ABDUL-MALEEK BOOK1 CHAPTER 2

Bayan sun koma mazauninsu akace su yanka cake. Mik'ewa sukayi suka k'arasa inda aka ajiye cake d'in mai hawa uku, Wanda tasha ado mai k'yau, Rah
ABDUL-MALEEK BOOK1 CHAPTER 2
Bayan sun koma mazauninsu akace su yanka cake.    Mik'ewa sukayi suka k'arasa inda aka ajiye cake d'in mai hawa uku, Wanda tasha ado mai k'yau, Rahma aka umarta tafara d'ora hannunta akan wuk'ar, sannan Bobo yad'ora nasa hannun akan na Rahma, bayan k'irga uku suka yanka, tafi akayi Raf raf raf.    Akace Rahma taciyar da Bobo, kunya dukta isheta amma yazatayine, haka taciro daidai bakinsa ta rissina tasaka masa abaki idonta ak'asa, aka kuma sakin tafi, tasaka masa kofin lemo abaki, kur6a biyu yayi tajanye tasaka hanky tagoge masa bakin, ihu aka saka ana bata tafi.   Itadai kanta nak'asa tayi d'an murmushi, bobo madai murmushi yakeyi.    Shima akace yabata.   K'aramin shima yaciro, yamatsa daf da ita sosai tamkar zai shige jikinta, batayi auneba taji yasak'alo hannunsa ak'ugunta, ajiyar zuciya ta sauke ahankali.   Cake d'in yasaka mata abaki, tafi mai k'arfi aka bashi, fuskarsa d'auke da murmushi yasaka mata cup d'in l…