Noor-Al-Hayat Hausa Novel

Muryar dattijuwar macen da baxata haura shekaru hamsin a duniya ba ne ya cika dakin, hankali tashe take jijjiga matashin saurayin da shekarunsa ashiri
Noor-Al-Hayat Hausa Novel
✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻 *All thanks to Allah S.W.T for giving me the chance and privilege to start this book* 1..... Muryar dattijuwar macen da baxata haura shekaru hamsin a duniya ba ne ya cika dakin, hankali tashe take jijjiga matashin saurayin da shekarunsa ashirin da takwas, kwance yake kan makeken gadon dakin, ta dinga cewa "Are you okay son, open ur eyes, Aliyuuuu ka bude idonka, What's ur problem..... Wani irin mafarki ne wannan ni fatima" sai a snn ya bude idanuwansa a firgice ya mike xaune yana bin dakin da kallo kirjinsa na heaving, lkci daya ya mayar da kallonsa kan mahaifiyarsa dake kallonsa ta ma kasa cewa komai, ya runtse ido cikin sanyin murya yace "Motherrr...." ta kamo hannunsa damuwa karara fuskarta tace "What's ur problem Aliyu? Meye matsalar ka ka gaya min, are you sick?" ya buda idanuwansa yana kallonta murya can kasa yace "Ki taya ni addu'a mum... I don't knw, I just can't have rest of mind…