Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

ZANEN DUTSE CHAPTER 3 BY AISHA-SHAFIEE

 ZANEN DUTSE CHAPTER 3 BY AISHA-SHAFIEE

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tafiyar motar a wane irin yanayi ne da Jidda ba zata iya fassara shi ba, ta kasa gane gudu suke ko kuma akasin sa, tunda ga abubuwa nan suna wucewa cikin matsanancin gudu amma kuma a cikin motar kamar a hankali suke tafiya saboda yadda komai yake dum-dum.+

Kuma har a lokacin tana takure a kan kujerar ta kasa ko motsi sannan in banda sanyin A.c da k’amshin turaren nan nasa ba abinda ke shiga kwakwalwarta.

Ga duhun magriba ya fara lullub’e gari a lokacin, ga k’afarta da ba takalmi duk ta tako shinkafar da aka zubar a k’asa sanda ya jawo hannunta zuwa waje, don haka tana son ta mik’a hannu ta karkad’e su amma tsabar tsoron yadda ingarman jikinsa ke zaune a gefenta yasa ko kwakwaran motsi ta kasa. Fuskarta na juye kawai tana kallon window, kuma da alama shima bai ko kalli inda take ba tuk’insa kawai yake.

Bata san inda suke bi ba amma hankalinta ya nuna mata cewa hanyar barin gari ne tunda ta fara ganin k’arancin gine-gine da kuma al’umma, sai kwallar data share sau ba adadi tun daga fitowarsu daga cikin masarauta ta sake taruwa a idonta…

Ina zasu je?

Ina zai kaita?

Shikenan tayi sallama dasu Baddo?

Wannan wace irin k’addara ce, dame zata ji ne wai?

Hawayen ya gangaro kan kumatunta a lokacin da sallar da maza keyi a gefen titi ta nuna mata cewa magriba tayi tunda gari ma yayi duhu, sai tunaninta ya lissafa mata cewa shima zai iya tsayawa yin sallar, kuma zata iya samun hanyar guduwa in har ya tsaya d’in don ko ya k’ulle k’ofar motar zata iya ta dukan gilashin har wani a waje ya ganta ya kawo mata d’auki…. Amma sai duk wannan tunanin ya rushe a lokacin da motar ta hau kan gadar flyover ta barin gari…

Ta san hanyar sarai, don hoton wajen na manne a tunaninta tun a ranar da suka shigo garin ita da su Baddo bayan rasuwar mahaifiyarta, flyover ce mai kyau data sha adon tarin fitilu, hakan yasa ta kasa mantawa da ita tun wancan lokacin, bakinta ya had’iye wani busashshen yawu sannan wata kwallar ta sake taruwa sanda hasken fitila ya dallare fuskarta…

Shikenan rayuwarta kuma ta shiga wani babin, sai yadda ubangiji ya k’addara da ita!

Zuciyarta ta matse sannan wani d’aci ya cika k’irjinta, sai ta rantse a cikin ranta cewar duk abinda zai faru daga yanzu itama zata kare kanta, ai ba laifinta ne kad’ai ba har da nasa shima, tunda ya kasa hana mahaifinsa abinda su duka biyun ke nadama tun a yanzu. Ta san tana d’an shakkarsa amma duk da haka bai isa ya cuce ta cikin sauki ba, ko namanta zai ci to lallai ba zai ci shi ta dad’i ba.1

Suna sauka daga flyover idonta ya nuna mata duhun dajin bishiyu fal a kowanne b’angarensu, ta k’ara tabbatarwa cewa sun bar gari kwata-kwata.

Allah ya isa!2

Bakinta ya furta a hankali sannan tayi kwafa, kwafar dake nuna cewa ta shiryawa koma me yake jiranta a gaba, tunda ya ruguza hasashenta na cewar sakinta zai yi, to zata bi shi a sannu har ta fahimci manufarsa akanta kafin ta san irin matakin da zata d’auka itama. Ta yarda cewa zuciyarta na da wannan k’arfin gwiwar, rauninta kawai shine zata je inda babu Baddo balle Jamila da Sadiya…

Tana wannan tunanin ne sai ga k’arar wayarsa wanda ya cika shirun motar, hakan yasa lissafinta ya tsaya cak sanda muryarsa mai zurfi ta amsa kiran.

Ina jinka…

Sautin muryarsa na farko ya kara tuna mata kusancin zamansa da nata, don da yake fuskarta a juye take sai take jin da kamar sun d’anyi nesa da juna ne, saboda haka tayi saurin matsawa ta k’ara mannewa da jikin k’ofar motar kafin sauran maganarsa ta biyo baya.

Eh, I’m on my way…

Na gaya maka su Habibu sun taho tunda safe…

Yayi shiru kafin ya sake fad’in

STORY CONTINUES BELOW

Yes, ni da ita ne…

Sai akayi wata tsawa har da walkiya a cikin kan Jidda jin ya danganta kansa da ita a cikin jimla d’aya, ta sake had’iye wani yawun sannan ta shiga motsa ‘yan yatsun k’afarta.

Wani dogon shirun ne ya sake biyo baya alamun yana sauraren tsararren bayanin da na cikin wayar ke yi masa…

Waye shi ne? Kuma me yake fad’a masa? Wani abu suke shiryawa akanta?

Kar ka damu Mubarak, babu abinda zai gagare ni insha Allah.

Muryar Madakin ta fito da wani irin yak’ini na cewar ya yarda da kansa kuma da gaske zai iya koma meye d’in.

Sai ta gyad’a kai itama sannan ta shiga kokarin d’aurawa tata zuciyar d’amarar yak’i, don koma me suke shiryawa shi da Mubarak d’in to sai inda k’arfinta ya k’are itama, ai hausawa sunce ba’a cizon mumini a rami d’aya… An wuce matakin farko an shigo na biyu inda itama zata iya d’in!

Kuma idan lissafinta daidai ne, zata iya cewa daga wannan wayar ya amsa tarin kira kusan guda ashirin kafin su kai ga tsayawa, amma da alama duk akan harkar aikinsa ne don ko kadan bata ji ya sake ambatar wani abu daya dangaci halin da suke ciki ba, yawanci da turanci yake maganar.

Hakan yasa ta shiga tunanin wane irin mutum ne shi mai comitments haka? Ta yaya yake jin dadin rayuwarsa babu wani abu sai aiki kawai, amma sai ta ture wannan tunanin lokacin da ta tuno zagayen halin da take ciki, babu ruwansa da rayuwarta tunda shi da ita yanzu kamar mai yak’i ne da abokin karawarsa.

**

Sun shigo Garin Kano da misalin karfe bakwai da rabi na dare.

A yanayin Jidda tana da baccin mota sosai, don a baya sanda tana k’arama ko ‘yar k’aramar unguwa za’a fita in dai za’a hau mota sai taji idanunta sunyi nauyi, balle ace barin gari za’ayi ai tun a go slow zata fara gyangyadi, kuma har lokacin da ta fara wayo, mahaifiyarta bata tab’a bari ita kad’ai a tura ta wajen da sai an hau mota, cewa take.’Idan Jidda ce sai a wuce da ita, a kai tasha, a sake lodi a juyo tana ciki tana bacci.’  saboda haka ko sanda zasu zo Kiyari Baddo ta tashe ta daga bacci ya yafi sau goma tana komawa.

Amma yau da yake a cikin masifa da hargitsi take, sai gashi idonta tarr ana tafiya har cikin Kano. Abu d’aya da ya canja shine ta fara sabawa da zaman motar har ta nad’o k’afafunta kan seat d’in kujerar tana faman baza ido wajen hasken fitilun kantina kala-kala.

Zata iya cewa rabonta da Kano tun bata da wayo, wani lokaci da suka zo biki a dangin babanta ita da mahaifiyarta, don haka ta shagala da kallon sababbin cigaban garin a gefe daya kuma zuciyarta na tunanin abinda zai yi a Kano… Ko kuma abinda zai yi da ita a Kano.

Idonta na kan titi har sanda motar tayi kwana ta shiga harabar wani katafaren gini da a samansa aka rubuta.

Hamrish Cardial Hospital.

Kalmar asibitin kawai ta fahimta saboda yadda tunaninta yake a hargitse, sai zuciyarta ta shiga hasashen me kuma za’ayi a asibiti? Waye bashi da lafiya? Kar dai ita ya kawo…. To me za’ayi mata?

Tayi tunanin ta juyo ta kalle shi amma zuciyarta ta gargad’e ta, ta gaya mata cewa dukkan kwarin gwiwar data tattaro zai rushe da kwarjinin wad’annan idanun nasa, saboda haka sai ta tsaida fuskarta akan wani gini da aka yi masa b’aro-b’aron rubutun Pharmacy, sai dai tana jin kamar ta tura idanun nata k’eya su gano mata me yake yi.

“Idan kika yi wani abu kafin na dawo, zan tarwatsa kanki.”

Abinda ta tsinta kenan daga can k’asan mak’ogwaronsa kafin k’ofar motar ta bud’e kuma ta rufe a lokaci d’aya.

***

09:10 PM

AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPOT.

STORY CONTINUES BELOW

“Kayi hakuri ranka ya dad’e, wallahi go-slow ne ya tsaida ni, hanyar ta cakud’e da yawa ga kuma sha’anin dare.”

Cewar Hamisu, mutumin da yake harkar cinikin mota dashi, a lokacin suna tsaye ne a harabar ajiyar motocin na filin tashin jirgi na Malam Aminu Kano.

Madaki ya girgiza kai yana mik’o masa muk’ullin motar dake hannunsa.

“Kar ka damu Malam Hamisu, nima da yake bayan shigowata garin na d’an tsaya a asibiti ne, to ban dad’e da k’arasowa ba.”

“Yauwa yallab’ai, nace kuma an d’an samu akasi wannan karon wallahi kud’i sunyi kad’an a hannuna, rabin kudin kawai na iya turowa, amma insha Allahu kafin k’arshen sati mai kamawa sauran na tafe.”

Madaki ya shafo hancinsa da d’an manunin yatsansa sannan yace.

“Ba matsala, nima yau abubuwa sun min yawa ne ban ma duba alert d’in ba.”

“Ayya to insha Allahu dai zan ciko maka su a satin nan ranka ya dad’e, ba zasu mak’ale ba.”

“Kar ka damu Malam Hamisu, idan ma sun mak’ale ai muna tare ko?”

Sai Hamisun ya kyalkyale da dariya mai nuna alamun cewa ya fahimci rahar dake cikin maganar.

A k’aida Madaki ya san cewa ya kamata ace murmushi yazo kan fuskarsa shima, don sun saba irin wannan wasan dashi a duk lokacin da yazo, amma yanzu da DA ba d’aya bace… DA wadda zai kira da JIYA kawai, don daga jiyan rayuwarsa ta canja kamar ruwan da aka gauraya da tab’o.

Yana jin kansa ne stranded, kamar mutumin da ya b’ata a tsakiyar sahara yake neman hanyar gida kawai, don duk abubuwan da ya shirya kuma ya tsara a cikin watan nan nema suke su kub’uce masa… Karo na farko a rayuwarsa a yau ya ture request din wani kamfani na tarin miliyoyi da suka nemi su shigo musu da kayan ceramics daga kasar Portugal.

Abinda ya fad’awa babban sakatarensa kenan wadda ya kira shi akan batun cikin harshen turanci, kuma a cikin zancen nasa ya hango irin d’imbin abinda suka rasa don ya sani cewa Mubarak ma akwai ayyuka a gabansa kuma su biyu kad’ai ke da ikon signing sababbin request.

Ya tafka asara yana ji yana gani, a dalilin wata ‘yar karamar halittar da ko plain sheet d’in kan teburinsa ta fita daraja.3

Ya had’iye wani abu a mak’ogwaronsa cikin tsananin fushin da ya fallasa girman Adams Apple d’insa, ya san cewa kamar irin contract d’in da yake dealing dasu, wannan ma ya riga ya tsara dukkan wata hanya da kuma matakan da zai d’auka, ya shirya komai tsaf! Ya shirya yadda zai d’aid’aita rayuwar yarinyar da kuma ta shugabarta (Fulani), ya gama shirya yadda zai kawo k’arshen wannan diramar da suka shirya akansa ta yadda zai zama wanda yafi kowa taka rawa a cikin wasan.

Amma lissafin yadda hakan zai kasance da kuma lokacin da za’a d’auka wajen cimma manufar tasa shi ke caja kwakwalwarsa. A hankali ya juya ya kalli fuskar motar dake tsaye baya dasu kadan, ta cikin gilashin dake haskawa da raflection d’in fitilun wajen ya hango ta.

Tana zaune yadda ya barta, sai dai ba’a juye ba, su take fuskanta sannan idanunta a tsaye kyam tana hangensu… A lokaci guda yaji wani abu kamar gumi ya tsatstsafo a tsakanin yatsuntsa, yatsun daya rik’o hannunta dasu… Sai ya had’iye yawu a mak’ogwaronsa sannan idonsa ya shiga hango plan d’in daya tsara akan zanen fuskarta.

Ya riga ya samu overview dinsa akanta, ya fitar da stretegy, ya zana mission statement sannan ya tsara dukkan goals and objectives d’in da yake son cimma, threat dinsa guda daya ne… lokaci, don ko ita baya lissafawa a cikin abinda zai iya kawo masa matsala, ya dad’e da soke kalaman da baiwar nan ta gaya masa akanta tun a lokacin da ta fad’e su tsugunne a gabansa.

‘Bata da kunya ranka ya dade kuma bata da tsoro…’

Abinda baiwar ta fad’a kenan.

‘Zan tarwatsa duk wasu halayenta Mubarak ta yadda zata tsorace ni kamar yadda bawa ke tsoron shaidan…!’

STORY CONTINUES BELOW

Maganar da ya fad’awa Mubarak a waya bayan fitar baiwar ta amsa a cikin kansa.

“Nace yallab’ai, yau tafiyar dare zaka yi kenan?”

Muryar Hamisu ta dawo dashi zuwa duniyar zahiri, sai ya juyo ya kalle shi sannan ya gyad’a kai.

“Eh Jirgin k’arfe goma zan bi, bari in fito da kayana sai ka d’auki motar.”

Sarai Hamisu ya san cewa Madaki baya tab’a bari ya d’auko masa kayansa, yasha hana shi hakan ba sau d’aya ba sau biyu ba, saboda haka yana tsaye yana kallonsa har ya juya ya k’arasa jikin motar, ya bud’e k’ofar baya ya fito da wani d’an madaidaicin akwati da kuma briefcase sannan ya dawo ya bud’e ta gaba.

Anan numfashin Hamisun ya tsaya cak saboda tsabar mamakin abinda ya hango.

“Come out.”

Madaki ya fad’a yana kallon ‘yar k’aramar fuskar Jiddan da har yanzu ke shaida kumburin kuka sannan kuma saman hancinta yayi ja saboda azabar sanyin A.c data da ya ratsa ta.

“Zuwa ina?”2

Wannan karon bayan karfin halin kallonsa da Jidda tayi, muryarta ma tayi k’okarin magana duk da ta sani cewa bayan zaman tarin awanni a cikin motar, ba abinda zata so irin k’afarta ta taka k’asa don ta gaji sosai, amma kuma ta riga ta fahimci cewa a Airport suke saboda haka ba zata fito ba sai taji me za’ayi tukunna, don ita bata tab’a tunanin hawa jirgi ba, balle har ta shirya hawansa a yau.

‘Yan kalilan d’in labaran data sani na fadowar jirgi su suka sa mata shakkarsa tun farko, don ko idan Baddo na fatan zuwa Makka, ita bata hango nata zuwan a kusa, gani take sai ta manyanta tukunna abin ba’a kusa yake ba… amma sai gashi tun ba’a je koina ba yau gata a filin jirgin tare da mutumin da bata san manufarsa akanta ba sannan babu ko takalmi a k’afarta… idan k’addara tana da sunaye dubu a duniya, to bata jin a cikin dubun nan za’a sami sunan irin tata k’addarar.

Karo na biyu kenan da Madaki yaji muryarta, kuma karo na biyun kenan da zuciyarsa ta gaya masa cewa akwai wani abu daban a cikin muryar da bai saba ji a wajen sauran mata ba, zuciyarsa ta ayyana masa cewa hakan na d’aya daga cikin tanadin Fulani, dole ne kafin ta aiwatar kudirinta, zata yi kokarin kokarin  cike duk wasu gurbin da take ganin zata yi nasara akansa, kuma ba laifi ya sara mata akan hakan tunda ga yarinyar ma na kokarin fara taka rawarta, tana kokarin nuna masa bata san abinda ke faruwa ba ko kuma inda suke shirin zuwa, wajen da ya tabbata an shirya mata tarin karatu akansa… babu karya kowannensu yana kokari a b’angarensa, abinda ya rage shine ya fara nasa takun wanda zai ruguza su har buzunsu. Sai dai komai d’an lokaci ne, bai cika gaggawa a al’amuransa ba.

Saboda haka ya maida akwatin d’aya hannunsa sannan ya sunkuya ya sake kamo hannunta, a lokaci guda yatsunsa suka nad’e cikin nata masu laushi… Kuma kamar d’azu sai wani abu da bai san sunansa ba ya ratsa har cikin kansa, zai iya lissafawa cewa tunda daga lokacin da ya mallaki hankalinsa a duniya bai taba rik’e ko da farcen wata mace ba balle har aje ga hannunta, watakila shi yasa yaji hakan watakila kuma wannan ma yana daga cikin wani tuggun na Fulani, sai kawai ya k’ara had’e yatsun nata tsakanin nashi sannan ya jawo ta daga cikin motar duk da alamun da yaji cewar tana tirjiewa.

Nazari, na daya daga cikin matakan da ya tsara akanta, don haka zai nazarci koma wane irin feeling ne wannan don ya san asali da tushensa…

Farkon farawa Jidda ta san ita ba yarinya bace k’arama da zai dinga kamo hannunta haka, sannan na biyu yana cin albarkacin kwarjininsa ne kawai da kuma wannan sunan da aka lak’aba masa na mijinta amma da tun a inda suka tsaya da farko zata iya tara masa mutanen da bai zai iya fitar da kansa cikin sauki ba.

Malam Hamisun na can tsaye yana kallonsu da dukkan wani mamaki na duniya, ya san cewa Madaki kaya yace zai d’auko, kuma shima kayan ya saba ganin yana d’aukowa daga motar duk sanda suka had’u a irin wannan lokacin, amma baya jin ko a zamanin siyan bayi ana saka kalmar ”Mace’ cikin jimlar kaya.

STORY CONTINUES BELOW

Ina Madaki ya samo yarinya budurwa a wannan daren?

Yana dai da tabbacin ba sato ta yayi ba kuma ya sani cewa fuskarta bata d’aya daga cikin ‘ya’yan Mai martaba balle har yace ‘yar’uwarsa ce…

Idan kuma harka ce ta rashin gaskiya ya tabbata Madaki ba zai rik’o mace a bainar jama’a haka ba saboda ba halinsa bane.!

Sai a lokacin da muryar Madakin ta k’araso gabansa sannan ya san cewa ba mamaki yayi da farko ba.

“Malam Hamisu sai muyi sallama kenan ko? Wannan matata ce sunanta…”

Sai ya d’an juya ya kalle ta kamar a fuskarta yake son tuna sunan kafin ya k’arasa.

“…Maijidda.”

Cikin sauri Hamisun ya shiga kokarin durkusawa yana fad’in.

“Masha Allah, wallahi bani da labari yallab’ai, ban san anyi ba. Allah ya sanya alkhairi ranka ya dad’e Allah ya bada zaman lafiya…”

A lokacin Idanun Jidda suka bi Madaki da kallo sannan zuciyarta ta shiga saka da warwara, akwai wani abu dake faruwa wanda bata san shi ba, dole ne ma akwai wani abu… In ba haka ba ta yaya mutumin da take tunanin zai sake ta tun kafin taron ‘yan masallaci da suka had’a su su gama watsewa zai zo kuma yana gabatar da ita a gaban mutane? Ai hakalina ma ba zai dauka ba ace daga had’uwarsu jiya, a daura aurensu a yau ba tare da ya san komai akanta ba kuma ya yarda da ita har haka? tunaninta ya katse sanda Malam Hamisu ya juyo da gaisuwarsa kanta.

“Barka da dare ranki ya dad’e, Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya.”

Taji gaisuwar amma bata juyo ba, don karo na farko kenan tun bayan lokacin da ya kamata a bayan labulen d’akinsa da ta k’ara had’a ido dashi, don shima a lokacin idonsa na kanta ne, kuma karo na farkon kenan da ta fara gane wani b’angare na manufarsa akanta

Ta fahimci tabbas akwai abinda yake shiryawa game da ita kuma bayan hakan yana kallonta ne kamar wata k’aramar yarinya da zai iya juyawa cikin ikonsa, maganar da ya fad’a mata sanda suka tsaya a bakin asibitin nan ta maimaita a cikin kanta, kuma tar a yanzu ta fahimtar da ita cewar ko kad’an tunaninsa bai sanya ta a cikin layin wad’anda suka san abinda suke yi ba.

Zuciyarta ta doka tsallen murna a take, don wannan hanya ce mai b’ullewa a gare ta, zata bishi a hakan, zata bashi dukkan wata hujja da zata k’arfafa tunaninsa har taci tata galabar akansa… Sunanta kawai ya sani amma ko kadan bai san wacece ainihin Maijiddan dake kwance a k’asan ruhinta ba. A yanzu rauninta d’aya ne, rashin su Baddo da kuma kewarsu da zata fuskanta, amma tunda bata da zab’i zata daurewa hakan har zuwa lokacin da komai zai k’are, zata fuskanci komai d’in da dukkan kokarinta ta yadda babu wanda ya isa ya cuce ta, me yace ne d’azu a waya?

Kar ka damu Mubarak, babu abinda zai gagare ni insha Allah.

Shine Madakin da babu abinda ya isa ya gagare shi, don haka ta ajiye matsayinta na Jiddan, itama a yanzu matarsa ce da babu abinda ya isa ya gagare ta..!2

Kwarai! Zata nuna masa hakan ta hanyar wani karatun da yafi k’arfin kwakwalwa ko kuma tarin takardunsa. Kyallin idonta daya rine da alamun kuka ya haska da wannan alwashin sannan ta juya a hankali zuwa b’angaren da Hamusu ke sunkuye don amsa gaisuwarsa…  Gaisuwar matar Madaki!

**

‘Matar Madaki…’

Sunan ya fice daga bakinta a lokacin da take tsaye tana k’arewa fuskarta kallo a gaban zank’alelan mudibin dake kafe a d’akin kwananta, wannan wani suna ne data lak’abawa kanta daga farkon kamawar satin nan kuma suna ne da ta yiwa zuciyarta tambari dashi, tambari irin wanda baya goguwa, wanda ta lak’abawa sunan ‘Mutu ka raba takalmin kaza.’

Saboda a dukkan tunani da hasashenta, bata hango wani dalilin da zai haddasa rashin tabbatuwarsa ko kuma wani mahalukin da zai iya tankwab’e mata wannan damar… Don matsayi ne da ta riga ta yiwa ruhinta alkawari har ma ta mallaka masa, to me yayi saura kuma?

Idanunta suka lumshe lokacin da ta hango hoton dogwayen gashin da suka yiwa idanunsa rumfa, suka fitar musu da wata siga kamar ta mai jin bacci, da had’addiyar sumar kansa bak’a wuluk! Sannan ma da wad’annan zara-zara yatsun nasa… Idonta ya hasko mata ranar da zai rike ta dasu, ya had’e su cikin nata a sigar alkawarin da ba zai tab’a kwancewa ba.

Zuciyarta ta kumbura a lokaci d’aya sannan kuma ta shiga narkewa cikin gulbi sanda kwakwalwarta ta tuno mata muryarsa a wancan lokacin.

‘Yawwa Amarya, kawo min duk abinda kuke dashi a gidan nan… Kin san ba abinda nake ganewa idan ina jin yunwa.’

Sai ta saki wani k’aton murmushi kwakwalwarta na hasko mata ranar da zai ci dadad’an kalolin nata girkin har ya ture.

Hannunta na dama ya d’ago da ninkakkiyar rigar dake shimfid’e a gefen kafardarta. Wannan karon muryar wanta ce ta haska a cikin kanta.

‘Kaya na karb’o daga lundary, suna bayan mota ki d’auko min su amma kar ki hado dana cikin wata blue leda, wannan na Mdee ne a ciki…’

K’amshin dake jikin rigar ya buso kan hancinta a take, sai ta k’ara lumshe idonta tana hango ranar da zata shak’i na gasken daga jikinsa.

‘Kace min Salwa tazo, kuma ban ganta ba…’

In da za’a sa mai bincike ya bincika rayuwar Madaki kaf! Ta tabbata a wannan ranar ne bakinsa ya fara ambatar sunanta, a wannan ranar dai da rashin sani ya hana ta fitowa ta ganshi, taga wannan Mdee da ya zama wani babban matallafi a rayuwarsu. Shi ya sa a yanzu bata ganin laifin wanta ko kad’an, akan fad’an daya balbaleta dashi bayan tafiyar Madakin ba tare da ta fito ba, laifin na Tariq ne, saurayin daya yaudare ta a wancan lokacin yaso shafawa rayuwarta wani bakin fenti mara goguwa.

Amma yanzu me ya rage? Rayuwarta ta baro gidan Aunty Sumayya ta dawo Lagos a wani sabon shafin da take son ta wanke kanta a wajen ‘yanuwanta, ta kuma samawa kanta kyakkyawar rayuwa…

Kuma hoton Madaki data fara cin karo dashi a wallet d’in wanta lokacin da yazo d’auko ta daga airpot shine sunan daya fara wanzuwa a wannan sabon shafin data bud’e.1

IBRAHIM AHMAD MADAKI.

**LAGOS.+

09:15 AM.

A safiyar ranar talata, Jidda ta bud’e idanunta a hankali cikin hasken ranar daya ratso ta labulayen d’akin, hasken ya sauka akan rabin fuskarta ne shi yasa sanyin A.c dake busawa a d’akin ma bai dame ta sosai ba.1

Babu d’ankwali akanta don haka garin juye-juye ribon din ya cire, gashinta da har a yau bai samu gyara ba yana barbaje a kowanne gefe na fuskarta, yawansa yafi tsawonsa shi yasa ya kusan ya binne fukartata baki d’aya, bayan haka jkinta na sanye da wannan leshin ne da Jamila ta bata tun a ranar da faifan rayuwarta ya canja, kuma bayan ita d’in babu wasu kaya a d’akin sai d’ankwalinta da kuma wannan k’aton farin mayafin data yafo, suna ninke akan bedside drawer dake jikin gadon.

Komai na d’akin kalar fari ne da kuma ruwan k’asa, haka nan komai din daya had’a da gado wardrobe da kuma d’an karamin centre carpet had’addun masu kyau ne da a ranar farko tayi ta santin kyawunsu kafin ta fahimci uk’ubar da take shirin fuskanta a cikinsu.

Idanunta a bud’e suke amma har yanzu bata tashi ba, kwalla a hankali kwalla ta shiga zirara daga idonta na sama tana sulalowa kan hancinta kafin ta had’e da ta d’aya idon. Ba wai kwalla ce ta kuka ko rauni ba, kwalla ce na irin d’acin da zuciyarta ke yi ganin cewar rana ta fad’i gari ya sake wayewa bata fitar da rashin mutuncin data tara fal a cikin kanta ba.1

Kwana d’aya, biyu, uku har hud’u kenan tana cikin wannan d’akin daya zame mata kurkuku ita kad’ai ranta… Don tun daga wannan daren da jirgi ya sauke su a airpot na garin Lagos bata kara ganin Madaki ba, tare dai suka fito har inda ya karb’i akwatunansa, kuma har suka k’araso wajen ajiyar motoci tana biye dashi k’afafuwanta har a sannan babu takalmi.

Sannan bayan jirin da take ji game da hawanta jirgi na farko, a lokacin cikinta na wani irin ciwo ne da take jin kamar zata yi amai, amma hakan bai sa ta tsaya ba tayi ta binsa don kar ya b’ace mata a cikin d’imbin mutanen dake wucewa ta kowanne direction… Ya dai juyo sau d’aya yaga tana binsa amma bayan haka bai sake ba har suka k’arasa parking space d’in inda yake a jik’e sharkaf alamun anyi ruwa mai yawa a garin… Kuma haka k’afafunta suka dinga bi ta cikin ruwan yayin da take rik’e da k’aton farin mayafinta mai santsi dake shirin zamewa.

Bata san ainihin lokaci a ranar ba, amma zata iya kintata cewa karfe sha biyu na dare tayi duk da babu alamun hakan, don mutane ne a wajen birjik ke ta harkokinsu kamar da rana.

Madaki bai tsaya ba sai a gaban wasu had’addun motoci guda biyu, dukkaninsu bak’ake wuluk sai kyalli suke alamun ruwa ya wanke su ga kuma hasken fitilar dake haskawa a jikinsu.

Har a lokacin waya ce kare a kunnensa yana magana, kuma da sauri wasu maza biyu dake jikin motar farko suka k’araso suka karbi akwati da kuma jakar hannunsa yayin da suke ta faman durkusawa suna gaishe shi cikin tsananin girmamawa, kuma anan dai ta tabbata ba don matsayin sarauta ake masa irin wannan gaisuwar ba sai don ko wani abu daban.

Direban d’aya motar da kuma wata mace inyamura suka iso gabansa suma da tasu gaisuwar, a lokacin ne ya ajiye wayar da yake yi sannan ya shiga amsa musu bakidaya.

Duk wannan abin tana tsaye daga bayansa jikinta na faman b’ari irin na jiri sannan k’afafunta camb’al akan jik’akk’iyar kwaltar wajen. Ta dai ji sanda yake yiwa macen nan magana amma bata fahimci me yace sosai ba saboda murd’awar cikinta da ya k’aru a lokacin.

Kuma daga nan bai ko juyo ya k’ara tabbatarwa cewa tana bayansa ba taga ya nufi d’aya motar data fi girma inda aka sanya masa kayansa, ya bud’e k’ofar baya kawai ya shige sannan matukin dake zaune a wajen direba ya danna wani abu daya zuge gilasan motar bakid’aya zuwa sama…. Sai idanunta suka ware da tsananin mamaki tana kallonsa ta tsakanin d’ige-digen ruwan daya fara sauka alamun yayyafi akan gilashin b’angaren da yake zaune, taga sanda ya sake kara waya a kunnensa sannan ya shiga magana idanunsa na kallon gaban motar kawai, kuma kafin tayi wani tunani ko yunk’uri motar tazo ta wuce ta gefenta yayin da tayoyinta suka fancalo ruwan da ya jik’a k’asan kayanta.

STORY CONTINUES BELOW

Sai tabi fitilun baya da kallo kyallin hasken jan danjojin na haskawa a cikin kwayar idanunta kafin muryar wannan matar ta shiga kunnenta.

“I’m here to escort you to your accommodation Madam.”

Ta juyo a hankali ta kalle ta, ta fahimci me ta fad’a abinda bata san me zata ce ba don haka ta cigaba da kallonta kawai, a cikin kanta kwakwalwarta na kokarin binciko ma’anar abinda ke faruwa ke shirin don a yanzu ta k’ara tabbatarwa akwai wani abu a zuciyar Madaki game da ita, wani abu dake shirin fahimtar da ita cewa abinda ya faru tsakaninsu ba k’addara ce kad’ai ba har da shiryawa da sa hannun wani.1

Amma wane ne wanin da zai shirya? Mene ribar yin hakan? Sai dai ko shi kansa ne yayi wannan tsarin, to amma ta yaya hakan zai yiwu? me tayi masa? A ina ya santa ma da zai jawo ta cikin rayuwarsa don kawai ya tozarta ta? Idan zancen tone layun nan ne ai a tunaninta ma taimakonsa tayi…”1

Sai ta cije lebb’enta kad’an zuciyarta na tuna mata alkawarin da tayi na cewar zata iya da duk abinda yake shirin shirya mata, zata iya d’in ta hanyar da itama zata yi tata galabar akansa. Don haka sai ta gyad’awa inyamurar dake tsaye tana jiran amsarta kai sannan suka k’arasa ta bud’e mata kofar daya motar dake tsaye, ta shiga baya yayin da matar ta koma kujerar gaba kusa da direba… Daga nan tayoyin motar suka murza zuwa hanyar barin cikin airpot d’in.

Sai dai basu wani yi nisa ba jirin dake jikinta ya k’aru sannan wani irin amai ya shiga taso mata, da kyar su duka biyin suka fahimci me take nufi sannan direban ya tsaya, ta fita bakin hanya ta dinga kwara aman dake tahowa kamar zai nad’o da hanjin cikinta don yawanci ruwa ne tunda babu wani kwakkwaran abinci a cikinta.

Matar ce ta taimaka ta rik’e ta har ta bata ruwan roba ma ta d’auraye bakinta kafin su koma cikin motar inda ta dukunkune tana jin kanta na ciwo da juyawa, saukin da ta samu d’aya ne, ciwon cikin ya tafi saboda dama rashin fitar aman ne ya kawo shi.

A sannan ta tuno sanda jirgin da suka hau ke k’okarin tashi, yana zaune a gefenta yana ganin yadda take ta mutsu-mutsu a cikin kujerarta amma baice komai ba, sai da yaga kamar tana kokarin tashi tsaye sannan ya damk’o hannunta cikin nasa kamar yana gaya mata cewar ta zauna, ya rik’e shi gam har sai da jirgin ya d’aga sararin sama ya tabbatar ta nutsu sannan ya zare yatsun nasa zuwa kan Tab d’in da yake rubuce-rubucensa, hakan yasa tayi zaton da d’an tausayawa a al’amarinsa, sai yanzu ta gane cewar yayi hakan ne kawai don kar ta kunyata shi a gaban al’umma ba don ita ba.

Tafiyar cikin motar mai tsayi ce sosai, don har sai da ta koma ta kwantar da kanta kafin su iso cikin wani gini mai dogwayen bene, kuma da yake ba’a haiyacinta take sosai ba, bata lura da komai a cikinsa ba har matar nan ta danganata da k’ofar wani d’aki da suka bi ta cikin wani dogon corridor.

Bayan sun shiga kuma bata yi mata bayanin komai ba sai ta ajiye ledar data rik’o tun daga cikin mota akan bedside drawer d’akin kawai sannan tayi mata sallama ta juya ta rufo k’ofar, kuma tabbas a lokacin Jidda taji sanda k’ofar ta fitar da wata ‘yar k’ara alamun had’ewa, abinda bata sani ba shine ashe muk’ulli tasa ta kulle ta bakid’aya daga waje.

Don tun daga wannan lokacin k’ofar bata k’ara bud’ewa ba balle har tasa ran ganin wani… Akwai bandaki a cikin d’akin, anan tayi alwala tayi sallolinta da kyar sannan taci abincin dake cikin ledar, kafin ta lalubi saman lallausan gadon d’akin ta kwanta.

Kuma shikenan kamar wasa daga wannan ranar sai  d’akin ya zama kurkukunta, a rana ta farko ta yini ita kad’ai tana yabawa kyan d’akin da kuma sa ran shigowar wani, amma babu wanda yazo d’in sai wata mata data kwankwasa windon d’akin ta mik’o mata abinci. A rana ta biyu ta fara gajiya da tsananin shirun wajen da kuma sak’e-sak’en jiran ganin Madaki, sai dai bata ganshi d’in ba sai matar nan ta jiya data sake zuwa ta mik’o mata ledar abinci. A lokacin jikinta ya gama dawowa daidai don haka ta tsayar da ita da tambayoyi, sai ta fahimci cewa yadda bata jin komai a yarenta haka itama bata jin hausa… Don haka a wannan daren ta fara kokarin bud’e kofar d’akin da jijjige k’arafan dake jikin window don ta sami hanya amma ta kasa, ba wai guduwa ta shirya yi ba don ta san bata da wajen da yake madafa a garin in ba nan ba.

STORY CONTINUES BELOW

Babu wanda zai maida ita Kiyari babu ko sisi a jikinta, kuma Allah ya sani duk karfin gwiwarta ba zata iya tafiya yawon neman kudi a wannan hargitsatsen garin ba, don haka fatanta kawai shine k’ofar ta bud’e yadda zata san tak’amaimai inda take kuma ta iya fita a duk lokacin da take so ta dawo.

A rana ta uku ne ta wanke kayan jikinta a band’akin sannan ta shanya su, dankwalinsu kawai ta d’aura a jikinta sannan ta rufa da k’aton farin mayafinta, kuma da yake lace d’in nada nauyi sai suka dad’e basu bushe ba har dare don haka bata sami damar magana da mai kawo mata abincin nan sosai ba.1

A safiyar yau kuma da ya kama kwana hud’u cikin shirun wajen, zuciyarta ta k’untata da yawa, tana jin kamar zata yi hauka saboda d’imbin maganganun data tara a cikin kanta ba fitarwa, ta yarda tsaf d’an adam zai iya haukacewa a cikin kad’aici saboda abu ne mai cin rai da yawa ka kasance cikin yanayin da ubangiji bai tsara halittarka a gurbinsa ba.

Alwashi ne ta riga ta d’auka cewa Madaki zai biya bashin wannan azabtarwar da ya sanya ta a ciki… Ai ta rantse cewar zata iya dashi don haka a yanzu ko rabuwa yayi da ita wallahi bai tsira ba… Sai ta rama komai tsaf kamar yadda alk’awarin ramuwarta akan Suraj ke kwance har yanzu a k’asan ranta.2

Tasa hannunta duka biyu ta tura gashinta baya sannan ta mik’e, a yau in ta shiga wanka tayi niyyar wanke shi tunda a cikin band’akin taga shampoo kusa da sabulun da tayi wanki dashi jiya.

… Kanki a wanke yake ma?’

Muryar Jamila ta haska a cikin kanta, sai ta girgiza kanta da sauri, ta riga ta yiwa kanta katanga da dukkan wani abu da ya shafi tunanin ‘Gida’ don hakan ne kad’ai zai iya sawa ta rayu…1

A yanzu ita wata Jidda ce daban mai tambarin ‘Matar Madaki’ don haka babu kowa a gabanta sai Madakin da kuma hanyoyin da zata tarwatsa shi!

Tayi kwafa a fili tana kallon fuskarta a hasken mudubin band’akin da take tsaye a gabansa, bata san me yasa ba amma wani gefe na zuciyarta na tunanin kamar da hannun Fulani a cikin wannan al’amarin, tunda in babu wani abu bata ga dalilin da zai sa matar dake binne asiri akan Madakin ta gaiyaci wani abu da ya shafe shi b’angarenta ba, ace ma a yadda auren yazo har tasa an shirya wani abu wai shi kamun al’ada, shi kuma bai saurari kowa ba kawai yaje ya taho da ita…

Dole ne ma akwai wani abu dake faruwa wanda bata sanshi ba, watakila irin k’addarar da ta kai ta tone asirin nan tun farko ce ta sake shigo da ita cikin k’iyayayar dake tsakanin wad’annan mutanen biyu, amma Allah ma ya san zata iya shibyasa ya kawo ta cikinsu tunda shi ba mai dorawa bayinsa abinda yafi k’arfinsu bane… Zata iya da duk wani tanadin Madakin dama ita Fulanin kanta, watakila kowannen su yana ganin cewa zai iya juya ta ne cikin umarninsa don ya cimma manufarsa, abinda basu sani ba zata zame musu k’adangaren bakin tulu ne, don duk da bata gama fahimtar tak’amaimai abinda ke faruwa ba ta sani cewar a cikinsu babu wanda ya isa ya cuce ta kuma ya tsira da hakan.1

Ta sanya hannunta duka biyu ta tattare gashinta zuwa sama, a cikin zuciyarta lissafi take ta inda zata fara da Madaki, shi da yake kusa da ita.

“Ibrahim…” Bakinta ya furta sunan a hankali tana kallon lebb’enta ta cikin mudubin…

Tausayin mahaifiyar data kawo shi duniya ya d’an gifta a zuciyarta, d’anta ya shigo hannun Jidda!6

****

139A Emina Crescent, Ikeja.

“Mdee…”

Muryar Mubarak ta sake amsawa a cikin shirun office d’in, kuma inda akwai mai lissafi a gefe, zai iya lissafa cewa Mubarak ya kira wannan sunan yafi cikin carbi tun bayan shigowarsa office d’in.

“Tambayarka fa nake ina ka kai yarinyar nan?”

Sarai Madaki ya san halin Mubarak ba kyale shi zai yi ba har sai ya bashi amsa, tunda yau kusan kwana hud’u kenan suna abu d’aya, amma duk da haka bai ko d’ago ya kalle shi ba ya cigaba da duba takardun gabansa kawai.

STORY CONTINUES BELOW

“Ibrahim ka dubi girman Allah kar ka cutar da ‘yar mutane akan wata akidarka ta daban, na gaya maka cewa ba’a komai ne kake yin daidai a rayuwarka ba, me yasa ba zaka fara bada dama ka fahimce ta ba? Zai iya yiwuwa yarinyar nan bata da lafi, kazo ka d’auki alhakin da ba lallai ta iya yafe maka ba…”

Maganar sabuwa ce da Madakin bai jita a cikin kwanakin ba saboda haka ya d’ago ya kalle shi, Wato shine ma yarinyar zata yafewa bashi zai yafe ba? fuskarsa ta nuna alamun nazari kafin kuma a hankali ta haska da wani guntun murmushin da ya kara k’awata dogwayen gashin idonsa.

“Dan Allah Mubarak ka kyale ni nayi aikina, kasan dai ba zan kashe ta ba ko? To me yasa zaka damu kanka? Idan lokacin da zan fito da ita yayi zaka ganta, na gaya maka na riga na tsara komai ne kuma ba zan canja tsarina ba..  And one more thing na fika sanin Fulani Mubarak, na fika sanin abubuwan da zata iya dama wanda da wanda zata iya sawa ayi.”

Mubarak d’in ya girgiza kansa.

“To yanzu ka gaya min, me kake tsoro game da yarinyar? Tunda ka d’auko ta ne daga ita sai kayan jikinta… Me kake tunani zata yi?”

Tsoro. Itace kalmar ta dakatar da Madaki daga abinda yake shirin rubutawa, ai babu kalmar tsoro a nasa b’angaren, ita d’in yake son ya tsorata don ta san cewa duk abinda suka shirya akansa ba mai yiwuwa bane, kuma ya tabbata duk irin k’arfin zuciyarta, a yanzu ta fara raunana da hakan.

Wannan shine tunaninsa, tunanin dake faruwa a kansa duk lokacin da Mubarak d’in ya tsare shi da tambayoyi game da ita, amma a bayan idanun Mubarak abinda ke faruwa daban ne.

Tun bayan rabuwarsa da ita, babu wani dogon tunanin da zuciyarsa ke iya ba tare da nata ya ratsa a ciki ba, kuma ba wai tausayinta yake ji ba, kawai wannan ‘yar mu’amalar data had’a su a hanya ce har yanzu bata gama ficewa daga kansa ba.2

Ya kasa daina hango kwayar wannan idanun nata da a lokacin da take kallonsa dasu yana iya karanto kokwanto da kuma tarin tambayoyi fal a cikinsu, kalar tambayoyin dake son nuna cewa ita mai gaskiya ce bata san ma’anar abinda ke faruwa ba, sai dai shi ba yaro bane k’arami da za’a raina masa hankali ta kowanne b’angare, ya riga ya sani cewa an gama tsara mata komai da komai akansa fitar da makaman yak’inta kawai ya rage.

Sannan bayan idanunta babban abinda ke k’ara haddasa masa tunaninta shine ‘Hannunsa’ tun daga wannan lokacin daya rik’e ta, hannunsa bai k’ara dawowa daidai ba, yana jinsa ne cike da rauni sannan kuma babu k’arfi kamar wanda aka sawa allurar drip ta goce a ciki, ko kuma wani abu dake jin yunwa yana neman abincinsa, a kodayaushe yana jin kamar d’umin nata hannun bai gama barin fatarsa ba sannan har yanzu yana iya jin rumfar da yatsunta suka yi a tsakanin nasa kamar dama an halicce su ne a wajen tun farko.

Ya cije lebb’ensa na k’asa cike da takaici lokacin da tunaninsa ya jiyo masa muryar Mubarak d’in na cigaba da magana yana k’ara jaddada masa cewa abinda yayi bai dace ba don bai san a wane hali take ciki ba.

Sai ya lumshe idonsa a hankali yana cigaba da rubutunsa, Mubarak bai sani bane amma kullum ta Allah sai ya kira Mary (matar da yasa ta kula da ita) a waya ta gaya masa yadda take, tsakanin jiya da yau ma su biyu ya kira tan kuma har hotunanta yana dasu birjik a wayarsa wandanda  Maryn ke d’auka ba tare da ta sani ba tana turo masa.

Yana da tsari kuma baya tab’a gaggawa a al’amuransa, shi yasa duk wani rintsi ba zai canja ra’ayinsa ba, zai tafi da komai yadda ya shirya don abubuwa su tafi daidai wajen kare kansa.

Fatansa kawai a yanzu shine ta fita daga tunaninsa ko ya samu damar yin abubuwan gabansa daidai kafin lokacin da zai sake biyowa ta kanta…

“Ka san cewa Habibu ya canja farashin DRD?”

Wata maganar daban da ba ta Jidda ba ta katse tunaninsa saboda haka ya d’ago da sauri ya kalle shi.

“What? Yaushe?”

STORY CONTINUES BELOW

“Kafin ka kira shi ya bika Kiyari. Wallahi Allah ne yaso kawai naji ina bukatar sake karanta sake karanta plan d’in nace Toyin ta kawo min kafin mu shiga final meeting din nan.”

A lokaci guda fuskar Madaki ta nuna wani irin fushi fiye da k’ima… Don dama mai neman kuka ne aka jefe shi kashin awaki.

“Amma kar ka damu na canja komai na gyara kafin yaje hannunsu, kuma na same shi da zancen bayan kun dawo sai yake ce min wai ai gani yayi tunda wannan shine karon kasuwancin mu dasu na farko gwara a sassauta yadda…”

Mubarak magana kawai yake yi amma Madaki baya jinsa, hannayensa sun riga sunyi nisa wajen neman Toyin a waya.

“Send Habibu in.”

Abinda yace da ita kenan kawai a cikin wayar sannan ya ajiye.

“Haba Mdee me zaka yi haka? Na gaya maka fa nayi solving issue din just let him be, ai da idonmu akansa… In har zai cigaba da hakan to lallai zai jawowa kansa a gaba, amma seriously ba zaka kore shi yanzu ba.”

Mubarak ya fad’i hakan ne don tabbas ya san cewa in har Habibu ya shigo office din a lokacin to yau zata zama rana ta k’arshe da zai kira kansa ma’aikacin ROYAK K.

Dalilin da yasa abubuwa k’anana irin wannan baya iya gayawa Madakin kenan don yana da wani irin fushin da bai iya d’aukan hukunci mai kyau a cikinsa ba. Ya lalubi wayar ya sake kiran Toyin da cewar kar ta aikawa Habibu sak’on kiran… A gefe guda kuma yana tunanin in har akwai abinda zai zama sanadin kore wannan fushin na Madaki.

Da ace shi yake cikin halin da gidansa ke ciki bai san me zai faru ba, don kusan gidansa yana kunne da wuta ne a yanzu, rayuwar k’anwarsa ‘Salwa’ ta dawo hannunsa akan gab’ar da matarsa Khadija ke ganin ba zata iya zama da ita ba.

Idan har Aunty Sumayya da take Babba ta kasa iyawa da ita don me kake tunanin ni zan iya Mubarak? Allah ya sani ina tsaron gurb’acewar tarbiyar ‘ya’yana, don haka sai dai ka zab’i wanda zai zauna ko ni, ko ita wallahi!

Abinda Khadijan ta fad’a kenan, kuma bai san dalilin da zai sa ta bashi zabi ba, ta sani cewa yana sonta da dukkan rayuwarsa, amma Salwa k’anwarsa ce, komai gurb’acewar halinta bai isa ya jefar da ita ba, tunda duk duniya a yanzu gidansa shine mafi dacewa da zamanta.

Yayi sallama da Madakin a lokacin da su duka biyu zuciyoyinsu ba dad’i, shi yana tunanin yadda zai shawo matsalar kan gidansa, Madaki kuma na tunanin yadda zai cire tunanin yarinyar da aka aura masa daga kansa, don da gaske hakan ya fara damunsa, baya iya tab’uka wani dogon aiki ba tare kwakwalwarsa ta katse shi ba.

K’arfe bakwai da rabi ya tashi daga aikin, kuma yana shiga cikin mota Tab dinsa dake yashe a seat din gefe wani abu ne da ya sake tuna masa da Jiddan, don a ciki Mary ke aiko masa da sakon hotunanta game da irin abubuwan da take yi… Wata ‘yar shud’iyar fitila dake haskawa a gefen Camera ta nuna masa cewa yana da wani sabon sak’on da bai duba ba, don haka sai ya d’auko ta ya bud’a, ilai kuwa sakon na Mary ne, ta sake turo masa ds wasu hotunan ne guda biyu wanda a k’asansu ta rubuta

She’s still trying to talk to me about getting out. (Har yanzu tana kokarin yi min magana akan in fitar da ita waje.)

Hannayensa suka shiga cikin hotunan, na farko tana zaune ne akan gadon d’akin kanta a sunkuye alamun tunani, na biyu kuma…  Shi ya tsaida dukkan wani abu dake motsi a jikinsa..

Tana tsaye a k’ofar toilet daga ita sai d’an k’aramin d’ankwalin kayanta wanda ya tsaya iya cinya, da alamu daga wanka ta fito don gashinta a jik’e yake sannan ta d’an sunkuyar da kanta ya zubo gabad’ayansa ta gaba alamun taza take yi da yatsunta.

Ba shiri hannunsa ya nemi zanen kwandon shara ya goge shi, amma aikin gama ya riga ya gama, kwakwawarsa ta riga ta d’auki nata samfurin, yana iya ganinsa tar! a cikin idonsa.

STORY CONTINUES BELOW

Sai kawai ya wulla Tab din zuwa seat d’in baya sannan ya tada motar, yayi kwana ya nufi hanyar fita… Daga wajen motar masu gadi ne da k’ananun ma’aikata ke ta sunkuyawa suna d’ago masa hannu alamun ya sauka lafiya amma idanunsa baya gano su, hoton ne kawai ke gizo a idanunsa ta kowanne b’angare, kuma a lokacin Cdn wak’okin dake cikin motar ya shiga playing wak’a ta gaba a jerin gwanon wak’okin jikinsa, wata wak’ar Stormzy da yayi featuring Ed Sheeran da Burna Boy….

Own it, girl you just own it!

‘Cause your body’s on fire

Show me how to control it

Girl, I love how you roll it

I put my hand there, hold it

I’ma be right by ya

I’ma be right by ya….

Ba shiri ya cusa hannunsa d’aya cikin gashinsa, sannan kamar koyaushe bakinsa ya shiga karanto addu’ar da ya saba.

Ya Allah!

Ya Rabbi!

Ka taimake ni,

Ka karb’i addu’o’ina,

Rayuwata ta hargitse,

Ya Allah ka tserar da zuciyata daga sharrin wannan k’alubalen,

Ka azurta ni da rahamarka…

Ka bani kwarin gwiwar fuskantar wannan lokacin ya Allah!2

Watakila kuma ya fad’a da bakin mala’iku har ubagiji ya amsa addu’ar, don a wannan daren bayan ya idar da sallar isha’i, zuciyarsa ta karya alk’awarin farko, tayoyin motarsa suka murza zuwa ‘Auberge World’…

Guest inn d’in daya bada ajiyar Jidda!

***

KIYARI

04:30PM.

“A lissafa min..”

Muryar Fulani Hafsatu ta fito tar cikin shirun da falon ya d’auka. A gabanta tarin kaya ne buhu-buhu da kuma kwali-kwali na abincin yau da gobe, bayan haka ga wasu manyan fanteku nan da aka shak’e su da kayan zaki irin dangin alkaki da kuma nakiya, akwai jarkoki ma na kowanne irin dangi na mai sannan akwai akwati guda shak’e da ‘yan k’ananan kayan masarufi irinsu maclean da da kuma sabulai na wanka masu tsada.

Jakadiya Babba ta k’ara durk’usawa cikin tsugunnonta sannan ta shiga fadin.

“Buhun shinkafa biyar ne ranki ya dad’e, na shinkafar tuwo uku, buhun sukari biyar, na gero uku, na masara uku, akwai garwar mai biyar, ta manja biyar, kwalayen taliya, macaroni cous-cous, da irin danginsu kowanne guda goma, a kayan zaki kowanne fanteka biyu ne, katan din madara biyar, sauran kayan shayin suma kowanne katan biyar-biyar ne, kwalin maggi biyar sannan da buhun gishiri biyu, sai akwati biyu da aka zuba shaddodi da yadika irin wandanda yake sanyawa ranki ya dad’e.”

Wani irin busashshen murmushi ne ya b’alle a fuskar Fulanin yayin da take k’arewa kayan kallo, busashshen murmushin dake nuna dauriyarta wajen danne d’acin da har yanzu bai gama washewa daga k’irjinta ba tun daga ranar da labari ya iso mata cewa Madaki ya d’auke matarsa ya bar garin, a wannan lokacin wani d’an tak’i ne kad’ai ya hana zuciyarta bugawa, don fad’uwa tayi har k’asa cikin ciwon k’irjin da ya turnik’e ta, sai da aka kira likitoci biyu suka rufa akanta sannan ta iya dawowa daidai.

Ba wai sai a lokacin ta sani cewa Madaki hatsabibin kansa bane, a ranar ne ta tabbatar da cewa halaiyarsa bata yi sanyi ba kamar yadda take zato, abinda yayi ya nuna mata cewar ya san da shirinta kenan, kuma kila shima yayi nasa shirin wanda idan har bata yi da gaske ba da alamu tarihi zai maimata kansa ne, don kamar yadda mai martaba ya yanke hukuncin aurensa cikin fushi m, tsaf! Ta san zai iya sake yanke wani hukuncin da zai salwanta nata auren in har ta bari Madaki yayi nasarar fahimtar dashi cewa da hannunya a cikin lamarin.

Saboda haka ba shiri washegari ta lalubi aminiyarta Hajiya Bilki a waya, wadda ta tabbatar mata cewar in har tana son al’amarinta ya tafi daidai ba tare da an samu matsala ba, dole ne a bi yarinyar nan a bata wannan tsadadden aikin data aiko mata tunda bata sami damar bata ba har ya d’auke ta.

‘Kince yarinya ce k’arama Hafsatu, don haka baki da matsala ki juya ta kawai da k’arfin dukiyar dake hannunki, irinsu basu da wuyar sha’ani musaman ita kakar tata da kika ce baiwa ce, da kin lasa musu wani d’igo na dukiya yanzu zaki ga sun rud’e ko sujjada sai suyi miki, balle ma k’aramin aiki irin wannan.3

Da an kafa kuma shikenan an wuce wajen, ina tabbatar miki ko kawar dasu d’in kika ce Madakin yayi da kansa wallahi ba zai musa ba. Sai dai kuma dole ki motsa da wuri, tunda baki san ra’ayin sa akan yarinyar ba, na gaya miki sai da hannun matar da bata taba haihuwa ba sannan asirin zai ci, don haka ko ciki yarinyar nan ta d’auka wallahi munyi asarar wannan damar, dole ne ki nemo dalilin da sakon nan zai isa gareta da wuri sannan ta hanyar da ko shi kansa uban gaiyar bai isa ya zarge ki ba… Idan kika yi komai daidai Fulani, na gaya miki zaki gode min daga baya.’

Wad’annan sune kalaman da Hajiya Bilki ta shaida mata ta waya, kuma shawarar a tafi da aikin ta cikin ‘Gara’, tunanin Jakadiya Babba ne. Sun riga sun tsara komai har an kira ‘yanuwan yarinyar an shaida musu cewa a matsayin alherin Fulani ta d’auke musu komai na harkar Gara, za’a d’ebe su kawsi har garin ikkon suje su kai, kuma yadda Hajiya Bilki ta fad’a ne, babu wanda a cikinsu ya hango rashin dacewar hakan sai faman washe baki kawai suke da godiya lodi-lodi, matsalar da take tunani kawai guda d’aya ce, bata yarda kakar yarinyar nan ba sam! Don duk da sun toshe mata baki da wadannan akwatunan, da kuma godiyar da itama ta durk’usa tayi, har yanzu tana hango wani abu kamar rashin yarda a fuskarta.

Amma meye ne? Wuyarta asirin nan yaci, kamar yadda Hajiya Bilkin tace ne, ko shi da kansa Madakin zata iya sawa ya kawar daga ita har jikar tata, ta riga ta gama yarda da yarinyar nan cewa zata iya, bari dai a lallab’a ta kawai su sami abinda suke so, komai mai sauk’i ne bayan nan!

Wani guntun murmushi ya sake b’allewa a gefen fuskarta ganin hak’anta na cimma ruwa, don ta tabbata Jakadiya Babba ba zata yi zuwan banza ba, in har ta sami yarinyar nan kamar anyi an gama ne.

Ko me kake shiryawa Madaki, kayi kad’an ka gujewa sharri na, tamkar alhaki nake a rayuwarka, dole ne in bibiye ka koina…

Na riga na tura maka abinda ba zaka iya juyawa ba, kuma wannan karon anzo k’arshe, da sannu gwiwoyinka zasu durk’ushe a gabana!

***Barka da dare ranka ya dad’e.”+

Muryar Madaki ta fada cikin tsananin girmamawa lokacin da yake tsugunne akan gwiwoyinsa.

Bayan sanda ya koma gida daga office, bayan yayi wanka yaci abinci har ma yayi sallar isha’i ne ya sami kiran Mai Martaba a wayar dake amsa duk wani personal kiran da bai shafi aiki ba.

Ba wai abu ne sabo ganin kiran nasa ba, don lokaci zuwa lokaci su kan yi waya akan yadda al’amuran aikinsa ke wakana har ma su tattauna wani abun daban, sabon abun shine bai tab’a samun kiran nasa a cikin lokaci kankani haka bayan rabuwarsa da gida ba, saboda haka duk wani tunaninsa ya rataye a iska tunda a yanzu shi mai laifi ne a wajensa, kwakwalwarsa ta kasa lissafa dalilin kiran balle har ya tanadi amsar da zai iya bayarwa, saboda haka ya durk’ushe gwiwoyinsa cikin lallausan carpet d’in dake falonsa yana jiran tsammani.

“Barkan mu dai, yaya kuka isa Ikkon?”

Sabon abu na biyu shine kalmar ‘Ku’ data maye gurbi akan jimla guda da yake danganta shi da ita a baya, hakan ya fara ne tun a ranar Juma’ar nan da ya sami ganinsa kafin tahowarsa, ya same shi ne a cikin turakar da a kullum yake zama don cin abincin rana, wajen da ba’a bari kowa ya shiga amma a wannan ranar bai san me bafaden dake tsaye a wajen ya gani cikin idanunsa ba har ya kasa yi masa shamaki da shiga.

“Allah ya kaiku lafiya.”

Abinda yace dashi kenan kawai a wancan lokacin, bai bashi damar da yin wani bayani ba balle har ya fahimci shi kuma ya sami irin addu’ar da yake binsa da ita a kullum, kuma hakan shine babban abinda ya k’ara tunzara zuciyarsa ya harzuk’a shi a ranar.

“Lafiya ranka ya dade, lafiya k’alau.” Tunaninsa ya janye lokacin da ya amsa gaisuwar.

Shiru ne ya biyo bayan amsawar tasa, kuma ba wai irin shirun da ya sani tare dashi ba, wannan shirun dake nuna matsayi da kuma girma na sarauta, wannan karon shiru ne mai yawa don har sai da ya janye wayar daga kunnensa yaga mintinun kiran na cigaba da tafiya, sannan ya mayar da ita kan kunnen nasa yayin da gwiyoyinsa suka kara lankwashewa a k’asa.

Taraddadin laifin da mahaifin nasa ke ganinsa dashi na kara kama shi, don tabbas ya sani cewa bai kira don yayi shiru ko kuma don komai ya wuce ba.

“Na sami labarin abinda kayi Ibrahim…”

Amon dake cikin muryar ya kad’a zuciyarsa, abinda yayi? Me yayi? Shiga cikin masarauta da mota? Ko kuma d’auko matar daya aura masa ba tare da neman izinin kowa ba?

“Idan kana ganin na sake baka dama ne ka cigaba da cutar yarinyar da kuma ire-irenta, ya kamata tun yanzu ka gayawa zuciyarka cewa ba zan d’auka ba Ibrahim…”

Yatsun hannunsa na dama da har yanzu basu da kwari suka shiga rawa a take don har yana jin yadda wayar ke gogawa akan fatar kunnensa, amma d’ayan yana dunk’ule a cikin carpet da dukkan dauriyarsa ta duniya.

“… Na kira ka ne bada matsayin shugaban da duniya ke kallo na dashi ba, na kira ka ne a matsayina na mahaifinka, na kira in gaya maka cewa ka dawo min da Ibrahim din da na sani tun da wuri, Ibrahim d’in da baya tab’a tsallake umarni na sannan wannan Ibrahim din da k’addara ta dank’a min a cikin hannuna… Idan ba haka ba Madaki… Ina tabbatar maka cewa zaka san wani b’angare na Ahmadun da baka tab’a sani ba!”

Madaki. Madaki. Sunan daya kasa mantawa kenan tun daga lokacin daya sauke wayar a kunnensa har zuwa yanzu da tayoyin motar da yake tuk’awa ke murzawa akan titin da zai kaishi Guest inn d’in ‘Auberge World.’

Sunan nasa ne ya sani, wanda ya samo asali tun a lokacin da bai fi shekaru shida a duniya ba, lokacin da wani tsoho mai rik’e da muk’amin Madaki a zamanin sarki mai rasuwa ke mutuk’ar son sa, har yau yana iya tuna dariyar tsohon da yadda yake haba-haba dashi, don duk da k’arancin shekarunsa a wancan lokacin zuciyarsa ta sanya shi cikin jerin ‘yan k’alilan d’in mutanen dake k’aunarsa a duniya, don bayan wajen Hajja bashi da wajen zuwa duk fadin masarautar nan sai wajensa.

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin da yake gab da shiga makarantar sakandire ne Allah yayi masa rasuwa, mutuwar ta shige shi mutuk’a ta yadda har ya fadi jarabawa a wannan shekarar sai da ya k’ara maimaita shekara guda a gida, hakan yasa a lokacin da zai sake registration sai kawai ya k’ara sunan ‘Madaki’ a gaban guda biyun da yake amfani dasu ‘Ibrahim Ahmad’ saboda duk cikin jikokin masarautar nan shi kad’ai ne babu jigon ‘Kamsusi’ a inkiyarsa.

Baya tab’a mantawa tun a wancan lokacin ran mahaifinsa bai so hakan ba, amma ganin yana so yasa ya kyale shi kawai, kuma tun daga wannan lokacin zai iya rantsewa da Allah Mai martaban bai tab’a kiransa da ‘Madakin’ ba sai a yau!

“Idan kana ganin na sake baka dama ne ka cigaba da cutar yarinyar da kuma ire-irenta…”

Bayan sunan, wannan maganar ita tafi tsayawa a ransa, ta sashi gasgata zancen wani mai magana dake cewar..

‘Ya kai d’an adamu, ya kai mai yawo a doron k’asa… Ka guji ranar da k’azafi zai hau kanka, don kuwa gwara mutuwarka da wannan lokacin!’1

A yanzu yana jin kamar ya yaga k’irjinsa ne ya fito da zuciyarsa, yaje ya d’auraye ta a famfo sannan ya koma Kiyari ya durk’usa gaban Mai martaba ya nuna masa ita, ya nuna masa cewa bai canja ba, shine dai Ibrahim d’in daya sani tun a baya, shine Ibrahim d’in da k’addara ta mallaka masa shi, shine Ibrahim d’in da ba zai tab’a sab’awa umarninsa ba, shine Ibrahim din da in duniya zata taru a gefe guda, mahaifinsa ya tsaya a d’aya gefen, zai goya masa baya koda da numfashi d’aya daya rage a rayuwarsa ne… Amma ya riga yayi sake, Fulani tayi nasarar goge wannan yardar a zuciyar mahaifinsa, kuma Allah ya sani bai san zuwa yaushe rayuwarsa zata sake dawowa daidai ba.

“Idan kana ganin na sake baka dama ne ka cigaba da cutar yarinyar da kuma ire-irenta…”

Maganar ta sake haskawa a cikin kansa, tunda yake a rayuwarsa bai tab’a rik’e koda farcen wata mace da ba muharramarsa ba, zai iya maye haka da kalmar ‘Duka mata ma’ tunda shi ba ‘yaruwa ce dashi ba balle ya sata a layi, amma a yauai martaba har tunani yake bayan yarinyar akwai wasu ire-irenta ma a gefe, a lokaci guda yaji wani abu kamar kwalla na k’okarin taruwa a idonsa amma a lokaci d’aya ya maida ita idanun nasa suka washe, zai iya yiwa alak’arsa da mahaifinsa kuka, amma hakan ba mai yiwuwa bane in har da sunan Fulani a matsayin sanadi, ya riga ya rantse cewar ita zai sa wannan kukan nan bada dad’ewa ba, duk cewa gashi a yanzu yana shirin karyawa kansa alk’awarin farko.

Zai je ya taho da ita zuwa gida, kalaman mahaifinsa sun ceceta daga siradi na farko daya shirya akanta, don zuciyarsa ba zata sake kwanciya ba in har tana wajen nan, zai ga kamar ya d’orar da kalaman mahaifinsa ne cewar yana cutar da ita.

Tayoyin motar suka yi kwana zuwa cikin gate d’in wani katafaren guri mai mutuk’ar kyau, a samansa an rubuta ‘Auberge World’…. Duniyar da Maijidda ke ciki.

A cikin parking lot d’in, ya saka motar tsakanin wasu motoci biyu daidai lokacin da Mary ta hango shi, don haka ta taho da sauri daga kan barandar wani gini a cikin harabar wajen da take tsaye.

Madaki bai fito ba har sai da ta k’araso daidai jikin motar tasa ta tsaya daga jikin k’ofar dake bayan mazaunin direban, sannan ya kashe motar ya d’auki wayar dake gefensa ya fito, zuciyarsa a cunkushe taf da al’amura kala-kala.

“Barka da zuwa yallab’ai.”

Mary ta fad’a cikin harshen turanci, kanta a sunkuye sannan hannunta na mik’o masa muk’ullin d’akin daya kira ta a waya yace ta kawo masa, yasa hannu ya karb’a a lokacin da sanyin jikinsa ya ratsa fatarsa, ya zama kamar wani abu dake gaya masa cewa abinda yake shirin yi ba daidai bane, baya cikin tsarinsa don haka bai kamata ya fara karya alk’awarin farko tun yanzu ba, hakan zai iya zama sanadin kwancewar abubuwa da yawa… amma ya zai yi ne? Ba zai tab’a yin wata rayuwa mai kyau ba idan har maganganun Mai Martaba ma haskawa a cikin kansa, suna gaya masa cewa da gaske ne ya sami damar cutar da ita.

STORY CONTINUES BELOW

“Yawwa Nagode, and na tura miki da kudinku, kin gani?”

Muryarsa ta fito tar! Cikin irin dauriyar da kullum yake kwana yana tashi da ita.

Sai ta k’ara sunkuyar da kai tana sosa jelar k’arin gashinta kafin tace.

“Eh na gani yallabai, Nagode sosai nagode. sai dai na tura maka wani abu daga baya kuma naga kamar baka duba ba shi yasa nace bari na tuna maka don ina tunanin in kaje wajenta yanzu akwai matsala.”

Girarsa biyu ta had’e waje d’aya alamun rashin fahimta.

“Wace irin matsala? A ina kuma?”

“Ita yarinyar da kasa muke kula da ita yallab’ai, na tura maka videon abinda tayi d’azu ne amma da alama baka duba ba.”

Sai ya fara fahimtar zancen, tabbas tun a hanyar dawowa office da ya cilla Tab d’in bayan seat bai sake bi ta kanta ba, amma me ya faru kenan? Me tayi? Sai kawai ya bud’e k’ofar bayan motar ya d’auko ta a cikin tarin takardun dake zube a ciki, notification d’in blue fitilar nan kuwa nata haskawa alamun sak’o ya shigo.

Mary na tsaye tana ta sunkuyar da kai ya bud’e cikinta ya shiga b’angaren sakon, alamun video ne ya nuna akan hoton da yake gani don haka ya danna shi.

Daga nesa aka yi d’aukan, amma duk da haka yana iya ganin fuskar Jidda tar data lek’o ta jikin tagar d’akin da take ciki, da hannayenta da suka shak’o wuyan wata mace mai sanye da kayan aikin hotel din kafin abinda muryarta ke fad’a ta biyo baya.

“…da kina jin hausa da ba kya ji duk bai dame ni ba, abu d’aya nake so ki sani shine Sunana Maijidda kuma  babu wanda yake cuta ta a duniyar nan ya tsira da hakan, wallahi, tallahi duk inda na tafi bayan na fita daga nan, sai na san yadda zanyi na dawo na kuntata rayuwarki kamar yadda kika yi min.”

Ba daga farko aka fara d’aukar videon ba, da alama tayi wasu maganganun kafin a fara, kuma wannan ba shine abinda ya tsaida tunaninsa ba, yadda idanunta suke tas! kamar ranar da ya fara ganinta, da yadda muryarta ke fitowa tar ba tare da wani karyewa ba, a yadda yake ganin hotunanta yana da tabbacin dama ba zai zai zo ya same ta mak’ure a kwana tayi zuru-zuru ba, tunda ba a kai wannan lokacin daya tsara hakan ba amma duk da haka babu a inda tunaninsa ya taba nuna masa cewa tana da k’arfin gwiwar da har zata iya cakumar babbar mace irin wannan.

Lebbensa na k’asa ya cije kad’an, idan har zata yiwa ma’aikaciyar dake kula da ita irin wannan kashedin, me Fulani ta tsara mata akansa kenan? Anya ba zaiyi kukuren fito da ita a yanzu ba kuwa? Anya ba yana shirin kai kansa cikin gadar zarensu bane? Sai kuma ya girgiza kansa, kome zai faru a yanzu dai ba zai sake iya barinta ta kwana a wannan wajen ba. Ba zai sake ba.

“Yallab’ai dama na gaya maka tana ta nuna mana alama ta maganganunta akan son fita, to d’azu ne da Elizabeth taje kai mata abinci kawai sai ta zuro hannu ta shaketa kuma take ta irin wad’annan maganganun, bamu san dai me take cewa ba, amma da dukkan alamu kashedi ne cewa ta shirya wani abin, shi yasa na tura maka ko zaka bari zuwa gobe, sai ayi tanadi mai kyau kafin a bud’e k’ofar.”

Cewar Mary, cikin hashen turanci a lokacin da videon ya kai karshe sannan ya shiga sake maimaita kansa.

Madaki ya jawo idonsa daga kan tab din zuwa fuskarta, a cikin idanunta yana iya hango wani abu kamar kokwanton da kuma son

sanin cewa ko dai mahaukaciya ya basu ajiya ne? Tambaya ce da baya fatan tayi masa duk da ya san ba zata iya ba d’in.

Shi kansa a yanzu bai san amsar da zai iya bayarwa ba inda wani zai tambaye shin, don duk da cewa a tarihin da wannan baiwar ta bashi game da ita babu inda ta furta ta tab’a samin wata matsala ta kwakwalwa, ba zai iya cewa komai ba sai da izinin likitan kwakwalwa tukunna. Saboda haka girgiza ya juya ya sake wulla tab din cikin mota ya rufe.

STORY CONTINUES BELOW

“Muje ki raka ni.”

Umarnin ya fito bayan ya dana lock a jikin muk’ullin hannunsa motar ta kulle kanta, sai ta juya ta shige gaba zuwa hanyar cikin ginin wajen, hanyar da zata kai su ga d’akin da matar da yake wa kallon wani b’ari na ‘K’addarar Rayuwarsa’ take.

Bayan sun wuce receiptionist, hanyar corridon doguwa ce inda suka yi ta wuce wasu d’akunan kafin Mary ta tsaya a daidai k’ofar da aka rubuta nambobin 1980 sannan ta juyo ta kalle shi alamun nan ne, sai ya d’aga mata kai shima alamun ya fahimta kafin ta sunkuya ta sake yi masa godiya, kuma kamar walkiya k’afafunta suka karya wata kwana data b’atar da ita daga wajen.

Idonsa ya tsaya akan lambar…

1980.

A lokaci guda tunaninsa ya lissafa cewa ta yaya hakan zai yiwu, Guest Inn d’in na da girma amma ba zai yiwu ace sun sami d’akuna har dubu d’aya da dari tara ba… Saboda haka ya juya a hankali ya kalli k’ofar wani d’aki dake bayansa, anan yaga shi tasa nambar 3180 ne ma saboda haka ya sake juyowa ya kalli nambobin a lokacin da mamakin adadin ya maye gurbi da tunanin wane irin coincedence ne wannan?

1980 nambobi ne masu muhimmanci a rayuwarsa, shekarar da aka haife shi, k’arshen nambar wayarsa, nambar daya rayu da ita a makaranta, password din duk wani credit card d’insa dama duk wani abu daya danganci password a rayuwarsa… Lebb’ensa ya sake cijewa a karo na biyu, me yasa k’addara zata had’a abubuwan alkhairin rayuwarsa da wannan b’angaren? Amma kamar yadda ya fad’a d’in ne coincedense ne kuma mai wucewa, daya fitar da ita daga d’akin shilenan hakan ya tafi.

Hannunsa ya zura muk’ullin ciki ya murd’a sannan ya tura k’ofar, kuma a lokaci guda wani abu ya zarce mak’ogwaronsa sanda da ta wangale akan idonsa…  Abinda ya fara gani itace, saboda gadon dake cikin d’akin na fuskantar k’ofar ne a tsaye ita kuma tana zaune a tsakiya daga can k’arshensa a k’asan rumfar adon da aka yiwa gadon. Tana sanye da kayan nan da ya barta a ciki, kayan daya taho da ita dasu sannan kayan data zab’i sakawa a ranar da suka canja rayuwarsa.

Da d’ankwali akanta amma kusan gabad’aya gashinta daya gani d’azu a waje yake saboda ya fito ta kowanne gefe a barbarje mai d’imbin yawa, sannan kafafunta na tankwashe ta bud’e kwalin takeaway har biyu a gabanta tana cin abincin da ta cika bakinta dashi, ga wani kuma tana shirin k’arawa a cokalin hannunta, yadda ya tsaya yana kallonta haka itama ta d’ago rik’e da cokalin da bai k’arasa baki ba tana kallonsa.

Kuma kamar yadda Madaki ya zata ne, bayan wani abu da bai gane ba a cikin idonta, kallonsa kawai take babu alamun mamaki a cikin idanun nata, kallonsa take tamkar dama ta san da zuwansa, kamar irin kallon da mutum ke yiwa wanda ya aika ya dawo, sai ya karasa ciki a hankali ba tare da ya rufe k’ofar ba.

Ya kula da sanda ta had’iye abincin dake bakinta kafin ta gyara zama ta amsa sallamar da ta fito daga can k’asan mak’oshinsa.

“Wa’alaikum salam.”

Muryarta na nan yadda take, d’auke da wannan abin da bai san meye ba, sannan a yanayinta babu wanda zai had’ata da ta cikin videon nan lokacin da take d’aga murya tana zarewa matar nan ido, a yanzu wani ma ba zai yarda cewa ta san ma’anar ‘Rashin kunya’ ba.

Jidda ta sauke abincin data rik’o zuwa cikin plate d’in, Idonta ya janye daga cikin nasa amma zuciyarta bata kasa gaya mata cewa ya rame ba, kwanaki hudu kawai amma sai taga ya canja kamar watanni hud’u, ta san ko kad’an bata yi tunanin ganinsa a yau ko kuma lokaci kusa ba, tayi zaton ai sai watanni sun rufa an doshi lissafin shekara sannan zai tuna da shanyar daya ajiye, amma duk da haka mamakin ganin ramar tasa yafi tasiri akan na ganinsa.

“Nazo ne mu tafi.”

Muryarsa mai zurfi ta fad’a sanda yayi wa kansa birki a k’arshen gadon, jidda ta sake maimaita kalamansa, yazo su tafi? Haka kai kai tsaye? babu tambayar komai? Ya barta a waje d’aya da kaya guda tsawon kwanaki hudu kuma abinda zai fara gaya mata kenan?

Bai san cewa ta tara rashin mutunci fal a akansa bane?1

STORY CONTINUES BELOW

Sai ta d’ago daga kallon abincin ta kalle shi, shima ita yake kallo da wad’annan idanun nasa masu tsananin kwarjinin da zai iya narka duk wani k’arfin gwiwar mutum… Amma a yanzu banda nata don da zata iya bashi shawara cewa zata yi ya taimakawa kansa tun a yanzu ya sake ta kawai, don bata san me yasa ba ‘yar ramar da taga yayi tasa ta jin wani abu da bata tsara dashi ba. Amma duk da haka ba zata hana abinda ta tara ya wuce mata a wuya ba, don haka ta bud’e baki tayi tambayar da ta zama masomin k’addarar ta biyu a rayuwarsu.

“Mu tafi ina?”

Madaki na nad’e da hannayensa a k’irji sannan idanunsa tsaye akanta, bai tsara lokacin da shi da ita zasu tattauna wani abun a yanzu ba don hargitsin dake faruwa akan sa kad’ai ya ishe shi.

“Nace ki tashi mu tafi.”

“Babu inda za ni.” Ta bashi amsa kafin ya kai ga rufe nasa bakin, sannan kai tsaye ta cigaba da cewa.

“Idan kana tunanin zaka iya juya ni ne ranka ya dade, gwara ka watsar da hakan tun yanzu, don wallahi babu wanda ya isa ya cuce ni kuma inyi shiru komai matsayin mutum kuwa, kuma ko kashe ni zaka yi a wajen nan sai inda k’arfina ya k’are.”

Taso ta kara da cewar ‘Na fahimci baka san daraja da kimar d’an adam ba, in ba haka ba ko wucewa ka taba yi ta gaban makarantar islamiyya ai zaka iya kwatanta cewa wannan abinda kayi zalunci ne.’

Amma ba yanzu zata fara kwance irin wannan k’ullin ba tukunna, suje zuwa dai tunda yace yaji ya gani.2

Har yanzu kallonsa take, hasken fitilar d’akin na haska mata kamanninsa da suka k’ara fik’ewa cikin ramar da yayi. Jira take ya sake cewa wani abun don ta mayar masa, bata gama ba, akwai wasu tarin kalaman a cikin kanta.

Da gaske ne ta iya fad’an sosai.

Madaki ya ayyana a ransa yana nazarinta, ko kad’an ba fahimtar abinda take cewa yake ba, fuskarta kawai yake kallo, yadda idanunta ke tsaye kyam tana kallonsa, da yadda lebb’enta ke motsawa wajen fitar da kowacce kalma. Bai tab’a k’are mata kallo irin yau ba, hakan yasa ya fahimci cewa ashe a da hasashen kamaninta kawai yake bai san ainihin zanen fuskarta ba.

Ya cigaba da kallonta a lokacin da tayi shiru tana kifta idanunta, jira take ya sake cewa wani abun ya sani, amma shi bai tsara yi mata wani bayani ba balle har ya fahimtar da ita, idonsa ya koma kan agogon dake kafe a d’akin, karfe tara har da ‘yan mintuna, dare ya fara kuma yana buk’atar ya kwanta da wuri don ya hutar da kwakwakwarsa kafin tashin safiyar gobe.

Saboda haka ya saki hannayensa sannan ya k’araso daidai gaban gadon ya ya tsaya, muryarsa ta fito cikin iko da isa.

“For the last time, I need you out of this room.”

Wani abu da tayi da idonta alamun gajiyawa ya sanya yaji kamar zuciyarsa ta k’ara nauyi a k’irjinsa.

“Nima na gaya maka cewa ba zan tafi ba, ko zaka min dole ne?”

A lokaci guda kafin ma ta kai ga rufe bakinta, Madaki ya cafki duka hannayenta biyu sannan ya jawo ta daga kan gadon, abincin dake kan cinyarta ya zube baki d’aya akan lallausan bargon dake sama, k’afafunta suka taka k’asa a lokacin da yasa d’aya hannunsa ya rik’o kanta ta baya, yatsunsa suka zarme cikin sumar kanta, yaga rudani a idanunta mai kama da fargaba amma bai damu ba, k’arfin hannunsa dake dawowa a wannan lokacin shine a gabansa.

“Zan iya karya ki anan ba tare da kowa ya sani ba, don haka kiyi abinda nace kawai.”

Madaki ya sani daman, bakinta ba zai mutu ba.

“Nima ina da hanyar da zan iya tara maka jama’a an….”

Bai bari ta k’arasa ba ya k’arasa janta cikin jikinsa bakidaya ta sigar sake matse hannayenta da iya k’arfin da yake ji na shiga jikinsa, abinda ya katse zancenta kenan kafin muryarsa ta lalubi daidai saitin kunnenta, numfashinsa na busawa akan fatarta ya rad’a mata.

STORY CONTINUES BELOW

“Ina da hanyar da zan iya miki dole Maijidda, ina da ita da yawa…”

**

A wannan daren.

“Akwai hanyoyi da yawa Salwa, zamu iya yi masa dole in har abubuwa basu tafi daidai ba.”

Salwa ta mik’a hannu ta d’auki kofin tambulan din dake gabanta, bakinta ya sauka akan straw d’in dake cikinsa sannan cikin zuk’a d’aya ta yi masa babban gib’i. Idanunta na kallon k’awarta dake tsallaken teburin tsakiyarsu ta girgiza kanta.

“Ai ba zamu kai wannan gab’ar ba Naja, na gaya miki mutumin nan fa babu abinda ya sani a rayuwarsa sai aiki, Yaya yasha gaya min cewar da kyar yake iya jawo shi gida ma su d’an ci abinci tare wani lokacin don kawai ya samu yayi wani abun daban da ba aiki ba, gashi bashi da wasu ‘yanuwa na kusa balle mahaifiya, ko can garinsu sai yayi shekara-da shekaru bai je ba, bayan hakan ni kaina shaida ce bashi da wani kula-kulen ‘yanmata don shekaru biyu da suka wuce, Yaya ya tab’a raka shi Abuja wai wajen wata k’anwar abokin aikinsu… Har yazo gidan Aunty Summayya yana mitar cewa da kyar ya samu ya yarda ya biyo shi suka taho, to ba’aje koina ba ma nake jin maganar ta rushe, tunda ba’ayi ba.

Don haka ki gaya min irin wannan mutumin ta ina kike tunanin za’a sami wata matsala dashi? Kawai hanyar da zan kai kaina gare shi zan nema don wuyarta mu had’u, ina tabbatar miki sai ya fada cikin tarkona.”

Naja’atu ta tab’e baki kad’an itama tana zuk’ar nata lemon, dukkaninsu suna zaune ne a harabar wani k’ayataccen gidan cin abinci mai d’auke da korayen shuke-shuke da kuma iska mai dadi.

“Ai wuyar kenan, meye har sai kin wani wahalar da kanki wajen bin dabaru? Kiyi magana a d’ora miki zuciyarsa kawai a tafin hannu ta yadda duk inda kike shi zai nemo ki zaki tsaya biyewa gaibu, tun yaushe aka wuce wannan wahalar ne wai Salwa?”

Salwa ta sake girgiza kanta.

“Na gaya miki so nake na wanke kaina a wajen ‘yan uwana, kuma ina ganin Yaya ya riga ya san Madaki fiye da kowa a duniyar nan, don haka in har nayi amfani da wata hanya da ba zata zama mai gamsarwa ba, ina gaya miki kamar in dora gini ne kuma inzo in rushe shi don wallahi tsaf Yaya zai k’alubalanci hakan.”

Ta sake kurbar lemon karo na biyu sannan kuma tayi murmushi a hankali.

“Ki barni kawai Naja, bani da kowacce irin matsala fa, don ni na san duk bak’in hali na, Yaya ba zai so nak’i had’a zuri’a da Madaki ba, shi kansa nawa yake yaga a wajensa balle ni?”

“Haka kika ce? Amma sanin kanki ne Salwa, mazan yanzu taurin kai gare su, wad’anda basu ko kai yadda kike fad’ar Madakin nan ba da yaya muka same su tun a baya? balle yanzu da zamani ya k’ara wayewa.”

“Wancan akan harkar banza kike magana, wannan kuwa aure na gaya miki zanyi, don haka dole matakan su banbanta.”

Sai Naja’atu taja tsaki.

“To wai ub*n me yasa kika taso ni gari ya gari tun daga Abuja zuwa Lagos? Don ki gaya min cewa kin tuba zaki yi aure ne ko me?”

Salwa ta sake wani faffad’an murmushi tana kallonta.

“Maida wuk’ar mana Zanzan d’in Sadiq, kema kin san ba haka bane ai… Akan zancen wannan matar ne, so nake ki taya ni muyi maganinta tunda nayi nisa da ‘Na Mama’ (bokonsu) yanzu, don ita kadai nake wa kallon cikas d’ina yanzu, ita kadai ce zata iya b’ata min al’amura.”

“Wa kenan?”

“Khadija, Matar Yaya.”

“Me kike so a mata?” Naja’atu ta sake tambaya fushin fuskarta na bajewa jin anzo gab’ar da take so.

“Inda hali kawai Na Mama ya kawar da ita daga duniyar nan, don raba min hankalin Yaya zata yi akan wannan al’amarin, wai har don nazo gidan zata debi kayanta ta fita da sunan yaji? Tana gaya masa cewa ni annoba ce zan iya b’ata mata tarbiyar ‘ya’ya? Shi yasa nake so kawai ayi maganinta Naja, don gani nake zata iya b’ata mun lokaci.”

Karo na farko da Naja tayi murmushi tun bayan fara maganarsu, tace.

“Lallai na yarda Tariq yaso ya b’ata min tunaninki Salwa, amma har wannan aikin wani babban abu ne da na zaki iya min bayani a waya na sai kinsa na tako kafata har nan? Don wata khadija? Ko yanzu na juya na gayawa Na Malam ai kin san ta tafi kenan har abada…”

Tunanin Salwa ya b’ata a cikin kalamanta tunda ta ambaci sunan Tariq, saurayin da taso kamar ranta har ta bashi dukkan wata amana da yarda a duniyar nan, amma ya yaudareta, yaso shafa mata bakin fenti mara goguwa a wajen ‘yan uwanta, ya d’auki sirrin boyayyiyar rayuwar da take yi ta fallasa ta a wajen yayarta marikiyarta, duk da irin asirin da tasa aka nannad’e mata zuciyarsa dashi…

‘Na fara nadama, wannan abinda muke bai dace ba Salwa, ina ganin rayuwarmu ba daidai take tafiya ba.’

Abinda ya fad’a mata kenan watarana da take kwsnce kusa dashi, kuma hakan shine masomin komai.

‘Ba zan iya sake nad’e miki zuciyarsa ba Salwa, tun farko na gaya miki cewa sai kin hana shi yawan addu’o’in nan nasa, ina ganin mun makara…’

‘Na so ka da dukkan soyayyar duniya Tariq, amma ka yaudare ni, ka fallasa ni a wajen ‘yanuwana, nasha gaya maka cewa zuciyata zata iya d’aukan komai amma banda tozarci daga gurin ‘yanuwana biyu a duniyar nan, don haka gwara ka tafi, gwara in san cewa baka raye Tariq, watakila raina zaifi saukin yafe maka…”

Abinda ta fad’a kenan a ranar data bawa wasu daga cikin yaran Naja umarnin hayar tifa irin ta d’aukar hashi suyi karo da motar Tariq lokacin da yake dawowa daga aiki, sannan abinda ta fad’a kenan a ranar da labarin mutuwar tasa ya iso kunnenta.

Don haka kamar yadda Naja’atu ta fad’a ne, Khadija k’aramar alhaki ce, tasa an kashe wanda zuciyarta taso ma balle ita, wani ganye da bai ko kai reshe ba? har ta isa ta tare mata hanyar isa ga Madakin da take son cimma burinta akansa?

Ai ko bishiya ce tayi kad’an ta tare ta.

Bishiya… Kalmar ta tsaya cak a ranta.

Bata gama bincikar rayuwar Madaki ba har yanzu, don a yadda taji daga bakin Mubarak kwanansa hudu kenan da dawowa daga can garinsu, kuma bata neme shi bane don tana bin komai a sannu, bata son tayi abinda zai shsllake tunanin Yayanta tun yanzu… Amma duk da haka ya kamata ta bincika, rayuwar mutum kan iya canjawa cikin abinda baifi minti guda ba, zai iya yiwuwa akwai bishiyar da bata san da tsironta ba a rayuwar Madaki.1

A lokaci guda taji jikinta ya nemi yin sanyi, amma sai fuskar Naja dake gabanta tana cigaba da wassafa mata yadda Na malam zai gama da rayuwar Khadija cikin k’ank’anin lokaci ta saita tunaninta.

Komai girman bishiyar da zata tarar, zasu sare ta ne har jiniyoyinta… Itace fa Salwa mai fuska biyu!

Ta fuskanci tarin abubuwa tun lokacin da take saliha a idanun danginta, balle a yanzu da d’aya fuskar ta riga ta ruguje, kowa ya san ainihin kalarta!

‘Matar Madaki!’

A hankali bakinta ya ambaci sunan da ta yiwa zuciyarta tambari dashi… Tambari irin wanda baya goguwa, wanda ta lak’abawa sunan ‘Mutu ka raba takalmin kaza.’2

**

A wannan daren.

Akan Expressway babban titin shiga garin Lagos, Go-slow ne mak’ure ko ta ina saboda fitowar da sojoji game da binciken da suke yi cewar a kwanaki biyu cikin watan ana yawon shigo da kayan ta’amalli da maye cikin garin, kuma a wannan satin ma ana zargin akwai motoci da yawa da zasu iso da kayan mayen, don haka gwamanati ta bada odar yin binciken, bincike sosai ake don kusan duk motar da tayi lodi sai an mata dogon nazari kafin ta wuce.

A cikin wannan go slown, akwai motoci uku dake d’auke da gara da kuma dangin Maijidda, tun bayan isowarsu garin ikkon da safe, a cikin wannan go slow suka yini saboda d’imbin motocin dake gabansu, kuma har sai da dare ya rufa kafin a k’araso kansu.

Don haka a daidai wannan lokacin marar Jakadiya Babba dake zaune a gaban motar farko ta cika fam! Da fitsari yayin da hannayenta ke damk’e da k’atuwar jakar asirin nan.08:00PM

Expressway, Lagos.+

“Kilo shele? (Me ya faru?)”

Cewar wani gabjejan soja a lokacin da yake Ζ™arasowa gaban wasu shuttle bus guda uku, inda inda sojoji biyu ke tsaye suna bincike kayayyakin da aka zube a k’asa.

“Akanwo awon bagi na. (Kawai muna duba jakunkunan ne).”

Cewar Ι—aya daga cikin Ζ™ananan sojojin dake tsaye akan kayan.

Idanun Jakadiya Babba dake tsaye a cikin mutanen motocin da aka firfito dasu yabi hannun sojan daya amsa tambayar, duk da duhun wajen tana iya ganin tudun kuΙ—aΙ—en da yake cusawa a aljihunsa wand’anda ya ciro daga aljihun jakarta, sai dai ba ta su take ba, da kowanne bugu na zuciyarta fata take kar ya gama bincika jakar ya koma kan jakar asirin nan dake gefe, taso ta riΖ™e ta, ta b’oye ta cikin Ζ™aton mayafinta amma daya daga cikin sojojin nan ya daka mata tsawa cewar ta haΙ—a ta ciin jakunkunan da aka jere akan titi kusan na motoci bakwai, don haka ba yadda ta iya haka ta kutsa ta ajiye ta kusa da jakar kayanta.

Tana iya jin Ζ™arar bugun zuciyarta kamar zai faso daga Ζ™irjinta wanda ke nasaba da abu guda biyu, tsoron kar sojan ya buΙ—e jakar da kuma tsoron kar Ι—aya daga cikin matan dake tsaitsaye a gefenta su gane ta, don ko kadan ba’a tsara cewar Ζ΄anuwan yarinyar zasu san da zuwanta ba, shi yasa ta zauna a Ι—aya daga cikin motocin dake Ι—auke da kayan garar.

‘Bayan mun isa zan aika a kira min yarinyar ba tare da sanin Ζ΄anuwanta ba, zan bata asirin tare da sharaΙ—in da bata isa ta bijire mana ba balle har ta sanar da Ζ΄anuwanta zuwana.’1

Maganar da ta gayawa Fulani kenan a daren da zasu taho, shi yasa bugun zuciyar tata ke bugawa tamkar zai faso daga cikin Ζ™irjin nata. Ilai kuwa, sai fatanta ya karbu da Ζ™arasowar wannan Ζ™aton sojan mai tambaya.

“Wetin be this? Who ask you to check their bags?” (Meye haka? Wa yace ku caje jakunkunansu?)

Cewar Sojan cikin wata gabjejiyar motar da tayi kama da saukar aradu da tsakiyar dare. A lokaci guda d’aya Sojan ya durΖ™usa da sauri ya zuge zif Ι—in jakar tata sannan cikin alamun rashin gaskiya ya shiga Ι—aga murya yana cewa sauran ‘yanuwansa an gama da kayan zasu iya wucewa su tafi.

Jakadiya Babba ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya a lokacin da aka bawa direbobin motocin umarni cewa su kwashe kayayyakinsu suyi gaba, idanunta na kan jakar ba tare da ko Ζ™iftawa ba aka fara d’iba ana maidawa cikin motar, duk jakar da aka d’ago sai mai ita ya d’aga hannu a saka a cikin motarsu, a haka har aka zo kan tata, wani soja ya gifta ta gabanta amma tayi nasarar Ι—aga hannunta dake rawa sama aka sanya jakar cikin motarsu sannan aka cigaba da sauran.

Kuma bayan nan sai da aka shafe wasu mintuna talatin d’in kafin su iya barin wajen saboda wani azababben go-slow da ya had’e ko ta ina, don haka kamar yadda aka tsara, suna isa cikin garin Lagos kai tsaye gidan Haj. Karima suka nufa, wata hamshakiyar ‘yar siyasa da take k’awa a gun Fulani.
Gidan k’ato ne mai d’auke da b’angare-bangare na gine-gine, tunda dama an san da zuwansu kasancewar Fulanin ta sanar da Haj. Karima. Motar dake dauke da kayan gara na farko ta dire Jakadiya Babba a wani Ι“angare na gidan yayin da a wani Ι“angaren kuma aka yiwa su Aunty Zainab, Jamila da sauran Ζ΄anuwan Baddo iso zuwa cikin wani gini mai d’auke da d’akuna huΙ—u da k’aton Falo, anan duk suka baje gajiyarsa suka dinga mik’e kafa suna mik’a kafin a kawo musu had’adden abinci abinci daga kwararrun masu aikin gidan, sai hankalinsu ya koma nan tunda dama banda ‘yan kame-kame a mota babu wani Ζ™waΖ™waran abinci da suka samu tsawon kwana biyu.

STORY CONTINUES BELOW
Gobe kuma sai su isa ga Jidda. Yadda aka tsara musu kenan.

***

09:30PM
Masarautar Kiyari.

Lafiya Sakin yaΖ™in sarakuna

Lafiya maida garin wani kango

Lafiya sukukun bakaka

Lafiya darzaza amalen sarakuna

Lafiya ba hau da wani ba sauken wani

Lafiya garΖ™ami wandon Ζ™arfe

Lafiya waliyyin Allah…

Wannan kirarin shi ke tashi daga bakin fadawa a lokacin da tawagar Sarki ta karaso cikin gida, zabiya kuma na gaba tana nata kirarin dake shaidawa jama’ar cikin gida dawowar Sarki daga Fada. Ma’aikatan bayi na ta zubewa suna gaisuwa a duk inda tawagar ta ratsa, Sarki ya shiga turakarsa yayin da Fadawa ma suka yi sallama suka juya.

Kamar koyaushe saΖ™o ya isa kunnen Fulani wadda ke da turaka a ranar, kuma a lokacin ne ta gama shirinta tsaf! Ta fito daga cikin tata turakar, sanye da wasu tsadaddun kaya dake walΖ™iya cikin hasken fitulun falukanta da take wucewa, daga nesa zaka rantse cewa leshi take sanye dashi, sai ka matso kusa sannan idanunka zai gane maka cewa kayan bacci ne kawai dake haΙ—e da mayafinsu tamkar lafaya.
A falo na uku dake tsakiya ta tarad da Ζ΄ar autarta Safina zaune tana waya, teburin dake gabanta zube da kayan cima kala-kala na dangin kayan zaΖ™i, bata ko ga shigowarta falon balle ta sauke wayar, murmushinta kawai take tana Ζ™ara lumshe ido.

“Rigima kake ji ne yau..?” ta tambaya cikin wayar muryarta Ζ™asa-Ζ™asa tana dariya.

Fulani ta Ζ™are mata kallo daga inda take tsaye, a kwanakin da suke ciki ta fahimci babu abinda tafi yi sama da waya, tunda dama ta dawo gida ne yin Siwes na tsawon watanni shida kuma ba zuwa inda ta samu take yi ba saboda haka bata da wani kwakkwaran aiki a yanzu sai wayar, ko abinci ba damunta yake sosai ba don a yanzu ma ga cake nan fal ta zuba a plate amma sai juya farantin kawai take yi akan cinyarta ta kasa ci.

“Safina..” sassanyar muryarta ta kira sunanta cike da iko irin na uwa ga Ζ΄arta.

Da sauri Safinan ta Ι—ago sannan ba tare da wani tunani ba ta katse kiran tana kallonta.

“Na’am Mama, ban san kin fito ba.”

“Ke da waye a wayar?” ta tambaya kai tsaye.

“Uhm… wani Ι—an ajinmu ne.”

“Kike waya dashi tun safe? To me yake so?”

Ta kalle ta alamun mamaki kafin tace

“Babu abinda yake so kawai gaisawa muke.”

“Bani wayar.”

Safina ta Ι—anyi diri-diri kafin ta miΖ™a mata wayar ba da son ranta ba.

Kai tsaye wajen messages Fulani ta shiga a wayar, kuma cikin abinda baifi minti guda ba ta sami amsar da take nema, saboda haka ta miΖ™o mata wayar tana Ζ™are mata kallo.

“Ɗan gidan waye?”

Safina ta bata rai kafin ta amsa.

“Babanshi Ι—an majalisar tarayya ne, a Abuja suke.”

Jin haka yasa a lokacin guda wani abu dake shirin tasowa a zuciyar Fulanin ya lafa, a tunaninta da gaske Ι—an ajin nasu ne irin shashashan yaran dake mannewa Ζ΄aΖ΄an manya don suyi maiΖ™o, saboda alΖ™awari ne ta riga ta Ι—aukarwa ranta kuma har a gaban ka’aba ta Ζ™udirta cewar Ζ΄aΖ΄anta ba zasu tab’a rab’ar talauci ba, bayan haka ma bokan dake bata kariya ya daΙ—e da shaida mata cewa duk wani jininta ba zai tab’a sanin BABU a duniya ba.1

STORY CONTINUES BELOW
“To zan yiwa Mai martaba magana sai a bashi damar aiko da magabatansa.”

A hanzarce Safinan ta zare ido tana kallonta.

“Mama ba sai na gama makaranta ba?”

“Aya ce hakan ko hadisi? Meye ya rage a gama makarantar taki ba shekara guda bane ba? Kan a kammala komai ma ai sai shekarar tazo, in kin zauna amfanin me zaki mun… Kuma kin sani ni ba son irin wannan shashancin nake ba don haka zan shaidawa mahaifinki.”

Safina ta haΙ—iye yawu a lokacin da tayi gaba ta wuce ta, da alama za’a sami matsala tsakaninta da Fulanin, don ita bata shirya yin wani aure yanzu ba, sannan shi kansa Ahmad Ι—in babu ma wannan zancen a kansa, irin samarin nan ne da chilling kawai suka sani da Ζ΄an mata ayi soyayya a wuce wajen tsakaninsu da aure sai dai gayyata. Don haka in har Fulanin ta san ba aurenta zaiyi ba dole tayi tunanin raba ta dashi, abinda ita kuma ba zata lamunta ba.

Fulani ta isa falo na Ζ™arshe a sashenta inda wasu daga cikin bayin sashen nata ke tsugunne suna jira a sallame su, kallonsu kawai tayi taji tayi kewar Jakadiya Babba, da yanzu ta fara rangaΙ—a kirarinta tana gaishe ta. Sai bakinta ya sub’uce da wani guntun murmushi tuno inda Jakadiyan take a halin yanzu, a Ι—azu bayan abinda bai gaza awa guda ba suka yi waya take sanar mata cewar sun shiga cikin garin Ikkon bayan checkpoint Ι—in da suka daΙ—e a cikinsa, kuma ma har sun isa masaukinsu gidan wata aminiyarta Hajiya Safiya.
Sai ta sake wani murmushin tana hasko yadda ruwa zai b’ulbulo daga hak’an da suka dad’e suna yi, don a zahiri ne sun riga sun k’araso gab’ar idonsa kuma babu abinda zai tsaida su, wuyarta kawai a sami adireshin gidan Madaki a gobe shikenan komai ya k’are don ta riga ta tura Jakadiya Babba da saΖ™on da yarinyar bata isa ta bijere ba. Lissafinta kenan!4

Ta isa cikin turakar Mai martaba a lokacin daya fito daga wanka, hannunta riΖ™’e da farantin nan tayi sallama, ya amsa mata tsaye daga jikin mudubi yana gyara jallabiyar jikinsa. Sai ta ajiye farantin hannunta sannan ta Ζ™arasa gareshi, Ζ™amshinta ya cika hancinsa kafin yayi tozali da kwalliyarta.

“Anyi wani zamani da wannan aikina ne ranka ya daΙ—e.”

Ta faΙ—a tana Ζ™oΖ™arin b’alle mab’allin rigar tasa, sai yayi murmushi sannan ya riΖ™o duka hannayenta biyu.

“A wancan zamanin kina matsayin Hafsatu ne ba Fulani ba.”
Itama tayi murmushi kafin tace.

“Wata Hafsatu guda Ι—aya jal a rayuwar Ahmad.”

“Har yanzu wannan Hafsatun Ι—aya ce.”

Sai ta Ι—an juya idanunta sannan tace.

“Sauran matanka fa?”

“Sunansu Maimuna da Hadiza, babu Hafsatu babu mai kamar ta a ciki.”

A lokaci guda murmushinta ya juye zuwa dariyar farin ciki da nishaΙ—i, daΙ—’i goma da ashirin ya haΙ—u ya tare a zuciyarta, har wani b’ari na zuciyar tata ya ayyana mata cewa haka rayuwa ya kamata ta kasance.

“Turaki ya gaya miki cewa zai karb’i sarautar Ciroma a watan gobe?”

Mai martaban ya tambaya a lokacin daya harΙ—e kan kilishinsa, sai ta Ι—ago ta kalle shi daga Ζ™oΖ™arin zuba masa shayin da take yi, mamaki ya Ι—arsu akan fuskarta.

“Saifudden? Wallahi bai sanar dani ba.”

Ya gyaΙ—a kansa yana Ζ™oΖ™arin duba wasu takardu da zai sa hannu akansu.

“Jiya muka yanke hukuncin bayan tashin Fada, na gaya miki ne don idan yazo miki da zancen ki bashi kwarin gwiwar yin aure, na tuntunb’e shi da hakan amma naga kamar bai shirya ba.”

Wani abu ya wuce ta maΖ™ogwaron Fulani, kwakwalwarta ta sake jaddada mata hasashenta na cewar in har bata yi da gaske ba tana gab! da rasa Ι—anta, don alaΖ™arsu a kullum baya take Ζ™ara yi kuma duk dai a sanadiyar Madaki. Zancen aurensa ba matsala bane don ta riga ta zab’a masa mata tuntuni, matsalar guda Ι—aya ce kamar kodayaushe, dole ne ta kawo Ζ™arshen Madaki kota wane hali in har tana son rayuwarta ta tafi daidai, don an daΙ—e ana ruwa kasa na shanyewa.

STORY CONTINUES BELOW
“Ina jiran shayin.”

Muryarsa ta katse ta daga tunanin da take shirin faΙ—awa, sai tayi saurin Ζ™arasa zuba sukarin ta juya sannan ta miΖ™’o masa, a lokacin ne kuma abinda bata tab’a tsammani ba ya faru.

Mai martaba ya turo mata wayar dake gefensa mai Ζ™irar landline, sannan ya faΙ—i abinda ya rusa dukkan farin cikinta na Ι—azu, abinda ya tunatar da ita cewa duk duniya babu mahalukin dake iyawa da al’amarinta irinsa, babu mai ikon tankwabe mata duk wani shirinta kuma ya kwana lafiya in ba Ahmadun ba, daga shi sai Ζ™addararren Ι—ansa ke sawa ta tuna cewa rayuwa na Ι—auke ne da kaloli mabanbanta, wasu ma baka tsara dasu ba.

“Na samu labarin abinda kika yi wanda bada yawuna ba, don haka ki kira mutanen da kika tura a waya yanzu ki shaida masu cewa su dawo Kiyari gobe da sassafe, idan har wani a cikinsu ya taka zuwan gidan Ibrahim, na rantse miki da Allah sunan Hafsatu zai fita daga cikin jerin matana har abada!”7

**

Washegari, Lagos.

04:30am.

Tsinanne, wanda Allah ya bak’anta fuskarsa, na rantse yadda asalinka yake haka zaka k’are…

Alheri ba zai tab’a isar maka ba, kasa a ranka wannan itace nasara ta k’arshe da zaka samu a rayuwarka, wannan rantsuwa ta ce…

Kuskure na k’arshe da zaka yi a rayuwarka shine ka karb’i dukiyar nan!

Idan har kana ganin wannan wata dama ce ta sake bud’e maka to kayi kuskure, Allah ya sani na tsaneka Madaki, ka riga ka san hakan kuma a yanzu ina ganin lokaci ya wuce da kalamaina ma zasu dinga b’oye manufata, kasa a ranka cewa ko zanyi yawo tsirara sai na kwatowa ‘ya’yana hakk’i da matsayinsu daka danne, ratsuwa ta ce Ibrahim!

Rantsuwarta. Kalmar ta maimaitu a cikin kan Madaki lokacin da yake kwance idanunsa na kallon rufin d’akin yayin da kansa ke nutse cikin lallausan filon gadon.

Babu adadi, shine abinda zai iya lissafawa na lokutan da Fulani ta rantse zata k’untata rayuwarsa, tun daga zamanin da baya iya fahimtar komai sai motsin fatar bakinta har zuwa lokacin da kwakwalwarsa ta fara wayon tsintar harafan magana, don haka rantse-rantsen da ta sha alwashinsu akansa da yawa, wad’annan daya tuna na daga cikin wanda kwakwalwarsa ba zata tab’a mantawa dasu bane, don kowanne ta fad’e shi ne a ranakun da ya samu wasu nasarori masu muhimmanci a rayuwarsa.

Yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya mik’o hannayensa duka biyu ya d’ora su a gashin kansa wanda ya d’an fara taruwa alamun ya jima rabonsa da aski, a yanzu k’arfe biyar da ‘yan mintuna ne na safiya, a jiya da kyar ya samu wajen k’arfe biyu bacci ya d’auke shi saboda tsabar sak’a da warwarar da kansa ya dinga yi.

Ya motsa yatsun hannunsa na hagu a hankali yana tuno sanda ya rik’e yarinyar nan dasu, riΖ™on da yayi shi da manufa biyu, na farko don ya k’aryata Fulani kamar yadda yasha k’aryata dukkan rantsuwarta akansa, don ya kwana da sanin cewa sai da ta rantse kafin ta Ι—ora masa Ζ™azafin da mahaifinsa ke kallonsa dashi tun farko, shi yasa ya rik’e tan don tunanin mahaifinsa ya tashi daga k’azafi, ya gwammace ya karb’i laifin da ya tab’a bari Fulani tayi koda guntuwar nasara ne akansa.

Dalili na biyu, ya rik’e ta ne don ya tabbatar da irin k’arfin halinta, ilai kuwa a wannan lokacin kallonsa take da idanunta farare fat! Yayin da take faman nishi saboda tsantsar fusata har k’ofofin hancita na d’agawa, a lokaci guda kuma ta fizge kanta daga gare shi sannan tayi baya tana cigaba da kallonsa, sai kawai ya koma ya zauna akan gadon d’akin sannan hankali kwance ya kira Mary a waya ya nemi data aiko masa da ire-iren security din da ya gani a waje.

STORY CONTINUES BELOW
Bai sake cewa da ita komai ba har lokacin da mutanen suka k’araso, wasu gabza-gabzan inyamurai guda uku, kowanne sanye da wasu shuΙ—ayen kayan da aka rubuta kalmar ‘SECURITY’ b’aro-baro a gaba. Yana iya tuno yadda idanuwanta ke kallonsu, da yadda fuskarta ke nuna cewa ta fahimci babu abinda zai hana shi basu umarnin cewa su d’auke ta, don haka tayi Ζ™wafa kawai sannan ta janyo mayafinta dake ninke a gefe.

Ring, ring, ring, ring…

Ƙarar alarm Ι—in wayarsa dake gefe ya katse tunaninsa dake shirin zurmawa wani babin, don haka ya mik’e tare da ambaton hailala a cikin kansa, ya nufi banΙ—aki ya Ι—auro alwala daidai lokacin da limamin masallacin unguwar ya fara kiran sallah, bayan ya fito ya canja jallabiyar jikinsa zuwa wata daban gogaggiya sannan ya fesa turare, a cikin chess-drawer Ι—akin dake gefe ya Ι—auki wasu manyan litattafai guda biyu don zai tsaya karatu bayan sallar kamar yadda suke yi a masallacin tare da malamai mabanbanta. Ya hado da wayarsa Ι—aya kafin ya fita zuwa falo, ya tsaya a jikin despencer ya tsiyayi ruwan Ι—umi kaΙ—an yasha kamar yadda yake al’adarsa a kullum.

A lokacin ne kuma hancinsa ya jiye masa sabon Ζ™amshin daya Ζ™aru a falon, wani irin cool k’amshin da yaji a jikinta jiya, alamun daya Ζ™ara tuna masa cewa bashi kaΙ—ai ne a gidan ba, karo na farko a rayuwarsa ya kwana gida Ι—aya da yarinyar dake amsa sunan matarsa, ya haΙ—iye yawu kaΙ—an a lokacin da yake ajiye kofin sannan ya juyo da niyyar fita, sai dai me? hasken fitilar waje daya shigo ta tsakanin labulayen Ι—akin ya haska masa fuskar Jidda, dunkule akan dogowar kujerar falon tana barcinta.

Kallonta yake yi da mamakin dama anan ta kwana? Baya nuna mata Ι—akin da zata kwanta ba ne kafin ya shiga ciki? Ta lullube jikinta ruf da katon farin mayafinta alamun sanyin A.cn dake aiki a falon na damunta, kamar ya wuce ta yayi tafiyarsa sai kuma yaga hakan bai dace ba, aΖ™alla ko ba zai ce ta koma Ι—akin ba ai ya tashe ta sallah tunda musulma ce.

A hankali Ζ™afafunsa suka tako lallausan carpet Ι—in dake shimfiΙ—e a tsakiyar falon ya Ζ™araso gabanta, kuma kafin yace komai idonsa ya lura da hannun damanta daya fito ta Ζ™asan mayafin dunΖ™ule da wani abu, kawai sai yaji yana son yaga meye a hannun nata don bai yarda da ita ba sam, saboda haka ya tsugunna a gabanta ya ajiye litattafansa akan carpet Ι—in sannan yasa duka hannayensa biyu da niyyar buΙ—e hannun, dana hagunsa ya tallafe nata gabaΙ—aya yayin da ya shiga ware Ζ΄an yatsun nata dana damansa a hankali, ya buΙ—e Ι—aya, biyu sannan idonsa ya gane masa wani abu kamar kwalbar turare Ζ΄ar Ζ™arama a ciki, sai dai kafin ya kai ga Ι—auko ta Jidda taji alamu hannu akan nata don haka ta damΖ™e yatsunta a lokaci guda wanda hakan ya haΙ—a har da nasa a ciki.

Da sauri ya kalli fuskarta, idanunta da basu gama budewa sosai ba amma itama kallon nasa take.

“Me yasa kika kwanta anan, bana nuna miki hanyar Ι—aki bane?”
Ya tambaya kai tsaye muryarsa na shaida tuhuma, sai ta shiga Ζ™iΖ™Ζ™ifta idanunta alamun tana son wartsakewa yayin da har a lokacin yatsunsa ke haΙ—e cikin nata.

“Hanyar da duhu babu fitila shi yasa na kasa shiga.”
Wani irin innocence Madaki ya tsinta daga cikin idonta da kuma muryarta a lokaci guda, kamar ba itace mai rashin kunyar nan jiya ba, ko don ta tashi daga bacci ne?

Motsa yatsunta data sake yi shi ya tuna masa cewa hannunsa na cikin nata ne, saboda haka yayi amfani da Ι—an Ζ™aramin Ζ™arfi ya buΙ—e shi bakiΙ—aya ya Ι—auke kwalbar nan yana karanta abinda aka rubuta a jiki.

Auberg World Fragrance.

Jidda tayi saurin sake haΙ—e tafin hannunta saboda wani irin sakayau da taji bayan ya dauke hannun nasa da kuma turaren, duk da bata gama wartsakewa ba zuciyarta ta ayyana mata cewa zata iya daukan mataki akan riΖ™e hannun nata da yake yi.

Madaki bai ce komai ba ya dawo mata da turaren don ya fahimci a cikin irin pack Ι—in nan ne na hotel da ake bayarwa ta taho dashi, ya Ι—auki litattafansa sannan ya miΖ™e zuwa koridon daya nuna mata jiya ya kunna switches Ι—in wajen, daidai lokacin da ladanin masallacin da zai je ya shiga rangaΙ—o kiran assalatu, don haka bai ce da ita komai ba ya nufi hanyar fita, idan har sun tsara mata da yin sallah a abubuwan da aka turo ta tayi ai ta jiyewa kunnenta.

STORY CONTINUES BELOW
Ya fita ya Ζ™ulle Ζ™ofar balcony Ι—in kamar yadda ya saba sannan ya murza Ζ΄an yatsunsa na dama.

*

Sai da Jidda ta tabbatar fita yayi sannan ta miΖ™e daga kwancen da take, ta kalli hanyar koridon daya kunna mata fitila sannan taja mayafinta ta miΖ™e, corridon yana da Ι—an tsawo kaΙ—an kuma Ζ™ofofi biyu ne kawai a cikinsa, tana buΙ—a ta farko taga daki ne kawai tayi shigewarta, ta ajiye mayafinta akan gadon data gani sannan ta shiga toilet din da ta gani a ciki, sai da ta Ι—an jujjuya kan fanfon sink Ι—in kafin ta gane yadda ake bude shi, tayi alwalarta ta fito.

A gefen gadon akwai wani Ι—an karamin carpet tayi sallarta akai hade da nafila sannan idonta ya shiga Ζ™arewa Ι—akin kallo, Komai tsaf yake a ciki ba laifi sai dai akwai kura kaΙ—an don ta shake ta sanda tayi sujjada, kuma duk tsaruwar Ι—akin ko kaΙ—an bai kai na wajen nan data fahimci kamar hotel ne ba kyau. Allah ya sani sam a jiyan nan bata so barin wajen nan ba, ba wai don bata gaji dashi ba sai don ta nuna masa gaskiyar abinda ta fada cewar ‘babu wanda ya isa ya juya ta.’1
Amma abinda yayi a lokacin shi ya tsallake tunaninta, waje ya samu kawai ya zauna sannan ya d’auki wayarsa yayi kira cikin harshen turanci, kuma tun daga nan ta fahimci cewa yayi a turo masa da mutane cikin wannan kwantacciyar muryarsa, sai dai bata san wane irin mutane ne ba sai bayan sun k’araso.

Taja tsaki a hankali saboda takaicin yadda bata Ζ™ara wani ja ba ta yarda ta biyo shi a lokacin, amma ya zata yi ne? Bata da wani zab’i da yafi hakan tunda ba zata tab’a bari waΙ—annan arnan su tab’a ta ba.

Ta shafa addu’arta sannan ta miΖ™e tsaye, ta ninke mayafin ta ajiye akan gadon kafin ta matsa jikin windon gefe, iyakar hangenta bayan ta Ι—age labulen bata ga kowa ba, gidan shiru yake sosai babu ko fitilu a waje sai na can wajen kan titi da take hangowa, kuma da alamu unguwar ba mai mutane bace sosai, irin wajen nan ne da kowa yana gidansa babu ruwan wani da wani, taji zuciyarta tayi wani iri don bata san har tsawon yaushe zata kasance anan kafin ta koma gida ba, ita da ta saba da cikin hayaniya, su yini suna yawo a b’ulla nan a fito ta can, ga mutane ko’ina sai ka yini ma a Ι—akin wani.

Taji baΖ™in ciki na neman turniΖ™e ziciyarta sai kawai ta rufe labulen ta dawo, ta matsa jikin wardrobe ta buΙ—e ta, babu komai a ciki sai wata riga guda Ι—aya irin polo shirt Ι—in nan fara Ζ™al, tasa hannu ta Ι—auko ta, alamun sabuwa ce don ga Ζ΄ar takardarta nan ma a maΖ™ale, wani abu mai kama da daΙ—i ya ratsa zuciyarta, Allah ya sani bata san adadin yadda jikinta yayi kewar wasu kayan ba, don ba Ζ™aramin kokari tayi ba na zama da lace Ι—in nan tsawon kwanaki ita da a gida ko kaΙ—an bata zama da duk abinda zai dami jikinta. Tana saka rigar ta koma da baya ta kwanta akan gadon nan jikinta na gode mata, ita da rigar Jamila kuma, ko a lahira.

Zuwa can taji cikinta ya murΙ—a alamun yunwa, sai ta tuna cewa bata gama cin abincinta ba a jiya suka taho, idonta ya hasko mata yadda abincin ya zube akan gadon nan sanda ya jawo ta, sai taja tsaki sannan ta miΖ™e, zuwa zata yi ta nemi abinda zata ci don ta san baza a rasa wani abu ba a gidan, kuma dai don taci abinci babu abinda zai faru, ta nemi Ι—ankwalinta ta yafa sannan ta fita.

Ƙofar nan ta biyu a cikin koridon ta fara buΙ—ewa sai dai maimakon kitchen, wani Ι—akin idonta ya gane mata don haka ta rufe shi ta biyo hanyar ta dawo falon, shima babu wani tarkace sosai kamar ba gidan namiji ba, sai dai kamar yadda ta ganshi jiya akan kowacce kujera akwai kaya a ajiye, wasu ma a cikin leda alamun daga wanki aka karb’o su, ta juya ta nufi wajen dining anan ta gano irin tasa Ζ™azantar.

Akan teburin dining Ι—in takardu ne fal layi-layi, wani layin ma har tsini yake babu koda gurin ajiye kofi balle asa ran zaman plate, da alama kwata-kwata ba’a amfani da wajen don cin abinci, sai ta tab’e baki sannan ta nufi Ζ™ofar data tabbatar nan ne kitchen Ι—in da take nema.

A lokaci guda zuciyarta ta matse guri Ι—aya sannan ta narke har gulbinta, a sakan Ι—in farko kasa tantance abinda idonta ke gani tayi, don tunda take a rayuwarta bata tab’a mafarkin cewa zata ga waje mai kyau irin haka ba… Ƙato ne mai madaidaicin girma, sannan an zagaye shi da wasu haΙ—aΙ—Ι—un drawers kalar lightbrown da baΖ™i da suka bada shape mai kyau, wasu wajen a rufe, wasu wajen kuma a buΙ—e an musu layi-layi mai kyau, ga wasu fitilu dake haskawa daga Ζ™asan durowoyin masu ‘dim’ haske. A tsakiyar kitchen Ι—in kuma wani ginin drawer ne da aka Ι—ora masa wani gilashi mai faΙ—i yanayinsa kamar ruwa ya zube a kai.

Ta Ζ™ifta idonta ta sake buΙ—ewa, Allah ya sani ko a hoto sau Ι—aya ta taba ganin irin wannan wajen, watarana da Aunty Zainab ta fito musu da tsofaffin mujallunta irin wanda mijinta daya rasu ke siyo mata, anan taga shigen wannan kitchen Ι—in, amma shima ko kad’an bai kai wannan ba. Sai ta saki Ζ™ofar a hankali ta shigo, tana jin wani abu mai kama da daΙ—i na giftawa a zuciyarta.

Waje mai kyau duniya ne Jidda, Allah ya kaimu inda zamu ji daΙ—i!

Ta tuno abinda Sadiya ta tab’a faΙ—a mata ranar da suka taba leΖ™awa b’angaren wani Ι—an mai martaba da tace sunansa Umarul-Faruk, wai yana Ζ™asar waje yana karatu ranar an buΙ—e wajen ne kawai ana share-share.

A hankali ta shiga buΙ—e drawers Ι—in da mafi yawanci ba komai a ciki, akwai wasu Ζ΄an plates da kofuna biyu a cikin sink da ba’a wanke ba. Ga wani Ζ™aton gas nan da kayan amfani da wuta kala-kala, daga Ζ™arshe ne tana buΙ—e wani waje taga ashe fridge ne, sai ta rufe shi ta sake Ζ™arewa murfin kallo, ba don handle Ι—insa ba babu abinda zai sa ta kasa rantsewa cewa shima drawer ce don kalarsa baΖ™i ne ya saje sak da kalolin drawers Ι—in, ta jinjina kai sannan ta sake buΙ—e shi, a ciki kaya ne fal irin na gwangwani da leda, sai kuma fruits kala-kala.

Kenan duk azabar kyan kitchen Ι—in babu wani girki da ake yi a cikinsa, wannan wace irin asara ce haka? Ta shiga Ι—aga kayayyakin da yawa bata san meye ba don haka ta ture su gefe, inda so samunta ne a yanzu ta sami Ι—umamen shinkafa ko wace iri ce, musamman ace da manja da yaji ai shikenan an wuce gurin, ko kuma ace ta dafa taliya tayi miyar attaruhu da albasa, zata iya nutsewa don daΙ—i.1

Daga Ζ™arshe kifin gwangwanin data sani kawai a cikin kayan ta Ι—auko da ragowar wani biredi, taja kujera Ι—aya a tsakiyar Ζ™itchen Ι—in sannan ta buΙ—e shi da kyar ta shiga dangwala biredin tana ci, ta hango katan-katan Ι—in ruwa don haka ta Ι—auko guda d’aya tana korawa, sai ta fara dawowa hayyacinta sannan take Ζ™ara ganin kyan kitchen Ι—in, a gefe guda kuma tana jin kamar damuwarta na yayewa.

A daidai wannan lokacin ne kuma idonta ya kai kan wani file dake ajiye a Ζ™asan glass Ι—in island Ι—in, ta sake tab’e bakinta tana tunanin watakila babu abinda yafi yawa irin takardu a gidan, kuma babu wani tunani ta janyo shi ya biyo hannunta cikin santsin glass Ι—in, ta buΙ—e shi a hankali tana tauna biredin dake bakinta, a ciki irin wannan baΖ™in abun ne na X-ray, ta fito dashi tana Ζ™are masa kallo, kamar hoton zuciya ne ko Ζ™irji amma bata gane ba, sai ta Ζ™arasa jawo shi lokacin da wata ‘yar Ζ™aramar takarda ta faΙ—o daga ciki.

Ta Ι—auka ta buΙ—e ta, a sama an rubuta tambarin sunan asibitin da kuma adireshinsa, sai wasu guraben da aka cike sunan mara lafiyar, shekaru da kuma jinsinsa, idonta ya tsaya akan sunan na Ι—an lokaci.

IBRAHIM AHMAD MADAKI

Ko banza ta san duk wanda zai bada labarinta a yanzu sai ya haΙ—’a da wannan sunan, ta girgiza kanta sannan ta cigaba da karantawa, bayan inda aka rubuta Madical Report idonta ya sauka akan rubutun da yake a Ζ™asa, wanda yake a buge ba handwriting ba.

Congestive heart Failure: Stage D
Prognosis: Still bleak.

Sai wasu dogwayen bayanai cikin wasu words masu tsayi da kasa ganewa, amma daga can Ζ™asa sai idonta ya tsaya kan wani layi guda.

Average life expectancy: Five years.

Babu shiri ta haΙ—iye ragowar abinda ke bakinta sannan ta Ζ™ara karantowa, idonta ya manne a layin Ζ™arshe.

Average life expectancy: Five years.5

(Wa’adin shekarun da ake hasashe: Shekaru biyar.)

**Tsawon wucewar mintuna biyu Jidda na kallon takardar nan, kwakwalwarta ta fahimci ma’anar abinda take karantawa amma ta gaza yarda cewa daidai ne, gani take kamar fahimtar nata turancin da abinda ake nufi sun banbanta, ta yaya za’a bawa mutum wa’adin shekarunsa a duniya? Ko ba gaskiya bane wane irin tashin hankali ne wannan?+

Dama bashi da lafiya kenan? Shi yasa a jiya taga ya rame? Idonta ya sake kaiwa kan layin farko.

Congestive heart Failure: Stage D1

A lokaci guda kuma ta tuno lokacin da suka tsaya a wannan asibitin a Kano.

Hamrish Cardial Hospital

Kenan ciwon zuciya ne dashi? Ciwon ma har ya kai wani mataki da za’a ce zuciyar na kasawa? Ta shiga jerowa kanta tambayoyi a lokaci guda kuma tana bawa kanta amsa da iya abinda ta sani, tunaninta ya sarΖ™e da hangen wane irin tashin hankali mutum zai ji ace ana maka zaton wasu Ζ™ayyadaddun kwanaki a duniya, ai Allah bai b’oye lokacin mutuwa haka kawai ba sai don rayuwar baza ta tafi cikin kwanciyar hankali ba ace kowa yana da lissafin kwanakinsa a Ζ™irge, bayan haka kuma ace kwanakin ma zasu tafi ne cikin ciwo da jinya, sai ta haΙ—iye yawu kaΙ—an don kwakwalwarta ta kasa fahimtar yadda hakan zai kasance.

Yatsunta suka ninke takardar a hankali sannan ta had’a da abin X-ray Ι—in nan ta mayar cikin file Ι—in. Ta janyo biredinta ta cigaba da ci amma idonta na manne da file Ι—in, wani tunani ne da bata so ke shirin dawo mata don haka ta shiga iya Ζ™oΖ™arinta wajen danne shi, amma duk da haka wasu kalamai suka yi nasarar kutsowa.

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un…

Hauwa’u riΖ™e min hannuna,

Bani ruwa in sha…

Yi min fifita…

Babu shiri ta miΖ™e tsaye, ta Ζ™ulle biredin ta mayar cikin fridge Ι—in sannan ta wulla gwangwanin kifin shara, kafin ta isa Ι—aki kwalla ta nemi cika idonta don ta kasa danne zuciyarta balle ta iya gujewa tunanin da yafi Ζ™arfinta, Ζ™waΖ™walwarta ta riga ta zarme zuwa wani lokaci can daya shuΙ—e, lokacin da ya tafi da wani abu mai muhimmanci a rayuwarta, sannan lokaci irin wanda ba zai tab’a dawowa ba.

Mamanki ciwon zuciya ne da ita, idan kuka siya waΙ—annan magungunan da wuri za’a iya shawo kan matsalar…

Cewar wani likita, a wancan lokacin da suke tsaye a ofishinsa ita da wan mahaifinta, Kawu Alhaji.

Har nawa ne kuΙ—in maganin likita?

Kawun ya tambaya.

Kuje office Ι—in da kuka fara zuwa za’a rubuta muku…

Ya bada amsa hankalinsa a kwance. Sai ta tuno sanda ta zube gwiwoyinta a Ζ™asa lokacin da Kawu Alhaji ke riΖ™e da takardar da aka rubuta musu zunzurutun kuΙ—in magungunan.

Babu shiri a yanzu ma ta durΖ™ushe gwiwoyinta akan carpet Ι—in dake tsakiyar Ι—akin sannan ta jingina bayanta da gado, idanunta na haskawa da kyallin kwallar da ta cika su taf!

Ɗauki waya ki kira min Baddo Hauwa’u, gwara su zo tun wuri, ciwona bana tashi bane..

Ba zaki mutu yanzu ba Mama, su Baddo zasu zo su ganki cikin Ζ™oshin lafiya insha Allahu zaki tashi…

Kayya! Jidda ni kaΙ—ai na san irin ciwon da nake ji…

Kawu Alhaji yace za’a sami kuΙ—in aikin nan insha Allah zaki warke ki tashi…

Tana iya tuna fuskar mahaifiyarta a lokacin, tana iya tuna wani busashshen murmushi da tayi, tana ganin komai kamar a yanzu yake faruwa.

Ni dake mun san su Kawu basu da dalilin waΙ—annan kuΙ—aΙ—en Jidda, ya faΙ—a ne kawai don hankalinki ya kwanta, sannan Baddo ma kinga ba wani Ζ™arfi ne da ita ba… Mu kuma babu abinda muka tara… Kiyi addu’a…

STORY CONTINUES BELOW

Kwallar ta gangaro kan kumatunta sannan wata ta sake taruwa lokacin da hoton da take gani a idonta ya canja, ya koma wata ranar daban, ginin asibitin ya koma zuwa na gidansu, cikin Ι—akinsu, sannan fuskar mahaifiyarta ta sake Ζ™armashewa…

Bana son ki koma wajen dangin mahaifinki Jidda, nafi son kije ki zauna tare da Baddo, ba wai don ina son zaman inda take ba sai don ko ba komai idan kina gabanta na san zaki tashi da irin tarbiyar data bani, watak’ila ma wannan halin naki ya gyaru saboda wata k’addarar…’

Ta runtse idanunta yayin da bakinta ya Ι—an tab’e cikin kuka, kamar koyaushe amon muryar rad’au yake amsawa a kunnenta don tana d’aya daga cikin doguwar magana ta k’arshe da mahaifiyar tata tayi mata kafin ciwon yaci k’arfinta ya zamo harshenta ya nad’e har ta daina iya magana kwata-kwata.

A wannan ranar ne kuma ta bata ‘Fullo’ d’an zagayayyen dunk’ulen zinaren data mallaka daga wajen mahaifinta, tace mata mahaifina ya bata shi ne a ranar da aka saka ranar aurensu, don haka ta sanya masa sunan ‘Fullo’ wanda ma’anarsa shine ‘Baiko’ da fulatanci.

A hankali ta miΖ™a hannunta na dama zuwa saman wuyanta, wajen da a koyaushe take Ι—aura Fullon kafin Ζ™addara ta sanya ta maida shi hannunta, hakan kuma ya zama sanadin samun kanta a wannan halin da take ciki.

…saboda wata k’addarar…’

WaΙ—annan kalaman suka maimaita a cikin kanta, haka mahaifiyarta tace, wai saboda wata Ζ™addarar… A wancan lokacin ta riga ta san duk wata tarin ma’ana ta k’addara, walau mai kyau ko akasinta, sai dai kamar kowa abinda bata sani ba shine…

Me cece tata k’addarar?

Yaushe zata fuskance ta?

A wane yanayi zata zo?

Mai kyau? Ko akasin haka?

Wad’annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk’alami ya bushe akansa. Don ta sani wata k’addarar tamkar zanen dutse ce… Babu wani abu da ya isa ya canja ta.

A yanzu kuma wani abu mai kama da tsoro ne taji ya kama zuciyarta, kar dai wannan itace tata Ζ™addarar, Ζ™addarar da take jira tsawon lokaci… Idan ba haka ba, me yasa tarihi zai sake zagayo da rayuwarta zuwa mutumin dake Ι—auke da makamancin ciwon daya kashe mahaifiyarta?2

***

Royal K Group of Companies.

139A Emina Crescent.

“Ka san cewa ciwon zuciyarka na gado ne?”

A waccan ranar da ya tsaya a garin Kano, muryar likitan ta tambaya cikin shirun daya gauraye office d’in.

Madakin dake zaune a kujerar tsallaken teburinsa ya runtse idonsa kad’an sannan ya bud’e su akan sabon file d’in da aka bud’e masa wanda ke rik’e a hannun likitan.

A lokacin tunaninsa ya shiga hasko d’imbin asibitocin da suka tab’a bud’e file da sunansa, saboda ba wannan ne karo na farko ba. Ciwonsa kan tashi a kowanne lokaci musamnan sanda yake gab’ar aiki, don haka d’aid’aikun garuruwa ne kawai a Nigeria zai d’ebe cewa baije asibiti a cikinsu ba.

Ya sani cewa ciwonsa na gado ne kamar yadda likitan ya faΙ—a kuma yana tare dashi har abada, manne da bugun zuciyar da kullum ke tunatar dashi cewa, duk yadda abubuwa zasu yi kyau a rayuwarsa… Akwai wani gib’i da babu mahalukin da ya isa ya cike shi.

STORY CONTINUES BELOW

“Na sani.”

Muryarsa ta fito a hankali cikin sautin da baka isa ka tsinto d’imbin damuwar dake tsere a cikin kansa ba. Likitan ya gyada kai.

“Kuma ka sani cewa ya kai matakin da ake kira Stage D, matakin dake Ι—auke da tsantsar haΙ—ari?”

“Na sani.”

Likitan ya sake gyaΙ—a kai.

“To ina ga babu sauran abinda ya kamata in gaya maka bayan abinda na san sauran liktocinka na baya ke yawan gaya maka cewa ka rage saka damuwa a ranka, tunda ka san wannan ciwo ne da yake tare da kai kullum sai dai fatan samun saukinsa. Dole ne ka dinga kiyaye abubuwan da zasu iya tayar dashi, ina ga da munyi X-ray zan Ζ™ara tabbatar da wani abun, saboda alamu sun nuna electrical system d’inka ya sake rauni wajen regulating bugun zuciyar.

A yanzu kana buk’atar hutu ne sosai don magungunanka ma naga suna kan kari, ina ga dai zan baka maganin bacci ne yadda zaka huta Ι—in sosai kamar na sati biyu.”

Madaki ya koma da baya ya jigina da kujerarsa sannan ya shiga juyawa a hankali, wannan maganar ta likitan itace dalilin da yasa a wannan daren da jirgi ya sauke su a airpot daga Kano, ya yanke shawarar tura yarinyar can wani wajen don ya huta aΖ™alla na tsawon sati biyun da likitan yace, kafin ya fara fuskantar duk wani abu da tazo dashi, sai gashi tun ba’a je ko’ina ba, kwana huΙ—u kaΙ—ai hakan ya rushe.

Yana da tsari. Haka ya gayawa kansa tun farko kuma ya yarda cewa duk wani rintsi ba zai canja ra’ayinsa ba, sai gashi abinda yafi rintsin ya sashi karya wannan ra’ayin tun ba’aje koina ba, fatansa kawai a yanzu shine abubuwa su cigaba da tafiyar masa daidai.

Ya motsa yatsun hannunsa a hankali yana cigaba da juyawa a cikin kujerar, har ya fito daga gidan a yau bai ganta ba, watakila bata tashi ba watakila kuma tana ciki tana shirya wani abun ne, sai yaja tsaki kaΙ—an a Ζ™asan numfashinsa kafin ya Ι—ago ya cigaba da aikin da yake yi cikin screen Ι—in computersa.

Ƙofar office Ι—in ta buΙ—e a lokaci guda kuma ya riga ya san waye, don mutum Ι—aya ne ke da hurumin yin hakan ba tare da izini ba. Yana jinsa har ya Ζ™araso ya zauna a kujerar dake tsallaken teburinsa amma baice komai ba bayan sallamar da yayi kuma ya amsa masa Ι—in, sai ya Ι—ago ya kalle shi, ya kishingiΙ—a abinsa da kujerar da ya zauna yana Ζ™arewa fuskarsa kallo.

“Me ya faru?”

“Tunani nake wane sunan ya kamata in kira ka dashi yanzu Mdee ko kuma Ango?

Jin haka yasa Madaki sake yin tsaki sannan ya haΙ—e ransa fiye da Ζ™ima.

“Bana son rashin mutunci Mubarak, abinda ya kawo ka kenan?”

Cikin dariya Mubarak Ι—in ya Ι—ago yana cewa.

“To fisabilillahi me kake tunanin ana kiran mutumin daya kwana gida Ι—aya da sabuwar amayarsa? Ka san Allah kamata yayi ma kawai na sauka Ζ™asa nayi annoucing wa sauran ma’aikata mu haΙ—a maka ‘yar walima yanzun nan.”

Bai ce dashi komai ba, ya cigaba da rubutu kan takardun dake gabansa. Ganin haka yasa Mubarak ya Ι—aga hannayensa duka biyu sama alamun sallamawa sannan ya gyara zamansa sosai.

“So me ake ciki yanzu?” ya tambaya muryarsa na shaida cewa ya bar fagen wasa.

Kuma ba sai ya fasa ba Madaki ya riga ya san me yake nufi da hakan, don lokacin daya gama waya da Mai martaba ya kira shi ya shaida masa abinda mahaifin nasa yace da kuma shawarar daya yanke cewa zai je ya Ι—auko ta, abinda basu tattauna ba shine yadda ya Ζ™arkare da mahaifin nasa, saboda haka ya tsaya da abinda yake yi kafin ya amsa.

STORY CONTINUES BELOW

“Yana gama bayanin ya kashe kiran ni kuma ban sake kira don in bashi haΖ™uri ba saboda na san ba zai saurare ni ba a wannan lokacin.”

Sanin hakan yasa Mubarak ya gyaΙ—a kansa ba tare da wani ja ba sannan yace.

“Ita kuma yarinyar fa?”

“Zan bincike ta ne a hankali ta hanyoyin dana tsara .”

Mubarak ya girgiza kansa.

“Kamar koyaushe kai da zuciyarka ka yanke wannan shawarar ko?”

“Haka ne, amma ka san zan jira ai ka fad’a min taka shawarar kafin dai in d’auki tawan.”

“Mdee idan kace zaka bibiyeta a hankali zaka bata lokacinka ne, tunda kace yarinyar nan Ζ™arama ce kaga definetely duk wani wayonta bai kai naka ba kenan, saboda haka ka shammace ta kawai ka jata a jiki, ka koya mata wata rayuwar da zata ji duk duniya bata da gata in ba naka ba, ina gaya maka da ka canja mata tunani in no time zaka sami duk abinda kake so.”

Karo na biyu Madaki ya Ι—ago ya kalle shi, yanayin fuskarsa na nuna kamar bai fahimci da yaren da yayi magana ba.

“Me kake nufi wai?”

Mubarak ya gyara zamansa kamar mai shirin biyo karatu a wajen musabaka.

“Ina nufin kayi formating kwakwalwar yarinyar nan, ka biya mata wani sabon karatun ta manta duk abinda ta taho dashi, me yasa ne ma zan maka wannan bayanin Mdee? Ka san hanyoyinka fa.”

Madaki ya cigaba da kallonsa kawai, kamar yana gaya masa cewa ya kara da jirgin sama ne a Ζ™irjinsa.

“Ina gaya maka idan ka Ι—auki shawarata zaka dace, zaka fahimci dalilin da yasa nake maka murnar auren nan, don sai yanzu na ga wallahi Mai martaba ba Ζ™aramar dabara yayi ba da bai tuntubeka ba, shekarata nawa ina roΖ™onka akan aure Mdee.”

Madaki ya girgiza kansa yana komawa rubutunsa sannan yace.

“Kaima ka san matsalata Mubarak, ba wai auren ne bana so ba, ina ganin kamar bani da lokaci ne kawai.”

A lokacin guda sai fara’ar dake kan fuskar Mubarak Ι—in ta gushe, ya cigaba da kallonsa alamun mamaki kafin yace.

“Kamar yaya baka da lokaci?”

Sai a lokacin kuma Madaki ya fahimci katobarar da yayi, ya manta ne cewar kamar yadda har yanzu yaΖ™i bawa kansa damar dashi da zuciyarsa zasu tattauna zancen result Ι—in daya karb’o kafin tafiyarsa Kiyari, har yanzu Mubarak ma bai san da hakan ba, don bai san ta yadda zai gaya masa cewa an kai gab’ar da likitoci ke sa masa rai da wasu Ζ™ayyadaddun kwanakin a duniya.

“Ina nufin bani da wani lokaci sai na aiki da jinyar kaina.”

Yayi saurin gyara zancen, kuma kamar hakan yayi tasiri don a lokaci guda annurin fuskar Mubarak Ι—in ya dawo sannan yace.

“Aure ba sai an nema masa lokaci ba Mdee, da kansa yake samarwa kansa gurbin da zai zauna a rayuwar Ι—an adam kamar yadda hakan ya faru yanzu, don haka ina gaya maka ka saki ranka game da yarinyar nan ka juye sharrinta zuwa alkhairi, ka fahimtar da ita cewa ba Ζ™aramar sa’a tayi ba data same ka.”

Sai ya sake girgiza kansa kawai sannan yace.

“Allah ya shirye ka.”

“Amin.”

Har Mubarak Ι—in kuma zai Ζ™ara magana Ζ™arar wayar Madakin ta katse shi, ya Ι—ago ta a hankali yana Ζ™arewa nambar kallo kafin ya Ι—auka, wani daga cikin abokan hulΙ—arsa ne da ya kira akan neman wani contract dasu, suka yi zancen hakan kafin suyi sallama, sannan ya Ι—ago ya kalli Mubarak Ι—in dake danne-danne akan Tab Ι—in hannunsa.

“Seriously wai nishadin me kake ji ne yau? Kwana biyu a baya kamar kana cikin damuwa, yau kuma sai farin ciki kake.”

Mubarak yayi murmushi ba tare da ya Ι—ago ba, me zai ce dashi? A kwanakin baya rayuwarsa na cikin kwale-kwale a yanzu kuma ya isa kan gab’a? Don Salwa taje har gidansu Khadija ta bata haΖ™urin da yayi sanadiyar dawowarta gidansa, kuma a cikin kwana biyun nan ta canja halinta bakiΙ—aya tana tabbatar da rantsuwar da tayi masa cewar ta canja Ι—in, don a jiya ma ya ganta har aiki ta taya a gidan.

STORY CONTINUES BELOW

Kai namiji ne Mubarak, ko ba komai zata fi shakkar aikata wani abun a gabanka…

Abinda wani Kawun mahaifinsa ya faΙ—’a kenan ranar da aka yanke shawarar zata koma gidansa daga wajen Aunty Sumayyan, wataΖ™ila kuma ya yarda da hakan. Sai dai tunda har bai gayawa Madakin matsalar tun farko ba, babu amfanin yi masa bayanin komai da ya riga ya wuce, saboda haka ya Ι—ago da kansa sannan yace.

“Na gaya maka nishaΙ—in da ya kamata ace kai kana yi nake maka.”

Kuma kafin Madakin yace wani abu sai ya canja zancen da wani daban. Kuskure na farko kenan.

“Yauwa, zancen Kamfanin Bird Crest dama zanyi maka, sun Ζ™aro wasu supplies Ι—in ne da suke so, jiya Samuel ya kawo min request Ι—in.”

Kamar Madaki ya sake tambayarsa sai kuma kawai ya fasa, ya karb’i zancen shima suka shiga tattaunawa. Kususkure na biyu kenan.1

Kusan minti talatin suna tattauna duk wasu harkokin kasuwancinsu kafin tunanin Madakin ya fara canjawa, cikinsa da bai iya riΖ™e yunwa ba sam! ya shiga bayyana Ζ™orafinsa, saboda haka ya jawo wayarsa ya kira Toyin da sakon cewa a kawo masa abinci daga restaurant Ι—in kamfanin inda ake masa girkinsa daban wanda ya dace da Ζ™a’idojin ciwonsa.

“Ita kuma ta gidan fa? Me zata ci?” Mubarak ya tambaya bayan ya ajiye wayar.

Bai ko kalle shi ba ya cigaba da dube-dube kan screen Ι—in computer dake gabansa. Sai Mubarak ya gyara zamansa sosai sannan ya kira sunansa, ainihin sunansa don ya fahimci cewa da gaske yanzu sun bar fagen wasa.

“Ibrahim…”1

“… Kar ka manta cewar duk wani abu dake cikin al’amarin nan fa still aure kayi, kuma ko ka Ζ™i ko kaso akwai wasu hakΖ™i na yarinyar nan da ya rataya akanka, hakΖ™in da ko ka rabu da ita daga baya Allah sai ya tuhume ka idan har ka cuce ta. Yanzu misali kace da kaya Ι—aya ka Ι—auko ta babu wasu, don haka siya mata wasu kayayyakin da zata saka da ‘yan sauran abinda zata buΖ™ata, sannan ka ajiye abinci a gidan tunda kaga duk lalacewar al’amarin nan ba zaka azabtar da ita da yunwa ba, ko ba komai idan kayi hakan ka tsallake maganar Mai martaba ta cewar kana cutar da ita ne.”

Madaki ya cije lebbensa na Ζ™asa yana jinsa, rauninsa a duniya guda Ι—aya ne, Mahaifinsa. Don haka zai iya rantsewa da Allah Mubarak Ι—in na sane ya faΙ—i haka don yaci galaba a kansa.

Sai dai kafin wani daga cikinsu ya sake magana Toyin ta shigo ta sanar da Mubarak cewa wasu ‘yan aike daga kamfanin DRD sun nemi ganinsa, don haka ya miΖ™e yana masa sallama.

Bayan wani lokaci kaΙ—an abincin ya iso, Toyin ta sake shigowa riΖ™e da dogon tray mai Ι—auke da abincin da kuma fruits kala-kala da aka yayyanka, ta jera a gabansa kuma a lokaci guda ya shiga ci, bakinsa na tauna a hankali tare da lumshe idanunwansa.

‘…sannan ka ajiye abinci a gidan tunda kaga duk lalacewar al’amarin nan ba zaka azabtar da ita da yunwa ba…’

Maganar Mubarak ta haska a cikin kansa sannan kuma fuskar yarinyar ta biyo baya, sai ya Ζ™ara lumshe idanunsa yana tuno sanda ya kamata a bayan labulen nan da ya zama mafarin Ζ™addararsu, da sanda ya riΖ™e hannunta a cikin jirgi, da sanda yake hango fuskarta a cikin motar nan, ‘yar k’aramar fuskarta dake shaida kumburin kuka da kuma saman hancinta da yayi ja alamun sanyin A.c da ya ratsa ta, da kuma sanda ta bude idonta akansa yau…

Mubarak ya riga ya faΙ—i abinda zai saka shi a tsaka mai wuya, don da gaske ne yayi amfani da kalaman da zuciyarsa ba zata taba kwanciya ba in har yayi biris da hakan. Ya kalli lokaci a jikin wani tafkeken agogo dake bango, Ζ™arfe huΙ—u na yamma na dab da Ζ™arasawa kuma shi shaida ne cewa babu abinci a gidan, don haka babu abinda taci kenan tun safe.

Ya Ι—ebo abincin kamar zai sake kaiwa bakinsa sai kuma ya fasa, ya mayar da cokalin ya ajiye sannan ya sake kiran Toyin a waya.

“Akwai wani sabon contract ne yau?”

STORY CONTINUES BELOW

“A’a yallab’ai, amma akwai ganawarka da shugaban kamfanin NID da misalin Ζ™arfe huΙ—u.

“Ki maida shi 4:30, zan fita ne kuma ba lallai in dawo da wuri ba.”

“Okay yallab’ai.”

Har zai ajiye wayar, sai kuma yace.

“Kizo ki kwashe abincin nan.”

***

Motarsa ta tsaya a cikin parking space Ι—in wani katafaren gidan cin abinci, inda a baya yake wajen zuwansa don shine waje mafi kusa da wajen aikin nasa.

Ya fito sannan ya rufe Ζ™ofar motar, yana shiga ciki Ι—aya daga cikin ma’aikatan wajen tayi murmushi haΙ—e da Ι—agawa Ζ™awarta gira Ι—aya alamun sun gane shi, ya Ζ™araso jikin kantarsu ya tsaya a lokacin da take Ζ™oΖ™arin Ι—auko wata folder.

“Barka da zuwa yallab’ai…”

“7, 8, 11, 19.” Ya katse ta tun kafin ta kai ga miΖ™o masa Menu Ι—in don tun a baya ya riga ya haddace kowacce number dake Ι—auke da sunayen abincinsu.

Sai ta gyaΙ—a kai tana Ζ™ara faΙ—aΙ—a murmushinta kafin ta juya, ya zaro wallet Ι—insa ya fito da wasu adadin kuΙ—i na abincin ya ajiye akan kantar sannan ya koma wajen motarsa, mintuna kaΙ—an wani daga cikin ma’aikatan nasu ya iso riΖ™e da ledoji biyu cike taf da abincin dake ta Ζ™amshi.

A hanyar komawarsa office Ι—in ya tsaya yayi sallah a wani masallaci dake kan titi, bayan ya idar ya jima a zaune yana addu’oinsa kafin ya shafa, addu’oin da suka zame masa babbar garkuwa a rayuwarsa don baya jin zai iya kaiwa matsayin da yake a yau ba don su ba. Idonsa ya kai kan wani Ι—an Ζ™aramin kanti dake Ι—aya tsallaken titin a lokacin da ya miΖ™e.

Sweesha’s Couture.

Fararen gilasai ne a jikinsa kotaina don haka ana hango statues Ι—in mata waΙ—anda ke sanye da dogwayen riguna. Yayi saurin Ι—auke kansa lokacin da wani dattijo ya nufo shi zuwa inda ya ajiye motarsa, bai san me yake cewa ba amma da alamun bara yake yi don haka ya zaro kuΙ—i kawai ya miΖ™a masa, ya shiga cikin motar ya tayar sannan yayi gaba.

Ya isa kan junction dake can gaba inda aka tsayar da motocin b’angarensa, wata mata tazo tsallaka titin riΖ™e da hannun Ι—anta, yabi ta da kallo, kayan jikinta lace ne kalar lemon green. Idonsa ya hango masa Jidda, sanye da Ζ™aton mayafin nan da kuma lace Ι—in jikinta kalar lemon green, ya hango wannan hoton lokacin da daga ita sai d’an k’aramin d’ankwalin lace Ι—in daya tsaya iya cinyarta, gashinta a jik’e ta sunkuya tana taje shi… Traffic light ta nuna alamun bangarensa su wuce.

Sai kawai yasha kwanar dake kan junction Ι—in maimakon ya miΖ™e, ya dawo baya hanyar dai da ya wuce kuma bai tsaya koina ba sai a Ζ™ofar kantin dogwayen rigunan nan.

“Guda goma.” yace da receptionist Ι—in dake wajen tun kafin ta gama gaishe shi, ta Ι—an tsaya kamar bata gane ba sai kuma ta fahimta tayi saurin fitowa daga wajenta, har tayi gaba kuma sai ta juyo tace.

“Kamar wani size yallabai?”

Madaki ya Ι—ago daga Ζ™oΖ™arin amsa wayar dake ringing a hannunsa ya kalle ta. Fuskarsa ta nuna alamun bai fahimce ta ba, sai ta sake yin murmushi sannan tace.

“Size Ι—in rigunan, kamar yaya yallabai?”

“Suna da size ne?” ya tambaya.

“Tana da tsawo wadda zata saka?”

Sai yanzu ya fahimci me tace, idonsa ya hango sanda Jidda ta tsaya a gefensa lokacin da zasu fito daga jirgin nan, saboda haka ya nuna mata Ζ™asan kafaΙ—arsa da hannunsa. Sai ta gyaΙ—a kai tana murmushi kafin ta juya.

Gudan goman kuwa ta zabo, Ι—aya daga cikin ma’aikatan da ya riΖ™o mata ya zube su akan kantar data raba tsakanin wajenta da inda ya tsaya, wayar yake yi har a lokacin kuma da alamun wani abu mai muhimmanci yake saurare, don kallo Ι—aya yayi wa kayan ya mata alama da yatsansa Ι—aya cewar ta saka su a leda, sannan ya miΖ™o mata credit card Ι—in dake riΖ™e a hannunsa.

Ana hada kayan ne kuma idonsa ya kai kan turarukan dake jere a cikin wani glass dake gefensu, sai ya tuno wannan Ι—an guntun turaren da ya gani a hannunta da safe, da alama tana son Ζ™amshi tunda har ta iya kasa barin turaren nan ta taho dashi, daboda haka ba tare da wani tunani ba ya sake yiwa receptioninst din alama data Ι—ebo guda biyar Ι—in dake saman glass Ι—in ta haΙ—a a cikin kayan.

“Malam Saminu gida zaka kai mun waΙ—annan kayan.”

Ya faΙ—a a lokacin da ya dawo harabar cikin kamfaninsa, Malam Saminun wanda yake direba a kamfanin ya durkusa cikin ladabi ya karbi Ζ™atuwar ledar da yake miΖ™o masa sannan yace.

“A buΙ—e gidan yake kenan yallabai?”

Yayi tambayar ne sanin cewa shi kaΙ—ai ya sani a gidan kuma in har yana nan to gidan a kulle yake don babu ko maigadi.

“A’a, akwai mutum a ciki, idan ka shiga gate Ι—in kayi knocking zata buΙ—e maka.”

“Toh yallabai an gama.” cewar Malam Saminun ba tare da ya bayyana mamakin daya Ι—arsu a ransa ba, sai dai kuma yana juyawa ya sake tsayar dashi, ya koma ya buΙ—e Ζ™ofar motarsa ya yago wata ‘yar jotter sannan ya Ι—ora ta a saman motar, ya rubuta wani abu cikin handwriting Ι—insa mai kama da signature sannan ya juyo ya bude ledar hannunsa ya saka a ciki ya masa alama da yaje.

Idanun Madaki suka bi Malam Saminun da kallo a lokacin da ya nufi inda zai Ι—auki mota ya fita, babu gaira ba dalili sai tunaninsa ya hasko masa fuskar Jidda ranar daya fara ganinta a Kiyari, ranar data juyo daga gaban wannan saurayin tana kallonsa d’auke da murmushin da ba nasa ba…

Wani abu ya yamutse a cikin ransa.

ZANEN DUTSE CHAPTER 4 BY AISHA-SHAFIEE

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

??????.

Jidda ta karanta rubutun dake jikin ‘yar Ζ™aramar takardar a karo na biyu sannan ta sake kai idonta kan kayan, ai bata yi zaton yana da sauran burbushin imani irin wannan game da ita ba, tayi zaton tunda ba zai sake ta ba zai azabtar da ita da yunwa ne ko wani abun yadda in bata mutu ba watarana da kanta zata gaji ta gudu.+

Ƙamshin abincin dake cikin ledojin nan ya bugi hancinta, babu shiri ta bude leda ta farko dake gabanta, wata irin jollof Ι—in shinkafa ce data sha vegies kala-kala da kuma hanta a ciki, yawu ya taru a bakinta saboda Ζ™amshin da take yi, a Ι—ayar ledar akwai wani kwanson dake Ι—auke da haΙ—in salad dana snacks da kuma wani cike da pepper chicken mai kyau a ido, sai ta tabe

bakinta kadan tana Ζ™arewa abincin kallo tare da jinjina kai, ko a Guest Inn din nan ba irin wannan abincin ake kawo mata ba, balle a kuma a koma Kiyari tsakaninta da irin wannan ai sai ana hidima a masarautar ko kuma Sadiya ta samo musu ragowar abincin wani b’angare na matan Sarkin,  ammayau gashi a b’agas wai shine abincin ranarta.

Sai ta maida su ta rufe sannan ta cigaba da kallon dogwayen rigunan dake gabanta da kuma kwalayen turaren nan, har yanzu ta kasa yarda wai nata ne gabaΙ—aya, wai ita zata saka, gani take kamar kasuwa ta raka Jamila suka tsaya a wani shago don suyi kallo kawai. Ta Ι—auki wata pitch colour mai adon baki ta Ι—aga ta, tayi mata kyau gaskiya, kamar ace ne mutum ne ya riΖ™a kallon abinda ba nasa ba, sai ta maida ita itama ta ajiye sannan ta cigaba da Ζ™are musu kallo.1

Tun bayan ganinta da file Ι—in nan bata san me ya dace ta riΖ™e a matsayi tunani ba, ta san dai duk wani Ζ™udirin data Ι—auka a baya game da Madakin ya narke a zuciyarta yabi iska, don tabbas ta yarda cewar Allah bai zagayo da rayuwarta gare shi a banza ba, ance Ζ™addara tana da siffofi mabanbanta, to ta yarda wannan itace tata kuma babu ta yadda za’ayi ta iya canja ta, wataΖ™ila shi yasa tun farkon al’amarin nan kowa ya kasa tabuka wani abu a cikinsa.1

Aure abu ne mai girma, kuma ko a wace irin siffa yazo abu ne nai daraja da karamci, don haka ta yaya zan iya zuwa in dakatar da Mai martaba Hauwa’u? Me na taka? Wace hujja muke da ita da tafi waΙ—annan?

Maganar da Baddo ta gaya mata a safiyar Juma’ar nan lokacin da ta tsugunna cikin kuka tana roΖ™onta da taje ta baiwa Mai martaba haΖ™uri ta haska a cikin kanta, a lokacin gani take yi kamar Ζ™arshen rayuwarta ne yazo amma saboda nauyin waΙ—annan abubuwa guda biyun haka tana ji tana gani aka canja rayuwarta. WataΖ™ila shima Madakin abinda ya hana shi sakinta kenan kai tsaye, saboda nauyin Mai martaba da kuma nauyin Ζ™addarar da ba mai iya canjata.

Sai ita karan kaΙ—a miya da take ganin zata taka rawar da kowa ya kasa gwadawa hatta Fulanin da take zargi kuwa tunda har yanzu bata ji wani motsi daga gare ta ba, ta cigaba da kallon kayan tana tunanin Allah yasa yadda idonta ke ganinsu haka suke babu wata kutunguilar ko wani kamashon da zai biyo baya.

Ta sake kallon Ζ΄ar paper nan daya rubuto sunansa.

??????…

Yana son sunan da alama, amma ita gani take Ibrahim yafi Ι—aΙ—i, yafi dacewa dashi ma, don inda ace zai kalli mutum da waΙ—annan oily eyes Ι—in nasa sannan fatar lebbensa ta furta sunan shi kaΙ—ai, Ibrahim… Babu abinda zai hana ka rantsewa cewa duk duniya babu wanda ya dace da sunansa sama dashi.

Ita kanta ta sani cewa Madaki irin mazan nan ne da mace zata shafe rabin rayuwarta kafin kafin taga giftawar irinsa a titi, ba wai don kyawunsa ba sai don Ζ™ima da kwarjininsa, irin kwarjinin da ko bai raΙ“i gidan sarauta ba dole ne ya karΙ“i respect daga hannun kowanne irin mutum a duniya. Shi yasa bata sa kanta a wahala ba tun farko, ta yankewa zuciyarta cewa zai sake ta ne da zarar an Ι—aura masa ita don shi da ita ba sa’annin juna bane, kamar ka shiga wani haΙ—aΙ—Ι—en kanti ne ka siyo ice cream mai daΙ—i da garΙ—i cikin flavors kala-kala sannan ka fito waje ka siya wannan Ι—an naira biyar Ι—in mai biscuit da dattijai ke turawa a keke.

STORY CONTINUES BELOW

Yana da komai, bata da komai. Yana da Ι—imbin gata kotawanne b’angare, inda take da gata baifi cikin yatsu ba. Ya taso cikin daula da wadata, ta taso a gidan da sai mahaifiyarta tayi aikatau kafin su iya kashe Ι—awainiyar gabansu. Yana da tarin ilimin da ko b’urb’ushinsa ita bata sani ba. Yana da kwarjini da Ζ™ima ita kuwa Ζ΄ar ficila da ita sannan ma babu wanda ya taba kiranta da kyakkyawa a duniya sai dai idan tayi kwalliya kawai a yaba, don haka duk da bata san taΖ™aimaimai dalilin da yasa Mai martaba ya haΙ—a aurensu a wannan lokacin ba amma dai ta san koma meye an aura masa ita ne a matsayin ‘Horo’ saboda wani abu da ake ganin yayi ba daidai ba.

Ta tuno idon Jamila a lokacin da suka ji sunansa ranar juma’ar nan bayan ta gama gaya musu cewa Mai martaba zai Ι—aura mata aure da wanda bata sani ba, rufe bakinta tayi a lokacin da duka hannayenta sannan tace ‘Madaki? Madakin da na sani dai Baddo?’

Kuma wannan kallon dake cikin idonta mamaki ne Ζ™arara don tayi imanin da farko dukkaninsu sunyi zaton ko wani mai gadi ne ko mai shara daga cikin ma’aikatan masarautar, amma tun daga lokacin da suka ji sunan ta lura hankalinsu ya Ι—an kwanta akan da farko, bama irin dangin Baddo da suka zo da tsananin murnarsu suna yi mata barka wai ta shiga Babban gida, haka ta dinga binsu da kallon mahaukata don tana tunanin sakinta zaiyi a ranar.

Tunaninta ya dawo zuwa lokacin da ya Ι—auko ta, a cikin motar nan data fara Ι—aura makaman yaΖ™inta akansa, da kuma zamanta a Guest Inn Ι—in data rantse sai ta Ι—anΙ—ana masa kuΙ—arsa, haka duka ya faru ne saboda fushin daya tunzura zuciyarta take ganin cewa an cuce ta, amma a yanzu komai ya ruguje saboda wannan file Ι—in kawai, ta nemi fushin da take akansa ta rasa, sai ma wani abu kamar tausayi da tunanin irin wahalar ciwon da yake ji kamar yadda ta san mamanta tayi fama.

Taja tsaki kaΙ—an, matsalarta kenan ‘Tausayi’, don akwai sanda aka taba bata riΖ™on wani aji Ζ΄an yara a islamiyya, wata daga cikin yaran ta mata rashin kunya, ai kuwa ta aro bulala ta zane ta tas saboda bacin rai, a ranar da taje kwanciya sai yarinyar ta dinga mata gizo a ido sanda take kuka tana bata hakuri, har taje makarantar boko washegari bata wani samu sukuni ba don haka kuΙ—in break Ι—inta ta tattara ta siyo su alawa da biscuit ta kawo wa yarinyar nan harda bata haΖ™uri a fakaice, sannan hankalinta ya kwanta da taga ta maye kukanta da murmushi.1

Da ace baki da tausayi a ranki Jidda wallahi tsaf zaki iya zama matar Ι—an fashi, ku yi ta cin zalin al’umma kuna jin daΙ—i.2

Abinda Jamila ta tab’a faΙ—a mata kenan watarana, ta tuno yadda ta haΙ—e rai a lokacin tana turo baki tare da faΙ—in ‘Allah ya kiyaye ita ta auri wani ba Suraj ba, balle kuma Ι—an fashi.’1

Sai tunaninta kuma ya zarme zuwa kansa, yana ina yanzu? Yaji aurenta? Allah yasa ma ya jin don ya Ζ™unshi baΖ™in ciki ko yaya ne kafin ta dawo ta Ζ™unsa masa na ramuwarta, ai ta rantse kowa yaci tuwo da ita to miya yasha. Don Madaki yaci albarkacin ciwonsa a wajenta, shi bai isa ya fanshe kansa da komai ba.1

Kewar Sadiya ta Ι—an kamata, da ita ya kamata ace tana wannan sirrin bada zuciyarta kaΙ—ai ba, Allah ya sani ko su Baddon bata kewa kamar yadda take kewarta don itace kullum suke tare, su da garin Allah ya waye sun tafi harkokinsu cikin gida ba zata Ζ™ara ganinsu ba sai in ta neme su ko yamma tayi, sau da yawa ita kaΙ—ai take dafa abincinta ma da rana taci, don su sai yammar da zasu taho suke dawowa da abincin dare. Shi yasa duk wani shige da ficenta tare da Sadiya ne musamman data raba ta da Ζ΄an group Ι—insu, da ace zata zo su zauna tare, ai sai a shekara ma bata yi tunanin gida ba.

Sai ta miΖ™e da ledar rigunan ta koma Ι—akin da take kwana a cikinsa, ta fito dasu ta jera tsaf cikin wadrobe sannan ta ware wata ash da taga kamar tsawon ta zaifi mata zama daidai, ta shiga toilet tayi wankan ta sosai sannan ta fito ta shirya a cikinta, zuciyarta na gaya mata cewar tunda har zai iya siyo mata kaya to zai iya siyo mata sauran kayan buΖ™atunta kenan, don ba riguna kaΙ—ai take so ba akwai wasu Ζ΄an tarkacen da rayuwar ba zata tafi ba in babu su, ko ba komai ma ai mijinta ne shi don haka tana da haΖ™Ζ™in sutura akansa.1

STORY CONTINUES BELOW

Ta faΙ—i hakan kuma ta yiwa kanta murmushi, wai mijinta? Ta hango yadda zasu durΖ™usa har Ζ™asa don dariya ita da Sadiya da ace a watannin baya wani zai tare ta ya nuna mata shi yace shine mijin da zata aura. Ta taΙ“a faΙ—awa Sadiya cewa maza irinsa masu kyau da aji kyawawan mata suke aura, farare ko kuma Ζ΄an gidan wasu shahararrun masu kuΙ—in, ba irinta normal mutanen cikin gari ba da babu wani Ζ™waΖ™Ζ™waran abu da za’a danganta shi dasu a kallo Ι—aya.

Tunaninta ya katse sanda ta juyo gaban mudubi tana Ζ™oΖ™arin Ι—aure jelar rigar, bata yi tunanin rigar zata mata kyau irin haka ba, don ta zauna a jikinta sosai, ta juya ta sake juyawa, ina ma zata iya aikawa su Jamila da guda Ι—ai-Ι—ai, taga abinda yaci ub*n lace Ι—inta.1

Ta dauki daya daga cikin turarukan nan ya fesa a jikinta, Ζ™amshinsa ya dauke ta zuwa wata duniyar dake gasgata mata cewar rayuwarta ta canja zuwa wani babin daban, gashinta dama a Ι—aure yake cikin Ζ΄ar doguwar jelar da bata wuce kamu biyu don haka ba tare da ta Ι—aura Ι—ankwalin rigar ba ta koma falo. Ta Ι—auki ledojin abincin nan tayi kitchen, ta dora su akan wannan island table Ι—in da take mutuΖ™ar so sannan ta bude wata cupboard ta Ι—auko plate ta sake Ι—auraye shi ta dawo ta zauna, har ta buΙ—e abincin kuma wani tunani ya Ι—arsu a ranta, ko makaho ya shafa zai san cewa abincin nan ya mata yawa, don haka tunda yar da makaman yaΖ™inta me zai hana ta rage masa tunda ko yaci abinci dai ai daga wajen aiki zai dawo dole zai nemi wani abun, kuma ita har yanzu bai zana mata wasu sharaΙ—ai ba balle ta san yaya tsarin zamanta a gidan zai kasance.1

Don haka ta mike ta nufi Ζ™ofar store Ι—in data gano Ι—azu a gyare-gyarenta, a cikin tarkacen wasu Ζ΄an kwalaye taga wani food flask mai kyau Ι—an karami, ta Ι—auko shi ta wanke sannan ta raba abincin nan biyu ta zuba a ciki,har da naman da sbacks Ι—in, salad Ι—in ne kaΙ—ai ta bari a Ζ΄ar robarsa ta tura gefe. Babu wani cokali tasa hannu ta fara cin abincinta, idanunta suka lumshe don daΙ—i, ai ko ma’aikatan masarauta basu iya irin wannan girkin ba, barshi dai a na biki idan an bada oda wa masu girkin na musamman.. Ita kaΙ—ai tana ci tana santi a cikin ranta don ko abincin Guset Inn Ι—in nan bai kai wannan ba.

Tunani take ba zata iya cin irin wannan abincin kullum ba don daΙ—in sai yayi yawa, gani take ma ai sai Allah ya kamata tunda mutane nawa ta sani da basa samun abinda zasu ci, ko a masarauta sai ta Ζ™irga Ι—akin da ba’a kullum suke cin abinci sau biyu a rana ba. Ta cigaba da yagar naman tana taunewa har Ζ™ashinsa, da farko tana ganin kamar wanda ta zuba ma ya mata yawa sai gashi ta cinye shi tas! (kuma dai.)2

Ta tattara Ζ™ashin ta zuba a shara sannan ta wanke plate Ι—in, kamar ta koma Ι—aki amma azabar son island Ι—in nan ya hana ta, sai ta dawo kawai tayi zamanta sannan ta Ι—ora kanta akansa, sanyin glass Ι—in na ratsawa cikin fatar ta, da yatsanta dake da danshi ta shiga zanen Ζ΄an smileys akai iska na gogewa, a haka sai wani bacci mai daΙ—i ya Ι—auke ta cikin Ζ™anΖ™anin lokaci, tunda dama jiya bata samu isashshen baccin ba sannan gashi yanzu taci ta Ζ™oshi.

Can cikin baccin nata taji wani abu kamar kamar ana taΙ“a gashinta.

***

Canjin da Ibrajim Madaki ya fara gani a lokacin da ya shiga cikin falonsa shine bayan sharar da aka yi komai tsaf yake, Ζ΄an tarkacen kayansa daya bari akan kujera an jera su gefe guda tsaf cikin tsari, idonsa ya kai hanyar dining table, takardunsa gabadaya babu su sai wasu kwalaye dake gefe a Ζ™asa an jera su Ι—aya bayan Ι—aya. Idonsa ya Ζ™arewa falon kallo, rabonsa da ya ganshi haka an daΙ—e duk da cewar duk sati akwai yaron da yake zuwa daga office yayi masa shara, amma baya tab’a masa komai, zaiyi sharar ne kawai yayi tafiyarsa.

A lokacin ne kuma tunaninsa ya gaya masa cewar ya dace yayi sallama aΖ™alla, tunda ko ba komai musulma ya ajiye a gidan, don haka yayi sallamar kuma ba tare da sa ran a amsa ba ya Ζ™arasa kan dining ya ajiye wayoyin hannunsa sannan ya nufi Ι—aki, kai tsaye toilet ya shiga yayi wanka sannan ya canja kayansa zuwa wasu Ζ™ananun kaya riga da wando farare tas, ya fesa turarensa na ‘Creme de Cacao’ sannan ya dauko Macbook Ι—insa ya dawo falon, ko’ina tsit yake har yanzu kuma bai damu da ya neme ta ba don ya rayawa kansa cewa ba zata wuce cikin Ι—akinta ba, saboda haka ya nufi wajen dining ya ajiye Macbook din sannan ya Ι—auki wayarsa da niyyar kiran Sunusi yaji idan a sama masa lokacin da zaiyi magana da Mai martaba, don tunda ya kashe wayar da yake amsa personal calls Ι—insa dole ne yabi layi a yanzu shima kamar kowa.

STORY CONTINUES BELOW

“Barka da warhaka ranka ya daΙ—e.”

Muryar Sunusin ta fito tar cikin wayar a lokacin da yaja kujera Ι—aya a jikin dining Ι—in ya zauna.

“Barkanmu dai Sunusi, yaya ake ciki?”

“Eh na samu ganin Jakadiyar, har ta bani lokaci ma wai gobe da Ζ™arfe huΙ—u na yamma.”

Gobe da Ζ™arfe huΙ—u. Ya maimaita hakan a ransa yana ayyano cewa dole ne ya dawo gida da wuri kenan, don office ba wajen waya da mahaifinsa bane.

“Nace ranka ya dade me zai hana baza ka zo ba kawai, don ina ganin hakan zai fi saukin al’amura.”

Ya Ι—an juya maganar Sunusin a ransa, kamar ya Ι—auki hakan kuma sai ya fasa don yafi kowa sanin cewa idan har Mahaifinsa yayi fushi to hanya ta farko da zaka kare kanka daga sake rincabewar al’amura shine kayi nesa dashi har sai ya huce, aduk wanda ya sanshi ya riga ya kwana da sanin hakan, sai dai a yanzu zuciyarsa ta kasa daurewa zuwan wannan lokacin ne shi yasa ne shi yasa zai gwada samunsa a wayar ko zai iya tantance girman laifin nasa.

“Allah ya kaimu goben kawai Sunusi, I’ll make sure I’m free.”

“To shikenan yallabai a huta lafiya, nagode sosai.”

Ya katse kiran sannan ya jawo Macbook Ι—in ya shiga scanning messages Ι—in da suka shigo email Ι—insa, wanda kowanne a cikinsu yana magana ne akan wani abu dake bukatar lokaci da dogon nazari, don haka saya koma da baya ya tallafo Ζ™eyarsa cikin tafin hannunsa, in ma yace zai je Kiyari a halin yanzu to abubuwa goma ne zasu lalace ba Ι—aya ba. idonsa yabi kan teburin da kallo, gyara ko yaya yake sai waje ya canja a idanunka, kullum teburin cike yake da takardu ya manta yaushe da ya zauna haka ma balle har ya ajiye labtop Ι—insa..

Sai ya lumshe idanun nasa yana kallon bangon dake fuskantarsa, har yanzu ya rasa yadda zaiyi overcoming sabuwar matsalar da yake fuskanta ta yawan tunanin yarinyar nan, babu wata matsala da ya taba fuskanta a rayuwarsa mai cin rai irin wannan saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa fassara kwakkwaran abu game da ita, magananun da ta fada masa a Guest Inn Ι—in nan ya san tayi su ne cikin fushi don ba ita ba ko waye zai iya yin hakan a lokacin da aka Ζ™ulle ka a Ι—aki tsawon kwanaki huΙ—u. Saboda haka wani bangaren na zuciyarsa na masa hasashen cewa abinda yake hangowa a idanunta gaskiya ne, she’s innocent bata da laifin komai Ζ™oΖ™arin kare kanta kawai take yi, don haka a yanzu ma da yazo ya tadda gidansa tsaf sai ya kasa tserewa wannan tunanin, amma kamar kullum kuma Ι—aya barin zuciyar tasa gaya masa yake cewa babu wani abu da ba zai iya zama cikin tsarinsu ba.

A Ζ™oΖ™arin ture wannan tunanin ya sake jawo labtop Ι—in da niyyar fara amsa sakonnin dake jiransa, sai kuma yaji cikinsa ya Ι—an murΙ—a alamun yana son yaci wani abun, don haka ya ajiye ta sannan ya mike da niyyar zuwa kitchen ya hada tea kamar yadda ya saba.

Kai tsaye ya nufi hanyar corridon da zata kaishi ga kitchen ya murΙ—a Ζ™ofar ya buΙ—e, kuma a lokaci guda idanunsa suka ci karo da abinda baiyi tsammani ba, Jidda ce kwance akan island Ι—in kitchen Ι—in tana baccinta tsakani da Allah don babu alamun taji buΙ—ewar Ζ™ofar ma. Me ya sami yarinyar nan ne? Bata san da Ι—aki a gidan bane har yanzu? Don me zata yi bacci a kitchen? Girki tayi ko me? Sai Idonsa ya kai kan flask Ι—in dake gefenta da kuma robar salad Ι—in nan, ko dai abincin da ya kawo mata ne bata ci ba? Sai kuma yaji wani abu ya ratsa zuciyarsa daban, kamar nutsuwa, irin nutsuwar da namiji ke samu a lokacin daya dawo gida ya iske matar da ya ajiye cikin kyakkyawan hali.

Ya maida Ζ™ofar ya rufe sannan ya Ζ™arasa ciki, Ζ™afafunsa da babu ko takalmi na taka sassanyan marbles din wajen cikin nutsuwa, ya tsaya daidai gabanta kuma babu alamun taji shi, idonsa ya shiga scanning kayan jikinta a lokacin da wani cool Ζ™amshi da ba irin na asubahin jiya ba ya ratsa hancinsa, ya kalli hannunta da yayi nesa da jikinta, ta fidda yatsanta Ι—aya kamar tana zana wani abu ne akan glass Ι—in, har yanzu bai ga dalilin da zai sa mutum ya kwanta anan ba har kuma bacci ya Ι—auke shi, wuyanta kamar ya Ζ™age amma ita bata damu ba. Sannan duk da idanunta a rufe suke, wannan innocence Ι—in da yake gani akan fuskarta ya fito tar! A haka babu wanda zai ce zata iya buΙ—e baki tayi rashin kunya ma balle abinda yake zargin an aiko ta don shi.

STORY CONTINUES BELOW

Iyayenta duka sun mutu ranka ya daΙ—e, a hannun kakarta take anan…

Maganar baiwar nan ta dawo cikin kansa.

RiΖ™on maraya sai Allah Madaki, Ι—an da baka haifa ba tarbiyarsa da wuya ba kowa ke iyawa ba.

Ya tuno maganar da Hajja ta tab’a faΙ—a masa wani lokaci, sai kwakwalwarsa ta shiga wani nazari daban, da ace a hannun iyayenta ta tashi da wataΖ™ila bata sami kanta anan ba, da wataΖ™ila ta tashi cikin isashshiyar kulawar da ko auren aka yi mata a yanzu, tana tare da wanda take so ne cikin ingantacciyar rayuwa.

Sai kawai ya juya jikin drawer da yake ajiye kayan tea Ι—insa ya buΙ—e ta, ya fiddo komai sannan ya shiga Ζ™oΖ™arin hadawa a cikin wata Ζ΄ar kettle dake jone a jikin socket Ι—inta.

Ya juyo don Ι—auko robar rowa dake can gefe sai idonsa ya kai kan gashinta, sai yanzu ya lura ashe babu Ι—ankwali a kanta, gashin nan daya gani a hoto na Ι—aure cikin jela guda, ya Ι—auke idonsa yaje ya Ι—auko ruwan amma idon nasa ya sake komawa, ya riga ya sani cewa babban abinda ke burge shi a jikin mata gashinsu ne, ko sanda Habibu ya dage da masa zancen Ζ™anwarsa, bai maida hankali akanta sosai ba sai ranar daya fahimci cewa tana da gashi tunda ita mace ce da bata fiye son Ι—aura Ι—ankwali ba, don haka zai iya cewa a lokacin da ta canja ra’ayinta akansa ta auri wani tsohon Ι—an siyasa, abinda yayi kewa daga gare ta kenan.1

Ya tsaya a bayanta riΖ™e da robar ruwan yana Ζ™ara kallon gashin, bai san sanda hannunsa ya kai kan jelar ba ya murza shi tsakanin yatsunsa, bayan ranar daya riΖ™e ta a Guest Inn Ι—in nan, ba zai iya cewa akwai ranar da hannunsa ya tab’a riΖ™e gashin wata mace ba sai akanta, ita Ι—in dake amsa sunan matarsa, wani abu ya shiga juya kwakwalwarsa kamar sanda yake riΖ™e da itan nan…

A cikin baccinta Jidda tayi yunΖ™urin gyara kwanciyarta sai taji kamar ana taΙ“a gashinta daga baya, don haka ta buΙ—e idanunta a hankali tana son wartsakewa, a sannan ne kuma ta tuna inda take saboda haka tayi saurin Ι—agowa ta mike zaune tana fatan ba daΙ—ewa tayi tana baccin ba, sai dai idonta kuwa yayi kyakkyawan gani sanda ta juya, Madaki tsaye daga can jikin drawers Ι—in riΖ™e da wata Ζ΄ar karamar kettle yana zuba ruwa a ciki… Hakan ya tabbatar mata cewar ta daΙ—e kenan don ga gari nan ma yayi duhu ta tagar dake wajen sink.

Ta san ya ganta amma Ζ™arar miΖ™ewarta bai sa ya juyo ba balle ya kalle ta, tayi kamar tayi ficewarta kuma sai taga bai dace ba saboda haka ta tsaya daga jikin Island din yatsunta cakuΙ—e cikin juna tace.

“Sannu da zuwa.”1

Babu zato kalaman suka daki tunanin Madaki, wanda ke hamdala a zuciyarsa da bai bari ta ganshi a kusa da ita ba, shi take yiwa Sannu da zuwa? Dama da wannan hankalin tattare da ita? A yadda take fiffike masa ai ya zata babu wannan alherin tsakaninsu, kamar ya juyo ya kalle ta sai kuma ya fasa, don bai tabbatar da halin da idanunsa ke ciki ba.

“Yawwa.” amsar ta fito kai tsaye ba tare da ya juyo Ι—in ba.

Hakan yasa Jidda ta Ι—an ji Ζ™arfin gwiwar sake magana saboda haka tace.

“Ga abincinka nan a wannan flask Ι—in.”

“Girki kika yi?” ya sake tambaya yana cigaba da abinda yake yi.

Ta girgiza kai kamar yana kallonta.

“Abincin daka aiko dashi ne na rage maka.”

Maganar ta tsaida tunaninsa na wucewar sakan Ι—aya, don ji yayi kamar tana Ι—auke da wani abu ne da ya zama babban gib’i a rayuwarsa… ‘Kulawa’, amma sai yayi saurin girgiza kansa sannan yace.

“Bana cin abinci mai nauyi da dare, so ki Ι—auki abinki.”

Ta Ι—an tsaya kamar bata so hakan ba sai kuma ta jawo flask Ι—in da ‘yar robar salad Ι—in ta buΙ—e fridge ta saka, sannan tayi hanyar fita don yin sallar magribar data tabbatar an idar da ita, sai da ta buΙ—e Ζ™ofar kuma sannan ta tuna wani abu don haka ta sake juyowa.

STORY CONTINUES BELOW

“Nagode da kayan daka aiko Ι—azu, Allah ya Ζ™ara buΙ—i.” Ta jawo masa Ζ™ofar ta rufe.

Madaki ya tsaida idanunsa kan Ζ΄ar coffe-maker dake gabansa yayin da kalmar godiyar ta shiga amsa amo a kansa, zai iya rantsewa a rayuwarsa tsakaninsa da wannan kalmar sai a bakin mutanen da yake wa sadaka ko kyauta, ko kuma ya ganta a rubuce idan an kawo masa takarda daga gidajen marayun da yake yawan tallafawa, bai taba samun wani makunsancin da zai gode masa akan komai ba.

Dole ne ya fara Ζ™oΖ™arin kawo Ζ™arshen al’amarin nan.

***

Washegari da Asuba.

05:30Am.

Jidda ta idar daga sallah amma bata miΖ™e daga kan Ι—an Ζ™aramin carpet Ι—in da ya zame mata sallaya ba, ta jingina kanta da karshen gadon tana salati a cikin Ζ΄an yatsun hannunta, tun jiya data shigo Ι—akin tayi sallar magriba bata kara fita ba, fito da kayanta tayi ta shiga gwada kowacce a cikinsu sannan ta sake ninke su ta jera a wardrobe din, tayi sallar isha’i sannan ta kwanta, dama ta saba baccinta da wuri saboda a Kiyari kusan kullum da sassafe suke zuwa Ι—ebo ruwa don haka tana dawowa daga makarantar dare Ζ™arfe takwas Ζ΄ar hirar kaΙ—an akeyi da ita zata yi baccinta, sai Jamila ta musu shimfida sannan zata tashe ta daga inda take. Saboda haka anan da babu makarantar daren kuma babu zuwa Ι—ebo ruwan ji take kamar ta fara gajiya da rashin abinyi, kewar gida ce ke son kamata duk yadda taso ga turewa.

Babu zato taji wata Ζ™ara kamar ana kwankwasa Ζ™ofar Ι—akin saboda haka tayi saurin Ι—agowa ta kalli wajen, duk da ta san wa ke da hurumin yin hakan tunda su biyu ne a gidan, amma sai da ta Ι—an ji wani iri haΙ—e da mamakin me zai kawo shi wajenta a yanzu, me zai ce mata da sassafen nan? Kuma kafin ta buΙ—e baki tayi magana aka murdo Ζ™ofar aka bude.

Yana tsaye da saΙ“anin kayan da ta ganshi jiya, don a maimakon farare yanzu yadi ne brown a jikinsa mai sealed aiki da rigar da bata wuce gwiwa ba, a lokaci guda ta fahimci masallaci yaje shi yasa ya canja waΙ—ancan kayan, a hannunsa kuma wani kofi da bata san meye a ciki ba.

“Kin idar?” muryarsa ta tambaya freely yana kallonta, sautin muryar tasa a kwance ya fito, cikin yanayin da ya Ζ™ara tuna mata cewa da gaske gari bai gama wayewa ba.

Sai ta Ι—aga masa kai sanda idonta ya hango ramar da ya Ζ™ara a cikin Ζ΄an kwanakin data sanshi zuwa yanzu, don hatta idanunsa sun zurma ciki Ζ™aΙ—an suna Ζ™ara fitar da sheΖ™in maiΖ™onsu, wai baya shan magani ne ko me?

Kai tsaye ya shigo ciki ya rufe Ζ™ofar sannan ya Ζ™araso inda take, ta shaΖ™i sabuwar iskar Ι—akin data gauraye da Ζ™amshinsa tun kafin ya zauna kan bedside drawer dake gabanta, sai taji ta Ι—an takura kaΙ—an saboda tsawo da girman jikinsa a kusa da ita, dama haka mata suke ji idan an kaisu gidan da daga su sai wani namiji daban? Ba kallonsa take ba amma taji alamun ya kurbi abinda dake cikin kofin hannunsa sannan yayi gyaran murya kaΙ—an.

“Baki iya gaisuwa bane?”

Ya cika garaje ne? Idan yayi shiru ai zata gaishe shi, ita fa ba’a cika mata dole ba saboda haka cikin son tura haushi idonta na kallon Ι—aya barin Ι—akin tace.

“Barka da Asuba ranka ya daΙ—e.”

Bai amsa ba kamar yadda ta zata, don ta sani dama basu yi nisan da giyar mulkin sarautar gidansu zata sake shi ba. Sai da ya shaΖ™i iska daidai gwargwadon muradinsa sannan ya sake magana kai tsaye.

“Ina son muyi magana ne akan wannan al’amarin daya haΙ—a mu don babu zaman da ke yiwuwa babu tsari.”

Zama? Jidda ta yiwa kanta tambayar a lokaci guda, ita fa har yanzu bata tunanin wani dogon zama tare dashi don ba son inda za’a wulakanta ta take ba, shi yasa bayan ta zubar da makaman yaΖ™inta gani take kamar a yanzu zata yi jiran wani sanadi ne da zai kawo Ζ™arshen komai ta koma inda ta fito, don haka tunaninta ya gaya mata cewar in har wani abu zai tambayeta to kawai ta gaya masa gaskiyar abinda ta sani in yaso idan yaga bata da laifi a ciki sai ta roΖ™e shi ya sallameta.

STORY CONTINUES BELOW

Tayi niyyar sake kallonsa amma jikinta ya bata kamar idonsa akanta yake saboda haka ta cigaba da kallon carpet Ι—in dake gabanta inda zara-zaran yatsun Ζ™afarsa suka so shigowa cikin hoton, dogwaye ne amma sai taga kamar sun kumbura kaΙ—an. Sai kuma ta haΙ—iye yawu don bata san ta inda zai fara ba, abinda ya haΙ—a su ai da yawa, tun daga lokacin da ta kai kanta Ι—akinsa a kiyari…

“Me ya kaiki masaukina a Kiyari?”

Ta yiwa Ζ™waΖ™walwarta jinjina kafin ta gyara zamanta, yatsun hannunta cakuΙ—e cikin juna tace.

“Naje neman abuna ne da nake zaton ya faΙ—i, nayi ta sallama ba’a amsa ba, kuma na duba ban ganshi ba har cikin jakunkunanka, sai nazo zan fita naga Ζ™ofar ta kulle, nayi-nayi na buΙ—e na kasa shi yasa na zauna a bayan labulen nan da niyyar idan an bude Ζ™ofar da safe sai na fita.”

Bayanin ya sarΖ™e tunanin Madaki dake zaune yana kallonta rike da kofin nan, bai taba tunanin zata bashi amsa haka kai tsaye ba, a tunaninsa rashin gaskiyarta zai sa tambayar ta shammace ta, amma yadda take koro bayanin haka kai tsaye ya bashi mamaki, anya gaskiyane? Ba shirya mata hakan akayi ba? Ya murza kofin hannunsa yana sake nazarin abinda tace, wato har cikin jakarsa ta buΙ—a kuma take faΙ—a masa hakan kai tsaye.

“Ta yaya abunki ya fadi a wajena? Sannan meye shi?”

Inda za’a Ι—an sami matsala kenan, don dai har yanzu bata tabbatar dashi ta buge ba a daren ba, wannan tsohon ne kawai ya gaya mata cikin hasashensa, amma bata da wani abun da zata faΙ—a bayan hakan don ita bata iya nuku-nuku da zance a ranta ba.

“Na buge wani mutumi ne da daddare sai na yarda shi a wajen, washegari da naje dubawa wani tsoho ya kwatanta min inda kake shine naje da tunanin dubawa ko ka haΙ—a shi cikin kayanka.”

Babu wani kwana-kwana, tunanin Madaki ya hango masa ita a ranar data buge shi bayan ya baro wajen Saifudden, da sanda ya ganta a bayan labulen nan… Wata zuciyar ta shiga tunanin kamar gaskiya take faΙ—a amma Ι—aya barin zuciyar tasa ya kore wannan tunanin, Kar ka fada cikin tarkonsu tun yanzu, me zai gagari Fulani a wannan al’amarin? Sun riga sun tsara komai tun farko.

Sai ya ajiye kofin hannunsa a gefe sannan ya sake fuskantarta sosai.

“Jinin me na gani a jikinki a wannan ranar?”

Tambayar tasa ta dago ta kalle shi sai kuma ta kawar da kanta, idonsa ya tsaya akan Ζ΄an curls Ι—in gashin kanta daya fara fitowa ta gaban mayafinta dake zamewa.

“Nayi Ζ™oΖ™arin fita ne ta windon toilet dinka sai naji ciwo.”

Ya cije leΙ“Ι“ensa yana shirin watsar da tunanin cewa hakan zai iya yiwuwa.

“Ke kika buΙ—e Ζ™ofar da safe kenan?”

“Dana buΙ—e ai dana fita, ni ban san ta yaya ta buΙ—u ba, na dai ji an bude lokacin da nake Ζ™oΖ™arin fitowa, har nayi tunanin ma ko na ciki ne ya fita yin sallah.”

Duk yadda ta kai ga nuna nutsuwarta anzo wajen da zai kamata a tunaninsa, don yana tabbacin cewa shi ya bud’e masaukin a ranar kuma bayan ya shigo sai da ya tabbatar ya Ζ™ulle sannan ya maida muΖ™ullin ta ciki ya Ζ™ulle, sannan a jikin Ζ™ofar ya barshi ba tare da ya cire ba, don haka babu ta yadda za’ayi wani ya iya saka wani muΖ™ullin daga waje balle har a iya buΙ—ewa ta shigo kuma a rufe, sannan da safe kuma azo a sake buΙ—ewa.

“Abubuwa zasu fi mana sauΖ™i idan zaki fadi komai a yadda yake.”

Muryarsa ta fita cikin jaddada iko fiye da yadda ya nuna a baya, sai ta juyo ta kalle shi a karo na uku, mayafinta na zamewa, me yasa ne yake zamewa?

“Kana ganin Ζ™arya nake yi? Meye riba ta idan nayi Ζ™aryar?”

Yaso ya bata amsa da cewar ‘Adadin abinda Fulani ta zana mata’ amma ya cigaba da kallonta kawai, don a tsarin daya dauka ba zai taba nuna mata cewa yana zargin haΙ—in kanta da Fulani ba, zai bita ne a yadda al’amarin ya fara ta yadda a cikin maganganunta zai cimma Ζ™udirinsa, don haka ba zai lalata komai a yanzu ba, yana buΖ™atarta shi yasa ya bari ta shigo rayuwarsa, yana buΖ™atarta har zuwa lokacin da zai tarwatsa duk wani shirinsu. A yanzu zai fara aiki da iya abinda ta gaya masa kuma dukkan wani kuskure daya samu a cikin maganganunta zasu tashi akansa ne a gaba, yanzu aka fara tafiyar.

Sai kawai ya Ι—auki kofinsa sannan ba tare da ya sake kallonta ba ya nufi Ζ™ofa yayi ficiwersa.

Jidda ta nisa kwakwalwarta na nazarin abinda ya wakana, da gaske ne hasashenta na farko cewa zarginta yake game da wani abu da bata fahimta ba har yanzu, Ance wai wani abu kan ci darajar wani, yau har ita ake zargi Ζ™iri-Ζ™iri ba tare da ta dauki matakin komai ba, hannunta ya kai kan wuyanta inda take Ι—aura Fullo, me yasa ne ta yarda cewa wannan itace ‘Wata kaddarar’ da mahaifiyarta ke faΙ—a?

Kai tsaye Madaki ya fita wajen motarsa dake harabar gidan, ya Ι—ora kofin hannunsa a saman motar sannan ya buΙ—e Ζ™ofar baya ya shiga laluben wannan Ζ΄ar Ζ™aramar jakar tasa a cikin takardun dake zube, ba’a wani daΙ—e ba ya gano ta kuma nan da nan ya zazzage ta gabaΙ—aya abubuwan dake ciki suka tarwatse akan takardun, a cikin duhun asubahin da bai gama washewa ba kyallin abinda ba nasa ba ya haska a idonsa.

Yasa hannu ya Ι—ago da Fullo a hankali yana Ζ™are masa kallo, wani abu ya tsarga tun daga kansa har zuwa tafin Ζ™afarsa, me yasa ne yake tunanin maganganunta gaskiya ne?Gari ya waye, duhun asuba ya yaye, hasken alfijir ya keto ya ratso ta cikin labulayen Ι—akin da Fulani ke zaune. Kamar koyaushe, kuma kamar wata tafiya mai cike da kudiri bata faru ba, Jakadiya Babba ce durΖ™ushe a Ζ™asan kujerarta tayi goho irin na bawan dake jiran wani tsatstsauran umarni daga ubangidansa. A tun bayan dawowarsu garin wajen Ζ™arfe sha Ι—aya na daren jiya, sai a yanzu ta sami damar ganawa da Fulanin.+

Cikin tsananin ladabi da kissa, muryar Jakadiya Babba ta baiyana a Ι—akin.

“Zance ya riga ya fita ranki ya daΙ—e duk yadda muka kai ga karewa, sai daga baya nayi tunanin da ace munyi komai iya mu, da ace bamu Ι—ebi Ζ΄anuwanta mun tafi tare dasu ba, da watakila har mu kai ga nasara Mai martaba ba zai ji ba.”

Fulani ta shiga kaΙ—a Ζ΄an yatsun hannunta akan hannun kujerar da take zaune kafin ta cije gefen lebbenta na Ζ™asa.

“Wannan matsala ce data riga ta wuce Jakadiya, idan bamu Ι—auki Ζ΄an uwan yarinyar ba kina tunanin acan Madakin ba zai barmu mu isa gareta ne? Ki bar wannan zancen kawai mu fuskanci abinda ke gabanmu. Don wannan ba shine Ζ™arshe ba, Ζ™oΖ™ari na ba zai tafi a banza ba, dukkan rantsuwata ba zata bi iska ba sannan kuΙ—i na ba zasu salwanta ba jakadiya… Komai rintsi komai wuya wallahi sai naga ranar da Madaki zai zube gwiwoyinsa a gabana cikin Ζ™asΖ™anci kafin in Ζ™wace duk abinda yake taΖ™ama dashi.”

“Wannan tabbas ne Garkuwar al’umma, kece da nasara a kowanne fanni kuma da yardar ubangiji zaki wayi gari a ranar da duniya zata tozarta Madaki, duk wani wayo da dabarar mai dabara bai isa ya dakushe kaifin naki ba. Wannan abinda ya faru ba karaya bace, wani Ζ™warin gwiwar ne da zai kaimu ga ci insha Allah.”

“Bani labarin wannan kwarin gwiwar..”

Muryar Fulanin a tsaye Ζ™yam! ta sake wadata shirun Ι—akin, kuma ta faΙ—i hakan ne ba don Jakadiyar tayi wani tunani ba sai don ta zayyana mata sabuwar hanyar da zasu tunkara, ta riga ta sani cewa hakan wani abu ne da tuni ta tsara shi.

Jakadiya Babba ta gyara tsugunnonta kamar kullum, zuciyarta na gaya mata cewar dole ne ta tallafi ragowar damar da take da ita a wajen Fulani kota wace hanya tun kafin gazawarta yasa ta canjata da wata, ta daΙ—e tana cin zamaninta kuma har yanzu ba’azo gabar da duniya zata juya mata baya ba.

Saboda haka abinda ta faΙ—a a wannan lokacin Ζ™warai ya taka rawar bajinta wajen Ι—ago da darajar tata, zata iya rantsewa ma taga kyallin hakan Ζ™arara a idanun Fulanin kafin kuma ta gyada kanta a hankali sannan ta furta wata magana data zama sanadin rushewar komai!

Komai kuma yana nufin komai, don haka wasu Ζ™addarorin suke, jigon su mai nisa amma sanadinsu guntu.

“Hakan za’ayi Rakiya, je ki Ι—auko min jakar don ance da zafi-zafi akan daki dutse!”

Maganar ta fito daidai lokacin da a wani bangare na masarautar, a cikin Ι—akin Baddo, Jamila ke nufar jakar kayanta don Ι—aukan hijabi tayi makararriyar sallar da gajiyar mota ta jawo mata.

**

LAGOS.

“Ina jinka Sunusi.”

Muryar Madaki ta faΙ—a a lokacin da yake kallon screen Ι—in Macbook Ι—in dake gabansa. Video call yake yi tare da Sunusi, wanda ya nema tun a safiyar cewar yana son ganawa da wannan baiwar da ta tab’a yi masa bayani akan Jidda.

“Suna tafe ranka ya daΙ—e, na kira su yanzu kafin kiranka ya shigo tace min suna hanya…”

Muryar Sunusin ta faΙ—a kuma kafin ya kai ga Ζ™arashe zancensa, Ζ™ofar Ι—akin daga baya ta buΙ—e, wasu mata biyu suka shigo kuma a lokaci guda Madaki ya tantance fuskar baiwar nan a cikinsu, ta yaya zai kasa manta ta ma? Itace halitta ta farko data fara sanar dashi wacece yarinyar da Mai martaba ya aura masa.

STORY CONTINUES BELOW

Sunusi ya miΖ™e daga kujerar yana amsa sallamarsu, sannan ya nunawa baiwar wajen alamun ta zauna, bata zauna Ι—in ba sai tayi saurin durΖ™usawa daga gefen kujerar ta shiga gaishe da Madaki yayin da Sunusi da Ι—aya macen daya kira da Safiya suka buΙ—e Ζ™ofar dakin suka fita.

“Ina son in tambayeki wani abu ne game da ita.”

Ya faΙ—a kai tsaye yana kallonta bayan ya amsa gaisuwar tata, ba sai ya fasa kalmar itan ba don ya san ko ba’ayi mata bayanin dalilin kiranta ba, ta riga ta san abinda zai sa ya neme tan. Baiwar ta gyada kanta alamun tana saurare yayin da ya sarke yatsunsa cikun junansu sannan ya Ι—ora su akan teburin da labtop din ke kai.

“Ita kadai ce a wajen kakarta?”

Ta girgiza kanta.

“A’a akwai wata Ζ΄ar wan mahaifiyarta mai suna Jamila, ta girme mata amma dai tare suke a wajen kakar tata.”

“Zaki iya sanin Ζ™arfin alakarta da Jamilan?”

“Eh to ranka ya dade suna jituwa dai, don tun bayan dawowar ita Jiddan gidan ba’a taba jin kansu ba, amma kuma ba tare suke sosai ba tunda ita Jamilar ta girme mata kuma ma tana aiki a cikin gida don haka ba tare suke al’amuransu ba.”

Ya d’an yi nazarin hakan kafin ya sake tambaya.

“To bayan ita babu wani da kika sani suna shiri sosai ko kuma ake yawon ganinsu tare?”

“Akwai ranka ya dade, jikar Hajiya Laraba ce mai suna Sadiya, itace Ζ™awarta don duk inda zaka ganta to tare suke, tun bayan dawowarta masarautar ita kadai take kulawa haka.”

Sadiya. Madaki ya maimaita sunan a cikin ransa kamar mai son ajiye shi, sai kuma ya jawo wata jotter a gefe ya rubuta shi don gudun mantuwa.

“Zaki iya samo min amsar wasu tambayoyi a wajen Sadiyar ba tare da kowa ya sani ba?”

Sai ta Ι—ago ta kalle shi amma kwarjininsa yasa ta sake saurin komawa.

“Sunusi zai gaya miki abubuwan da nake so ki tambaye tan sai ki san ta sigar da zaki yi mata magana ba tare da ta fahimci komai ba.”

Ta sake yin shiru kamar hakan zai yi wuya kafin ta gyaΙ—a kanta a hankali.

“Zuwa yaushe zan saka ran ganinki kenan?”

“Inaga kamar zuwa jibi ranka ya daΙ—e.”

“Ki maida shi gobe, Sunusi zai kira ki da yamma.”

Mamaki ya kamata, in har zai sa lokaci me yasa zai bata zabi da farko? Ta yaya zata iya  tunkarar Sadiyar har ta sami amincewarta a wannan Ι—an Ζ™anΖ™anin lokacin?

“Sunusi zai baki saΖ™onki.”

Ya faΙ—i hakan alamun ya sallameta sannan Ι—if! Ya katse kiran.

Baiwar tabi screen Ι—in computer Sunusi da kallo, kuΙ—in da aka bata wancan karon har yanzu bata gama tsakurarsu ba tana kashe Ζ΄an matsalolin gabanta gashi yanzu kuma za’a Ζ™ara mata wasu, tuni ta manta Ζ™orafinta da tunanin dole ne ma ta nemo Sadiya a goben, wannan ai itace sa’a da tafi manyan kaya!

Bayan ya kashe kiran, Madaki ya cigaba da aikace-aikacen dake gabansa ba tare daya bari tunaninsa ya zarme zuwa kan komai ba, don ya riga ya yanke cewar idan har ya samu Sadiyar da yake tunanin zai samu gamsashshen bayani daga gareta, sai ya ware lokaci na musamman a goben da zai yi nazari akan komai, saboda ya lura in har ya biyewa yawan tunane-tunanen, aiki zai yi ta Ζ™arar masa ne ba tare da ya kawar dana gabansa ba.

Samuel ya shigo tare da wata ma’aikaciyarsu mai suna Halima, suka tattauna akan wani sabon tsari da ita Haliman ke son su fito dashi a kamfanin, Madaki ya gamsu sosai da shawarar har ma ya basu goyon baya kan cewar su fara samar da hanyoyin da za’a tsara komai kafin a zauna meeting don jin ra’ayin sauran ma’aikatan nasu. Habibu ya shigo da ban hakurin katob’arar canja farashin da yayi. SadiΖ™ ya shigo da zancen wasu kayayyakinsu da suka Ζ™araso daga kasar Spain. Toyin ta kawo reports Ι—in data haΙ—a na watan daya gabata, bangaren customer care suka kawo file na Ζ™orafe-Ζ™orafensu… Haka dai yayi ta amsa saΖ™onni Ι—aya bayan Ι—aya har wajen azahar, a lokacin ne kuma Mubarak ya shigo Office Ι—in.

STORY CONTINUES BELOW

“Ina muΖ™ullin motarka?”

Ya tambaye shi bayan sun gaisa.

“Me zaka yi da motata?”

Shima ya jefa masa tambaya.

“Na fara harkar smuggling ne zan tura ta Nijar in siyar.”

Madaki ya gyaΙ—a kansa.

“To ai ta hanya biyu zaka bi ba wannan ba, ko dai muyi cinikinta ka bani kuΙ—in sai kaje ka siyar ko kuma ka biyo dare ka Ι—auka.”

“Inaga zan dauki shawara ta biyun, don sata a gidan ango sauΖ™i zata yi.”

Sai a lokacin Madaki ya dago ya kalle shi.

“Me zaka yi mota ta Mubarak?”

“Zanje yiwa Khadija cefane ne, nace tunda bayan ita mun ajiye wata ma, to bari inyi abinda kai ka kasa.”

Sai ya juya ya cigaba da aikinsa.

“Kar ka wahalar da kanka, zan siya mata abinci kawai.”

Maimakon ya bashi amsa, Mubarak ya juya shiga dube-dubensa, can a tsakiyar office Ι—in inda wani Ι—an zagayayyen waje yake kamar falo ya hango briefcase Ι—in Madakin dake yashe akan kujera, sai kawai ya miΖ™e ya nufi can, ya buΙ—e aljihun farko ya Ι—auko mukullin motar a ciki yana faΙ—in.

“Ka cigaba da zama anan kana ganin wahala nake.”

**

Tun daga kan kayan buhunhunan abinci, zuwa kwalaye, ledoji, gwangwanaye, har vegetables da kayan miya da nama dasu kifi babu abinda wannan tsohon da yace sunansa Malam Saminu bai shigo dashi cikin kitchen Ι—in da Jidda ke tsaye tana kallo ba, don cewa yayi ba zasu shigo ta falo ba ma saboda kayan na da yawa, don haka ta buΙ—e musu Ζ™ofar baya suka yi ta jibge su shi da wani saurayi da suka zo tare a motar Madakin, haka ne ma yasa bata bukaci sanin wanda ya turo su ba. Murna ce a ranta fal, sai daΙ—i take ji wanda hae ya kore Ι—an bacin ran da Madaki ya Ζ™unsa mata da asuba.

“Yawwa Hajiya su kenan kayan nace akwai inda za’a jera sune? Musamman buhunhunan.”

Cewar Malam Saminun bayan sun gama shigo da kayan.

“Eh Baba ga store nan, bari in kwashe kwalayen ciki sai a zuba anan ko?”

Ta faΙ—a tana nufar hanyar store din, ta fito da duk wasu kwalayen data gani a ciki sannan suka shiga jera mata kayan buhunhunan da kuma na kwalayen da jarkunan mai, na cikin ledoji kawai suka bar mata anan tace zata kwashe.

“Yawwa ga wannan kuma yace a kawo miki.” cewar Malam Saminun, ya zira hannunsa a aljihu ya zaro kuΙ—i ya mika mata.

“To Baba nagode, Allah ya huta gajiya, nagode sosai.”

Kuma ba tare da ta Ζ™irga ba ta zaro dubu daya a ciki ta miΖ™a masa, da Ζ™yar ya karba yana ta faΙ—in ai aikinsa ne kafin ya koma shine mai godiyar, zuciyarsa cike da mamakin al’amarin da ya kasa tantance shi, zuwa yanzu dai ya san tabbas yarinyar matar ubangidansu ce amma mamakinsa shine na yadda har yayi aure ba’a sani ba, watakila kuma komai ya faru ne cikin Ζ™anΖ™anin lokaci.

Amma ko ba komai yayi dace da Ζ™addara mai kyau!

Malam Saminu ya ayyana a ransa.

Jidda tabi ledojin nan da kallo bayan fitarsu sannan ta kirga kudin data ajiye kan island, dubu tara ne cif alamun kuΙ—in gabaΙ—aya dubu goma ne kenan, ta jinjina kai tana juya su cikin hannunta, ba zata ce bata taba mallakar dubu goma ta kanta ba don ko bayan rasuwar mahaifiyarta, Baddo ta sanar da ita cewa akwai wani fili da aka siyar a garinsu tace mata gadonta ne data mallaka a wajen mahaifinta, kuma da kuΙ—in tayi amfani dasu wajen siya mata Ζ΄an kayayyaki da suturu a lokacin, amma ace wai ga ranar data rike kuΙ—in kanta a hannu irin wannan, to tayi karya in tace akwai.

STORY CONTINUES BELOW

Ta ajiye kuΙ—in a gefe sannan ta koma kan ledojin ta Ι—ebi wanda taga nama da kifi a cikin ta buΙ—e fridge ta saka su a sama, su maggi, gishiri, curry, da Ζ΄an tarkacen girki ta ware musu waje cikin wata cupboard. Akwai wasu tarkace irin su Bama da ketchup duk ta dura su a fridge suma kusa da kayan gwangwaninsa.

Kayan tea ma ta saka su a drawer da yake ajiye nasa sannan ta dawo kan kayan miya, kwata-kwata babu wani plate ko roba mai girma a gidan don haka ta zube su a cikin sink, sauran kuma irin su cabbage ta samar musu waje a can kasan fridge suma. Sai da ta kintsa komai tsaf sannan ta dawo kan kayan miyan, ta rage albasa a cikinsu sannan ta wanke su haka a ciki, sai ta dinga Ι—iba da kadan-kadan tana zubawa a blender data gani a gefen kettle, ta kunna ta markada na ciki sai kuma ta rasa a ina zata zuba… GabaΙ—aya kitchen Ι—in daga plates sai kofuna, Ζ΄an tuΖ™wanen guda biyu ne kuma kanana.

Ƙwakwalwarta ta tuno mata da wasu manyan ledoji data gani a cikin kwalayen store Ι—in nan don haka taje ta Ι—auko su, tsaf kuwa zasu Ι—auki markaΙ—en don haka ta wanke Ι—aya ta juye a ciki, haka ta dinga markada kayan miyan nan tana zubawa har ta gama tsaf, ta Ζ™ulle manyan ledojinta guda uku suma ta sama musu waje a freezer kusa da ledojin naman.

Wallahi da daΙ—i kaga wai kaine da gida sai yadda kaga dama kayi da abubuwanka babu mai ce maka ga yadda zaka tsara komai, kiga dai uwar wahalar da Nuriyya ke sha a gidan kakarta amma gashi yanzu ta sami Ζ΄ancinta, ai dole ne in matsawa Sulaiman ayi zancen saka ranar nan Jidda.

Ta tuno maganar da Jamila ke faΙ—a lokacin data rakata gidan wata kawarta da tayi aure, a wannan lokacin kallon Jamilar kawai take a matsayin mai hangen Ζ΄ancin dake nesa, sai gashi ko shekara ba’a rufa ba anyi juyin waina, wannan Ζ΄ancin yazo gareta ta tsallake Jamilar dake ganin tana kan gab’a a lokacin.

Ta kalli kitchen Ι—in ta Ζ™ara kallonsa, yanzu girki kawai ya rage mata, sai wani daΙ—i ya kara ratsa zuciyarta a take, har tayi guntun murmushin da taji shi kamar sabon abu akan lebbenta, rabonta da murmushi tun a can Kiyari lokacin da Sadiya ta miΖ™o mata Ζ΄an kunnayen nan, bata sani ba ashe tazararta da sake yin wani mai tsayi ce sai yanzu.

Abinda ta sani kawai shine idan har Madaki zai dinga kawo mata irin wannan kayan abincin, to ya shekara yana zarginta ma ba zata damu ba, duk ranar da yaga damar gamawa sai ya sallameta.

*

“Sannu da zuwa.”

Muryarta ta faΙ—a a lokacin da ta fito daga Ι—akinta bayan sallar magriba, sai dab da magribar ta gama aikin girkinta don haka tana gamawa ta tafi wanka kuma tun tana wankan taji Ζ™arar shigowar motarsa, daga nan taji shi sanda ya fita masallaci da sanda ya dawo saboda haka dama ta san tabbas tana fitowar zata ganshi, kuma yau a cikin falon yake zaune ya Ι—ora labtop dinsa kan center table yana aiki.

Tana furta gaisuwar ya juyo ya kalle ta da waΙ—annan kyawawan idanun nasa masu kwarjini, hakan yasa zuciyarta ta Ι—an buga kafin tayi saurin dauke kanta amma duk da haka sai ta taho da guzurin hoton fuskarsa, don yayi wanka, yayi wani irin fresh, kwantaccen sajensa na nuna alamun danshi kamar yadda Ι—an madaidaicin gashin kansa yake, sannan kuma idanunsa na Ι—auke da wannan sheΖ™in nasu kamar ya Ι—iga mai a ciki.

“Yawwa.”

Kamar jiya amsar ta fito sannan ya juya ya cigaba da aikinsa.

Sai ta sake juyowa ta cigaba da kallonsa daga inda take tsaye, wandon jikinsa da kaΙ—an ya wuce gwiwa baki siΙ—ik! rigarsa kuma light blue ce irin loose Ι—in nan mara nauyi… Zaiyi kyau sosai ace tallan kayan yake yi.

“Naga kaya da yawa, Madallah… Allah ya kara buΙ—i.”

Ta yanke shawarar sauke nauyin godiyar dake maΖ™ale a kirjinta, sai ya gyada mata kai kawai ba tare da ya juyo ba. Ta kalli cikin screen Ι—in labtop Ι—in, wani abu yake rubutawa a ciki mai yawa, sai ta tab’e bakinta tana tunanin ba dole ciwo yayi ta cinye shi ba ace mutum bashi da wani lokacin hutu a rayuwarsa sai aiki kawai. Saboda haka ta watsar dashi ta wuce kitchen daΙ—i na cin zuciyarta na hango abincin da zata je ta zubo.

STORY CONTINUES BELOW

Shinkafa da wake ne da yayi wani irin dafuwa mai kyau, sai tayi miyar jajjage da atturuhu da albasa da tafi yawa, ta saka spice din garlic da curry da naman kasuwa zuΖ™u-zuΖ™u sannan ta soya ta da manja, don a Ι—azu data buΙ—a jarkokin nan biyu taga Ι—aya mai ne Ι—aya manja sai da ta tsugunna a Ζ™asa don daΙ—i. Ta zuba abincin iya cikinta sannan ta zuba sauran a wani plate ta sanya a fridge, dama bata yi girkinta dashi ba don tunda har ya gwaleta jiya to ya yiwa kansa, ba zata Ζ™ara masa tayi ba balle har ya sake wulakanta ta.

Ta Ι—auko ruwa ta dawo falon, kamar ta wuce Ι—aki kuma taga don me? Ita ta gaji da zaman shirun nan don haka ai ba laifi bane don ta zauna a falon tana jin motsinsa, sai ta jawo kujera Ι—aya a jikin dining ta zauna tana fuskantar kujerar da yake kai.

HaΙ—aΙ—Ι—en Ζ™amshin miyar nan shi ya fara ziyartar hancin Madaki kafin ma ya san da shigowarta, a lokaci guda cikinsa ya murΙ—a cikin Ζ™orafi yayin da bakinsa yayi magiya, yau a office snacks kawai ya samu yaci don haka cikinsa kusan fanko yake, yaji sanda taja kujera a dining ta zauna amma bai juyo ba ya cigaba da abinda yake yi yana Ζ™oΖ™arin saita tunaninsa, don baya jin ko yunwa zata kashe shi a yanayin da suke ciki zai iya cin wani abun hannunta, in har yayi hakan, to ko a duniyar mahaukata za’a kira shi da ‘shashasha’ ne wanda ke gini yana ruguje shi da kansa.

Ƙ’amshin abincin ya cigaba da gauraye Ι—akin, sannan Ζ™arar cokalinta akan plate Ι—in ya fara damunsa, sai yaji ransa na shirin b’aci, da gajiyar dake bibiyar jikinsa zai ji ko kuma da maganganun da Mai martaba ya gaya masa yau a waya cewar ‘Komai zai iya wucewa idan har bai watsa masa Ζ™asa a ido ba’ maganar da har yanzu duk koΖ™arinsa ya kasa gano me take nufi, sannan ga aikin da yake son Ζ™arasawa kafin gobe, to don me zata zo ta sashi gaba tana cin abinci?

“Tashi ki bar nan.”

Muryarsa ta fito cikin Ζ™oΖ™arin danne fushinsa ba tare da ya kalle ta ba.

Kusan dama abinda Jidda ke jira kenan, jira take yayi magana ko yaya ne don ta sami Ζ™ofar da zata ce wani abu itama, kwana biyu bakinta har Ζ™aiΖ™aiyi yake saboda tsabar rashin abokin surutu.2

“Saboda me?”

“Saboda bana son ganinki a wajen.”

Sai ta Ι—anyi shiru tana cigaba da juya cokalinta akan plate Ι—in kafin tace.

“Bayan nan kuma sai ina?”

Cike da mamaki ya juyo ya mata wani irin kallo daya haddasa nauyi a kirjinta, amma duk da haka itama shi Ι—in take kallo kuma kai tsaye ta bashi amsar tambayar da bai furta ba.

“Ina nufin ka gaya min duk wajajen da baka son ka dinga ganina sai in kiyaye, saboda ni bana son ana wulaΖ™anta ni.”

Kamar maganar ta dake shi, sai ya juya ga barin kallonta ya cigaba da aikinsa kafin ya sake cewa.

“Zaki tashi ko kuwa?”

Maganar ta wuce da wani hoto a idanun Jidda, sanda ya riΖ™eta, ya raΙ—a a kunnenta.. ‘Ina da hanyoyin da zan iya miki dole…’

Sai ta had’iye yawu amma bata tashin ba tace.

“Zan tashi mana, gidana ne? Ba kai ke da iko da abinka ba, in dama zaka maida ni gidanmu komai zaifi sauki ai.”

Baice komai ba, ta sake kai lomar abinci bakinta sannan ta cigaba da cewa.

“Ni kaina dama ba jin daΙ—in wajen nake yi ba don dai kawai babu yadda zanyi ne, amma ace tunda na baro gida babu abinda nake yini dashi sai Ζ™arar kukan tsuntsaye, ba a wajen da kasa aka Ζ™ulle ni ba, ba anan Ι—in ba. Yau ma haka na yini da wani Ι—an guntun ciwon kai kuma na san duk dalilin rashin kitso ne…”

Sai kuma ta Ι—anyi shiru tana tauna abincin dake bakinta, kamar mai nazari kafin ta Ι—ago ta sake kallonsa.

“Ka san gidan da ake yin kitso anan unguwar?”15

STORY CONTINUES BELOW

**

“Daddy wancan… bashi ba mai kama da pink Ι—in, na kusa da mai rainbow, gashi nan.”

Ζ³ar Ζ™aramar yarinyar mai suna Hanan ke faΙ—a tana tsallen yunΖ™uri yayin da Mubarak ke lalube a saman wata kanta dake cikin tsohon garejin gidansa, inda suka maida shi store. Baban Ι—an nasa Aliyu na tsaye a gefe yana jira a Ι—auko littafin don Ζ™ure musun da suke yi shida Hanan din akan homework Ι—in da yake koya mata, don ta kafe kai da fata tace yadda yake yi mata ba daidai bane irin na ajin data baro primary 1 shine daidai shi kuma yace ba haka ba, shine aka taho lalubo littafin primary 1 Ι—in, don duk da Mubarak din ma yasa baki yace daidai ake yi, Hanan ita bata yarda ba.

“Shine Quantitative Reasoning?” Mubarak din ya tambaya daga saman kantar.

“A’a daddy Maths ne fa, Essential Mathematics…” sunan ya fito mai daΙ—i cikin Ζ΄ar muryarta.

“Okay, ashe da sauran shan Ζ™ura ta.” Ya fada yana cigaba da duban. Zuwa can ya gano shi, bangonsa mai kama da pink Ι—in kuwa kamar yadda tace. Ya diro Ζ™asa daidai lokacin da Khadija ta shigo rike da tambulan mai cike da fresh milk.

“Me akeyi ne anan? Inata nemanku.” Ta tambaya tana Ζ™arasowa.

Mubarak ya sauko ya miΖ™awa Aliyu littafin da cewar a nemo shafin yayin da jin muryar mamanta yasa Hanan ta juyo tace.

“Mummy kina bayana ai ko?”

“Me ake yi?” Khadija ta Ζ™ara tambaya tana murmushi.

“Musu akeyi, kema sai ki zo ki zabi team Ι—in da zaki shiga.” cewar Mubarak yana Ζ™arasowa gabanta da niyyar rungumeta, sai ta ture shi tana miΖ™a masa glass Ι—in madarar.

“Kaima ka san kullum ina bayan Ι—iyata ai.”

Mubarak ya lumshe idonsa yana shan madarar yayin data Ζ™arasa wajen yaran tana kallon me suke yi.

“Gashi nan, gashi nan na gaya miki. Wancan multiplication ne wannan kuma Division ne.” Aliyu ya faΙ—a cikin fushin dake koΖ™arin kama shi.

“Allah ba haka bane ba haka bane ba, gabadayansu Division ne.” Hanan ta faΙ—a tana turo baki.

A lokaci guda Aliyu ya fizgi littafin yayi hanyar fita yana fadin.

“Zo muje to a gwada.”

Kafin Khadija tace wani abu kuma Hanan Ι—in tabi bayansa tana Ζ™unΖ™uni.

“Wai musun me ake ne Daddy?”

Cewar Khadijan tana juyowa daga inda take tsaye, sai ya ajiye kofin ya Ζ™araso wajenta, ya rungumota ta baya sannan ya sanya fuskarsa cikin wuyanta.

“Wallahi ni kaina ban gama sani ba, don Maths Ι—in primary gabadaya baya kaina.”

“Shine har kake zaban team?” Ta tambaya tana dariya.

Yayi dariyar shima sannan yace.

“Wai don in nuna na san me akeyi ne.”

Shiru ya Ι—an biyo baya tana tsaye a jikinsa tana wasa da yatsun hannayensa da suka zagayeta. Zuwa can sai muryarsa ta fito a hankali.

“Ina Ζ™ara baki haΖ™uri Yaarym, mun tuba mun kuma tuba, Insha Allah ba zamu yi abinda zai dame ki ba balle har mu b’ata ranki, don wallahi bana jin zuciyata zata iya sake Ι—aukan irin wannan hukuncin daga gare ki, ranar da kika tafi kika barni nutsuwata gabadaya na rasa Yaarym… ji nayi kamar an kaini kabarina.”

Sai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba tana cigaba da wasa da hannayen nasa. Allah ya sani anfi Ζ™arfinta ne amma duk yadda zuciyarta ta kai ga son Mubarak bata so dawowa gidansa da wuri haka ba, taso barazanarta ta tsorata shi sosai har sai ya san inda zai Ι—auke Ζ™anwartasa ya kai, amma sai gashi wai Salwan ce da kanta taje har gidansu ta dinga bata hakuri ita da iyayenta har da kuka, don haka ba yadda ta iya haka aka lallameta da maganganu ta dawo, amma har yanzu zuciyarta bata natsu da ita ba.

“Zo in gaya miki wani abu.”

Ya katse tunaninta yana jan hannunta zuwa wajen teburin daya ajiye glass Ι—in madarar nan.

*

“Nifa gani nake har yanzu zuciyarta bata gama nutsuwa dani ba.”

Cewar Salwa a cikin wayar da take yi tsaye a kitchen, Naja’atu taja tsaki a cikin wayar tace.

“To dan ub*nta kar ta nutsu dake Ι—in mana, ai dai yanzu bata da wata hujjar da zata iya buΙ—a baki tace wani abu akanki. Ke dai kawai ki cigaba da takunki tunda farkon satin nan Namama yace aikin zai zama ready ai shikenan, daga lokacin baki da wata sauran wata damuwa.”

Salwa ta juya miyar dake zaΙ“alΙ“ala kan gas Ι—in gabanta sannan tace.

“To yanzu manta da wannan, mu koma zancen Madaki, na gama shirya komai kuma a gobe ko jibi nake son fara aiwatar da takuna, kuma ina tabbatar miki idan har komai ya kankanma ba za’a wuce cikin watan nan ba tarkona zai kama gafiya.”

Naja’atu ta saki dariya daga cikin wayar kafin tace.

“Bana jinki ai Hajiyata, in dai a wannan fagen ne na yarda dake, matsalar da nake jiye miki guda Ι—aya ce, tunda har kika kai wannan lokacin baki bayyana masa kanki ba to wallahi ina tsoron ki sami wata a rayuwarsa.”

Zancen yayi nauyi a Ζ™irjin Salwa kamar yadda hakan ke faruwa duk lokacin data faΙ—a mata hakan, amma sai taja tsaki sannan kashe wutar gas Ι—in.

“Na gaya miki Naja wannan ba matsala ce a wurina ba, don ko uw*rsa yake shirin aure wallahi sai naga bayanta balle wata mace daban.”2

Tana faΙ—in haka ta kashe wayar ta ajiye ta a gefe sannan ta zubo abincinta ta dawo falo, don haushi bata Ι—auko ta ba, a falon ta tarad da su Hanan suna ta cece-kuce kan wani abu a littafinsu.

“Ina Abbanku?” ta tambayi Aliyu.

“Yana tsohon Garage.”

Sai ta ajiye abincin nata akan table ta tafi nemansa, don tun Ι—azu yace ta same shi akan maganar karatun da yake son ta fara, karatun da take ganin dashi da fafutukar nema matan da zai fara duk a banza ne, saboda ita nata karatun dake gabanta daban ne, kuma tata fafutukar ta ninka tasa. Kawai tana biye masa ne don kar ta Ι“ata rawarta da tsalle.

Ta nufi hanyar garejin ba tare da ta damu ta raba faΙ—an yaran ba, ta isa daidai Ζ™ofar shiga garejin lokacin da maganar ta fara shiga kunnenta.

“… Komai yazo ne a lokaci guda, an Ι—aura auren a ranan kuma har ma ya taho da ita nan garin.”

Ƙarshen maganar Mubarak kenan kafin muryar Khadija ta maye gurbin tasa.

“Da gaske kake Daddy? Da gaske Madaki yayi aure??”

Wayar hannun Salwa ta faΙ—i a dandaryar wajen ta tarwatse, ta fashe, zuciyarta ta buga cikin allon Ζ™irjinta sannan wani irin duhu ya mamaye duniyar a idanunta, baΖ™iΖ™-Ζ™irin!1

**

Ƙofar net Ι—in Ι—akin Baddo ta bude, Aunty Zainab ta sako kafarta ciki da ragowar saurin da take tafe dashi, daidai lokacin da Jamila ta fito daga can cikin Ι—akin dake manne a falon..+

“Baddo da Hajiyan suna ciki.” Muryar Jamilan ta fito a wani irin sauti da Ζ™arara zaka tsinto fargaba a ciki.

Aunty Zainab ta juya ta rufe Ζ™ofar da Ζ΄ar sakatar ciki kafin tabi bayanta cike da taraddadin da tayo dakonsa, don jiya da suka dawo daga wahalalliyar tafiyar da suka yi zuwa Lagos ba tare da sanin dalilin dawowar tasu ba, a cikin gari ta sauka gidan Ζ™anwar Hajiya (mahaifiyarta) inda take tunanin zata huce gajiyarta kafin ta ziyarci asibiti don a duba lafiyar cikinta da tayi ta fama dashi a hanya, amma sai wayar da Jamila ta rangaΙ—o mata da asubahin yau ta katse duk wani shirinta.

‘Aunty Zainab, Baddo ce tace in kira ki kizo, wani abu ya faru… Wani abu muka tsinta a cikin jakar kayana kamar asiri.’3

Ta kutsa kai cikin Ι—akin a lokacin da zuciyarta ke Ζ™ara bitar maganganun. Dukkaninsu suka amsa mata sallamar kamar yadda idonta yaga dukkanin nasu a lokaci guda.

“Da gaske ne abinda Jamila ta kira ni a waya ta gaya min?”

Kai tsaye tayi tambayar tana kallon tsofaffi biyun dake zaune a cikin Ι—akin, musamman Baddo wadda ke zaune fuskarta fayau! Ba zaka iya tsinto ainihin abinda ke wakana a tunaninta ba. Hajiya Laraba dake gefe ta gyara zamanta sannan tayi magana.

“Gaskiya ne Zainabu, ai ki san wannan zancen baiyi kama da Ζ™arya ba, tana buΙ—e jakar kayanta ne da asuba zata Ι—auko hijabi sai ganin sassaΖ™e tayi a cikin leda jiΖ™e sharkaf da jini, kuma sai da Baddo tasa ta kira ni nazo ma sannan muka ga ashe jakar ba tata bace canje akayi da ta wata. Sai dai abinda muka kasa ganewa shine wa zai aikata irin wannan abun alhali duk mutanen gida aka tafi dasu a motar babu wani bare, sauran motocin biyu kuma direbobi ne kawai da kayan abinci…’1

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un… Yanzu tana ina jakar?”

Aunty Zainab Ι—in ta katse dogon bayanin da mahaifiyar tata ke shirin yi don ba shine mafi a’ala ba, Jamila ta miΖ™e da sauri ta buΙ—e cikin wata Ζ™aramar wardrobe dake gefe ta Ι—auko jakar.

“Tsoro muke kar wani ya shigo ya gani.” Muryarta ta sake fitowa da irin sautin Ι—azu.2

Aunty Zainab tasa hannunta dake tsaye kyam saΙ“anin na Jamila dake rawa ta zuge zip Ι—in jakar a hankali, kamar mai fatan jinkirinta ya canja abinda ke ciki, amma ina! A ciki sak ledar da Hajiya Laraban ke Ζ™oΖ™arin siffanta mata ce. Taji gabanta ya faΙ—i a lokaci guda amma duk da haka ta kai tafin hannunta ta taΙ“a ledar, sanyin daskararren jinin dake ciki ya ratsa fatarta lokacin da tunaninta ya hasko mata zancensu da Baddo a daren da zasu tafi.

‘Me yasa muna ji muna gani zamu biye musu Baddo?

Me yasa zamu karΙ“i garar nan?

Me yasa zamu bari suyi amfani damu su cimma wata manufarsu?

Kamata yayi muma mu tashi tsaye mu kare Jidda da dukkan iyawarmu..

Tambayoyin da suka yi Baddon kenan a daren da Fulani ta kira su ta shaida musu cewavta dauke musu Ι—awainiyar Gara za’a debi su ne kawai suje su kai kayan, wanda hakan ya zama tamkar an Ζ™ara ingiza wutar hasashen da suke yi ne akan ita Fulanin, don ba su kadai ba kowa a masarautar ya san k’iyayyar dake tsakanin ta da Madaki ba abu ne da zata watsar dashi rana tsaka kamar komai bai taΙ“a faruwa ba.

Kuma duk da cewar al’amarin ya shafi Fulanin da kowa ke shakka, haka bai hana Ζ΄an Ζ™ananan surutai akansu tashi ba, to ta yaya kuwa zasu yarda su karΙ“i Garar duniya ta Ζ™ara zaginsu? Tunaninsu kenan a wancan lokacin, amma amsar da Baddo ta basu ita ta kore duk hakan, ita ta kaisu ga karΙ“ar garar har ma da tafiya Ikkon.

STORY CONTINUES BELOW

‘Fulani tana taΖ™ama da wani iko ne da yake gaibu a duniyar nan, kuma idan har muka ji tsoron wannan ikon nata kamar mun butulcewa yardarmu ga Allah ne mun saka shakka a cikin nasa ikon. Mutane da yawa kanyi wannan kuskuren a lokacin da wani mai barazana ya tsorata su, da sun bari imaninsu ya girgiza sai ki ga abubuwa sun Ζ™ara lalace musu ta yadda da wuya a kai ga ci.3

Amma insha Allahu mu ba zamu kasance a wannan layin ba, nayi istikhara kuma zuciyata bata canja daga abinda nake ganin shine daidai ba… a yanzu bamu da wata mafita sai ta karΙ“ar Garar nan, don haka mu bi su a hakan mu karba, ni na yarda Allah yafi Ζ™arfin duk abinda suke shiryawa kuma shi zai kare daga mu har Jiddan cikin irin nasa ikon…’5

“Zainabu…”

Muryar Baddon ta zahiri ta katse Aunty Zainab daga tunanin ta, kuma muryar fayau take babu wani abu da zaka iya tsintowa a ciki, sai dago ta kalle ta.

“Kinga ikon Allahn da nake faΙ—a muku ko? Kinga sakamakon Ζ™arfin imani da tauhidin bawa ga ubangijinsa?”2

Sai ta gyada kai tana cigaba da kallonta.

“Na gani Baddo, amma me hakan yake nufi?”

“Hakan na nufin ubangiji ya Ζ™addara wannan tafiyar ne ba don kuje wajen Maijidda ba ko don abinda Fulani ke Ζ™ullawa ya kai ga ci, sai don sharrin nasu ya suΙ“uce daga hannunsu ya iso wurin da zaifi dacewa dashi. Don haka ki gaya min a cikin Ζ΄an tafiyarku wa kike zargi?”

Sai ta haΙ—iye yawu kaΙ—an a lokacin da idonta ke hango mata wata mata a cikin rububin mutanen wajen check-up Ι—in da aka tsayar dasu, a baya ta wullar da hasashenta ne da cewar abu ne da ba zai yiwu ba, amma a take a yanzu sai ta Ι—auko shi ta karkaΙ—e, ta goge har ya fito da kyallinsa kafin ta furta sunan da yayi tasiri a zuciyoyin mutane ukun dake gabanta.

“Jakadiya Babba.”1

*

“Jakadiya Babba ce.”

Sassanyar muryar Fulani ta furta sunan a matsayin amsa cikin wayar data keyi.

Hajiya Bilki ta nisa a cikin wayar sannan muryarta ta fito.

“Ba zance kinyi wauta ba Hafsatu tunda Jakadiyarki ba karamar yarinya bace amma duk da haka kinyi sake, wannan aikin ba Ζ™aramin abu ne ba, yadda yake da tasiri wajen aikinsa ina tsoron abinda zai biyo baya in har aka sami akasi.”

“Akasi? Akasi fa kika ce Bilki.” Muryar Fulanin ta fito cike da Ι—imbin mamaki.

“…Kefa kika ce babu akasi a wannan aikin, kika ce abinda kake kokwanto akansa shi ake samun akasi amma banda wannan…”

“Tabbas haka na faΙ—a Hafsatu don kuwa ta yaya zanyi tunanin wani akasi bayan duk mutanen da nake hulΙ—a dasu babu wanda ya taba irin wannan ‘saki na dafen’ da kika yi, kowa ya tafiyar da al’amarinsa daidai har ya samu nasararsa, to ta yaya kuwa zance miki ana samun akasi?”

Fatar goshin Fulani ta Ι—an tattare cikin layi biyu.

“Ban gane saki na dafe ba? Shawarar wa nabi na tura aikin nan a mota zuwa can? Har ma zaki kawo kalmar saki na dafe anan Bilki? Naga har ce miki nayi in da zan iya ma tsaf zanyi aikin nan da kaina amma kika furta cewar babu matsala in samu wadda na yarda da ita kawai in bata, to meye saki na dafen da nayi anan?”

“Kar mu Ι“ata ran juna Hafsatu…”

Cewar Hajiya Bilkin, muryarta na shaida halin ko in kula da kuma gargaΙ—in kar a fusata ta.

“… Jakadiyarki tayi laifi cikin jagorancin rashin kashedinki da kuma nuna mata muhimmancin aikin nan, don haka duk yadda zaki yi a yanzu kamata yayi a san inda za’a nemo jakar tun kafin ta faΙ—a hannun waΙ—anda zasu iya salwantar da aikin saboda idan haka ta faru ina jiye miki halin da zaki iya faΙ—awa. Kar ki manta aikin nan da farko ba naki bane, da kika ce zaki karΙ“a takanas nasa aka sake tsuma shi da sunanki kuma ba tun yau ba kin san sharaΙ—in waΙ—annan mutanen, idan har rana ta Ι“aci alhakin komai kan ki zai dawo ba gare su ba.”

STORY CONTINUES BELOW

Dib! Wayar ta katse a kunnen Fulani wadda a lokaci guda duk wata jijiya ta jikinta ta saki tamkar an zare mata laka, kuma ko kaΙ—an bata damu da kashe mata wayar da Bilkin tayi ba don a lokacin abinda take hangowa a cikin idanunta yafi Ζ™arfin hakan…

…idan har rana ta Ι“aci alhakin komai kan ki zai dawo ba gare su ba…!2

***

Lagos.

?There goes my mind racing,

‘nd you’re the reason

that I’m still breathing,

I’m hopless now…

There goes my hand shaking,

‘cus you’re the reason

my heart keeps beating,

I need you now…?

A hankali wannan sautin waΖ™ar ke fita cikin sautin rediyon motar Madaki, da misalin karfe shida ne na yamma, lokaci irin wanda ya saba komawa gida bayan ya tashi daga aiki.

Yaja tsaki sannan ya mika hannu ya kashe waΖ™ar, zata dame shi ne don baya jin dadi sam! A kwana biyu ba Ζ™aramar wuya yasha ba saboda wasu ayyuka da suka taso musu, sun riga sunyi budget sai Ζ™arshen shekara zasu yi su, amma sai ga wani dalili ya taso da dole ne ayi su a yanzu don haka suka ajiye komai suka duΖ™ufa, kuma ba shi kaΙ—ai ba duk wani wanda aikin ya haΙ—a dashi yana tare da irin wannan gajiyar, Ζ™arin tasa shine ciwon dake Ζ™oΖ™arin kwantar dashi amma yana dagewa.

Yana tsaye ne cikin hold-up dake kan shataletalen da zai juya kafin ya Ι—auki hanyar gida. Ta cikin mutanen dake wucewa a can gefen titin idonsa ya hango masa irin Ζ™abilun nan dake tallan magungunan gargajiya a cikin robobi suna yawo dashi a kansu, a lokaci guda ya tuno da Jidda, don a washegarin ranar data tambaye shi gidan kitso ne ya koma ya tarad da ita tare da wata mata irin wannan Ζ™abilun tana mata kitson.

Sun fito barandar waje, an shimfiΙ—a carpet sannan ta Ι—aukowa matar Ι—aya daga cikin kujerun dining, ga robar kayan magungunanta a gefe sai hira suke alamun matar ta iya hausa ana kitson, kuma har ya shigo da motarsa yayi parking basu tashi ba, sai da ya hawo kan barandar ne sannan ita Ι—in ta Ι—ago ta kalle shi da wadannan idanun nata da zuciyarsa bata manta su sannan ta furta kalmomi biyun da take binsa dasu kullum.

Sannu da zuwa.

A wannan ranar suka fara aikin don haka ya Ι—ebo gajiya bata wasa ba ga yunwar dake damunsa tun safe, saboda haka ransa ya taru ya Ζ™ara Ι“aci don a zatonsa mugun kallon da ya bita dashi lokacin da take tambayarsa gidan kitson zai sa ta cire maganar a ranta ashe ta riga ta Ζ™udirta niyyarta, don haka bai jira komai ba ya haΙ—e rai yace da matar ta tashi ta fitar masa daga gida. Yana iya tuno yadda jikinta ke rawa kafin ta suri robar magungunata ta fita babu ko waiwaye, ta biya ta ma kuΙ—inta ko bata biya ta ba, bai sani ba don kitson rabi kawai akayi.

Kuma duk yadda ya kai ga haΙ—e ransa yarinyar nan bata tsorata kamar matar ba, hasali itama haΙ—e fuskarta tayi a lokacin da yake tambayarta inda ta samo ta.

Fita nayi a titi na ganta zata wuce na tambayeta in ta san inda ake kitso tace min ai itama ta iya…

Waya baki izinin fitar?

Ya tambayeta a lokacin. Sai ta danyi diri-diri alamun mara gaskiyar da ba zai yarda da laifinsa ba sannan tace.

Ba kowa, ai Baddo bata nan balle in tambayeta, kai kuma ka fita…

Zuciyarsa ta daΙ—e tana bitar wannan maganar, tunaninsa ya daΙ—e yana Ζ™ara hasashen cewa akwai wani abu tattare da ita da yake Ζ™in barin kansa ya gani, kamar bata san komai ba, kamar wayonta bai kai don tazo taga bayansa ba…

Danja ta haska da alamar kore a daidai wannan lokacin, titin ta fara buΙ—ewa, motoci suka shiga motsawa har zuwa kan tasa, sai ya juya kan sitiyarinsa ya dawo kan titin da zai kaishi zuwa gidan.

STORY CONTINUES BELOW

Tun daga wannan ranar da yayi mata zancen baya son ganinta a falon bata Ζ™ara zuwa ba Ι—in, a yanzu iya haΙ—uwarsu in tazo wucewa zuwa kitchen ne kawai zai ganta ko kuma zata koma Ι—aki, kuma yana jin kamar bai kyauta ba, kamar maganar daya faΙ—a mata bata dace ba don har yanzu duk binciken da yake yi a kanta daga wajen baiwar nan basu taΙ“a nuna masa wani aibunta ba, baiwar ta sami Sadiyar kamar yadda tace amma duk yadda ta kai ga tambayarta abubuwa bata sami wata gamsashshiyar amsa daga gare ta ba.

‘Kamar a tsorace take ranka ya daΙ—e duk abinda na tambaye ta sai tace bata sani ba, daga Ζ™arshe ma roΖ™ona ta dinga yi in Ζ™yaleta.’

Abinda ta faΙ—a masa kenan kuma a wajenta bata samo komai ba, amma shi ya tsinci wani muhimmin abu da zai iya kafa hujja mai Ζ™arfi dashi, Tsoro. In har aminiyarta zata ji tsoron wani ya tuntuΙ“e ta da zancenta to akwai wani abu da suka yi kenan da suke Ι“oyewa wanda ba kowa ya sanshi ba, kuma babu gaira ba dalili yaji zuciyarsa na hasashen cewa koma meye wataΖ™ila ba sharri bane don har ga Allah ya fara yarda cewa zuciyar yarinyar nan babu mugunta a ciki, barta kawai da rashin kunyarta da kuma kuri kamar yadda kowa ya mata tambari, shi yasa a yanzu yake ganin wataΖ™ila waΙ—annan abubuwan itama Fulani ta hanga take ganin zata ci galaba dasu akansa.

Ya isa gidan yayi parking motarsa sannan ya fito zuwa ciki da Ζ΄ar sallamar da ya san ba mai amsata a kusa, kamar kullum ko’ina a gyare yake tsaf babu ko kwayar Ζ™ura, sai ya ajiye kayayyakin sa akan dining sannan ya zarce zuwa Ι—akinsa ya shiga wanka, bayan ya fito a daddafe ya shirya cikin wani farin sweatpant da lemon green riga, zafin da Ζ™irjnsa keyi ya fara Ζ™aruwa a lokacin don haka ya jawo bedside drawer dake Ι—akin ya fito da magungunan sa da ya kwana biyu bai sha ba, har zai rufe sai idonsa ya hango masa wannan maganin baccin da likitan nan ya bashi a Kano.

A yanzu kana buk’atar hutu ne sosai don magungunanka ma naga suna kan kari, ina ga dai zan baka maganin bacci ne yadda zaka huta Ι—in sosai…

Maganar daya faΙ—a ta haska a cikin kansa, sai kawai ya jawo shi ya haΙ—a har dashi, ya buΙ—e fridge Ι—in Ι—akin ya Ι—auko ruwa mai rangwamen sanyi ya kora su a lokaci guda sannan ya jingina da fridge Ι—in, zuciyarsa cike da taraddadi na tsoron fadawa wani hali da ya nemi mantawa dashi a cikin Ζ΄an kwanakin nan.

Zuwa can ya tuna da yin exercise Ι—in da likitoci suka gindaya masa cikin sharuΙ—ansu da cewar zai taimaka sosai wajen wartsakar da jijiyoyin dake yin rauni a zuciyar tasa, shi ma Ι—in ya manta rabonsa dashi, don haka ya miΖ™e da sauri ya nufi Ζ™ofar wani Ι—an Ζ™aramin Ι—aki dake manne da nasa inda ya maida shi kamar store, a ciki ya ajiye machine Ι—insa na ‘Treadmill’ wanda zai iya cewa baifi sau biyu ya taΙ“a amfani dashi ba, ya jawo shi cikin Ι—akin sannan ya hau ya fara binsa, gudun na Ζ™aruwa a hankali yayin da idonsa ke manne da bango, kwakwalwar sa kuma cike da abubuwan da yake son turewa, abubuwan da yake son mantawa dasu su bar cikin tunaninsa har abada ya zama kamar basu taΙ“a wanzuwa ba, ya koma kamar yadda yake a shekaru goma da suka wuce, wani Ibrahim da babu komai a gabansa illa fafutukar samun ribar kasuwanci kawai.

Akwai sanyi A.c a Ι—akin kuma bai wani daΙ—e yana yi ba sai ya fara jin iska na neman yi masa kaΙ—an, amma duk da haka bai tsaya ba sai da yaji ya fara tari sannan ya tabbatar cewa abinda yake ba daidai bane, ba exercise Ι—in ne ya dace a wannan lokacin ba don haka ya tsayar da injin har ya ragu da kansa sannan ya kashe.

Ai kuwa kamar dama jira ciwon yake ya tsaya, a take Ζ™irjinsa ya cika da wani irin zafin dake harbawa har bayan kansa da wuya da kuma kafaΙ—unsa, ya fara nufarfashi a hankali sannan jiri ya mamaye shi, da kyar ya daddafa ya koma kan gadon yana ganin komai bibbiyu yayin da yake jin kamar zai amayar da Ι—an abincin dake cikinsa.

Abinda yake gudu ne ya riga ya faru, Ζ™afafunsa suka shiga shure-shure akan bedsheet Ι—in cikin azabar da yake son dannewa, a lokacin ne kuma maganin baccin nan ya soma aiki sannan wani dunΖ™ulen abu ya tsaya a maΖ™ogwaronsa kafin wani irin mummunan bacci kuma ya Ι—auke shi zuwa wata duniyar da bata rage dukkan azabar da yake ji ba.

STORY CONTINUES BELOW

Daidai sanda limamin unguwar ya Ζ™walla kiran sallar magriba.

*

Jidda na zaune saman bathtub tana wanke Ζ΄an undies Ι—in da wannan mai siyar da magungunan ta siyo mata, mita take a cikin ranta har yanzu na cewar matar ta cuce ta, yaya za’ayi ace kayan dubu huΙ—u sune iyaka waΙ—annan? Bayan sau nawa tana gani idan Jamila ta shiga kasuwa da Ζ΄ar dubu biyunta sai ta dawo da kaya fal leda.

Ai dama tun daga lokacin data fita waje ta taro matar ta lura da alamun tayi niyyar cutar ta, musamman da suka shigo cikin harabar gidan taga Ζ™aton compound Ι—in nan da shuke-shuke, sai ta hau murmushi tana kara bayanin cewa ai kitso ba irin wanda bata iya ba, amma da yake itama Jiddan ba baya bace lokacin da tayi tunanin ta fara aikenta kasuwa kafin ayi kitson, sai ta fara tambayarta kuΙ—in magungunan dake kanta tukunna, aikuwa ta shiga lissafa mata kuΙ—in kowanne daban roba-roba irin ta ruwan nan kowacce da kuΙ—inta, sai da ta Ζ™arewa kayan kallo ta tabbatar ko ta Ζ™ara kuΙ—i lallai kayan bokitin nan zasu fi dubu goma sannan ta tuntuΙ“e ta da zancen zuwa kasuwar, tace Ζ΄an undies take so da kuma sauran tarkacen mata irinsu pad da razors.

Tana amincewa zata je kuwa ta kafa sharaΙ—in sai dai ta ajiye bokitinta taje ta dawo, fuskarta ta canja alamun ba haka taso ba amma dai ta karΙ“i dubu huΙ—un data bata ta tafi. Kuma tun daga sanda ta dawo da wata Ζ΄ar Ζ™aramar leda ranta ya bata cewa an daki hancinta kenan don ita kanta matar har da bayanin wai kayan Ikko tsada ne dasu ba kamar na sauran garuruwa ba.

Jidda tace ‘Haka ne’ kawai ta karΙ“i kayan amma ta kudirce a ranta cewar ta biya ta har kuΙ—in kitson kenan, don bata isa tace ta sake bata wani kuΙ—i ba. Shi yasa koda ‘Uban Ζ΄an zafin kan’ yazo ya koreta bata ji komai ba tunda dai anyi rabi, dama tana ta tunanin yadda zasu kwashe da ita in an gama kitson, damatsanta kawai take kallo tana hasashen idan Ζ™arfinsu zai kai Ι—aya don ta san ba abu ne mai wuya ta takale ta da dambe ba.2

Ta Ζ™ara zazzaga omo akan kayan tana dirje su, tunda tayi amfani da guda Ι—aya taji Ζ™aiΖ™aiyi shikenan ranta bai kwanta dasu ba duk da cewa kuwa daga leda ta buΙ—e su gabaΙ—aya. A lokacin ne kuma limamin unguwar ya Ζ™walla kiran sallar magriba, saboda haka ta shiga Ι—auraye su sannan ta shanya akan railer towel.

Sai da tayi alwala ta fito har zata tayar da sallar sannan ta tuna da Madaki, kusan kullum i-yanzu yake dawowa gida don baya taΙ“a bari magriba tayi masa a waje, sai ta matsa jikin window ta buΙ—e labulen jiki, a can parking space ta hango motarsa a ajiye, ta Ι—anyi mamakin yadda har motar ta shigo bata ji Ζ™arar bude gate ba kuma bata juyo motsinsa a cikin gidan ba.

Ta dawo ta tayar da sallarta sannan ta fita zuwa falo bayan ta idar, so take kawai taje tace masa sannu da zuwa sannan kamar kullum taga kayan da ya saka, shi yasa ta bar wani guntun wanke-wanke bata Ζ™arasa ba kar ma ya gane ba abinda ya fito da ita.

Ta isa falon daidai lokacin da Ζ™arar ringtone na wayoyi biyu ke tashi, suna zube akan dining tare da briefcase Ι—insa alamun ya dawo kenan, ta matsa jikin wayoyin ta kalli sunayen masu kiran.

Daya Habibu, daya kuma Janet, wato har dasu Janet a rayuwarsa kenan, ta tabe baki kawai sannan tayi kitchen, kuma sai da ta Ι“ata lokaci bayan ta gama wanke-wanken sannan ta fito da tunanin duk tsiya dai yanzu ta san ya fito falon yana aikinsa, amma abin mamakin shine har a lokacin babu shi sai ringtone Ι—in wani kiran daban saΙ“anin guda biyun dake ta faman Ζ™ara alamun shigowar messages. Ta sake wuce su ta koma Ι—aki.

Haka kurum sai taji jikinta wani iri kamar ma abincin ba dadi, haka ta dinga tura shi Ι—aya hannunta na kanannaΙ—e da Ζ™asan rigarta alamun ta Ζ™agara ta cinye, so take kawai ta gama ta koma falon taga ko zata ganshi, wannan ne kawai lokacin haΙ—uwarsu don haka ya kamata aΖ™alla ace ta ganshi Ι—in.

Lokacin da ta koma falon ta sake arba da kayansa maimakon shi sai da gabanta ya fadi, wayoyin sun daina Ζ™ara sunyi shiru suma kamar masu neman nasa, don kullum i-yanzu suna cikin hannayensa, sai ta wuce su ta koma kitchen Ι—in ta Ι—auraye plate Ι—inta sannan ta cigaba da tsaiwa a jikin sink Ι—in, jira take taji motsi ko yaya yake kafin ta fita amma har ta gaji babu sautin komai sai na fridge dake aiki.

STORY CONTINUES BELOW

Ta koma wajen dining Ι—in ta tsaya akan wayoyin tana Ζ™are musu kallo, kamar yana gidan kamar baya nan, ita bata taΙ“a shiga Ι—akinsa ba balle taje ta duba, me zai kaita ma? Bayan ko a falon ba son ganinta yake ba, amma ita bata son irin wannan abin shi yasa sanda tana yarinya ko wasan Ζ΄ar Ι“uya bata yi, wannan taraddadin na kaje ka Ι“oye kar a ganka ba sonsa take ba sam, sai kawai taja kujerar dining Ι—in ta zauna da tunanin ta inda zai fito. Tun tana zaune har ta jingina kanta a kusa da wayoyinsa, har akayi kiran sallar isha’i ba alamarsa sai kuma tayi tunanin ko tunda yaje masallacin magriba bai dawo bane don haka ta koma Ι—aki tayi sallarta, ta daΙ—e anan zaune tana Ζ΄an tunane-tunanenta kafin ta sake komowa falon.

Ƙafafunta suka ja birki tun kafin ma ta gama Ζ™arasawa ciki, wayoyin na ajiye, komai na inda yake babu kowa sai shirun da ya sake gauraye wajen, sai taji tunaninta ya tsaya cak, zuciyarta na sake tabbatar mata cewar da gaske wani abu ba daidai yake ba, kuma kafin ta fitar da komai a cikin kan nata Ι—aya daga cikin wayoyin ta shiga Ζ™ara alamun wani kiran, bata motsa ba balle taga wa ke kira wannan karon har ta katse, sai kawai ta juya ta koma ciki.

Ta nemi kan gadon Ι—akin ta kwanta, dogwayen jelar kalbar da tayi a inda ba’a Ζ™arasa kitson ba suka zubo kan fuskarta, ji take wani irin kaΙ—aici ya mamaye zuciyarta fiye da wanda take ji da rana ma idan baya nan. Idonta ya manne akan zanen wata Ζ΄ar flower ta jikin bedsheet Ι—in har bacci ya kamata, wani irin bacci da babu nutsuwa a cikinsa ko kaΙ—an, ga kwanciyar da tayi ma ba daidai ba, dole wajen Ζ™arfe goma saura ta farka a firgice.

Tana buΙ—e ido kuwa ta tuna komai, don haka ta miΖ™e da sauri ta nufi Ζ™ofa bata ko damu da duba lokaci ba balle Ι—aukan Ι—ankwalinta dake kan gadon, komai na falon kuwa ya sake tabbatar mata da cewar abinda ya faru ba mafarkinta bane, ta matsa ta danna Ι—aya daga cikin wayoyin dake yashe kan dining Ι—in, 15 missed calls idonta ya fara gani kafin ta lura da lokacin da take nema.

Goma saura minti biyar, a take sai zuciyarta ta bata shawarar cewa ta shiga Ι—akin nasa kawai ta duba don hakan shine fatanta na karshe, in har baya ciki sai ta fara neman mafita don al’amarin yafi karfinta kenan, in kuma yana ciki shikenan komai ta fanjama fanjam, yayi mata duk rashin mutuncin da yaga dama zai fi da wannan halin da take ciki.

Ta bi cikin koridon da Ζ™afarta bata taΙ“a takawa ba ko garin share-sharenta, ta isa ga kwallin Ζ™ofar dake fuskantarta fara Ζ™al sai Ζ™yalli take kamar kullum sai ya wanketa kafin ya fita. Da Ζ΄an siraran yatsunta ta kai hannu ta Ζ™wankwansa sau biyu, zuciyarta na gaya mata cewa da taji yayi magana ta juya abinta kawai lafiyarsa kalau kenan, sai dai shiru babu ko motsi balle maganar.

Ko dai yayi bacci ne? Ta tambayi kanta, kin taΙ“a ganin wanda ya kwanta baiyi sallar magriba da isha ba? Ko kin taΙ“a ganin ya bar wayoyinsa a falo ya kwanta? Wata zuciyar ta tambayeta, sai ta maida hannunta ta sake kwanΖ™wasawa, sau Ι—aya, biyu, uku babu amsa.

Sai kawai tasa hannu ta murΙ—a da niyyar ya san da gaske Ι—akin ake Ζ™wanΖ™wansa masa, amma ga mamakinta sai Ζ™ofar ta buΙ—e, gabanta ya Ι—an faΙ—i kafin tayi kasadar wangaleta haΙ—e da yin sallama. Duhu idonta ya fara gane mata kafin ta lura cewa akwai hasken wata Ζ΄ar Ζ™aramar fitila a can gefen gado, don haka bata lura da komai na Ι—akin ba amma ta hango alamar mutum kwance akan gadon, saboda haka ta sake yin sallama a karo na biyu amma banda sanyin A.c dake hurowa akan fuskarta ba abinda ya mata maraba.

Abu biyu ne suka haΙ—u suka kore taraddadin dake cikin ranta, na farko hasken Ι—akin da yayi wani irin ‘Dim’ mai shiga zuciya sai kuma alamun mutum data gani a kwance, duk da bata tabbatar shine ba amma dai ta san ba wanda zai shigo Ι—akinsa ya kwanta masa a gado, don haka ya Ζ™araci baccinsa tunda yau aljanun baccin ne suka zo, ai sun kyauta masa ma ya huta da azababben aikin da yake Ι—orawa kansa.

Ta jawo Ζ™ofar da niyyar rufewa ta koma lokacin da abin ya faru… Wani nishi dake Ζ™oΖ™arin yankewa da numfashi ya ratsa cikin kanta, wani irin sauti ne da take kwana tana tashi dashi a shekarun baya, sautin da ya zame mata tamkar wata hanyar sadarwa tsakaninta da mahaifiyarta duk sanda ciwonta ke Ζ™oΖ™arin tashi, ta riga ta haddace kowanne irin amo dake cikinsa.

STORY CONTINUES BELOW

A wancan lokacin ta farka cikin baccinta sannan cikin wani irin sauri ta isa shimfiΙ—ar mamanta, hannunta ya taΙ“a Ζ™asan hancinta sai ta kwance Ι—ankwalinta sannan ta zuge zip Ι—in rigarta…

Ƙafafunta suka Ζ™arasa cikin Ι—akin da azama, ta tsugunna gaban gadon, hannunta na dama ya taΙ“a Ζ™asan hancinsa da iska bata fita sosai, hannunta na rawa ta shiga Ζ™oΖ™arin Ι“alle maΙ“alli biyu dake gaban rigarsa…

A wancan lokacin hannayenta na rawa take lalube cikin tarkacen maganin mahaifiyar tata, ‘wannan maganin zaku dinga bata duk sanda ciwonta ke koΖ™arin tashi, sunansa aspirin…’ Haka mai siyar da magungunan ya faΙ—a musu…

Ƙafafunta suka shiga zagaye a Ι—akin tana bude duk drawer da ta gani don neman inda yake ajiye magungunansa, a saman wata chess drawer ta gano su, hannunta na rawa ta shiga lalube cikin kwalayen kuma cikin wata sa’a mai kyau sai ga irin maganin da take nema…

‘Mama, Mama…. Ga magani zaki iya tashi?’

“Zaka iya tashi? Ga magani…”

Muryarta ta faΙ—a a karye sanda ta dawo Ι—akin, baya ko jinta, kamar ma bai farka ba, Ζ™afafunsa motsi kawai suke saboda azaba. Sai ta manta komai ta hawo gadon gabaΙ—aya, ta tallafo kansa sannan ta Ι—an marmasa maganin kafin ta saka masa a baki kamar yadda likita yace ta dinga yiwa mamanta…

Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un…

Hauwa’u riΖ™e min hannuna,

Bani ruwa in sha…

Yi min fifita…

Kalaman mamanta suka haska a cikin kanta, sai ta kamo hannunsa na dama dake riΖ™e da zanin gadon, yatsunta suka ratsa a tsakanin zara-zaran nasa sannan ta damΖ™e su, sai ya buΙ—e bakinsa sosai yana koΖ™arin haΙ—iye maganin amma duk da haka bai farka ba, a cikin takardun dake gefen gadon ta jawo wani file ta shiga yi masa fifita duk da sanyi Acn dake hurawa a Ι—akin, sai kuma taji hannunsa na karkarwa a cikin nata, ta taΙ“a jikinsa taji yayi yayi zafi rau alamun har da zazzaΙ“i a cikin nau’ikan ciwon da yake ji…

Kuma kamar wancan lokacin da take jinyar mamanta, hawayen da bata san dasu bane a fuskarta yayin da tunaninta ya Ζ™ara rikicewa musamman da ta lura ya daina motsa Ζ™afafun nasa, hankalinta ya Ζ™ara tashi, bata san yaya zata yi ba in har tarihi ya sake maimaita kansa, in har wani dare da baza ta taΙ“a manta shi ba ya sake wanzuwa a rayuwarta, daren da mala’ikan Ι—aukan rai ya zare ran mahaifiyarta yayin da hannunta ke riΖ™e cikin nata…

“Dan Allah kar ka mutu, dan Allah…” Kalaman suka fito cikin karkarwar kukan dake Ζ™oΖ™arin neman Ζ΄ancinsa a bakinta.

‘Innalillahi wainna ilaihir raji’un… Jidda tashi ki fita, jeki buga gidansu Hasiya ki kira min Babansu…’

Kalaman da Aunty A’i ta gaya mata a wancan daren kenan, wata mata dake haya a gefen Ι—akinsu, haka ta gaya mata bayan ta shigo dakin maimakon tace ‘Mahaifiyar ki ta mutu Jidda..’

Kukan da take dannewa yaci Ζ™arfinta, ta Ζ™ara taΙ“a fuskarsa da Ι—aya hannunta sannan ta kara yatsunta a Ζ™asan hancinsa taji ko iska na fitowa, shirun da taji ya Ζ™ara hargitsa ta…

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un dan Allah kar ka mutu, dan Allah kar ka mutu Ibrahim…”

Ta cigaba da faΙ—in haka cikin kuka yayin da komai ya sake kwance mata kuma ta manta komai Ι—in, sai kawai ta sunkuya gabaΙ—aya ta kara kunnenta akan Ζ™irjinsa, a lokacin ne kuma abinda bata shirya masa ba ya faru, Ibrahim Ahmad Madaki yasa Ι—aya hannunsa ya jawota gabaΙ—aya ya naΙ—e ta cikin jikinsa sannan ya kai bakinsa daidai wajen kunnenta.

“Wa ya gaya miki mutuwa zanyi ne?”4

Muryar tasa daga can Ζ™asa ta fito, amonta a wahale cikin tsananin dauriyar da zaka tsince ta a ciki Ζ™arara kuma har a sannan bai buΙ—e idanunsa.

Jidda ta sandare yayin da wannan sassanyan Ζ™amshin turaren data daΙ—e da haddace shi a nesa ya shiga ratsa fatarta kota’ina haΙ—e da zafin zazzaΙ“in jikinsa, hawayenta ya Ι—auke a lokaci guda sannan wani abu kuma ya shiga tsargawa tun daga tafin Ζ™afarta har cikin yatsun hannunta, amma duk da haka ta kasa kore mamakin ‘dama yana jinta kenan tun Ι—azu yayi shiru?’

Jin bata motsa ba yasa a cikin baccinsa Madaki ya sake riΖ™e ta, sannan ya maida kansa saman gashinta, hancinsa ya sauka a tsakanin tsagun kalbarta… Wani abu da ya haddasa zuciyar tasa motsawa sannan Ζ™arfin bugunta ya karu a lokaci guda!

Sakan Ι—aya, biyu, uku…

Sakan Ι—aya, biyu, uku…

Kafin komai ya Ζ™are.

Washegari.

11:30 AM.+

Jidda ta tsoma slice Ι—in dafaffiyar doyar data dauko cikin Ζ™wan data fasa a wani Ι—an bowl sannan ta saka cikin man da yayi zafi a frying pan, Ζ™amshin albasar dake cikin kwan ya tafaso ya shiga hancinta amma duk da haka wanda take ji a jikinta yafi Ζ™arfi, sai ta sake shanshana fatar hannunta sannan ta kai Ι—aya hannun ma kan hancinta, ta rasa wane irin azababben turare ne wannan, ace har tayi wanka amma har yanzu bata daina jinsa ba, shi ba wani Ζ™arfi ba amma ya kama fatarta kamar tare aka halicce su.

Ba sonsa ne bata yi ba, abubuwan da yake tuna mata dasu ne bata so, farko shine can ‘Gida’ don a jikin layar nan data fara tone asirin Fulani ta sanshi da kuma sanda suka tone asiri na biyu ita da Sadiya. Biyu kuma shine ‘Jiya’ daren jiya da ya zama wani alaΖ™aΖ™ai a ranta ta kasa manta tarin abubuwan data fuskanta a cikinsa, mafi girma a ciki shine lokacin da Madaki ya riΖ™e ta.

Sai ta juya doyar zuwa daya Ι“angarenta zuciyarta na hasashen da ta bari ta daΙ—e a jikinsa ma shikenan ko wankan inji za’a mata ba zata taΙ“a fita ba, don sakan Ι—aya biyu, uku kawai akayi ta miΖ™e da sauri ta zare jikinta daga nasan tunda dama ba da Ζ™arfi ya rike ta ba, don me ma zai rungume tan ne wai? Har yanzu ta kasa lissafawa, yana fama da azabar ciwonsa sannan bai ko yi sallar magriba ba balle isha amma ya san ya rungume ta? Ita da ta san ba mutuwa zaiyi ba ma me zai kaita har kan gadonsa…1

Tayi tsaki a hankali tana tunanin Allah yasa yanzu ba zai dinga kallonta da wani abun ba, tunda dama tun farko ba yarda yayi da ita ba, amma sai Ι—aya Ι“arin zuciyarta ma yayi nasa tsakin, ‘Kar Allah yasa ma ya fasa kallon naki da wani abun, duk tsiya dai ai ya san taimako ne ya kai ki wajensa ba wani abin ba.’ A hankalin ta sunkuya ta kashe gas Ι—in sannan ta tsame doyar.

Tunda ta tashi bata ganshi bama, taji Ζ™arar motarsa wajen karfe bakwai na safe ya fita amma kafin goma ma ya dawo shaidar ba aiki yaje ba, kuma haka kurum taji yau bata son haΙ—a ido dashi, ya sha zamansa ai ya warke tunda har ya san ya rungume Ζ΄ar mutane, ta zubo doyar haΙ—e da Ζ΄ar sauce Ι—in da tayi sannan ta zauna kan island din kitchen Ι—in ta fara ci tana kurΙ“ar tean data haΙ—a. Sai dai bata ko yi nisa ba ta fara rage taunar tata a hankali tana kallon fuskarta ta cikin reflection na glass Ι—in teburin, me yasa ne take jin jikinta wani iri har yanzu? Me yasa ta kasa daina tuna abinda taji a lokacin daya riΖ™e ta? Wannan abun daya tsarga tun daga kafafunta har zuwa yatsun hannunta, me yasa yaΖ™i wucewa a ranta har yanzu?3

Allah zai saka mata! Ta ayyana hakan a ranta don jikin nata ba daΙ—i sam, kamar bata da Ζ™arfi ko kuma kuzari haka take ji tunda ta tashi kuma ita ba haka take so ba, lafiyarta Ζ™alau ta yini jiya kuma haka take son taji ta ma yau don taci burin yin wani alala mai kifi da Aunty Zainab ta taΙ“a koya musu.4

Da Ζ™yar ta iya cinye doyar nan ta tashi, ta Ι—auraye kayan data Ι“ata sannan ta fita zuwa falo, sai taji babu sharar da zata iya yi yau saboda haka ta nufi hanyar Ι—akin da take kwana tana fatan idan yaga dama ya kafa hujja da rashin sharar ya sallameta kowannensu ya huta. Ta nufi jikin dressing mirrow dake Ι—akin ta zauna akan stool dinsa tana kallon fuskarta.

Da wuya, Da wuya sosai wannan sabuwar rayuwar da take ciki, ko kwalli ta manta rabonta da tasa a idonta balle aje ga sauran abubuwan da ba zata iya lissafo su ba, musamman karatun Alqur’ani tunda yanzu babu islamiyya balle makarantar dare. Idonta kai kan jelolin kalbarta da suka fito ta gefen Ι—ankwalin rigar dake jikinta, sai kwakwalwarta ta sake tuno mata da sanda ya riΖ™e ta, sanda taji alamun hancinsa a tsakanin kitson, wani sanyi ya sake ratsa ta, taji kamar zazzaΙ“i ne ma ke shirin kamata. Allah sarki Baddo! Da tana kusa da ita da tuni ta jiΖ™a mata Ζ΄ar tazargadi ko sabara tace ta fara sha a matsayin rigakafi.4

STORY CONTINUES BELOW

Sai kawai ta zame Ι—ankwalin ta fara tsefe kalbar, watakila in babu ita zata daina wannan tunanin, don a yanzu gani take indai dama haka zaman auren yake to gaskiya ita bata ga wani abin so a cikinsa ba, gwara a Ζ™yale ta tayi ta gararambarta a gari da jawowa zuciya abinda zai dame ta, don tunda Mai martaba ya furta kalmar auren nan akanta farin cikinta ragagge ne, ta rufe idanunta a hankali tana zare kitson kalbar yayin da wani abu kamar Ζ™walla ya taru a cikinsu.

‘…wata Ζ™addarar…’

Haka mahaifiyarta tace.

*

‘… dan Allah kar ka mutu, dan Allah kar ka mutu Ibrahim…’

Kalaman dake maimaitawa a Ζ™waΖ™walwar Madaki kenan tun daga lokacin ya iya farkawa wajen shida na safiya har zuwa yanzu, yadda muryarta ke karyewa, yadda take magiyar, da kuma yadda harafan sunansa ke fitowa a sautin muryar…

A daddafe ya jero sallolin da ya rasa tun daga daren jiya, sannan ya haΙ—a da nafilfili na neman yafiya a wajen Allah duk da bai yi hakan da gangan ba don ko a musulunce an Ι—auke lokacin sallah akan masu irin uzirinsa na halin rashin lafiya da kuma bacci.

Kuma har yaje asibiti ya dawo wajen goma saura yana iya tuna komai daya faru sama-sama, yadda ta bashi maganin nan da yadda ta tallafi kansa cikin wani irin riΖ™o da yaji ya fara samun iska fiye da yadda yake kwance, shi yasa har yanzu kwaΖ™walwar sa ta kasa lissafin yadda akayi ta san me ya same shi har kuma da maganin da ya kamata ta bashi a lokacin, tunda ya san ita ba likita bace kuma ya san cewa kaf duniya daga shi sai Mubarak suka san ciwon nasa, abu ne da yake Ι“oye shi a kullum don baya so ko kaΙ—an duniya tayi masa kallon nakasu kotawanne Ι“angare.

Yafi son har ya Ζ™are rayuwarsa ya zama cikin sahun irin jajirtattun mutanen da za’a iya kafa misali dasu har su zama abin kwakwayo ga wasu, bayan haka kuma yana daΙ—a Ι“oye shi ne saboda koda wasa kar a sami wanda zai canja ra’ayinsa ya nesanta shi daga wani guntulallen tarihi da yake ganin shi kaΙ—ai ya mallaka a duniyar nan.

Amma sai gashi yarinyar da bai taΙ“a yiwa kallon abu mai muhimmanci ba, yake ganin ko plain sheet d’in kan teburinsa ta fita daraja a rayuwarsa ta ganshi a wannan halin (the worst side of him) abinda ko Mubarak bai taba gani ba, kuma har ta taimake shi da wani abu da yayi Ζ™aranci a rayuwarsa ‘Kulawa’ musamman a jinsi na mace tunda ko ‘Uwa’ bai taba sanin yaya take ba.

Ya tuno yadda ta dinga kuka cikin dishi-dishin hoton da yake gani a lokacin har da hawaye tana roΖ™onsa kar ya mutu, ganin tsananin ciwon nasa tayi ko kuma wani ne ya bata bayanin cewa mutuwar zai yi? Ya kasa tantancewa, abinda ya sani kawai shine, karo na farko a rayuwarsa yaji wata daraja ta ‘Mutum’ ta ratsa shi, yaji kamar yayi tasiri a wata zuciyar da zata yi alhini in har babu shi Ι—in, ba kamar a baya da yake ganin Mai martaba da Mubarak kawai ya mallaka ba, wasu mutum biyu da su duka yake ‘substitute’ a rayuwarsu ba ‘priority’ ba.

Yasa towel ya tsane ruwan dake fuskarsa bayan ya fito daga wanka, wani tunani ya haska a cikin idanunsa, sai ya wular da towel Ι—in kan gado sannan ya nufi Ζ™ofar Ζ΄ar Ζ™aramar walk-in wadrobe Ι—insa, har buΙ—e Ζ™ofar sai kuma ya tsaya ya Ι—ago da tafukan hannayensa sama yana kallonsu, wasu Ζ΄an sakanni yake tunawa da yayi wani abu bada niyya ba sai don ya katse magiyarta dake damunsa a lokacin, ba zai iya magana da Ζ™arfi ba shi yasa har ya jawo ta jikinsa don taji shi sosai, sai dai ya kasa manta hakan, ya kasa gayawa zuciyarsa ta yarda cewa hakan ba wani abu bane don kuwa wani abun ne, karo na farko a rayuwarsa yayi experiencing wata pleasure da bai taba saninta, Ζ΄an sakanni kawai amma yana jin kamar an saka soso da sabulu ne an wanke wani Ι“ari na zuciyar tasa.

Da za’a hasko masa hakan a farkon zamansa da ita watakila zaiyi dana sani sau dubu, amma a yanzu babu ko Ι—aya a ransa, hasalima wani Ι“ari na tunanin nasa tuhumarsa yake da dalilin da yasa ya bari ta tafi a lokacin, Ko ba komai kana buΖ™atar wannan kulawar dake cikin idonta. Zuciyar tace.

STORY CONTINUES BELOW

Ya fito daga wajen bayan ya shirya cikin wani light brown yadi mai irin sealed aikin da ake masa a kullum, kai tsaye ya fita zuwa wajen dining inda ya san ya bar kayansa jiya, suna nan kuwa a zube kamar yadda ya barsu, ya buΙ—e wayar farko dake Ι—auke da personal layinsa ya tarar da rututun missed calls Ι—in da baya mararin ganinsu, saboda haka yayi clearing Ι—insu kawai sannan ya nemo nambar Mubarak.

“Ka gaya min cewa baza ka sami damar zuwa office yau ba dan Allah.”

Cewar Mubarak Ι—in muryarsa Ι—auke da tsananin raha tun kafin ma ya bari yace wani abun.

Madaki ya murza yatsun hagunsa cikin tafin hannun dake Ι—ore a saman table Ι—in sannan kai tsaye ya bashi amsa.

“Eh, bana jin zan shigo.”

Yana iya jiyo wani sautin murmushin nasa kafin yace.

“A huta lafiya Mdee, kar ka damu da komai. We are here.”6

Ɗib! Kiran ya katse ba tare da ya tambaye shi dalilin rashin zuwan nasa ba, sai ya girgiza kansa kawai yana fatan shiriya wa Mubarak kafin ya jawo sauran wayoyin, kuma ba tare da ya duba halin da suke ciki ba ya danne switch Ι—in kowacce ya kashe, A yau zaiyi forcing kansa ya samu hutun da likitan yayi ta jaddada masa tare da Ζ™orafi, don haka yake fatan ko bai zauna haka ba ya Ι—anyi wani abun daban da ba aiki ba ko zuciyar tasa ta yi refreshing wa sababbin abubuwa.

Banda Iphone Ι—insa, ya jefa sauran wayoyin duka cikin briefcase Ι—insa sannan ya nufi kitchen saboda azababbiyar yunwar da yake ji dunΖ™ule a cikinsa tun jiya, ga kuma jiri-jirin da bai gama sakinsa ba. Yana taka cikin kitchen Ι—in Ζ™amshin wani abu mai daΙ—i ya ziyarci hancinsa tun kafin ma yayi la’akari da tsaftar wajen, don komai a shirye yake tsaf duk da alamun cewa anyi girki, bai sa ran ganin mai girkin ba dama tunda ya san ba lallai ta fito ba in taga yana nan, amma shi zai je ya neme ta ai, ko yaya ne ya kamata ya nuna godiyarsa kafin ya san yadda akayi ta san lalurarsa.

Ya buΙ—e drawer kayan tea lokacin da idonsa ya kai kan wani flask a gefe, sai kawai ya kai hannunsa ya buΙ—e shi, yawunsa ya tsinke tun kafin ma ya gama jin Ζ™amshin sauce da kuma soyayyar doyar data sha suyar Ζ™wai a ciki. Ya sani cewa a yanzu abinci irin wannan yake buΖ™ata ba tea Ι—in ba, tunda rabonsa da cin wani Ζ™waΖ™Ζ™waran abu ba zai iya tunawa ba, amma sai ya mayar da murfin ya rufe shi sannan ya shiga Ι—ebo gwangwanayen su madara da Nescafe yana fito dasu.

Idonsa ya sake komawa kan food flask Ι—in, abincin ya bashi sha’awa gaskiya sai dai kuma baya tunanin ma zai iya ci tunda bai sani ba ko ta saka gishiri da yawa tunda shi baya cin abinci da gishiri, sai kuma wata zuciyar ta bashi shawarar cewa ya Ι—anΙ—ana yaji in da gishirin, don haka ya sake buΙ—e shi ya Ι—auki guda Ι—aya yasa sauce Ι—in nan ya kai bakinsa.

Allah ya sani ko da gishirin, to shi kam bai ji ba, wani irin daΙ—i ne mai barazanar motsa kunnuwa ya ziyarci dukkan Ζ™ofofin Ι—anΙ—anonsa, yasa hannu ya sake Ι—aukan wata ya cinye tas, sai kuma zuciyarsa tace ai ko zai Ζ™ara biyu ma ba lallai ta gane anci ba don haka ya Ζ™ara Ι—aukan biyun kuwa yana kallon ragowar na ciki, kamar ya Ζ™ara kuma sai ya rufawa kansa asiri ya mayar ya rufe sannan ya haΙ—a tea Ι—in nasa.7

Ƙarar knocking daga can waje ta katse Ζ™oΖ™arinsa na zama kan island Ι—in, saboda haka ya ajiye kofin sannan ya nufi hanyar fita har zuwa can gate din, wani maΖ™ocinsa ne kamar yadda ya zata don dama kwanaki sun fara magana akan cewar zasu haΙ—a kuΙ—i a siyo Ζ™asar Birji a zuba a layin nasu saboda yadda caΙ“in damina ke Ι“ata wajen.

Da kyar ya iya tsaiwar mintunan nan har suka gama tattaunawa kan cewar za’ayi aikin weekend don haka kowa ya turo da contribution Ι—insa kafin ranar. A haka suka yi sallama sannan ya juyo ya dawo ciki.

*

Jidda taji sanda ya fita, amma har ta gama wankin toilet dinta bata ji dawowarsa ba don haka ta fito da niyyar zuwa kitchen ta dauki ragowar doyarta, a lokacin jikinta ya fara dumi sosai alamun da gaske zazzabi ne ke shirin kamata, don haka so take kawai taje ta dauko abincin da ruwa sannan ta dawo ta Ζ™udunduna kan gado ta yadda duk sanda taji yunwa ba sai ta fita har zuwa kitchen Ι—in ba. Sai dai me?

STORY CONTINUES BELOW

Tana buΙ—e Ζ™ofar kitchen din Madaki na zaune kan island din yana kurΙ“ar shayinsa, babu waya balle computer a gabansa don haka tana bude kofar idanunsu suka hade guri daya, taji kamar ta juya ko kuma ta Ι“ace kawai ma zai fi sauki… Amma kallonta yake, hasken rana ya haske fuskarsa tas tare da zara-zaran yatsunsa da suka nade jikin kofin, yayi kyau sosai! Kamar wani kyakkyawan Ι—an jarida dake Ζ™oΖ™arin fara gabatar da shirin safe (Morning show) zuciyarta ta shiga harbawa fiye da Ζ™ima, wa zai taΙ“a yarda da ita in har tace wannan mutumin ya riΖ™e ta a daren jiya? ta haΙ—iye yawu da Ζ™yar sannan ta tako ciki ba tare data rufe Ζ™ofar ba.

“Barka da safiya.” Ta faΙ—a a hankali har a lokacin tana jin tasirin idanunsa na shiga jikinta tun daga can.

“Kin tashi lafiya?”

Kamar da wasa sabuwar amsar ta fito maimakon yadda yake amsawa da ‘Yawwa’ a kullum.

Sai da ta Ι—an tsaya da tahowar da take yi sannan ta iya amsawa.

“Yaya jikin ka?” Ta sake tambaya a hankalin, taso tayi shiru ma kawai ta Ι—auki flask Ι—inta ta fita amma sai ta kasa hakan saboda bai dace ba.

“Alhamdulilah.” Amon muryarsa mai zurfi ya amsa a lokacin da ta wuce shi ta isa wajen flask Ι—in nan.

“Yaya akayi kika san bani da lafiya?”

Kamar saukar aradu, Jidda taji tambayar tayi wani rugugi a cikin kanta don bata taΙ“a tsammanin zaiyi mata tambayar a yanzu ba, sai ta sake haΙ—iye wani yawun cikin maΖ™ogwaronta kafin ta amsa.

“Naga ban ganka bane tun magriba shine naje na duba…”

Ta faΙ—i hakan kuma sai taji banbarakwai, ita bata iya Ζ™arya ba da cewa zata yi gobara ce ta tashi taje kiransa ya kashe, in ba haka ba ai cewa zaiyi ta damu dashi ya sake samun hanyar wulaΖ™anta ta, saboda haka ta Ζ™ara da…

“… Saboda kar in Ζ™ulle gidan kazo ka kwana a waje.”

Saura kaΙ—an murmushi ya suΙ“uce a fuskar Madaki jin hakan, wato shi da gidansa amma shi za’a Ζ™ullewa Ζ™ofa har ya kwana waje. Sai ya gyaΙ—a kansa kawai, tana tsaye a bayansa har yanzu.

“Ya akayi kika san abinda ya same ni?”

Tayi shiru bata amsa ba, har zai sake maimaita tambayar sai tace.

“Wannan file Ι—in na Ζ™asan table Ι—in nan na gani ance baka da lafiya.”

Kafin yayi nazarin wane table take nufi, idonsa ya kai kan wani file dake ajiye a Ζ™asan glass na island Ι—in, sai ya zura hannu ya jawo shi cikin santsin glass Ι—in, ya riga ma ya san menene don kusan shekarsa Ι—aya kenan a wajen, tun lokacin da asibitin da yake zuwa a baya suka yi katoΙ“arar canja masa report Ι—insa dana wani tsoho mai shigen sunansa ‘Ibrahim Adam’ suka bashi result Ι—in tsohon a maimakon nasa, shikenan hankalinsa bai Ζ™ara kwanciya da asibitin ba ya canja shi, daga bayanin har hoton zuciyar dake jiki ba nasa bane shi yasa ma bai Ζ™ara bi ta kansa ba ya barshi a kitchen Ι—in tun wancan lokacin.4

Saboda haka ya cigaba da kallon paper yana tunanin wato abinda ta gani kenan tayi tunanin mutuwa zai yi har take fitar da hawayenta akan hakan, sai yaji tausayinta ya ratsa zuciyarsa sannan wani Ι“angare a cikinta ya Ζ™ara yarda cewa wataΖ™ila da gaske ne babu mugunta a zciyarta kamar yadda yake hasashe, bai lura ba har tazo ta wuce wajen fridge ta Ι—auko ruwa sannan ta nufi hanyar fita, sai jin muryarta yayi daga can bakin kofa tana tambayarsa.

“Akwai Alqur’ani anan gidan?”

Ya Ι—ago ya kalle ta a hankali cikin nutsuwa, itama shi take kallo alamun har zata fita ne ta dawo, a lokaci guda idonsa ya hango masa wani abu da bai gani ba tun bayan shigowarta, don sai yanzu ta kalle shi sosai, fuskarta tayi wani irin fayau! Sannan idanunta sun zurma ciki kaΙ—an.

STORY CONTINUES BELOW

Kallonsa Jidda ta cigaba da yi, bai ce komai ba, ko dai tambayar bata dace bane? To ai bata san me zata ce ba bayan hakan. Idanunsa akanta, waΙ—annan oily eyes Ι—in…

“Me ya same ki?”1

Maimakon amsar wata tamabayar da bata taΙ“a tsammaninta ba ta fito cikin amon muryarsa, sai a lokacin ta lura kuma kallon nazari yake mata.

“Baki da lafiya?” Ya kara tambaya yana kallonta, sai ta girgiza kanta.

“Bana jin daΙ—i ne kawai.”

Tana kallonsa ya ajiye file Ι—in nan sannan ya taso ya taho har gabanta, kamar ta juya kafin ya Ζ™araso amma ta daure zuciyarta ta tsaya Ι—in, ai dai duk tsiya tana da ragowar Ζ™arfin da ko shaΖ™e ta zai yi zata Ζ™waci kanta.

Fuskarsa take kallo har ya tsaya a gaban nata, don haka bata ga sanda ya Ι—ago hannunsa ba sai kawai jin tafin hannayen nasa tayi duka biyun a Ζ™asan haΙ“arta, dogwayen yatsunsa suka ratsa tsakanin kunnuwanta ta kowanne Ι“angare sannan sassanyan Ζ™amshin turaren da take yaΖ™i dashi a jikinta ya sake ratsa Ζ™ofofin hancinta. Ta tabbata yaji yadda ta zuΖ™i numfashi cikin Ζ™irjinta don ko ba ji ba ma faΙ—awar da wuyanta yayi zai fallasa hakan.

“ZazzaΙ“i kike yi?”

Ya furta tambayar a hankali da wani irin amo daya haddasa diri a Ζ™irjinta, dole ta sunkuyar da idanunta kasa tana tunanin shima hannayen nasa har yanzu da Ι—umi alamun zazzaΙ“in jiya bai gama barinsa ba.

Taji numfashinsa yayi dab da fuskarta saboda haka ta kara faΙ—awa cikin ruΙ—ani mai haΙ—e da mamakin Meya same shi ne daga jiya zuwa yau? Anya kuwa a cikin hankalinsa yake? Ko dai fuskarta ta canja masa da wata ne? taso tayi magana amma tasirin hannayen nasa a jikinta ya hana ko iskar kirki fita daga Ζ™irjinta, so take tace ya daina, ya janye hannunsa, ya daina taΙ“a ta ko kuma ita ta matsa, amma Ζ™afafunta suka manne a wajen, wani abu dake tafiya tun daga yatsun Ζ™afarta har cikin kwaΖ™walwarta ya narkar da duk wata tsiwa da kurinta, ya mantar da ita cewa shine silar koma meye ya same tan, ya kasa hango mata cewa zata zo ta cigaba da jinyar zuciyarta ne da zarar ya janye hannun nasa…

“Baki da lafiya amma baki sani ba?”

Ya sake tambaya da wani irin husky tone yana motsa yatsunsa a bayan kunnen nata, Jidda taji kamar mafarki take yi, kamar tana yawo ne a gajimare, kuma abinda take ji Ι—in yayi yawa har yayi nasarar tuna mata da cewar wannan gaibu ne, Madaki bashi da asara kotawanne Ι“angare a rayuwarsa, in ta bari ya rinjayi zuciyarta, duniyarta ce zata yi baΖ™i ita kaΙ—ai don misalin jiya kaΙ—ai ya ishi hankalinta, saboda haka ta tattaro dukkan Ζ™arfinta ta sake damΖ™e flask Ι—in doyarta sannan tayi yunΖ™urin matsawa baya amma sai ya hana ta, ya sake riΖ™e fuskarta sosai cikin hannayen nasa, sai ta Ι—ago ta kalle shi da tsananin mamakin dake haskawa a idanunta kafin kalamansa na gaba suyi barazanar yankewar numfashi a Ζ™irjinta.

“It’s my time to heal you…”16

(Lokacina ne da zanyi taki jinyar…)

***

Ƙauyen MaΙ—iga.

“Hajiya kin tabbata kuwa bamu Ι“ace hanyar nan ba?”

Sani Direba ya tambaya a lokacin da motarsu ke Ζ™ara luluΖ™awa cikin wani Ζ™ungurmin daji da basa ganin komai sai ciyayi da tafasar dake faman dukan motar kotawanne Ι“angare, Ζ™ararsu kake ji kawai fat!fat! Musamman a gilashin motar.

Jakadiya Bbba ta juyo ta kalle shi, ranta a Ι“ace fuskarta a haΙ—e tamkar baΖ™in hadari.

“Yau muku fara zuwa ne Sani? Ko kuwa yau ka taΙ“a bin hanyar? Inace har ita Fulanin da kanta ka kawo wajen nan? Shine har kake tambaya ta? Idan baka gane ba sai ka juya, mu koma ka gaya mata ub*n daya mantar da kai hanyar.”

STORY CONTINUES BELOW

Muryarta ta fito a kausashe cikin wani irin amo dake shaida tsananin Ι“acin rai da Ζ™unci, sai Sani Direba ya jinjina kansa daga can gaba ba tare da ya juyo ba, shi yayi tambayar ne da tunanin ta zama mafarin hira a tsakaninsu tunda yaga tunda suka taho bata ce komai ashe cibi ya taΙ“o bai sani ba.

Jakadiya Babba ta Ι—auke kanta ga barin kallonsa, taso ya sake cewa wani abun ta Ζ™ara yaΙ“a masa wata maganar ko ta samu baΖ™in cikin dake ranta ya gushe, don tun daga wannan ranar data koma Ι—aki don Ι—auko jakar nan ta tarar da jakar wani Ι—an bautar Ζ™asa a maimakon tata, ta tabbatar haske ya disashe daga duniyar ta kenan, ga dai jakar a jiki sak tata ce amma data zazzage ta tas babu komai sai kayayyakin maza da kuma wasu tarkacen takardu, tayi tunanin duniyar nan amma Ζ™waΖ™walwarta ta kasa gane yadda bata gane cewar ba jakarta bace har aka je aka dawo.

A wajen check-up Ι—in nan ne aka mata canje tabbas ta sani don bayan an fito da kayayyakin su, an haΙ—a tare dana wasu motocin. Kuma Allah shine shaidarta ta tsaida idonta sosai har aka zo kan nata kayan kuma tana kallo aka saka jakar a motarsu, don haka a wannan lokacin duk tunanin duniyarta ta ta kasa gane sanda abin ya faru, sai daga baya data zurfafa bincike a cikin kan nata sannan ta tuno cewa wani soja ya gifta ta gabanta lokacin da aka Ι—ago jakar da tayi mata gizo taga kamar tata ce, har ta Ι—aga hannu aka sanya ta a cikin motar.

Ta tuno kuma tashin hankalin data shiga lokacin da ta iya tattaro dukkan dauriyarta ta shaidawa Fulani cewa anyi mata musanyar jaka data wani Ι—an bautar Ζ™asa a wajen da sojoji suka tare su… Kallonta Fulani ta dinga yi a lokacin kamar ta yarda cewa ciwon hauka ya fara kamata kafin bakinta ya suΙ“uce da wannan sassanyan murmushin nata, murmushin da a yanzu take ganin kamar shi zai zama na Ζ™arshe da zata sake gani a fuskar uwargijiyar tata, don in har ba’a sami jakar nan ba Allah ya sani suna cikin mummunan hatsarin da ba zata iya hasaso Ζ™arshensa ba.

‘Mun bar fagen wasa Jakadiya, je ki Ι—auko min jakar nan don mu fara aiwatar da shawarar taki, bana son in sake asarar lokaci ko ya yake.”

Abinda Fulani ta faΙ—a a wancan lokacin kenan kafin ta gyara tsugunnonta cike da tashin hankali sannan ta rantse mata da Allah cewar babu jakar… Rantsuwar data zama silar shigarta tashin hankalin da take fuskanta kwana biyu, don Fulani rufe idonta tayi daga duk wani tarin alkhairin da ta taΙ“a yi mata ta gaya mata maganganun da bata jin tsawon rayuwarta kaf ta taΙ“a jinsu, da sharaΙ—in cewar zata iya zama sanadin lalacewarta a duniya in har bata nemo jakar nan ba.

Ta cije leΙ“Ι“enta kaΙ—an tana cigaba da kallon ciyayin dake duka da kartar motar tasu kotaina, a yau da safe ne Fulanin ta same ta da cewar ta taho wajen wani tsohon bokanta ‘Mai babban Ι—aki’ data bar mu’amala dashi tun shekarun baya don ya taimake su da gano inda jakar take tun kafin lokaci ya Ζ™ure, tunda ta raina duk Ζ™oΖ™arin da ita take na neman jakar ba tare da Ζ΄anuwan yarinyar nan sun fahimci komai ba, tace idan shi Mai babban Ι—aki ya shaida musu inda za’a ganta komai zai fi sauΖ™i suje su karΙ“o ba tare da kowa ya sani ba sannan ba tare da sun Ι“ata lokaci ba, dalilin wannan tafiyar kenan! Suka rabu kowa ransa a Ι“ace da Ι—ayan.

Kuma basu suka isa Ζ™auyen MaΙ—iga ba sai yamma sosai, MaΙ—iga wani Ι—an Ζ™aramin Ζ™auye ne dake tsakiyar dokar daji inda bokan yake, kwata-kwata mutanen dake cikinsa baza su fi Ι—ari ba, don ance ma Ζ΄anuwan bokan ne da iyalansa kawai. Motarsu tabi har cikin lungun da tafkekiyar rumfar bokan take tsaye Ζ™iΖ™am daga Ι“angaren gabas, kamar kowanne zuwanta idon Jakadiya Babba ya hango mata dogon layin mutane dake tsugunne fal, maza da mata, manya da samari gasu nan duk a tsugunne kowanne fuskarsa na nuna alamun gajiya, kuma har zuwa yau ta kasa daina mamakin ta ina waΙ—annan mutanen ke zuwa, don a baiyane yake cewa da yawansu basu da abin hawa, don haka ta kasa hango ta yadda kafa zata keto dasu cikin wannan Ζ™ungurmin dajin. (… Idan imani ya gushe ba abinda baya yiwuwa a wajen bawa.)

Sani Direba ya fita ya kira Ι—aya daga cikin muΖ™arraban bokan dake tsaye a harabar wajen, tana ganin sanda ya nuno masa motar da take ciki haΙ—e da wata magana da bata ji ba amma ta san me yace, sai saurayin ya juya har da Ι—an gudunsa ya shiga rumfar bokan nan ta wata hanya daban da ba ta nan mutane ke shiga ba.

STORY CONTINUES BELOW

WataΖ™ila zaman minti biyar ko fiye kaΙ—an, sai gashi ya fito yayi wa Sani magana, tana ganin haka tun kafin Sanin ya fito ta damΖ™o ledar dami-damin kudin dake gefenta ta fita, kuma bata ko saurari Sanin ba ta wuce kai tsaye zuwa wajen rumfar, mutanen nan suka dinga Ι—ago kai suna kallonta amma ba mai cewa komai, to suma ce mana, ai sun san a inda suke.

“Nasara da Ι—aukaka gare ka suke Mai Babban Ι—aki!”

Ta furta hakan tun kafin ta gama shiga cikin rumfar.

Dattijon dake zaune kan wata fatar kada sannan tsakiyar hayaΖ™in dake tashi daga tandunan gabansa ya kyalkyale da wata irin dariya yana kaΙ—a kai kafin muryarsa ta fito da Ζ™araji.

“Nayi kewar wannan kirarin Rakiya, nayi kewarsa!”

Jakadiya Babba ta nemi waje ta zauna sannan tace.

“Kamar yadda ni da uwargijiyata muka yi kewarka Babba mai ikon nasa….”

“Wannan kuma Ζ™arya kike…” Ya katse ta tun kafin ta karasa yana mai Ι—aure fuskar tasa a lokaci guda.

“… Ƙarya kike Rakiya, ku da kuka canja ni saboda son zuciyarku, kuka raina aiki na, kuke ganin kamar zamanina ya dusashe kuka kai kanku wajen Ζ™yalΖ™yalin banzan da ba zasu taΙ“a Ι—orewa ba, yanzu sai in lissafo miki yawan adadin jahilan da kuka ziyarta bayan barinku wajena. Ko kuwa kin zata ban san me ya kawo ki bane? Rana taso ta kwace muku game da aikin wani shine kuka lallaΙ“o ta turo ki don ni in gyara, to wayonku yayi kaΙ—an kuma Ζ™aryarku tayi Ζ™arya, Mai Babban Ι—aki baiyi wannan lalacewar ba! Ba’a karaso ranar da duniya zata tozarta ni irin haka ba!”

Yayi maganar cikin Ι—aga murya da fushin dake fesowa daga zuciyarsa, amma Jakadiya Babba gyara zamanta kawai tayi ba tare da taji ko Ι—ar a ranta ba, sannan ta shiga magana.

“Rantsuwa dubu zancenka haka yake Mai babban Ι—aki, maganganun ka haka suke, kuma gaskiya ne mun yi kuskure mai nasara, kuskure mai muni amma ka sani cewa mu masu rauni ne waΙ—anda basu cika da cikarka ba Mai babban Ι—aki, mun yi mantuwa! Mun mance cewa duka wata nasara da ikonka take wanzuwa, mun mance matsayinka wanda da za’a buΙ—e shi sai zukata sun girgiza, mun mance cewa kaine mai bawa duk wanda yazo wajenka nema, mun manta kaine mai buΙ—e dukkan abinda aka Ζ™ulle, mun manta kaine asirin da ba za’a iya tona shi ba Mai babban daki, madafar masu rauni irinmu.2

Kayi mana afuwa, ka saya mu cikin afuwarka don kaine mai garkuwar da zata iya kare mu, uwargijiyata ta turo ni da ban haΖ™uri a yau, muna roΖ™on ka ji Ζ™anmu ka yafe laifinmu don mun fahimci kai kaΙ—ai ne tabbacin da zai iya bamu tabbatarwa, gamu yau mun dawo Ζ™ofarka Mai nasara, kofarka wadda na san bata Ζ™ullewa ba ga masu buΖ™ata irinmu…!” (A’uzubillah)

Wata irin dariya da Bokan ya karaΙ—e wajen da ita, sai da taso ta jijjiga rumfar da suke ciki, sannan ya kaΙ—a kansa dama da hagu cikin tsananin nishaΙ—i tamkar mai rangaji kafin muryarsa ta fito, wannan karon a sauΖ™aΖ™e.

“Shi yasa nake mararin zuwanki Rakiya ko ba komai akwai ki da kalaman da zasu sanyaya zuciya.”

Jakadiya Babba tayi murmushi kaΙ—an ganin haΖ™anta ya cimma ruwa sannan tace.

“Ba kalamai bane mai nasara, tambari ne na girma da Ι—aukakar ka, mu namu aikin biyawa ne kawai don Ζ™ima da darajarka ta cigaba da Ι—aukaka har gaban abada.”

Mai babban daki ya sake wata shu’umar dariyar sannan ya faΙ—i tambayar da take ganin samuwarta shine kaΙ—ai sanadin sake samuwar haske a rayuwarta.

“Me ya kawo ki Rakiya?”

Sai ta gyara zama, sannan cikin raunanniyar murya tayi masa bayanin komai, tun daga karΙ“o asirin nan, da sharuΙ—ansa, da haΙ—a tafiyarsu zuwa Lagos, da Ι“atansa da kuma halin da suke ciki a yanzu.

STORY CONTINUES BELOW

“Komai mai sauΖ™i ne…” Muryarsa ta fito bayan ya shafe mintuna yana lalube cikin wata randar jini dake gabansa.”

“Jakar tana cikin masarautar taku a yanzu haka…”

Kafin ta Jakadiya Babba fitar da tsantsar mamakin dake nunawa a fuskarta ya cigaba da magana.

“A wajen da sojoji suka tsayar daku canjin ya faru, akwai jakunkuna guda biyu irin taki, Ι—aya ta Ζ΄ar uwar yarinyar da kuka aura masa ce mai suna Jamila, Ι—aya kuma ta wani matashi ce dake bautar kasa a garin, an baki ta matashin, an bawa Jamilar jakar ki, sannan an bawa matashin jakar Jamila.”

“Jamila…” Jakadiya Babba ta furta sunan idanunta na haskawa da tsantsar mamaki da kuma hanΖ™oron dake kama zuciyarta a lokaci guda.

“Sai dai akwai wata matsala..” cewar Mai Babban daki ya na kaΙ—e saman jinin dake cike taf da randar, jinin ya shiga tartsatsi yana zuna a Ζ™asa kamar abinda ya tafasa akan wuta, kuma sanin halinsa yasa Jakadiya Babba bata yi magana ba ta rike tarin tambayoyin da suka Ι—arsu take a ranta. Zuwa can sai ya tsaya ya tsirawa jinin ido.

“Nan da awa uku su Ζ΄an uwan yarinyar zasu Ζ™ona asirin, sun shirya hakan tun jiya kuma bana hango wani abu da zai iya tsaida su.”

Farkon zancensa kawai Jakadiya Babba ta fahimta ba tare da ta bari Ζ™waΖ™walwarta ta fahimci ma’ana karshen ba, da wata irin azama ta yunΖ™ura ta miΖ™a masa baΖ™ar ledar kuΙ—in nan sannan ta miΖ™e tayi waje, Mai Babban Ι—aki ya bita da wani shu’umin murmushi yana girgiza kansa sannan yaja ledar kuΙ—insa gefe.

“Sani ina wayarka?” Jakadiya Babba ta tambaya bayan ta isa jikin motar inda Sanin ke tsaye yana jira.

“Hajiya wayata an sace jiya, daga zuwa kallon kilisa shikenan na neme ta na rasa a aljihuna.”

Saura kadan Jakadiya Babba tayi ihu jin hakan, ya zata yi da ranta kenan? So take ta kira Fulani ko wani wanda zai iya kai mata sako cewar a kira Ζ΄an uwan yarinyar nan a karΙ“e asirin kafin su kai ga aikata niyyarsu, amma itama bata zo da tata wayar ba, don tun ranar data wullar da ita bayan dawowarsu bata sake ganinta ba, gashi ita ba haddace nambar mutane take ba balle su aro wayar wani a wajen su kira, ta cije leΙ“Ι“enta ta sake cijiewa zuciyarta na tafarfarsa da wani irin hanΖ™oro kafin wani tunanin ya gifta a ranta.

“Sani nambar wa ka haddace a masarauta?”

Sani ya gigiza kansa.

“Hajiya ai kin san ni banyi karatu ba, to wallahi ko tawa nambar ban sani ba, mutanen da nake kira duk alama Ζ™anina ya saka min a jikin nambar tasu da haka nake ganewa.”

Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Shikenan sun shiga uku, watakila a yau zasu fuskanci wannan karshen da suke gudu a kullum, wannan ranar da suke ganin kamar baza ta zo ba, ranar da abubuwa suke lalacewa… Don in ba haka ba yaushe suka koma cikin garin Kiyari a kafin magariba?

Jikinta yayi sanyi hannunta ya fara rawa, taji dukkan tunaninta na sulalewa kafin da Ζ™yar tayi nasarar kamo guda Ι—aya a cikinsu.

“Sani me kake bukata yanzu a rayuwarka?”

Sautin muryarta kadlfai ya canja sanda ta Ι—ago ta faΙ—i hakan.

Sai yayi diri-diri yana kallonta alamun bai fahimci inda ta dosa ba.

“Meye burin da kake son cimma a yanzu? Me kake so a rayuwarka?”

Duk da haka sai da ya Ι—anyi tunani kafin ya Ι—ago bakinsa a washe yace.

“Nanah, ranki ya daΙ—e!”

Jakadiya Babba ta yamutse fuskarta.

“Meye kuma Nanah?”1

“Wadda nake son aura ce ranki ya dade, wallahi shekarar mu uku tare amma har yanzu na kasa haΙ—a Ζ΄an kuΙ—in da zan tunkari auren, gashi iyayenta ma sun fara Ζ™osawa da jiran nawa.”

Sai ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan tace.

“To nayi maka alΖ™awarin idan har ka maida mu Kiyari cikin awa biyu a yanzu, ni zan zame maka uwa da uba a auren nan, zan baka dukiyar da zaka auri Nanah a cikin watan nan har ma da jarin da zaka kama wata sana’ar.”

Idanun Sani direba suka zare a lokaci guda, yanayin idanunsa na shaida kamar wanda yaga mafarkinsa a zahiri ne.

“Da gaske? Da gaske kike ranki ya daΙ—e??”

Kafin ta amsa yace.

“Shiga mota mu tafi, aradun Allah ni mai maida ke Kiyari ne cikin abinda bai kai awa biyu ba. Shiga muje Hajiya.”

Bai ko jira abinda zata ce ba ya buΙ—e mazauninsa ya shige, da azama ta buΙ—e nata Ι“angaren itama ta shiga, zuciyarta na fitar da wani irin huci tun daga Ζ™asanta ruhinta, bata san abinda ya kamata ta riΖ™e a matsayin tunani ba har sanda Sanin ya juya kan motar ya cillata hanyar wannan Ζ™ungurmin dajin da suka fito ta cikinsa.

Ubangiji kan Ι“oye sanadin kowacce Ζ™addara daga sanin Ι—an adam ba don komai ba sai don rayuwar ta tafi kamar yadda ya hukunta.

Da ace daga Jakadiya Babba har Sanin sun san Ζ™addarar dake jiransu cikin awanni biyun nan, da tabbas ba’ayi wannan alkawarin ba.!

***

“Kin san su basa aiki a gida, kuma a shirye suke koyaushe, sannan in har ba kiyi musu wasa da kudi ba to da kin faΙ—a musu location they are just ready, don haka kin tabbata?”

Muryar Naja’atu ta tambaya cikin wayar da wani irin seriousness da ba’a kowane zamani a rayuwarta ake samunsa ba.

“Na tabbata…”

Salwa ta amsa da wani irin yaΖ™ini da babu ko Ι—igon kokwanto balle algus a cikinsa, idanunta a tsaye kyam tana kallon fuskarta ta cikin mudubin banΙ—akin dake gabanta.

Ta riga ta Ι—auki wata niyya da babu wani dalili ko mahalukin da take ganin zai iya canja ra’ayinta, hakan shi kaΙ—ai ne mafita a gare ta kuma zata aiwatar dashi duk da irin hatsarin da Naja’atu ta lissafo mata a farkon wayarsu.

A cikin idonta hoton yadda komai zai kasance ne ke haskawa, komai Ι—in da shi zai zama buΙ—uwar hanyar samun cikar burinta, wata Ζ™ara, wani kuka sannan wani malalar jini…

“Na tabbata Naja, ki aika musu!”

***A gefen babban titi, expressway wanda ke Ι“ullewa zuwa mabanbantan garuruwa, wata Ζ΄ar Ζ™aramar rumfa ce irin ta kara da reshunan itace a Ζ™asan inuwar wata bishiya, irin dai rumfunan da motoci ke waucewa cikin matsanancin gudun da zaka yi mamakin a yaushe suke ciniki, a cikin rumfar tebur ne mai Ι—auke da manya da Ζ™ananun kwanduna masu Ι—auke da albasa da dankalin turawa, an kasa su manya-manya gwanin ban sha’awa.+

Isah mai rumfar ya kalli abokinsa dake zaune yana cinikin dafaffiyar masara akan wata budurwa data tsallako daga cikin Ζ™auyen nasu ta kawo musu.

“Ke wai ba Ζ΄ar gidansu Habu mai kayan miya bace?”

Abokin nasa, Jamilu ya tambaya.

“A gidan nake mana amma ai kowa da shashinsa.”

Yarinyar ta amsa tana Ι—an haΙ—e rai, alamun ba za’ayi mata wayo ba.

“To ko ba komai ai Ι—anuwanki ne, ni kuma abokina ne, don haka ai kya siyar mun hudu hamsin Ι—in nan.” Cewar Jamilun yana washe baki.

Yarinyar ta sake hade rai.

“To ai wadda ta Ι—oran tallan bata ce in siyar haka ba, in zaka ban saba’in na siyar, in ba haka ba ka zube min kayana in koma.”

“Saba’in?…” Cewar Jamilun.

Isah ya juyo daga wanke dankalin da yake a cikin wata Ζ™atuwar roba yace.

“Haba wai ya kake haka ne? In baza ka bata saba’in Ι—in ba ka ajiye daya mana ka karbi uku hamsin, amma ka zaunar da yarinya tun Ι—azu sai maimaita abu Ι—aya kuke? Ko girman masarar ka kalla ai taci saba’in.”

“Ni fa kaga shi yasa bana son ciniki a rumfarka, don kana siyarwa da masu kuΙ—i kayanka gani kake kowa ma kuΙ—in ne dashi?…”

Sai ya sake juyawa wajen yarinyar.

“… Ke kin siyar sittin? In ba haka alqur’an na fasa, don ni uku ba zata ishe ni ba.”

Yarinyar ta haΙ—e rai alamun ba haka taso ba, baΖ™ar jagirar data lafta a fuskarta ta kanannaΙ—e cikin tattarewar goshin nata kafin tace.2

“Kawo.”

“Yawwa ko ke fa, yanzu ake ciniki, wallahi in muka saba ma har gida zan dinga biyo ki ina siya.” Cewar Jamilun yana dariyar shakiyanci, Isah ya sake juyowa ya kalle shi, har zai yi magana sai lokacin yayi daidai da tsayuwar wata farar mota a Ι—an gaba dasu kadan, don haka ya saki wankinsa ya Ι—auki kwanon albasa Ι—aya na dankali Ι—aya ya ruga da gudu zuwa wajen motar.

“Alhaji barka da zuwa.”

Ya faΙ—a daidai lokacin da gilashin motar ke zugewa, wani magidanci ne da matarsa da kuma yara biyu maza a gidan baya, sai dai mijin amsa waya yake bai ko kalle shi ba don haka matar ce ta amsa.

“Nawa ne kwanon dankalin?”

“Duba daya da naira Ι—ari ne Hajiya.”

“Na albasar kuma fa?”

“Dari takwas.”

Sai ta juya ta kalli mijin nata, bai ji me ta faΙ—a ba don a hankali tayi maganar, cikin wata siga da in ba wanda aka saba yiwa ba, ba zaka ji komai ba, mijin ya juyo ya kalli kwandunan dake hannun Isah na wasu Ζ΄an sakanni sannan ya gyaΙ—a kansa kafin ya juya ya cigaba da wayar.

“A zuba min kowanne kwando biyar.”

“An gama Hajiya!” Cewar Isah da azamarsa zai koma wajen rumfar, sai dai yana yin taku na farko, kafin Ζ™afarsa ta sauka akan kwaltar da taku na biyu wani irin abu tamkar almara ya faru, daga cikin dajin dake gefensu can bayan rumfar Isan, wata irin Ζ™ara kamar ta fashewar wani abu mai girma ta cika iska, tayi amsa amo wanda ya taho kuma tare da girgizawar da tayi karaikin ruguginta.

STORY CONTINUES BELOW

Daga Isan har masu motar, da kuma tarin jama’ar Ζ™auyen dake Ι—aya tsallaken, kowa idonsa ya kai wajen da Ζ™arar ta bayyana a lokaci guda, sannan kuma a lokaci gudan bakin kowa ya kaure da salati wanda ya zama tamkar haΙ—in baki don kafin kace kwabo Jama’a sun shiga tsallakowa musamman samari ana rugawa cikin dajin inda hayaki ya turnike alamun wuta ce ke Ζ™oΖ™arin tashi akan koma meye a wajen.

Da gudu Isah ya koma rumfarsa da babu kowa don Jamilu yayi cikin dajin shima yayin da mai masarar nan ma ta ruga ta cikin mutanen dake tsallakowa ta koma wajen Ζ΄anuwanta cike da tsoro.

“Ina zaka je Hamza? Ba dai kaima binsu zaka yi ba?” Matar nan ta fada cikin tsananin ruΙ—ani tana kallon mijinta dake Ζ™oΖ™arin kwance seatbelt din jikinsa.

“Baki gani bane? Mota ce fa take Ζ™oΖ™arin kamawa da wuta, I have to help.”

A lokaci guda sai ta ruΙ—e.

“Kalli yawan mutanen dake tafiya fa, ka kyale su kawai mu bar wajen nan dan Allah, zasu iya komai ba sai da kai ba.”

Bai ko saurareta ba ya damΖ™i hannun motar ya fice tare da rufo Ζ™ofar da Ζ™arfi, wani abu da ya sake tsorata Ι—an Ζ™aramin Ι—ansu dake cikin a baya, ya kwallara kukan da ya sake hargitsa matar, ba shiri ta juya ta kwanto shi cikin belt Ι—in ta rungume yayin da hayaniyar mutanen dake durfafowa suna wuce su zuwa cikin dajin ke Ζ™aruwa.

A lokacin hayaki har ya karaso inda suke ya fara turnike cikin motar don haka ta miΖ™a hannu da sauri ta zuge glass Ι—in bangaren nata data bude,sannan daga ita har babban Ι—an nata dake baya suka bi hanyar da kallo, inda ba’a ganin komai sai turnikin baΖ™in hayaki da kuma yawan mutanen dake shigewa cikinsa, basa ko tsoron koma meye zai iya fashewa tare dasu, zuciyarta na faman bugawa tamkar zata ratso Ζ™irjinta ta fito, fata kawai take taga mijinta ya dawo sun juya sun bar wajen.

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un…”

Wannan kalmar ita ke tashi a bakin mafi yawancin mutanen dake turuwa a wajen yayin da idonsu ke kokarin gane musu lotsatstsiyar motar da ta daki wata Ζ™atuwar bishiya tana faman fidda hayaki kotaina.

“Zata iya kamawa da wuta. Ayi Ζ™oΖ™arin fito da mutanen dake ciki.”

Muryar Hamza ta faΙ—a a cikin hargitsin mutanen dake ta Ζ™oΖ™arin ganim me zasu yi.

“Kai Jamilu ku samo mana ruwa… A kawo ruwa!”

Cewar wani dattijo yana nuni da wasu matasa.

“Akwai bokitai a gonar su Halliru..”

“A kawo ruwa… Fetur ne ke zuba ta nan..”

“Tankin ya fashe…”

“Bana jin da mutane da yawa a ciki…”

“Ga jini yana zuba anan Ι“angaren…”

“Innalillahi wa’inna ilahir raji’un… Ζ™afa ce kamar ta mace anan Ι“arin.”

“Kar wanda ya taΙ“a komai sai an kawo ruwan…”

Muryar Hamza ta Ι—aga a cikin hayaniyar.

Hayakin ya cigaba da fita, cikin turnuΖ™owa baΖ™iΖ™ Ζ™irin, yayin da mutane da kuma hayaniya ke Ζ™ara cushewa a wajen, a lokacin ne kuma wasu samari bakwai suka karaso da manyan bokitan Ζ™arfe dana fenti, aka shiga kwarawa akan motar yayin da wasu ma suka sake Ζ™arasowa daga tsallake da wasu, sai da aka juye kusan bokiti ashirin sannan hayakin ya fara raguwa aka fara gane komai, sai dai komai Ι—in bai zo da sauΖ™i ba don motar da baya ta bugi bishiyar don haka gidan baya gabadaya ya mokaΙ—e ya lotse, daga bangaren kofar dama kuma wadda ta Ι“ame Ι“am! Jini ne ke ta malala yayin da Ζ™afa guda daya wadda da alama ta mace ce ta Ι“ullo ta saman windon da gilashinsa ya tararratse sannan tayi baΖ™iΖ™ Ζ™irin da jini.2

STORY CONTINUES BELOW

Dole aka koma ta gaba aka shiga koΖ™arin buΙ—e kofar da sanduna da Ζ™arafa da komai, Hamza wanda yafi kowa dabara shi ya bada umarnin da aka samu aka bude Ζ™ofar. Direban na manne da lankwashashiyar kujerarsa yayin da kansa ya banΖ™are ta Ζ™asa, sannan tun daga Ζ™ugunsa har zuwa Ζ™afafunsa jini ne kawai ke zuba, kuma daga yadda aka samu aka fito dashi ko Ζ™aramin yaro zai shaida cewa da wuya in kafafunsa zasu sake aiki a duniya.

Hamza ya tsugunna ya lalubo wata jijiya a kasan wuyansa cikin kwarewar aikinsa na likita ya taΙ“a sannan ya tabbatar wa da mutanen cewa da ragowar rai a jikinsa, a lokacin wani magidanci a kauyen mai sana’ar Ι—iban itace da motarsa akori kura ya Ζ™araso wajen don haka da gudu mutane suka tallafa aka sanya SANI DIREBA a ciki.

Cikin jagorancin Hamza, aka Ι“anΙ“are kujerar da aka fitar da Isah don dauko matar da ake tunani akwai ta a baya, sai dai tun daga yadda jini ke malalowa daga kasan kujerar da aka cire kowannensu ya san al’amarin yafi wanda suka gani don kusan saman motar ma ta baya ya hade da kujerar, aka sa wani Ζ™arfe samari majiya Ζ™arfi suka banΖ™ara shi sannan kowannensu yaci karo da wanin hoto mafi muni

da babu shakka zai iya shiga cikin kundin abubuwa mafiya tashin hankali a duniyar nan.

Matar dake kwance ta dagargaje akan kujerar motar da duk ta fatattake kuma ta jiΖ™e sharkaf da jini, fuskarta ta kwankwantse har zuwa wajen kafadunta, Ζ™afarta daya ta fita ta window sannan gabakidaya gilashin baya ya tarwatse akanta, mutuwa ce da ta tabbas komai saurin da tayi wajen daukar rai, lallai ruhin ya azabtu da mafi munin azaba.3

Dattijai da yawa juyawa suka dinga yi suna bari wajen saboda tsoron bugun zuciya, sai samari kadai ke ta hayaniyar sallallami, hatta Hamza wanda babu irin mutuwar da bai gani a fagen aikinsa ba sai da zuciyarsa ta razana da ganin gawar.

Aka rasa ma ta yadda za’a fito da ita, sai komawa tsallaken Ζ™auyen akayi wajen masu katako, Hamza ya bada kudi aka sayo wani falankace sannan shida wasu samari suka shiga aka dauko ta da kyar, duk da haka wani Ι“ari na naman jikinta na manne da kujerar motar.

Wani ya karbo zani daga gidansu har guda biyu aka lulluΙ“e ta har a lokacin jini bai bar zuba ba, a bayan akori kuran nan inda wasu samari biyu ke rike da Sani aka sanya katako, mutane biyu na dafe dashi ta gaba da baya, a lokacin duhun magriba ya fara lullube gari, kuma cikin jagorancin Hamza wanda ya koma cikin tasa motar futu-futu da kurar hayaki da kuma jinin daya bata kayansa, suka luluΖ™a gari mafi kusa daga nan, KIYARI.5

*

Daidai lokacin da aka sallame sallar magriba, Aunty Zainab da Sadiya suka Ζ™arasa can karshen masarautar Kiyari, cikin wani tsohon fili inda a bayi akayi bargar sarki mai rasuwa kafin daga baya a camfa wajen da cewar dawakai na yawan mutuwa don haka sai aka canja bargar. A cikin kan Ζ™waΖ™walwar Jamila ta tuno da maganganun da suka yi a hanya kafin shigowarsu.

“Ina mamakin yadda har yanzu ko cigiya bamu ji daga wajen Fulani ba Aunty Zainab, daga gani fa asiri irin wannan ba karamin abu bane.”

“Wani abin ai sun fi karfin cigiya da baki, to me zasu ce? Suna neman asirin da suka yi niyyar cutar da Jidda ne ko kuma shi Madakin? Na tabbata akwai abinda suke shiryawa shi yasa gwara mu kawo Ζ™arshen koma meye tun kafin lokaci ya canja da wannan damar.”

Basu taho da ko Torchlight ba don haka cikin dishi-dishin hasken farin watan dake wajen, Aunty Zainab ta buΙ—e bakar ledar viva dake hannunta ta fito da asirin nan, yana nan har yanzu a cikin tasa ledar daskare da jinin dake fitar wani irin sanyi mai ratsa fata da Ι“argo da zarar mutum ya taΙ“a shi, jamila ta buΙ—e galan din kanazir din dake hannunta ta zazzaga akai yayin da Aunty Zainab ta sunkuya ta kyasta ashanar hannunta, A lokaci guda wata irin wuta ta kama mai ci tartsatsa duk da cewar jinin dake jiki kamar ruwa yake, hasken wutar ya haske fiye da rabi na filin wajen yayin da Ζ™arar tartsatsinta ke cika wajen. Babu wanda yayi magana a cikinsu, kallon wutar kawai suke kowa da irin abinda yake saΖ™awa a ransa don zuciyoyinsu babu daΙ—i sam!

STORY CONTINUES BELOW

A cikin kan Jamila tunanin halin da Ζ΄aruwarta ke ciki take kawai, wani tunani da tun bayan faruwar al’amura dashi take kwana take tashi a cikin kanta, zuciyarta ta kasa nutsuwa tun daga ranar da Madaki yazo ya tafi da Jiddan nan, ta riga ta san Ζ™iyayyar dake tsakanin Fulani da Madaki kuma ta san cewa ba lallai da wuri  ya fahimci cewa Jidda ta taka sahun Ι“arawo bane bata laifi a rayuwarsa. Kyallin wutar ya haska a idanunta a lokacin da  zuciyarta ke fatan Allah yasa Jidda ba’a cikin matsala take ba.

Abinda bata sani ba shine, fatanta ya babbanta da Ζ™addarar da Ubangiji ya halatta a wannan daren!

***

LAGOS.

“Wai Mdee sauro ka bari ya cije ta ko me?”

Mubarak ya tambaya cikin wayar da yake yi, Madaki yaja karamin tsaki kafin ya amsa.

“Ya za’ayi in sani? Ni dai kawai naga bata da lafiya ne, nake tunanin zazzaΙ“i ne…”

Daga can Ι“angaren Mubarak yayi iya Ζ™oΖ™arinsa wajen danne dariyar dake yawo a leΙ“Ι“ensa amma sai da ta fito cikin wani sauti a hankali. Hakan yasa Madaki ya dan haΙ—e girarsa a lokacin da yake zaune kan daya daga cikin kujerun waiting area wani private asibiti.

“Me ya same ka?”

Mubarak ya girgiza kai kamar yana kallonsa yayin da yasha kwanar wani round about cikin motarsa.

“Babu komai I’m just amazed that’s all, saboda baza ka san yadda na shafe rabin rayuwata ina fatan zuwan irin wannan ranar ba, gani nake kamar an buΙ—e min mafarkina ne a zahiri, it’s unbelievable wai yau ni da kai muke wata maganar da ba ta aiki ba, and above all maganar mace.”

Madaki ya cije leΙ“Ι“ensa zuciyarsa fal da takaici, Allah ya sani sai da yayi yaΖ™i da zuciyarsa kusan sau dubu kafin ya Ι—auki kiran Mubarak Ι—in, don sai a yanzu sannan ya zaΙ“i ya kira shi yaji dalilin da yasa bai shigo office ba. Kuma har ya Ι—auka bai so gaya masa inda yake ba sai da wani yaro daga can pharmacy ya Ζ™wallara Ζ™ara alamun allura ake masa sannan a dole bayan ya tambaya ya sanar dashi cewa a asibiti yake amma ba kansa ya kawo ba.

“Yanzu tana ina?” Mubarak ya Ι—in ya sake tambaya jin yayi shiru alamun ba zai ce komai ba.

“Tana ciki ta shiga ganin likitan.”

“You should have been with her… Haba mana Mdee ya zaka Ι“ata al’amarin?”

In da za’a lissafa, tabbas Madaki ya sani cewa Mubarak zai Ι—auki kaso fiye da tamanin na alhakin halin da yake jin kansa a ciki, don kalamansa zuciyarsa ke Ι—auka tana biyawa har take hangen wani abu da shi bayan ganin yiwuwarsa. Saboda tun daga daren da ya rungume yarinyar nan zuciyarsa ta Ζ™ara damalmalewa game da tunaninta, yake jin kamar akwai wani abu tattare da ita wanda Allah ya sani baya son buΙ—ewa balle ma har ya fahimce shi.  Don ya yarda cewar ko ya fahimta Ι—in baya jin zai iya karΙ“arsa a cikin rayuwarsa sai dai ma ya Ζ™ara Ι“ata al’amuransa kawai.

Shi yasa a Ι—azu da ya riΖ™a jin wani abu na yawo a kansa bayan ya janye hannunsa daga fuskarta, baiyi wata-wata ba ya dauki muΖ™u’lin motarsa ya fice daga gidan, yaji cewa watakila yana buΖ™atar wata iska daban saΙ“anin ta office da kuma ta gidan da ya saba shaΖ™a, watakila yana buΖ™atar wata tatacciyar iskar da zata kakkaΙ“e tunaninsa yayi refreshing wa sababbin abubuwa ya daina hangen abinda zai zo ya zamo masa Ζ™alubale.

Kuma bai zame ko’ina ba sai ‘Lekki Conservational area’ wajen da ya kan je a duk sanda abubuwa suka nemi cakuΙ—ewa tunaninsa, ya biya kuΙ—i ya shiga, ya sami benci kawai yayi zamansa, kusan awa guda yana shaΖ™ar sassanyan iskar bishiyun wajen nan ba tare da ya bari kowanne irin tunani ya Ι—arsu a ransa ba, yaji shi ya zama free kamar bashi da kowacce damuwa a ransa, kamar ba shine mai tulin ayyuka dake kan teburin ofishinsa ba, kamar ba shine a cikin Ζ™ullin Fulani da sharrinta ba, Free! Kamar shima daidai yake da cikar kowanne Ι—an adam mai daraja a duniya… Free! Kamar bashi da wani babban giΙ“i da ba zai taΙ“a cikewa ba har abada a rayuwarsa.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma kamar duk lokutan da yake zuwa wajen don kore damuwarsa, sai ya Ι—auko hoto guda Ι—aya wanda yake ganin duk duniya bashi da kama a wajensa ya manna a cikin idonsa… Hoton wani dattijo a lokacin da Ζ™afafunsa suka kumbura, a lokacin da yake wani irin tari wanda yake fitowa tare da fallatsowar jini…!

A wajen yayi sallar la’asar sannan ya taho, ya juyo ya dawo gida yana mai jin sauΖ™in nauyin daya fita dashi a ransa, sai dai daga lokacin da ya shiga gidan ya sake haΙ—a ido da Jidda, waΙ—annan idanun da suka canja daga yadda ya sansu, sai komai ya sake dawo masa sabo, ya fahimci cewa abubuwa sun canja a rayuwarsa kuma ba lallai ne su dawo kamar da ba. Abinda yaji yana yawo a kansa kafin fitarsa ya sake dawowa, da wani irin Ζ™arfi kamar iskar dake hurawa a sahara, ya kasa gane wai har yaushe zuciyarsa ta yarda da ita ne da zai damu haka don bata da lafiya? Daga Ζ™arshe sai kawai ya alaΖ™anta hakan da watakila don bai taΙ“a samun wani makusanci dake Ζ™arΖ™ashin kulawarsa bane, watakila don bai taΙ“a rainon wani a Ζ™arΖ™ashin sa bane.

“Wane asibiti ne?”

Muryar Mubarak ta janyo shi daga dogon tunanin da ya riga ya faΙ—a, har a lokacin da alamun murmushi a cikin muryar.

“VoilΓ‘…” Ya furta sunan a hankali yana Ζ™oΖ™arin kakkaΙ“e sauran abinda ke ransa.

“Okay, Allah ya sawwake. Amma na fara tunanin watakila lokacin da zata san mu ya kusa kenan.”

“Kamar yaya?” Madaki ya tambaya a taΖ™aice.

Sai dai kafin Mubarak Ι—in ya amsa, idonsa ya hangi Jidda ta fito daga office Ι—in likitan, a lokaci guda kuma focus Ι—insa ya janye daga komai ya koma kanta, tana sanye da Ι—aya daga cikin dogwayen rigunan daya siyo mata, pitch colour mai adon baΖ™i, ta yafa baΖ™in mayafin rigar a kanta, Ζ΄ar Ζ™aramar da ita amma ta haska wajen don idanunsa basa ganin kowa sai ita din dake tsaye da alamun tana nemansa, sai dai kamar Ι—an Ζ™aramin mayafin yayi kaΙ—an akan rigar, Me yasa bai kalle ta sosai ba kafin su fito?

“Yanzu zaka shiga kenan tunda ta fito.”

Cewar wani saurayi a gefensa yana magana da abokinsa, sai kawai ya juya ya kalle su, maganar suke amma idonsu gabaΙ—aya na kanta ne, ita suke kallo babu ko Ζ™iftawa duk da basu Ζ™ara cewa komai ba bayan hakan. A lokaci guda ya katse kiran tare da yiwa Mubarak sallama sannan ya miΖ™e tsaye, ai kuwa ta hango shi, idanunta suka shiga nasa, sunyi wani iri har yanzu, Allah yasa likitar bata ce ciwon mai yawa bane.

A Ι“angaren Mubarak, a cikin motarsa yayi dariya kawai yana Ζ™oΖ™arin shan kwanar da zata kaishi gidansa, sai kuma ya Ι—aga kansa ya kalli sama, akwai hadari wanda ke nuna cewar za’a iya yin ruwa a yau, wataΖ™ila ma har da Ζ™anΖ™ara, don gani yake kamar hakan ne kaΙ—ai zai tabbatar masa cewar da Madakin da ya sani yayi wayar ba wani daban ba. Ya cigaba da tuΖ™insa ba tare ya damu da yiwa Salwa dake zaune a gefen kujeararsa bayanin komai ba, dawowarsu kenan daga fafutukar nema mata admission Ι—in da suka fita tun bayan dawowarsa daga aiki.

Sau da yawa sanadin Ζ™addara kan fara ne da wasu Ζ΄an Ζ™ananan abubuwan da wucewar sakanni kawai zata iya jirkita su, sai dai ubangiji bai hallicci rashin sani a banza ba sai don kowacce Ζ™addara ta wanzu kamar yadda aka tsara mata.

Da ace idanun Mubarak sun ankara da abinda Salwa ke rubutawa cikin wayarta a wannan lokacin, da tabbas wasu abubuwan basu faru ba!

‘Ba zan iya jira sai gobe ba Naja, I need d operation NOW! basa gida, Voila Hospital, near Gyari Park, suna can… Naja bana son a canja komai ki gaya musu kawai, ki sake tura musu hotonsa, duk yarinyar da suka ganshi tare da ita ITACE!’

**

“YallaΙ“ai test ne na Malaria za’ayi mata.”

Cewar wata ma’aikaciya dake tsaye a cikin lab Ι—in tana kallon Madaki, Fuskarta Ι—auke da Ι—an murmushi, don tun shigowarsu daga ita har sauran ma’aikatan wajen da mafi yawancinsu mata ne suka juyo da attention Ι—insu kansa, kowacce a cikinsu kallonsa kawai take yi tana dan fakaicewa da aikinta, wani abu da in da sabo Madaki ya saba dashi, shi yasa a koyaushe bai fiye son zuwa wajen da zai tadda mata ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Okay anan za’ayi?”

Muryarsa ta tambaya cikin amon da ko baka kalle shi ba, zaka shaida wani irin class da kasaitar da take Ι—auke dashi. Zuciyar ma’aikaciyar nan ta shiga narkewa kafin ta lalubo tata muryar da kyar tace.

“Eh, amma za’a biya kuΙ—in ne a… a office na gaba kadan… Zan iya zuwa ma in biya sai ayi matan kawai….”

Ta Ζ™arasa tana Ζ™ara Ζ™awata fuskarta da murmushi haΙ—e da Ζ™ifta idanu.

Sai kawai Madaki ya miΖ™a hannunsa ya zare takardar daga cikin nata hannun sannan yace.

“Kar ki damu, zanje in biya.”

Sannan ya juya bayansa inda Jidda ke tsaye kamar zata manne da jikinsa, tunda yace da ita Lab zasu je take binsa Ζ™afa da kafa kamar mai jin tsoron wani abu, bata dai ce komai ba amma shi ya hango abinda yake tukani tsoron ne a idanunta wanda hakan ba Ζ™aramin mamaki ya bashi ba, yarinyar is so complicated! Har yanzu ya kasa gane al’amarinta! Don a ganinsa kamar ita da zata iya shake Ζ™atuwar inyamura a Guest Inn Ι—in nan tana mata kashedi me yasa zata ji tsoron wani abu ‘Allura’.

“Ki zauna bari in dawo.”

Ya faΙ—a kuma ba tare da ya jira abinda zata ce ba yayi gaba ya fita daga lab din.

Jidda tabi shi da kallo, tsoronta daya kar ace allura za’ayi mata babu gaira ba dalili, don ita a yanzu jinta take garau, fitowar da duka yi taga titi da mutane kowa nata harkokinsa ta kore wannan nauyi da damuwar dake cikin zuciyarta, har taji ma gwara da Allah yasa ta yarda ta biyo shi Ι—in a lokacin da ya dawo bayan la’asar ya lalubo ta a Ι—aki tana jinyar zuciyarta yace ta shirya asibiti zasu je.

“Kinga, nace wannan yayanki ne?”

Muryar ma’aikaciyar nan ta tambaya daga gefenta, sai ta juyo ta kalle ta, murmushi take har yanzu tana fara’ar da bata ga ma’anarta ba, daga bayanta sauran ma’aikatan sun zubo mata ido alamun suma amsarta suke jira, wani irin abu ya turniΖ™e zuciyarya a take, idan wanta ne me za’ayi? Zasu karbi nambarsa ne dukkaninsu su kai kansu gare shi ko me? Sai ta gyara tsayuwarta sannan ta girgiza kanta tace.

“A’a Babana ne.”9

“Babanki?” Cewar wata daga baya cikin tsananin mamaki irin wanda ke haskawa a fuskar sauran.

“Amma kamar bai haife ki ba, shekarun ki nawa ke?”

“Shekara goma ya bani.”4

“Kamar yaya? Yana shekara goma ya haife ki?” Ta farkon ta sake tambaya.

Kafin ta bada amsa sai wata da ta Ι—an mnyanta a baya tace.

“Ke kar ki mana rashin kunya fa, babu sa’anki anan.”

Jidda bata ko ji Ι—ar a ranta ba tana hangenta tace.

“Babu zancen rashin kunya anan, in ma akwai, to kuwa babban ne ya yar da girmansa har yaro ya sami damar takawa. Daga kun tambaye ni na baku amsa sai ki kira hakan rashin kunya?”

So take su cigaba da tanka mata, in yaso ko fadan ne ayi, watakil’a ma ta samu ta zazzage abinda take ji a ranta, amma shigowar Madaki ta katse komai, don takunsa kaΙ—ai taji daga bayanta ta gane shine tun kafin sauran ma’aikatan su ankara, don haka ta juya da sauri sanda ya Ζ™araso gabanta.

Sai da ya miΖ™awa Nurse Ι—in nan takardun hannunsa kafin ya kalle ta, a hankali cikin wannan tattausar muryar tasa yace.

“Test za’a miki na jini, may be Malaria ke damunki.”

Idanunta yake kallo, yana son tabbatar da zarginsa na Ι—azu cewar tsoron allurar take, kuma bayi wani nazari ba maganarta ta tabbatar masa da hakan.

“Wallahi fa na warke, babu abunda ya same ni, na gaya maka bana jin dadi ne kawai kuma ya daina.”

Tsakaninta da Allah tayi maganar alamun da gaske bata son a huda jikin nata, amma yanayin yadda muryarta ke fita yaji shi ne kamar wani maganaΙ—isu a cikin kansa, don tun a lokacin da yake tsaka da zarginta yake jin kamar akwai wani abu daban a  muryar tata balle kuma a yanzu da zuciyar tasa ke tsere wajen kokwanton abubuwa da yawa game da ita.

STORY CONTINUES BELOW

Sai kawai ya kamo hannunta Ι—aya, ya shiga nannaΙ—e dogon hannun rigar, Abinda ya kashe bakin Jidda kenan, taji dukkan maganar dake bakinta ta dunΖ™ule waje guda, dukkan wani tunani mai kyau a ranta ya wargaje tare da bugun zuciyarta, sannan wani abu kamar kasala ya saukar mata yana wucewa har cikin yatsunta, Me yasa ne Ubangiji ya bashi wannan tasirin akanta?

Tuno inda suke da amsar data gama gayawa ma’aikatan yasa tayi Ζ™oΖ™arin janye hannunta amma sai yasa Ι—aya nasa ya damΖ™e shi a hankali.

“Na gaya miki its my time to look after you… sanda kika bani magani nace ba zan sha ba?”

Yayi amfani da wani irin sauti ne wajen yin maganar yadda ita kadai zata ji, fuskarsa dab da tata, kuma ta tabbata yana iya jin Ι—umin numfashinta dake fita a tsorace wanda ya haΙ—e wuri Ι—aya da nasa, amma duk da haka tsoron shigar allurar nan bai bar Ζ™asan ranta ba don wani abu ne da bata san yaushe rabonta dashi ba.

Madaki na sane da abinda yake yi kuma bai manta cewar da idanun ma’aikatan na kansu ba don haka sai da ya Ζ™arasa naΙ—e hannun rigar har saman gwiwarta kuma ya tabbatar baza tace komai ba sannan ya juyo ya kalli ma’aikaciyar nan wadda ta shirya tsaye da allurar da kuma wata siririyar roba a hannuta.

Fuskarta a haΙ—e ba kamar Ι—azu ba ta Ζ™araso jawo hannun Jiddan ta fara Ζ™oΖ™arin Ι—aura robar, hakan yasa Jidda ta juyar da kanta Ι—aya gefen ba tare da tace komai Ι—in ba amma sai hannunta Ι—aya ya fara rawa a gefe, wanda hakan baiyi nisa ba taji Madaki yasa Ι—aya hannunsa ya riΖ™o shi cikin yatsunsa, wani abu da ya sanya duk dauriyarta sai da taja numfashi a hankali cikin Ζ™irjinta. Madaki yaji hakan kamar yadda yaji a Ι—azu ma da ya riΖ™e fuskarta, me take ji ne idan ya rike ta? Zai so ace ya samu wannan amsar don shi baya iya fassara abinda yake ji Ι—in, sai dai kawai ya nutse cikin tunaninsa da zarar ya janye daga gare ta.

“Sai ta dunΖ™ule hannunta tukunna.” Cewar Matar tana kallonsu.

Sai kawai ya sake sa Ι—aya hannunsa ya kamo natan da aka Ι—aura robar, ya naΙ—e yatsunta sannan ya dunΖ™ule su cikin tafinsa.

“Yayi?”

Ta gyaΙ—a kanta ba tare da tace komai ba, a cikin ranta tana hango yadda zasu shafe satin a Lab Ι—in nan suna hirar wannan rashin ta idon dake faruwa a gabansu, don ko Ζ™ananan yara ai ba’a?usu wannan lallabawar, don sauran abokan aikin nata ma kallonsu suke da mamakin dake fallasawa a idanunsu yayin da wasu ke dariya kasa-kasa, wasu kuma zuciya fal da haushin da basu san dalilinsa ba.2

Allurar na shiga jikinta Madaki yaji sanda ta sake jan wani numfashin haΙ—e da Ι—age Ζ™afafunta sama alamun zafin daya ratsa kanta, aka fara zuΖ™ar jinin kuma har a lokacin bata bar juya kanta kowanne Ι“angare ba, sai yaji wani abu kamar tausayinta ya shiga ratsa zuciyarsa, ya tursasata akan abinda bata so kuma bata yi masa musu ba, sai kawai ya lulubi saitin kunnenta guda Ι—aya ya shiga raΙ—a mata harafan ‘Shshshshsh….’ da fatan hakan ya Ι—an Ι—auke hankalinta daga kan zafin.

Ba shiri Jidda ta dunΖ™ule yatsun kafarta sakamakon yadda siririyar iskar bakin nasa ke shiga cikin kunnenta, numfashinta ya dauke sannan ya dawo a lokaci guda, taji ta manta ma da zafin allurar, abinda ta sani kawai shine duk jinin da ake Ι—iba a lokacin to tabbas yafi ruwan zafi tafasa don Ζ™arfin abinda ke shigarta tana jinsa ne kamar Ζ™arfin wutar transformer ba ma na wutar lantarki ba.2

So take tace ya daina kamar na Ι—azu, ta gaya masa cewa wannan abin da yake yi shine ciwonta ba wani abun daban ba, amma bugun zuciyarta da ya cika kunnenta, ya hana ta ko motsin kirki balle har ta iya furta wata magana.

“An gama.”

Bayan wani lokaci, muryar ma’aikaciyar tayi nasarar jawo hankalin dukkaninsu ba tare da sun lura cewar ta cire allurar har ta matsa ba, kallonsu kawai take tana tunani a ranta cewar abinda ya rage kawai shine su siyo kayan decoration su kafe harafan ‘Booked for Honeymoon’ a Ζ™ofar Lab Ι—in koma asibitin baki daya don gani take abinda ya rage daga hakan kaΙ—an ne.2

STORY CONTINUES BELOW

Wannan tunaninta ne kawai, wani hasashe da zuciyarta tayi cikin Ι—an guntun kishin da take ji a Ζ™asan ranta, sai dai abinda bata sani ba shine, wasu Ζ™addarorin na faruwa ne kamar yadda bawa ya hango su.

Kusan minti talatin sannan result din test Ι—in ya samu, wanda kafin nan Madaki yaje yayi sallar magriba kuma ya amsa waya fiye goma ta ma’aikatansa da sai a yanzu daya kunna Ι—aya wayarsa suke ta jajensa. Jidda na zaune da wajen waiting area tana kurban Ζ™atan yoghurt din daya sa wani mai shara a wajen ya siyo mata, kallonsa kawai take yi daga can wata Ζ΄ar baranda da ya fita yana wayar a cikin kanta tana mamakin tsananin riΖ™on aiki irin nasa, a tunaninta Ι—azu da ya fita office din yaje ya dawo amma kuma duk da haka ace a yanzu ma ayyuka basu Ζ™are ba?

Sai kuma ta Ι—auke kanta ga barin kallonsa sannan ta murza duka tafukan hannayenta a jikin robar yoghurt din, sanyin dake jiki ya ratsa fatarta amma duk da haka bai kore Ι—umin hannayensa da take ji har yanzu ba, wani Ι—umi mai kama da zafi da kuma zugi dake harbawa har cikin kanta, Gani take kamar abinda ya faru a Lab din nan bai faru ba, don shi gashi ya manta ma ya shiga harkokinsa.

Ta sunkuyar da kanta a hankali tana tunanin idan ma wani abu yake shiryawa akanta da wannan hanyar daya Ι“ullo da ita, to tabbas tana hango masa nasara, don Allah ya sani a yanzu bata tsarawa kanta wata mafita, daga ya rike ta ba abinda tunaninta ke iya taΙ“ukawa sai yadda Ζ™waΖ™walwarta ke juyawa da tasirin hakan.

Bai Ζ™ara ce mata komai ba har suka karΙ“i result Ι—in suka Ζ™ara komawa wajen likitan, wannan karon ya bita ciki kamar yadda suka je Lab Ι—in tare, likitar tace babu wani Ζ™wakwaΖ™waran abu dake damunta, malaria ce kawai Ζ΄ar Ζ™adan da bata yi wani tasiri ba, saboda haka ta rubuta mata Ζ΄an magunguna kawai suka fito.

Ran Jidda fes da tunanin watakila zai rufa mata asiri yanzu ya daina damun kansa da taΙ“a ta rayuwar ta dawo kamar yadda suka faro ta a farko, yadda duk ranar da ya gama bincikensa akanta zai iya sallamarta ta koma gida.

Tunani ne kaΙ—ai hakan amma sai taji jijinta ya Ι—anyi sanyi, me ya same ta ne? Yaushe ta fara tunanin cewa baza a wayi gari ranar da zai kore ta ba? Don kawai ya riΖ™e fuskarta a dazu ko don ya riΖ™e hannunta yanzu an mata allura? Saboda  baza a ma lissafa da lokacin da ya rungume ta ba, wani abu ne da yayi ba’a hayyacinsa ba kuma ta tabbata bayan ya farka yayi dana sanin hakan.

To me yasa zuciyarta zata fara tunanin wani abu don tace zai kore ta? Watakila saboda kitchen Ι—in nan ne, ta bawa kanta amsa kuma babu wani musu ta yarda da hakan, tabbas zata yi kewar kitchen Ι—in nan ne sosai!

A daidai lokacin Madaki ya fito daga wajen siyan magungunan da ya shiga, da hannu yayi mata alama da ta taho don haka ta miΖ™e tare da robar yoghurt Ι—inta da bata shanye ba tabi bayansa, suka nufi hanyar fita daga ginin asibitin kowa da irin abinda yake tunani a ransa, sai dai duk yadda tunanin kowannensu ya kai ga yin zurfi, babu wanda ya hango faruwar Ζ™addarar dake jiransu a wannan daren balle har su Ζ™iyasta lokacinta.

**

Ginin asibitin hawa uku ne, kuma duk da nisan dake tsakanin sama da Ζ™asan, yana iya hango fuskar mutane dake zirga-zirga a harabar wajen tar cikin wani Ι—an rami na kwarmin zungureriyar’ bindigarsa, wadda ya saita ta ta tsaya tsaf hancinta na fuskantar wajen ajiyar motaoci na asibitin.

Wani gabjejen Ζ™ato mai irin siffarsa ta irin tantiran garin na Lagos ya zaro wani evelope cikin aljihun bakar rigar sanyin da  yake sanye da ita, ya yage samansa sannan ya fito da hoton ciki ya miΖ™a masa, ya Ζ™arΙ“a ba tare da ya janye idonsa daga cikin ramin bindigar ba sannan ya haska shi a gaban idonsa, fuskar matshin dake jiki ta baiyana cikin wani annuri wanda ya inganta kwarjininsa, yana sanye da coat Ι—in da ko a ido zaka Ζ™iyasta kuΙ—inta da dubunnai.

Sakan Ι—aya, biyu, uku, yana kallon hoton kafin ya janye shi Ζ™asa, kuma cikin wata irin Ζ™addararriyar sa’a sai idonsa ya hangi mai irin fuskar sak! Wannan karon sanye da kayan hausawa da ake kira da jamfa, saboda haka yayi saurin karkata kan bindigarsa zuwa gefe, biye dashi kuwa wata mace ce da babu shakka itace dalilin zuwansu wajen, ya cigaba da bin takunta a hankali ta cikin kwarmin bindigar yana Ζ™oΖ™arin saita aikinsa.

“Umbuwoni yan. (Na ganta.)”

Ya faΙ—a a hankali cikin yarensu yana gayawa na gefensa, sai kuma ya juya zuwa turanci yace.

“An innocent girl walking respectful steps behind the guy.”

Dukkaninsu suka yi dariyar shakiyanci kafin na tsayen yayi alamar bindiga da hannunsa sannan ya Ι—auke ta a iska tare da fadin ‘Bam!’

Mai bindigar ya sake yin dariya sannan ya cigaba da auna saitinsa yana murΙ—a abubuwa a jikin zungureriyar bindigar, ya gama tsara komai a lokacin da suka isa wajen motar su, a lokacin da yarinyar ke Ζ™oΖ™arin bude Ζ™ofar motar data cije, Ι—an mitsitsin jan hasken bindigar tssa ya sauka a saitin zuciyarta ta baya, saboda haka ya Ι—ora hannusa akan hannun bindigar cikin saitin da bai taba kuskurewa ba a rayuwarsa.

Kuma komai ya faru ne a lokacin da ya saki hannun bindigar, a lokacin da harsashin ciki ya fito cikin tsananin gudu zuwa inda aka aike shi…. A lokacin da wannan matashin ya shigo cikin hoton da yake hangowa ta cikin ramin bindigar alamun yazo ne ya buΙ—e Ζ™ofar motar da yarinyar ta kasa buΙ—ewa….26

***

Ehem ehem ehem….

Me kuke tunanin yana shirin faruwa ne??

Post a Comment for "ZANEN DUTSE CHAPTER 3 BY AISHA-SHAFIEE"