata shige jikinshin daga tsaye...wanda ko kai makaho ne kasan dole ne da wani abu dat is going on awajen musm da abokansa suka famar nuna gamsuwar su da ynyin ayaana sosai..har jamal yanacewa wata rana zai kawo mata matarsa har gida suna gaisawa.


sabida wannan dan uban embrassment din yasa uncle moh yay saurin kauda kansa bai sake abokansa sun dago da wuri ba face Alhaj ameer da already yasan fuskar ayaanah a hoto atake atake jikinsa ya bashi cewa abokinsa baijin dadi kishi har ya sauya ma ruwan idonsa kala cikin rufa masa yay maza suka bar ta wajen suka fita can can waje

...yayi ta basu haquri wai amaryan tashi tayi nisa amma soon zai kawota har gidajensu agaggaisa.


suna rabuwa da aboknsa ya shigo gidan da bacin rai baiko kallesu ba ya wuce ciki ya kira mujaheed yace maza maza yaje ya kira masa ayaanah ynxun nan...mujaheed har yaji tsoro da irin tune din daya masa maganan..ya fito kenan sai ga zainab arifah ta fito a rude suna hade ido tace "hey dan Allah ina gayun nan sukayi? yace ohh ai ibaad yazo sun fita waje halama sun tafi

...da wani irin sauri ta kama hanyar wajen har tana haki tana kuwa hangosu da ayaana ta tsaya cak jin numfashin ta ya dena fita wani abu kamar mashi taji ya cakke ta dagata yadda ibaad ya wani makale ayaana agefensa hannunsa sakale da juna...at that moment da kallon banza na kisa da tuni ta kashe ayaana dashi daga inda take,saida ta gama kare ma yanayinsu kallo da kyar cikin fizgo kanta daga fushin ta karaso wajen su da wani irin murmushin makirci tace "hi..sauran suka mata kallo daya farhan ne kawai ya amsa ta.., tace har zaku tafi awwn..nd i tot we shud get to knw each oda more..tana maganan amma so take tazo kusa da ibaad sai taga ayaana ta daga ido tana kallonsa da wani irin shagwabben ido kusan babu hali takwace hnklinsa daga wajen ayaanah


...zatay magana cikin katseta jamal yace "whats dat ur name ma..anyways. sum oda time in munxo.. da wani irin kinibibi ta takune fuska tace but he dint even introduce us..da karfi tace ibaad...a dan shashance yace ohhh guys this is a cousin sister..prince hassan da already is very irked da kalar rawan kantan a mugun miskilance ya daga hanci sama yace "huhhnn i felt that. ta iya surutu kam, sannunki toh! farhan yadan yi dariya baice komi ba ya kalle ayaana with soft smiles a fuskanshi yace baby gal it was nice meeting u, ayaana tay mrmshi tace pleasures! wani irin rudani zainab arifah taji ya rufeta ta kasa gane komi sai tay shiru


...jamal yace guys ya kamata muje ko..shima ya kalle ayana yace madam we will meet at the dinner, yeah? ahnkli tace yeah..ta kallesu duka da sanyin murya tace thank you i raally apreciate..prince yace pleasues is all ours babygal..


"..ibaad ne ya fara hango mujaheed, yana isowa  ya babbasu jamal hannu akay sai anjima snn ya kalle ayanah yace "softy in kin gama kixo ure needed inside urgently

..ibaad yay kamr zai dago abun sai kuma ya basar ya mata ido akan taje, sallama ta ma su jamal snn tabi mujaheed din abaya cikin sanyin takunta mai daukar hankli basuyi nisa ba mujaheed yace mata babansa ke kiranta a sama snn ya dawo


kamr lost zombie zainab arifah ta tsaya cos they dint really give her an ounce of attention musmn prince da gabaki daya ajin yarinyar bai masa ba..


she is too over confident nd wild for his liking, irin babu nitsuwa da jan aji na mata ajikinta sai sam baison suyi hiransu da ita..ayaana na shiga baifi da minti biyu ba ibaad ya shiga motarsa sauran abokan ma kowa ya shiga nasa motar suka bar gida suka nufi hotel inda ango yake domin a shirya xuwa dinner da dare.. tsaye xainab tay da mujaheed awaje tun bayan tafyarsu take kawo masa sukar ayaana, sai ce masa take ayaana bata da tarbiya, bata da aji tabiyo abokan ibaad ne dan wani acikinsu ya ganta yace yana sonta, ah ah ayaanah is too cheap, ayaana is too fake , bata san meyasa ibaad yake sake mata ba, bla bla bla..suna tsaye awajen ta kirga kagagun lefukan ayaanah sunkai dubu but still bataji zucyarta yaimata sanyi ba.. 


hakanan ta nace mujaheed ya rakata wajen kawayenta su nala acan xata shirya sai suje dinner tare dan tanaso ne no matter what dai abokan ibaad su san da ita she just cant be feeling left out while ayaanah is enjoying all the petings frm ibaad alone.



daga bangaren ayaana kuwa tana isowa ciki already mujaheed daya rakota ya koma waje ya gaya mata babanshi ne yake nemanta a sama


sosai gabanta ya fadi amma sai ta basar cos her heart is too happy abt ibaads gesture for her to feel fear, da dan gwarin gwiwarta ta karasa har sashensa..


tay sallama bai amsa ba harta karaso ciki da ladabi ta tsuguna tace uncle ance kana nema na..


mikewa zaune yay yana mata wani irin kallon bacin rai yace "sai yanxu ne aika na ya isa wajenki..zatay magana ya haura mata "Dont speak when i am speaking..kawai dan kin maidani bansan menakeyi ba kika kama kikaje wajen wanda suka fini muhimmci awajen ki dake baki da kunya ko, is it akan those chewing gum boys zaki share kirana? ayaana kin ban mamaki wallh


fushin da hatsala da yake mata maganan dashi yasa tay shiru batace komi ba for a while sai can tace uncle nifa yanxu ne akace min kana kirana


.. da bacin rai ya mike tsaye "Hey Dont you ever lie to me.. kar ma ki soma maidani bansan menakeyi ba, anan agaban abokaina safiya tace min kince acemin ba aganki ba..i have to pretend, it hurts me.. but i make a joke out of it nace musu safiya batason taje aikin ne kawai tace haka...nd i was calling ur line kinata wani danna min user busy ashe keee kinsan me kikeyi..ure with those chewing gum boys ai dole ne bazaki dauke wayata ba..nd u saw me outside kikay banza dani wai yaushe na fara wasa dake ne ehhh..


hawaye masu zafi ya cika akwayar idanunta sabida fushin da yake mata maganan dashi muryanta na rawa rawa tace  i am sorry uncle, i tot she was joking shiyasa nace mata haka kuma ni ban san ma ranka zai baci ba har haka ba dan Allah kay hakuri...


memakon data fadi hakan ya rage fushin mana sai ma ya cigaba da mata ihu sai hargagi yake yana cewa haba da Allah ayaana kin bani kunya yau wallah..kin kunyatar dani agaban mutane, he was angrily stressing dat he has plans

yace..baki kyautamin ba

snn..bazaku tashi bada hakuri ba sai kinga kun cuce mutum nd please mind urself, kome kikeyi inhar ni ne nace mikizo to maza kizo.. shi ibaad ne waye shi?ai in da kina darajani koda wasa bazaki dauki kirana abun wasa ba.


tunda yafara masifar shiru tay masa batace uffan ba hawayenta na zuba ahnkli, 


he talk , talk, talk..har ya gama batace masa komi ta tashi tana kuka ta fita..


tana ficewan kuma sai yaji hanklinsa ya bala'in tashi, wanda kusan hali ne ajikinsa, he love to over react musmn in abu ya shafi kishi ko wani abu da baixo dede da raayinsa ba..


sashen ammi karama ta nufa takoma dakinta da zafin masifar da yy matan aranta tana gama share hawayenta ta shiga wanka tabi ta doro da alwala tay magrib da isha snn ta sako doguwar hijab ta wuce dakinsu kulthum inda za'a musu shiri na fita dinner tareda amarya, jim kadan aka fara tsantsara musu make up, amarya zata saka champainge gold sukuma wani irin saki ne burnt orange me masifar kyau sukay ankonsa. aka tsantsara musu kwalliya still ayaana ta maida abun wuya da ibaad ya bata a wuyarta dake gwal ne me tsadan gaske kowa sai yaba design in yake bcos of how unique nd simple akayishi babu hayaniya, tuni ta debi kashin uncle moh ta watsar cos she was abslutly feeling herself da abun wuyan nan da yayanta ya bata kowa yake yabawa...


around 10pm aka gama komi kusan kowa xaije wajen dinner biki ammi karama ce kawai bappa zaidu yaqi sam ya amince mata taje wani taron dare dan haka ita da wasu bakinsu tsofi aka bari agidan suka dai. kowa yaga amarya kulthum da abokanta sai an ce tubarkallah masha Allah, so young so beutiful and elegant

kayansu is extremely sophiscated da slay queen styles na dinkunan zamanin nan..


tsabar rawan kai haka zainab arifah ta dinka wata expensive lush material kalar kayan kawaye zak zak dan kawai ta jero da ibaad a bridal train a musu hotona, unfornatly sai shikadai ne bai iso hall din da wuri ba, ya zamana abdlgaffar ne yau zai tsaya a spot din babban abokin ango, addini ya shiga jikin ibaad and it feel odd for him yaja jama'a sallah bada jimawa snn yaxoshi tsakiyar jama'a yana dantse rawa byan bai ma iya rawar ba. 


in oda not to spoil maher day sai ya bar abdl gaffar a spot dinsa he was no where to be found har aka gama shirya train din amarya da ango zasu shige cikin hall kenan zainab arifah ta jirashi har ta gaji sai daga baya ta hakura taje ta mannu da mujaheed suka shiga atare..bayan shigarsun bada jimawa ibaad ya taho ankon fararen kayan sukayi ango kuma yasa brown kusan irinna matarsa bakaramin kyau sukayi ba. table of six six aka bawa duka abokai da kawayen amarya prince hassan yaxo da yar budurwansa yasmine

kaita babanta is a minister she was soo cute too, farhan da jamal agefe, tun kafin ibaad yazo jamal ya kirawo musu aayaanah tana zaune dasu, ibaad yana zuwa table dinsu ya cika..


wani irin haushi da karsashi kamar zai kashe zainab arifah da already ta hakura ta zauna tare da mujaheed da su anty safeera da mum dinta hajy hamida da hidimar dinnern kawai ta iya zuwa dan tasan akwai masu kudi anan xa'a bajintar nuna arxiki...


yau kusan ranan ammi babba ne da kawayenta duk dama sunji mugun haushi da sukaga ammi karama batazo ba dan dagangan suka yi plan na games na truth or dare, quiz, wakokin habaici da wasu shagalinsu na mata da zasu walakanta ammi karama dashi abainar jama'a ita da gang din kawayenta su kusan sunkai sha biyar anci ado kure adaka kamr matayen sarakuna da gwamnoni


haka aka sha shagali

hanklin zainab arifah da uncle moh gabaki daya nakan table din ibaad da ayanaz kowa yana jira daya acikinsu ya tashi, zainab tana Allah Allah ayaana ta mike sai ita ta koma seat inta, she cudnt go dazu sabida abokan ibaad din basu wani bata fuska ba kuma da sukazo ayaana kawai suka jawo jiki, shikuma uncle moh ya rasa yadda xai yi su kebe da ayaanah ya lallabeta ya bata hakurin akan irin abunda ya mata daxu har ya sata kuka..


the waiting seems endless all this while ibaad yaki ya tashi koda xai tashin ma tare da ayaanah suke zuwa sama daga manni sai daukar hoto kuma haka zai sakota agaba tana gefensa har su dawo wajen xamansu atare, here nd der cikin jama'a zakaji ana bala'in ririta gulman dacewarsu..


it was the worst night for xainab arifah tun tana daurewa bata son daukar abun serious har ciwon ta yaso yafara tashi mata, worst not with the way with the way her friend ruqqy is qouting" wann yarinyar kam ta kwace miki saurayi".all the pain has gotten to her neck, duk da uwar notice me da barin kudin manni data dingayi

haka har aka gama dinner arnd 12pm na dare tanaso waikoda ibaad yaganta su gaisa da kawayenta da nashi abokan amma inaa, ashema 11:30 ya sabule ya kai ayaanah gida yace ma abokansa ai tana da ciwon mura wai sanyi zai kamata....


har gidan kuwa yakaita kafin ya dawo hotel few minutes kafin sauran angwaye suka fito washe gari sassafe ya raka jamal har airpot da suvenrs na biki sabida aikin dake gabansa da gaggawa. da shi da su farhan dukka aka gama hidiman budan kai da su da sassafe, sann aka ma kulthum nasiha aka kawota gidan ammi babba, anan za'ayi wuni snn amarya da ango su kwana daya kafin nan washe gari su wuce malaysia atare. .


Ammi babba bakinta har wuya tsabar murnan irin goma na arxikin tsaraba da ta samo abikin nan...not untill dataje tana ma maheer ɓaɓatu ta tsince shi yana waya da ammi karama duk ya daga hankli ita kuma tanata bashi hakurin cewa ai babansa ne ya hanata zuwa dinnern sa amma in sha Allah itace zata fara xuwa gidansa bayan sun wuce malaysia da amaryansa gobe

...daga jin haka kishi ya bi ya rufe ma ammi babba ido..


duk inda bappa zaidu yay sai ta bishi da habaici damuwarta wai baya kishinta fatima dake itace gwall dinsa ai bai sake tay kwalliya taje ta shiga cikin maza tay rawa da dansa ba..


Shareta yay har ta gaji da habaice habaicen tay shiru bai kulata ba..



bayan biki family house yadan yi shiru dedekun bakin nesa ne kawai basu watse ba washe gari da sassafe uncle moh ya dinga tura ma ayaanah text akn taxo ta samesa yana son magana da ita,wanda ko daya bai shiga ba dan tun wajen dinner data lura da take taken sa tabi tay blocking layinsa ta hada da dansa dayake aikowan ma tay blocking..


tun jiyan kuwa mujahed yaso ya nunnata ma abokansa as wife to be dinsa, like he alwys told them shima auren gidan nan dai zaa masa da ayaanah irin yadda akayi na kulhum da maherr, yayita kiranta wajen dinnern nan amma lambarta bai shiga ba kuma althrou yaganta tana tareda ibaad ne wanda kowa yasan ba a ma ibaad irin wann rainin bare yazoshi ya kirata agabansa sai kawai ya basar da komi 


dake tay blocking dinsu both uba da dansa tay baccinta bata ga wani abu da suka turo ba kuma kirar kodayansu bai shiga wayarta ba, kwanan kulthum daya tare da angonta agidan su bappa zaidu yay musu nasiha duk family aka rakasu airpot da yamma suka wuce malaysia atare da zimman few weeks frm now zasu dawo gida sabida krban trnscrpt da sauransu wanda zaa ma kulthum transfer ta koma da karatun can malaysia inda mijinta yake da zama yanxu..


bayan wucewar amarya da ango satin gabaki daya an daukeshi ne wajen kewa da kuma sallaman baqi musmn ma na nesa da sukaxo musu, for good 6 days ayaanah taki sam ta hada hanyarta da su uncle moh, tun bai gane tana dodging insa ba har yaaxo ya gane mujaheed ne kawai hanklnsa yay nisa sabida shine yake yawancin jigilar kai jama'a aiport ko tasha sai bai wani lura da cewa blocking insa ayaana tay ba, he just tot irin mood swing na missing din kulthum ne kawai yake kan damun su ita da sultana bcos they really cried lkcin da kulthum zata bar gida.


daga gefe kuwa uncle moh sosai ya shiga hayyacinsa ya sissiya abubuwan duniya da yawa harda sarkan wata gwal wanda zai lallashe ayaanah dashi dan ta dena fushi su dawo daidai. sam baiyi tsammani dan ya mata fada zata dauke masa wuta haka ba. he was really worried nd remorseful gashi so yake within 8 months frm now tana gama scndry school dinta sai ya shigo ma hajya mairo da batun aurensa da ita..



bayan sati guda da biki anty safeera ta farka da wani irin laulayi dake ta jima tana family planing harga Allah bata masan ciki ya shigeta ba kawai gani tay kominta na canzawa she just left it a matsayin stress ne na bikin yarta datayi


ranar asabar da sassafe ta gaya ma uncle moh cewa batajin dadin jikinta xataje asibiti yace mata bari yay wanka kawai yazo yakaita dakansa a duba masa ita.


dakinta ta nufa dan ta shirya tagama amai kenan sai ga mujaheed ya shigo dubata...


shiya taimaka mata ta kimtsa kanta, lckin duk ta damu sosai harma tafara suspecting cewa koma cikin ne da ita, tafara hawaye tana cewa mujaheed gaskiya batason ta sake haihuwa sabida dakyar take sha kuma gashi ta balain jimawa bata haihu ba zata sha wuya..mujaheed yanata dariya yana lallashinta yana ce mata zata iya, ahaka ahaka har ya shigo mata da batun ayaana


saidai wann karon he was damn serious abt it, yace mata in 1 nd half years zai gama 4yr course nashi daykey a univrsity dan haka yanaso shima yay aure kafin yaje masters a dinsa kasar waje kuma harga Allah ayaana yake so kawai ya aura


anty safeera taji dadin haka, kodan ma kanana kanan zargin dake ginuwa aranta game da alaqar ayaana da uncle moh ya kare akawo ma weird gifts dinsun nan full stop...


tana murmushi tace masa inkuwa ayaana zai aura zata goyamai baya dari bisa dari..


he was soo happy da yanayin yadda anty safeera ta amshi maganan, sharply yace mata zaiyi tunanin yadda sai fito fiki ya gaya ma ayaanahh qudirinsa acikin satin nan ko kafin watan nan ya kare kar kuma wani ya rigasa furtawa.


daga kofa uncle moh yay shiru yana jin duk wani hira da sukeyi gabansa yarinka faduwa yana jin wani irin jiri jiri na shirin kwasarsa daga tsaye


sanin cewa yana da zafin zuciya bazai ma iya jurewa ya kallesu da wanna maganan har a tunkaresa da shi ba yay maza ya fasa shiga dakin ya koma room dinsa ya dauki car key yabar gidan, basu kara ganinsa ba, duk kirar data masa saican ya tura mata text yace mata "urgency ne ya fitar dashi, kawai taje asibitin ita daya inya dawo zaizo yaji.


awajen abokinsa ya wuni wajen neman mafita., ita kuwa tun da laulayi ya lafa ta debi kashin asibiti ta watsar bataje ba, kowa ya hallara akayi wkends babu uncle moh ranar agidan gabaki daya sai can dare ya dawo nan ma bai kula kowa ba ya kulle kansa a daki cikin tunanin shawarar da alhaj ameer ya bashi na tura mujaheed karatu wani kasa tareda saka masa sharudan cewa bai amince yay aure ba sai ya kammala har matakin masters dinsa da niyar kafin nan ya dawo ai riga y aure ayaanah sai kuma yaga ta tsiyan.


zainab arifah ta musu sallama, itama tabar nigeria ranar sunday da matsancnin damuwr ayaana a ranta..



bayan kamar sati biyu masu kyau da kammala bikin kulthum lokacin komi na gidan ya fara dawowa daidai ranar alhamis da yamma ayaana ta dawo daga lesson wanka kawai tay ta saka doguwar rigan atampa holland dark green colour ya mata kyau sosai ta daura dankwali, kunun madara me dumi da ammi karama tay ta dauka tazauna tana sha gidan yay shiru she was just wondering yaushe ammi karamn zata dawo daga aiki dan tunda kulthum ta bar gida she have been lonely dake safiya bata ma kulata ita dayanta yanxu take zama inba dai chating sukeyi da sultana awaya ba....


toh yanxu ita kanta sultanan bata da wani time sosai sabida soyayyarta da ahmd ya kara yin karfi ya dage da batun zai shigo gida da maganan aure.



ayaanah tagama shan kunun ta kenan har zata danna ma ammi karama kira tamata shagwaba caraf sai ga safiya ta shigo suna hade ido tace ke ayaanah hajiya tana kiranki acan shashenta ta ni kiy sauri kifita kallon series zanyi tun kafin ammi ta dawo ki hada mun makrcin dakika saba..


ayaana batace mata uffan ba ta bar wayarta anan daga ita sai dankwalinta data kifa akan doguwar sumanta ta wuce sashen hajya mairo,...


tana isa ta bakin kofar ta tsaya cak musmmn da taji muryan uncle moh ne ata ciki suna magana da hajiya mairo yi tay kamr zata juya ta koma sai kuma she cant run away from him forever gara dai tay facing issure din, ita haka kawai de takejin batawani son ta cigaba da tarayya dashi,koma meyene intention dinsa kawai gara ta hakura, kwana biyun nan data guje shi ya zamana da babu shi arayuwarta bakaramin kwanciyar hankli ta samu aranta ba.


dakyr ta tattaro makanta nitsuwa tay sallama a nitse ta shigo babban falon wanda tun shigowarta wnn dan uban qamshin turaren wutar dake mamayrta ya sa ya zuba mata idanunsa har ta karaso ta zauna kasa cikin nitsuwa


fuskarnta a basake ba murya kasa kasa tace "ina wuni uncle...yay wata yake yace lafiya dear yaya kike..kafin ya dora tace" hajy ke kika aika nazo??" cikin kyabe baki..haj mairo tace o.. o..o ..o dama muhammadu ne yazo min da wata magana, yace ranar daga miki fada kawai kika hau dokin zuciya kika dena gaishesa waike kina fushi dashi, yoh inbanda kinsamu kansu suna shagwaba ki har ke kin isa babban mutum dayakai ya haifi biyun ki ya miki fada kihau fushi dashi kudai rinka ma kanku fada ayaanah


muryanta kasa kasa tace "hajy nifa banyi fushi da kowa ba


"to toh muhammadu kaji ai agabanka ta karyata ka,ikon Allah ayaanah ashe haka kike baki da kunya?


cikin katsesu yana wani irin sum sum yace aah hajiya karki mata fada dan Allah. ai leifina ne da ban tsaya na lura da uzurinta ba...ayaana dear, i am sorry kinji ko i shundt have shouted at you ranar kiyi hakuri kinji dear


hajy ta nuna masa yatsa kai muhammadu ya isheka haka, akan me? ita awaye da zaka zo kana wani langwasa mata murya..ba kirarta kay ranar tay banza dakai ba shone kuma kaine zakazo kana bata hakuri..daka mata fadan sai me? waye ke moruwa dakai inba ita ba, har wani fushi kika tsira da manyan ki..lallai tab di jamm...irin tarbiyan da kuke basu kenan, basu darajaku yanxu ke ayaana ko duka muhammadu ya miki shi ba' kusan asar ubanki bane.? tunda ya kai haifeki ai sa'an ubanki ne marar kunya kawai taɓabbiya. maza maza ki bashi hakuri bana son iskanci da bude idon banza da wofi.


muryan ayaana na rawa rawa tace "kayi hakuri uncle nifa ban rainaka ba..ranar naga kanata masifa ne shiyasa sai bance komi ba amma ni ban raina ka ba


yadda ayaana tay maganan da bacin rai hajiya ta harxuka tace 'ke da Allah karya kikeyi inba raeni ba meye ne..kice kawai kina dai tare da ubanki rayyanu bazaki iya saba masa ba dake ya hure miki kunne kina raina manyan gidan nan kamar yadda shima yake raina uban kowa.. toh muhammadu ya gaya min komi, ince dai akan shi rayyanun ne kikaki zuwa kirar da ya miki ranar? toh wllh wallah ahir dinki da raina min ɗana akan rayyanu, dan kinga yana sake miki.. yana tausayin rayuwarki toh wallah bazaki hada kai da rayyyanu kuna walakanta shi ba..tunda kikazo garin nan meye muhamadu ya ke miki inba alheri da rufin asiri ba...snn kece ynxu zaki tsiro masa da iskanci da rashin kunya har wani kina fushi dashi kajimun shashasha marar hankli toh wllh karna sake jin haka


kaikuma muhammadu wallah banason irin wannan shegen gurbataccen tarbiyan da kuke bawa yaran nan, yanxu ka kinkimo wayann kyautuka harda sarkan gwal zaka bata ita da laifi kuma zaka kara lallata da kyauta wato kenan tacigaba da yin abunda take maka na rashin kunya kenan ko?


yace ahhh hajiya Allah ya huci zuciyarki nifa bance ki kirata ki haura mata da fada ba,  ai leifi na ne dana mata fadan ko..ni sulhu kawai nake so.


ya juya ya kalle ayaana a marairaice yace ayaana dear kiyi hakuri...i bot this gifts for u ina fatan zai saka komi ya wuce...


ayaanah tafara hawaye

batace komi ba dan ranta bakaramin soyuwa yake mata ba...


hajya tace ohh bazaki amsa shi ba, ni wallh da bari kay naci ubanta toh meye haka ana bata haquri tana mana kuka ke kenan baza a gaya miki gaskiya ba ko rainashi dakikeyi  abu mekyau ne...


ta share hawayenta ahnkli tace hajiya naji nace yayi hakuri...ke fa bakisan asalin abunda ya faru ba kinata min masifa


 ..tace nayi din, saiki tashi ki dakeni nasan cewa a nonon rayyanu kika tsotsi rashin kunya Toh wallh baki isa k raina muhammadu agidan na zuba miki ido ba


mikewa ayaana tay tace "ni zanje daki kaina namin ciwo..


hajy zatay magana uncle moh ma ya mike tsaye da wani irin sigar lallami hajya dan Allah ya isa haka..kinga kinsa kanta na ciwo..dear kije abunki kihuta nasan kin gaji...ince dai komi ya wuce..ahnkli ya matsao kusa da ita yace i wll call u with my new numbber dan Allah ki dauka zamuy magana a atacan i am sorry for all this kinji ko...ayaana taki tace masa uffan hawaye na zuba a idonta...ya kuma cewa zan bar miki gifts dinki anan inkin huce saikizo ki dauka kigayamin in sun miki kyau...


da wani irin masifa hjya tace "ana miki magana kinayin shiru ma mutane..chab din jammm ahhtoh lallai ayaana wuyarki yakai na yanka..toh wallh wallah har shi rayyanun dake hure miki kunne bai isaaa muhammadu yana masa magana yana kin amsashi ba maza kifita kibamu waje marar kunya kawai. inbanda samun waje waye zai dauki wnn rainin agidan nan inba muhammdu ba..


da wani irin sauri ayaanah ta fice a sashen tana shiga sashen ammi karama suka ci karo da ita a kofa tana kkrin shiga, suna hade ido wani irin kuka ta fashe da shi cikin sauri ta rungumi ammin tana kuka mai zafi jikinnta atake atake ya dau wani irin zafi sosai...


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[06/12, 14:58] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahms.




⏯️3️⃣8️⃣


yadda ayaana take rabza kuka me cike da bacin rai da fushi yasa jikin ammi karama yay wani irin sanyi kanta a dan daure tarikota cikin damuwa kuma ahnkli snn taleka corridor ko zataga wani na biyo bayan ayaanan sai bata gan kowa ba, jawo ta cikin sashen tay suka wuce har cikin dakin baccin ammin direct safiya tabisu da kallo suna shigewa daki ta taho cikim sanda ta manna kunnenta ajikin kofar dan taji meke faruwa.


ammi ta zaunar da ayaanah akan gado tanamai rungume da ita cikin muryan lallashi  me taushi da nuna tausayi tace haba haba ayaanah kukan me kikeyi haka keda waye, snn me aka miki kike wann kukan? dada shigewa jikin ammi tay tana kukan sosai harda rufe idonta, da muryan damuwa ammi karama tace' kiy hakuri mana mamana, nd pls can u tell me what is going on zakifa sa hanklina ya tashi, ke da ibaad ne ko?? 


cikin tattaro makanta nitsuwa daqyar, yadda zakasan abun ya mugun bata mata rai hawaye nazuba a idonta cikin zafin shesshka dakyar tadago kai ta kalle ammi snn tace ammi dan Allah dan Allah kice ma uncle nifa bana son gift din dayake bani, haka ma ranar bikin kulthum ya kirani falonsa wai dan bansamu naje ba shine yau yajeshi ya gayawa hajiya wai ina masa rashin kunya ina rainashi ita kuma bata san kan maganan ba kawai tanata zagina, ammi nide dan Allah kije kice musu banaso..ni nagaji wallah banason komi nashi, kawai ki gaya masa yadda zai dan fahimta ya kyaleni...


jawota jiki sosai ammi tay jin yadda ta karashe mgnan da matsanancin kuka ahnkli tana cewa "its okay ayaanah ya isa haka. karkiyi ki daga ciwonki abarni damuwa ita hajiya batasan illar haka bama..calm down zanje na sameta anjima kidena kuka mamana..


ahaka ta dinga lallashin ayaanah har tay shiru kafin nan ta kyaleta akan gadonta tana kwance ita kuma ta shiga bayi tay wanka ta canza kaya ta fito suka fito falo atare, kallon ta safiya ta dingai tana mata dariyar mugunta kasa kasa sai can tace 'toh gacan wayarki yana ta ringing gashi kinje kinsaka privacy screen baya nuna suna halama uncle moh ke kiranki.


..da sauri ayaanah ta karaso ta dau wayar tana budewa taga tarin miscalls har 12 da new number sai 3 miscalls da lambar ibaad, da uban text message da uncle moh din ya turo mata na lallashi da ban hakuri da wata sabuwar numbershin dayagaya mata cewa zai nemeta dashi daxu.


dake ana daf za'a kira magrib ne dakinta kawai ta nufa bata bi takan calls din ba tana xama akan gadonta tay dialling number ibaad dabai dauka ba ta tura masa sako.. daga nan aje wayar tay taje bayi tay alwala har ta fara sallan magrib ta idar ibaad bai kira ba sai kuma taji hanklinta ya fara tashi cos she hate to miss his call dake bai saba kiranta haka kawai ba, ana daf za'a shiga sallan isha tay banza da new calls din uncle moh dake kan kara shigowa wayarta sai ta fada gidan wanka, tana fitowa tazo tay yan shafe shafenta sama sama tay kyau snn ta saka wata fitted gown na material sea green colour ta gyara sumanta tay parking dinsa baya gaba daya, tana gamawa tay sallan isha'i har yanxu uncle moh bai dena kiranta ba,she was so annoyed gabadaya mood dinta canza, tafito ta samu ammi karama harta gama musu dinner suna hade ido da sanyin jiki tace sannu da aiki ammi, da murmushi ammi tace yawwa ayaana ynxu an huce ko? to kizauna kici abinci dan Allah  bana son hayaniya zanje na ci nawa da hajiya kinji ko? da ladabi tace toh ammi amma a koshe nake bana jin sha'awar cin komi kawai saikin dawo! babu yadda ammi batay da ita ba tace sam bata jin yunwa ne ammi na ficewa kuwa safiya ta dauke abincintan tawuce daki dashi ita kuma ammi karama ta wuce sashen hajiya da cooler data zuba nata abinci itama, wanda tun zuwanta sashen mgna akan lamarin ayaanah kawai ammin take ma hjya mairo amma hajia taqi jinta sam sai cewa take ai tsoron rayyanu ne yake lalata tunanin ayaanah shiyasa har take raina manya..



ayaanah tarasa abunda ke mata dadi, tafi minti 30 bata motsa akan gadonta ba wayarta na ajiye agabanta dacan harzata dauka takashe shi gabaki daya kenan saiga wani sabon saƙo yashigo pingggg da can kamar bazata duba ba da tunanin ko uncle moh ne tana kuwa daukawa taga lambar ibaad ne rubutu ne ke yawo akan screen din ya nuna "can i see u outside?? wani irin dadi taji tuni ta ture wayar gefe ta sauko kasa ta jawo chantilly veil dinta ta kara fesa turare snn ta fito tana takowa a sannu-sannu, gidan ya dau wani irin shiru veil ɗinta yana motsawa a iska tana kuma jin bugun zuciyarta na tahowa da karfi karfi


banda securitynsu a harabar gidan bataga alamar kowa ba ,gashi ta bar wayarnta aciki dan bataso tazo gabansa da wayar yaga shegen kiran da uncle moh ya isheta dashi bata san wani kalar bayani zatamasa akai ba.


Bata ganshi nan kusa ba har sai da ta karasa bakin gate. hadadden  Motarsa na kunne, headlights dinsa kawai yabari ata ƙasa, yana zaune a ciki da kananan kaya fari kal din T shirt yasaka da blue jean, yay jimm  kamar wanda ya dade yana jiranta awajen


tun tana bude gate din ya zuba mata ido yanata kallonta ta cikin gilashin mota har ta karaso cikin sanyin takunta me daukar hankali...bai janye ruwan idanunsa akanta ba har saida ta bude murfin motar ta shiga a hankali daddadar kamshin motar dana jikinshi atake ya wani gauraya da kamshinta. sallama tamasa tana zama ta dan lumshe idonta kadan tana jin nauyin dake karsashi a zuciyar na kkrin lafawa.


...kallonta yake har ta dago suna hade ido ta marairaice murya da sanyi tace "yaa good evening"..idonshi still fixed on her face yace "evening madam nd why did u ignored my calls?


...karamin ajiyan zuciya ta sauke tace "wayar ne nabari a falo lkcin hjiya ta kirani kuma i called u back baka dauka ba 


cikin kyabe baki yace "olryt., na kira ammi ai tace min kinata fada da hajiya wai kinki cin abinci ko?, batace mai komi ba ta sunkuyar dakai tana wasa da yatsun ta..shiru ne ya dan ratsa wajen ya dada kallonta yace "Are u okay? daga idonta tay da wani irin shagwaba tabi ta marairace kmr yar 4yrs har zata kalle cikin kwayar idanunsa sai taji wani irin raunataccen hawaye yaciko mata ido kuma, da sauri yace aa aah malama dakata, kafin kifara min kuka anan kisani kaina na min ciwo ynxu haka daga asibiti na fito ko gida banje ba... yana maganan ya miƙa  hannunsa baya ya jawo wani brown eatry bag a seat din bayan snn ya miƙa mata fuska ba yabo ba fallasa with his calm cute voice yace...will you eat this for me tonight? it contains ur favourite starters, fruit salad, nd tasty chicken..


hawayenta me sanyi datake dannewan ya zubo tare da murmushi ahnkli tace "i will

..thank you yaa..ba yabo ba fallasa ya gyada mata kai tare da jawota jikinshi ahankli tareda narkewa cikin qamshin turarensa ta lafar dakanta akan kirjinshi batasan sanda yaciro hankynsa ba ji tay yana share mata hawayen ahnkli kuma cikin tsananin kulawa muryansa kasa kasa yace

"once i get home we will have 5 min to chat, saiki gaya min menene matsalarki da kike son min kuka, nd dont forget to send me the pictures of you after uve eating everything here... kinji ko?


Dada jingina tay ajikinshi kadan cikin sauke ajiyan zuciya ta gyada masa kai, they remain like this for a while suna jin bugun zuciyar junansu dake yi da karfi kafin can ya bude lumsashun idanunsa tare da janyeta ajikinshi ahankli ya sauka ya bude mata kofa ta fito ya raka ta har bakin gate suna kallon juna muryanta  kamar  na wacce zatay mai kuka tace "thank you"

..murmushi me sanyi kawai ya mata tare da shafa gefen fuskarta da cool hands dinsa baice mata komi ba ya juya ya koma cikin car dinsa within minutes ya bar wajen,.ta doso cikin gidan kenan, uncle moh dake rike da wayarsa acan corridor ya hangota daga can sama ta waje.


he was shocked daya ganta ta fito daga ta bakin gate da kuma babban ledan eatry a hannunta, jikinshi har na rawa rawa yafara saukowa da sauri, idonshi a rufe ya bi matakala yayo waje ita kuwa a dede main door taci karo da mujaheed shima ya tsareta yana kkrin tambayarta da mmki ina ta fito dan yasan 6pm ne deal breaker agidan mace bata fita koina inba da kwakkwarn dalili ba..


bata kuwa boyewa mujaheed ba tagaya masa yaa ibaad ne ya kirata waje harma ya tafi, dake zuciyarsa a wanke yake bai dau abun da wani issure ba har yasa ta bude bag din yagani sai ta bashi pack na chokolate guda daya 

..immidietly ya bude yakai bakinsa ya gutsira yana kkrin bata da wasa kenan sai ga uncle moh ya iso wajen, wani irin mugun kallo ya masa da kakkausar murya yace "kaii mujaheed me kake yi anan 

wani irin firgita mujaheed yay


ayaana tay saurin dauke kanta suna hade ido da babansa ya dan sosa keya yace bbu komi baba i am just coming in ne fa yanxun nan na dawo, atake atake wata wutar zargi ya cakka kahon zuciyar uncle moh, "coming in frm where? sai yay asuming cewa fita yawon shagalinsu awani waje sukayi da ayaanan shiyasa ma hala taki daukar wayarsa gashi har ya siya mata abu sundawo suna ci atare


...da bacin rai yace "ure very stupid mujaheed get inside..ya kalle ayanah da tulin kishi a idanunsa yace" ke kuma ba anhanaku fita da dare ba..

where is ur phone? muryanta na rawa rawa tace "yana cikin daki..tsabar kishi muryansa harna rawa yace ohh barin wayar kikay aciki kika bishi kuka fita. hmm bakomi, get inside ryt now...yanayin yadda yay maganan da authourity da kuma zargi yasaka tay sauri ta shiga cikin itama da mugun sauri..


bayan ya koresu haka ya dinga safa da marwa a harabar gidan yanajin kirjinsa na tafasa, wai shin duk wahalar rainon zcyr ayaanah dayayin nn tun tana karama sai dansa mujaheed ne zaizo yasa ya tashi abanza kenan...


wato harma ayaana zata iya sneaking da dare ta fice yawon banzanta da dare da mujaheed amma shi babu yadda baiyi da ita suje ko ice cream sunasha awaje ba amma sai taki wato ma yarinyan na ta mugun raina masa hankali kenan kome?


da matsanancin fushi tare da zazaafar zargi ya hana kansa sakat a tsakar compound har sai da yaji kansa da zcyarsa yana neman fashewa da fushi snn ya daga wayarsa maza maza ya tura ma Alhaj ameer text an suyi chatting akwai wata magana very urgent


within few minutes alhaj ameer din kuwa yay reponding, tun suna chat yana ranting har ya koma ciki ya dauko key din mota ya shiga motarsa ya kulle kansa dan suyi waya kawai anema masa mafita 


ayayinda yake jin matsanancin kishi, zargi da kuma haushin ayaanah alhaji ameer kuma is busy telling him cewa ai dama yarinyace dolene hanklinta yafi karkata gun samari dede da ita, kawai mafita daya ne yay gaggagwa cikin satin nan ya daga mujaheed agidan tun kafin komi ya lalace.


fannin ayaana kuwa tunda ta wuce ciki bata wani samu sararin nazari akan reaction din nasa bama dan tana shiga dakinsu kirar ibaad ya shigo kuma yabi ya umarceta akan taje room dinsa taci abincin awajen suyi video call he want yo watch her eat aikuwa atake ta tattara ta koma room dinsa ta zauna da abincin agabanta tun ana wayar 5 min basu da gamawa har saida karfe 10.30 na dare yay


baima tsaya jin tarkacen labarin abunda ya farun tsakaninta da hajya ma he just focuse on making sure she has eaten nd her mood was uplifted, sha daya saura bayan sun gama video call in ta koma dakinsu yau ba karamin farinciki tay bacci dashi a daren ba, she slept smilling with alll the sudden care nd flirtious gesture da ibaad ya dinga nuna mata kmr wanda yasan abunda ke faruwa da ita..


bayan kwana biyu haka kawai taga uncle moh ya wani irin dauke mata wuta, baya kiranta awaya, in sun hadu ma saida ta gaishesa a ladabce ta wuce, 


shikuwa satin gabaki daya wai fushi yakey da tsananin kishi ga zargi, yabi ya saka ma mujaheed kahon zuƙa duk motsinsa sai ya saka ido akai, babu dama yaji mujaheed baya na ydinga kiransa kenan just to make sure baya tare da ayaana


yana ayyana hakan at same time shida abokinsa alhaj ameer suna ta famar gathering all transcripts, course descriptions, credit hours daga makarntar da mujaheed yake ynxu infact they have already writen a formal letter of intent/explanation to ta  Chinese university on why he want to transfer his son and to esure they meet all their requirements.


ma agent dinsu ya barma aiki kiraye kirayen International Admissions Office of the Chinese ya zuba kudinsa bana wasa ba dan a samar masa Zhejiang University of Technology agaggauce


dan tsabar zafin kishi da zargi har can can china yake kkrin tura mujaheed, gashi yana sane da cewa in yaje za'a maida karatunsa baya but he dont care


agarin cuccusa kai da tsabar neman alfarma agaggauta abun yasa har anty safeera ta fara dagoshi, afarko ta kasa  gane meye ne yake faruwa tsakaninsa da mujaheed da kwana biyu ya zama so hyper reactive, ya dena sake ma mujaheed fuska ga takuri ga yawan kiransa awaya akai akai muddin baya gida 


his real intentions nd reason basu fito mata asarari ba, amma wani abu yana bata cewa dolene akwai wani babban matsala daya shiga tsakanin uncle moh da mujaheed.


a sati na biyun while ayaana na kkrin fara test a schll anfara maganan biya mata su waec da neco da jamb, cos in aprox 6-7 month ake tsammanin zata gama secndry schl, unknown tension da sudden canjin fuska tsakanin mujahd da babansaa yabi ya hana anty safeera kwanciyar hankli daga can kuma shirin gaggauta daga mujaheed a nigeria yay nisa sosai, harma sun samu admission din  duk bai sanar da kowa ba ya fara batun kama ma mujaheed permnt haya acan inda sai yay watanni fiye da goma ba bai dawo gida ba.


da balain zafi ya dauki abun aransa, gani yake babu mahaluki da ya isa yay masa asarar qudirinsa na samun auren ayaanah musmn yadda yaga kayan marmari ajikinta na bala'in habbaka, nonon ta ya fara cike kirji gasu round gasu a tsaye, gata da tumin shape komin ta dai dai kuma me masifar daukar hankali kuma tana da tsayi kusan halittar jikin mahaifiyarta tawure ta dauko zak zak..the more she grow the more sexy nd fresh she look. gabaki daya ya kwadaita da samun wann yarinyar a turakar sa gani yake randa ya same ayaana akan gado toh kakarsa ta yanke saka, gabaki daya tsufarsa sai ya zabgeshi adanyen jikinta kasa da kusan shekaru ashirin nd he want to have cute cute kids with her...


wann satin anty safeera kusan kullum sai ta tambaye mujaheed ko wani abu ya shiga tsakaninsa da babansa shikuma haryau bai san mezaice ba,dan baima kawo tunanin zai iya taɓa kasancewa akan ayaana ba.


ranar juma'a da sassafe anty safeerah tafarka da laulayi sosai tanata amai yau kowani baccin kirki basuyi ba amma memakon ya tsaya ya bata cikakken hanklinsa sai kuma ya kasance yana murna na ganin fitowar ticket din mujaheed ranar sunday da sassafe wajen karfe 7.30am ranar sunday jirgi zai daukesa double way trip ne, jirgi biyu, daya zai saukesa sai daya yakaisa china he will first of all go to Abuja then Istanbul kafin ya samu direct plane to Beijing

inteconecting flight is almost 18hrs journey on plane.


anty safeerah ta koma dakinta kenan zata dan watsa ruwan dumi da sassafen mujaheed na fitowa a masjid uncle moh ya kirasa a sashen hajy mairo, bayan sun gaggaisa kawai ya fara musu bayani wai zai tura mujaheed china ranar sunday, kamr almara mujaheed ya dinga jin maganan a kunnensa..worst part yadda atake ya jujjuya zancen ya dawo dashi kamr zai turasa ne kawai dan yaje yay ilimi me inganci kuma harma ya gama komi, wanda hakan yasaka hajiya mairo ta hau kai da murna da tunanin babban gata akayi wa mujaheed.. 


duk dama kan mujaheed ya balain rikicewa agaban hjy baiy nuna komi ba har saida suka dawo sashensu snn ya samu baban nasa a daki ya gaya masa cewa gaskiya shi bazai iya komawa china kwasam karatu ba...duk dama gentle parenting ake musu, ana barinsu suna fadin raayinsu amma wnan karon uncle moh haura masa yayi da buhun masifa har da gaura masa mari yace masa umarni ne yake bashi ba neman shawara ba...


abu tun yana wasa wasa mujaheed ya dga hanklinsa duk gidan sai da aka shiga tashin hankali sosai it turns out babu wanda yabi bayan uncle moh sai hajy mairo tace sam ba ayi ma muhammadu adalci  yana kawo cigaba agidan ana kushe shi...kan anty safeera kamr zai fashe 

,mujaheed yana magana yana kuka shima uncle moh yana magana yana daga jijiyar wuya wai an rainashi har ta rasa na waye guda daya zata ji


karshe dakyar saida bappa zaidu da yazo weknds ya tarasu duka aka warware magann shidakansa ya lallaba mujaheed ya bashi haquri sosai snn ya amince zai tafi amma ba har ransa yaso ba saidan out of immense respect dayake ma bappa zaidun kawai ya amince dake ma yaga bappa zaidun ya nuna ya fahimce shi sosai..


inkaga mujaheed tsakanin friday da sartuday dolenka ne ka tausaya masa gabaki daya ya fita a ahayyncin sa, fushi, rudani da baqin cikin rushe masa karatunsa anan tare da maidashi baya yasa ranar sunday ne daya tashi yin tafiyarsa ma mahaifyarsa da sauran kawai yay wa sallama baice uffan ba babansa da hajya mairo ba ya wuce abuja, ever since ya kama hanyar abujan ya kashe wayarsa for hours ranar sunday babu wanda ya samesa


ranar kusan wuni anty safeera tay tanata kuka ta rasa abunda yake mata dadi, babu yanda bata danta langwasa mijinta ya gaya mata meyasa yay ma mujaheed haka  ba amma inaa yaqi sam ya kula kowa duk da abun yamasa zafi sosai da mujaheed ya tafi bai masa sallama ba.


kin kunna waya da mujaheed yay all thru his jouneuy bakaramin cusa gidan yay acikin  tsananin fargaba da baqin ciki ba, hajy mairo kullum tana jigila asashen anty safeera tana bata haquri.. 


for almost 15hrs babu labarin mujaheed lissafin duniya anty safeera tay harta fara tunanin koma duniya zai shiga bazai jeshi wani karatu a chinan ba


hanklin uncle moh yabi ya tashi, he is feeling the urge to keep calling his agents, ko kuma koda ya rarrashe matar sa ta dena yawan kukan nan datakeyi tun jiya amma ina, abokinsa yace mai kar ya sake emotional draman mace ya rushe masa qudurinsa ai ita macece zatayi ta bari.


tashin hankli bai kare agidan ba face har saida bappa zaidu yazo gidan da yamma ranar monday da news din cewa yayi yawa da mujaheed yana lafya kuma ya isa china kalau.. dagajin haka  hanklin uncle moh ya kwanta. anty safeera kuma ta kasa nitsuwa harsaida mujaheed ya huce can cikin dare ya kirata sukayi magana yay assuring inta ya isa snn ta kwantar da hanklinta, altho tay tay mujaheed ya sake ransa yaqi, daga ta masa da maganan ya kira babansa da bacin rai ko kuka zasu rabu...kawai gani yake kamar da akwai wani boyayyen lefi daya masa babansa da har yamasa wnn mugunta, cos he cant just send him far away from home gatsau, kuma ya maida masa karatu baya batare da wani kwakkwan dalili ba.  kwana biyu anty safera tafara sawa aranta wai koda zata lallaba mijinta taji dalili abakinsa, she have been tryn her best amma yaki sam ya bata fuska, sai kawo mata wasu dalili yake har yasa ta fara zarginsa da wani abu duk dama bata kawo ayaana bane


aikuwa a satin data dage agarin bincike kwasam ta samo information cewa da alhaj ameer aka hada komi kuma acikin gaggawa...

tundata bincika ta gane kmr abokaine suka zugashi


ranar data dage zata je asbitin a dubatan she became all hormonal sassafe ta tashi da bori sosai, uncle moh ya shirya zai fita tay confronting dinsa akan batun sako abokai cikin harkan rayuwr su da na yaransu, tun suna magana na fahimta abunka da me sabon ciki aka fara haurawa juna, ya dinga mata ihu yace ta dena ce masa bai isa ya yanke hukci a akan rayuwar mujaheed 


cikin gushewar hankli da subucewar baki ta fara shigo masa da gori da kuma barazanar cewa zata kai kara wajen mahaifinta kawai adawo mata da danta tunda bayaso, ita ba zaa saka danta karatun dole a inda baiso ba.


ran uncle moh ya baci ganin ta hatsala ta dauki mayafi shikuwa yace mata taje gidan amma tasani kafin ta dawo wallah aure zaiyi kuma zai aure wacce zatazo ne ta masa biyayya agidan nan  ba wacce zata nuna masa gadara da iko da dukiyar ubanta ba.


tunda ya furta mata wann maganan kara auren ya fita taji cikin ta da duniyan na ma gabaki daya na juyawa


ficewarsa agidan da fushi bada jimawa ba aka kirashi awaya ahujajan cewa anty safeerah tana asibiti ruwa ruwa har ta samu miscarriage...tundaga inda aka gaya masa jikinshi ya fara rawa rawa dan bawai baya kaunar matarsa bane, kawai dai zuciya ce irin tasa, wanda bata da linzami ko kadan. a hujajan ya wuce asbiti


ya samu an shiga da ita ciki za'a wanke mata ciki hajy mairo ne da ammi babba kowa yana neman jin meyafaru da doc yake batun ma safeerah ciwon hawan jini...


tunda ya iso asbirin yake safa da marwa akan likitoci dan sosai ya shiga hanklinsa ido ya raina fata, ganin ana batun complication na hawan jini, tsoro ya kamashi marmaza ya jawo hajy mairo gefe ya zaunar da ita ya fara mata bayani abunda ya faru da kalar kalaman da ya furta ma safeera kafin abun ya faru


salati ta dingayi cikin raki ta zazzageshi tace masa maza maza ya janye wann maganan koda dagaske ne zai kara auren yay maza ya karyata, kar yaje ua kashe matarsa abanza gashi yau yay asarar haihuwa

kawai ya san yadda zaiy ya karyata kansa inyaso nan gaba inma auren zaiyi saiya san sigar daa zai gaya mata.


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[06/12, 15:50] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️3️⃣9️⃣

baida mafita hakanan ya saukar dakansa ya amshi shawarar hajiya mairo hannu bibbiyu sbd yana balain jin nauyi da kuma tsoron yarasa aurensa da kyakkwan matarsa safeerah, few minutes suna zaune awajen tana bashi shawara har akagama wanke ma anty safeera ciki snn aka fito da ita likeyly uncousious an saka mata drip idonta a lumshe da alama har ynxu a tsorace take batama san inda take ba tukuna.. 


a wani private VIP room aka sakata, uncle moh yay nan yay can duk ya kasa nitsuwa, tun bata farka a bacci ba ya fita ya siya babban bonquet na red flowers da get well soon cards manya manya ya jejjera mata a agefen gado, uban damuwa da rawan kafa dayake yasaka har su ammi babba suka fara tausaya masa, kmr mutunin arxiki ya nuna a fili kamar subutar baki ne yasashi ya furta ma safeerah cewa zai kara aure. ana daf wajen za'a kira sallan azhr anty safeeran ta dawo hayyacinta tafarka lkcin u hajiya ne kawai a dakin haka nan suka yanyaneta kowa yana fadin iya albarkacin bakinsa akan lamarin


kai kafin ma uncle moh ya dawo hajiya tay kkri wajen ganin ta karyata batun aurensa a zuciyar anty safeerah


ammi babba sai ce mata take bataga yadda uncle moh ya damu bane har hawaye saida yay suka taru suka babbata hakuri suka lallabata, kafin can uncle moh din ya shigo, data kallesa yadda yake sum sum kusan rabin abunda takeji a zuciyrta na fushi da kishi sai ya gushe musmn dataga flowers da abubuwan daya jejjera mata na soyayya kmr ba shi ba...


ana idar da sallahn azhar su haj mairo suka basu waje yazo ya zauna a kusa da ita irin dan basarwa na matan nan kawai ta iya mishi, yanata lallabata akan tay hakuri taki cemai komi tanata kuka hankalin sa yay bala'in tashi, har da guntun mata hawayensa akan cikin nata daya zube sosai yazo yafara bata tausayi ma.. ba a jima ba ammi karama ta kawo musu abinci tay musu jaje da gaisuwa.


kwanansu daya a asibitin uncle mohd yana kan bikon matarsa, bata kuwa kulashi ba har saida aka sallamesu suka dawo gida, bayan kusan kowa acikin yaran gidan anzo an gaisheta hajiya mairo ta hadasu a falonta tay musu nasiha, as usual sai nunawa take cewa safeeran ma tana da laifi akan meyasa zata na jayayya da mijinta bacin niyyarsa akan dansa mujaheed mai kyau ne aishi uba ne bazaiso ya cutar da dansa ba, sai da ta wanke anty safeera tass ta mata fada, snn shima ta wankesa tace masa bata son ta kara jin irie iren wann magnn banza yana fitowa daga bakinsa. ranar gabaki daya uncle moh ya sauya ma anty safeera ya dawo kmr wani sabon mutum, he was with her all thru the healing journey sai da ya tabbata sun sasanta kansu, harda dansa mujaheed da situation din yasashi yaji kamar sanadiyarsa ne auren iyayensa ya samu tangarda gashi har mamansa tay bari


shima baida wata mafita haka ya bawa uncle moh hakuri ya hakura yace zai masa biyayya yay karatun kawai saboda karda acigaba da samun matsala tsakanin iyayensa..


bayan kwana biyu soyayya me matukar tsafta da sanyi ke wakana tsakanin uncle moh da anty safeera everyhing seems fine, mujaheed, kulthum da mijinta maheer ma suna kiran gida akai akai ana gaisawa.


duniya sosai tay ma ayaana dadi kwana biyu da uncle moh ya maida hanklinsa kan zallan matarsa, baida lkcin damunta da kira ko wani sakon gifts,.. rayuwarta takeyi cikin sauki da kwanciyar hankali time to time suna waya da yayanta suna dada shaquwa da juna cos she is getting all the lovely feeling nd butterflies frm the little attention nd love dayake bata sosai, yanxu bata da wani aiki face karatu sai in sun hadu da sultana kowani wkend ko tay sleep over. most of her time da ruthy take spending a shagon hajiya, by now she have learnt alot of things na baking, local dishes, drinks, cullinary skills,

traditional dishes duk dama takanzo ta takura ammi karama agida ta koya mata wasu abbwn da ibaad yake so a rayuwarsa cos she loved him soo much har batasan kalar yawan son datake mashi ba. 


nd for the fact that duk wani abu na duniya da zai mata tsakaninsu kawai yake karewa, he even hire a social media manager nd distrubutor for her online imported abaya business daya kafa mata dan kawai ta sa hanklinta akan karatu sosai..


duk wani hidiman kudi duk wani alheri da zai mata bata taɓajinsa ko a bakin yaa maheer ba bare kulthum, bare kuma su ammi. hakan yasa bakaramin kallon ibaad da daraja take yi ba, it feels like tsakani da Allah kawai yake mata abu, kai ko safiya datake yawan wasting kudin shi a poor investment baiya mata gori akai saidai ya kara mata wani kudin ta sake trying wani

.. she respect ibaad much more than she loved him.


rayuwarsu ya kasance normal ana neman wata daya da sati biyu da auren kulthum bayan komi ya dawo normal hanklin uncle moh ya fara dawowa kan ayaanah, musnm yanzu da gabaki daya ya kasa gane inda ta dosa, shi sam sam bai lura da alamar tama yi missing din mujaheed ba, duk dama yana zargin ko suna waya, 


soyayyarta da ibaad kuma is not childish nd loud yafi ganin kamar tsoron ibaad takeyi shi yasa bata iya saɓa masa in yay magana bata tsallakewa bai fahimce komi dake gudana atsakaninsu ba


ayan kwana biyun nan da ya maida hanklinsa kan safeerah sosai ya lura da cewa har girki take ma ibaad yazo gidan ya ci ko tay packging masa, nd he just tot is normal, untill ranar shima ya fara cewa ta masa abu sai yaga ta kawo masa ruwan jajjagen complain ko ta share batun tace ta manta.


sai kuma sabuwar kishi 

ya fara ginuwa a ransa game da ibaad, badai kamar yadda yaji akan mujaheed ba wann karon gani yake kmar ibaad yafishi power akan ayaana, har ransa yaji yanaso ya kwace wannan matsayin amma ya rasa ta ina zai fara


ana fitowa da sabuwar iphone yay maza maza ya siya mata da wasu expensive perfumes koda ya kirata ya bata sai ya fara requesting wai ta masa girki shima kuma baya tashi fada sai yaga anty safeera bata nan. da kyar ranan yaci sa'a hajy mairo ta sakata ta masa kunun madara yasha, akan wnn abun saida yay sati yana yabonta har abun ya fara bawa anty safeerah haushi sosai.


shikuma so yake wai koda ayaanah zata dauki hint itama tafara masa abubuwa na kyautatwa dana nuna biyayya kmr yadda take ma ibaad gashi his birthday is around the coner duk ya mata text message ko suka gaisa sai ya tuna mata birthdaynsa awasa, he was stylishly suggesting suje outing ayaanah sai tay kamr bata gane meyake fada ba dan bala'in mamaki yake bata musmm da ruthy tafara fayyace mata cewa da yuwar uncle moh yana crushing akanta ne


dariya ma abun yake bata tana ganin kamr ko tsabar zuga kyanta da akeyi, da kuma bude idon su yasa har ruthy take tsammanin ko uncle moh zai zubda mutuncinsa da dukkan girmansa yace yana sonta, cos she tot is impossible for him to even think about that dan a matsayin uba kawai take kallonsa har yanxu...


ruthy ne tay introducing inta da daka abubuwan zamani kamrsu saka jigida, sarkan kafa da kitso, sosai ta koya ma ayaana kitso da gyaran gashi  musmn in suka je gidanta har yadda ake hada maganin mata tana koya mata dake ita tana harka da maza sosai, kusan ma abun da yasa ayaana bata iya kaiwa yamma kenan a dakin ruthy cos all kinds of ruggerd guys da girls suna zuwa wajenta, and she is highly suspecting cewa ruthy tana cikin wani kungiya sabida nacewa datay tana saka jan kaya, no matter what intay dressing sai ka ganta da red colour ajiki, sumtimes ko red scarf ko hanky ko handfan, u will neva see her witout red hakama abokan nata suke. 


duk sanda ayaana kuwa ta tambaya sai tay dariya tace mata ai kalar  youth church fellowship ne kawai ba wani abu diabolical ba.


most time ayaana will just mind her busines dan bakaramin koyan abubuwan duniya take yi awajen ruthy ba all this relship secret data san su ammi karama dai bazasu zaunar da ita su gaya mata ba, difrnt kinds of stories akan maza, cos ruthy ta bala'in iya hirar sex, da abubuwan da maza ke so ana musu. with all this emergency kayan mata data iyasu sosai duk tana gayama ayaanah, sun yarda da junansu sosai, the frienshp is not tight amma is very loyal dake sun fito gari daya yasa sukema junansu kallon sisters kawai.


cikin wann satin ya kasance uncle moh yana ta xumudin samon first gift dinsa daga wajen ayaana dan yanaso inta bashi gift dinne sai yay inviting inta suje wani waje tare su shakata, daga nan kuma ya qudura in har ta amince ta fita fashi to babu sauran jira kawai zai fara bayyana mata kansa a sarari dan tasan intention insa akanta tun yanxu


anty safeera ma anata gefen bakaramin shirya ma birthday din nasa takeyi ba, he is a very generous husband dan haka kowani shekara xaka ga ta masa cake kala kala, suyi hotona ayi decorating waje.


ana saura kwana biyu birthdayn nasa da yamma ayaana tana daki kwasam sai taji muryan kulthum da wani irin sauri ta fito suna hade ido suka rungume juna suna tsalle suna murna, gabaki daya kulthum ta sauya ta kara haske tana blushing kamar mai sabon ciki. jiya da dare suka dawo daga malaysia suka kwana agidan ammi babba, da safe kuma sukaje schl dinta suka karbo duk wani document na transfer dinta, 


ranar murna awajen su ayaana kamar bazai kare ba. daren ranan wajen kulthum din ta kwana kafin washe gari jumaa sultana taxo musu kwana biyu.


rayuwa yay dadi kulthum ta dinga basu labarin yadda aure yake da masifar dadi musmmn ma da wanda kakeso, yadda rayuwarta yake tafiya da yaa maheer kamar wani labarin novel, har sultana dake jan baya baya da abun tafara jin kwadayinsa, ayaana kuwa gani take in har yaa ibaad zata aura hala nata soyayyar sai ya ninka wannan ma.


ranar asabar wkend kuma ranar ne birthday uncle moh he wake up smilling expecting to see ayaanas text msge  da

sasssafe amma sai shiru daga na matarsa saina yaran sa ne tun 12pm na dare shiru shiru har karfe 10am ashe ayaana km tunda yaa maheer yaxo da safe sukabarsa da kulthum a dakin suka koma sashen ammi karama, tun sassafen kuma ta tura ma ibaad good morning text dan da balain shauqin sa tay bacci, musm yadda kulthum ta gwadaita musu dadin aure duk suka susuce sultana ta makale a lungun gado tana waya da ahamad ita kuma ayaana tana kwance akan sallahya busy smilling at the gud morning reply daya turo mata bada jimawa ba.


jira take ya dawo daga gym dan yace zai kira yaji muryanta, kuma so take ta masa surprise meal na fattah lahmp nd flour bread which is his favourite kanuri meal da amminshi take masa ocassionally which she learnt very well awejen ammin.


sunayin wanka tasa sultana agaba ta rakata sukaje mall suka siya wasu abubuwan da babu har akayi family breakfast basa nan, kuma anan ne aka ma uncle moh wakar happy birthday masu bashi gifts irinsu anty safeera da kulthum da su maheer duk suka bashi


hanklinsa yaki kwanciya sabida babu ayaana, he comforted himself da tunanin hala surprise take hadamai baisan ma kwata kwata ita tamance da batun yau ne birthdaynsa ba she was busy buying spices to impress ibaad da favourite dinsa yau inyaxo wekends...


around 12 suka dawo gidan ita da sultana lkcin su ammi babba har sun iso gida ya cika anata hayya hayya birthdayn uncle moh hajy tana ta basu labarin haihuwarsa su anty safeerah anata kyakyawa da dariya


maheer da ibaad ne kawai basa gidan cos he had to escort him to the hospital zaiy test cos ders this problem na rhesus tsakaninsa da kulthum cos he carry a minus baison ya mata ciki azo ana samun matsala ko ta sha wuya sosai..


anata shagali kulthum da sultana suka cika ayaanah da hirar soyayyarsu a kitchen din ammi ayayin da take shirya ma ibaad abinci, dake ammi takan kyalesu suyi komi da suke so, kulthum ma tay fresh ginger juice da samosa wanda zata tarbe maheer dashi, banda hirar soyayya babu abunda suke yi, da mamaki duk kuwa basu dago lamarin zciyarsa ayaanah ba, they just tot yaa ibaad is too hot nd godly handsome nd will neva ever pick any girl acikin gidan musmn da batun soyayya, but dake sunsan yana daga ma ayaanah kafa a komi yasa suke dauka kawai normal alaqar shakuwace dana kulawa a tsakaninsu ke gudana


..bayan sun gama suka sha wanka kowacce tay kyau sosai

ayaana ta saka baby pink lace, dinkin ya dan bi hour glass shape inta tana baza wani irin qamshi, zak zak inda ammi ta koya mata har suman kanta tana turarawa, gashi sun iya kabbasa din nan bana kadan ba.


tunda su ibaad suka dawo ya dora idanunsa akanta yaji ya kasa nitsuwa gabaki daya dan bawai zallan kyaun datayn bane ya rikita shi,qamshin, kunyan, da kuma yadda take masa magana da shagwaba da kuma nitsuwa yasa with each passing minute yakejin jijiyarsa na tashi sosai, for the first time in his life yaji yana matukar shaawar wata ya mace a duniyar zuciyarsa da rayuwarsa har gangan jikinsa yafara jin yanajin sha'awar ayaanah.


waje guda suka hada musu chops din ita da kulthum, ayaana tana gefensa yanacin fatta lamp da flour bread din har yana lumsshe idonsa ji yake da sukadai ne a wajen baisan wani irin sakin layi zaiyi mata ba...


sun jima awajen maheer is unpolegstically showering kulthum da soyayya dan har wani dorata yay akan cinyarsa suna cin chop din suna hira acan gefe


tsakanin ibaad da ayaana kuwa bakajin me ma suke fada dan kasa kasa sosai yake yabon girkin nata, dadi kamar zai hallakata murmushi kawai take zuba masa tanajin kamr ruwan shauqin soyayyarsan har cikin jininta yana malala kmr zai hadiyeta, sun jima a falon kafin nan shida ayaana suka fita waje suka bawa su maheer waje...cikin motarsa ya bude mata ta shiga shima ya zago ya zauna ya kullesu da tinted aciki, dan kadan ta jingina ajikinshi suna kallon reels daga wayarsa, which is mostly abt medicals nothing fun in it but she like it this way atleast baiya kallon yan mata


tay tay ya sakar mata wayarsan tarike dan yasan damuwarta shine kawai tay masa bincike taga ko yana kan magana da zainab arifah tanayi tana basarwa amma sosai ya fahimce shagwabn tan sosai. dada narke masa take ajiki har abokinsa jamal ya kira, jin yace masa yana tare da ayaana, jamal din ya dawo da call din video suka gaisa, da mamaki taji yana bawa jamal labarin dadin abincin data masa, she was so happy acikin ranta musn yadda jamal yake cewa very soon zasu zo tay musu me dadi suma agidan ibaad din suci..


hira me dadi sukayi daga nan ya hadata da matarsa mufeeda suka gaisa cikin aminci she was just gushing akan irin kyaun ayaanah..ita direct take tambayarta yaushe xakuyi aure muxo shagali ayaana saidai ta kalleshi tay murmushi, shine kawai yaketa cewa "soon!! but she dont knw weda he is serious ko kawai yana biye musu ne.


bayan sun gama call din ne ya bude gallery din sa yanuna mata project dinsa na gidansa  can United Kingdom, very sleek country classic mansion ne me aji,fully energy effecient ga water pond ga garden ga kuma kids backyard ga pools guda biyu daya a sama daya awaje snn za'a musu glass walls a katon kitchen dinsu, just 4 bedroom, daya nashi daya na matarsa, sai na yara dana baki. plan din gidan mace daya yay which make her heart beat faster dan bata san ya al'amari zai juya ba, she is desperatly hoping ace itace akayi wa wann gidan ba zainab arifah ba, even tho he is asking for her gunuine suggestion awasu abubuwan still dai tana cikin fargaba sosai. while suna nan mota daga cikin gidan ammi karama ta nemesu sama da kasa ta rasa, kawai sai ta share.. kowa saida ya taru a falon anty safeera aka yanka cake din uncle mohd aka masa abubuwa gogan naku he was just pretending to be so  happy da irin romantic suprises din da anty safeera ta masa mai ban sha'awa kuma ta kashe kudi fa sosai ta masa gifts na kece raini har dasu agogo masu matukar tsada..


ibaad da ayaana na mota basu gama tattauna sauran plan din gidansan ba har saida aka kira sallahn azhar snn suka gama, lura da fargaban dayake idon ta na kokonton samun shi a matsayin miji yasa ya dinga mata dariya kasa kasa yana dan tsokanarta cewa in yatafi can ma da wuya ne ya dawo 


da sanyin shagwba tace yaa yanzu dama saika tafi can kabarni anan? yadan ja cheeks dinta yace inace zaki koma can U.K din dai tare dani?but is totally ur choice madam, i cant force u inkince baki son zama dani ai shikenan..tana kallonsa kamr zatay kuka tace kai bakason zama dani kenan? cikin kyabe baki yace"who wudnt??ahnkli ya dan rankwafo fuskarta nmfashinsa na gogar nata yana mrmshi cikin lumshe ido tare da budewa da kasallaiyar murya yace 'u're beautiful, smart,..sexy...cikin jan numfashi yace "but...


...maraitaccen idon ta fixed acikin nashi ahlkli tace 'but what? yace "i dont knw if ure strong enuf to cook me as hot as d way u cook ur delicious food'..ahnkli tace "cook you?? 


shiru yay yana mai kure kwayar idonta da kallo yana murmushi me sanyi har saida brain inta ya fara harsasho mata meyake nufi da wani irin sacewar jiki ta rufe idanunta da duka tafukan hannunta yana murmushi ya jawota jikinshi ahankli ya rangwafo cikin kunnenta yace kin gane kenan ko?? ta dada boye fuskanta akan kirjinsa

..ahnkli ta gyada kai..yana dariya yace "good..go nd think abt that hard nd long. yana furta hakan yadaga ta ajikinshi ganin taki ta hade ido dashi yace "bakinki ya rufu ko?to kije ciki karki hanani alwala, we wll talk later, yeah?? kanta na kasa tana murmushi ahnlki tace yeah.. karamin kiss ya dora mata a hannunta daya rike snn yasaketa cikin nitsuwa ta bude motar ta nufi cikin gida da bala'in sauri..


tsabar kirjinta na bugawa batama lura da cewa babu kowa ba kawai ta nufi daki da shauqi ta wani irin sulalewa akan gadonta tanamai sauke ajiyan zuciya me karfi da kuma shauqinsa me balain yawa aciki dake mata rairayi ajiki, masifaffen qamshin turarensa daya gama mata malala a jiki hade da nannauyar kalamansa ke dirar mata acikin kunne da kwakwala yasa taji gabaki daya gabobin jikinta sun mutu murus...


wani irin shauqaqiyar juyayi take y akan gado ba acikin hayyacinta tana ji aranta kamata domin ita Allah ya halicce ibaad dan wani irin makahon sha'awshi taji yana dirar mata wanda damshinsa tuni ya fara kkrin jike mata panties, tajima akwance tana sauke ajiyan zuciya daga bisani ta cire kayan jikinta tay wanka tazo tay sallah


sai taga text dinsa akan ya fita amma baizai dawo da wuri ba ka inbe dawowa anjima kawai zasuy waya..


tana murmushi ta amsa masa, kafin ta jawo qur'ani ta cigaba da karantawa da tsakar rana dan gabaki daya bata gane kanta ba, dan daga tafara tunaninsa sai taji sha'awa me karfin gaske yana kkrin rufeta

ganin bazata iya jurar wankan tsarki ba yasa ta cigaba da karatun qur'ani har saida abun ya gushe mata aranta snn tay bacci.


uncle moh har yagaji da jiran yaga ayaana awajen birthday insa har ya cire kunya ya tambaye ammi karama

tace masa ita dai tabar ayaana tana girki ma su ibaad ne amma bata san ko ta gama ba


ransa sosai ya sosu da jin haka, wato ibaad haryau dai bazai daina shigewa hancinsa ba, sai yau yaji yana nadama dama a hannunsa ibaad din ya girma da duk wann rainin dayake masa bazai kai nan ba.


but now da dayekeji yayi karfi yay kato yana wasa da kudi yaron gani yake kamar shi sa'arsa ne.


da wasa wasa kuwa har akagama shagalin birthday ayaana na shekar bacci, sultana ta gama shagalin birthday snn taje tay hirarta awaje da ahmad ta dawo itama ta jonata suka sha bacci.


sai cahn yamma suka farka kulthum sun fita da yaa maheer dan haka a sashen ammi karaman suka cigaba da zama safiya kuma na kallonta a falon anty safeerah tana ta ciye ciyen cakes da abubuwan birthday


nan ne da sultana tafara bata labarin barin kudin da anty safeera tay sai ta tuno tace shit kice dai nikadaine banje bazday uncle ba, sultana tace ehh wallh ke da mutuminki yaa ibaad  ba??? dama kuma ba ɗasawa sukeyi da uncle moh ba..

ayaanah ta kyabe baki tace "hmm,wallh ni mantawa ma nayi toh Allah ya karo masa shekaru masu albarka


...sultana tace ameen..wai ina kukaje ne da yayan? kefa yaa ibaad yana balain shagwabaki..


ayaana tay kwafa tace kai sultana bashi yaje ya dauko ni ya kawoni garin nan ba aikuwa dolensa ya kulani? suka fashe da dariya..tace "kai ayaana kamr wani zaki iya fadan ahaka agabansa aje dai a yana shagwbaki amma dai kinsan gayen nan baida dadi..in ya hade rai kamar mala'ikal mutuwa.. ke wallah ya ibaad is unbelivble ni bansan ya zasu kare da budurwansan can ba kiga dan uban wuyan dayake bata. wani cak dariyar ayaana ya katse da harara tace wa knn badai anty zainab arifah ba datake nace masa ba? Sultana ta fashe da dariya tace "Allah ya shiryeki ayaana wato kedai bazaki kyale matar nan ba ko?..


jan pillow tay kirjinta tace inhar ta kyale shi zan kyaleta..kwana biyu ma banga ta dawo ba hala karatu yay zafi


sultana tace eh amma next week kuwa zaki ga ta dawo kinsan kmr mayyace bataza sake tay missing  birthday yaa ibaad ba, kinsan he is a november born ko??


ayaana tace "really? nov when? tace nov 18th. ayaanah tace whow amma ko sau daya bai taba furta min wani abun birthdaynsa ba


cikin sace ajiyan zuciya sultana tace "Dats bcos he lost his dad dat day ..nd you know what...ranar fa suna tare da babansan ya rasu, so i ques it bring back bad memories

for him..jikin ayaana atake yay sanyi tace "Allah sarki, Allah ya jikansa..i feel really sorry for him. sultana tace "yeah, lets call this lover gal yanxu haka zaki samu sunacan dakin yaa maheer a gida suna morar juna ni wallah bansan wani irin maganin mata ammi karama ta bata ba yarinya ta sake ma miji jiki ayita haƙarta bata gajiya? 


dariya ayaana tay tace barta ta more abunta shima ai yanaso ne da baya so bazai nanike mata ba ni wallah abun ma tsoro yake bani...


sultana tana dariya tace yarinya kiyi shiru sai mun dandana munji dai, i feel like we are missing sumting over der...ayaana ta fashe da dariya tace we are definatly missing

...Muma Allah ya aurar damu

..sultana tace Ameen very soon in sha Allah, koki riga ni ko in rigaki, amma bana so amana rana daya inba haka ba duk banda kawaye wallah yadda yaa maheer yakeji da umminsan nan bafa kyaleta zaiy tamin kawance yadda ya kamata ba...ayaana tace wallh kuwa toh ai gara ke..nifa ko schl friends banda shi yaa ibaad kuma jininsa bai hadu da ruthy ba so she doesnt count. sultana tace ayya kuma ruthy is a nice girl fa. anyways arniya ce kinsan shikuma uztazi ne hala baisan teddy bear dinsa tana wasa da kafurai...


kara fashewa da dariya sukay tace lallai sultana wato ma nice teddy bear din yayan ko?


sultana na dariya tace toh ai naga wai duk duniya kece kawai kika mallake masa zuciya


ayaana tace hmmm abeg dont deceive me zainab arifahn tasa tana ina??..


sultana ta kara fashewa da dariya tace ita ai "fan" dinku ce.. 


atare suka kara kwashewa da dariya har suna tafawa..


hira me dadi suka cigaba da yi har kulthum ta dawo hirar ya rikida ya dawo na soyayya duk sai da ta sa musu shaukin son suyi aure sosai.



uncle moh yay yaga ko wulgawar ayaana bai gani ba, babu text babu komi har washe gari sunday da yamma har saida sultana taxo musu sallama zata wuce gida snn ya hade idanunsa da ayaana normal ta gaishesa saj jin ana hirar cake din birthday cikin rubibi tay amfani da damar tace masa happy birthday..


he was deeply hurt data shashantar da abun, gashi da aukin saurin fushi kawai saiya dena kiranta ya dena tura mata sako, ya fara avoiding inta ita kuma ashe ma batasan yanayi ba, ranar wednesday da yamma tasha wanka ta bi ibaad suka raka su maheer har airpot ranar ma bai dawo da ita ba sai can da yamma bayan sunje wajajen shan iska tare


wkedns ne birthday she was deeply thinking abt it tarasa me zata masa wanda zai saka yaji sanyi kuma bazai feeling offended ba gashi aranar satuday still nashi ma zai fado


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[06/12, 19:54] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE BOYE

arewabooks@surayyahms


WKND BONUS


MY COMENT SECTION U PPL ARE THE BEST❤️💋 PREMIUM LAUGHER, PREMIUM HATE❤️😂TEAM UNCLE MOH SHOUT POWER!!!!


kafin ranar friday hakanan ta zauna ta shirya very beaufitul hand written cream colour note fancy writing pad with few comforting words on it da very fine bold handwriting inta...


_"I know this day carries weight for you.I don’t expect you to celebrate it Just know you’re not alone today.”_ snn tay signature dinta ajiki 


snn ta tattara rabin kudin da uncle moh yake xuba mata taje ta siya quality leather wristwatch tasa aka rubuta " _only time will tell how much u mean to me"_ abayanshi wajen silver palate in..da  wani simple men bracelet black colour mai hade da matured ring nothing flashy in it sai ta saka fancy notebook bcos she knew him to be a very reflective person.


tun a schll tay wrappin gashi batason kowa ya gani tarasa yadda zatay, kawai sai ta yanke draw ta xuba a wani white closed up box ta kai ma sultana tace mata dan Allah tana komawa gida taje ta aje mata a closet din shoes na yay ibaad karkuma ta bude


taki sam ta gaya mata meye ne aciki amma dakyar sultana ta amince sabida tana tsoron kar abu yaje yay backfire a hada har da ita aci ubansu atare. tsabar tsoron ibaad datakey tana kuwa komawa saida ta bari yamma yay yaje sallan magrib tasan bazai dawo ba xai yaja su ishha da sauri taxo dakinsa ta bude wajen shoes dinsa ta saka box din ta rufe tay sauri tabar wajen taje ta kira ayaana tace mata ta saka mata acan.


ita kanta ayaanan da fargaban ko zai ji dadin hakan ko zai bata mai mood dinsa tay bacci da wuri, washe gari ta farka taga miss call dinsa tana kira taji be dauka ba saita tura masa text na good morninng, after ta idar da sallah sai taga reply dinsa, wanda ya tabbatar mata cewa bai bude wajen shoes dinsa ba tukuna, she deliberatly plant it der sabida tasan shi da shegen tsafta inbadai awajen shoe bane dole ne dazai gani tun jiya da dare. 


lura da cewa bai gani ba yasa ta tura masa text cewa she kept him a piece of her thougts acikin closet dinsa, at first bai gane me take nufi ba, saida yaga tanace masa akan yje wajen dayake aje shoes dinsa, da mamaki yaje ya bude sai kuwa yaga box din a aje.


daukowa yay ya fito dashi waje ya warware box din, da hadadden note din ya fara cin karo which actually really really calm him down, sanin cewa she knew what dis day meant to him, she carefully choose her words. hmm kawai ya furta daya karanta snn yasaki murmushin da bai shirya masa ba nan da nan yabude sauran ya ga abubuwan data saka, and he was like its the best gift he has ever received in his entire life, musmn message din da akay carving abayan agogon daya mugun tafiya dashi, hakan datay masa bakaramin karama mata daraja a idonsa yay ba. he re-fell 1million time stronger nd deeply in love with her. such a totful timeless nd calming gifts wanda babu shirme ajiki ko kadan.


ya jima baiy kalar murmushin dayakeyi a  wann safiyar ba but dan ya tsorata ta saiya kashe wayarsa, ta nemesa kamr tay kuka bata samesa ba, duk ta damu saida ammi ta mata fada kafin ta fito ta karyawan safe.


atamfa me shegen kyau ta saka purple colour nd her heart was seriously beating if not for mujaheed daya kirata dazu suka gaggaisa da bata san ya zatay ba, altho distance make it harder for him to call her akai akai ga karatunsa acan babu sauki ko kadan..


har su sultana da su ammi babba suka zo wkdns ayaana bataga ibaad ba, sultana ce tace mata ai tun safe ya fita itama bata gansa ba kuma ba tare suka zo ba. bayan sallan azhr unxpectly saiga zainab arifah, omo she changed level gabaki daya ta dawo American girl tadada kwaila jiki tay haske sosai an mata lippo sunction ta kara shaping lips dinta , she came with a huge flower bonquet da su ballons da fancy luxury gift boxes na perfumes,shoes,dollar bonquet da karamin box me dauke da key din new brand alfa romeo 

car. 


tana zuwa da kibibinta she have to make everybody knew today is ibaad birthday duk dama tasan cewa gidan ba a celebrating but she dont care, ita mutuwar baban nashi bawai darata yay can can ba, "he died along time ago nd so what? kusan words din ta gaya ma kawarta rukayya kenan datake kkrin hanata wann shirmen, nala kuma sosai ta zugata itace ma ta zuga mata ta siya masa mota na yayi.


tana zuwa taga tagama haukarta babu ma ibaad agidan kuma bata wani samu fuska awajen hajy mairo ba sabida kowa yana jimamin mutuwar mahaifin ibaad a wann rana. ammi babba kuma gabaki daya mind inta nakan bappa xaidu ne, tay kababa ta hana shi motsi, she knw zaiyi waya da fatima zai lallabeta zaice mata shine zai cike mata gurbin maragayi mijinta..she is 100% certain he wll do that, shiyasa ta hanasa sakat ta hanashi motsi bare yaje kusa da fatima, babu yadda ya iya haka shima yasakai ya fita...



ganin kininibin zainab yay yawa anty safeera ta jawota sukeje can sama, tafara mata fada akan wann gift din yay yawa nd is not proper tunda tasan bayaso batason azo a memeta abunda yamata ranar 


zainab dake jin ta girma yanxu she is in her 20s taje ya tabo rayuwar america bawani shege takalle tsakar idon anty safeera tace mata ita bakauyiya ce shiyasa batasan ya ake soyayya ba. ita abunda taga dama shi kawai zatay cos how can she even let her lover to kill his joy bcos of a mere corpse dat elapse long time ago.


baki bude anty safeera ta dinga kallon zainab arifah da mamakin jin kalamanta, dan  kuwa zuwanta american nan dataje tagamo da yaran turawa it seems like bakaramin kara lalacewa tarbiyanta yay ba, ga wani dan iskan nose ring datake sawa ynxu bama asaman hanci ba a ata ciki like a she-bull da wani irin strong make up din datakeyi..


tunda anty safeera ta lura da yanayin danyen rashin kunyar dake kan zainab arifah sai kawai ta kyaleta..


ayaana suna sashen ammi karama amma sosai labarin gift din arifah ya iso garesu mood din ayana sai ya dada canzuwa sosai ta dawo kamar wata wacce bata jin dadin komi, can da yamma kusan magrib ibaad ya dawo daga asibiti dan suyi sallah da su bappa zaidu da uncle moh ya gaida amminshi da su hajiya kafin ya wuce gida. yana kuwa zuwa shashen hajiya mairo ta taresa da batun irin abubuwan da zainab ta taho masa dashi, 


atake atake ya hada rai ya sauya fuska, the same siyasan da uncle moh yake zuwa ya shimfidamata ya nuna mata abu babu kyau haka shima ya mata ya haura mata da bori


yace mata last week anan nan falonta tazauna tana bada labarin haihuwar uncle moh ana buga shagali ana celebrating ana dariya

wato yau dayazo na mutuwar babansa shine zata mance ta kawo masa wani batun gifts din zainab arifah sabida bata dauki mutuwar babansa komi ba ko, dagan gan ya masifeta yace bata damu da ubansa ba, dama kuma ai ta jima tana nuna warayya akansu..tunda ya hade rai ya fadi haka shikenan kuma yasaka tsohuwa tafara kuka


ibaad yana wucewa sashen amminshi maza maza tasaka aka kira zainab arifah tana kuka wiwwiii tace mata sam sam ta tattara wann kayan ta koma dashi gida, rayyanun ma yace bazai karba ba, yau ranar baqin ciki ne, ita bata son wani kyautar da zaizo ya saka aga kamar tana nuna ma wasu warayyya. 


duk rashin kunyar zainab saida hajiy mairo ta fita bori tace sam rayyanu yace bazai karba wani kyauta ba kawai ta koma dashi inyaso ta kawo masa kyautan wani lkci amma ba a wann ranan da suke fama da jimamin mutuwar ubansa ba..


da tsananin fushi zainab arifah ta koma sashen anty safeera taje tana kuka..daga fannin ibaad kuwa babu yabo babu fallasa suka gaisa da amminshi a daki sukay jimamin su duk dama ita abun ya riga ya wuce mata aranta sosai dake bappa zaidu ma ya jima da hanata saka ire iren wann damuwa aranta har abun yaxo yay mata sauki.


 ta tambayesa  meyasa baizo tun dazu ba yace mata aiki ne ya masa yawa a asbiti duk dama sun kusa gamawa, ynxu nysc kawai ya rage masa kafin ya tattara komi nashi ya koma UK da zama dan acan zai dora da duk wani tarkacen major courses dinsa until he became a full cardiologist consultant

a imperial college dake london.


suna gama hirarsu ya wuce dakinsa direct yana zama akan gadonsa ya cire shoes dinsa tareda cirowani abu me kyau a aljihunsa a karamin box, sai yanxu ya kunna wayarsa text dinta guda uku ajere ajere daya gani yasaka shi yay dariyar bazata gamida kyabe baki


kan last text din ya danna mata reply ya rubuta waiting for u in my room..tana gani ta kalle sultana ahnlki tace "wayyo Allah na sultana yaa yana kirana...caraf sultana  ta mike tsaye da fargaba tace toh nide bari na koma wajen ammi karama duk abunda kuke ciki dashi ina can nasan dai bazai ci ubana agaban amminshi ba


baki bude ayaana yace haba sis meye haka dan Allah keda zaki rakani wajenshi ynxun nan muje mudawo


sultana ta dafe kirji tace  niii??? lallai ma ayaana toh inkin ganni a lahira kaini akayi

...kefa kinsan ba uban da zai miki kawai kije.. abubuwa nawa ne kikayi agidan nan yaa yay kamar baigani ba,kefa yar gaban goshinsa ne kijje kawai. 


a marairace ayaana tace shikenan..amma dan Allah karki gaya ma ammi kinji? inma yamin wani abu banason tasani ne bare ma ta masa magana bazaiji dadi ba


sultana tace toh sann ta fice da sauri ta nufi dakin ammi karama tana zuwa ta dale gadonta tafara zabga mata ruwan surutu duk wani hirar saurayinta ahmad kai tsaye take gaya ma ammi karama inna fada ne amata, inna dariya ne duk ayi. wann kusan wani babbam dama ce da ammi babba bata taba basu ba, cos she is always angry at her husband and plotting evil na yadda fatima bazata shigo mata gida ba, batama da lkcin sauraran yayan cikinta, gashi ynxu da maheer yay aure ko kadan baison kulthum tana shiga harkan mamansa yanama daya daga cikin manyan reasons dinshi dayaki sam su zauna anan nigeria da matarsa gabaki daya.


mikewa ayaana tay ta gyagyara fuskarta da powder, ta dau turarenta na black opium asalin na saint laurent da shine yafara saya mata, ta shafa shi dan kadan sabida yana qamshi me mugun kama jiki, batay wani kwalliya ba ta goga chappet akan lips inta me qamshin straw berry nan ta dau mayafinta cikin nitsuwa ta karaso har kofar dakin sa


tsayuwar minti biyu tay a kofarsa da fargaba tanamai kkrin tattaro ma zuciyarta da hanklinta nitsuwa waje guda. 

jin motsin kamr sun ammi zasu fito yasaka tay saurin yin sallama tun kafin ya amsa ta kuso kai suna hade ido yadan hade rai yace yawwa kinxo ko? oya..come over here".


wani irin kara bugawa kirjinta yay tafara tahowa ahnkli kafafunta har na harhadewa tana tafiya ahnkl kmr antsamo ta daga kankara ta taho, da gefen idonsa yake kallonta yana kkrin gintse dariyarsa ya ga idanunta ya ciko da ruwan hawaye, dahar zata tsuguna agabansa abazata taga ya miƙe tsaye ya tattarota a hannunsa ya dagata cak in a romantic bridal style.


cikin sauri da kuma bugun zuciya ta runtse idonta ji datay yay karamar dariya yasata sace wani tsoraccen ajiyam zuciya ta bude lumsashen idonta ta zuba acikin nashi ganin ita yake kallo da wani irin malalaciyar shauqi a kwayar idanunsa tay wani irin narkewan da bata shorya ba tareda saurin shagwabe masa fuska.


ahnkli kmr wacce zatamai kuka tace "where hve u been? bai amsa ba saida ya taho tare da ita ajikinsa suka zauna abakin gadonsan snn ya gyara mata zama akan cinyarsa yana kallonta yace" where u lookng for me?? adan kunyace ta gyada masa kai yace' toh gani..zaki cinyeni ko? 


childishly ta girgiza masa kai, gefen fuskarta ya shafa kadan snn yadago habarta datattausr  hannunsa,ahnkli suka hade ido yace"arent u going to ask me if i have loved the gift??? da tsananin fargaba acikin kwayar idonta tace"did you? 


saida yadan ja numfashi snn ya bita da wani irin piercing looks me narka gabobin jiki muryasa a kasa kasa yace "Best gift ever"..thank you! "i love it.. Dariya me sanyi me tafe da hawaye ya kufce mata tace well, i am glad u liked it

..karan hancinta yaja yace

"but ure scared ai..how did u fixed it over der?ahnkli tace its a secret..cikin kyabe baki yace "okay..by sending ur minions to my room.. so, shud i qurd my heart? kar wata rana in tashi abacci inji kin sace min shi


."dariya tay me sanyi adan kunyace tace"i wish i can...i will take you. yana kallon cikin idonta yace"nd u think u dindnt? tana murmushi tace i dont knw yet, yace hmm kajimin pretender! zagaya hannunsa yay ta bayanta ya zaro karamin box ya dora mata akan hanunta dake dafe da kirjinshi yace toh this is my return gift..ina so kisaka a yatsanki nd each time u miss me u look at it nd rembr u're very important to me

...tsiririn hawayenta ne ya sauka mata amidts her smiles cikin sauri ta bude ring din taga irin wanda ta bashine zak akayi replicating tace "ohh my god. thank you yaa! yace ure welcome.. ya karbi ring din yasa mata, dan kadan yay kissing hannun tanajin kamar zata narke dan dadi. suna hade ido girarsa na sama a dage yace nd ure to heavy sauka min akan cinyana karama dake kina da nauyi.


a mugun kunyace ta dan jingina ajikinsa snn ta zame ta sauka ta zauna daf dashi..


hira kadan sukayi sai sann ma tay noticing cewa agogon ne ahannunsa yace mata yay aiki ya gaji zaije gida cos he need to sleep early yau..har waje ta fito ta rakosa jikin motarsa ya sallameta kenan har zai shiga masjid suyi isha su wuce gida sai yaji ankwala masa kira da karfin tsiya da saida securitty men suka jiyo.


ganin zainab arifah ke zuwa yasa ya tsaya cak har ta karaso, da wani irin yanayi a fuskanta like she wanted to blow hot akan maganan gift din nan da sukay hajiya da yace bazai karba ba ta karaso, 


saidai already anty safeera tay warning inta, tace mata ba a awannan haukar ma ibaad dan zai iya gaura mata mari kuma tasan tana sonshi bata son suyi hatsaniyar da zaisa ya dena ma kulata kwata kwata


tana isowa babu wani sallama tace.. ibaaad .


yace yess.


tace 'wai ina ka shiga ne "ive been waiting for u..did  u have a minute?


ba yabo ba fallasa yace 

"ah huh...


wani irin yangataccen rolling idanunta tay tace "ibaad wai meke faruwa ne?i came all the way from manhattan to come home and celebrate ur birthday i even bot you a car with my own money. amma sai kaje kace ma hajiya kuma acemin bazaka karba ba..please what in the hell is the meaning of that..dont i mean enuf to you?? 


shiru yay har saida ta gama hucin snn yace "excuse you

...are you talkng to me or u are shouting at urself???cos nobody dare talk to me like that..


dan karamin tsaki taja a mugun hatsale tace "but of course i am talking to u..look ibaad pls dont say No to me

..just take the gifts.


yace "ohhh akan gift dinne kike wann ihun mtssss but i dont take gifts on my birthdays. anyways, thanks for trying.


tace "ni ba godiya nake so, just take the damn birthday gift please... wallah kawayena zasumin dariyaa wai mesa kake so walakantani ne ehhh?...tafada desprately looking soo silly nd authorative.


yace zainab yaushe muka fara wann wasan ne? you knw i am not the type da zaki bada oder. so take ur gift nd leave.


cikin katseshi tace ibaad

ban fahimce ka bafa why can't we be normal..all my friends have their lovers kuma wallah ba haka suke musu ba


yace ohh thank GOD i am not ur LOVER. or FRIEND. 


kamar zatay exploding da muryan ta da already yake rawa rawa tsabar bacin rai tace "what?


calmy yace "ohhh...ure not expecting me to act like ur lover or friend are u?


muryanta harna rawa rawa tace "But amma ai kasan ina sonka,i love you, nd i tot we are..we are.. in love for a long time


cikin katse yace "cousins dai ko"..kina so na sani, naji, kowa ya sani. no one stoping you, but u can't force love on ppl zainab. as matter of fact, i think...ive fallen for sumone else, nd u knw how it feels..

..nasan zaki fahimta.


tunda ya furta mata hakan kalmomi suka dauke abakinta hawayenta na zuba yarrr kamar ruwan rafi kuka mai matsancin karfi na shirin kurfce mata tay saurin toshe bakinta da wani irin bacin rai da isa tace "wallah wallah baka isa ba..kay kadan kace min kanason wata ko wacce ita wallah wallah bata isa ta kwace min soyayya na ba

..cikin matsancin kuka ta karashe atake taka fuskarta yay wani irin ja jikinta ya fara rawa sosai.


ahnkli yace "just tot i shud let u know i am taken. karkizo kice nay deceiving inki cos actually kece dama kikeso na nikuma yanxu inason wata daban.


kara fashewa da kuka tay tace ...'and you will regret it..we shall see wallahi, babu wata yar iskan data isa ta kwace min soyayya na..


tana fadin haka ta juya da sauri tana kuka ta koma ciki


kamar mahaukciya ta shigo sashen anty safeera tana wani irin kukan bori, anty safeera tay sauri zata riketa da wani irin fushi da hargagi ta wani irin bangajeta jakarta da key din motarta kawai ta dauka ta fice a gidan a mugun mugun fusace


hanklin anty safeera ya kasa kwanciya ko sallahn isha batay ba ta fito ta jira ibaad har yagama jansu sallah


yana fitowa ta tareshi da maganan yace mata shi baisan komi ba maybe akan gift dinne kawai asaka driver ya tarkata yabita dashi..


tunda ya gaya mata haka sai batace komi ba dan tasan tunda har zainab tay borinta tagama bai karba toh tabbas bazai taɓa karba ba koda duk duniya ne za'a taru.


washe gari sassafe haka ta anty safeerah tarkata komi da key din motar tasaka driver ya mayar mata gidansu, nd ever since yestade zainab arifah bata ci abinci ba, batay wanka ko sallah ba, dan ji tay kamar duniyar ne gabaki daya ya rushe akanta da har ibaad zai iya budan baki after all this years yace mata he is in love with sumone else kuma ba ita ba, shin wacece yarinya? a ina take, yar gidan dan uban waye, "wallh sai ta kashe ta, dan ko sharing in ibaad bazata iya ba. "he has to remain hers nd hers forever and alone, she kept telling herself cewa bata da kishiya a duniyan nan shiyasa ko awajen iyayenta Allah baima yita da kannen ko yayu ba, she is meant to be alone and alone forever in his heart wallh koma wacece yarinyar  ko tabar mata shi ko ta wuce lahira direct dan wallah bazata taba sharing ko hada hanya da wata mace akan ibaad ba..


ENJOY UR WEKEND DEARIES AKASSHE MU NIDA UNCLE DINA UNCLE MOH  DA PREMIUM COMENT SABIDA MONDAY MU TASHI DA ZAFI ZAFI HAR AGAMA BOOK 1 A SATIN GABA IN SHA ALLAH💋❤️



I REMAIN ON 08060712446

SURAYYAHMS

ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣0️⃣


wannan mummunan tunani na kisan kai zainab arifah ta dinga lailayawa aranta gata da dan uban zurfin ciki musmn in abu ya shafi matsalar soyayyarta da ibaad saidai kawai aga ta dawo gidan tana bori tana wasu irin dabiu kamar me aljanu saidai duk tsiya bazata taɓa sakewa har ta gayama iyayenta ko ta barsu su gane ba dan tasan yadda suke matsanancin sonta da shagwabata, they are almost too emotional abt duk wani bacin rai da takurawa da zai shafi rayuwarta, tasani sarai inta fada zasu iya daukar tsatsauran mataki akan ibaad itakuma sam batason akaiga wani matsayin da zata rasa shi kwata kwata...


Dan ma karta cigaba da zama da tunaninsa har ciwon damuwarta ya tashi yasaka on sunday night ta bada maid inta oder aka mata parking in kayanta na komawa schll ranar monday da sassafe jirgin karfe 9 ya wuce da ita U.S duk dama tunda ta isa schll bata samu wani nitsuwar zuci ba dan duk maganganun da ya furta mata akan he has fallen for sumone else yafi komi daga mata hankli yanzu tana da wani irin zazzafar kishi ne wanda yake ci kmr wuta a tsakiyar zciyarta kusan dakyarma take iya bacci abinci kuma ynxu bakomi yake burgeta ba kowa ya dawo yana bata haushi. kusan sati tay tana jin mugun zafin maganan ibaad aranta, a school ta dawo shiru shiru,.. she is alwys thinking. bata cika yawan kula kowa, koyaushe brain inta yana neman sanin wacece wann yarinya da ibaad yaganta har ta sace masa zuciya ba ita ba Allah Allah take tasan wacece dan taga shin dame yarinyar tafita, waye ubanta, nd how did she even get ibaad to fall in love with her wani irin dukiyaa wayewa ko kyau ne da ita bata dashi da wacn take dashi.


saidai tasan bata da wani hanyar da zata iya sanin dukkan wayann tambayoyin face sai tay amfani da private investigator agents din mahaifinta,kimtsa baqin cikinta tay acikin ranta, kusan ko kawayenta ma bata gaya musu komi ba duk dama sun damu da suddn sauyawarta sosai dan cikinsu nala ce kawai take karatu a cikin kasar england not so far from them, ita kuma rukky anan US din itama take karatu saidai iliminta baikai tashiga mkarntr su zainab Arifah ba amma sunfi kasancewa a anguwa kurkusa..a satin ta na biyu da dawowa tafara bada oder ma private investigator akn a duba mata duk wani movement na ibaad agarin kano da kewaye, she dsnt want them to track his phone cos it maybe a bad idea tasan inyaxo yasan tana stalking insa har haka wani sabon case ne..she trust her dad's agent to do the work secretly, tunda ta bada aikin taji dama dama ta dan komar da mind inta kan karatu.


Daga nigeria kuwa tun bayan da akay birthday ibaad kusan kowa ya koma hidimar rayuwarsa, safiya da ayaana suna daukar extra lesson sosai sabida tarin jarabawar kammala secondry dake gabansu, gashi almost the same time take kkrin yin sauka, abubuwa suka taru suka mata yawa, ga boko ga islamiya she hardly find time to breath inbawai ibaad ne ya kirata awaya ya sanyaya mata zuciyarta da kalamai ba. cikin wayann lokutan shakuwace mai bala'in karfi take dada ninkuwa acikin zukatansu, duk dama anayi yana jan mata aji da girma amma bata damu ba dan ji take kmr ma tafishi zurmawa.


tunda kowa ya dawo nrml life insa ynxu kwata kwata bata fiye lura da obsession din da Uncle moh yake nunawa akanta dan tuni ya dawo da tsoffin dabiunsa na yawan kashe mata kudi da baya kayan duniya anyhow, ko tana so ko bata so, xai siya ya kai ma hajiya mairo ita kuma hajiya haryau gani take kamr duk ahalin gidan babu wani namiji wanda yake mutuwar kaunar yaga cigaban rayuwar ayaanah kamar danta muhammadu duk dama ta dora fushin ayaanahn arannta da tunanin tana raina masa hankali,  tare da yawan dogding na kirarsa shikuma nunawa yake agaban hajiya kamar ma bai damu ba. 


but deep in his heart the way her body is evolving and changing yafi komi rudashi yanxu.


musammn irin healthy youthful glow da fuskrta yake dada haskowa dashi da uban freshness na fatar jiki datayi, da wannan wayewan fallin balagan nan dayake gani a kwayar idonta yadda ta iya kwalliyya ga sumulmulallen dirin jikinta dake kara susutar masa da kwalwalwa.


a dede wann gaɓar ammi karama take fara shirya yan matanta musmn ata ciki. ana daf da za'a yimasu waliman sauke qur'ani ammi tafara harhada abubuwan gyara da ake basu wanda kowa acikin yaran gidan ana bashi tun daga kan kulthum har sultana daga zarar ka gama secndry zasu fara gyaraka sabida rayuwar aurenka a gaba tunda su basu dogara da ikon maganin mata na wucen gadi ba.


ammi karama cikakkiyr yar maiduguri ne she have all this tactics datakey wajen gyara kanta ita kanta, shiyasa haryau alaman tsufa bai fara bayyana a gangan jikinta ba, despite her mid- age she is still very well menstruating sabida halittar da Allah yay mata  haɗe da yadda take balain kokari wajen kulawa da reproductive health inta sosai, wanda dama sbwar bincike yana bullowa game da lafiyar jikin mata nacewa boyayyun matsalolin rashin dedetuwar sinadarin kwayar halittar jikin mace shine yawanci silar daya saka wasu matan suke saurin tsayawa da al'adar su da wuri ko su shiga early menapouse a early 40s dinsu wasu ma a 35s. duk dama akwai na nature, saidai sabbin bincike kimiyyya suna dada fitowa suna nuna cewa jikin mata xai iya bambamta daga kan halitta har izuwa cikakken lafyar jiki zai iyayuwa daga inda watavta tsaya da haihuwa wata kuma ke dauka.  


yau shiyasa duniya take samun kala kalan testimonies na matayen da suke fara kafa labarin haihuwarsu daga kan shekara 45,47,50-52 har izuwa sama at rate of 1 to 5% na duka kiyasin matayen duniya gabaki daya. Ammi karama tafi kyale nata slow aging process in amatsayin halitta ne bata taɓa daukarsa abun damuwa ba, duk dama taga kawayenta da yawa yanxu sun fara shiga matakin tsayawa da haihuwar ma gabaki daya. ita kuma sai taga kamar ma yanxu ne kominta yake balain dada haɓaka da zafafawa musnmn ma sha'awa, koda ta tambaye abokiyrta dake aiki a asibiti kawai misali take kafa mata da manyan mata wanda yanxu ne ma suke fitowa duniya neman maza masu jini a jika domin biyar bukatr kansu saboda karuwar sha'awa. tunda tazo ta gane cewa kowacce mace da kalar halittarta she just ignore it saita cigaba da kulawa dakanta tunda babu wanda yake iya ja da ikon Allah.


ayayinda ake rububin shirya waliman saukar qur'ani na su ayaana da safiya, ammi ta nemo aya me kyau da dabino

busassu da farin ridi dan dede kamr 4 cup, da busasshen garin xogale shima bamai yawa ba, sai hulba dan kadan da small pinch na Cardamom


iyaka farin ridi da hulɓan ne kawai ta soya du sama sama snn tay Dry blending everything into smooth powder tay Storing insa a dry container..


1 table spoon na garin nan ake debawa a zuba musu acikin madara ko kunu wata rana asaka xuma wata rana kuma plain baifi sau 2-3 haka a sati ba...wanda duk wann shirin anayi ne dan lafiya da niima ya zauna ajikinsu sosai


da hadadden gumbarta datake kirarsa matar rarrashi, shima da gari dabino da garin almond da garin ridi da aya akeyinsa sai ana sumulmulasu acikin Raw honey har su dawo cikakaken gumba, each time in za'a basu su sha dissolving ake saka su suyi acikin wani abu shansu musmn ma madarar shanu. sai hadadden curves boost powderta data musu da garin Gyada, dana kwakwa, ridi, busasshen dankali,aya da kuma original dabino, dukansu in powder wanda zai na ciccko da dirinsu snn niima ya zauna ajikinsu amma ahnkli ahnkli.


batasaka kayan yaji kamr su citta,  kanunfari ba, hulba ma saffa saffa, saboda tasan yara ne, koda ake yawan musu tsammanin yin auren da wuri batason a ballo musu jarabar sha'awa da wuri shiyasa take bi ahnkli bakoyaushe take basu suna sha ba.



Dagata fannin zainab arifah kuwa bincike yay bincike amma duk kokkofin agents dinta basu samu komi ba saidai komi dayake ciki game da business insa da karatunsa sun samu sunga bala'in nisan dayay a dukiya, da irin yadda joint business empire dinsu Na Q4 sovereing ltd yake tafiya multinationals duk dama  duk sun yi re-investing wasu kudi into indivisual personal business, they are able to move they busines very fast sabida alfarma da kuma metwk of connection da suke da shi sosai da sosai suna cikin shekaransu na biyar kenan but each is networthing a personal billion naira in joint business alone.



sundauka duk abunda take son gani kenan amma inaa, aikuwa ko bude files din batay ba dan tunda taji babu abunda take nema acikin file dinsun tace musu suje sukona kawai dan karma babanta ya gani yaxo ya tambayeta meke faruwa.



time to time haka kishi data dora ma zuciyarta yake nadota tadawo nigeria, wata rana bata ma bari iyayenta su san tazo zataje hotel ne tay 2 days,intay wkend a family house sai ta koma schll saidai duk da haka babu wani abunda ya sauya a tsakaninsu the more she ask him questions the more yake dada jadadda mata cewa yana da wacce yake kauna yanxu.


bayan kmr wata biyu suna abu daya sai abun taji kamr ya fara taɓa mata kwakwalwa worst enuf that she cant find the girl nd bisa ga dukkan alamu ibaad is damn serious abt his secret new rlshp.


ta saka ido kota ina bataga komi ba, saidai tunda akay waliman saukar su ayaanah taga irin special abubuwan da ibaad ya siya mata ranar sai taji bala'in kishi da haushi sai bata kara dawowa nigeria ba.



zazzabi me rai da lafya tay harna sati biyu insctint inta sosai yafara gaya mata kode ma ayaanah ce budurwan tasa dan taga kamar  ibaad baiya wasu gentle nd soft loving behaviours din dayakey da kowa face ayaanah


And...God!!! she hates that girl so much,..tana jin tsanar ayaanah da zafi zafinsa har wuyarta yana mata kaikayi kullum.


ranar juma'a bataje lectures ba tanadai kwance akan couch dinta ta lullube jikinta da off white comfoter tay shiru cikin tunani, dan tsabar damuwar kishi da yunwa jikinta na rawa rawa kmr me ciwon masashhar kaji, daga ita sai masu mata aiki acikin apartment inta saiganan nala ta taho, ta danna bell ya kai sau uku zainab na ji bata miƙe ba har saida maid ta sauko kasa tazo ta bude nala ta watsa ma maid din harara ta karaso da masifa har ciki tasaka wani damammen riga da wando da wata babban jaka tanamai karewa zainab arifahn kallo "Babe ke kuma meye haka? ashe abunda rukky take gaya min ba karya bane kenan? what is wrong with you look at you so unkempt kamr ba ke ba?


wani soft tissure ppr zainab arifah tajawo tanamai tare sauran hawaye da majinan dake shirin sauka mata muryan ta adan dashe tace "nala kenan aike bazaki gane bane..i am lost..i am going insane. bana tsammanin ina da karfin cigaba da rayuwa ta, i am so confused nala ibaad is going to leave me wallah i can feel it in my hrt!!


da wani irin sauri nala ta karaso ta zauna kusa da ita cikin lallashi ta dafata da maraitacen murya tace


yanxu dan Allah akan sa kike wann abun ynxu fa almost 2 weeks kenan akace min baki da lafya..wai meyafaru ne tsakaninki da shi?? i tot u guys are cool by now ai.


cikin cizza labba da baqin ciki tace "no we are not nala, ahnkli ta dada rushewa da kuka tace "na shiga uku,na boyewa kowa damuwata ne sabida a tunani zan iya samun mafita..but nothing really works....nala hankalin ibaad yakoma kan wata yarinya, ya zanyi????


cikin matsanancin kuka take furta hakan gabaki daya saida hanklin nala yabi ya tashi ta rungumota..


tace 'its okay Zee-Arifah, its okay babe, kidena wann kukan kinsan dad dinki yaji labarin nan it will affect ur life nd studies.


cikin kukan tace "i know. nadaure nadaure amma bangane komi ba,..he keep spoiling one little brattttt, giving her all his attentions asif i dont even exist...ni ko ma yarinyar nan me yake cewa yana so? toh wallah in itane saina kasheta, she cant take him away. i will kill her..i will make sure she is deadddddd...


da karfi cikin girgiza ta nala tace "haba!! 'Enuf Arifah!!!!  wai me haka ne, kiga yadda jikinki yake rawa fa.. snn kar ki manta ba a nigeria muke yanxu ba..u got to mind ur own words..why wud kill her when ure not even sure itace..


da zafi aranta tace amma ai yafi sakaltata fiye da kowa a duniyan nan nala, wallah ko kece kikaga yadda yake janta ajikinshi yake mata wani murmushi saikinji kamar zaki hadiyi ranki ki mutu...i even did everything to look as beautful as her inma wai kyaunta yake gani but he is not even looking at me.


nala tace okay maybe ure looking at the wrong girl..ni fa wallah ban yadda wnn gayen zaice yana son yarinyan nan ba, waima me take dashi, tsabar kyau kawai??Zee-Arifah babu mahalukin da zai ganki a duniyan nan yace baki hadu ba, plus kinfita gata, kin fita arziki

..girl next week fa babanki zai daura ki a akan kujerar daya daga cikin babban kamfaninsa nd u want to kill urself over a  guy?downplaying ur value nd beauty over a village girl haba karki bada ni mana..i hate to say this, but gaskiyar rukky ce datace min kamar baki yarda dakanki ba. karki ga muna yawan kushe ra'ayin ruky amma sumtimes gaskiya take fada mana..zainab arifah akan

gayen nan kina bala'in zubda class dinki tun ba yau ba, ke ko dan ajn ajin nan baki masa

,..even rukky thinks ure soo classeles for him, dagske ne baki handling insa yadda ya kamata, tunda yace miki akwai wata macen ba kuka zaki zauna yi ba mafita zamu nema .


shiru zainab arifah tay dan tunda aka haifeta ba ataɓa tsaya an gaya mata maganan daya shige jikinta kao tsaye kamar wann ba, cak ta tsaya da gunjin kukan, ta zubawa nala ido can cikin jan numfashi tace "okay fine i think u might be ryt..i loved him soo soo much shiyasa banama iya gane me nake aikawa..tou ke yanzu me kika ganin zanyi? i really really want to knw that girl ko nawa ne san bata ta kyalemin mijina i knw i am meant to be his wife, in ibaad bai aureni ba zan mutu nala


nala ta riko hannunta tace zamu nemota but you wont kill her zainab..kisa fa yana da mummunan hatsari snn kituna strong international reputation na babanki da familynki gaba daya kika kashe wata wallh u have alot to looose.


Da wani irin hatsala tace "toh me kike so nayi nala?in zauna in zuba ido ya aure wata??lkcin dana bar nigeria ya riga ya gama housemship dinsa har ya fara nysc nd he will soon leave the country kuma bana cire tsammanin da aurensa zai taho UK karatu kamr yadda brother maheer yayi..u knw my family da wuri ake musu aure fa..and ibaad is very stubborn in yace zaiyi bamai hanashi


Nala tace okay calm down..i have n idea amma bansan ko kinada ra'ayinsa ba


desprerately zee arifah tace kigayamin kawai koma miyene ki gayamin zanyi.


ahnkli nala tace i know a woman in nepal, around northen india zata iya taimaka mana musan wacece yarinyar, ko kuma ta taimaka kawai a raba tsakaninsu all we need is just alot of money nd strict intentions


wani dan uban harara zainab arifah ta watsa mata da hatsala tace tuntuni kinsan da irin haka kika kyaleni inata damuwa??amma nala kema ai kinsan nafi karfin kowani irin kudi ko? ...a mugun dame tace so when are we leaving? ni wallah nafi damuwa da insan wacece yarinyar tunda kince min halama ba wancan bane


cikin kyabe baki nala tace "toh why not now tunda yau friday ne ba schl muje da wuri, dan acn acikin kathmandu take zama we need to book her early. inmunje yau muka huta gobe zuwa jibi sai tamana aiki.


cikn sauke ajiya zuciya zainab arifah tace cool toh muje ciki in shirya please help me call my maids daga nan suka mike suka haura sama kusan atare suka fara shirin tafiya india cikin gaggawa



Suna gama shiri jirgin karfe 6 na yamma ya saukesu a yankin garin kathmandu dake cikin north indian cos shi kathmandu is the capital city of nepal amma dake duk waje guda ne most ppl think is just north india.


gari ne me masifar kyau na gargajiya it doesnt shout luxury at all, manyan masana sunfi kirarsa da the Gateway city cos Kathmandu is the doorway to the beautifl Himalayas, mountain Everest, Annapurna, nd Langtang. 


akwai manyn wajajen bautan gumaka da aljanu bana kadan ba. duk dama gari ne na tarihi but yanada tarihi na sihiri da tsafi, maita da duk wani naiuinkan evil jinns, devilish act, da bokan ci me bala'in karfi. addini awajen baiya wuce Hinduism da Buddhism cos they live side by side  naturally ga monkey temple for (lord Boudhanath and Swayambhunath) ga ka babban lord shiva temple (Pashupatinath) na yan mabiya addinin hinduism wanda yafi kowanne mabiya a duniyar masu bautar gumaka

..wann gumaka da mai hankli yariga yasan cewa bakomi bane acikinsu face manya manya kuma bakaken tsofaffin aljanu da mutane suke kan bautawa.


garin kullum acike yake da baqi masu zuwa neman kowani irin mafitar rayuwa, da masu neman ilimin tsafi da masu neman normal ilimi, da writers, da su monks, wandarers da sauransu.


Da yamma suna isa nala ta bar zainab a local motel tafita neman lay practitioner da zai musu jagora gobe da sassafe 


tunda tafice bata dawo ba sai can wajajen karfe sha biyu na dare. 


baccinsu suka sha washe gari da safe mutumin yazo ya kirasu suka fito yakaisu can KOPAN Area inda taron buddist women suke nasu bokancin, kowace mace awajen ana ce mata ANI shiyasa ake ce matayen wajen ANI gompas..direct wajen wata ba indiya aka kaisu wacce itama budhism intakeyi

yauko karyawa basuyi ba aka kaisu wani dakin hutu aka basu herbal tea me masifar dadi suka sha after like 40 min of waiting aka musu iyo suka shigo ciki....


wata kiɓabbiyar mata ce a zaune akan jan dadduma kararrawa da jan candle yagewayeta


tana ganinsu tafara murmushi kamr wacce tasan me ya kawosu dake mahaifyar nala regular customer ce sunsan ta anan sosai shiyasa bata shan wahala indan tazo.


tun basu gaishe da matar ba suna zama ta fara gayawa zainab arifah damuwarta.


hanklin zainab ya kara harzuka ya tashi tafara rokon matar akan ta duba mata komi.


matsafiya Ani gompas tace  mata ta kwantar da hanklinta, nan ta xana wani circle da farin chalk tace ma zainab din ta taso tazo ta zauna aciki..


tana zama aciki aka sa ta nade kafafunta a tsakiya, Ani gompass ta dau chalk din ta kara sana circle da cross a goshin zainab arifah snn ta saka ta lunshe idonta karta bude, tana yin hakan, ita kuma ta fara zana abubuwa kmr astrology stars tana yi tana wasu sibbace sibbace bayan ta gama ta umarce zainab ta bata tafin hannunta


tana mikowa ta danna sau buyu akan stars din snn ta sakata ta doka goshinta da aka mata zanen circle din akai duk tayisu babu garga dama.


bayan nan ta bata ruwa a wani bakin kwarya ta sha kadan snn tace musu suje dakij jira su jira fitowarta, suna fita ta dauko sauran ruwan tamike dashi ta shiga wani waje..


tunda suka zauna a falon jira nala sai ce mata take ai daga yanxu matsalarta da ibaad ya kare kenan har abada dan wann matar bata wasa ko kadan..


sunfi awa suna zaune da fargaban kalar sakamakon da zasuji duk dama sunriga sun saka aransu nasararsu kawai zasuji


can wata mata tazo ta kira nala wai tazo ta karbi aikan mamanta, sai aka bar zainab arifah anan azauna,  nala tana shiga dakin kuwa ta samu matar a tsaye Da alaman Hankalinta yayi matukar tashi dan ko murmilushi bata iyawa


sun tsani suyi aiki a dawo musu dashi da wani evil energyn. it turns out sosai juma da taawure suka kulle jikin yaransu da kariya asalin irin tasu na fulani da buzaye.


ashe abu kam tayi duba an gano cewa tauraron ibaad dana zainab arifah ne ma kwata kwata basu hadu ba dan haka zaman aure ko yin auren ma tsakaninsu zaiyi matukar wuya


Ani gompas ta tabbatar mata cewa ibaad yana da matarsa and she cundt see even her bare ta gaya musu wacace sabida an rufe ta kirif da kariya, snn bazasu iya raba soyayr ba sabida me daurewa ce. ita kuma zainab wnm soyayar tata kamr karman ta ne.


da baqin ciki aran nala tace haba Ani amma dai kinsan hakan bazaiyu ba. dan idan naje na gaya ma zainab wann magana daga kaina zata fara kisan kai just do sumting abt it ...



babu bayanin da Ani gompas bata ma nala ba amma taki sam tace badai agaya ma zainab arifah wann batun ba tunda suna da power suyi kkri abasu wani abu da zaisa koda ace soyayyar ibaad zainab arifah ta dandana..


daga nan Gidan wani mutum aka kaisu Gidan kamar temple din bautar gumaka duk an sakaya shi da jan kyalle an kuma ajiye wasu halittun gumaka ga hayakin dake tashi daga manyan kaskon wuta wanda basusan me aciki Ba.


Wani tsohon ba indiye ne yafito kirjinsa babu riga yadaura wata farar kyalle akan kugunsa goshinsa an zana farin layi har zane biyu


Yaren su yake yi dan haka ba sujin meyake fada .


Wani daki ya nuna ma zainab arifah anan aka shiga aka fito da ita daure da jan yadi Ta fito narai narai Ko dan kwali babu akanta.


Ita dai binsu take amma badon ta gane komi ba domin kuwa idon nala akan ta yake takuma hanata yin questions akan komai..


wani shirgegen bath mai fadi da sakewa mutumin ya mata nuni yace ta shiga har sai da ruwan dake ciki ya rufe mata goshi


Aciki ta nitsu,ba abunda take yi sai yatsine, Sau uku mutumin yana sata tana nitso tana fitowa daga bisani sai yace ta fito ta zauna akasa


Tana zama ya shiga wasu irin addaoin irin nasu ma india,

yana turara ta da wani irin hayakin ganye.


nala tana zaune tana kallon su haka ma Ani gompass


Haka akayi ma zainab arifah wannan wankan sau biyu har na ranar sunday  kafin nan suka biya kudi suka fara shiri zasu dawo gida.


wani kasko aka basu an rubuta sunanta dana ibaad akan jan kyalle sa bebin roba namji da mace aciki sunce daga taje dakinta daf ana kirar sallan magrib ta dau kaskon ta rike ta kalle gabar gudu da arewa ta kira sunan ibaad sau uku uku da zimman zaiji wann kiran a duk inda yake zaiji hanklinsa ya mugun tashi ya rasa nitsuwarsa bazai kuma taba samun nitsuwa ba har saiya taho inda zainab arifah take



nala duk bata gaya mata meye hakan yake nufi akan ibaad ba duk dama tay tay a fada mata menene wannan din kuma waye yarinyar amma sai shiru wani bin sai tace bazata gane ba.



Haka suka dawo UK  babu wani kwakwaran bayani, nala warn her to take care of the clay pot kar ta bari a fasa ko ta zubar da abunda yake ciki.



daren ranar suna rabuwa zainab ta dau magananin ta saka a drawa inta tay banza dashi sabida batasan asalin amfanim da xai mataba, tafi maida hankli wajen son sanin wacece yarinyar.


washe gari monday a lalace ta tashi sabida tana da sakalci da lalaci dan haka wanka kawai tay ta wuce schll abunta bata kara duba kaskon na.


ata bangaren nala kuwa tsabar gulma tun jiya da dare da suna dawowa data bar gidan zainab arifah direct ta sauka agida kawarsu rukky jikinta na rawa ta fara bawa rukkyn labarin duk abunda yake faruwa


wanda haryau rukky mamaki takeji, na yadda nala take nuna tana tare da zainab arifah dari bisa dari amma a zahiron gaskiya kuma ta tsaneta, tana balain kishinta, da duk wani gatan datake dashi, infact batun cewa za'a dora zainab next week akan kujerar daya daga cikin mayan kamfanin babanta yana balain cixon nala aranta har yanzu


da murna da rawan jiki tace ma rukky kawata ingaya miki matar nan tace min she is just wasting her time on ibaad, yarinyar da yake so din ma tafi karfinsu, bansan wani karya zan mata bane yasa nayi shiru amma zuwa gobe idan nay tunani i will tell her  cewa boka takasa raba soyayyar, then i wll be collecting alot of money from her cewa ni zanna zuwa nepal ina mata jigila untill i become god damn rich hahahahaah..


da mamaki rukyya tace toh yanxu intazo taga abu baiyu bafa, ke fa kinsan zainab arifah once she is angry kisa ne kawai ke zuwa mind inta.. 


snn banga amfanin soyayar da babu riba da kika karbo mata ba. wallah wahala zatasha koda yajuyo yana sonta. matar nan ta gaya miki they dont match, soyayya babu aure meye amfaninsa? kenan dukansu biyu kin lalata musu rayuwarsu gashi kuma zaki amshi kudi...nala i knw dis isnt my businsss but i think  this it too much for zainab you went too far gaskiya


wani yatsina fuska nalan tay tace "wann fa ita taso, dan ni bai shafe ni ba. banyi kkri bane dana samu mata soyayyarshin ma ? abeg abeg i know she will be thanking me soon in ibaad ya fara kulata.


rukky sai batace komi ba ta kyabe baki suka gama hirar nala ta kwana agidanta washe gari sassafe ta koma england tabar rukky da tunani, she started to feel like in suka ma zainab arifah haka basu kyauta ba, or lets just get to the queen of pretence..


gaban madubi rukky ta je ta kura ma kanta ido cikin lumshe ido da budewa tafara tuna cewa fa itama son ibaad dinnan takey kamar zata mutu aranta, kuma yana daya daga cikin manyan dalili datake kushe lamarin zainab arifah dashi, she wanted to use logic ta cire ma zainab sonshi sai ita ta samu daman shigewa jikinshi amma inaa ga nala yau tanaso ta jawo mata babban matsala yanxu..


daukar wayarta tay ta kira zainab arifah jin datay ance tana school yasaka tay maza maza ta fada wanka zuciyarta cike da sake saken abunda zata aikata. tana fitowa ta tsantsara shiri, direct ta dauki spare key ta wuce gidan zainab arifah masu aiki ne  kawai dake ma sunsan zainab bata da wasu kawaye face su daga sukaga rukkyn ta iso agaggauce sai basu damu ba.


rukky tana gama parking tun daga kofa tafara pretending kamar bata san zainab tana schl ba nan tafara kwallara kira zainab arifah...zeee baby, ..Arifah...masu aiki na kkrin gaya mata batanan tawani daka musu tsawa tace karsu sake su zo jikinta suna warin baki...


kai tsaye cikin izgili tawuce dakin kmr zainab din kawai take nema, sharply tayi dube dubenta har ta samu kaskon tsafin da sauri ta saka a katon jakarta ta fito da sauri, ta shiga wani sashe...kafin ta sauko can kasa, while still pretending tace ma masu aikin ina zainab take? nan suka mata bayani, cikin bude musu ido tace musu surprise tazo ta mata dan tagaya mata cewa tay sabon saurayi amma tunda bata sameta agida ba karda wata acikinsu tay gigin gaya ma zainab din cewa tazo idan ba haka ba saita saka an koresu a aiki....wasa da hanklin su tay sosai ta tsorata su, kafin ta wuce ta kama hanyarta tafi..


tana zuwa gidanta ta karewa kaskon kallo wani irin baqin kishi ya turmusa mata rai ganin har wani doli doli mace da namiji aka saka aciki aka daure da igiya snn aka rufesu da jan kyalle me dauke da sunan arifa da ibaad


haushi ya kamata ta rantaba kaskon akasa saida ya fashe into tiny pieces tana huci tace "if i cant have him kema wallah baki isaaaa ki mallake sa ba, daukar doli dolin tay ta kunce tana kuncewa daga can school kawai aka ga zainab arifah ta yanki jiki daga zaune ta suma


maza maza akay rushing inta medical emergency and her cause of pass out is still unknwn for hours bata bude ido ba but she is still breathing


haka rukky tasa wuta ta kona daga jan yadin har doli dolim snm ta kwashe kayan banza ta zubasu a shara nan ta shirya babu jira tawuce dubai hutun sati biyu..


Post a Comment